Thursday 22 December 2016

WANI HASKE...! 62-END

[9/12, 1:07 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE............!*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_61-63_


~~~Dabarun kulawa da mai gida wanda ba duk macece ta sansu ba yayarta ta fara bata, dafa kafadarta anty Bilkisu tayi tace da ita,

"My dear sister hak'ik'a nasan a zaman da kikayi ko kuma ki keyi agidan aurenki baki taba sanin mai ya kamata kiyiwa mijinki ko kuma ki aiwatar gareshi ba dan haka to ga shawarwari ko kuma ince hanyoyi guda goma sha biyar wanda suka kamata ace ko wacce mace ta sansu kuma ta kiyayesu domin samar da zaman lafiya tsakaninta da mai gidanta da kuma tabbatar da dankon kauna a tsakaninsu, ina so ki bude kunnuwanki sosai ki saurare ni da kyau domin fahintar karatun da zan koyar dake a halin yanzu,

Abu na farko da ya kamata ki sani kuma ki kiyaye shine daraja mijinki da kuma ganin girmansa da kimarsa, anan ina nufin kar ki kuskura ki fara kace nace da mijinki ta fannin zamantakewar auratayya kar wai dan kina ganin ya zama kamar abokinki ki rainashi, a'a anfi so mace ta zama tana bawa mijinta wani girma na daban acikin zuciyarta da kuma fili,

Na biyu kuma shine ki girmama iyayensa da yan uwansa tamkar yanda zaki girmama naki iyayen da yan uwan kar ki kuskura kiyi aiki da wannan karin maganar wacce hausawa ke cewa "'ba a iya musu ya dangin miji"',duk namiji yana son a girmama iyayensa da yan uwansa,

Abu na uku shine ki zama mai mutukar hakuri da juriya agidan aurenki domin zaman aure zama ne na hakuri da kawaici, ki k'i ji ki k'i gani sai ki zauna lafiya da mijinki,

Abu na hudu kuma shine kar ki zama d'aya daga cikin matan nan masu bayyanar da sirrin mazajensu da sirrin gidan aurensu ga kawaye ko kuma abokan gaisawa hakan haramun ne,

Sai abu na biyar shine ki kasance mai tattalin dukiyar mijinki ma'ana banda almubazzaranci da kayan miji, ki kasance mai tattalin dukiyarsa da kayansa domin kowanne namiji yana k'in jinin yaga yasha wahala ya nemo abu sannan an wulakanta,

Abu na shida shine kar ki zama mai yawan bin k'wakk'wafin mijinki, komai yake yi idonki da kunnenki akai, kar ki zama haka domin maza basu kaunar mace mai bin diddigin abubuwan da suke yi,

Abu na bakwai shine binciken wayar miji ko kuma abubuwan da ba su shafeki ba, kar ki zama mai yawan binciken al'amuran mijinki wanda bai saki aciki ba domin duk namiji baya son bincike da tuhuma,

Sai abu na takwas shine kula da abincin mijinki, ki zama macen data kware wurin iya girki domin hakan yana sawa miji yaji kin kara shiga cikin ransa,

Abu na tara shine ki zama macen da ta iya furtawa mai gidanta maganganu masu laushi da taushi, kar ki zama daya daga cikin matan da basu iya magana ba duk kalmar da tazo bakinsu sai su kwabawa mai gida ita,kar ki zama daga cikinsu,

Abu na goma shine kar ki yarda ki rinka daga muryarki sama da ta mijinki, akoda yaushe idan kina magana da mijinki to ya zamana muryarki ce a kasa tasa a sama,

Abu na goma sha daya shine ki zama mai iya kallon soyayya domin kallon da zaki yiwa mijinki ana so ya banbanta da kallon da zaki yiwa sauran mutane, idan kina kallon miji anfi son ki karkada idanuwanki ki sauya musu launi su koma tamkar kina jin bacci yanda zaki ja hankalinsa gareki,

Sai abu na goma sha biyu shine kula da tsafta, mata da yawa suna sakaci wurin kulawa da tsabtar jikinsu da ta muhallinsu, to agaskiya ya kamata su gyara saboda duk namijin duniya baya son mace k'azama yafi son kullum yaga gidanki a tsaftace jikinki a tsaftace,

Abu na goma sha uku shine ki zama macen data kware wurin iya kwalliya, maza suna son macen data iya kwalliya sosai kar ki zama irin matan nan da sam kwalliya bata damesu ba sai dai su zauna kullum fuskarsu a kod'e wannan kuskure ne babba domin maza da dama abinda ke sakasu kara aure shine matansu basa kwalliya kullum jiya iyau alhalin kuma ita mace "yar kwalliya ce koda yaushe ana son aganta dadas kamar fulawa,

Sai abu na goma sha hudu kar ki zama mai tsananin kishi domin zafin kishi baya haifar da zaman lafiya tsakanin mata da miji,

Abu na karshe nagoma sha biyar shine ina so ki bani aron hankalinki kiji abinda zan fada miki, abu na karshe ki zama yar soyayya, ki zama macen da ta kware a fagen soyayya sannan ki nunawa mijinki so da kauna, ki rinka zama kina shiryawa mijinki kalamai na kauna da soyayya wadanda zaki rinka tararshi dasu da zarar ya dawo gareki, ki nuna masa shi kadai kikeso acikin maza sannan shi kadai ne namijin da yake burgeki, ki kula da duk wani motsinsa da abinda yafi kauna atare dake, kar kiyi sakacin kasa gane yanayin da yafi sha'awar ganinki atare dashi da irin sutturar da yake son ki rinka sakawa aduk sa'ilin da kuke tare,

Ki nazarci abubuwan da suka fi sakashi nishadi atare dake sannan ki kasance akoda yaushe mai nuna son kasancewa dashi kar ki nuna gajiyawa dashi kuma kar ki rinka hanashi kanki aduk lokacin da ya nuna bukatarki domin maza suna tsanar mace mai irin wannan halin,

Ina so ki lak'anci gyara jikinki da kayan gyara wadanda ko a lafiyar jiki basa cutarwa kamarsu kankana, madara, zuma, da sauran yayan itatuwa, sannan ki tabbatar kullum jikinki yana fitar da kamshin dadi yanda mijinki zai rinka dokin zama kusa dake,

Sannan ya zama wajibi ki gane yanayin mijinki a makwanci domin mata da dama sunada matsala sai ka samu mace tafi shekaru goma da mijinta wata ma fiyeda haka amma bata taba samun gamsuwa atare dashi ba dalili shine tana jin kunyar ta sanar dashi ko kuma ta nuna masa hakan, wata matar kuma zaka samu mijinta sam bashida yawan bukata ita kuma tana bukatarsa to ba zata iya nuna masa ba haka zata hakura ta danne har sai lokacin da shi yaji yana bukatarsa dan kansa saboda ita tana kunyar nuna masa cewar tana bukatarsa to duk wannan kuskure ne, ita mace ana son ta zama mai kunya acikin mutane amma kuma acikin dakin mijinta anfi son ta zama fitsararriya wacce bata da kunya kuma hakika maza sunfi son irin wannan matar domin itace take gamsar dasu take yi musu duk abubuwan da suke so,

Ta cikin kissa da dabara zaki nunawa mijinki kina son kasancewa dashi wanda ta sanadiyyar haka shima zaiji yana bukatarki ba tareda ya shirya ba amma rashin wayewa ne da iya zaman aure mace ta shafe sama da sati uku ba tareda mijinta yaga wani abu a tare da ita yayi sha'awarta ba, (masu karatu kar kuce ummi A'isha ta cika rashin kunya bari nayi shiru haka amma agaskiya matan hausawa muna yiwa kanmu illa da yawa, kunya tana cutarmu sosai),

Dafa kafadar goodness anty Bilkisu tayi tana murmushi, "yanzu abinda nake so dake shine ina so ki zauna ki nutsu ki gane mijinki wanne irine a ta fannin rayuwar auratayya domin ki san irin abubuwan da ya dace kiyi masa dan ganin rayuwar aurenku ta inganta",

Jijjiga kai goodness tayi duk tana cikeda kunyar yayar tata "thank you anty"

Tun lokacin ta zauna da niyyar yin duk wasu abubuwan da yayarta ta koyar da ita, satinsu daya a lagos suka dawo gida, gidanta ta wuce bayan sun gaisa da mahaifinta, tana zuwa gida ta ajiye kayayyakinta tabi lafiyar gado ta kwanta sai da ta sha bacci ta more sannan ta tashi ta kikkintsa gidan tayi wanka tana tunanin jabir aranta domin yau ba suyi waya ba kwata kwata.

Kitchen ta shiga ta dafa indomie ta je falo ta zauna ta kunna tv tafara kallon Nigerian film, tana nan zaune har jabir ya kirata,

Murmushi tayi ta dauki wayar ta lankwashe murya "hello sir" wani yar yaji ajikinsa saboda yanda tayi maganar yau ya banbanta da na kullum,

"Ya gida?" Ya fada cikin muryarsa mai mutukar sanyi da dadi,

"Am cool sir but am still missing you" ta fada bayan ta sake kasa da muryarta,

"Gobe zan dawo ai, me zan siyo miki? Koda yake nasan abinda zan siyo miki" ya fada shima muryarsa kasa kasa,

"Sir what? Me zaka siyo min? Chocolate?" Ta ce dashi tana mai tausasa harshenta ta yanda muryar tata zata sake zaki da taushi,

"No,i will buy u hydrogen, so that kinga next time idan kika sake jin ciwo sai asaka miki" ya fada yana mai yin murmushinsa mai sanyi,

"No Sir, i don't like it, pls don't buy me hydrogen, chocolate nake so"

Wani irin shock yaji tun daga babban dan yatsan kafarshi har zuwa cikin kwakwalwarshi saboda yanda tayi maganar cikin shagwaba da kuma wani irin salo na daban.

"Where is my boy?" Ta sake fada ahankali domin jabir ya kasa sake magana,

"Gashi" ya fada dakyar, al'amin ya bawa wayar wanda yake kwance akan ruwan cikinsa domin ummu ta fita cikin gari, yana jinsu sunata shirmensu ita da al'amin, sunfi rabin awa sunata surutu kafin suyi sallama, karbar wayar yayi ya kashe yana kallon al'amin amma acan kasan ranshi tunani yake yi shin wanne abune yake shirin faruwa dashi ne yanzu akan goodness? Shi dai har yanzu he didn't believe that he's in love with her, sannan yasan yanzu dai bashida burin yin rayuwar auratayya da ita,ya shafe tsawon lokaci yana tunani amma ya kasa gane cewar ya kamu da soyayyar goodness ko kuma akasin haka.

Daren ranar yaje supermarket shida al'amin ya fara debowa goodness tsarabar chocolate din da take so amma yana son ya siya mata wani abu mai muhimmanci sai dai ya rasa abinda zai sai mata, tunowa yayi duk lokacin da yazo umarah ummun al'amin tana bashi sautun farin almiski duk da bai san abinda take yi dashi ba amma yasan dai yana da amfani agun mata, hakan da ya tuno ya sashi siyawa goodness farin muskin har guda goma sha biyu, wato dozin daya,

Wasu kayan bacci ya hango masu mutukar kyau da daukar hankali ajere a wani bangare, sai kawai ya tsinci kansa da son siyawa goodness kayan saboda yasan ba karamin kyau kayan zasu yi mata ba duk da ba wai zai bata su yanzu bane,

Wurin kayan yaje ya zabo guda biyu daya pink colour ce yayinda dayar kuma milk colour amma kayan sun tafi da hankalinsa domin shara shara ne sosai kuma masu santsi ne ba masu laushi ba, daga kirji anyi yar karamar bra ajiki sannan ga dan siririn hannun nan irin na bra, tsayinta bazai wuce iya cinya ba gashi yadin jikin rigar kamar net yake,

Gurin biyan kudi yaje ya biya kudin rigunan kowacce guda daya kimanin naira dubu biyu ta kama,

"Abbu Anty ka siyawa ko ummu na?"

Al'amin ya jefo masa wannan tambayar,

"Antynka na siyawa" ya fada atakaice,

"Shukran abbu i know this dress will suit my anty"

Murmushi yayi yaja hannun sa suka fita, koda suka je gidan ma bai bari ummu ta gani ba boyesu yayi cikin wata jakar kayanshi domin yasan idan ta gani ko bata fada masa ba sai taji bacin rai tunda ya fuskanci su mata komai abin yiwa kishine awurinsu.

***

Goodness kuwa ba karamin farin ciki ta shiga ba domin jabir bai taba yin doguwar hira da ita ba makamanciyar wannan tabbas yanzu ta kara samun karfin gwiwar nuna masa soyayya zalla gashi ta kara samun dama tunda yanzu su biyu zasu kasance agidan babu al'amin babu ummu al'amin.

  Tunda anty Bilkisu ta fada mata kayan gyaran jiki ta fara hadawa da kanta, yau kwakwa da dabino da kankana da zuma da peak ta ruwa ta bawa mai gadi ya siyo mata a kasuwa, gaba daya hadasu tayi tai blending dinsu acikin blender ta saka zuma ta juyo peak gwangwani daya ta ruwa ta saka acikin fridge, ita ta wuni tana sha har dare kasancewar da yawa tayi.

  Washe gari ma ranar da jabir zai dawo sai da ta sake hadawa cikin babban jug sannan ta shiga kitchen ta shiryawa jabir farar shinkafa da miyar hanta wacce tasha kayan lambu duk da dai bai kirata ba amma yayi mata text cewar karfe _4_ zai sauka.

Tana gama dukkanin ayyukanta ta shiga wanka ta sillo jikinta ta fito, kwalliya tayi ta gyara fuskarta sosai tasha jan baki dau akan lips dinta kusan kwalliyar da tayi yau tafi ta kowacce rana da ta saba yi tun bayan zuwanta gidan,

Doguwar riga roba ta saka baka mai layi layin kaloli ajiki kama tun daga blue, pink, red, white da sauran kaloli daban daban, rigar tsayinta har kasa yake sannan tanada gajeren hannu amma mai kama jiki ce sosai, kasancewar tayi gyaran gashi tun a lagos ya sata daura dan siririn bakin dan kwali akanta, kamar kullum yauma turaren _rocking girl_ ta fesa bayan ta shafa roll on kala daban daban, agogon dakinta ta kalla karfe 3:58 na yamma hakan ya sata komawa falo ta zauna ta fara kallon wani Nigerian film da ta tarar ana nunawa a tashar _African magic_ mai suna _ladies without borders_ kallonta take yi cikin nishadi har lokaci yaja sosai ba tare da ta sani ba, tana nan zaune taji alamun shigowar mota cikin harabar gidan, daga kai tayi ta duba lokaci,karfe _5_ saura minti _9_ ,zumbur ta mike ta leka _window_ jabir ta hango yana fitowa daga cikin mota yana yin waya hannunsa kuma dauke da littattafan addini wanda bata san ko na menene ba yana sanye cikin bakar doguwar riga ta jallabiya haka kansa ma kamar kullum yasa yar mitsitsiyar hula baka, cikin sanyinshi yake tafiya yana magana a waya,

Sai da ya bacewa ganinta sannan ta koma kitchen taje ta kwaso kayan abincin da tayi mishi ta zuba cikin wani katon _basket_ ta kinkima ta nufi sashensa, yana kwance sambal akan doguwar kujera kansa yana kallon sama har yanzu wayar yake yi bai gama ba amma ayanda ta dan fuskanta da ma'aikatan office dinsa yake wayar, kallonsa tayi ahankali daidai lokacin da taje wucewa ta gabanshi, "my cool ba dai tsayi ba" ta fada acikin zuciyarta domin gaba daya kujerar ya dan zartata kafafuwansa sun wuce hannun kujerar.

Kan dining ta wuce taje ta fara jera flaks din abincin, binta da kallo jabir yayi rigar jikinta gaba daya ta gama bayyanar da surar jikinta,kallonta yaci gaba dayi yana waya yana karewa halittar jikinta kallo a karon farko ya fara kissima yanda halittar ta take, doguwa ce ba can ba amma tanada kiba dan har tsayin nata ya buya ata sanadiyyar kibar tata, tanada dantse masu kauri gata da cikar kirji sosai, hips dinta da mazaunai kuwa abin ba acewa komai, fatarta baka ce dan har ya dan fita haske ma duk da cewar shima bakin ne, tanada round face ma'ana fuskarta a kewaye take mai dauke da fararen idanuwa madaidaita zagayayyu masu zubin k'wai, tana da yalwar gashin ido dana gira, sannan tanada zankadeden dogon hanci tamkar ummi A'isha ta sammata, bakinta shima zagayayye ne ba mai girma ba sannan ba dan tsul ba sai yar hab'arta wacce ta sake kawata fuskar tata domin harda dan beautiful point a tsakiyarta,

Idanuwansa ya sauke daga kallonta ya mayar dasu kan carpet, tana kammala jera masa abincin ta koma inda yake ta tsaya tare da zuba masa ido, zara zaran yatsun hannunshi ta kalla na tsakiyar da na kusa dashi duk sanye suke cikin zoben azurfa, yan yatsun nashi yake lank'wasawa suna k'as k'as, yayi kyau sosai yau dinnan,

Tana tsaye har ya gama wayar ya tashi zaune yana kallonta, "welcome sir"

"Yawwa thank you, ya hanyar okene kun dawo lfy?"

"Yes Sir lfy lau, ina al'amin?"

"Al'amin yana gaisheki shida ummunshi"

"Ina amsawa sir"

Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya shiga cikin bedroom dinshi, kujera ta samu ta zauna, mintuna goma sha biyar sai gashi ya sake fitowa cikin wata farar doguwar jallabiya bisa dukkan alamu wanka yayi,

Kan dining table ya wuce ya zauna ya zuba abincin data jere masa yaci, sai da ya k'oshi sannan ya dawo falon ya zauna ya dauki remote ya kunna tv ya kamo huda tv, hankalinta itama ta mayar kan tv din wurin kallon program din da suke gabatarwa a lokacin  _(financial crisis and Islamic analysis by sheikh Muhammad Akbar India)_,shima jabir hankalinsa duk ya tattara ga program din, suna nan zaune basu sake magana ba har lokacin sallar magrib yayi domin shi jabir mutum ne shi marar surutu, kallonta yayi yace,

"Bari naje salla nadawo"

"Adawo lafiya Sir" tace dashi, mikewa yayi ya fita ya tafi masallaci ita kuma taci gaba da zama awurin.

Sai misalin karfe 8:30 jabir ya dawo gidan har lokacin goodness na zaune a inda ya barta tana kallo amma ta canza channel daga huda tv zuwa mbc 3 abin ma dariya yaso bawa jabir lokacin da ya shigo ya ganta tana kallon cartoon,

"Kin zama al'amin ne?" Ya fada yana tsareta da manyan idanuwansa,

"No sir" ta bashi amsa,

"Koda yake naga kema banbancinku da al'amin din kadan ne" ya fada tareda zama akan kujera,

"No,nidai nafi al'amin sosai kadaina cewa mate dina ne shi" tafada cikeda shagwaba tareda tsuke dan madaidaicin bakinta, kallo ya bita dashi shidai shagwabar da take yi mishi ba karamin burgeshi take yi ba,

"To in banda yaro ki fada min wanda yake bada sautun chocolate" ya fada ahankali da niyyar sake zolayarta,

"Dan na bada sautun chocolate shine zaka cemin nima small girl ce? Am not small girl" tafada cikin wata shagwabar, murmushi yayi ya cire hular kanshi ya fara shafa sumarshi.



_*Ummi A'isha*_🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [9/12, 9:59 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE........!*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_64-66_

~~~<Kallonta yayi yana shafa kanshi, "keda al'amin daya nake kallonku"

"Ai kuwa tsakanina da al'amin akwai banbanci da yawa" ta fada tana mai saka dan yatsanta a baki tana tsotsa kamar wata karamar yarinya,

Murmushi yayi ya kalleta "to ina tsarabata ta okene? Ko baki kawo min komai ba?"

