Thursday, 1 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 35,36,37

[5/19, 2:48 PM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_


*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


     _Thanks to my masoya masu yimin fatan samun lafiya, nagode muku sosai especially masu kirana awaya da masu turo min text da duk wani wanda yadamu dani acikin mind dinsa...one love_


   *_35_*

aishaummi.blogspot.com


  ~~~Ita dai maryama shiru tayi tana sauraren bak'ak'en maganganun da shaddad ke faman fada mata, masu video da camera kuwa sai aikin haskasu suke domin ba karamin kyau suka yiba,

"And last abinda zan fada miki shine babu zuwa club agidana, babu zuwa stadium sannan babu zuwa aiki, mutukar kina son auren mu yaci gaba da numfashi to sai kinbar wannan aikin da kike yi saboda nariga da nadade da sanin duk doctors din wurin abokan mu'amularki ne more especially ma wannan karamin yaron da kike bibiya wanda baifi sa'an kaninki ba amma tsabar jaraba irin taki binshi kike.."

Maryama ji tayi kamar zata fashe da kuka saboda tsabar bakin ciki domin har idanuwanta sun fara kokarin kawo ruwa, sai dai kuma ta dade da yiwa kanta alkawarin cewa  shaddad bazai taba ganin kukanta ba wannan dalilin ne yasata yin gaggawar hadiye kukan bawai dan zuciyarta ta daina kuna ba a'a kawai bata son yagano lagonta ne domin tasan muddin shaddad yagane tana jin dacin maganganun da yake fada mata to zai cigaba da fada mata sune har illa masha Allah,

Watsi tayi da al'amuransa ta mayar da hankalinta kan program din da aka fara gudanarwa,

Anty karama ce ta bude taro da addu'a sannan aka bayar da tarihin ango da amarya a gurguje, daga nan kuma aka fara chashewa, ganin su anty maijidda sun fita suna rawa yasa maryama kokarin tashi domin tana son taje tayi musu lik'i, amma kuma bazata iya tashi ba domin shaddad ya matseta sosai,

"Zan tashi.."

"Na rikeki ne..?" Ya fada yana dauke kanshi zuwa wani wuri, kokarin tashi tafara ta samu ta tashi dakyar ta nufi filin rawar tana tafiya ahankali saboda tsinin takalminta,

Liki tafara yi nan da nan wuri ya kancame, tana liki ana yi mata, shaddad yana daga can zaune yana kallonsu, tashin shima yayi ya sauko ya nufi wurinsu,

Rafar kudi ya ciro daga aljihunsa yafara zubawa jama'ar dake cikin filin, yana tsaye a bayan maryama sai kudi yake zuba mata, amma ita bata saniba saboda yanda taga yana jin kai bata zaci zai fito yayi liki ba, daga ita har shi atsaye suke cak babu wanda yake yin rawa sai liki kawai suke yi,

Kasancewar bata son hayaniya yasa taji kanta yafara juyawa, hakanne ma yasata niyyar fita daga filin, tana juyawa taci tuntube da kafarshi nan tatafi zata fadi, cikin sauri ya tareta ta fada jikinsa,

"Ka riketa ku koma sama.." Anty babba tace da shaddad da karfi tana ta faman tikar rawa,

Riketa yayi kamar yanda yayi mata lokacin da zasu shigo cikin hall din, har kan kujerar da suke zaune ya maida ta ya zaunar sannan shima ya koma ya zauna,

Dafe goshinta tayi saboda ciwon da kanta ke yimata, ita dai kawai tana zaune ne awurin amma bawai dadin zaman takeji ba,gashi duk ta takura ko yaya tayi motsi jin jikinta take acikin na shaddad,

Bayan angama cashewa ne aka kira amarya da ango domin yanka cake, tashi suka yi suka sauka zuwa inda cake din yake suka yanka ya dauka ya bata a baki itama ta dauka ta bashi bayan ta dan rissina,

Fuskarshi babu yabo babu fallasa yake gudanar da komai, haka taron yaci ya watse,

Karfe 10:30 aka gama dinner din aka fito domin tafiya,yana rikeda ita ajikinsa har wurin motar da takawosu,har zata shiga anty babba tazo tace,

"Ba a wannan motar zata koma ba, kar ta shiga tazo tare da ita zamu tafi, kai kaje kawai.."

Sakin baki yayi yana yiwa anty babba kallon mamaki ganin yanda taketa kaffa kaffa da maryama, murmushi yayi yace,

"To shikenan anty sai mun hadu agida"

Saboda yasan dalilin da yasa anty ta hanashi tafiya tareda maryaman tunani take ko zai yimata wani abu bayan itace bata saniba amma shi babu wannan acikin tsarinsa,

Gaban motar ya shiga sulaiman yaja suka tafi,

"Wallahi Navy kayi sa'ar mata, matarka masha Allah kyakkyawa babu wanda zai ganta yazaci tayi wadannan shekarun.."

Shiru shaddad yayi bai tankawa sulaiman ba saboda yasan shi sulaiman din bai san wacece maryama ba shiyasa amma shi dayake yasan wacece maryama sam kyawunta baya rudarsa.

  Abangaren maryama kuwa da ciwon kai takoma gida saboda hayaniyar wurin dinner dinnan,

Suna zuwa gida khairat ta zuba mata ruwan wanka acikin dakin hajiya, ganin babu kowa acikin dakin yasa maryama zuwa ta shiga wankan, lokacin data fito khairat na zaune da food flask agabanta tana jiran fitowarta,

"Adda maryama wai me yaya navy yake fada miki lokacin da ya rikeki acikin mota ya hanaki fitowa, nasan koma dai menene ba abu mai dadi yake fada miki ba.."

"Ba wani abu bane khairat, wai sarkar da nasa akafata yace sai nacire saboda kar mutane suyi min mummunar fahimta, nikuwa banga laifin sarka akafa ba saboda wasu kwalliya ce kawai kesasu sakawa bawai wani abuba.."

"Hakane adda maryam, ai naga kun dade ne baku fito ba shiyasa"

Murmushi maryama tayi ta zauna agefen gado tafara shafa mai marar maiko sama sama....




*_Ummi Shatu_*
[5/19, 2:48 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


   *_36_*



  ~~~Dak'yar maryama ta iya tsakurar abincin da khairat ta kawo mata taci ta nemi wuri ta kwanta, tun daga wannan lokaci bata sake ganin shaddad ba, hajiyarshi kuwa sai nan nan take da ita cikin so da kauna domin tana tsananin son maryama,

Kwanansu biyu suka shirya aka yiwa hajiya sallama suka tafi Lagos, gidan Dada aka fara kai maryama nan suka kule a daki Dada yana yimata nasiha akan tayi kokari tayiwa mijinta biyayya sannan ta kasance mai rike sirrinta,

Kuka maryama tasha shi kamar ranta zai fita, dakyar anty maijidda ta samu ta banbareta daga jikin dada, shi kanshi dadan shima saida ya goge kwalla saboda rabuwar da zaiyi da tilon yar tashi,

Kai tsaye gidanta aka wuce da ita dama shi shaddad ya rigasu tahowa shida su anty Zainab wadanda suka yi jere suka shirya gidan wasu kayanma basu gama shiryasu ba sai gobe,

"Wallahi ban so zamu kwana agidan nan ba naso mubawa yaran nan wuri su sakata su wala suci amarcinsu" anty babba tafada tana kokarin zama agefen gadon maryama saboda bazai yiyu su tafi yanzu ba dole sai dai su kwana tunda dare yayi,

"Babu komai ai iya yaune kadai gobe iyanzu mun dade da bar musu gidansu"

Anty maijidda tabata amsa, ita dai maryama tana kwance tana jinsu amma har ga Allah har tafara jin tsoron tafiyarsu domin tasan zama zatayi irin zaman k'unci kamar yadda shaddad yayi mata albishir,

Dayake agajiye take babu bata lokaci bacci ya dauketa tabar su anty maijidda sunata faman hayaniyarsu suna hira ba ita ta tashiba sai da gari yawaye,

Wanka tayi ta shirya cikin wata dakakkiyar shadda light pink dinkin riga da skirt ne,daga rigar har skirt din sunyi mutukar amsar jikinta, lokacin da ta fito tasamu har su anty maijidda sun gyara mata gidan sun shirya sauran kayan da suka rage ba ajera ba sannan sun turare gidan da turaren wuta mai kamshin gaske ga abinci nan kuma fal cikin kuloli wanda Dada yayi order aka kawo musu daga wani hotel,

Ruwan tea kawai maryama ta iya sha daga nan bata kara iya cin komai ba har saida anty maijidda ta zo ta tisata agaba sannan ta danci faten doya dan kadan,

12 narana nayi su anty maijidda suka fara shirin tafiya ai nan da nan maryama idonta ya kada yayi jajur kafin wani lokaci har tafara kuka, ita kanta anty maijidda itama kukan take ita dasu khairat babu mai rarrashin wani ahaka suka kammala shiryawa suka tafi suka barta ita kadai sai faman kuka take, gashi wani abin karin bacin ranma unguwar barikice babu mai shigar mata,haka tayi kukanta tagama babu mai rarrashinta, mikewa tayi ta kwanta akan doguwar kujera saboda ciwon da kanta yake mata daga nan bacci ya kwasheta ba ita ta tashiba sai da misalin karfe 2 saura yan mintuna,

Bedroom dinta ta shiga tayi salla ta sake yin wanka ta shirya cikin doguwar riga ta material kalarsa purple, ta fito, dakin dake kusa da ita ta leka wanda su anty babba suka kwana aciki nan ta ganshi shima ashirye da kaya kamar nata sai dai kawai kalar kayan sun banbanta,nan tayita bin ko ina nagidan da kallo domin ba karamin kudi Dada ya kashe mata ba wurin zuba mata furnitures hadaddu,

Daya bedroom din dake can gefe daya tanufa domin dama three bedrooms ne acikin gidan, ahankali ta bude ta shiga daga ganin tsarin dakin tasan shine na shaddad saboda ga kayanshi nan aciki sannan ga uniform dinshi nan shima akan gado, karasawa tayi ta debi uniform din ta ninkesu tasaka cikin drewar ta fita,

Falo ta koma shiru ta zauna, daga karshe ta tashi ta hada kayan kallo ta kunna ta kamo tashar mbc action nan taji dadi saboda suna nuna wani american film true blood a lokacin,

Tana kwance tana kallon taji an bude kofa anshigo, kanta ta daga ta leka, shaddad tagani ya shigo yana sanye da kananan kaya,

"Sannu da zuwa.."

Tafada tareda kokarin tashi zaune saboda ita rabon da ta ganshi tun ranar dinner dinsu,

"Yawwa" shine kawai abinda yace ya wuce cikin dakinshi,

Kitchen ta shiga ta zubo masa abinci ta kai kan table ta ajiye tana jiran fitowarsa amma shiru shiru bai fitoba ganin haka yasata tashi tabishi cikin dakin, kwance ta ganshi yana bacci dan haka ta juya takoma falo taci gaba da zama,

Har karfe hudu tayi shaddad bai fitoba, tana zaune a falo akan sallaya bayan ta idar da salla sai gashi ya fito, ganin zai fice yasata dakatar dashi,

"Navy ga abincinka nan akan table.."

"Kidaina raba abincinki da ni saboda baci zanyi ba"

Wannan shine kawai amsar da ya bata yasaka kai ya fice, da kallo tabishi har yafice,

Tagumi ta rafka tafara tunanin irin zaman da zasuyi dashi....