"Sir na kawo maka let me go and bring it here" mikewa tayi ta tafi sashenta taje ta kinkimo akwatin data ciko masa da kaya ta jawota ta kawo part dinsa, agabansa ta ajiye akwatin ta tsura masa ido ba tare data bude ba domin tana son taga yanda zai karbi kayan ko zai yi murna dasu ko kuma sabanin haka, jan akwatin yayi ya bud'e ya fara cicciro kayan ciki, kayan bacci ya gani irin nasu na maza riga da wando sai short trousers kala kala sannan ga jeans da t shirt nan suma kala kala, mamakine ya kamashi ya dan kalleta yana duba kayan shifa kusan ma idan ba mantawa yayi ba rabonshi da kananan kaya tun yana saurayi lokacin yana dan makaranta kuma yana kammala karatunshi ya tattara kayan ya bayar lokacin da zai dawo gida Nigeria,

"To in banda abinki goodness wadannan kayan ai na samari ne ni kuma kinga ni na nafara tsufa" yace da ita yana dan murmushi mai tsada,

"Sir kaima ai saurayinne tunda baka tsufa ba" ta bashi amsa tana kallon kayan,

"Na tsufa mana gashi nan har al'amin ya fara zama saurayi"

"Sir baka tsufa ba i swear, wlh idan ka saka zasu yi maka kyau"

"To nagode sosai, zan saka" ya bata amsa,

Mikewa tayi "sir sai da safe"

"Ok" ya fada a takaice, sashenta ta koma tayi shirin bacci tayi kwanciyarta, shi kuma jabir kallon kayan kawai yake yana mamaki acikin ranshi ta yadda goodness har tayi tunanin siya masa kaya, hakika hakan ya sashi farin ciki domin kyauta tana kara dankon soyayya ga ma'aurata,sannan ma ai abun burgewa ne tsakanin mata da miji yawan bawa juna kyaututtuka lokaci zuwa lokaci, cikin akwatin ya mayar da kayan aransa yana ganin dolensa ya sanya kayan tunda siyo masa aka yi.

  Washe gari da safe goodness ta tashi ta hada abin karyawa soyayyiyar doya da kwai da miya sai ruwan zafi, bata jima da kammalawa ba ta fita falo tana mopping tana sauraren wakar d banj, daga ita sai rigar bacci irin wacce Ummu al'amin ta aiko mata da ita a tsaraba waccen zuwan da jabir ya rakata,

Tana cikin aikin ne jabir ya shigo,kallonta yayi, "ki kawo min breakfast ina son zan fitane"

"Ok sir"

Da sauri ta shiga kitchen ta debo kayan ta nufi sashensa tana shiga bayan ta ajiye flasks akan dining  ta jiyo tana kallonsa,

"Sir the food is ready"

"Ok am coming" ya fada ahankali, juyawa tayi ta fita takoma sashenta tayi wanka a gaggauce ta fito ta shirya cikin riga da wando blue, tana daure gashin attach dinta da ribom jabir ya shigo cikin farar shadda yana ta zuba kamshi,

"Bari naje gidan Malam" yace da ita,

"Sir zan bika pls" tace dashi a shagwabance,

"Kiyi zamanki agida naje na dawo tsarabarsu zan kai musu kema idan nadawo zan baki taki"

Juyawa tayi ta fara doddoka kafa a kasa irin na yara idan suna rikici,

"Nidai,nidai, nidai sai na bika" haka taketa fada cikin muryar shagwaba,

"Zo mu tafi" yace mata yana mai juyawa dan tafiya, cikin sauri ta dauko doguwar bakar rigarta ta dora akan kayan jikinta ta nada dan kwalin rigar tabi bayansa, lokacin da taje inda yake yana tsaye yana jiranta, gidan baya suka shiga dukkansu driver yaja motar suka fita daga gidan, kasa kasa take kallonshi tana murmushi hakika tasan ta fara cin gari awurin jabir koda baya sonta tasan ya bata wani matsayi na daban,

Shiru motar har sukaje gidan malam, fitowa sukayi suka shiga gidan a tare, a soro suka sameshi yana karatun littafi mai tsarki, ba karamin dadin ganinsu yaji ba musamman ma ganin goodness tayi shiga irinta musulmai, cikin gidan ta shiga bayan sun gaisa ta barsu domin su tattauna.

Sun dade agidan malam tun safe har wurin 3 gashi taji dadin zama da mutanen gidan babu tsana babu tsangwama babu komai saima tarairayarta da suka yi koda zasu tafi kuwa tsintsiyar laushi da muficai suka babbata hakan ba karamin dadi yayi mata ba.

Suna komawa gida ta wuce part dinta,yau tunda bata wuni agidan ba ya sanyata niyyar yin tuwon amala miyar yauki, kitchen ta shiga ta soma aikace aikacenta daga falo ta kunna music tana jiyowa daga cikin kitchen din, jabir yana hangota ta window din dakinsa lokacin da ya shiga dakin.

Lokacin sallar magrib kafin ya fita ya shiga part dinta ya bata tsarabarta ta farin almiski amma kayan baccin da ya siyo mata ya boye mata su acikin dakinsa, karbar turaren tayi ta bude ta fara sinsina shi kamshinsa yayi mata dadi wannan dalilin ne ma ya sata zuba shi acikin ruwan da zata yi wanka, nan jikinta ya gauraye da kamshi bayan ta fito daga wankan, rigar bacci tasaka riga da wando masu laushi green ta dauki abincin jabir ta kai masa lokacin karfe 9 na dare,

A falonshi ta iskeshi yana kallo kamar koda yaushe jallabiya ce jikinshi, a gabanshi ta dire abincin,"ajiye min wannan cikin waccan drewar din" ya mika mata wani kwali, tashi tayi taje ta bude drewar din ta saka kwalin ta tura murfin drewar din dan ta rufe cikin tsautsayi ta matse da dan yatsanta daya,

"Ohhhhh" tafada da karfi tana jan dan yatsan amma yaki fitowa,

"Sir my pinger, i done close it with my pinger inside" ta fada tana mai ci gaba da janyo yatsanta,

Tashi yayi yaje inda take, da sauri yakai hannunshi mai mutukar taushi ya kamo nata yana ja, duk da tana halin jin ciwo sai da taji yarrrrrr! Ajikinta kamar yadda shima yaji,

Drewar din yayita kokarin budewa amma bata budu ba haka ya dage yanata kokarin zare yatsan nata amma abin yaci tura, dakyar da sudin goshi ya zaro yatsan nata wanda duk ya yanyanke da glass din jikin drewar din,

Yau za ayita kenan ya fada aranta domin yasan zasusha kokawa da ita kafin ta yarda ya saka mata hydrogen, ai kuwa hakance ta faru lokacin da taga ya nufi kan wata drewar domin dauko kwalbar hydrogen din da sauri ta tashi zata fita ta gudu, cikin azama ya kamo hannunta ya fisgota ta fado kanshi, tun kafin ya fara kokarin bude kwalbar ta fara kuka,

"Pls sir don't open it, pls i beg you" hannunta takai ta rike kwalbar, har lokacin tana rike acikin jikinshi, janta yayi zuwa kan kujera,

"Ki bari kadan zan saka miki"

"No sir ba sai ka saka ba"

Kwalbar ta rike sosai, dakyar ya murde hannunta ya kwace nan kuma sabon dambe ya tashi domin shigewa cikin jikinsa tayi ta kankameshi yanda har suna iya jiyo bugun zuciyoyin junansu,

"Sakeni nasaka miki"

"No sir" ta bashi amsa bayan ta sake makalkale shi tare da rirrike hannunshi duka biyu, hannun nata ya kamo ya dage ya bankare dan yatsan da taji ciwon ya zuba mata hydrogen agun,

Kuka ta kwalla ta fara yarfe hannunta tana kuka, tashi tayi ta fita tana kuka ta koma sashenta tana zuwa ta shiga bedroom dinta ta kunna air condition tabi lafiyar gado amma har lokacin yatsanta zugin zafi yake yi mata, mintuna kadan bacci ya dauketa.

Bata jima da yin bacci ba jabir ya shiga sashen nata tunda yaji tsit bata kunna kallo ba aranshi yace "yau hydrogen yayi aiki kenan tunda gashi har ya hanaki raba dare kina kallo"

A cikin bedroom dinta ya sameta tana bacci hannunta da taji ciwon ta ajiyeshi akan _pillow_ yana shan iska gashi ta rungume wata katuwar teddy wadda ta siyo daga lagos sannan da kadan tafi teddy din girma, murmushi yayi ya karasa gaban gadon yasa hannunshi ya dago hannunta da lausassan hannunshi mai laushin gaske wani zimmmmm!,yarrrr! Yaji ajikinsa,dan yatsan nata ya kalla sannan ya mayar mata da hannun ya ajiye shi akan pillow din kamar yadda tayi,

Juyawa yayi ya fita bayan ya kashe mata wutar dakin.

Washe gari da safe tana cikin kitchen tana aiki gefenta kuma wayarta ce ta ajiye ta kunna waka tana ji, tana aiki tana bin wakar _every body move your body now, tomorrow is a good day,good day, every body move your body now forget about the blue day, blue day imagine that_,

Daga ita sai wata yar karamar _vest_ yellow mai yar tattara agaban kirjinta, sai dan wandon vest din iya rabin cinyarta ta dage sai aiki take tana juyi tana bin wakar da take ji,

Ya jima akofar kitchen din a tsaye yana kallon ta acikin ranshi yana fadin "wannan yarinya kina adon tsokoki agidan nan" ,cikin kitchen din ya shiga ya mika mata wayarshi yana karewa kitika kitikan cinyoyinta kallo,

"Take this phone al'amin want to talk with you,ban san me yake son fada miki ba da sanyin safiyar nan"

Yace da ita cikin cool voice dinshi yana mai mika mata wayar tare da bin jikinta da kallo bayan ta makala wayar ajikin kunnenta ta matseta da kafadarta da kanta,

"Hello my boy what's happen?" Tafada bayan ta juyawa jabir baya,

"Anty albishirinki?"

"Goro my son"

"I have a dream about you yesterday" yafada da karfi,

"Oya fada min abinda ya faru my boy, am hearing you,tell me the story"

"Anty nayi mafarki kema kinzo wurinmu nida ummuna, munata wasa dake" ya kyalkyale da dariya bayan ya gama maganar,

"Woohhh al'amin and then what happened next?"

"Lala anty nidai nayi murna ko ummuna da abbuna ban bawa wannan labarin ba sai ke"

Thank my boy, ya sch dinka?"

"Anty sch dinmu alhamdillah har nayi sabon aboki mai sunana kuma shima yanada surutu Irina"

Jin hirar tasu taki karewa yasa jabir juyawa ya fice ya bar mata wayar taci gaba da surutunta ita da al'amin wanda sun shafe tsawon lokaci suna yinshi.

Misalin karfe _11_ na safe ta shiga wanka sai da ta gama sabe jikinta da kumfa ta ji motsi akan window da sauri ta wanke idonta ta duba nan ta ga kadangare lab'e ai cikin sauri ta finciki towel dinta ta daura jikinta duk kunfa ta fita ta kofar baya ta tafi sashen jabir, tana shiga ta sameshi zaune kan kujera a falo yana karanta wani littafi mai suna _tarbiyatul aulad_ kansa ya dago ya kalleta,

"Meya faru?"

"Sir is lizard inside my toilet"

Littafin ya ajiye ya tashi yafita, bayanshi tabi tana saka gefen towel dinta tana goge cikin kunnenta, koda suka shiga toilet din saura kadan jabir yayi dariya domin kadangaren ba wani babba bane jaririne saboda dan karami ne sosai ta wata yar karamar kofa ya samu ya shigo,

Daga kanshi yayi ya kalli pant da bra dinta dake shanye akan karfen jikin cikin toilet din, nan mamaki ya rufeshi domin bra din wata katuwa ce ba ta wasa ba haka ma pant din,

"Lallai yarinyar nan katuwa ce, yanzu wadannan kayan take sawa" ya fada acikin zuciyarshi domin ko Ummu lokacin da take shayar da al'amin bata saka bra rabin girman wannan,

Jelar kadangaren ya dauko ya jiyo zai fitar dashi, k'ara goodness ta saka ta fita da gudu, a falo ya ganta tsaye tana rikeda towel din jikinta wanda iya mazaunan ta kawai ya rufe amma cinyoyinta duk a bayyane suke,

"Look at what you called lizard,even you, you can catch this small thing but you are afraid " ya fada tare da fita da kadangaren, dawowa yayi bayan ya fitar dashi yaje ya toshe yar kofar da kadaganren ya shigo ya fito ya wuceta ya koma sashensa, a tsorace ta je ta karasa wankan ta fito ta shirya tayi kwalliyarta cikin riga da skirt jajaye masu adon stones ajiki.

Sashen jabir taje bayan ta shirya, baya falon yana cikin bedroom dinshi, a falo ta zauna tana yin game din _angry run_ a wayarta, ta dade a zaune kafin ya fito, kamshin turarensa kawai taji, tana zaune ahankali ta dan daga idonta ta kalleshi "wow" tafada ahankali, yayi kyau sosai acikin daya daga cikin kayan da ta kawo masa, jeans black sai t shirt coffee colour mai gajeren hannu, bashida maraba da saurayi dan _27_,

Sir this dress suits you" ta fada tana Mai cigaba da kallonsa,

"Thank you goodness" ya bata amsa bayan yaje ya zauna, ci gaba da satar kallonshi tayi domin ba karamin kyau yayi ba, tun daga ranar indai yana gida kullum kananan kayan yake sawa sai dai idan zai tafi masallaci ne yake saka jallabiya,duk lokacin da ya saka kananan kayan fito mata yake a saurayi sak domin kayan suna tsananin yi masa kyau.

  Misalin karfe _3_ na yamma tana cikin kitchen tana aiki kasancewar yau ranar juma'a ne, wainar fulawa take soyawa wani katon bera ta gani ya taho da gudu ya shige cikin drewar dinta ta kasa, tsalle ta daka ta kashe rishon ta fice da gudu ta tafi wurin jabir,

Bai dade da dawowa gidan ba yana kan dining yagama cin abincin daga shi sai dogon wandon farar shaddar da ya saka da farar singileti ta maza, arude goodness ta shigo cikin falon nashi,

"Excuse me sir, sir rat ne acikin kitchen"

Kallonta yayi abin nata ma abin dariya ita komai tsoronshi take ji kenan "beran ma tsoronshi kike ji?"

Yace da ita "sir, sir katone fa i swear"

"Its ashamed, ke komai tsoro yake baki" tashi yayi ya fita ahaka ba tare da ya saka riga ba, bin bayanshi tayi tana lallabewa har suka je kitchen din, yana bude drewar din beran yayi tsalle ya fito ya wuce ta window ya fice, juyowa yayi ya kalleta,

"Nasha fada miki ki daina barin windows dinki a bude saboda ta nan duk abubuwan da kike tsoron zasu rinka shigowa"

"Yes sir i will maintain it sir" ta bashi amsa, wainar fulawar da take soyawa ya kalla tasha kayan hadi gashi tasha curry tabada kala mai kyau,

"Wannan bakin ya iya kwadayi" ya fada ahankali yanda ba zata ji ba, bata jin ba kuwa kawai dai ta ga dan mitsitsin bakinshi ya motsa kadan amma bata san abinda yace ba, juyawa yayi ya fita ita kuma ta koma taci gaba da suyar wainar fulawarta.

  Wurin karfe _5_ tana zaune a falo tana cin wainar fulawar da tayi sai gashi ya shigo yanata zuba kamshi.

"Bari naje aski na dawo" yace da ita yana mai gyara zaman hularshi,

"Sir zan rakaka" ta fada cikin shagwaba,

"Aski fa zanje, barbing"

"I know sir, zan rakaka pls"

Girgiza kai yayi wato yarinyar nan fitinanniya ce itama nan gaba daina gaya mata zaiyi idan zai fita saboda yaga tana ji da rigima,

"Yi sauri kizo mu tafi"

Zumbur ta mike ta tattare kwanukan wainarta takai kitchen ta shiga bedroom ta shafa powder ta sako doguwar bakar riga ta fito suka tafi. Lokacin da suka je shagon askin a mota ya barta ya shiga ciki aka yi masa bai wani jima ba ya fito yazo ya sameta suka tafi wata unguwa inda zai gudanar da wata tattaunawa da wani mutum acanne ya dade sosai kafin ya dawo suka koma gida.

  Ranar Sunday wuni tayi tana wankin kayanta sai yamma ta gama bayan ta gaji likis, dakyar ta iya yin abincin dare taliya da miya, na'a na'a ta dafawa jabir ta kai masa sannan ta koma sashenta tayi wanka ta saka kayan bacci lokacin karfe _8_ na dare, zama tayi ta fara kallon wani Nigerian film mai suna _the night of spirit_ film din ya tara abubuwan tsoro daban daban amma haka ta tsaida idonta take kallo, tana zaune part one ya kare aka saka part two shima ya kare aka saka part three duk tana zaune tana kallo, ba agama film dinba sai karge 1:30 nadare, tana gama kallon ta karkashe komai taje ta kwanta anan kuma tsoro yace salamu alaikum domin abubuwan da ta gaggani a film dinne suka fara dawowa kwakwalwarta gashi wani irin kukan aljanun take ji acikin kunnuwanta, tsorone ya kamata sosai acikin duhun daren take ganin halittun data gani dazu,

Kun san goodness da tsoro ai aguje ta tashi ta bude kofa ta nufi sashen jabir da gudu kanta babu dan kwali kafarta babu koda takalmi.


*_Ummi A'isha_*🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [9/19, 9:16 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE....!*

_*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_



_67-70_

~~~ A firgice ta kama kofar falon jabir ta bude ta shiga jikinta yana karkarwa, acikin falonshi ta hangoshi yana tsaye akan darduma yana salla, yana sanye da kayan bacci light blue masu santsi riga da wando,

Lungun kujera taje ta takure tana jiranshi ya gama, amma da yake doguwar sura yake karantawa sai da ta shafe wurin mintuna 20 kafin yayi sallama ya juyo yana kallonta, duk kitson attach din kanta ya gama yamutsewa sannan kallo daya zaka yi mata ka fahimci cewar a tsorace take ainun,

"Goodness meya faru?" Ya tambayeta yana mai kallonta,bakinta yana rawa tace,

"Sir i can't sleep inside my room"

"Why?" Ya sake tambayarta,

"Sir i can't, am afraid" ta sake bashi amsa,

"What do you want now?" Ya tambayeta,

"Sir i want to sleep inside your room pls"

"Ok shiga ki kwanta" yace da ita,

"No Sir ka gama sai mu shiga tare" ta fada tana tattara gashin kanta,

Bai sake magana ba ya tashi ya gabatar da shafa'i da wutri, duk tana zaune agefe tana kallonshi, hannuwanshi ya daga sama ya fara addu'o'i bayan yayi sallama, mintuna kadan ya shafa ya tashi ya juyo ya dan kalleta,

"Shigo" ya fada a takaice, tashi tayi sim sim sim ta bishi tana mai cigaba da karkarwa, wannan shine karo na farko da ta fara shiga bedroom dinshi, wani sanyin kamshi ne mai dadi ya bugi hancinta lokacin da ta saka kai domin shiga, katon gado kirar royal bed ta gani coffee colour wanda akalla mutane sama da guda biyar zasu iya kwana akai, gefe mirror ne cike da turarurraka kala kala, daga bari daya kuma dan karamin library ne cikeda littattafan addini iri iri sannan ga wani kebantaccen wuri nan wanda da alama wurin salla ne,

"Kije ki kwanta" ya fada yana nuna mata gadon,

Ahankali ta hau kan gadon taje jikin bango ta takure tana mai runtse idonta,

Zama yayi agefen gadon yana kokarin bude laptop dinshi nan ya fara daddannata wanda bata san iya adadin lokacin da ya dauka ahaka ba bacci yayi gaba da ita.

Ya dade azaune yana amsawa mutane fatawarsu wato tambayoyin addini ta kafar sada zumunta na facebook kafin ya kashe laptop dinshi ya juya ya kalli goodness tana kwance rub da ciki tana makalkale da pillow tana ta sharar baccinta,

Light din dakin ya kashe ya kwanta agefen gadon ya fara addu'a,mintuna kadan da fara baccinshi yaji goodness tana k'ara tana tuje tuje, mafarki take yi wai aljanun da ta gani a film din dazu sune suka biyota bakinsu duk jini suna son shan jininta,

Wata k'ara ta sake saki cikin razani ta farka tana zare idanuwa, kusa da jabir ta matsa ta kwanta agefenshi ta kankameshi,

"Goodness wai meke damunki ne?"

"Sir wani film na kalla dazu shine nake tsorata" ta bashi amsa cikin razani,

"Shiyasa na hanaki kallon dare amma kullum bakida aiki sai in dare yayi ki zauna kallo wani time dinma har 3 kike kaiwa kina kallo"

"Sir ai nadaina, daga yau bazan sake ba"

"Shaidan ne kawai yake razanaki domin kyakkyawan mafarki daga Allah ne, mummunan mafarki kuma daga shaidan haka annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam ya fada, tsaya nayi miki addu'a" addu'ar da akeyi idan anyi mummunan mafarki ya fara karanta mata a tsakiyar kanta wato _Allahumma inni a'uzibika min sharri fi manami an yadurruni fi dini wa duniyaya_,yana gamawa ya karanto ayatul kursiyyu da amanar rasulu sai falaqi da nasi ya shafa mata a fuskarta, wani sanyi taji yana shigarta, lafewa tayi luf acikin jikinsa tana shakar daddadan kamshin da yake fita daga jikinsa na turaren madinatul akram, lokaci k'ank'ani bacci ya sake dauketa, yana jinta tana fitar da numfashi ahankali wanda yake sauka akan kirjinsa, gaba daya jikinsa yarrrrrr! Yake jinsa amma ya daure ya kyaleta ajikinsa yau kadai domin itama taji irin dumin da mata ke samu ajikin mazajensu, bedside lamp ya kunna ya kalli agogo _2:50_ na dare, fitilar ya kashe ya mayar da idanuwansa ya lumshe har shima baccin yayi nasarar saceshi.

  Sai misalin karfe _6:15_ jabir ya iya farkawa, lokacin gari har ya soma haske, idanuwansa ya bude ya saukesu akan goodness wacce ke mak'ale dashi tana bacci gaba daya ta kanannade ajikinshi ta cusa fuskarta cikin kirjinshi asalima bakinta akan kirjinshi yake, shi kuma ya zagaye hannuwanshi ya rungumeta wanda bai san lokacin da yayi hakan ba amma yasan acikin baccine,

Ahankali ya zame jikinsa ya tashi ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito yazo yayi salla yana idarwa ya fara kallon gadon inda goodness ke kwance shidai rabon da ya rasa sallar asuba har ya manta saboda kullum cikin jam'i yake yin sallarsa, jijjiga kai yayi acikin zuciyarshi yana cewa "kenan kwanciyar da yarinyar nan tayi ajikina ne yasa na makara"

Alqur'ani mai girma ya bude ya fara karantawa har rana ta fito sannan ya rufe ya tashi yana kallon goodness, idonta ta bude ta kalleshi,amma ta kasa tashi, yana nan tsaye yana uzurinsa har ya gama ya shiga toilet domin yin wanka tana ganin haka tayi maza ta tashi tana duba wurin da take kwance duk gurin ya baci da jinin period din da yazo mata bata sani ba cikin dare, pillow ta dora awurin ta tashi ta fita ta koma sashenta domin shiryawa.

  Bai jima ba ya fito daga wankan anan yaga bata dakin, zobenshi daya yaga ya fice daga dan yatsanshi hakan ya sashi matsawa gaban gadon ya fara dubawa, pillow din data dora akan wurin da ya baci ya janye nan yaga wurin ya gama baci da jini,

"Oh shiyasa dazu taki tashi? To ai dole nasan zata dawo tunda ban bata always din da na siyo mata ba" ya fada aranshi, pillow din ya mayar ya saka kamar yadda ta ajiye, a kasa gefen gadon ya hangi zoben nashi ya dauka.

Shiryawa yayi cikin farin boyel ya gyara sajensa da dan madaidaicin gemunsa,

Ita kuwa goodness tana zuwa dakinta wanka ta shiga amma koda ta fito sai ta tuna da bata da always ko daya, babban towel ta daura ta dauki wani dan madaidaici ta yafa ta rufa akanta tabi ta kofar baya ta shiga sashen jabir,

Yana tsaka da fesa turare ta shigo,

"Um, uhm good morning sir" ta fada kanta a sunkuye,

"Morning" ya fada atakaice,

"Sir wannan month din baka kawo min...!" Shiru tayi ta kasa karasawa,

"What?" Ya tambayeta yana kallon fuskarta,

"Sir.....!" Ta sake yin shiru,

"Go and carry it inside that drewar" ya nuna mata bedside drewar dinshi, wuceshi tayi taje ta dauko guda biyu tazo zata fita,

"Kar kiyi breakfast dani ina azumi" ya fada cikin muryarshi mai dandano,

"Ok sir, but sir pls don't  lock your room,i want to clean it before you come back"

"Ok" ya fada ahankali, mitsitsin bakinshi ta kalla ta fice tana mai tunanin hali irin nashi, yanada kyawawan halaye wadanda kusan ma ita sune suka jata har ta fada cikin kaunarshi,

"He's a nice person" ta fada lokacin da take shiryawa, lokacin da ta gama kintsawa ta fito kitchen ta shiga ta hada tea tana tsaye tana sha ya shigo yayi mata sallama ya fita, agurguje ta shanye tea din ta tafi sashen jabir, gaba daya zanin gadon nashi ta yaye da pillow case din takai cikin toilet, acikin toilet din taga kananan kayanshi da kayan baccinshi acikin laundry basket, hadasu tayi duka ta wanke taje ta shanya ta koma ta wanke cikin toilet din sannan ta gyara dakin ta fesa room freshener,

Sashenta ta koma ta dora girki tunda shi jabir yana azumi kayan shan ruwansa daban zata yi masa dama ta saba ko lokacin da tana gida tana yiwa mahaifinta girkin shan ruwa,

Dankali da kwai ta soya masa ta dama kunu sannan ta dafa masa cous cous da miya, fruit ta gyara masa tayi musu design mai kyau, ita kuma ta hadawa kanta lemon kankana da kwakwa wanda ya zame mata jiki saboda kusan kullum sai ta shashi.

Bayan ta kammala komai ne taje sashen jabir ta shiryasu akan dining ta kwashi kayan da ta wanke ta zauna a falonshi ta fara goge su. Sai _6_ daidai ya samu damar shigowa gidan domin yau meeting yayi da directors dinshi a office sai 5:30 suka fito,

Yana shiga falonshi ya sameta tana goge kananan kayanshi da kayan baccinshi, tana yi tana rera yar wakarta,

"Welcome sir" tace dashi lokacin da ta dago ta ganshi,

"Thank you" ya fada ya wuce cikin dakinshi, dakin ba karamin kyau yayi ba gashi sai kamshine ke tashi, koda ya shiga cikin toilet dinma abin haka yake komai fes fes tsaf tsaf, cikin nishadi yayi wankanshi ya fito ya shirya ya fita lokacin an kira sallar magrib, hannunsa rikeda dabino yana ci ya sameta a falon har lokacin gugar take yi,

"Sir sannu" ta fada ahankali,

"Yawwa" shima ya fada ahankali tare da fita, bai dade da fita masallaci ba ta gama gugar kayan ta koma sashenta.

Sallar magrib kawai yayi ya dawo gida yasha ruwa, lokacin isha nayi ya koma masallaci, bashi ya dawo gidan ba sai wurin karfe 9,

Sashensa ya shiga ya yi wanka bayan ya dawo daga mosque, kayan bacci yasa maroon colour masu taushi, kamar kullum laptop dinshi ya bud'e ya shiga net ya fara amsa tambayoyin jama'a, yana nan zaune agefen gadonshi laptop din na ajiye akan cinyarshi goodness ta bude kofar dakin ta shigo, daga kai yayi ya kalleta tana sanye da kayan bacci doguwar riga mai rubi biyu iya gwiwarta light purple kanta sanye da hular roba baka, tana rike da karamin tea flask wanda ta zubo masa dafaffen shayin na'a na'a aciki,

"Weldon sir" tace dashi tareda karasawa gaban gadon ta ajiye masa tea flask din akan dan karamin stool dake ajiye agaban gadon,

Da mamakinsa sai yaga ta haye kan gadon tana cewa "sir aikin office ne kake yi har agida"

"Ba aikin office bane" ya bata amsa a takaice, pillow taja ta kwanta ta dora kanta akai tana mai fuskantar jabir wanda ya tsaida idonsa akan laptop din dake gabanshi lokaci lokaci kuma yana dan kurbar shayin dake ajiye agefenshi,

Fuskar nan tashi mai kyau ta zubawa ido tana kallo ko kiftawa bata yi, kamarsu daya sak da al'amin danshi sai dai shi al'amin din yafi shi hasken fata domin ummunshi ya dauko a haske amma baya ga haka komai na al'amin irin nashine,

"Oh my al'amin am missing you" tafada ahankali,

"Abbu bani aron wayarka" ta fada tana daga kwance, ahankali ya jiyo ya kalleta tareda maimaita sunan aranshi "abbu" yafada acikin zuciyarshi,

"Me zaki yi da wayata?" Ya tambayeta, "pls abbu i want to hear the voice of my lovely son al'amin" ta fada cikin shagwaba, daga kai yayi ya kalli agogo karfe _10_ saura yan mintuna,

"Yanzu al'amin yayi bacci amma gashi ki kira kiji" mika mata wayar yayi ta mika hannunta ta karba ta fara neman layin ummu al'amin din amma wayar akashe, ta dade tana kiran wayar amma bata samu ba dole ta hakura ta mika mishi,

Kallonsa tayi tace "abbu kayi min addu'a ina son zanyi bacci"

Dago kanshi yayi ya kalleta,

"Wacce irin addu'a?" Ya tambayeta tare da mayar da hankalinsa kan laptop dinshi,

"Irin wacce kayi min jiya, ban taba yin bacci cikin nutsuwa kamar wanda nayi jiya ba"

"Kawo hannuwanki inyi miki" ya fada ahankali, zaune ta tashi ta matsa kusa dashi ta hada hannuwanta wuri daya ta mika masa tafin hannuwan nata, addu'o'in kwanciya bacci ya karanto yana tofa mata acikin tafin hannunta har ya kammala ya dubeta,

"Ki shafe jikinki"

"Thank you abu al'amin" ta fada tana shafe jikinta kamar yadda yace, hakan data fada sai ta tuno masa da matarshi Salma wato ummu al'amin.

Kwanciya ta koma tayi tana kallon kyakkyawar fuskarshi har bacci ya dauketa, sai da ya kammala abinda yake yi sannan ya tashi yaje toilet ya dauro alwala yakoma inda ya keb'e domin gudanar da ibadarsa ya fara sallar nafila.

Can tsakar dare goodness ta farka daga bacci tafara dube dube domin taga gadon wayam babu jabir, acan gefe ta hangoshi yana salla, jijjiga kai tayi ta koma ta kwanta tana mai jinjina rikon addinin da jabir yake dashi, sai wurin _3_ ya hawo gadon ya kwanta har lokacin goodness idonta biyu tana kallonshi, addu'o'in kwanciya bacci yayi kafin ya kashe wutar dakin,

Minti 10 atsakani taja jikinta taje ta shiga jikin jabir kamar yadda tayi jiya, cikin barci ya rungumeta tareda k'ankameta ba tare da ya sani ba, tamkar zasu mayar da junansu cikin cikinsu haka suka yi.

  K'arfe _5:30_ ya samu ya farka bakinsa dauke da salati,mamaki ne ya kamashi jin yadda shi da goodness suka makalkale junansu kamar wasu tif da taya, hannuwanshi yasa masu mutukar taushi ya janyeta daga jikinsa ya tashi ya shiga toilet, bin bayansa da kallo goodness tayi aranta tana mai burin inama zasu dawwama ahaka ita da jabir.

Tun kafin ya dawo daga masallaci ta koma sashenta tayi wanka ta shirya ta shiga kitchen ta hada abin karyawa ta dauka ta kaiwa jabir nashi sashensa sannan ta dawo dakinta tafara gyara kayan sawarta tana shisshiryasu cikin sif,

Stool din madubi ta dauko ta taka tahau dan ta dora wani akwatin kayanta asama, cikin tsautsaye ta goce ta fad'o, gefen kunkuminta sai da ya bugu da gadonta, tashi tayi kokarin yi amma ta kasa dan haka ta ci gaba da zama awurin har jabir yashigo yace mata ya tafi office.

Tunda ta buge agefen kunkumimta ta baya take tafiya dakyar tana dingishi, da haka ta samu tayi duk wasu ayyukanta har yamma tayi jabir ya dawo, ganinta tana yin dingishi ya sashi tambayarta abinda ya sameta, bata boye ba ta sanar dashi,

"Ok dauko Robb acikin dakina sai ki shafa awurin bayan kin gasa gun da ruwan zafi" ya fada yana kallonta,

"No abbu" ta fada tana mak'e kafadarta,

Bai sake cewa komai ba ya tashi yafita ya tafi salla sai da ya dawo yana zaune akan gado hannunsa kuma rikeda littafin _sahihul bukhari_ ta shigo tasha kayan baccinta doguwar riga fara sai faman kamshi take zubawa,

Kan gadon ta hau ta kwanta tana gyara hular kanta, mikewa jabir yayi ya ajiye littafin hannunsa akan drewar din gadon ya shiga toilet, ruwan zafi tafasasshe ya taro acikin karamin baho ya dauko towel karami wanda yake goge jikinshi dashi idan yayi wanka,

Tana kwance ta yi rub da ciki tana fuskantar bango yazo inda take,

"Oya tashi" yafada ahankali,

Tashi tayi babu musu ta juyo tana kallonsa ganinshi da kayan gashi ya sanyata mikewa da sauri domin guduwa, robar ruwan zafin ya ajiye ya yi sauron rikota babu zato ta fado jikinsa ta baya nan ya rungumeta baiyi wata wata ba ya dage rigar dake jikinta nan take farin pant din dake jikinta ya bayyana, da saninsa ya sake dage rigar domin yana son ganin kalar bra din da ta saka, itama fara ce sol,

"Hmmmm to match akayi kenan, komai white, that's good" ya fada acikin zuciyarshi, jin tana kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata ne ya sanyashi dawowa daga duniyar tunanin da ya lula, towel din ya tsoma cikin ruwan zafi ya dauko shi yana tiriri gashi harda ruwan ajiki ya manna mata akan kunkuminta,

"Abbu, pls da zafi ka bari" ta fada arude, bai kulata ba ya sake tsoma towel din ya ciroshi ya dora mata akan wurin gashi idan ya dora baya daukewa har sai ya huce, haka yayi ta mata har sai da ya tabbatar gurin ya gasu sannan ya kyaleta,tashi tayi tana goge gumin da ya feso mata agoshinta dan azaba idonta kuma yayi rau rau tana son yin kwalla,

"Ungo Robb shafa awurin, ko ba zaki iya ba na shafa miki?" Ya fada yana bin lukuta lukutan cinyoyinta da kallo,

"No abbu zan iya" tafada cikin sauri tareda amsar Robb din, toilet ta shiga ta shafe wurin da Robb amma ba karamin dadi taji ba saboda har taji saukin ciwon da wurin yake yi mata,bude kofar toilet din tayi ta fita aranta tana jin dadin yadda jabir wani lokacin yake sakin jiki da ita har yayi mata wasu abubuwan masu kama da na masoya gashi yanzu ya sake shiga ranta sosai dalilin kwana da ta fara yi dashi a gado daya,

Yana zaune yana jona laptop dinshi a charge ta fito tana kawar da fuskarta, ta gefen ido ya dan kalleta yayi murmushi wanda shi kadai yasan yayishi, ya gane nufinta na shiga toilet wato dan kar yaga jikinta ne ya sanyata yin haka, bakinshi ya tabe aranshi yana cewa,

"Na nawa kuma? Jiki kam ai nagama gani yarinya sai dai ki kiyayi gaba kuma" idonshi ya lumshe ya tuno manyan cinyoyinta da ya gani dazu, juyawa yayi ya kalleta lokacin da take kokarin hawa kan gadon,

Gyara zamanshi yayi ya dauki laptop dinshi ya kunna ya dorata akan gadon ya fara lallatsawa,

"Abbu addu'a" ya jiyo muryar goodness tana fada masa cikin wani salo na daban,

Kamar yadda yayi mata jiya yau ma haka yayi mata ta shafa ta kwanta, amma kuma bacci yaki daukarta son jabir ne kawai ke azalzalar ruhinta, tana son amon muryarshi domin idan yana yin magana har ji take kamar dodon kunnenta zai suma da dadin muryarshi.

  Fiyeda minti talatin ta shafe tana kallonshi yanata rubuce rubucenshi acikin laptop gashi ita kuma baccin yaki zuwar mata, tashi tayi zaune ta saisaita muryarta tace,

"Abbu kayi min labari, bacci yaki daukata yau" ta fada tareda jan wani dan guntun tsaki, kallonta ya dago yayi,

"Ni ban iya labaran duniya ba sai dai labarin da alqur'ani yazo dashi idan kina so sai in baki" ya bata amsa,

"Yes ina so" ta fada tana gyara pillow dinta domin kwanciya, laptop dinshi ya rufe ya ajiyeta agefe ya juyo yana kallonta.

_*Ummi A'isha*_🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [9/21, 8:45 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE...!*

  _*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_71-75_

        _*Wannan babin nakune kyauta wad'anda suka yi mafarkin wani haske adaren shekaran jiya da daren jiya, ina fata daren yau babu mafarkin wani haske,ina sonku fiye da yanda kuke son wani haske, masu mafarkin wani haske nagaisheku kyauta gashi kunada yawa balle na zayyano sunayenku,asha karatu lafiya.*_


~~~Laptop dinshi ya rufe ya ajiyeta agefe ya juyo yana kallonta, "kika ce kina so?"