*_Ummi Shatu_*
[5/19, 2:48 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



   _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


    *_37_*


~~~Zaman kad'aici maryama taci gaba dayi har dare yayi, nan kuma taji zaman yafara damunta,daki takoma tayi wanka tayi shirin bacci cikin wata hadaddiyar doguwar rigar bacci ash colour, kwanciya tayi tana jin shaddad ya dawo, a falo ya yada zango ya kunna kallo,

Ahankali ta lab'ab'a ta lek'ashi nan ta ganshi zaune yana kallo komawa tayi ta kwanta saboda tasan dama babu abinda zai shigo dashi dakinta daga karshe dai har bacci ya kwasheta bata san lokacin da yabar falon ba.

   Misalin karfe 8 tafito bayan tasha kwalliya cikin dark purple din shadda dinkin riga da skirt, kitchen ta shiga nan taga buhun semovita guda daya sai ko kayan tea,mamaki ne ya kamata saboda tasan sai da mahaifinta ya cika mata store da duk wani abu wanda zata bukata, hatta chocolate da biscuits saida ya hado mata dasu saboda yasan tana yawan mu'amula dasu,

Dakin shaddad ta nufa lokacin data shiga yana zaune a bakin gado yana gyara sumar kanshi jikinshi sanye da uniform da alama fita zaiyi,

"Ina kwana?" Ta dan rissina tana gaidashi,

"Lafiya" ya amsa a takaice,

"Navy nace ko mukullin store yana hannunka?"

"Meya faru?"

"Zan dora girki ne"

"Baki ga wasu kaya awaje ba?"

"Nagani"

"To sune iya abinda zaki rinka dafawa kina ci.."

"Garin tuwo ne fa kawai sai lipton da sugar.."

"Ehh sufa, ko tuwo ba abinci bane?" Ya tambayeta yana kallonta saboda yadade da sanin babu abinda ta tsana irin tuwo dan lokacin da yana zuwa gidansu yana jinta tana yiwa kuku masifa duk ranar da taga ya dafa tuwo,

Bata kara magana ba ta fita zuwa kitchen ta shiga ta dora ruwan zafi,

"Lallai yaron nan mugune, wato nufinshi tuwo shine abincina kullum kenan? Tab"

Tafada ahankali,

Tea kawai ta hada ta fito kafin fitowarta har shaddad ya fita haka ta zauna shiru bayan tasha tea din, waya tayi ta kira blessing akan tazo, nan blessing ta tattaro kayanta ta taho, adakin kusa da na maryama ta ajiye kayanta ta fara dan shasshare gidan da goggeshi,daga nan ta shiga kitchen ta yi musu tuwo miyar kubewa, ita dai maryama da yake ta tsani tuwo baifi lauma biyar tayiba ta dauraye hannunta.

  Suna falo zaune da yamma suna hira ita maryama har ta danji sanyi saboda zuwan blessing, shaddad ne ya dawo yana shigowa ya tsaya yana kallon blessing wacce ke zaune a kasa ita kuma maryama tana kan kujera tana yin game a laptop dinta,

"Ke mekika zo yi agidan nan?"

"Anty ce ta kirani tace nazo zan rinka tayata aiki"

"To ba agidan nan ba, baki da wurin zama agidan nan, aikin gidan nan ita zata rinka yin kayanta idan kuma dole ne sai kinyi mata aikin to sai dai ta tattara ku koma gidansu sai kuje can kici gaba da yimata aikin..." Yana kaiwa nan ya wuce cikin dakinshi,

Ganin idon blessing yayi rau rau zatayi kuka yasa maryama katseta,

"Babu komai blessing ai ba rabuwa muka yiba muna tare, dauko kayanki ki koma gida, bari na dauko miki kudin okada"

Duk da abin yayiwa maryama ciwo amma haka ta danne bata nuna ba sannan tasan shaddad yayi mata hakane saboda ya kuntatawa rayuwarta domin baya son taji dadin zaman gidansa,

1000 ta daukowa blessing ta bata ta tafi tana matsar kwalla, komawa falo maryama tayi ta zauna tana tuna abinda shaddad ke shirin yimata, nafarko ya hanata aiki, ya kulle store ya boye mukullin sannan gashi yanzu ya hanata zama da yar aiki yace itace zata yi aikin gidan gaba daya.

  Tun daga ranar maryama ta shiga damuwa kafin sati har ta rame saboda bata cin abinci domin abincin tuwone ita kuma bata so gashi ya hanata siyo kayan abinci yace wallahi muddin yaga ta siyo koda indomie ne sai ya dauki mataki, dan haka ta hakura bata siyo komai ba bawai dan bata da kudiba sai dan hanawar da shaddad yayi, kullum cikin shan ruwan Lipton take ga aikin gida wanda bata saba ba jikinta ma bai sababa, ga zaman kadaici nan abu yataru yayi mata yawa, sanin idan taci gaba da damuwa zata iya kamuwa da hawan jini yasa tayiwa blessing waya ta shiga kasuwa ta kwaso mata English novels kala kala ta kawo mata, kullum aikin kenan daga kallo sai karatun novel, girki kuwa ba tayi sai ta gadama saboda shima shaddad din baci yakeba idan yana so da kansa yake shiga kitchen ya yi tuwonshi, wannan abu ba karamin damun maryama yakeba saboda tsakaninta da shaddad sai kace wasu kishiyoyi bazai ci abincinta ba bazai yimata doguwar magana ba, babu sakin fuska babu magana mai dadi, da haka suka shafe wata daya cis da aurensu.

  Yauma kamar kullum tana zaune a falo tana karanta wani novel mai suna sameer & sameera khairat ta kirata, dauka tayi tana murmushi,

"Adda Maryam ko kina wurin aiki ne?"

"Wanne aiki kuma khairat bayan yayanki ya hana, ai yace shi baya son aiki"

"Ya hana? Wai yanzu agida kike zaune?" Khairat ta fada cikin tsananin mamaki,

"To ya zanyi khairat, tunda yace bazanyi ba"

"Lallai to Allah ya rufa asiri"

"Amin khairat nagode agaida su anty"

Katse wayar tayi taci gaba da karanta novel dinta, ita kuwa khairat tana kashe wayar ta fada dakin hajiya domin dama tana Kaduna bata koma abuja ba,

"Hajiya kinji wai Yaya Navy ya hana adda Maryam zuwa aiki, kiji mugu"

"Mugun gaske kuwa autata, bani wayata in kirashi in tsigaleshi,in banda ma aure daga Allah yake shi ya isa yaje neman auren wannan yarinyar har abashi? Fitinannen yaro mai shegen taurin kan tsiya,bari na kirashi yanzu na wankeshi"

"Wallahi kam hajiya karki raga masa kiyi masa kaca kaca" khairat tafada cikin zuga tana mikawa hajiya wayarta,

Shaddad yana headquarter dinsu hajiya ta kirashi yana dauka yaji tace,

"Sannu kasaitaccen maigida,namiji mai cikakken iko, kai mazaje ka fita daga idona inrufe, meyasa ka hana matarka komawa aiki? Saboda mugunta ko me? To wallahi ban yarda ba indai na isa to gobe goben nan tafara zuwa wurin aikinta,aikin ai rufin asirinka ne idan baka saniba tunda idan tana dashi basai ta tambayeka ba, kana jina?"

"Ina jinki hajiya"

"Yawwa kaji dai nafada maka lallai lallai gobe kabarta takoma aikinta saboda dama dashi kaganta tun kafin ka aureta,idan kuma mugunta ce tasaka kake kokarin hanata aiki to wallahi baka isaba,ni nan ina mai baka umarni da kabarta taci gaba da zuwa aikinta"

"To hajiya"

Katse wayar yayi cikeda takaici, wato ma kararshi takai wurin hajiya kenan?, ko office bai komaba ya nufi gida, tana zaune a falo daga ita sai wata yar half best ta cire rigar jikinta domin bata taba zaton zai dawo yanzu ba, karatun novel take ta ajiye ta kwanta tafara bacci,k'afarshi yasa ya bugi tata,

"Ke kikayi wa hajiya waya kika fada mata cewar nahanaki zuwa aiki ko?"

Taji muryar shaddad sama sama cikin bacci, bude idonta tayi ta tashi tana kallonsa,

Sake maimaita abinda yafada da farko yayi,

Girgiza masa kai tayi "wallahi ni bamu taba yin waya da hajiya bama, sai dai idan khairat ce ta fada mata"

"To koma dai menene hajiya tace sai kinyi aiki, kuma naji nayarda zaki koma aikinki gobe amma kisani,

Wallahi wallahi duk ranar da na kamaki kina abinda bai gamsheniba da abokan aikinki wallahi abakin aurenki, daga ranar nagama aurenki,

Ke ko ganinki nayi a office din daya daga cikinsu ko kuma su naga wani a office dinki to wallahi aurenki kika yiwa saboda nadade da sanin akwai mummunar alaka tsakaninki dasu tunda kun saba shek'e ayarku acan..,

Sannan kisani shigar da kikeyi ada idan zaki fita to yanzu baki isa kinyi irinta agidan nan ba dan haka ki tanadi kayan fita unguwa.."

Wuceta yayi fuuuhhh ya nufi dakinsa, ajiyar zuciya ta saki, ita sai yanzu ma ta kula da babu riga ajikinta ta manta, duk da wadannan dokokin da ya kafa mata tasan dai idan ta fita din zata ji dan sanyi sabanin da datake zaune agida....







*_Ummi Shatu_*

MARYAMA SARAUNIYA.. 32,33,34

[5/18, 8:37 AM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_


_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*



     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _Kuna ina? Aminiyata ta k'warai cwt Kausar luv, and my besty Pherty Xarah, idan kuna kusa to ga shafinku ummi shatunku ta baku domin jin dadinku..._



   *_32_*

aishaummi.blogspot.com


   ~~~Haka Shaddad ya shirya ya tafi cikin bacin rai, aranar da yaje aranar yagama komai yawuce masaukinsa, yana kwanciya ko gama hutawa baiyi ba hajiya ta kirashi awaya,

Yana dauka yaji tafara fadin,

"Lallai lallai kaje wajen amaryarka ku gaisa kafin kadawo, kajini ko mazaje?"

"Ehhh hajiya naji.." Yafada yana jin wani irin kunci yana shiga zuciyarsa,

"Yawwa idan kaje kace ina gaisheta"

"To zataji"

Daga haka ya kashe wayar cikeda bacin rai saboda shi sam baya son wannan auren na maryama domin yana ganin kamar wata wahala ce zai tsunduma kansa aciki,

"Nidai kawai sangartacciya zan aura, yarinyar da babu abinda ta iya sai shan cyrup da zuwa club da bibiyar maza wai kuma yanzu azo ace itace matata, kai gaskiya nidai wallahi ba akyauta min ba,yarinyar nan babu abinda ta iya, ko shara bata iyaba bare girki"

Yafada afili yana cizon leb'e amma yasawa ransa cewar shi babu wani gidansu maryama dai zaije kawai dama ya amsawa hajiya da to ne saboda gudun bacin ranta.

   Abangaren maryama kuwa tana can sun fara tunkurar shirin biki itada Dada domin har Dada yayi order akawo furnitures din da za akaiwa maryama gidanta daga kasar Italy,

Ranar alhamis da safe su anty maijidda da anty zainab suka zo gidan dauke da kaya niki niki wanda sai sojoji ne ma suke binsu da akwatunan,

Maryama tana zaune afalo da filet a hannunta tana cin soyeyyen plantain ga waya makale a kunnenta suna hira da dr fahad sai ga su anty maijidda sun shigo, ajiye wayar tayi ko tsayawa kashewa batayi ba ta tafi da gudu ta rungumesu,

"Yata kayanki muka zo kawo miki"

Anty zainab tace tana ajiye kit din dake hannunta,

"To anty zainab kuma baku barinshi anan idan nazo sai nagani"

"To uwar yan hankali ai akawowa dadan naki yagani ko?"

Anty maijidda tafada tana yaye mayafin dake kanta saboda zafi,

"To anty ai mantawa nayi"

Tafada tana bin akwatinan da kallo saboda sunyi mutukar daukar hankalinta gashi best colour dinta aka samu wato pink and blue,

Gaban akwatin ta karasa tana shafashi saboda ganin hoton butterfly ajikin mirfin daga sama,

"Wowwww,anty wadannan akwatinan sun yimin kyau"

"To ai dama nakine" inji anty zainab,

"Yata albishirinki"

Anty maijidda tafada tana murmushi,

"Goro anty.."

"Me zaki bani tukwici"

"Idan labarin mai dadine anty zan baki salaryna na 1 month"

"Nawa kike karba per month?"

"Anty dubu dari bakwai da hamsin ne kacal"

"Ke yar nan ashe kudi kika tara bamu saniba, wannan uban kudin ya kike yi dashi?"

Anty zainab tafada tana zazzare ido dan tsananin mamaki,

"Wallahi anty ginin asibiti ake yimin, so nake nagina asibitin yara nawa na kaina, kuma inada gidan gona.."

"Ato kinyi dabara ai hakan yayi kyau"

Anty zainab tafada tana murmushi,

"Albashinki na wata yayi min yawa maryama amma dai dole kibani tukwici tunda har nakawo miki kayan lefen shaddad gidan nan.."

Mikewa tsaye maryama tayi, "anty wanne shaddad kuma?"

"Wanda dai kika sani, shaddad dinki, Navy.."

"Wayyo anty maijidda tsokanar har takai haka"

"Ke idan zaki ware ki ware babu wani tsokana wallahi dagaske ne shaddad shi zaki aura shine ya kawo miki wannan kayan"

"Alhamdulillah.." Shine kawai abinda maryama tafada ta fadi tayi sujjada tana murmushi, kallon kayan jikinta anty maijidda tayi daga ita sai farar body hug da jeans ta tattare kafar wandon sai kace wata yar kokawa,

"To yanzu dai ciwo ya kare, ankusa aje gidan shaddad ayita tsukewa da kananan kaya tunda kedai bakya kaunar kayan hausawa"

"Ai anty ni wallahi bana jin dadin kaya indai ba doguwar rigane ko riga da wando ba, ni kwata kwata ma bana son wasu kaya inba english wears ba.."

"Zaki saka da kyau ai" anty zainab tace da ita,

Blessing ce tafito hannunta rikeda faranti takawo gabansu ta dire,

"Woww anty kayan aurenki ne? Ni inama in samu quarter din wannan da naji dadi.."

"Kayanta ne blessing zauna kigani"

Anty maijidda tafada tana tsiyayar juice acikin cup,

"Kema kije kiga kayan lefenki yarinya"

Anty zainab tace da maryama.

Matsawa gaban kayan maryama tayi suka fara kallo itada blessing,duk abinda blessing ta daga sai kaji tana cewa,

"Woww anty wannan zai yi miki kyau.."

"Kema za akawo miki irinshi wata rana blessing ai tunda zanyi aure to kowa ma zaiyi.." Maryama tafada tana murmushi,

Da haka suka gama kallon uban tulin kayan wanda sai hakura ma sukayi basu iya kallo gaba daya ba, ko tashi daga wurin basuyi ba Dada ya shigo yana rikeda sandar da yake dan dogarawa da ita duk lokacin da ciwon kafarshi ya tashi,

"A'a kayan maman nawane suka sauka.."

Dada yace yana murmushi,

"Ga kaya nan kam mun kawo" inji anty maijidda,

Zama shima dadan yayi blessing tafara daga masa kayan yana gani sai sanya albarka yake,ita dai maryama tashi tayi ta shiga kitchen ta dorawa su anty maijidda abinci, zuciyarta tana cikeda tarin farin ciki wanda ba zata iya kwatantashi ba sai dai kuma tana jimamin irin zaman da zatayi da shaddad kafin ta samu hankalinsa ya dawo gareta ya fara kaunarta...