Kai ta d'aga sannan ahankali tace "yes i like it"

Dan kishingida yayi yana mai fuskantarta, "zan fara da baki k'issar d'aya daga cikin annabawan da Allah ya aiko zuwa ga al'umma, yanzu ki zabi guda acikinsu sai na baki labarinsa ina nufin kissarshi"

"To ai ban sansu ba" ta fada tana shafa fuskarta da hannunta,

"Eh nasani amma zaki sansu yau, ki zaba acikin guda ukun nan, annabi Adam, annabi musa, annabi Yusuf,wanne kike son na baki k'issarsa aciki yanzu?"

Kallon fuskarsa tayi tana murmushi, "annabi Adam"

Gyara zama yayi ya fuskanceta sosai ya fara bata kissar annabi Adam tun daga halittarsa har zuwa kan halittar matarsa hauwa'u da zaman da suka yi a aljanna har zuwa kan lokacin da suka ci ganyen itaciyar da Allah ya hanesu,

Idanuwan goodness a lumshe suke ta nutsu tana sauraren sautin muryar jabir yana bata labari, yanda take jin labarin gani take kamar a tv take kallo gashi tamkar jabir zabo kalmomin da yake fada mata yake yi, labarin gaba daya ya tafi da ita, musamman ma daddadar muryar jabir da take sauraro,

"Zan barki haka sai gobe zan k'arasa miki" ya fada yana kallonta,

"No abbu kar kayi min haka, pls ina son jin abinda ya faru dasu bayan sunci ganyen itaciyar, pls abbu"

Dan murmushi yayi da dukkan alamu bukatarsa zata biya tunda gashi tana da interest akan k'issar da ya fara bata,

"Sanadiyyar cin wannan itaciyar da nana hauwa'u tayi shine mata suke yin jinin al'ada domin lokacin da ta hadiyi ganyen take jini ya fara fita daga jikinta, shine sauran mata suka yi gadonta suma suke zubar da wannan jinin lokaci zuwa lokaci, shi kuma annabi Adam bai hadiye ba, nan gaba daya sutturar dake jikinsu ta bar jikinsu, Allah ya sauko dasu daga cikin aljannah"

"Oh God" ta fada tareda dafa goshinta tana runtse idonta,

"Sun koma kuma?" Ta tambayeshi,

"Sun koma domin Allah mai yawan yafiya ne ga bayinsa"

Murmushin farin ciki tayi, "gaskiya abbu labarin nan da dadi, kai da waye ya baka shi?"

Kansa ya girgiza yana murmushi "Allah ne ya sanar damu acikin littafinsa mai tsarki, duk wannan labarin da na baki ba wani bane ya zauna ya shiryashi ko ya kirkireshi ba, no, abunda ya farune Allah ya sanar damu ta harshen annabinsa"

Kallonsa kawai take yi yanda yake furta maganganun daya bayan daya da dan mitsitsin bakinshi,

"Duk wani abu da kika sani na rayuwar duniya da rayuwar da za ayi bayan anbar duniya to duk alqur'ani ya sanar damu"

"Tunda hakane kullum zaka rinka bani labarin nima ina ji, sannan nima zan fada maka irin namu labarin wanda Bible yazo mana dashi"

Murmushi ya danyi mai kayatarwa wanda har sai da fararen hakoransa masu mutukar haske kamar farar takarda suka bayyana,

"Ashe kema kina da labari?"

Ya tambayeta,

"Yes, i have it, indai zaka ji zan baka"

Murmusawa ya sake yi yana kallonta, tana kwance ta rungume pillow sannan duk wadannan maganganun da suke yi idanuwanta a lumshe suke, amma aranta tunani take yi lallai tunda aka samu labari irin wannan acikin littafin musulmai to za asamu wasu labaran masu kayatarwa wadanda suka fi wannan.

"Nima ina so indai zaki fada min" ya bata amsa yana kallonta,

"Zan baka sai bayan ka bani wani gobe"

"Allah ya kaimu, yanzu dare yayi ki kwanta kiyi bacci nima bacci zanyi tunda yau kin rikeni kin hanani sallar dare"

Murmushi tayi bata ce komai ba ta juya ta gyara kwanciyarta, toilet ya tashi ya shiga ya dauro alwala ya fito yazo ya kwanta agefen gadon bayan ya gabatar da addu'o'insa, tana jinsa har ya gama ya kashe wutar dakin, kasa bacci tayi sai tunanin labarin da jabir ya bata take yi amma wannan abin mamaki da yawa yake yanzu wannan labarin dagaske ya faru? Ta tambayi kanta, tana nan kwance tana ta sharhin wannan labarin har bacci ya dauketa.

  Asubar fari jabir ya tashi kamar jiya yau ma ganinta yayi kwance ajikinsa ta rungumeshi tana ta bacci, janyeta daga jikinshi yayi ya tashi ta shiga _bathroom_,masallaci ya tafi bashi ya dawo ba sai wurin 6:30,lokacin da ya dawo yana shiga bedroom dinshi ya hangota acikin kitchen tana aiki, kwanciya yayi ya dan mike domin jiya bai samu bacci da yawa ba.

Wunin ranar goodness ta yishi ne cikin doki domin alla alla take yi dare yayi su zauna da jabir domin ya bata labari, tunda wuwwuri tayi wanka ta shirya tasaka _sleeping dress_ dinta light brown colour, ta kinkimi abincin jabir ta nufi sashensa amma har lokacin bai dawo ba gashi wurin karfe 9,cike da damuwa ta ajiye kwanukan abincin ta juya ta koma sashenta, kallo ta kunna ta fara kallon wani american film mai suna _the chronicles of narniar_ tana kwance tana kallon har ta fara dan bacci sama sama daga karshe ma baccin ya dauketa gaba daya.

Karfe _10_ jabir ya dawo, sashensa yaje ya ci abinci yayi wanka ya sake sabon shiri cikin gajeren wando baki da yar t shirt fara mai gajeren hannu (su mal jabir an dawo samari), net ya shiga na wasu yan mintuna, baifi 30 minutes ba ya fita ya rufe laptop dinshi,

Sashen goodness ya shiga ta baya, tana falo tana bacci ga tv tana yi ita kadai,

Sunkuyawa yayi ya fara kiranta ahankali "goodness" sai da ya kirata wurin sau uku sannan tayi firgigit ta tashi,

"Abbu yaushe ka dawo?" Ta tambayeshi tana murtsuke idanuwanta,

"Yau ba kya son labarin ne kika kwanta kike bacci?"

"No, ina so na kwantane kafin ka dawo"

Tv din ta kashe tabi bayanshi zuwa sashensa, ba karamin kyau yayi mata ba domin ya zama dan saurayi sak,

Acan inda ta saba kwanciya yauma ta kwanta, shi kuma yana daga farkon gadon azaune,

"Yau wanne labari zan baki? Ko kece zaki bani?"

"Ka fara bani, nima zan baka idan ka gama"

K'issar annabi musa da dan uwansa annabi harun ya fara bata da irin gwagwarmayar da suka yi da fir'auna da hamana da dan karuna,

  Bakinshi kawai take bi da kallo tana mai jin wani irin sanyi acikin zuciyarta wai yau itace jabir yake yiwa dogon labari irin wannan duk da tasan sa'a kawai take ci domin surutu ba sabonsa bane,a bangare daya kuma na zuciyarta tana jinjina labarin domin labarin yakai inda duk wata hikima takai domin ba karamar hikima bace acikin rayuwar annabi musa,

Zumbur ta tashi zaune tana kallon jabir,

"Abbu kar ka cemin basuyi nasara ba a gasar da aka shirya ta matsafan nahiyar"

Kallonta ya daga kai yayi "sunyi nasara ai sandar annabi musa micijiya ta zama ta rinka hadiye duk wasu abubuwa wanda suke ba kanana ba, anan sauran mutane suka yi imani dasu"

Komawa tayi ta kwanta tana murmushi domin labarin da yake bata har wani imagining din abin take acikin kwakwalwarta.

Lokacin da ya kammala fada mata k'issar ba karamin mamaki tayi ba jin wai har yanzu fir'auna yana nan aduniya agidan tarihi a kasar misra,

"Abbu wannan labarin da ka fada min dagaske ya faru?"

Daga mata kai yayi "its true life story, ni har fir'aunan nagani lokacin da naje gidan tarihin, ai Allah ne ya fada cewar zai tseratar da gawar fir'auna daga lalacewa domin ta zama aya ga mutane"

Mikewa tayi daga kwanciyar da take "gaskiya sunsha gwagwarmaya daga shi har dan uwanshi, sannan abinda yafi bani tausayi agame dashi shine irin yanda dan uwansa d'an karuna ya juya masa baya yakoma ya hada kai da fir'auna bayan ya zama mai arziki, ya manta da cewar shine yayi masa addu'a har Allah ya bashi arzikin"

"Ba mantawa yayi ba tsabar shak'iyanci ne kawai,amma duk wannan tawayen dasu fir'auna suka yi hakan bai hana annabi musa samun nasara ba domin yanada yawan al'umma shiyasa afilin alk'iyama za ahango wasu al'umma masu yawan gaske har annabi Muhammad (s.a.w) zai taso domin ya zata al'ummarsa ce sai ace wannan al'ummar annabi Musa ne (A.S)"

Shiru tayi zuciyarta cikeda mamakin yadda aka yi har teku ya daskare ya rabe gida biyu mutane suka wuce ta cikinsa,

"Tunda nagama baki labarin to nima ki bani wani inji" yace da ita yana gyara kwanciyarsa,

Dan murmushi tayi tace "ni labarin ruhu zan baka domin labarinsa yazo mana acikin Bible, shi ruhu ba mutum bane kuma ba aljan bane sannan bashi da farko kuma bashida karshe....!"

Katseta yayi "shima kenan ubangijinku ne?"

Kai ta girgiza "no, he's not our lord but...!"

"But what? Goodness don't deceive your self,indai wannan ruhun da kike fada ba ubangijinku bane to babu hujjar da zai sa ki kira annabi Isah a matsayin ubangijinki domin shi wannan ruhun da kikace Bible yazo muku da labarinsa ai yafi annabi Isah abin mamaki, dalili shine shi annabi Isah baku bashi wannan siffofin ba amma shi ruhu gashi kun bashi"

Kallo ta bishi dashi tana dan nazari akanshi, "Kaine fa kace in baka labari kuma shine daga fara fada maka zaka yi interrupting dina" ta fada fuskarta ta kwakkwabe kamar zata yi kuka,

"Ba katse ki nayi ba, ki bari gobe zan baki k'issar shi kanshi annabi Isah din da ta mahaifiyarshi Nana maryam, labarin nakine bana son jinshi saboda na rigada na sanshi tun dadewa, ko baki san nima na karanta bible ba?"

Kallonshi tayi da sauri "are you serious?" Ta tambayeshi,

"Am serious goodness, duk wani abu wanda ke cikin Bible na sanshi na karantashi"

Jingina tayi da jikin _pillow_ tana kallonsa, "ki bari sai gobe zan fada miki waye yesu, almasihu, zan sanar dake k'issarsa tun zuwanshi duniya da kuma dawowar da zai yi nan gaba"

"Dawowa? Zai dawo nan gaba?" Tafada cikeda mamaki,

"Yes zai dawo nan gaba haka Allah ya sanar damu" ya bata amsa yana kokarin tashi,

Batare da tace masa komai ba ta koma ta kwanta tana binsa da kallo har ya shige cikin _bathroom_. Tana nan kwance har ya fito ya tsaya agaban gadon ta taso tazo inda yake ta mika masa hannuwanta ya karanto mata addu'o'in kwanciya bacci ta koma ta kwanta tana shasshafe jikinta da tafukan hannayenta.

Ido ta tsura mishi lokacin da ya tada kabbarar sallar nafilar da zaiyi, tana nan kwance tana kallonsa har bacci ya dauketa bata san lokacin da jabir ya dawo kan gadon ya kwanta ba.

  Washe gari da safe da ciwon cibiya ta tashi amma bata sanar da jabir ba har ya shirya ya tafi office aranar mamanta tazo gidan domin ganin lafiyarta duk da cewa suna haduwa a church duk ranar lahadi, huduba iri iri ma tayi mata kafin tabar gidan, a irin kudin da wani lokacin jabir yake bata ta dauko ta bawa ma _2000_ haka ma ta karba babu wani farin ciki domin jikinta ya gama yin sanyi da lamarin goodness gani take kamar goodness din zata karbi addinin musulunci.

K'arfe 8:30 jabir yana zaune a falonsa yana kallon huda tv inda ake gudanar da wani program _(Qur'an and the science)_ gefenshi kuma wasu littattafai ne a ajiye wadanda ya gama dubasu,

Kallonsa goodness tayi lokacin da ta shiga cikin falon acikin ranta tana cewa "kullum baka gajiya da karance karance da kallon wannan channel din"

"Sannu abbu" ta fada tareda zama a k'asa can nesa dashi kadan,

"Yawwa" yace ba tare da ya jiyo ya kalleta ba,

"Abbu ina son zuwa hospital gobe, zan ga dr"

Sai a lokacin ya juyo da hankalinsa zuwa gareta,

"Meya faru?"

"Cikina ne yake ciwo" tafada kanta a sunkuye,

"Cikinki ko mararki?"

"No,cikina ne"

"Ba period pain bane?"

"Abbu ba shi bane, cibiyata ce ke yin jini"

"Jini? Tun yaushe?"

"Abbu dama ya jima yana yi to yanzu ne yayi yawa yau da safe naga jinin yana fita da yawa"

"Let me see"

D'agowa tayi ta kalleshi amma ta kasa motsawa daga inda take,

"Ba kiji abinda na fada bane? Zo nagani"

Hada ido suka yi amma har lokacin bata da niyyar tashi,

"Abbu ba sai ka gani ba"

"Ok ni ba sai Nagani ba amma zaki iya nunawa dr shi yagani ko? You are not serious"

Wayarshi ya dauka ya fara kiran dr din da yake dubashi idan ba shida lfy, nan ya fara fada masa matsalar goodness, tambayarshi dr din yayi cewar yaya cibiyar tayi, tayi rami ne ko kuma daga can ciki jinin ke fitowa,

Goodness ya kalla ya dan janye wayar daga jikin kunnenshi,

"Come here"

Ahankali ta tashi ta matsa inda yake, bai jirata ba ya daga rigarta, ya fara duba cibiyar ta,dan yatsanshi ya saka akan cibiyar cikin sauri ta rike yatsan nashi "ohh wash abbu da zafi",

Wayar ya mayar jikin kunnenshi yana yiwa dr bayani, ido ta zuba masa aranta tana tunanin to me kenan? Meye dalilinshi na kin barinta taje taga dr Kodai kishi yake?? Hhhh masu karatu nikaina ummi A'isha tambayar da nake son inyi muku kenan kodai kodai??? Anya kuwa mal jabir ba a kamu ba?? Hmmm muje zuwa zamu gane ai.

Sai da ya gama wayar sannan ta saki dan yatsan nashi tana kallonshi shikuma fuskarshi na kallon wayarsa,

"Bari zai turo da sunayen magungunan da za asai miki kisha yanzu, idan ya turo sai nabayar a siyo miki",

"Thank you abbu"

Tashi tayi ta koma part dinta tayi wanka tayi shirin bacci ta fito ta shiga kitchen ta dafawa jabir shayin na'a na'a ta dauka ta nufi part dinsa.

Yana falo azaune jikinsa sanye da kayan bacci _lemon green_ yana dudduba magungunata wanda ya bayar aka siyo mata,

"Zo ga maganinki"

Karasawa tayi ta zauna tana kallon maganin itama harda wani mai kamar hydrogen amma ba shi bane sai nasha kala daban daban,

"Ki dauka kisha yanzu, shi kuma wannan goge wurin zaki rinka yi dashi"

"Toh" ta karba tana kallonshi, dakyar ta iya daurewa ta goge cibiyarta da spirid domin yanada zafi dan dai kawai tana tsoron jabir ne kar yayi mata irin na rannan.

Kallonta yayi lokacin da take shan maganin tasha kayan baccinta riga fara mai digon pink ajiki sai wando pink colour, mikewa yayi ya shiga _bedroom_ dinshi nan ta tashi tabi bayanshi, agefen gado ta sameshi zaune yana waya da ummu al'amin, bata iya jiyo abinda yake fada hakan ya sata kwanciya acan karshen gadon ta juya masa baya tayi ruf da ciki.

Sun jima suna yin waya da matarshi tana jinsu har ya gama wayar, jin shiru yasata juyawa tana kallonshi,

"Abbu labarin da kace zaka bani jiya"

Juyowa yayi gareta "labarin wa nace zan baki"

"Jesus" tafada tana kokarin gyara kwanciyarta,

"Kamar yadda nafada miki yesu ba Allah bane kuma ba dan Allah bane, asalima idan aka ambaci wannan kalmar sama da kasa sai sunyi kamar zasu hade domin Allah bai cancanci wannan siffar ba, annabi Isah annabin Allah ne wanda mahaifiyarshi ta haifeshi ba tare da uba ba kuma itama Qur'ani ya sanar damu cewar mutuniyar kirki ce tagari mai yawan ibada, amma da Allah ya tashi nuna hikimarsa da ikonsa sai ya nufeta da haihuwar annabinsa ba tareda ta taba saduwa da wani d'a namiji ba, kawai mala'ika ne ya hura mata iska take ta dauki cikin annabi Isah, lokacin data dawo cikin gari wurin mutane suka ganta da d'a sai abin ya basu mamaki har suna son jin abinda ya faru da kuma inda ta samu d'a, alokacin annabi Isah yayi magana cewar shi bawan Allah ne kuma sannan Allah zai bashi wani littafi zuwa ga mutane, hikimar yin haka shine domin akore Kalmar can ta farko ta cewar shi annabi Isah Allah ne shiyasa ya fada da bakinsa cewa shi bawan Allah ne sannan Allah ya sanar damu cewa misalin annabi Isah kamar misalin mutum ne wanda aka halicceshi da tabo sannan aka ce dashi ya kasance take sai ya kasance, gashi Allah ya bashi mu'ujiza domin yana tayar da matacce yana warkar da makaho, kuturu amma duk da izinin Allah, yakan zana tsuntsu da tabo ya hura shi sai ya tashi sama da izinin Allah yabi iska yayita gudu,har yanzu yana nan a sama araye kuma bai taba aure ba saurayine,a karshen duniya annabi Isah zai dawo kuma zai saukone ranar laraba bayan an idar da sallar la'asar, zai sauka a masallacin k'udus (Jerusalem) sannan zaiyi aiki da shari'a da sunnar annabi Muhammad (s.a.w),shiyasa alokacin malamai sunce za awayi gari mutum yana da dunbin dukiya amma babu wanda zai bawa zakka saboda kowa alokacin mai arziki ne, arziki zai wadaci kowa domin zamanine wanda babu zalunci acikinsa, alokacin kuma dujal tuni ya bayyana yanata batar da mutane daga kan hanyar gaskiya to annabi Isah zai nemoshi kuma zai kasheshi idan ya kasheshi shima Allah zai karbi rayuwarsa zai koma ga Allah"

Kwalla taga jabir yana gogewa daga idanuwanshi hakan ya sanyata tashi zaune ta karasa gabanshi ta kamo hannuwanshi ta rike acikin nata,

"Abbu abin da abin tausayi amma kar kayi kuka pls"

"Bayan nan kin san abinda zai biyo baya?? Aranar tashin alqiyama Allah zai tambayi annabi Isah cewar yakai Isah dan maryam shin Kaine ka cewa mutane ku rikeni nida uwata abubuwan bautawa biyu bayan Allah?, sai annabi Isah yace tsarkinka ya tabbata! Baya kasancewa agare ni in fadi abinda babu wani hakki agareni. Idan na kasance na fadeshi to lallai ka sanshi, kana sanin abinda ke cikin raina, kuma bani sanin abinda ke cikin ranka. Lallai ne kai masanin abubuwan boye ne, ban fada musu ba face abinda ka umarceni dashi wato Ku bautawa Allah ubangijina kuma ubangijinku,kuma na kasance mai shaida mutukar na dawwama acikinsu sa'annan alokacin daka karbi raina ka kasance kaine mai tsaro akansu, kuma kai halartacce ne akan dukkan komai. Idan ka azabtar dasu to lalle ne su bayinka ne, idan kuma ka gafarta musu to lallai ne kaine mabuwayi mai hikima, Allah yace wannan ce ranar da masu gaskiya gaskiyarsu take amfanar dasu suna da gidaje a aljannah koramu suna gudana daga karkashinsu suna madawwama acikinsu har abada, Allah ya yarda dasu kuma sun yarda dashi, wannan ne babban rabo mai girma"

Hawaye ne suka ciko idonsa, hannu goodness ta saka ta goge masa su tana kallon kyakkyawar fuskarshi.

Har lokacin hawaye ne na tsantsan imani ke kwaranya akan lausasan kumatusa, ganin haka yasa goodness itama fashewa da kuka duk da cewar bata san abinda jabir yake yiwa hawaye ba shi kukan tunawa da ranar alqiyama yake yi yayinda ita kuma kawai take tayashi ganin abin sonta na zubar da kwalla akaron farko na tarihin rayuwarta,

Hannuwanshi ta damke tana cigaba da kukan, sauke idonsa yayi akan fuskarta ahankali ya rungumeta tsam tsam ajikinsa yana hawaye, kankameshi itama tayi tana mai cigaba da kukan da take yi, sun jima ahaka kafin jabir ya iya dagota daga jikinsa yazuba manyan idanuwansa akan fuskarta,hannunsa yasa yafara share hawayen fuskarta yana murmushi, nata hannun itama ta sanya tafara share masa nasa hawayen tana kallon fuskarshi amma har lokacin bata daina kukan ba.



_*Ummi A'isha*_🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [9/24, 7:40 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*

*_NA_*
_*UMMI A'ISHA*_

_76-80_

           *_Wannan Shafin nakune masu yiwa wani haske dariya, ina fata dariyar yau zatafi ta kullum, sannan dariyar da kuke yiwa wani haske nima takan sani dariya domin ku kun san abinda kuke yiwa dariya haka kuma nima nasan abinda nake yiwa dariyar, wannan fa shi ake kira da kallon kallo, asha karatu lafiya_*


~~~Ido ta tsura masa tana kallonsa acikin zuciyarta tana jinjina labarin da yasanar da ita tun daga kan na annabi Adam har zuwa na annabi Isah (AS) hakika ita dai tasan tun lokacin da tana karamar yarinya ake basu tarihin annabawan nan kamar yadda sunayensu yazo acikin wasu wurare nacikin Bible, yawancin annabawan tanada labarinsu dan tun daga kan Adam,Moses, Jacob,abraham,Jesus, har zuwa kan annabi Muhammad (S.A.W) babu wanda ba asanar dasu ba sai dai its different da wanda jabir yake bata domin shi nasa labarin jinsa take da banbanci da wanda ita tasani,

Har alokacin shima jabir kallonta yake bayan yagama share mata hawayen kan fuskarta, hannunta bisa kuncinsa tana share masa hawayen ya kalleta yace,

"Pls kidaina kukan nan haka"

Girgiza masa kai tayi tana matso wasu hawayen "how can i stop it bayan kai kuma kana yi? Kadaina kaima pls"

Hannunta dake kan kuncinsa ya rike da nashi hannun,

"Ai ni ba kuka nayi ba hawaye ne kawai"

Murmushi tayi tana mai tsayar da ragowar kukan da yake taho mata,

"Abbu wadannan labaran duk da kabani nasan dan kadan game dasu but nawa wanda nasani yasha banban da naka wanda kake fada min"

Har lokacin yana rike da hannunta guda daya akan kuncinsa,

"Goodness shi alqur'ani ba a canjashi,tun lokacin da aka saukar dashi har kawo yanzu babu ko harafi daya da aka canja sannan labaran dake ciki sahihai ne kuma tacaccu, sabanin bible wanda duk an sassauya abubuwan dake ciki, asali ma ba shine littafi nagaskiya ba domin wani bayahude ne ya rubuta shi bayan ya hada kai da wani bamaguje, shiyasa zaki ga Bible din da kuke using yanzu dashi an rubuta _Red letter edition_ ma'ana duk wurin da aka rubuta shi da jan tawada to shine wurin da ake da yakinin maganar Allah ce amma duk inda akayi rubutu da bakar tawada to ba fadin Allah bane sannan kuma kinga ai inda akayi rubutu da jan biron basu da yawa sai acan karshe karshe ma sannan ake samunsu"

Hannunsa ta sake makalewa cikin nata ta gyara zamanta daga durkushen da take ada,

"Abbu naji kace wani bayahude ne ya rubuta wannan _Bible_ din bayan kuma ni nasan bulus ne ya rubuta shi"

"Tabbas bulus ne ya rubutashi kuma asalinsa shi bayahude ne, akwai banbanci tsakanin Christians da kuma masihiyyuna, masihiyyuna sune wadanda suke bin almasihu nagaskiya wato annabi Isah sune wadanda basu sauya ba sannan ba suyi bidi'a ba,

Basu kirkiro ba dangane da abinda aka aiko annabi Isah dashi wadannan su ake kira da nasara (masihiyyuna), _Christians_ kuma sune wadanda suke bin jabun addini wanda aka dangantawa annabi Isah ta hanyar manzo bulus, wanda yake bayahude yayi barna da yawa akan mutanen annabi Isah ta hanyar kashesu da azabtar dasu da kuma haifar musu da yakoki na kare dangi,

Duk da yagama wannan kisan da cewa bai taba ganin annabi Isah ba kuma shi ba sahabinsa bane, daga baya sai yazo ya bayyana tubanshi ga mabiya annabi Isah,majority dinsu basu yarda dashi ba domin sun gane cewa wani makirci ne ya kullo domin ya lalata addinin,

To amma sai _Barnaby_ wanda akafi sani da Barnabas sai ya nuna cewa akarbeshi tunda ya tuba kasancewar ko Allah ma yana karbar laifi idan aka tuba, amma matasan tafiyar irinsu _Mathew_ sam basu amintu da tuban bulus ba,

Haka suka ci gaba da tafiya _Barnabas_ ya aminta da bulus amma _Mathew_ bai aminta ba ana nan ba adade ba sai bulus yace yayi mafarki yaga annabi Isah (AS) yace ya rubuta injila (Bible) cikin jeren almajiran annabi Isah masu rubuta injila,

Sai aka ga gashi ya rubuta injila amma tana dauke da cewa Isah dan Allah ne, Allah yana da d'a, maryama Allah ce, mala'ika jibrilu Allah ne, sai aka samu wadannan akidodi sun fantsama cikin mutane wasu har sunyi na'am dasu, saboda yayi da'awar cewa annabi Isah ne ya bashi umarnin ya rubuta,

Koda maganar ta fito sai mabiyan annabi Isah sukace basu yarda ba amma ya rigada yayi musu raraka dayawa domin jama'a da dama sun yarda da abinda ya rubuta,

Koda mabiyan annabi Isah sukace basu yarda ba sai magoyan bayan bulus sukace su sun aminta tunda mafarki yayi kuma acikin addinin annabi Isah akwai halarcin kayi mafarki da shi ya fada maka abu ka rubutashi kabayar akarba ba tare da anyi bincike ba,

Dan haka shima dole akarbi abinda ya rubuta, Ashe dan kwangila ne, kwangila ya karbo daga wurin yan uwansa yahudawa ciki harda Sarkin wata kasa (kwantastaniya), wato kasar turkiya wanda shi wannan sarkin ya kasance bamaguje ne mai bautar Alloli dayawa sakamakon haka suka sha alwashin sai sun bata addinin annabi Isah, shiyasa suka dauki kwangila suka bashi, da ya hada wannan rikici yaga komai ya rikice sai yace to mai zai hana adauki wannan case din akaiwa wani wanda shi abinda yake bautawa dabanne da nasu, sai sukace kamar wa? Sai yace kamar sarki kotasten,

Cikin rashin sani sai suka amince, koda suka je suka fada masa sai ya karbe dukkan injilar datake hannunsu yace za asamu babban abu azuba aciki asamu kyalle arufe da daddare, idan gari yawaye duk wadda aka samu asama sauran na lullube to itace ta gaskiya dukkaninsu sukace sun yarda,

Koda aka wayi gari sai aka ga wannan injilar mai cewa Allah yanada da, maryamu Allahce, jibrilu Allah ne alloli ukune sai aka tarar itace asama, _Mathew da Barnabas_ da suka ga haka sai sukace to lallai yaune ranar farko na lalacewar addinin da annabi Isah yazo dashi,dan haka bazasu tsaya suga wannan barna da idanunsu ba, sai suka kama hanya domin yin hijira, Adaji akaga gawawwakinsu an daddaba musu wuka an kashesu"

Daga kanta tayi tana kallonsa "ehem ina jinka, duk nasan wannan labarin karshen nake son ji"

Cigaba yayi da cewa "ba asan waye ya kashesu ba amma ana tunanin su bulus ne da sarki kotastan ko kuma wasu yan ta'adda wadanda ba a sansu ba, sai aka koma cikin gari aka hallakar da duk injilolin in banda wadda Allah ya tseratar kwaya daya wacce yanzu akafi sani da _the gospel of Barnabas_, har yanzu tana nan ayadda take da asalin rubutun hannunta tana nan a _Barnabas square_ akasar _Italy_ an kewayeta acikin wani gilashi,yawanci Christians yanzu kuna inkarinta saboda sunayen annabi Muhammad ya bayyana karara acikinta, amma kuma itace injila mafi kusantar gaskiya da sauran injilolin da suke hannunku ayanzu,

To kinga kenan wannan shine asalin addinin kiristanci da kike bi wanda Barnabas ya tsarawa mabiyan annabi Isah akarshen zamani, har suka dauki cross suna ratayawa awuyansu wanda har yahudawa suka fara yi musu ba'a suna kiransu da chritian wato masu bautar wanda aka gicciye, to da zamani yayi tsawo sai su da kansu suka yarda suka amsa sunansu na Christians, kinga kenan idan kin fahimci abinda nafada miki wannan addinin da kike bi ayanzu ba shine asalin addinin da annabi Isah yazo dashi ba, wani abune ake bi daga cikin tsarin sarki kotastan bamaguje da bulus wanda ya shigo domin ya lalata addinin,wannan shine asalin addinin kiristanci, shin idan baki san wannan ba baza kiyi mamaki ba kiji Allah ya tsinewa bani isra'ila ta harshen annabi Isah da annabi dawud ba? Alhalin shima annabi Isah ba'isra'iliye ne,

Shi kansa bani isra'ila ne amma meyasa Allah ya tsine musu? Allah ya tsinewa wadannan masu sauya littafin Allahn ne Wanda ya turo annabi Isah dashi,

Wannan tarihin nasan kin sanshi domin haka yazo acikin Bible kuma mutane da dama sunyi bincike sun ganoshi har sunyi rubutu akansa misali Alhaji _Adelege_ ya rubuta littafi mai suna _historical Jesus_ wato Jesus nagaskiya da kuma almasihu wanda aka kirkira domin abata addinin, acikin wannan littafin akwai tarihi nagaskiya na injila wanda yasha banban da tarihin wannan littafin ayau"

Hannuwanshi ta sake rikewa cikin nata tana kallon kyakkywar fuskarshi,hakika yau ta yarda cewar jabir mutum ne mai ilimin gaske wanda ba iya na addininsa kadai ba har na addininta ya hada,

"Abu dukkan abubuwan da kafada nasan gaskiya ne sai dai akwai daga cikin labaran da ka fada min wanda mu ba haka yazo mana acikin Bible ba"

Manyan idanuwanshi ya zuba mata yana wani salihin murmushi,

"Shiyasa nace miki tun farko ancanja littafin ne kuma labaran da suka zo acikin Bible suna wuce iyakane, suna zarce inda ya kamata su tsaya shiyasa acikin alqur'ani mai girma ubangiji ya kira yahudawa da wadanda suka sauya littafinsa, Allah yace "'Gwalalon azaba ya tabbata ga wadanda suka yi rubutu da hannunsu sannan suke cewa wannan rubutun daga Allah yake saboda wasu yan kudi kadan wanda zasu samu ,

Azaba ta tabbata agaresu gameda abinda suke rubutawa, azaba ta tabbata akansu gameda kudin da suke samu"'  _(alqur'an, chapter 3)_,

Kinga kenan shi kansa Bible din littafine wanda aka canjashi tunda ansaukar da alqur'ani ne abayan an saukar da injila (Bible) amma gaba daya acikin ayoyin alqur'ani mai girma duk inda Allah ya tashi yin magana akan injila yana cewa an canja littafin, Allah yayi mana bayanin hakan dalla dalla acikin suratul Al'imran surah ta uku daga farkon aya har zuwa ta karshe"

"Hakane abbu,yanzu nagane jawabanka gaba daya"

"Tunda kin gane to ki kwanta kiyi bacci saboda dare yayi sosai"

"To kar ka sake yin wani kukan pls" tafada cikin shagwaba tana zare hannuwanta daga cikin nashi, tashi yayi ya shiga bathroom yayi alwala ya fito yana kallon agogon dake makale a bangon cikin dakin, karfe 2:30 nadare, gafen gadon yaje ya kwanta yana kokarin jan bargo domin rufe jikinshi,

"Abbu yau baka yimin addu'a ba" ya jiyo muryar goodness abayanshi tana fada, juyawa yayi yafara karanta mata addu'a, sai da yagama sannan yayi wa kansa ya shafe jikinsa yagyara kwanciyarsa,

Goodness najinshi tana kwance tana kallonsa ta kasa bacci tunani ne kala kala ke zagaya kwakwalwarta, ita dai tasan acikin Bible akwai abubuwan da suka zo nagaskiya amma basa aiki dasu misali, abangaren hukunce hukunce akwai hukuncin saka hijabi amma kuma basa sakawa, sannan akwai hukuncin alwala wato an koyar dasu yanda zasu yi alwala itama basa yi, akwai hukuncin sata idan mutum yayi nanma ba ayi, kuma ta taba ganin wani hoto da aka zana nana maryam mahaifiyar annabi Isah da hijabi ajikinta taga an zanata ba azanata da siffa irin wacce su suke da ita ayanzu ba, gashi ba salla suke yiba amma idan sunje masallacin Jerusalem aikin hajjinsu dolene sai mutum yayi alwala yayi salla raka'a biyu, kai anya kuwa babu wani boyayyen al'amari acikin wannan lamarin?

Juyi tayi takoma rigingine tana kallon sama acikin duhun dakin, tafi minti 30 tana tunane tunane wanda ta kasa gane kansa daga karshe taja jikinta ahankali taje ta kwanta ajikin jabir tana mai kudurin idan gari ya waye akwai tambayar da zata yi masa, hannunshi ta lalubo ta rike cikin nata tana matsawa ahankali, duk jabir najinta domin ba bacci yake yiba idonshi biyu kawai yayi mata shiru ne.

Yana jinta ta fara fitar da numfashi ahankali alamun tayi bacci, hannuwanshi yasaka ya zageyata ya rungumeta acikin jikinsa, hannunshi guda daya yasa ya shafo tulin gashin kantin dake kanta wanda yake himili guda shi dai har yanzu bazai iya cewa ga yanayin gashinta ba saboda tun zuwanta gidan kullum cikin attach take idan ba kitso ba to kalba,

Yanata yan tunane tunane har baccin shima yayi nasarar awon gaba dashi.

Kamar kullum washe gari da safe bayan ta kammala shirya komai tayi wanka da ruwan data zuba turaren almiski aciki kasancewar ita bata San amfaninsa ba,

Kwalliya tayi tasaka English wears wanda jabir ya siyo mata lokacin da yaje _madinahtul munawwara_ rigar bakace mai adon duwatsu yayinda skirt din kuma blue colour ce mai santsi, bakar hula ta saka ta sake shafe jikinta da turaren muski da sauran turaruka masu dadin kamshi,

Breakfast din jabir ta dauka ta nufi part dinsa, tana shiga yana fitowa daga cikin bedroom dinsa cikin hadadden farin danyen boyel dinkin riga da wando da kuma babbar riga, ba karamin kyau yau dinnan yayi ba dan ji take inama tana da camera da ta haska shi,

"Good morning abbu" ta fada tana karkace kanta gamida langabar dashi,

"Morning, kar ki ajiye min anan miko min shi nan" yafada lokacin da ya ke zama kan kujerar dake cikin falon, fasa dorawa tayi akan dining table din ta dauko ta kawo masa ta dora akan center table din gaban kujerar da yake zaune,

Tea ta tsugunna ta soma hada masa, kasa kasa yake kallonta gaba daya kamshinta ya gama cika masa hanci ji yake yasan kamshin tiraren amma ya kasa gane wanne irine,haka itama kamshinsa gaba daya ya cika mata hancinta domin numfashinta har wani sauya launin fitarsa yayi,

"Gashi abbu" tafada tana dora masa bisa kan table din

"Yawwa nagode ya fada ahankali"

Zama tayi agefensa tana kallon yanda yake shan tea din cikin sanyinshi ahankali ahankali kamar wani marar lafiya,

"Abbu inada tambaya,Acikin bible an fada mana cewar Jesus zaiyi ceto shida ruhu (haske),Ku wa akace muku zaiyi ceto acikin littafinku?"

Cup din hannunsa ya ajiye ya dan kalleta

"Ceto gaskiyane za ayi ceto ranar alqiyama to amma suwaye zasu yi ceton?,da farko dai annabawa zasuyi ceto, shahidai zasu yi ceto wato wadan da sukayi mutuwar shahada sannan siddikai zasuyi ceto, siddikai sune wadanda Allah ya basu wata karin daraja bayan annabta, misali annabi Idris da annabi Ibrahim kowannensu Allah ya bashi matsayin siddiki acikin alqur'ani mai girma,

Allah yace _"Wazkur fil kitabi Idris innahu kana siddikan nabiya, acikin wata surar kuma yace wazkur fil kitabi ibrahim innahu kana siddikan nabiya"_

Bayan siddikai sai yara kanana wadanda suka rasu kafin su girma suma zasuyi ceto sannan alqur'ani mai girma shima zaiyi ceto kamar yadda annabi Muhammad (S.A.W) yafada,

_"Ku yawaita karanta alqur'ani musamman suratul bak'ara da suratul al'imran domin kowannensu ranar alqiyama zai zama giza gizai zai yiwa mai karantashi rumfa, zasu zo filin alqiyama domin ceton masu karantasu"_

Sannan wasu malaman sunce mutane na kwarai salihan bayi suma zasu yi ceto sai dai amma duk wanda za aceta sai yana da imani, mutukar bai mutu da imani acikin zuciyarsa ba to bazai samu wannan ceton da ake fada ba ina fata kin fahimceni"

Kanta ta daga duk jikinta amace,

"Yes,na fahimta"

Mikewa jabir yayi yana gyara babbar rigarsa ya fice, zama tayi cikin falon tana nazarin amsoshin da jabir ya bata.

Haka suka ci gaba da kasancewa da jabir amma kullum yana bata kissar annabawa, har yau bai daina ba yanzu ya bata ta annabi Yusuf da yan uwansa da irin rayuwar da yayi agidan kurkuku da kuma haduwarsa da yan uwansa har lokacin da ya koma ga ubangijinsa.

Duk ranar Sunday tana zuwa church acan take haduwa da ma, shikuma jabir ya fara shirye shiryen  tunkarar azumin watan ramadan,

Tunda watan azumi ya kama baya zama ga zuwa office da yake yi baya tasowa sai 5 da zarar ya dawo kuma zai tafi wurin da yake yin tafsir, sai bayan sallar isha zai dawo gida kasancewar wannan azumin bai tafi wata jahar ba saboda goodness amma da lokacin da shida Ummu al'amin ne wata state din yake zuwa,

Yanzu zamansa agidan babu yawa ba kamar da bane domin kullum bashida lokacin hutu, duk goodness tabi ta damu na rashin zamansa agidan sosai, amma tana iya kokarinta na ganin ta yi masa duk wani abu wanda zai sakashi farin ciki, tsakaninta dashi kuwa sai dai kallo domin yanzu baccin ma bayinsa yake yi sosai ba kullum yana cikin ibada gashi da rana ba damar ta ganshi tunda ba agida yake wuni ba.

Goman karshe na kamawa ya tafi umarah yabarta ita kadai agidan,tafiyarsa ta sakata cikin damuwa kullum adakinshi take kwana kasancewar abude yabar mata shi, sannan akoda yaushe yana kiranta awaya suna gaisawa wani lokacin kuma yabarta da al'amin suyita faman surutunsu,

Kwanansa goma sha daya da tafiya ta tashi da wani yanayi yanayin kuwa shine ji tayi ta tsani halinda take ciki gaba daya labaran da jabir ya bata sune ke mata yawo acikin brain dinta,so take kawai taganta tana salla domin taji irin abinda jabir yake ji, sannan ta fuskanci jabir bazai taba sonta acikin wannan yanayin da take ba, tasan idan ta zama musulma jabir zai sota zai kaunaceta kuma zai nuna mata soyayya, tunanin abinyi tafara acikin ranta shin ta musulunta ko kuma ta zauna acikin addinin da take???????

Masu karatu mu jira shafi nagaba domin jin abinda zai biyo baya.amma shin kuna ganin cewa jabir zai so goodness kuwa koda ace ta musulunta?? Nidai ummi A'isha bani da wannan amsar. Sannan ina mai baku hakuri da yanayin irin turancin da nayi amfani dashi aciki (broken) ni anawa ganin yawancin Christians musamman ma na kudu turancinsu ba pure bane sunfi yin broken ina fata hakan bazai zama matsala ba, burina dai kawai Ku fahimci sakon da littafin yake dauke dashi ba turancin ba.

_safiyya Ummu Abdul nagasheki gaisuwa marar adadi._


*_Ummi Shatu_*🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [9/27, 11:26 AM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*


     _*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

      _*Masoya ina godiya agareku, wadanda sakonsu ya iskeni da wadanda sakonninsu basu samu damar zuwa gareni ba duk nagode Allah yabar zumunci da soyayya, da ace da hali da na lissafo sunayenku amma babu damar yin hakan, nagode sosai ina sonku fiyeda yadda kuke sona.*_


_81-85_