*_Ummi A'isha_*
[5/18, 8:37 AM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _Gaisuwa mai yawa ga antyn amarya, antyn ummi Shatu wato anty maijidda musa.._


    *_33_*

~~~Kwanan shaddad 5 a Lagos bai tafi Kaduna ba har sai da yagama dukkan abubuwan da suka kamata sannan ya nemi hutun sati biyu saboda bikinsa,hatta mukullin gidan da zai zauna sai da ya karba, wasu sabbin gidajene masu dakunan bacci guda uku da babban falo guda daya sai kitchen da store, a unguwar Victoria island yake shima na sojoji ne aka gina musu musamman,

Aranar da yagama komai yayi tafiyarsa Kaduna bai ko nemi ganin maryama ba balle yaje inda take,

Lokacin da yaje gida tisashi da tambaya hajiya tayi kan ya yabaro maryama, shikuwa kawai amsawa yake da tana nan lafiya, saboda yasan idan tagane baijeba zai sha fada.

  Maryama kuwa daren ranar da su anty maijidda suka zo kasa bacci tayi dan tsananin murna nan ta kira khairat tana yi mata godiyar ceton rayuwarta da tayi,

Kusan kwanan zaune suka yi dasu anty maijidda suna hira,kwanansu biyar agidan suka tattara har maryaman suka nufi abuja saboda suna son suje su gyarata, za ayi mata gyaran jiki da sauran abubuwan da suka kamata, sallama tayiwa dada da sauran mutanen dake gidan domin idan tatafi bazata sake dawowa gidanba sai ranar da za akaita gidan mijinta aranar ne za akawota dan tayiwa dada sallama,

Tattarawa sukayi suka tafi ita dasu anty maijidda zuwa abuja, suna zuwa kuma ta shiga busy domin bikin saura kwana biyar kacal, shagunan dinki sukaje takai dunkunanta sannan suka shiga kasuwa suka dan iyo siyayyar da baza arasa domin ashe gaba daya anty maijidda tagama siya mata kayan kitchen da sauran kayan kwalliyar falo zuwa bedroom da sauransu,

Suna komawa gida anty maijidda ta kira hajiya fiddausi Sodangi kwararriya wurin gyara amare tazo takanas tun daga garin borno domin gyara maryama,tana zuwa tafara tsumata da kayan gyara sahihi dan borno,

Nan aka fara dirjar fatarta ana shafeta da kayan hadin gyaran fata, cikin kwana biyu kacal maryama ta juye ta zama balarabiya,sai dai tulin abubuwan dasu anty maijidda da hajiya sodangi suke dura mata amai yake sata, daga tasha sai amai gashi sam bata iya cin abinci kwata kwata,

Kallon anty maijidda tayi sannan ta kalli cup din dake hannunta cikeda wani abu mai kamada madara,take tafara jin zuciyarta tana tashi,

"Anty dan Allah kiyi hakuri kibar abin nan wallahi amai karninsa yake sani.."

"Sai fa kinsha garama ki daina hadani da Allah, ko kin amayar ai dole wani zai zauna acikinki.."

Anty maijidda tafada tana mika mata cup din,

"Anty zainab,anty zainab.."  Maryama tafara kwalawa anty zee kira wai ko zatazo ta ceceta, amma koda anty zainab din ta shigo itama rike take da farfesun yan shila acikin plate ta kawo mata, haka suka tisata agaba sai da ta cinye sannan ta shanye wannan abun, kullum haka suke yimata tun tana yin amai har ta daina.

A bangaren shaddad kuwa shi babu wani shiri da yake yi, su hajiya ne kawai ke yin shirinsu sai sauran jama'ar gidan amma shi sam babu abinda ya d'ad'a shi da k'asa da wannan bikin,

Ita kuwa hajiya tsabar soyayya cewa tayi bayan an daura aure akawo mata maryama tayi kwana biyu sannan su tafi Lagos itada shaddad din.

   Tun ranar laraba gidan anty maijidda ya dinke da dangi da yan uwa harda abokan arziki, maryama tasha kunshi da gyaran gashi tafito tayi kyau sosai,fatar nan tata kamar ta jarirai domin ta yan hutuce gashi kuma ta had'u da gyara na musamman,

Aranar sulaiman abokin shaddad yazo kawo mata kudaden da zata yi hidima dasu kamar yadda ake bawa kowacce amarya da kawayenta, to ita bata da kawayen ma, bata da wata kawa ko daya komai nata ita kadai take yi,

Lokacin data fita sulaiman yaganta sakin baki yayi ya tsaya yana kallonta, shi mamaki yake da ganin wautar shaddad da yaketa ikirarin baya sonta, shikuwa sulaiman sam baiga laifinta ba asalima babu wanda zai ganta yace takai wadannan shekarun gata kyakkyawar gaske,

Gaisawa suka yi yabata kudin ya tafi, itama cikin gida ta koma tana cike da murnar ashe dai shaddad yana sane da ita.

  Ranar alhamis da yamma aka yi kamun maryama awani babban hall dake cikin Real Hotel, kamun yayi kyau sosai kuma ya kayatar, karfe shida aka gama aka watse kowa ya koma gidansa, anty babba yayar shaddad suma sun halarci wurin itada sauran dangi,

Washe gari ranar juma'a aka daura auren SHADDAD A SADIQ da DR  MARYAMA FARUQ BELLO akan sadaki naira dubu hamsin agarin jimeta, kuma aranar su anty maijidda suka shirya suka tafi Kaduna tareda amarya,

Suna zuwa aka karbesu cikin mutunci da girmamawa, hajiya kuwa kamar zata karawa maryama numfashi dan tsananin so, jin anty maijidda ma tace bata ci abinci ba haka ta zauna ta bata abincin tanayi tana lallabata da haka har sai da ta koshi,

Sosai itama maryaman taji tana kaunar mahaifiyar shaddad domin itama tana tsananin sonta gashi dadin dadawa ma ashe sunansu daya itama hajiyan sunanta hajiya maryam,

Dare yanayi misalin karfe 8 aka fara shirin tafiya dinner wacce sisters din shaddad suka shirya, nan aka rangadawa amarya kwalliya aka shiryata tafito cikin doguwar wedding gown pink and blue colour, tasha head shima pink, komai dai pink,

Gabanta ne ya fadi lokacin da anty babba ta kaita gaban motar da shaddad ke ciki yana zaune agidan baya saboda rabonta dashi tun ranar da yaje abuja, shikuwa shaddad ta cikin glass din window din motar ya zuba mata ido yana kallonta dan kyau kam tayi kyau shi kawai matsalar baya sonta ne bata cikin irin tsarin matan da yake son aura,

Bude mata kofar motar anty babba tayi ta shiga ta zauna, yana zaune yasha farar shadda sai kyalli da maiko take daga gani an kashe naira wurin siyanta...

*_Ummi Shatu_*🏻
[5/18, 8:37 AM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


   *_34_*

aishaummi.blogspot.com


~~~Shima shaddad din kallonta yake yi ta gefen idonshi yana ganin irin dukiyar da aka kashe ajikinta domin bayaga tsadadden materia din da tasa wasu gwala gwalai ne aka zuba mata ajikinta tun daga kan sarkar da ke wuyanta wanda Allah ne kadai yasan adadin kudinta zuwa kan abubuwan hannunta da agogo da zobbuna sannan ga wata yar karamar barima akan hancinta barimar tayi mata mutukar kyau kamar indiya haka ta fito, ko yaya ta juya kyalli da walwali take yi wal wal,

"Ina yini..." Yaji ta gaisheshi mamaikon ya amsa sai ya matsa kusa da ita nan kamshin turaren da yake addabarshi ya sake karuwa,

Bakinshi yakai saitin kunnenta saboda baya son sulaiman ya jiyo abinda zai fada,

"Congratulations, ina tayaki murnar zama matata tafarko da kiyi, sannan kinyi namijin kokari wajen shiga da fita har kika mallakeni, to ina son nasanar dake abu guda daya,

Kisani kamar yadda kika yi kokarin auren yaro sa'anki to da fatan zaki yi hakurin zama da shi, zama da yaro sa'anki sai kin jure sannan sai kin daure, saboda zanyi mutukar kuntatawa rayuwarki ,zan tsananta miki ko kadan ba zakiji dadin zama daniba saboda dama sai da nafada miki bana sonki bana kaunar zama dake, ke ba irin matan da nakeso bace amma sai da kika nace kika mayance har nakai ga aurenki,

To kinyi nasara kuma kinyi sa'a sannan zakara yabaki sa'a kin aureni sai dai kuma ina mai shawartarki da ki shirya zama dani zama na raba raini, ki shirya zama da sa'anki a matsayin mijinki..."

Shiru yayi sakamakon jin motar ta tsaya har sunzo wurin da za a gudanar da shagalin,

Ita kam maryama duk murnar da take ciki yau sai da gabanta ya fadi hankalinta ya tashi saboda jin kalaman shaddad, banda cin fuskar da yayi mata harda bakaken maganganu ya fada mata,

Bude kofar barin da take akayi domin ta fito har ta zira kafarta daya zata fita idonshi ya hango masa sarkar gold din dake daure akafarta ta hagu,

Rikota yayi ya dawo da ita cikin motar ya janyo kofa ya rufe,

"Cire wannan sarkar ta kafarki, ko baki daura ba dama nasan kina hulda da mata kamar yadda kike yi da maza, basai kin nunawa nawaje koke wacece ba.."

Sunkuyawa kawai maryama tayi batace dashi ko uffan ba ta fara kokarin cire sarkar da take daure a kafarta, tajima a sunkuye amma ta kasa cirewa,

"Kaga taki ciruwa, nakasa.."

Ta dago tana yimishi magana cikin maganarta mai sanyi hadeda shagwaba shagwaba saboda ita tsabar gayu da gatan da ta taso aciki maganarta ma gaba daya ta shagwababbu ce,

A zuciye ya kwaye rigar tata wanda ba kwaurinta kadai ba hatta cinyarta sai da ta bayyana jan kafar yayi wacce ke sanye cikin wani dogon high hill pink colour,yafara kokarin kunce sarkar amma shi dinma dakyar ya iya kuncewa dan sai da sarkar ta wahalar dashi, nan ya dago da sarkar a hannunshi yana dubawa,

Inbanda kyalli babu abinda takeyi domin ta gold ce, akan cinyarta ya cilla mata, nan ta dauka ta saka acikin jakar hannun dake rike a hannunta,

Anty babba ce ta bude kofar motar suka firfito nan tabi shaddad da kallon tuhuma,kasancewar su sun rigasu tahowa sannan tun dazu itama ta karaso tana jiran su fito amma taga shiru har sai yanzu da tayi kundunbala ta bude su,

"Kai shaddad meye hakan? Idan kayi hakurima gobe za akawo maka ita amma nan wurin mutane kazo ka makaleta ka hanata fitowa bayan ga mutane nan sunata faman jiranku"

Shiru shaddad yayi cikeda bacin rai wato ita anty ta zargi ko wani abu ya rike maryama yake yimata kenan, dan karamin tsaki yaja,

"Inma yanzu daga nan can zaku wuce ku kaita ni babu abinda ya dameni" yafadi acikin zuciyarsa,

Ganin maryama nagaba yana baya yasa anty babba dakatar dasu,

"Haba haba ai ba haka akeyi ba"

Janyo shaddad tayi zuwa wurin maryama ta sakala hannunta cikin nashi ta rab'ata da gefen kirjinshi,

"Yawwa kunga yanda akeyi,ai haka ya kamata kuyi tunda an rigada an daura muku aure da ba adaura bane shine, kai shaddad ka ruketa fa sosai saboda wannan dogon takalmin nata wahalar tafiyane dashi idanma tazo da tsautsayi zata iya faduwa.."

Shi dai bai tsaya jiran jin karshen zancen anty ba ya, ya rike maryama ba wai dan yasoba, tana rab'e a kirjinshi ya ziro daya hannunshi ta bayanta ya rike kugunta, karshen kyau ma'auran sunyi kuma sun hadu duk wanda ya kallesu bazai iya hakuri ba sai yaji ya sake maimaitawa gwaurayen wurin kuwa take suka fara burin suma kasancewa a irin wannan rana,

Suna shiga cikin hall din kowa da kowa ya mike tsaye, su anty maijidda da anty babba na biye dasu har suka hau kan dining table,

Sai da shaddad yaje ya zaunar da maryama akan kujera sannan shima ya zagaya ya zauna a kusa da ita domin wata kujerace ta alfarma aka ajiye musu wadda tasha decoration,

Yanayin kujerar yasa dole sai da suka matsi juna domin bata da fadi sosai girmanta bai kai na two sitter ba dan haka dole manne suke da juna,

"Ina son kisani na aureki ne kawai domin yin biyayya ga mahaifiyata bawai dan so ba saboda ko sau daya ban taba jin sonki acikin zuciyata ba kuma nasan bazan sokin ba har abada domin inada wacce nake so yarinya mai hankali,

Mai nutsuwa mai addini, mai kamun kai, sannan gata yarinya karama danya shakaf yar shekara goma sha takwas ba irinki ba wacce ta tara shekaru ba aure..."

Duk da taji zafin maganganunsa sai bata ko tanka masa ba saboda nasihar da anty maijidda tayi mata tun dadewa ita take tunawa inda anty maijidda take cemata,

"Maryama zaki samu shaddad kuma zaki aureshi amma sai kinyi hakuri sai kin jure, ko bayan aurenku dashi dole sai kinyi hakurin zama dashi har zuwa lokacin da Allah zai karkato miki da hankalinsa gareki.."

To duk lokacin data tuna wannan maganar ta anty maijidda sai taji sanyi taji cewar zata iya jure duk wasu miyagun maganganun da zai jefeta dasu,

"Kuma ina so ki sani, wallahi zaman gidana zaman ukuba ne agareki.."

Ta jiyo muryarsa a saitin kunnenta, kai idan ba jin abinda yake fada kayiba zaka zaci wasu kalaman soyayya yake fada mata ko wasu kalamai masu sanyaya zuciyar masoya saboda irin yanda sukayi zaman, hatta cinyarta guda daya akan tashi take, gaba daya acikin jikinsa take shikuma yasa hannushi guda daya ya zagayeta, gashi sai saitin kunnenta yake kai kanshi, dan kamshi kam yashaki kamshi har ya cika masa ciki domin tako ina kamshi ne yake ambaliya daga jikin maryama to amma shi shaddad sam ba kamshin ne sababin kai kanshi jikinta ba asalima yana yin hakane domin ya kuntata mata.....