~~~Tunanin abinyi ta fara yi amma kuma acan kasan ranta tana jin tsoron mamanta domin bata mantawa tun kafin aurenta da jabir ma tace indai ta sake ta musulunta sai ta yankanta,

"Ohh my God" tafada gamida dafe goshinta, yanzu a yan kwanakin nan duk ta sauya hatta dabi'unta ma sun sauya ta daina sauraron wakokin da ada sune suka zame mata abin ji akoda yaushe sannan yanzu ta rage yawan karanta Bible dinta domin tunowa da tayi wata rana ta taba bawa jabir bible din sai yaki karba da ta matsa masa da maganar sai ya jiyo ya rike yan yatsunta yana mai fuskantarta,

"Goodness baya halatta agareni da na karanta bible bawai ina nufin ya zama haramun bane sai dai ni yanzu alqur'ani shine littafin da yafi cancanta da na rike kuma na karanta akoda yaushe saboda azamanin annabi Muhammad (S.A.W),annabi ya taba ganin sayyadina umar yana karanta wata takarda sai annabi yake tambayarsa menene wannan yake karantawa? Sai sayyadina Umar yace injila ce, wato wani dan yanki ne nacikin injila, anan sai fuskar annabi ta sauya zuwa fushi, ransa ya baci mutuka har yace da sayyadina Umar ko annabi Isah ne ya dawo awannan lokacin to wlhi dole yabishi yabi sunnarsa, atake sayyidana Umar ya nemi afuwar annabi yace bazai sake karantawa ba"

Zama tayi na dirshan tana tuno kyawawan halayen mijinta jabir, komai nashi mai nagarta he, bashida yawan hayaniya gashi ya rike addininsa da hannu bibbiyu, adan zaman da tayi dashi daga lokacin data fara hada makwanci dashi har zuwa wannan lokacin da yayi tafiya ta fahimci shi mutum ne mai mutukar tsoron Allah ga tarin ilimi akansa kamar ruwa, komai nashi Allah ga yawan bincike akan abubuwan da suka shafi addininsa, idanuwanta ta lumshe tana mai tuno da kyakkyawar surarsa wacce take mai daukar hankalin duk wata mace,

"To yanzu menene abin yi?" Ta tambayi kanta, Kodai babanta zataje ta fadawa? Ita dai tana son yanzu ta zama kamar jabir ta fuskar rayuwa,

Yayarta ta kira wato Anty Bilkisu tafada mata tana son ta karbi addinin musulunci, ba karamin murna anty Bilkisu tayiba domin dama addu'ar da ta dade tana yiwa goodness kenan na ta samu *Wani Haske* acikin rayuwarta,nan anty bilkisu ta bata shawara akan taje gida ta sanar da babansu tukunna,

Shiryawa tayi tabi shawarar Anty Bilkisu ta tafi gidan iyayenta, kamar kullum gidan babu kowa sai mahaifinta kadai wanda yake zaune a tsakar gidan ya shimfida tabarma yana kishingide yana sauraren radio,

Shigarta shigace ta mutumci domin bakar rigace ajikinta ta yafa bakin dan kwalin rigar, ko ba afada mata ba tasan ma tatafi church,

Agefen tabarmar ta zauna bayan sun gaisa tafara yiwa babanta bayani,

"Papa munyi magana da anty bilkisu ne nafada mata ina son zan musulunta shine tace inzo in sanar dakai"

Zaune baban nata ya tashi daga kishingidar da yayi, jin maganar yake kamar a mafarki wai goodness zata musulunta,

"Alhamdulillah, lallai Allah shine mai iko akan dukkanin komai, sannan kuma dama rahamar ubangiji haka take, wani baya musulunta sai har yaga wani mutum yana salla alhalin kuma ba aranar yafara ganin ana salla ba, wani kuma karatun alqur'ani zai ji sai kawai yayi sha'awar musulunci bayan ba ranar ya fara jin karatun qur'anin ba, kai koma dai menene to wannan wata babbar rahama ce daga Allah,

Goodness hakika ubangiji yasoki da rahama kuma yasoki da samun babban rabo acikin rayuwarki, yanzu abinda nake so dake shine kar ki yarda ki sanar da mahaifiyarki sannan kije gidan mahaifin jabir mijinki ki karbi musulunci agurin mahaifinsa, bana son mamanku tazo ta tarar dake agidan nan,ubangiji Allah yayi miki albarka yasake baki *Wani haske* acikin rayuwarki"

Mahaifinta yafada yana kwallar farin ciki, ita kanta goodness itama hawayen take yi, tashi tayi tafita ta koma gidanta, katoton dogon hijabin da Ummu al'amin ta bata ta dauko ta dorashi asaman doguwar rigarta ta tafi gidansu jabir,

A soro ta tarar da Malam mahaifin jabir, Malam yayi mamakin ganinta amma lokacin da yaji kudirinta sai mamakinsa ya sake karuwa gamida farin ciki, wanda har sai da hakoransa suka bayyana,

"Dafarko dai ina fata ba wani ra'ayine yasaki sha'awar karbar musulunci ba? Ina fatan zaki yi hakanne domin Allah saboda dukkan aiki sai da niyya shiyasa acikin hadisin da aka karbo daga Umar Allah ya kara masa yarda yace annabi Muhammad yace dukkan aiki sai da niyya sannan kowanne mutum akwai abinda yayi niyya, duk wanda yayi hijira domin Allah da manzonsa to sakamakon hijirarsa tana ga Allah da son manzonsa,wanda yayi hijira kuwa domin duniya ko wata k'awa, ko dan wata mace da zai aura to sakamakon hijirarsa tana ga abinda yayi hijira dominsa, shugaban masu rawaito hadisai ne ya rawaito wannan hadisin _(imamul muhaddasina)_"

Kanta ta daga "ba wani ne ya tilastani ba, kuma ba dan wani nayi hakan ba face dan Allah"

"To alhamdulillah, da farko dai ina son kisani shi musulunci yana nufin mika wuya ga Allah, da jawuwa agareshi da biyayya,da kuma tsarkakewa daga shirka,

Sannan shi musulunci yana da ginshikai  guda biyar kamar yadda annabi Muhammad yafada acikin ingantaccen hadisi cewar angina musulunci akan abubuwa guda biyar, nafarko shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah sannan annabi Muhammad manzon Allahne, sai tsayar da salla, salla itace aiki nafarko da zafara bincikawa ranar tashin alqiyama, idan ta gyaru dukkan ayyuka sun gyaru idan kuma an samu sabanin haka to abin sai dai ace Allah ya kyauta,abu na uku shine azumin watan ramadan,

Amma babu tilas akan marar lafiya, ko kuma tsoho wanda shekarunsa suka ja ko kuma karamin yaro, ko matafiyi duk an samu rangwame akan wadannan mutanen,

Abu na hudu kuma shine bayar da zakka ga wanda ya kasance mai arziki, sai abu na karshe, ziyartar dakin Allah ga wanda ya samu dama, dalilin haka saboda hadisin da aka karbo daga Umar Allah ya kara masa yarda yace: wata rana muna zaune da annabi Muhammad sai wani mutum ya bullo mana, mai tsananin farin tufafi, mai tsananin bakin gashi, babu alamun tafiya agareshi kuma babu daya daga cikinmu wanda ya sanshi har ya zauna akusa da annabi Muhammad, ya jingina gwiwowinsa ajikin gwiwoyinsa ya dora tafukan hannunsa akan tafukan hannunsa yace ya Muhammad bani labarin musulunci, sai annabi yace,

Musulunci shine shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ni manzon Allah ne, da tsayar da salla da bada zakka da azumin watan ramadana da ziyarta dakin Allah ga wanda ya samu iko, sai yace kayi gaskiya, sai muka yi mamakinsa yana tambayarsa kuma yana gasgata shi,

To wannan shine musulunci sannan kuma duk musulmi ana son ya zama mai imani, rukunan imani guda shida ne, imani da Allah, imani da mala'ikunsa,littattafansa,manzanninsa da ranar karshe, da yin imani da kaddara mai kyau da marar kyau,

Dalilin wadannan rukunai guda shida shine fadin Allah madaukakin sarki "'Ba aikin alkairi bane kadai ku juyar da fuskokinku gabas da yamma ba, sai dai aikin alkairi ya hadar da yin imani da Allah, da ranar karshe, da mala'iku, da littafi da manzanni"' _(Qur'an chapter 2)_,

Dalilin kaddara kuma fadin Allah madaukakin sarki "'hakika mun halicci dukkan komai cikin kaddara"'

Gyada kai goodness tayi "Malam nagode madalla Allah ya saka maka da alkairi"

"Babu komai malama domin yanzu kema kin zamo malama, sai dai akwai abubuwan da nake so ki kiyaye,

Abu nafarko shine kowanne aiki akwai sharuddan karbar aikin, sharrudan sune nafarko sai anyi aikin domin Allah, na biyu kuma sai anyishi irin yadda annabi Muhammad ya koyar dashi, baya halatta ga mutum domin yana son ya samu lada ya kirkiri wani aiki dakansa acikin addini, anfi son komai zaka yi kayi shi kan koyarwar annabi shiyasa awani hadisi annabi sallallahu alaihi wasallam yace:

"'Duk wanda ya kirkiro da sabon al'amari acikin wannan addinin, wanda baya daga cikinsa, to anmayar masa dashi"' _(muttafakun Alaih)_

Ko wanne aiki mutum idan zaiyi to yayishi akan sunnah, sannan yayishi yanda sahabai suka yi domin acikin addini bai halatta mutum ya kafa hujja da iyayensa ba ko kuma malamansa, acikin musulunci mutum dayane aka yarda ya kafa hujja da mahaifinsa shine wanda ya kasance babansa annabine to wannan an yarda yayi koyi dashi amma bayan wannan to haramun ne mutum ya tashi yana bin addinin iyaye da kakanni, mutukar ba akan daidai suke ba,

Shiyasa sharadin karbar aiki sai anyi aikin kamar yadda annabi ya koyar ko kuma yadda sahhabansa suka koyar ko yadda salihan bayi suka yi,

Son manzon Allah wani yanki ne daga cikin yanki na imani, domin acikin hadisin da aka karbo daga Anas dan malik Allah ya kara masa yarda yace annabi Muhammad sallallahu alaihi wassalam yace:

_"'Imanin dayanku bazai cika ba har sai nafi soyuwa agareshi fiyeda yayansa, da iyayensa, da sauran mutane baki daya"'_

Son annabi shine kiyaye dukkan abinda yayi hani dashi da kuma yi masa da'a da yarda da dukkan abinda ya fada, mutum baya zama mumuni na kwarai har sai yayiwa annabi da'a, fadin Allah madaukakin sarki:

_"'kuma abinda manzo ya baku to ku karbeshi, kuma abinda ya haneku dashi to ku barshi. Kuma kubi Allah da takawa, lallai Allah mai tsananin ukuba ne"'_ _(Qur'an, chapter 59,verse no 7)_,

Ya zama wajibi ga dukkan mai imani yaso annabi kuma yayi koyi dashi sannan yayi koyi da sahabbansa ya sosu ya kaunace sannan ya nisanci dukkan kirkirarren abu wanda annabi bai yishi ba kuma sahabbansa ma basu yi shi ba, bayan mutum yaso annabi da iyalan gidansa ana so yaso sahabbansa ya kaunace su domin babu wasu wanda suka fi kusanci dashi sama dasu, sunada daraja da matsayi har awurin Allah, sune mutanen da suka rayu dashi suka taimakeshi suka bashi kwarin gwiwa suka yi masa biyayya alokacin da kowa yayi masa tawaye, matsayin sahabbai awurin annabi Allah ne kadai yasan yawanshi shiyasa ahadisin da aka karbo wurin Abi sa'idil kudri manzon Allah (S.A.W) yace:

_"'Kada Ku zagi sahabbai na, na rantse da wanda raina yake hannunsa da ace dayanku zai ciyar da zinare (sadaka) kwatankwacin girman dutsin uhudu to bazai kai matsayin dayansu ba adaraja,koda rabin dayansu bazai kai ba"'_ Bukhari ne ya rawaito,

Sannan dukkan abinda zakiyi wanda ya shafi ibada to kiyi bisa sunnar annabi Muhammad koda kuwa ace salla ce domin ita kanta sallar annabi yace: _"'kuyi salla kamar yadda kuka ga ina salla"'_ amma sam sallar ma yanzu ba ma yinta cikin kushu'i da nutsuwa, sannan na horeki da nisantar duk wani Sabon abu domin bidi'a batace haka annabi ya fada kai asalima annabi cewa yayi _"'Duk wanda yayi min karya da gangan to ya tanadi wurin zamansa agidan wutar jahannama"'_
Nasan dukkan wadannan abubuwan mijinki zai sanar dake idan ya dawo, amma yanzu bayan na baki Kalmar shahada kin karba zakije kiyi wankan shiga musulunci sannan kuma zaki shiga cikin gida domin zasu koyar dake abubuwan da zaki gabatar"

Anan take Malam ya bawa goodness Kalmar shahada ta karba, sannan yace wanne suna take sha'awar komawa tace A'isha sai Malam yace mata,

"Hakika sunan A'isha sunane mai girma domin sunane na daya daga cikin matan fiyayyen halitta wacce yafi so yafi kauna domin an tambayeshi aduniya waya fi so yace A'isha, akace amaza fa yace babanta Abubukar, to amma ni anawa ganin ki karbi suna *BAHIJJA* domin sunane mai daraja awurin jabir mijinki, sunan mahaifiyarsa ne wacce ta rasu tun yana jariri dan wata takwas shiyasa yayi burin inama ace al'amin mace ne da ya mayar da wannan sunan"

"Malam asamin bahijjan domin yanzu nima naji ina kaunar sunan" tafada idanuwanta dauke da kwallar tausayin jabir mijinta domin ita bata taba sanin shi maraya bane, Allah mai yadda yaso hakika Allah baya barin wani dan wani, ita dai yanzu ta yarda addinin musulunci akwai tarin *Wani haske* mai yawa acikinsa wanda ta shaida hakan.