   _Fans ku taya Ummi shatunku da addu'a mura nakeyi duk hancina atoshe, muryata adashe.. Luvs you all._



*_Ummi A'isha_*

MARYAMA SARAUNIYA.. 29,30,31

[5/17, 4:31 PM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


    *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _Ina jida ku Nana Hafsat (miss Xoxo),Zainab Y Hussain (autar hajiya), Allah ya k'ara raya minku yan matan kirki.._


    _*29*_

  ~~~Rawa jikin anty maijidda yafara take ta saki kara ta tashi aguje tafita,

Mintuna kadan sai gata da wani saurayi dan makotansu, kinkimar maryama akayi aka sa a mota suka nufi daula clinic, suna zuwa aka bata gado,

Tsabar tausayi anty maijidda harda kwallarta,

"Dan Allah maryama kar kema ki tafi kibarmu kamar yadda mahaifiyarki ta tafi tabarmu domin ke kadai muke gani a madadinta muji dadi.."

Haka anty maijidda taketa furtawa tana kuka,

Kanwarta zainab ta kira dama su ukune daga marigayiya mahaifiyar maryama sai ita sai mai binta zainab wacce take aure a Kaduna,

Tana dauka ta fada mata rashin lafiyar maryama, nan zainab din tace tana nan zuwa,

Maryama kuwa tunda tayi wannan dogon suman bata farfadoba sai da yamma tayi,

Bude idonta tayi taf da hawaye ta rike hannun anty maijidda,

"Anty mutuwa zanyi, wallahi ina son shaddad shikuma baya sona, ya tsaneni anty"

Rufe mata baki anty maijidda tayi itama idonta dauke da k'wallar,

"Ya isa kiyi shiru maryama insha Allah bakida miji sai shaddad.."

Haka anty maijidda tayita fada mata kalamai masu dadi dan kwantar mata da hankali,

Ba asallamesu ba sai bayan sallar isha kasancewar clinic din basa barin patients su kwana,

Suna isa gida anty zainab na isowa, kamar dama tare suke,

Murmushin yake kawai maryama keyi saboda ita kadai tasan irin radadin da zuciyarta keyi,

Ciki suka shiga ta kwanta akan doguwar kujera tana sauraren zancen dasu anty maijidda sukeyi itada anty zainab sunata jajanta abin,

Tashi tayi dakyar ta nufi cikin dakinta, wayarta ta dauka ta fara kiran khairat kanwar shaddad, cikin yanayin bacci ta dauka,

"Adda Maryam"

"Khairat ki taimakeni dan Allah, ina daf da rasa yayanki kuma wallahi idan har ban sameshi ba mutuwa zanyi.."

Zunbur khairat tayi ta tashi daga kwanciyar da take babu shiri taji baccin idonta ya wartsake,

"Adda Maryam kin sani aduhu meke faruwa?"

"Khairat son shaddad nake tun ba yauba, na dauki tsawon shekara biyu ina fama da ciwon sonshi, amma shi ya tsaneni"

"Kiyi hakuri adda Maryam gobe zanzo yanzun ma saboda dare yayine da sai nazo amma gobe zaki ganni"

Kashe wayar maryama tayi tasake fashewa da kuka, tana cikin yin kukan ne su anty maijidda suka shigo nan suka shiga rarrashinta har tasamu ta yi shiru, wanka ta shiga tayi da ruwa mai dumi ta fito, dakyar anty maijidda tasamu ta bata abinci ta dan ci ta kwanta.

  Washe gari kamar yadda khairat ta alkawarta sai gata da misalin karfe tara nasafe, adaki ta samu maryama tana kwance ana yi mata karin ruwa,

"Sannu adda Maryam..."

"Yawwa khairat sannu"

"Adda Maryam wai meya farune haka...?"

Labarin abinda yafaru maryama tabata tun daga kan farkon haduwarta da shaddad har kawo yanzu babu abinda ta rufe mata komai saida ta fayyace mata,

Kama hannunta khairat tayi tana zubar da hawayen tausayinta,

"Yanzu adda Maryam akan son yaya shaddad kike kwance bakida lafiya? To ki kwantar da hankalinki nayi miki alkawari zanyi iya kokarina naganin kin mallaki Yaya shaddad, insha Allah sai kin aureshi, nidama tun farkon ganina dake naji kin shiga raina, yanzu gida zanje in fadawa anty dama gobe zamu tafi kaduna saboda yayarmu ta haihu jiya da daddare"

"Nagode khairat, nagode.."

"Kibar godiya anty dama yarinyar da yake son ya aura ma hajiya ba son auren takeba shine yake so, duk yanda ake ciki dai zakiji daga gareni"

Sallama khairat tayi mata tatafi, tana zuwa gida ta kwashe zance tas ta fadawa antyn ta, nan itama antyn ta hau fadin,

"Ai kuwa wallahi wannan yarinyar ni banga laifinta ba da zai wulakantata,yarinya kyakkyawa da ita, dama wannan yarinyar da yake jiran tagama makaranta ya aureta ma ba lallai ne abashi ba, Allah yakaimu gobe muje gida wallahi hajiya zataji komai, kuma muddin hajiya taji to dolensa sai ya aureta, haba zamanshi haka babu aure ai ya isa kidubi sulaiman fa har yayi yara biyu shi yana nan yanata jiran gawon shanu..."

Haka antyn khairat wacce ake kira da anty babba tayita bambami tana fad'a da alama itama ta goyi bayan sai shaddad ya auri maryaman, dan haka washe gari da sassafe suka dauki hanyar Kaduna garin governor.....


*_Ummi A'isha_*🏻
[5/17, 4:31 PM] Ummi Shatu: _®HWA_


_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

     _Gaisuwa ta musamman ga masoyan maryama sarauniya musamman ma ke k'awata Halima Lawan Bala, and babbar Yaya Anty Sis (Maman sultan)_


    _*30*_

~~~Koda su khairat suka je gida samun hajiya mahaifiyarsu suka yi suka kora mata jawabin abinda ya faru tsakanin maryama da shaddad nan anty babba takara da cewa,

"Ni hajiya abinda nake gujewa wannan yaronma shine wallahi indai bai auri yarinyar nan ba to ya tafka babbar asara saboda baki ganta ba, yarinya yar mutunci mai nutsuwa,mace iya mace.."

"Wallahi anty gata da hakuri babu ruwanta da hayaniya" Khairat tafada cikin zuga,

"To ai ko baku fadi haka bama anty yazama dole ya aureta tunda tana sonsa, kinga sansdiyyar son da take yimasa bazata saba masa ba kullum cikin faranta masa zata kasance"

"Ku kyaleni dashi zai zo ya sameni ai yazo tun jiya yana nan agari..."

Hajiya tafada tana gyara zamanta daga zaune zuwa kishingide, cikeda murna khairat tace,

"Yawwa hajiya wallahi har rashin lafiya takeyi akanshi".

  Abangaren maryama kuwa yanzu ta dan fara warwarewa saboda nasihar da anty maijidda da anty zainab keyi mata, babu laifi yanzu ta danji sauki sai uwar ramar da tayi.

  A Kaduna kuwa shaddad hankalinsa kwance ya shiga falon mahaifiyar tashi bai san akwai wata a kasa ba saboda tun ranar da yabar abuja ya rufe shafin maryama rufewa ta har abada,

"Kai shaddad wai yaushe zakayi hankali ne? Saboda kaga yarinya na sonka shine zaka rinka wulakantata? To bari kaji kar kaji da wai wallahi sai ka auri wannan yarinyar saboda nagaji da zamanka ahaka kanata sauraren wata yarinya wacce ba asan ranar aurenku ba.."

Ido ya kwalalo jin abinda hajiya tace,

"Hajiya wai akanwa kike magana ne?"

"Akan wannan yarinyar maryama ta abuja"

Gabansa ne ya fadi to taya akayi hajiya tasan maganar,

"Hajiya wa zan aura? Wannan yarinyar yar shekara 30? Sa'ata cefa, bayan haka kuma ni wallahi bata yimin ba saboda batada tarbiyya gata marar kamun kai kullum cikin zuwa wurin maza take ga shaye shaye.."

"Kai ka rufe min baki, wannan sharrin da kake kagowa kana fada bashi zai hana auren nan ba wallahi, aure sai anyishi ko baka so, tashi kabani wuri"

Tashi yayi fuskarsa a hade ransa abace saboda shi aganinsa yanzu ai andaina auren dole, ko mata andaina yimusu auren dole balle shi namiji,yana fita ya iske Suleiman abokinsa a kofar gida yana jiransa,.

"Sulaiman kaji abinda hajiya ta tsiro dashi kuma yanzu? Wai sai na auri wata yarinya sa'ata"

"Ah to meye aciki? Nifa age mate dinama naso aura Allah ne baiyi ba"

"Kajika da wani zance kuma, ana ga gabas kana ga yamma mtswww"

Shaddad yafada cikeda jin haushi yatafi yabar sulaiman awurin bai ko kara bi ta kansa ba,

Ran shaddad idan yayi dubu to yagama baci aranar musamman ma da ya sake shiga wurin hajiya yaji tana waya da baba Ahmadu kanin mahaifinsu kan cewa suzo ranar asabar shida kawu auwalu zasuje nemarwa shaddad auren maryama,kasancewar mahaifin su shaddad din yajima da rasuwa,

Zama yayi yana jiran tagama wayar idonshi jajur,

"Yanzu hajiya idan aka yimin haka anyi min adalci kenan, taya za adage kan lallai sai na auri matar da bana so, yarinyar nan wallahi hajiya bata da tarbiyya ko kadan gata da bin maz.."

Dakatar dashi hajiya tayi, "wai kai ban hanaka wadannan maganganun bane? Kar nakara jin wannan maganar a bakinka koma yaya take to itace matar aurenka.."

Shiru yayi bai sake magana ba har babban yayansu ya shigo wato yaya Yusuf, yana jinsu shida hajiya suka fara maganar yanda za aje neman auren,

"Ai ni hajiya ina ganin ma kawai da munje to agama magana har rana asaka mutaho da ranarmu.."

Yajiyo yaya Yusuf yana fada,

"Ehh nima dama nayi wannan tunanin Yusuf, kamar ka shiga zuciyata wallahi, ni amma bana son asa doguwar rana idan har son samu ne karshen wata mai zuwa ayi bikin nan kowa ya huta, kaga yau 20 ga wata amma ya kagani?"

"Hajiya hakanma yayi daidai tunda kinga ai dama nan din muma ashirye muke kuma insha Allah suma gidansu yarinyar nasan ashirye suke.."

"Yawwa Yusuf Allah yayi maka albarka zan fadawa baffan nakuma dan Allah duk yadda zakuyi to kuyi abar ranar auren nan akarshen wata mai zuwa.."

"To hajiya insha Allah za ayi yanda kikace"

"Yawwa nima yanzu kiran yaran nan zanyi ana gama hidimar sunan nan su shiga kasuwa su fara hado kayan lefe muyi muyi mu kai musu can mu huta inyaso sai mu jira ranar biki"

"To Allah ya sanya alkairi hajiya" Yaya Yusuf yafada yana kokarin mikewa, Yaya Yusuf shine babba agidan shima soja ne sai dai shi ba Navy bane army ne dagashi sai anty babba wacce ke aure a abuja sannan sai shaddad sai anty karama wacce ta haihu yanzu sai yar autarsu khairat,

Da harara shaddad ya raka yaya Yusuf sannan shima ya mike zai fita,

"Zo nan mazaje" wannan shine sunan da hajiya take kiransa dashi tun lokacin da yana karami yana burin zama soja,

"Ai ba tafiya zakayi ba ban gama dakai ba"

Komawa yayi ya zauna yana kallonta, shi bakin cikinsa ma tayanda akayi wannan maganar har tazo kunnen hajiya,

"Kaima idan Allah ya kaimu wani satin bayan anje an tambayo maka auren zaka shirya kaida sulaiman kuje ya rakaka ku gaishe da mahaifin yarinyar sannan ku tattauna da ita kana ji?"

"Naji hajiya"

"To tashi kaje Allah yabada sa'a"

Mikewa yayi ya fita fuskarsa adaure, ko su khairat bai kulaba wadanda ke zaune atsakar gida suna gyaran kayan miya wasu kuma na yin wanke wanke, kamar zai fashe da kuka haka yasa kai yafice daga gidan....


*_Ummi A'isha_*🏻
[5/17, 4:31 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


    _*31*_

aishaummi.blogspot.com

  ~~~Ita maryama tana can abuja bata san abinda ake ciki ba, duk tabi ta rame ta kanjale tayi kashin wuya,

Dakyar anty maijidda da anty zainab suka samu suka rabata da damuwar datake addabarta, anty zainab bata bar gidan ba saida taga maryama ta dan murmure,

Nasihar da anty maijidda keyi mata yasata ta dangana ta cire damuwa daga cikin ranta domin kullum anty maijidda cemata take,

"Maryama idan har shaddad mijinki ne to zaki sameshi ta inda baki zataba idan kuma ba shine mijinki ba to da yardar Allah wanda yafishi zaki aura"

Wannan maganganun na anty maijidda suke sa zuciyarta ta yi sanyi dan haka yanzu ta cirewa ranta damuwa har tafara maida jikinta sabanin da datayi rama,

Komawa tayi taci gaba da al'amuranta tacigaba da zuwa makarantar islamiyyarta, kusan kullum sai sunyi waya da khairat amma bata taba fadawa maryama abinda ke faruwa ba,

Ranar asabar da yamma Dada yakirata awaya yace mata bakinta sun zo kuma ya yaba dasu harma an tsayar da ranar aure karshen wata mai kamawa dan haka tayi kokari ta dawo gida,

Mamakine ya kamata nan tafara tunanin to ko fahad ne ya tura iyayensa ko kuma dr naz? Amma tafi zaton fahad ne saboda kwana biyu ya matsa da kiranta awaya,

Tabe baki tayi "koma waye damuwarsa ce, naji zan aureshi ahaka" tafada acikin zuciyarta,

"Shiyasa maryama nadade ina yimiki nasiha akan karki damu kanki akan maganar aure domin komai da kika gani na rayuwa to da lokacin sa yanzu gashi kina zaune Allah ya kawo miki lokacin, nasan babu surutun da bamu sha ba nidake akan naki aurar dake to yau gashi Allah zai nuna min wannan lokacin, Allah yasa ayi a sa'a mai sunan mama.."

"Amin Dada, insha Allah zan sa rana nadawo gida"

"Yawwa mai sunan mama Allah yadawo dake lafiya, kigaida antyn naki"

Katse wayar tayi bata sake bi takan zancen ba har saida tayi baccinta ta gama sannan ta tashi taje tana fadawa anty maijidda abinda Dada ya fada,

"Koma waye maryama kiyi hakuri ki aureshi kinji tunda har ya aika gidanku to yana sonki da gaske, ki cire batun shaddad dinnan aranki"

"Dama haka zanyi anty, insha Allah zan manta dashi har abada"

Tun daga wannan lokacin ta cire batun shaddad acikin rayuwarta bawai ta daina sonshi bane a'a har lokacin tana kaunarsa kawai karfin halin rabuwa dashi tayi bata san shi dinne yake shirin zama mijinta ba.

A can Kaduna kuwa ana can ana shirye shiryen hada lefen shaddad wanda za akaiwa maryama, ranar lahadi hajiya tasa ya shirya shida sulaiman suka nufi lagos kai gaisuwar surukai,

Lokacin da Dada yaga shaddad ba karamin mamaki abin yabashi ba amma sai bai nuna komai ba haka ya karbesu hannu bibbiyu saboda duk atunaninsa maryaman ce tabashi damayazo neman aurenta dan haka cikin sakin fuska ya gaisa dash, kuku ya shirya musu table,

Karfe biyar na yamma suka jiyo kasancewar ajirgi sukaje kuma ajirgin zasu dawo, duk wannan aikin hajiya ne kasancewar mai kudin gaske ce dama can ita mai tarin dukiyace saboda tana yin kasuwanci sosai, plaza plaza da take da ita acikin central market na Kaduna sunfi talatin,

"Shaddad ka kwantar da hankalinka zakaji dadin zama da wannan yarinyar"

"Ba wani dadin zama da zanji da ita, bafa yarinya bace, shekararta 30 me zan samu awurinta?"

"Duk wani abu da zaka samu awurin wata mace itama zaka samu awurinta wallahi domin duk mace macece"

"Banda wannan saboda sam bata da tarbiya ga bin maz.."

Shiru yayi saboda sai yaji kunyar fadawa sulaiman munanan halayenta tunda ko babu komai dai yanzu tana shirin zama matarsa,

Haka sulaiman yayita bashi baki daga karshe ya b'ige da tsokanarsa,

"Yo kai in ba yar shekara talatin din ba wacece zata iya daukar dawainiyarka, ai kafi karfin yar sha takwas"

"Kuma sai na auri yar sha takwas dinba, me zanyi da tsohuwa yar shekara 30,ni wallahi yarinya nake so karama"

Shi dai sulaiman cigaba da tsokanarshi yayi har suka sauka.

  Sati biyu da saka ranar auren maryama ta shirya ta koma Lagos, kukan da tayi lokacin da zata tafi ba kadan bane, ita tana kuka anty maijidda na kuka har suka rabu,

Karfe shida na yamma ta sauka Dada sukaje suka dauko ta, daren ranar kusan kwana suka yi suna hira da Dada,wani ikon Allah kuma har suka kammala hirar bata iya tambayar Dada waye yake shirin zama mijinta ba.

Kwana biyu da dawowarta takoma office taci gaba da zuwa aikinta sai dai yanzu sam bata sakarwa su dr sameer fuska kamar da saboda tace musu aure zatayi nanda karshen wata,

"Wannan sojan ne ya kadamu ko?"

Dr sameer yafada yana dariya,

"Ehh shine" tafada cikin gatse,

"Yawwa nidama nasan sai dai shi"

Shiru tayi taki zancen taci gaba da aikin da takeyi saboda bata son afama mata ciwon son shaddad dake cikin zuciyarta.

   Gidansu shaddad sun gama hada lefe, akwatina goma sha biyar hajiya ta hada da kudinta,blue and pink shine colour din akwatinan, komai naciki mai tsadane domin khairat tacewa hajiya itama maryaman Yar gayuce bata saka kaya sai masu tsada saboda kwararriyar likitace duk wata albashi take dauka,

Anty babba da kanta tasaka khairat agaba sukaje gidan anty maijidda sanar mata zasu kawo lefe gidanta jibi, tsabar murna anty maijidda dai gud'a ta shiga yi saboda tsabar murnar jin shaddad ne zai auri maryama, saida ta gama gud'a sannan tafara yiwa annabi salati,

Ki'n fadawa maryama tayi amma ta kikkira danginsu da kanwarta anty zainab ta fada mata, nan tazo suka hau shirin tarbar bakinsu, sai da suka soya kaji cikin katuwar bakar roba ta zuba ruwa, banda cake da meat fie wanda suka yi order dasu donotes,spring rolls da sauran kayan makulashe,

Ranar juma'a kamar yadda sukace aranar suka kawo lefen maryama murnar da anty maijidda da anty zainab sukayi ko ranar aurensu basuyi haka ba,

Jan anty maijidda anty zainab tayi zuwa cikin daki, suna shiga ta rike haba tace,

"Anty Maijidda nawa zamu bawa mutanen nan kudin tukwici kiduba kiga uban kayan da suka kawo mana fa"

"Dubu dari cif zamu basu zainab, dama dadyn su Faruk yabayar yace gashi nan abasu, ai batayi kadan ba ko?"

"A,a baiyi kadan ba hakanma yayi"

Komawa falo sukayi suka bada tukwici da sauran kayan dadin da suka tanadar musu, yan kawo kayan basu wani jimaba suka tafi saboda kaduna zasu juya a lokacin,

"Har yaufa yar taki bata san waye mijin nataba, bata san wanda takeso zata auraba, amma karki fada mata fa"

Anty Maijidda tace da anty zainab bayan yarage su biyu acikin falon suna sake ganin kayan,

"Allah Sarki maryama, jinkiri alkairi ne yau dai kiga yarinyar nan shekararta talatin kamar bazata yi aureba yau kiga irin uban kayan da aka kawo mata, wallahi duk wata wacce ta jima batayi aureba sai kiga idan Allah yatashi bata yabata mai nagarta kuma son kowa kin wanda ya rasa"

"Ah tun yaushe ai mai hakuri mai komai ne zainab yanzu dai duba kiga wannan uban kaya wai na maryama ne ita kadai"

Anty Maijidda tace tana rufe akwatin dake gabanta,

"Allah dai yasa rabonta ne"

"Amin zainab jibi sai muje mukai musu can Lagos din ko idan makota da yan uwa sunzo sun gama gani"

"Ehh sai mukai"

Haka suka yita murna suna maganar kayan har zuwa wani lokaci.

Abangaren shaddad kuwa takaici goma da ishirin ne yake ciciyarshi saboda anturo masa posting letter cewar an sake turashi aiki Lagos sai dai wannan karon ba barikin su maryama bane wani barikin ne daban dake can gaba da nasu maryama amma shi dinma acikin Victoria island dinne,

Kamar zaiyi kuka haka ya shirya yatafi kai repot gashi yau aurensu shida maryama saura kwana goma cif...


*_Ummi A'isha_*

MARYAMA SARAUNIYA.. 26,27.28

[5/16, 8:01 AM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


    _*Gaisuwa mai dumbin yawa ga duk members na haske writers association, ina alfahari daku Allah yaci gaba da hada kanmu,wannan shafin nakune domin jin dadinku.*_

 
    *_26_*

   ~~~Jiki asanyaye maryama ta dauke idonta daga kan hoton tafita zuciyarta sai ambulo mata tarin tambayoyi take wanda bata da amsarsu, gashi lokaci guda kirjinta ya hau harbawa da sauri da sauri banda bugun da zuciyarta take dum dum saboda duk atunaninta nan gidan shaddad ne,

"To kodai shaddad yayi aure ne? Innalillahi amma da na shiga uku.."

Komawa falon baki suka yi suka zauna amma ita maryama duk ji take zaman ya gundureta babu abinda take kauna irin taganta agida,

"Khairat bari muje mu tafi ga wannan babu yawa.."

Mikewa tayi takama hannun A'isha idanuwanta har sunyi jajur,

"Kai adda Maryam daga zuwa sai tafiya?"

"Ehh khairat bana jin dadin jikina ne shiyasa"

"Ayya to Allah yabaki lafiya ashe gobe ma ba lallai kizo makaranta ba"

"Ehh sai yanda ta yiyu dai"

Daukar ledar kayan khairat tayi tanufi falon antynta tana kwalla mata kira,

"Anty zo ki tayani godiya kinga kayan da adda maryam ta kawo min.."

Fitowa matar tayi fuskarta dauke da murmushi,lokacin itama maryama har sun fito zasu tafi,

"Ahh duk wannan, maryama harda wahala haka? To angode madalla Allah yabar zumunci"

Ita dai maryama yaken dole kawai take tana amsawa daga nan suka fice daga gidan,

Har kofar gida antyn khairat tabisu tana yiwa maryama godiya,

"Adda Maryam angode madalla"

"Babu komai khairat"

Shine kawai abinda maryama tace ta tashi motar da suka zo da ita ta dauki titin da zai mayar dasu gida,

Ko kadan bata jin surutun da Aisha take yimata tana bata labari saboda gaba daya hankalinta ba ajikinta yake ba,

Koda sukaje gidama dakin da yake a mazaunin nata ta nufa taje tafada akan gado tana jin kamar kanta zai rabe gida biyu,

Ita anty maijidda ma bata san sun dawo ba saboda tana can baya wurinda samarin 'yayanta suke buga ball suda yaran makota tana kallo, har saida ta shigo ciki taga Aisha a falo tana kallo sannan tasan sun dawo,

"Yaushe kuka dawo ku kuma?"

"Yanzu muka dawo"

"To ina addar taku?"

"Tana daki"..

Dakinta kawai anty maijidda ta nufa saboda tayi tunanin ko kawai maryama ta shiga dakine domin ta huta shiyasa bata bi ta kanta ba.

Ita kuwa maryama tana can tana fama da ciwon zuciya gashi kirjinta sai wani irin zafi yake yimata, kanta kuwa kamar zai fita yabar gangar jikinta,

Dafe kan tayi tana numfashi da kyar kafin wani lokaci har numfashinta ya tsaya cak ya daina fita,

"Momy ara min wayarki zan kira dady nace masa ya taho min da laptop tunda waccan ta daina yi.." Faruk second born din anty maijidda ne yayi wannan maganar,

"Ni wayata bata nan Sadiq ya fita da ita sai dai ka aro ta addarku"

Dakin maryama faruk din ya nufa yana cewa, "ai momy kece kika hana dady ya bamu waya da yanzu kowa da tashi mun huta aro"

"Ba wanda za abawa waya sai yayi candy, jimin yaro da iyayi"


Shiga dakin faruk yayi  ya karasa wurin da maryama ke kife akan gado,

"Adda Maryam bani aron wayarki nakira dadynmu"

Jin shiru bata amsaba yasashi zuwa kusa da ita yafara bubbuga gefen da take kwance amma nan dinma shiru bata motsa ba, har ya juya zai fita yaji tayi wata irin jan zuciya mai mutukar karfi sai kuma yaji k'attt,kamar fitar rai, wata kara ya kwalla, take su anty maijidda suka taho aguje domin hatta ita dake zaune a falo sai da suka jiyo wannan k'att din,

Juyowa da ita anty maijidda tayi arude anan taga idanuwanta akakkafe ga shatin hawaye nan akan kuncinta amma kallo daya zaka yi mata ka fahimci cewar bata numfashi,

"Maryama.." Anty maijidda takira sunanta da karfi tana jijjigata,

"Nashiga uku, faruk kaga bata numfashi, ke A'isha meya sameta ahanyarku ta dawowa?"

"Momy kibar wannan maganar muje mu kaita asibiti" faruk yace yana kokarin ciccibar maryama, wani aiki sai maza, kasancewar namijine nan ya cirata ya dauketa, binsa da kallo anty maijidda tayi saboda kwata kwata shekarunsa basu fi sha biyar ba,

Ko mayafi babu ajikin ta tabisu tana salati sai A'isha ce ta bita da mayafin,

Wani clinic dake cikin unguwar suka kaita mai suna, Daula clinic, suna zuwa aka shiga da ita aka kaita emergency,

"Ikon Allah yanzu dama wannan shiga dakin da maryama tayi ba lafiya ba?" Anty maijidda tafada a diririce, duk tabi ta fita hayyacinta.

Bayan awowi uku ne suka samu shiga dakin da take, har ta dan wartsake amma da gani kasan tana cikin damuwa,

"Sannu maryama, wai meya sameki ne?"

Murmushin karfin hali tayi, "babu komai anty"

"A,a ai kuwa kowa yaganki yasan kinada damuwa"

Korar su faruk anty maijidda tayi yarage daga ita sai maryama ta titsiyeta, nan maryama ta sanar da ita,

"Kashh amma maryama kema dai kinyi rashin hakuri, shiyasa nace miki zaki samu shaddad amma sai kinyi hakuri sai kin jure, sannan ta yiyu shima shaddad baiyi aurenba kila nan gidan yan uwansa ne, ai a hikimance zaki ji duk wani bayani a bakin khairat tunda tanada surutu babu abinda bazata fada miki ba, kedai kawai kiyi hakuri kuma kiyi addu'a.."

Ko babu komai kalaman anty maijidda sun sanyaya mata ranta da zuciyarta domin kullum karfafa mata gwiwar cewar zata samu shaddad take, kuma itama ta daura aniyar yin duk wani yaki domin mallakarsa..