Cikin gidan suka shiga tare da Malam yayi musu bayani, nan suka shiga gwada mata yanda ake yin wankan musulunci da dukkan sauran wankan da ya wajaba akanta, dama alwala ta iya domin akwaita acikin bible,

Har dare takai agidan ana koya mata abubuwan da suka shafi addini, littattafan addini wadanda aka rubuta da turanci Malam ya bata irinsu, _40 Rabbana_, _Good Muslim_, _40 hadiths_ da sauransu,

Gida ta koma ta zauna tafara tsefe tulin gashin kantin dake kanta, yau jinta take cikin wani farin ciki gashi wata iska mai dadi tana shigarta ta ko ina lallai musulunci shine addini na gaskiya, hakika musulunci shine addinin Allah .

Anty Bilkisu ta kira tayi mata albishir sannan ta roketa kan tazo gobe domin sake koyar da ita wasu abubuwan masu muhimmaci, washe gari kuwa sai gata nan ta wunar mata sai yamma ta tafi amma fa mahaifiyarta har yau bata san abinda ke faruwa ba haka shima jabir bata sanar dashi ba har lokacin tafi so tayi masa bazata sai ya dawo zata sanar dashi.

***

Jabir kuwa yana can madina tare da ummu al'amin da al'amin din, in banda soyayya babu abinda suke yi shida ummu, yauma kwance yake agefenta yana rungume da ita ta baya, yana shafa gashin kanta, jin tayi shiru ya tabbatar da cewar tayi bacci, ahankali ya tashi ya fita,

Zama yayi yafara kiran wayar goodness,lokacin da ya kirata tana zaune afalonshi tana karanta abinda aka dora mata agidan malam saboda kullum sai taje an doro mata karatu wani lokacin ma can take wuni,

"Hello abbu" tafada acan Kasan makoshinta,

"Kidaina kirana da sunan nan fa" yafada cikin sanyayyiyar muryarshi,

"Saboda me?" Ta fada tana murmushi,

"Saboda ban haifi kamarki ba, iya al'amin na haifa" ya bata amsa,

"Inji wa? Nima fa ka haifi kamata" ta fada cike da son ta zunguroshi,

"Kar ki kashe min kasuwa, yanzu idan naje neman auren ta uku taji kina cemin abbu sai taki aurena tace nayi mata tsufa tunda na haifi katuwa kamar ki"

Ba karamin mamakin abinda ya fada tayi ba wato ashe shima ya iya bayar da amsa, wani abu taji ya soki ranta wanda tafi zaton kishine, zuruf ta tashi zaune tana sake makale wayar acikin kunnenta,sannan abinda yafi bata mamaki shine kiranta da katuwa da yayi,

"Abbu me kace?" Ta sake tambayarsa,

"Abinda kunnenki yaji, ni kidaina kirana da abbu" ya mayar mata da martani amma aranshi yana tuna girmanta, tabbas yarinyar katuwa ce ta wasu wurin,

Shiru tayi ta kasa yin magana gaba daya kishi ya gama lullube zuciyarta,

"Hello goodness are you there?" ya kira sunanta

"Nima kadaina cemin goodness" tafada tana zumburo baki kamar yana kallonta,domin yanzu ji take ta tsani wannan sunan,

"Why?"

"Saboda na sauya suna"

Dariya ya danyi amma sai bai dauki maganar tata dagaske ba,

"Yaushe kika canja suna ban sani ba, sannan wanne sunan kika koma?"

Shiru tayi masa domin tasan idan ta fadi sunan zaiji babu dadi saboda sunan mahaifiyar sa ne,

"Bana fadar sunan?"

"Meyasa?" Ya tambayeta wanda shi kansa ya rasa gane kansa da kansa, dadin hirar da suke yi yake ji,gashi yau tunda yaji muryarta sai ya ke jin wani irin yanayi atare dashi wanda bai san menene ba, amma jin abin yake tun daga babban dan yatsansa har zuwa tsakiyar kansa,

"Saboda bana fadar sunan" ta bashi amsa,

"Oya fada min kawai tunda baki son waccan sunan kinga idan kika fada min sai in daina kiranki dashi"

"Bazan iya fada ba" tasake bashi amsa tana lankwashe murya,

"To kashe wayar ki yimin text sai in kiraki"

Wayar ta kashe ta tura masa text din sunan, lokacin da ya ga text din,mamaki ne ya kamashi gamida al'ajabi, to a ina tasan wannan sunan yana da muhimmanci awurinsa, murmushi yayi ya sake kiranta,

"Hello binti, waye ya fada miki sunan nan?"

"Menene binti?" Ta tambayeshi,

"Yarinya, ke ai yarinya ce tunda kina kirana da abbu"

"Abbu a ina ta ukun take?" Ta tambayeshi cikeda shagwaba, shi yama manta da maganar budurwar da yayi ashe ita abin yana ranta bata manta ba,

"Wacece?" Ya tambayeta shima,

"Agaida al'amin" tana gama fadin haka ta kashe wayar gabaki daya cikeda kishi, abin dariya ya bawa jabir,

Motsin da yaji abayansa ne yasashi juyawa nan yaga Ummu tsaye tana rikeda labulen dakin, tana kallonshi da alama duk taji hirar da suka yi da binti.

_Masu karatu sai mun hadu ashafi nagaba (shafin soyayya)._


_*Ummi Shatu*_
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [9/29, 9:02 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE..!*