*_Ummi Shatu_*
[5/16, 8:01 AM] Ummi Shatu🏻: _®HWA_

_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

 

    _Fatan alkairi agareku Hawwa (Hawy) & uwa tagari Halamcy.._


    _*27*_

  ~~~Gyara kwanciyarta tayi idanuwanta suna fitar da kwalla,

"Shikenan anty zan jarraba yadda kika ce"

"Yawwa maryama ko kefa amma da har zaki karaya tunda wuri, ai ba akaraya akan abinda ake so, yanzu ki kwantar da hankalinki kibi khairat ahankali har ta fayyace miki komai"

Haka anty maijidda taci gaba da lallabata tana bata shawarwari har na wani lokaci,basu suka bar wannan clinic dinba sai dare anty maijidda tana cike da tausayinta saboda ganin soyayya tana ta faman wahalar da ita.

Tunda suka dawo gida anty maijidda ta hada mata tea tasha tayi wanka ta kwanta dan haka da safe ras ta tashi sai ciwon kan dake damunta ganin haka yasa ranar bata samu zuwa islamiyya ba har sai washe gari,

Aranar ma kawai dai daurewa take yi amma bawai dan ta warke sumul ba,

Suna zaune a aji bayan angama yimusu dori ta kalli khairat wacce ta maida hankalinta kan alqur'anin dake gabanta tana ta faman maimaita wurinda ya sayyadi ya dora mata,

"Khairat nikuwa na tambayeki mana.."

"Allah yasa nasani adda Maryam" khairat tace bayan ta rufe alkur'anin dake ajiye agabanta,

"Am ranar da naje gidan nan naku naga hoton wani guy soja wanda kamar na sanshi.."

"Yaya Navy kika gani ko Yaya army?"

"Wani fari dai mai tabon salla agoshinsa ina jin indai ban manta ba sunanshi shaddad.."

"Ohh Yaya Navy, ai brother nane, a ina kika sanshi"

Murmushi maryama tayi,

"A Lagos"

"Kwarai ya taba zama a Lagos"

"To yanzu yana ina?"

"Yanzu yana Benue state"

"Yayi aure?"

"A,a amma dai yakusa wata yarinya yake so to kuma bata gama karatu ba"

Ajiyar zuciya maryama ta sauke saboda jin baiyi aureba,

"Wacce makarantar take yi?'

"Yarinyace fa yar secondary school sai yanzu ma ta shiga SS 1 fa, batafi 15 years ba"

Maganar ba karamin sukan zuciyar maryama tayiba amma haka ta daure,

"Ko zaki bani number dinshi zan kirashi amma kar kice masa kin bani, ko maganata ma kar kiyi masa"

"To adda maryam gashi"

Number dinshi khairat tabata tasaka acikin wayarta, tana dubashi a whatsapp taganshi sai dai da alamun yajima bai hau online ba fiyeda watanni hudu, amma ga hotonshi nan abakin wani rafi yana sanye cikin uniform dinshi na navy,

"Wannan antyn nawa da kika gani ita yake bi nikuma akwai wasu mutum biyu atsakaninmu amma dayan ya rasu"

"Allah sarki Allah ya jikanshi"

Haka suka yita hira har lokacin tashi yayi,

Cikeda murna maryama ta koma gida tasamu anty maijidda tabata labarin yanda sukayi da khairat,

"To yanzu dai kece zaki yimasa dabara irinta mata har hankalinsa yadawo kanki"

Cikin jin kunya da murna maryama ta tashi ta shige daki, number tashi ta kira cikin sa'a kuwa sai ta shiga, ta dan jima tana ringing kafin ya dauka,

Sallama yayi, "assalamu alaikum"

"Wa'alaikumussalam" ta amsa masa, duk da bai santa ba amma sai da ya lumshe idonshi saboda zakin muryarta,

"Shaddad ne?"

"Ehhh shine wake magana?"

"Wata baiwar Allah ce"

Shiru yayi yana sauraron daddadar muryarta, jin tayi shiru yasashi yin magana,

"Daga ina?"

"Daga wani gari"

Murmushi yayi wanda har saida tajishi acikin kunnenta,

"To ya akayi kika samu number ta?"

"Saboda nadamu dakai, kanada muhimmanci acikin rayuwata"

"To indai hakane maiyasa bazaki bayyana min kanki ba, meyasa zaki boye min ko ke wacece?"

"Zaka san ni wacece amma sai lokacin hakan yayi"

"To shikenan babu damuwa nagode"

Katse wayar tayi tana hamdala ga Allah saboda jin shaddad bai gwaleta ba, tasan insha Allah hakanta zata cimma ruwa.

Wurin anty maijidda takoma tafada mata yanda sukayi dashi,

"Ashema bashida wahalar kamawa indai kin dage nan da lokaci kankani zaki sameshi a hannunki wallahi"

Tun daga ranar maryama kullum saita kirashi awaya idan ya daga suka gaisa sai tace lafiyarshi ta kira taji banda text massages da take tura masa, nasafe daban, narana daban, na yamma daban, na dare daban,da yake yau da gobe sai Allah ko sati biyu ba ayiba yafara mayar mata da reply din massages din da take tura masa sannan shi dinma wani lokacin yana kiranta, shi dai bai san wacece ba amma muryarta tana bala'in yimasa dadi, da ya tambayeta sunanta sai tace sunanta Nana,

Kullum suna waya da ita tun bai damu da itaba har yazo yafara damuwa da ita idan bata kirashiba sai yaji duk yadamu,

Ahankali suka fara soyayya awaya, shidai bai san waceceba kuma yaji zuciyarsa ta aminta da ita,

Tana kwance tana baccin rana ya kirata, cikin yanayin bacci ta daga wayar,

"Hello Navy.."

"Nana ko bacci kikeyi natasheki?"

"Me kaji?"

"Naji muryarki ta canja ne"

Murmushi tayi, "bacci na danyi wallahi, nadawo daga islamiyya ne agajiye shine ina yin salla sai na kwanta"

"Ayya sannu, yau me aka koyo a makarantar?"

Murmushi tayi, "abubuwa da yawa ciki harda muhimmancin karbar kaddara kyakkyawa da mummuna"

"Wannan haka yake malama nana, har yau dai kinki turo min hotunanki naganki ko?"

"A'a ni baki nayiba"

"To me kikayi?"

"Nidai nafi son kazo kaganni face to face saboda kar kaganni a hoto kaga banyi maka ba"

"Babu wannan maganar, ai tundaga voice dinki naji kin yi min, kuma ko ya naganki zanci gaba da kulaki ahaka"

"Nidai fa sai kazo gaskiya.." Tafada cikin shagwaba,

"To shikenan tunda kince haka, zan samu lokaci na musamman nazo naganki, tunda kinyi min wayo kin hanani ganinki"

"Ba wayo bane ni nafi son kazo ne"

"Shikenan ai tunda nace zanzo amma sai nanda 2 months saboda yanzu aiki ya rikemu"

"Babu damuwa ina jiranka koma yaushe ne",

Haka suka cigaba da kasancewa a waya kullum sai dai kuma ita maryama kullum cikin fargaba take saboda bata san ya zata kasanceba idan har shaddad yazo yaganta amma anty maijidda tana kokarin kwantar mata da hankali da cewa ai yanzu idan yaganta bazai k'ita ba tunda ta nutsu ta zama irin macen da yake so, duk lokacin da anty maijidda tafadi haka sai taji hankalinta ya dan kwanta.

  Akwana atashi har sai da maryama da shaddad suka dauki kimanin watanni biyar suna soyewa awaya, kullum wuni suke suna hira, yauma kamar kullum bayan sallar isha tana kwance ya kirata,

"Kin fara bacci ne baby?"

"Idona biyu navy,me kakeyi yanzu?"

"Abinci nake ci, bude bakinki kema in sammiki"

Murmushi tayi, "to na bude.."

"To gashi nan tauna"

"Uhmmm wannan abinci amma badai dadiba.."

"Girkin hajiyata ne ai, albishirinki?"

"Goro" tafada tana daga kwance idonta a lumshe,

"Nazo Kaduna yau, gobe insha Allah zanzo abuja naganki..."

Zumbur ta mike daga kwancen da take jikinta yana rawa, sam bata son yazo idan yaga itace ya juya mata baya daga daddadar soyayyar da suke gudanarwa....


*_Ummi Shatu_*🏻
[5/16, 8:01 AM] Ummi Shatu🏻: _*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_


   *_NA_*

*_UMMI AI'SHA_*


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


    _*28*_

  ~~~Duk kokarinta na kar shaddad yagane rudun da ta shiga saida ya fahimta,

"Baby... Lafiya kuwa?"

"Lafiya lau mana, me kaji?"

"Ai najine kamar bakiyi murna da maganar zuwan nawa ba"

Murmushi ta kakaro tayi,

"Haba dai Navy kai kaji dadin danaji, tsabar dadi fa ji nayi kamar amafarki kake fada min shiyasa ma na burkice"

"Masha Allah, gobe iyanzu nasan nadade da ganinki,idanuwana sun jima da yin tozali da kyakkyawar fuskarki mai tsada.."

Shiru ita dai tayi tana jimamin wannan rana wacce Allah ne kadai yasan ayanda zata tsinci kanta,

"Yana ji kinyi shirune baby, Kodai baki shirya ganina yanzu ba nahakura?"

"Hmm ba haka bane Navy kawai dai ina tsoron abinda zaije yazo ne"

"Kamar me kenan?"

"Ina tsoron kar kaganni ka juya min baya, kamanta duk wadannan maganganun masu dadi da sanyaya rai da kake fada min, karka ganni ka tafi ka manta dani wannan shine abinda yake sakani cikin zulumi akoda yaushe, saboda idan har hakan takasance Allah ne kadai yasan makomata..."

"Ni bana son ki rinka furta irin wadannan maganganun, nariga da nafada miki babu wannan a tsakaninmu, bazan taba gudunki ba, idan ma tunani kike cewar idan naganki zanga bakiyi min ba to kidaina domin ni duk a irin kamar da naganki zanci gaba da sonki ahaka"

Kwallar idonta ta goge, "Allah yasa hakan takasance"

"Insha Allah hakance zata kasance baby, kidaina doubting akaina"

Sosai taji dadin kalamansa nan ta danji hankalinta ya kwanta,

Suna gama waya dashi ta tafi dakin anty maijidda wacce ke zaune tana goge kayan dadyn su A'isha,

Abakin gado ta zauna ta rafka tagumi ta juya tana kallon anty maijidda,

"Lafiya kuwa?"

"Anty Navy ne wai zai zo gobe, ina jin tsoro anty, kar yazo yaganni yagudu yabarni saboda ya tsaneni bai san cewar dani yake waya ba"

"Haba maryama ai maganar baya tawuce  maganar yanzu akeyi,sanin da yayi miki ada daban yake da wanda zaiyi miki ayanzu"

"Wallahi anty hankalina atashe yake"

"Ki kwantar da hankalinki insha Allah babu abinda zai faru"

Maganganu masu dadi anty maijidda tai ta fada mata har ta danji dama dama sannan takoma dakinta ta kwanta, yanda taga rana haka taga dare kwata kwata takasa bacci, sai sake sake da zuciyarta keyi akan haduwar da zasuyi da shaddad gobe bayan shekaru biyu da suka wuce rabonsu da ganin juna.

  Tunda asuba anty maijidda ta tasheta suna idar da salla suka shiga kitchen domin shirya abinda za a tarbi shaddad dashi,

Abinci kala kala aka yimasa da drinks masu dadi, ga hadin salad da pepe chicken agefe,

Karfe goma sha daya tuni sun kammala komai an shirya a falon baki,

Maryama na shirin shiga wanka kenan taji kiran shaddad ya shigo sai da gabanta yayi mummunar faduwa yau sunyi waya yafi sau goma dashi tun daga wayewar gari zuwa yanzu,

"Hello.."

"Nakaraso kofar gidan"

"Ok maigadi zai zo ya shigo dakai idan kayi hon, ni ban shirya bane yanzu zan shiga wanka"

"To ranki yadade afito lafiya.."

Kashe wayar tayi ta saki ajiyar zuciya, "yau dai za ayita takare ni maryama", tafada acikin zuciyarta,

Jikinta asanyaye ta tashi ta leka falo, "anty ya karaso"

"Ato sannunsa da zuwa, meye haka duk jikinki asanyaye, dan Allah ki saki jikinki kiyi kiyi ki shirya kifita"

Ciki ta koma ta shiga wanka har lokacin jikinta asanyaye yake, wanka tayi tafito ta zauna ta shirya, kwalliya tayi sosai da sosai tasha jan janbaki tazana jagira dama kun san maryama badai iya kwalliya ba,

Jar wata doguwar riga hadaddiya tasaka ta yane kanta da madaidaicin mayafi kashka shima kalarsa ja,babu karya tayi kyau iya kyau kuma ta fito a maryamanta,

"Wowww my daughter kin dauku fa, kinyi kyau ba karya.., Allah yabada nasara sai kin dawo"

Anty maijidda tace da ita cikeda karfafa mata gwiwa, fita maryama tayi gabanta yana faman faduwa ta nufi falon baki inda shaddad ke zaune yasha wani hadadden bakin yadi lallausa wanda yayi mutukar yimasa kyau,

Agogon azurfa ya daura yasa bakar hula,

Hango fuskarshi maryama tayi lokacin data je kofar falon, cikin sanyayyiyar muryarta tayi masa sallama ta shiga, cikin fara'a da shaukin kauna ya amsa mata hannunshi rikeda cup yana kurbar juice,

"Barka da fitowa sarauni...."

Zumbur ya mike ya ajiye cup din hannunshi saboda ganin fuskarta,

"Meya kawoki nan?" Yafada cikin tsawa wanda har sai da bangon falon ya amsa,

"Please shaddad kar muyi haka dakai, karka manta cewar kayi min alkawarin cewar bazaka gujeni ba aduk yanayin daka ganni.."

"Wai dama kina nufin kece Nana..?" Yafada yana nunata da yatsa,

"Tabbas nice shaddad..."

"To bani hanya inwuce, wallahi da ace cewar nasan kece da babu abinda zai kawoni nan.."

"Navy karka manta da alkawarin..."

"Wanne alkawari? Alkawarin da nayishi cikin rashin sani?, me zanyi dake, ko matan duniya sun kare kina zaton zan aureki? In aureki ince na auri wa? Ko kin manta da cewar nafi kowa sanin wacece ke, nafi kowa sanin halinki,ke mazinaciyace, marar kamun kai, jahila marar ilmin addini, marar tarbiya, mai kula maza, mai zuwa club, mai shan kayan maye, marar girmama mutane, idan kin manta to natuna miki, daga karshe ina son kiyi nesa dani saboda natsaneki tsanar da bata da adadi..."

Idanuwanta ne suka kada sukayi ja kamar yadda nasa idanuwan suma suka rine sukayi ja,

"Shaddad idan har kayi min haka baka yimin adalciba, idan har ban kasance dakaiba wallahi ina iya..."

"Wallahi indai sai kin kasance danine zaki rayu to sai dai ki mutu saboda bazan taba auren mace irinki ba.."

Yana kaiwa nan ya ketareta ya wuce zuciyarsa tana faman tafarfasa, ransa abace yafita ya shiga motarsa ya figeta,

Durkushewa maryama tayi awurin tana wani irin kuka mai cin rai, kokartawa tayi ta tashi ta nufi cikin gida, tana shiga falo taje tafada jikin anty maijidda tana wani irin numfarfashi,

"Anty...anty wallahi yabarni, yatafi..,anty yatafi,yace bazai aure ni ba,.... Anty mutuwa zanyi.."

Tana kaiwa nan ta sankame numfashinta ya tsaya cak, zuciyarta ta daina bugawa numfashinta ya daina fita, idanuwanta suka kakkafe....


  _Gaisuwa mai yawa ga yan uwa najini, Hajja (mom ihsan) & Halimatus Sadiya (stylish)_


*_Ummi Shatu_*

MARYAMA SARAUNIYA.. 24,25

[5/15, 10:04 AM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

    _Fatan alkairi ga duk masoyan littafin maryama sarauniya, masoya ina ganin sakonnninku kuma ina godiya, bazan iya zayyano sunayenku bane saboda yawanku amma sai dai duk wacce ta turo sakonta agareni mutukar ya riskeni to tana nan acikin zuciyata..._


   *_24_*


     ~~~Cikin lokaci kankani anty maijidda tasaka maryama awata islamiyya ta kudi wacce ake zuwa kullum da misalin karfe 10 nasafe a taso karfe 1 na rana,

Registration anty maijidda tayi mata har na naira dubu talatin sannan duk karshen term ana biyan dubu goma sha biyar amma kuma makarantar taci kudinta saboda akwai mazakuraren malamai masana wadanda suke koyarwa sannan duk dakikancin mutum cikin lokaci kadan zai kai matakin da akeso,

Dogon hijab har kasa ash colour shine uniform din makarantar dolen maryama haka ta burmashi ta tafi,

Tunda tafara zuwa makarantar kuma sai tazama busy koda yaushe bata da lokacin kanta gashi tana dawowa gida kuma anty maijidda zata fara dora mata wani sabon karatun, dan haka ba adauki wani dogon lokaci ba maryama tafara haddace azkar da hadisai marassa tsawo,

Yauma kamar kullum ta taso daga makaranta tana rikeda alqur'aninta tana kokarin karasawa wurin da ta ajiye motar da tazo da ita,

"Malama maryama..."

Juyawa tayi anan taga ya sayyadi dinsu ne malamin dake koyar dasu darasin alqur'ani,

"Ohh ni maryama nikuma da haka Allah ya jarrabeni wasu na sona nikuma ina son wani.."

"Ya sayyadi" tafada fuskarta babu yabo babu fallasa,

"Malama maryama kenan, wato nidai tun ranar da nafara tozali dake na yaba da kyakkyawar surar da Allah madaukakin sarki yayi miki..., ataikace dai maryama..., atakaice gaskiya kin kwanta min arai"

Murmushi tayi ta bude motar, "to ya sayyadi nagode madalla, yanzu sauri nake yi dan haka gobe ma karasa maganar"

"Ato a sauka lafiya malama maryama, Allah ya tsare"

Shiga motar tayi ta dauki hanyar gida tana yi tana tsaki saboda ita kullum burinta da addu'arta shine Allah ya hadata da shaddad amma maimakon su hadu sai haduwa take da wasu daban,

Kamar zata fashe da kuka haka ta shiga cikin gidan tana rikeda  kayan karatunta, a falo ta zube kayan sannan ta nemi wurin zama saboda yunwa takeji gashi ta gaji lis,

Anty maijidda ce ta fito daga cikin kitchen inda take shirya abincin rana,

"Yata andawo ne?"

Hamma tayi ta rufe bakinta sannan tayi magana "nadawo anty...."

"Angaji ko?"

Kai tadagawa anty maijidda tana jingina da jikin kujerar da take zaune,

"Ai naga alama tunda gashi nan ko magana bakya iyawa,bari nakawo mana abinci tunda na kammala.."

"Yawwa anty"

Cikin kitchen anty maijidda takoma taje ta zubo musu abincin data shirya jalop din shinkafa da taliya sai hadadden salad agefe da lemon kwakwa mai sanyi,

Tunda maryama ta zauna tafara cin abincin bata yi maganaba har saida tagama saboda yanzu tana dan iya cin abinci ba kamar da ba da sai ta wuni bata ci komaiba sai zallar tea empty,

Tashi tayi ta shiga daki tayi wanka tayi salla ta kwanta domin yin baccin rana amma kuma sai hakan ya gagareta maimakon ta runtsa ma sai tunanin abin sonta tafara yi dole babu yanda ta iya ta hakura ta tashi ta koma falo ta kunna kallo ta dauki wayarta ta kira Dada.

Yau tunda taje islamiyya taga wata bakuwar fuska a ajinsu wanda bata santa ba, yarinyar kyakkyawa da ita ya sayyadi yana yimata dori idan yafada itama ta fada ba karamin burgeta yarinyar tayiba saboda jin yanda take rero karatunta cikin kwarewa da iyawa gashi tsakiyar kur'ani ake biya mata kasancewar kowa dorinsa ake masa daban,

Sai da aka gama dorawa yarinyar sannan maryama taji ya sayyadi yace,

"Yawwa malama khairat Allah yabada Sa,a"

Juyawa yayi ga maryama "malama Maryam bismillah ko.."

Ita maryama ma sai taji kunya ta kamata saboda ganin ita ba wani nisa tayi acikin alkur'ani ba amma ga yarinya karama wacce bata wuce shekaru 25 ba ta kusa sauke alkur'ani,

Ahaka dai ta daure taje aka dora mata ta taso ta dawo ta zauna dama ita bata fiya shiga cikin yan ajinba saboda taga duk yarane ta girmesu ba sa'anninta bane,

Tana zaune ita kadai tana amsa wayar dr yazeed wannan yarinyar da aka kira da suna khairat tazo kusa da ita ta zauna tana murmushi,

Sallama tayi da dr yazeed ta juya wurin yarinyar,

"Adda maryam ina wuni..?"

Murmushin yake maryama tayi kafin ta amsa,

"Lafiya lau yagida"

"Lafiya lau, amma baki dade da fara zuwa makarantar nan ba ko saboda naga ban sanki ba, nima gida natafi shiyasa bana zuwa sai jiya nadawo, yan gidanmu duk suna Kaduna nan awurin yayata nake to shine last week muka tafi gida nida ita.."

Maryama dai sakin baki tayi tana ganin ikon Allah azuciyarta kuwa cewa take,

"Wannan yarinyar amma kinada surutu.."

"Kefa kema yar nan garince?"

Ta sake jiyo muryar khairat tana tambayarta,

"A,a nima zuwa nayi, a Lagos nake"

"Ohh Allah sarki nima kuwa ina son zuwa Lagos wallahi, amma dai ba canne asalin garinku ba?"

"Uhm.." Maryama tabata amsa a takaice saboda ita bata son yawan magana"

"Inane asalinku?"

"Jimeta.." Maryama tabata amsa cikeda kosawa,

"Ashe shiyasa naganki haka tubarkalla, Allah sarki"

Ita dai maryama shiru tayi mata tana binta da ido domin ita dai tunda tafara zuwa makarantar nan babu abinda yake hadata da yan ajin sai gaisuwa daga nan kuma bata shiga harkarsu saboda tana son taja girmanta..



*_Ummi A'isha_*🏻
[5/15, 10:04 AM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOC.(HWA)_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

    *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _*25*_

aishaummi.blogspot.com

  ~~~Zubawa yarinyar ido kawai maryama tayi tana ganin kokarinta yanda ta dage take tayi mata surutu kamar ba yaune ranar farko data fara ganinta ba, ita idan itace tayi wannan surutun ai sai kanta yayi ciwo,

"Adda maryam wacce makarantar kikeyi?"

Murmushine ya subucewa maryama saboda ita rabonta da makaranta ai tafi shekara biyar saboda tun tana 25 years tazama kwararriya kuma cikakkiyar likita,

"Ni ai najima da gamawa, yanzu bana zuwa school"

"Ohh Allah sarki nikam iya diploma nayi amma ana nema min admission a federal university dake Kaduna da zarar nasamu zan bar abuja nakoma can nafara zuwa makaranta"

"To Allah ya bada sa,a"

Ita dai yarinyar nan khairat haka kawai taji maryama ta burgeta saboda yanda take yin komai nata a nutse babu hayaniya gata yar gayu kyakkyawa fes da ita komai nata cikin jan aji,

Yayinda ita kuma maryama ta kosa da maganganun da khairat keyi mata saboda ita bata son hayaniya,alla alla take atashi ta tafi gida domin taji kanta yana neman ciwo,

Koda aka tashin ma biyota khairat din tayi har wurin motarta tana yimata zance,

"Adda maryam kibani phone number dinki mana saboda wani lokacin ko bazan samu damar zuwa ba sai in sanar dake"

Bata phone number din maryama tayi ta shiga mota ta wuce, tun daga kofar gida tasan yan makaranta sun dawo saboda yanda take jiwo hayaniyarsu,

Tana shiga kuwa ta gansu barbaje a falo suna ta faman cin abinci,

Yaran anty maijidda biyar duk maza dayace mace yar autar wadda yanzu take jss 1 a Nigerian Turkish school dake nan cikin birnin abuja,

"Ahh anty dama yau yan makaranta zasu dawo shine baki fada min ba?"

"Ina sone in baki surprise dama tun safe driver yatafi debosu"

Tasowa sukayi yaran dukansu suka rungumeta, itama rungumesu tayi saboda tana jin sonsu kamar ciki daya suka fito, zama tayi tana binsu da kallo daya bayan daya domin har yanayi suke yi da ita afusge, nan anty maijidda tafara tuna mata sunayensu domin duk sun giggirma shiyasa ma takasa banbancesu,

"Kinga sadiq nan ga faruk, ga haydar, ga usy nan ga kuma yanmata na nan aysha autata, ko autan mama" anty maijidda tafada tana dariya,

"Anty ai ke duk sunayen iyayena kika hada hadda fa sunan surikina baban shaddad"

"Shi din ya sunan baban nashi?"

"Sadiq wallahi"

"Ahh to kai sadiq kazama surikin adda maryama dan haka sai tafara girmamaka tun daga yanzu.."

Dariya maryama tayi tace "ai ko baki fada ba anty.."

Haka suka cigaba da barkwancinsu da raha itama ta shiga ta zauna suka fara cin abincin tare da ita domin ita bata san dadin yan uwaba tunda ta taso ita kadai take rayuwarta babu yaya babu kani, koda yamma tayi ma kwasarsu tayi suka fita yawo har anty maijidda basu suka dawoba sai daf da sallar magrib,

Agajiye suka dawo tana bawa anty maijidda labarin khairat yar islamiyarsu mai surutu, sai dariya suke anty maijidda nacewa,

"Kin hadu da aku kenan gashi ke kuma bakya son surutu"

"Ai anty wannan yarinyar tafi parrot..".

Haka rayuwar maryama taci gaba da kasancewa kullum bata fashin zuwa makaranta shiyasa sannu ahankali har tayi nisa a karatu, khairat kuwa koda yaushe a makaranta tana kusa da ita tana yimata zance shiyasa yanzu itama har ta saki jiki da ita tana biyeta suna hira, yauma kamar kullum bayan angama yimusu dorin karatu malamin ya fita maryama take cewa khairat,

"Khairat ina gayyatarki birthday dina gobe, ko baza abarki agida ba?"

"Za abarni mana anty, shekaru nawa zaki yi? Ko 26?"

Murmushi maryama tayi, "26 khairat ai sai dai yata kuma na 30 years zanyi"

Kwalalo ido khairat tayi amma bawai dan tayarda ba duk a zatonta maryama bata kai haka ba,

"To Allah ya kara nisan kwana zanzo"

Washe gari da yamma akayiwa gidan anty maijidda decoration aka shirya abubuwa duk da cewar ba wasu mutane akayi inviting ba iya maryama ne kawai sai yaran gidan sai ko khairat da tazo,ko ina maryama tayi binta take da kallo saboda yanda tayi kyau cikin blue din gown mai tsada wacce tasha stones ajiki,

Sosai suka taya maryama celebrating akaci aka sha sannan aka yanka cake, sai mangariba sannan khairat tatafi gida,wannan dalilin ne yasa washe gari itama maryama tace da anty maijidda zataje ta ziyarci khairat din ta kaimata ziyara tareda yimata bangajiya saboda zuwan da tayi mata jiya, duk da cewar yarinyar ba sa'arta bace amma tana son yin zumunci da ita,

Shiryawa sukayi ita da A'isha suka tafi, sai da ta biya ta wani store tayiwa khairat yar siyayya na kayan kwalliya da turare sannan suka je gidan wanda ke cikin unguwar mai tama,

Murnar da khairat tayi kamar zata yi hauka,cikin rawar jiki ta kaisu falon baki taje ta fara kokarin kawo musu kayan motsa baki, sai murna take ta kawo musu ruwa da lemo suka sha,

"Kuzo muje ku gaisa da antyn nawa to"

Fita sukayi zuwa wani falo inda matar ke zaune tana rubutu acikin wani littafi,da fara'arta ta karbesu suka gaisa suka tashi zasu fita, har sunkai bakin kofa kamar wadda aka cewa maryama juya sai ta jiyo nan idonta suka sauka kan hotonshi kato wanda ke manne ajikin bangon falon yana sanye cikin uniform dinshi na sojoji yayi kyau har ya gaji...

*_Ummi Shatu_*

Wednesday, 31 May 2017

MARYAMA SARAUNIYA..22,23

[5/14, 4:31 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _Wannan Shafin nakine yar uwa rabin jiki Khairat Dandawakee keda duk k'awayenki.._

    *_22_*


   ~~~Ganin tayi shiru ta shiga duniyar tunani yasa anty maijidda fahimtar cewa akwai wani abu dake damunta,

"Maryama meyake damunki ne? Ki fada min mana, nifa mamanki ce haifarki ne kawai banyi ba, wallahi dake da dan da nahaifa acikina duk daya nake ganinku babu banbanci..."

"Anty maijidda wallahi nima ina son nayi auren to amma wanda nake son aurar ne shikuma bani yake soba asalima ya tsaneni, rabona dashi anfi shekara daya da rabi..." Nan ta kwashe labarin komai ta sanar da anty maijidda,

Zuba mata ido anty maijidda tayi tana kallonta cikin tausayawa amma sai ta dake domin tana son karfafa mata gwiwa har ta samu wanda take so ta aura,

Dan haka cikin sigar lallashi anty maijidda tace,

"Haba maryama to kuma menene na daga hankali? Ki kalli fa irin baiwar kyau da Allah yayi miki, wallahi babu wani d'a namiji da zai ce bakiyi masa ba sai dai idan har yasan bazai sameki ba,

Kina da baiwar da kowanne namiji zai so ya mallakeki dan haka ko kaffara bazanyi ba idan na rantse miki kan shima shaddad din yana sonki, yatafi da tabon sonki acikin zuciyarsa, son da yake miki ma koke bakya yi masa, kuma koda bai fito ya furta miki ba afili to azuciyarsa hakane,

Dan haka ki kwantar da hankalinki ki nutsu Ki saurareni domin zan doraki akan hanya wacce zata kaiki ga muradinki har burinki ya cika,

Nafarko dai sai kin zama mai hakuri da juriya domin hakuri shine matakin da yake kai bawa ga kowanne irin nasara, idan kika kasance mai hakuri da juriya to wallahi zaki kai ga nasara, ba yanzu ba ko bayan aurenku da shaddad to sai kin zama mai hakuri da juriya, bari nabaki misali, zakiga akwai matan da suke zaune lafiya agidan mazajensu ko kansu ba aji amma idan zama ya hadaku dasu zaka fahimci tsananin hakurinsu ne yakaisu ga wannan matsayin wanda har ake yimusu kallon marassa matsala agidan aure, dan haka samun nasararki yanada alaka ga hakurinki da kuma juriyarki,

Abu nagaba kuma shine ki zama mai zurfin ciki marar tona sirrinta ko kuma matsalarta, dayawa daga cikin mata zaki samu bamuda sirri idan abu yana damun mu to sai kowa yaji bama iya rike abin acikin ranmu, to ki zama mai rike sirrinki duk abinda ya dameki Allah zaki fadawa sannan awurinsa zaki nemi sauki,

Wadannan abubuwan guda biyu sune masomin samuwar nasararki, sannan insha Allah a wannan zaman da zamuyi dake zan koyar dake abubuwa da dama kama tun daga kan girki, kula da maigida,gyaran jiki da sauransu, sai abu na karshe shine ilmin addini, ya zama dole maryama ki shiga makarantar islamiyya har yanzu baki makaraba,idan kika shiga makaranta zaki karu da abubuwa da dama kafin kibar garinnan, kin san kowanne namiji baya son jahilar mace domin tarbiyar yaransa zata samu nakasu,ita mace duk kyanta duk arzikinta duk kyawun nasabarta to mutukar bata da ilmin addini to wallahi ansamu matsala..."

Ajiyar zuciya maryama tayi sannan ta bude bakinta dakyar tayi magana,

"Nagode anty maijidda sannan insha Allah zanyi yadda kikace.."

"Yawwa 'yata, insha Allah sai kin mallaki abinda kike so"

Murmushi maryama tayi acikin zuciyarta tana addu'ar Allah ya amsa,

"Yawwa tunda kinzo sai ki rubuta min maganin ciwon baya wallahi bayana ciwo yake, baby likita.."

Murmushi maryama tayi saboda jin yanda anty maijidda tayi maganar cikin barkwanci.

  Tunda maryama tazo gidan anty maijidda tare suke shiga kitchen kullum su shirya abinci banda drinks kala kala da take koya mata gashi babu kunya ko wani abun ta hadawa mijinta da ita kanta sai tafito ta fada mata amfaninsa da kuma dalilin yinsa,

Satinta biyu da zuwa suka fara fita ganin gari, sune wurin shakatawa da super market da duk wani wuri wanda masu son bude ido suke ziyarta,gashi duk lokacin da suka fita to maryama bata dawowa sai da sabon saurayi,

Yauma kamar kullum agajiye suka dawo daf da sallar magrib, hannun maryama dauke suke da ledojin ice cream da cake ga wata ledar kuma mai dauke da dambun nama dan gaske,

Tunda suka fito daga exclusive supermarket wani guy yake faman binta ganin taki kulashi yasashi shiga motarshi kirar Lexus ya biyosu, har gida ya bisu amma ita sam bai burgeta ba, dakyar anty maijidda ta lallabata taje ta saurareshi nan dinma duk fuskarta babu walwala,

Bayanin kanshi yayi mata yace sunanshi mufid kallonshi kawai take kyakkyawa ne kuma daga gani dan manyan mutane ne amma bata jin zata iya amincewa ta aureshi, nan yabata phone number dinshi ta karba tana yatsina fuska, ganin kamar atakure take yasashi yi mata sallama ya tafi,

Tafiya take tana tsaki har ta shiga falon inda anty maijidda ke zaune tana cin dambun naman da suka shigo dashi,

"Yata mai farin jini wannan kuma waye? Ni ai da shi dinma kika aura.."

"Tab haba anty maijidda ni wallahi sai navy.."

Dariya anty maijidda tayi ta bugeta akafada cikin wasa,

"To shima ai naga dan gayune kakkarfa.."

"Kinga anty ni idan kina da pad kibani kawai uzuri gareni.."

"Kashhh ai kuwa saura kwaya daya kuma ina jin guda bakwai ne aciki da kamar tun dazu muka yi maganar ai da mun siyo wani, koda yake dayanma ai zai isheki.."

"Anty wallahi yayi min kadan"

"Kai maryama har kwana nawa kikeyi?"

"Kwana takwas anty"

Ido anty maijidda ta zaro tana kallonta,

"Kwana takwas? Amma idan kinyi aure zaki rinka shan maganin da zai rage miki kwanakin ko? Ai wannan kwanakin yayi yawa maryama gashi maza basa so saboda takura suke.."

Sunkuyar da kanta tayi saboda kunya ita kuma anty maijidda sam babu boye boye komai fada take yi afili baro baro....



*_Ummi Shatu_*
[5/14, 4:31 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

   _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _*23*_

aishaummi.blogspot.com

  ~~~Jin tayi shiru yasa anty maijidda taci gaba da fadin,

"Kidaina wani kunya da nuku nuku maryama, ba abin kunya bane dan kin san wadannan abubuwan,

Ni kinganni nan tun kafin nayi aure lokacin ina budurwa nasan abubuwa da yawa wadanda suka shafi al'amuran aure wallahi, ba laifi bane dan budurwa ta samu ilmi na rayuwar aure amma sai kiji wasu suna cewa wai yan matan yanzu menene basu saniba ai practical ne kawai basu yiba amma sun san komai, to wannan din shine daidai domin yanada kyau budurwa tasan hakan tun kafin tayi aure ba wai sai lokacin da tayi auren sannan zata fara tunanin tayaya zan zauna da mijina ko kuma me mijina ya kamata inyi masa ba,

Wallahi maryama nasan abubuwa da dama ina budurwa wanda wasu matan auren da yawa basu saniba kuma zurfi acikin karatun addini shine yakaini ga wannan matakin, saboda alokacin nakasance ma'abociyar karance karancen littattafan addini da sauraren wa'azozi wadanda malaman addini sukayi akan rayuwar aure, amma mu yanzu sai muke ganin abin banbarakwai idan budurwa tasan abubuwan da suka shafi, sai mu rinka yi mata kallon yar duniya ko kuma ai yar iskace, to wallahi ba iskanci bane kuma ba mummunar wayewa bace asalima wannan itace wayewa irin wacce musulunci ya tanada mutukar ba ta mummunar hanya tasan hakanba, shiyasa nake cewa zaki shiga islamiyya domin ina son ki kara samun gogewa da wasu tarin ilmin wanda ya shafi lamarin aure duk da nasan kin san dayawa daga cikinsu tunda ke likita ce amma wannan wanda zaki samu a makaranta daban yake,

Kuma nasan zakiyi alfahari dani koba yanzu ba saboda zaki gane cewar nayi miki babban gata wurin doraki akan turba mai kyau, sannan ko bayan kinyi aure zaki ji dadin zama da mijinki batare da matsala ba,

Shiyasa kika ga tunda nake babu wurin wacce nake zuwa neman shawarar wai ya zan yi inbawa mijina kulawa, domin nadade da sanin abubuwan da maza keso da wanda bakya so, shiyasa nazama star mai haskawa awurin mijina"

Dafa kafadar maryama anty maijidda tayi sannan taci gaba,

"Yanda nasamu fada awurin mijina kema haka nake miki fata yata, amma sai kin nutsu sannan kuma kin jajurce, akwai wa'azi dayawa da malamai suka yi akan yammata da masu shirin shiga dakin miji musamman dan abasu wani ilimi na yanda zasu kula da mazajensu ya kamata ki nemesu ki adana kuma ki rinka saurara sannan kinga idan har hakan ba abune mai kyau ba to da malamai basu bata lokacin su sun zauna sun rubuta ba, kamar yadda nafada miki ba iskanci bane kuma ba abin kunya bane saboda acikin magabata ma ansamu matar da tayiwa yarta nasiha tabata shawarwari lokacin da zata kaita dakin miji, hatta yanda yadace ta kula da mijinta da irin yanda zata faranta ran mijinta da abinda zata yimasa lokacin rayuwar auratayyarsu duk sai da wannan matar ta koyar da yarta,kuma hakanne ya kamata ko wacce uwa ta zama, mu rashin zurfafa awurin karance karancen addini da sauraren malamai duk shine ya mayar damu baya har muke aibanta abinda yake mai kyau,wallahi indai yarinya mai addini ce hadisin zadiz zaujaini kadai ya isa ya sanar da ita ilmin aure dan haka yana da kyau mu tashi mu nemi ilmi,

Wadannan kwanakin kamar yanda nafada miki sunyi yawa maryama musamman ma awurinki keda kike saka ran cewar zaki auri soja, kin san karfin sha'awar sojoji tafi ta sauran maza saboda su yanayin motsa jikinsu da shan wahalarsu, idan normal namiji zai bukaceki adare sau biyu to soja sai dai sau uku ko hudu, kinga kuwa indai hakane bazaku shirya dashi ba mutukar kina yin period har tsawon kwanaki takwas, wani namijin ma ko kwana hudu kikeyi sai kinga ya shiga damuwa, yanzu dai nasan bakya gane abinda nake sanar dake sai dai idan lokacin yayi zaki fahimta"

Mikewa maryama tayi cikeda jin kunyar anty maijidda ta nufi bedroom taje ta dauko pad din ta shiga dakinta,

Wanka tayi ta shirya cikin wasu pink din riga da wando masu laushi ta koma falo inda anty maijidda ke zaune tana kallon _Dhoom_ a tashar mbc Bollywood,

Zama tayi ta dauki robar dambun nama ta bude tafara tsakura tana ci,

"Maryama mai zaki dan dafa mana muci?"

"Duk abinda kikace anty"

"To dafa mana taliya sai ki danyi mana sos da kifi.."

"To anty.."

Tashi tayi ta ajiye dambun naman da take ci ta nufi cikin kitchen, tana ji wayarta na kara amma ko ta kula saboda tasan samarin dake damunta kullum ne,

Binta da kallo anty maijidda tayi fuskarta dauke da murmushi saboda da saninta take saka maryama aiki kamar su girki da sauransu saboda tana son kiwar dake tattare da ita ta ragu sannan idan tana yawan yin girki akai akai to hakan zai sata ta goge ta kware afannin girkin shiyasa yanzu yawancin girkin ita take barwa tayi musu kuma alhamdulillah tun ba ayi nisa ba har maryaman tafara kwarewa sabanin da wanda babu abinda ta iya ko dafa ruwan zafi ma wahala yake mata saboda ita tunda ta taso agidansu kuku ne yake dafa musu duk abinda zasu ci,

Jin karar wayar maryama yayi yawa ya cikawa anty maijidda kunne yasata dauka ta kaimata kitchen din,

"Ungo phone dinki samarinki sai cika min kunne suke da kira.."

Hannunta ta tsame daga robar da take wanke kifi sukumbiya da ruwan kal saboda magance karninsa,

Daga wayar tayi tana murmushi saboda ganin dr fahad ne wanda ke kiranta,

Makale wayar tayi akafadarta tafara amsawa yayinda anty maijidda ta juya ta fita daga cikin kitchen din,

"Hello fahad...." Tafada tareda jan sunan,

"Hy maryama ta, yakike?"

Murmushi tayi "lafiya lau fahad ya aiki?"

"Alhamdulillah maryama, ya lagos"

"Lfy, ni ina abuja ma nazo hutu"

"Ahh daidai kenan, zanzo miki mu gaisa sai mu gama maganar bikinmu ko, saboda nidai na kosa.."

Tana jin haka ta bata fuska kamar yana ganinta saboda ita ta tsani taji anyi mata zancen aure mutukar ba za a danganta maganar auren da shaddad ba,

"Ok, to kabari zan kiraka yanzu ina kitchen ne"

"Me ake dafa mana sarauniya?"

"Cikin kosawa da maganar ta amsa masa, "ina wanke kifine so we will talk later.."

"Ok queen bye"

Ajiye wayar tayi tana tsaki, "yara kanana basu taka kara sun karya ba suce wai kaine Sa,an aurensu saboda tsabar rashin kunya, ko idan sun aureni ina zasu kaini oho.."

Da haka ta samu ta kammala girkin tana yi tana ta korafi ita kadai,

A babban farantin tangaran ta zuba musu abincin itada anty maijidda ta fita,

A inda ta tafi tabar ta anan ta sameta tana rikeda remote tana rage volume din tv,

Ajiye abincin tayi wanda yaketa faman kamshi domin sos din tasha curry kala kala,

Fara cin abincin sukayi, girkin ya danyi sai dai kuma akwai yan kura kurai wanda ba arasa ba nan anty maijidda ta danyi mata gyaran da yadace saboda gaba....


*_Ummi A'isha_*