  _*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_86-90_


~~~Jiyowa yayi yana kallon ummu al'amin,

"Har kin tashi daga baccin?"

"Wallahi kuwa amma yanzu zan koma, naji kana waya da antyn al'amin"

"Ehhh nida itane, yau rikici take ji, da alama yarintar ta motsa" ya fada yana murmushi,

"Yarinta?" Ta tambayeshi,

"Ehh mana, ai dan bakiga shirmen da tai tayi bane itada al'amin lokacin da yana can"

Murmushi tayi ta juya ta koma cikin dakin, tashi shima yayi yabi bayanta.

  Kishi fal dankare acikin kirjin goodness tunanin jabir kawai take yi da tuno kyakkyawar surarsa mai daukar hankali, gaba daya hankalinta ya gama tashi gani take kamar dagaske auren zai sake yi,

Wayarta ta sake kunnawa ta fara kiransa, yana kwance ajikin ummu ya daga wayar,

"Binti" shine kawai abinda yace,

Cikeda shagwaba tafara magana "abbu dagaske kake yi?" Ta tambayeshi wanda ita kanta bata san lokacin data yi tambayar ba,

"Wai me?" Shima ya tambayeta, tashi yayi daga kusa da Ummu ya koma falo,

"Abbu wai meyasa kake cemin katuwa ne?" Tafada ashagwabance, jin shagwabar da take yi masa yake har cikin ransa,

"Ke katuwa ce mana,ko baki sani ba?"

"Abbu nidai ka fada min idan dagaske kake yi"

"Wai menene dagaske"

"Ta ukun da kace zaka yi"

  Dariya ce taso subuce masa jin maganarta, gashi duk tabi ta damu bata san shi da wasa yake yi mata ba,

"Dagaske mana, bayan itama zan sake aurar wata kinga hudu kenan"

Kirji ta dafe da karfi, sai kuma ta kashe wayar kit ta ajiyeta agefe, tunani tafara tana dafe kuncinta, kishine tsababa acikin ranta,

Wayar ta sake dauka ta kirashi,

"Yau ba zaki barni inyi bacci bane?" Ya fada lokacin da ya daga wayar,

"Abbu yanzu nida Anty bamu isheka ba har sai ka sake wani auren?"
 
Tafada tamkar zata fashe da kuka, har sai da yaji mamakinta aranshi yana tunanin kishi irin nata,amma burgeshi shagwabarta take yi,

"Ehhh" yafada kansa tsaye yana dan nazarinta,

"To a ina take?"

"Tana Nigeria ki bari idan nadawo zaki rakani wurinta"

Ranta taji yayi bakikkirin amma ta daure tace,

"Yaushe zaka dawon?"

"Acikin next week zan dawo"

"Allah ya kaimu, agaida ummu al'amin"

Wayar ta katse bata jira amsarshi ba, ruf da ciki tayi akan doguwar kujerar shi, kishine kawai ke dawainiya da ita,

"Mtsssss me za ayi da auren mai mata yanzun ma tasan yana can tare da matarsa ita kuma gashi tun zuwanta gidan babu abinda ya taba hadasu"

Tafada acikin ranta, haka ta zauna ta bata lokaci da yawa tana cikin yanayi na bacin rai,

Lokacin da taje bacci ma ta dade bata yi baccin ba juyi kawai take tana tunanin jabir, pillow taja ta rungume tana tuno mijinta abin sonta.

*

Tunda satin da jabir zai dawo ya kama tafara shirin tarbarsa, kullum sai ta shirya masa kayan dadi amma shiru sai taji babu alamunsa, yauma sai da tayi masa girki tayi kwalliya sosai amma har 9 shiru,

Wayarshi ta kira yana dauka ta fara kukan shagwaba,

"Abbu bazan sake yi maka girki ba har sai ka dawo, kullum sai nayi sai kaki dawowa"

Sai da tsikar jikin jabir ta tashi saboda yanda take masa wannan kukan shagwabar,

"Binti dama ai cemiki nayi acikin satin nan ban fada miki date dinba, kidaina wahalar da kanki, ki bari kawai duk ranar da nadawo sai kiyi min girkin ina gidan, kinji?"

"Nidai abbu ban yarda ba ka fada min" ta sake fada cikin shagwaba,

"To ai kinga saura 3 days week din ya kare, dan haka may be gobe zan dawo ko jibi ko...."

"No abbu nidai ban yarda ba ka fadamin Allah"

Lumshe idanunshi yayi acikin ranshi yana cewa "yarinyar nan tana son tayar min da hankali fa" amma afili sai yace,

"Kwana uku ne fa kawai binti ai kinga nabaki satar amsa"

"Ok to nadauki jibin, gobe bazan yi maka girkin ba, sai jibi, idan ranar ma baka dawowa shikenan ko ranar da zaka dawo bazan yi maka ba"

Duk wadannan maganganun cikin kukan shagwaba tayi su,

"Haka kika tsara?"

"Ehh abbu" tasake fada cikin sigar farko, ita kanta wani iri takeji ajikinta bare kuma jabir wanda ko kwakkwaran motsi ya kasa,

"Ohhhhh abbu my cooking, girkina ya fara konewa, bye bye" wayar ta katse ta ruga kitchen da gudu inda take dafa indomie guda daya tal dan shegen kwadayi,

Bin wayar jabir yayi da kallo yana murmushi tareda tuno shiririta irin ta goodness.

Aranar da zai dawo wani boutique ya shiga ya kwaso mata english wears hadaddu _(sexy dress)_ masu kyau da aji domin yasan bata saka atamfa ko shadda kullum cikin kananan kaya take,

Wasu kyawawan braziers yagani amma yana tantamar ko zasu yi mata daidai kuwa saboda yaga ita din bata wasa bace, braziers din sunyi masa kyau sosai domin masu daukar hankaline, diba kawai yayi aranshi yana tunanin idan sunyi mata kadan tasan yadda zata yi dasu,

Akwati guda ya ciko mata da kananan kaya bayan shima ya lodi nashi, gida ya koma inda ummu ke jiranshi ita da al'amin duk tabi ta damu saboda tafiyar da zaiyi ya barta,

Hannunta ya kama ya kwantar da kanta agefen kafadarshi al'amin kuma yana kan cinyarshi,

"Haba Ummu menene abin damuwa ne?"

"Abu al'amin dan Allah kadawo hajji, zamu yi kewarka nida al'amin"

Murmushi jabir yayi "ummu ba lallai ne nazo aikin hajji ba saboda wasu dalilai masu yawa, kiyi hakuri idan sabuwar shekara ta kama zan turo muku kudi sai kuzo gida"

"Yawwa abu al'amin Allah ya saka da alkairi, Allah ya kaika lfy"

Ya dade tare dasu yana rarrashinsu kafin yayi wanka Ya shirya suka rakashi har airport, wani kwalin chocolate al'amin ya bashi wai ya kaiwa goodness, murmushi jabir yayi,

"Ohh Al'amin ka rasa abinda zaka bawa antyn naka sai chocolate?"

"Abbu anty mayyar chocolate ce wani lokacin ko abinci bata ci sai dai tai ta shan chocolate"

"To shikenan al'amin zan kai mata"

Sallama yayi musu ya shige cikin jirgi, Ummu harda yar kwallar ta yayinda al'amin keta daga masa hannu, suna nan tsaye har jirginsu ya tashi,sai da suka ga tafiyarsa sannan suka koma Gida.

K'arfe uku na yamma jirginsu ya sauka yayiwa driver waya yaje ya daukoshi,

Tana falonshi ta baje akasan carpet tana bacci daga ita sai yar body hug dinta baka da short trouser milk colour, dama tana hutun salla,

Yana saka kansa cikin falon ya hangota, idonsa ya sauke akan lukuta lukutan cinyoyinta wadanda suke afili domin wandon data saka iya rabin cinyoyinta ya iya rufewa,

"Masha Allah"shine kawai abinda ya iya fada bayan ya lashi lips dinsa,

Ciki ya karasa ya tsaya akanta yana karewa halittarta kallo kamar yau ya soma ganinta,

Babu zato tayi wani juyi tare da wata mika nan rigar jikinta tayi sama cikinta ya bayyana,

"La ilaha ilallah, muhammadur rasulillah"

Shine abinda yaji ta fada, ahankali ta soma bude idonta, shidai jabir mutuwar tsaye yayi saboda jin abinda ta fada,

"Lahh abbu yaushe ka dawo?" Tafada tana kokarin tashi zaune,

Kan kujera ya karasa ya zauna yana kallonta,

"Yanzu shigowata kenan yar lukuta"

Bakinshi ta kalla ta hadiyi yawu ita dai aduniya tana son bakin nan na jabir, duk ranar data kamashi babu sauki ta ayyana hakan acikin ranta,

"Sannu da zuwa, bari naje nayi maka girki abbu" tashi tayi tana sake yin wata mikar ta fita, kitchen ta shiga duk tana cike da murnar ganinsa jinta take kamar anyi mata albishir da gidan aljanna,

Kasancewar tanada kayan amfaninta wanda zata bukata yasata dora jalop din shinkafa da kayan lambu, sai murna take har ta yanke hannunta wurin yanka cabbage,

Tana kokarin yanda zata yiwa yatsan nata jabir ya shigo cikin kitchen din,

"Yankewa kika yi?"

Boye hannun tayi ta bayanta ta jiyo tana kallonshi, bata son ya gani saboda kar yace sai ya saka mata hydrogen,

"No abbu" tafada tana raurau da idanuwanta,

"Ya salam" yafada acikin ranshi,

"Bani to ingani, bazan saka miki hydrogen ba Allah"

Fito da hannun tayi ta mika masa, rike hannun yayi ya fito da ita zuwa falonta, dan kyalle ya samu ya daure mata wurin ita dai tana daga tsaye tana kallonshi yana sanye da jallabiya ruwan kasa kansa babu hula amma ba karamin kyau yayi mata ba ahakan,

Kitchen ta koma ta ci gaba da girkin da take yi shikuma jabir ya fita zuwa masallaci domin lokacin sallar la'asar yayi,

Bayan ta sauke girkin sai da ta hada lemon kwakwarta kamar yadda ta saba amma na yau harda jabir tayi shi,

Wanka ta shiga tayi ta fito daure da towel sai ga jabir ya shigo sashen nata,

Dan doddoka kafafunta akasa tafara yi tana rike towel din jikinta,

"Abbu bana salla kabani pad"

Dama can ai ba sallar kike yi ba ya fadi hakan aranshi amma afili cewa yayi,

"Ke wai kullum acikin jini kike ne? Koda yaushe jini,koda yaushe jini sai kace wata marar lafiya"

Farr tayi da idanuwanta tana matse cinyoyinta gudun kar tayi staining,

"Abbu lafiyata k'alau, ni sau biyu nake yi awata"

Tab nashiga uku kenan, yafada aranshi danma shi ba mai yawan bukata bane, sai yayi wata bai bukaci mace ba wani lokacin ma zai iya yin fiyeda haka,

Kallonta yayi sai ya hango jinin yana bin cinyoyinta,

"Ina zuwa bari na kawo miki" juyawa yayi ya fita, yana fita ta fashe da dariya dama tana sane tayi masa haka saboda tun lokacin da yayi mata maganar wannan ta ukun da yace zai aura ta daura aniyar haukatashi da salonta kala kala wadanda anty Bilkisu ta koyar da ita,

Tana nan a inda yabarta har ya dawo yana rike da pad din guda biyu,

"Gashi,amma haka wannan abin yake yi miki rushing?"

"Ehhh abbu amma zuwa kwana ukune, yana yin kwana uku zai daina"

Juyawa yayi ya fita baice da ita komai ba, nan tasake komawa toilet tayi wani wankan ta fito, shiryawa tayi cikin riga da wando na jeans baki rigar kuma light green mai gajeren hannu,

Abincin da ta shirya ta dauka ta nufi sashen jabir, yana zaune yana waya dasu al'amin da ummu, abincin ta ajiye ta tasashi agaba kamar zata shige cikin cikinsa, abin har dariya yaso bashi gashi ta wani kafeshi da ido duk motsin da bakinsa yake yi akan idonta ne,

Wayar ya mika mata yaja abincin ya zuba ya fara ci yana sauraren hirarta itada al'amin wanda gaba daya yarintace aciki,

Har yagama cin abincin bata gama wayar da al'amin din ba, lemon kwakwar da tayi yasha madara dan haka ba karamin dadi yayiwa jabir ba, sai da ya shanye rabin jug amma abincin kadan yaci,

Kan doguwar kujera ya koma ya zauna ya kamo huda tv yafara kallon wani program da suke yi alokacin mai taken _Da'awah workshop_,

Yana jin lokacin da goodness tagama wayar ta ajiye,guntun abincin da ya rage acikin filet tasa hannunta zata ci sam ta manta da yankewar da tayi dazu a yatsanta, tana saka hannunta taji yaji ya ratsa wurin, babu shiri ta zubar abincin ta zabura tayi inda jabir ke zaune,

Tana zuwa tasaka kuka tare da zama akan cinyarsa,

"Abbu yaji..."

Hannun ta mika masa tana kuka,

Rike hannun nata yayi baiyi wata wata ba yasa dan yatsan abakinsa ya fara tsotse mata shi,

Kanta ta kwantar acikin kirjinshi tana jin wani sanyi har cikin ranta,

Tsotsar dan yatsan nata yaci gaba dayi yanayi yana hura mata iskar bakinshi a wurin, acikin zuciyarsa kuma yana tuna rak'i irin na mata su mata babu wuya sun yiwa abu kuka komai kankantarsa.

In banda haka menene abin kuka dan yaji yashiga wurin da ta yanke,

Cusa kanta cikin jikinshi take tayi tana shakar kamshin turarensa na _beautiful touch_ wanda ya cakudu da kamshin _special oud_ ita dai arayuwarta tana tsananin son jabir domin jin sonshi take har acikin jinin jikinta yana yawo,

Mak'aleshi tai tayi shikuma sai tsotsar yatsan nata yake yana hura mata iska awurin, gaba daya ta gama shagala sai kamshinsa take shaka mai mutukar dadi, hakika babu abinda yafi kamshi dadi ajikin mutum musamman ma Ma'aurata amma wasu mazan sam tsafta bata damesu ba harma wasu matan suma duk samma kal, ya kamata arinka kulawa da tsafta domin tana daga cikin imani inji fiyayyen halitta, sannan turare abune da yake kara soyayya, duk lokacin da mutum ya kasance mai mu'amula da turare to kowa zakaga yana burin zama kusa dashi amma idan sabanin hakane to mutane basa kaunar hada wurin zama dashi,

Tana ta yan tunane tunanenta idonta a lumshe bata san lokacin da bacci ya dauketa ba shi kansa jabir bai san tayi baccin ba kawai dai yaji shiru ta daina kakkamashi sabanin dazu data rinka kankameshi tamkar zata koma cikin cikinsa,tana faman cuccusa kanta acikin kirjinsa,

Yana rikeda hannun nata acikin tattausan hannunsa wanda yafi na baby pherty Xarah laushi, dan yatsan abakinshi ya dago manyan idanuwanshi ya kai dubansa gareta nan yaganta tana bacci abinta,

"Wuh binti case, komai kuka kike masa, hydrogen kuka, pepe kuka,ruwan zafi kuka, zan so naga ranar da zaki je maternity" ya fada ahankali kamar da wani yake maganar, koda yake matanfa kenan,ya ayyana hakan aranshi,

Zare dan yatsan nata yayi daga bakinshi ya zameta daga jikinshi ya kwantar da ita akan doguwar kujerar ya tsaya yana kallonta yana tunanin anya kuwa idan tayi kwakkwaran juyi ba zata fado ba,

"Kai ai yarinyar ce ta fiya lukutanci yanzu idan nace zan kaita daki wuya zansha, kila ma ta tashi tai tayi min rikici" ya fadi hakan acikin zuciyarshi,

Rabuwa yayi da ita ya shiga cikin _bedroom_ dinshi yayi wanka yasha manyan kaya, dafaffen boyel light blue riga da wando harda babbar riga, hularshi samfarin dinkin zannabukar itama light blue,agogon da ya daura na azurfa ne kirar kamfanin _Gucci_ ,kamar koda yaushe turare masu dadin kamshi da sanyi ya fesa, yasaka takalmi half cover light blue ahankali ya fito daga cikin dakin nasa idonsa akan goodness wacce take mike tana faman bacci,

Sadaf sadaf ya fice daga falon domin yasan idan har ta tashi cewa zata yi sai tabishi,

Fita yayi shida mal idi driver, shagon aski ya fara zuwa bayan ya fito kuma ya nufi gidan mahaifinsa,

Acikin babban falonshi ya sameshi zaune yana hutawa amma hannunsa kuma rike yake da carbi yana ja,

Bayan yan gaishe gaishe ne Malam yake ce masa,

"Kaga abinda nake fada maka ko jabiru? Yanzu gashi ta sanadiyyarka musulunci ya samu karuwa, dama shiyasa tun farko nace kayi hakuri wannan yarinyar *wani haske* ce agareka kamar yadda kaima kake *wani haske* acikin rayuwarta, sanin kankane duk mutumin da yayi sanadiyyar da wani ya shiga musulunci yanada rabo mai girma, rannan kawai ina zaune sai ga yarinyar nan tazo min da magana mai dadi cewar zata karbi musulunci, agaskiya nayi farin ciki kuma dan Allah jabiru ka zauna da yarinyar nan zama na amana, tunda yanzu kasan dole zata fuskanci matsalar rayuwa dalilin shiga musuluncin da tayi, sannan kuma yanzu ta amshi sunan mahaifiyarka, wato BAHIJJA, nasan ta sanar dakai komai"

Tunda Malam yafara wadannan bayanan jabir sakin dan mitsitsin bakinshi yayi yana kallon malam domin bashida masaniyar duk wadannan abubuwan, haba lallai biri yayi kama da mutum tunda dazu lokacin da ya tarar da ita tana bacci tana farkawa da salatin annabi ta fara,bayan haka kuma lokacin da zata karbi pad awurinshi ce masa tayi yau bata salla,sannan lokacin da yana madina tafada masa cewar yanzu ta koma bahijja sai dai shi sam bai yarda ba ashe dagaske take, wani farin cikine marar misaltuwa ya soma shigarsa ga wani yanayi da ya samu kanshi aciki, kyakkyawar fuskarta ya shiga hangowa acikin zuciyarsa,

"Jabiru lafiya?" Malam ya tambayeshi jin yayi shiru bai bashi amsa ba,

Sai alokacin ya dawo cikin hayyacinshi,

"Lafiya lau malam, Allah ya kara girma, Allah yasa ta shiga musuluncin kenan har abada kuma Allah yasa ta mutu akansa"

"Amin jabiru",nan Malam yayita saka masa albarka yana yi musu kyakkyawar addu'a shida iyalansa, awurin malam yayi zamansa bai koma gida ba har wurin 9 nadare.

***

  Tunda jabir ya fita ya barta take bacci sai daf da magrib ta iya tashi, bude idonta tayi taganta akan kujera,

Tunowa tayi da abinda ya haddasa mata barcin, wani murmushi tayi tana mai kallon dan yatsan nata wanda jabir dazu yayita tsotsa kamar ya samu sweet, "tabbas maganar Anty Bilkisu ta zama gaskiya" tafada cikin zuciyarta domin itace ta bata wannan sirrin cewar awurin mijinta ta zamto yar karamar yarinya tamkar yar 14,sannan ta dimamci shagwaba kamar yar yaye hakan zai sa miji ya mace akan kaunarta,

Yanzu gashi tun ba aje ko inaba har tafara ganin amfanin shagwaba,murmushi ta sake yi akaro na biyu ta tashi taje wurin abincin da tabari dazu bata ci ba, dauka tayi taci ta koshi sannan ta kwashe kwanukan ta nufi sashenta aranta tana tunanin yadda akayi jabir yabar gidan batare da taji motsin fitarsa ba,

Sabon wanka tayi ta hade cikin wata doguwar riga ja mai siririn hannu, tattauran gashinta ta kama ta tufke tanayi tana tsaki domin duk ya yi under grow, dolenta tasaka masa relaxer indai tana son taji sawaba gashi gashin mai cika ne cukus,

Turarruka masu kamshi ta dan feffesa amma sai taji kamshinsu baiyi mata dadi irin na jabir ba, sashensa taje ta shiga _bedroom_ dinshi taje gaban mirror ta dauki nasa ta feffesa nan dakin ya gauraye da kamshinsa,

Fitowa tayi yanzu jinta take kamar suna tare dashi saboda ga irin kamshinsa nan tana shaka,

Part dinta ta koma ta kunna kallo yanzu bata yin kallon ma da yawa sama sama take yinsa, ganin har 9 tayi yasata fara tunanin to ina jabir ya tafi kodai wurin ta ukun ya tafi ne, itafa ta ukun nan ta shiga ranta tun lokacin da jabir ya fada taji ta kasa mantawa da maganar.

Tana nan zaune ita kadai tana kallo har 9:30 tayi,

Idonta kyar akan tv ko kiftawa bata yi ya turo kofar ya shigo tun kafin yayi sallama kamshin turarenshi ya ziyarci hancinta,

Dagowa tayi ta kalleshi lokacin da yake rufe kofar bakinshi dauke da sallama,

Sallamar ta amsa tana mai cigaba da kallonsa yau dinnan ba karamin kyau yayi ba cikin blue din boyel din da yasa,

"Wowww....!" Tafada ahankali tana kallonsa,

Zama yayi akan kujera "wato bakya jin magana ko? Har yanzu kina nan da wannan mayen kallon Daren da kikeyi ko? Dama baki daina ba?"

Kallonsa ta sake yi kamar yaune tafara ganinsa "abbu wlh ba nayi, anadade inkai 11"

Tafada cikin shagwaba,

"Ahaf" kawai yace ya mike zai fita,

Mikewa tayi da sauri, "abbu tsayani mu tafi tare"

Kayan kallon ta kashe ta bishi suka fita tare, a falonshi ta zauna ta fara duba kayan ciye ciyen da ya shigo dasu, kaza ce gasasshiya da fruits su kankana, apple, banana, oranges da sauransu, sai kuma chocolate wanda tasan ko ba afada mata ba ita ya siyowa,

Filet da fork ta dauko da wuka ta zauna ta yanyanka masa fruits din tabar sauran da zummar gobe zata yi musu lemon kankana dasu,

Tana tsaka da shan chocolate dinta ya fito sanye da kayan bacci, _maroon_ colour masu santsi riga da wando, tana kasa akan carpet azaune shi kuma yana kan kujera zaune, akan stool din gabanshi ta ajiye masa fruits din takoma ta zauna taci gaba da shan chocolate dinta sai da tasha da yawa sannan ta fara cin gasasshiyar kazar, yana zaune yana kallonta ta gefen ido yanda bama zata san yana kallonta dinba,

Sai da taci rabin kazar sannan ta tashi ta dauki tsinken sakace hakori tafara sakatar hakorinta tana son cire naman da ya makale mata ahakori, kasa cirewa tayi dan haka ta matsa kusa da jabir,

Kneel down tayi agabansa ta mika masa tsinken,

"Abbu pls ka cire min, nakasa cirewa"

Kallonta yayi ya karbi tsinken "oya bude bakin" budewa tayi ta daga kanta ya fara cire mata, ido ta runtse ta dafe hannunsa wanda ya dafe kanta dashi,

"Ko sakacen hakorin ma kuka zaki yi masa?" Ya tambayeta yana mai sake tura tsinken matsematsin hakorinta,

Janyewa tayi ta matsa gefe "abbu barshi haka, idan nayi brush zai fita"

Tashi tayi ta kwashe sauran kayan ta fita taje bedroom dinta tayi brush ta sake shafa turare ta dauko wata arniyar rigar barci _coffee_ colour mai santsi wacce sai ta baya ma ake daureta da madaurinta, bata da wani girma dan iya gwiwa take sannan siririn hannu gareta,

Yar karamar hula ta dauka ta saka akanta takoma sashen jabir, acikin dakinsa ta sameshi zaune agefen gado gabanshi laptop ce a ajiye yana dubawa,

"Abbu daure min rigata ta baya nakasa daurewa"

Dagowa yayi yana kallonta, wani irin kyau yaga rigar tayi mata gashi tayi mata cif cif komai yaji,

Shagala yayi lokacin da yake d'aure mata rigar, saboda gaba daya gadon bayanta a bayyane yake gashi wasu zarirrika ne wanda suke a tagaban rigar suka taho har ta baya,kwata kwata ma ya kasa d'aurewar, idan ya d'aure sai ya kunce sai ya sake d'aurewa haka yayita yi har wurin sau goma, ita dai goodness tana zaune ta juya mushi baya tana jiran ya gama,

Dakyar ya iya hakura ya d'aure mata ya janye hannunshi daga jikinta,

"Abbu ina al'amin, shine ko yace yana gaisheni ko?"

Tafada tareda hawa kan gadon ta kwanta agefenshi daf dashi, domin har jikinta yana gogar nashi,

"Yace agaisheki mana, har da sako ya bani in kawo miki, sai gobe zan baki idan na bude kayan"

"Yawwa nagode, Allah sarki my boy i missed him so much"

Idanuwansa ya mayar kanta ya kalleta,

"Dazu da naje gidan malam yayi min maganarki, ina tayaki murna, barka da shigowa addinin musulunci, addinin gaskiya,ina yimiki addu'ar kasancewa acikinsa har karshen rayuwarki"

Hannunsa ta kama ta rike acikin nata ta lumshe idanuwanta,

""Abbu nagode, bayan tafiyarka nayi mafarkinka"

Hannun nata ya sake makalewa cikin nasa "meya faru a mafarkin? Me nayi miki? Fada min"

Murmushi tayi tafara shafar gashin da yake kwance a hannunshi, wani irin yammmmm! Yafara ji amma sai ya dake,

"Abbu ganina nayi acikin wani bakin daji mai tsananin duhu sai kawai nafara hango *wani haske* yana tahowa daga nesa har ya karaso kusa dani yana karasowa sai naga ashe kaine,kana zuwa sai ka kama hannuna muka yita tafiya har muka fita daga cikin wannan bakin dajin muka shiga wani wanda yake mai tsananin haske ga wani kamshi mai dadi yana tashi ga ciyawa koraye awurin sannan ga tsuntsaye sunata rera kuka mai dadi, ka bude baki kenan da niyyar fara yimin bayani sai nafarka, naji haushi ba kadan ba saboda naso ace naji abinda kayi niyyar fada min"

Hannunsa daya yasa ya rike dayan hannunta wanda take shafar gashin hannunsa dashi,

"Shigowarki addinin musulunci shine fassarar mafarkinki binti, hakika kafurci duhune yayinda musulunci kuma ya zama *wani haske* wanda ya haskaka dukkan komai"

"Hakane abbu, yanzu na tabbatar da duk abubuwan da ka fada min abaya"

"Dazu kikace min sau biyu kike yin jini awata?"

Idanuwanta ta rufe duk ya sakata taji kunya saboda yadda yake fadin maganar afili inama laifin ya dan sakaya yace period,

"Uhmmm?" Ya sake tambayarta, daga masa kai tayi batare da tayi magana ba,

"Yaushe da yaushe?"

Dakyar ta iya bude bakinta "farkon month da karshensa" ta fada cikin shagwaba ga wata uwar kunya data lullubeta,

Kin taba ganin dr akan hakan" ya tambayeta gamida murza yan yatsunta,

Kai ta sake dagawa batayi magana ba,

"Me yace miki?"

"Yace ba problem bane" ta bashi amsa har lokacin idonta arufe yake amma tana jinshi yana matsa yatsunta duka,

"Allah ya albarkaci rayuwarki binti"

"Amin abbu, kayi min addu'a inyi bacci"

Kansa ya rankwafar zuwa kusa da ita ya fara yi mata adu'o'in Wanda har lokacin tana rike da hannuwansa duka biyun, sai da ya kammala tofeta da addu'a sannan ya kalli idanuwanta wadanda suke a lumshe,

"To ki sakeni mana binti"

Murmushi tayi tasaki hannun nashi duka biyu acikin sloww motion ba dan taso ba,

Murmushi yayi ya koma yadda yake yaci gaba da aikinshi, sake matsawa daf dashi tayi bada jimawa ba bacci ya dauketa,

Ya jima zaune yana amsa fatawar mutane daban daban kafin ya rufe laptop din ya jiyo yana kallon goodness wacce take kankane ajikinsa domin lokacin da tayi baccin batare data saniba acikin barci ta sake shiga jikinsa dan harda zira hannunta acikinsa da haka har ya gama aikinshi tana zagaye dashi da hannuwanta,

Hannunta ya zare ahankali ya dubi lukuta lukutan cinyoyinta wadanda ta yayesu ba tare da ta sani ba, rigar yaja ya gyara mata yaje ya dauro alwala ya fito yazo gefenta ya kwanta yana mai karanto addu'o'in neman tsari daga dukkan abin k'i.





_*Ummi A'isha*_🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [10/2, 3:45 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*

   _*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_91-95_

~~~Bargo yaja ya rufa mata sannan shima ya dan rufe rabin jikinsa,shiru yayi yana tunani aranshi wanda kusan rabin tunanin akan goodness ne, hakika Allah shine mai yadda yaso aduk halin da yaso kuma alokacin da yaso,

Tun farkon haduwarshi da goodness lokacin data fara aiki a office dinshi har yau dinnan da suke tare a matsayin Ma'aurata duk sai da ya tino su acikin wannan dare,

Jinta yayi ta matso jikinshi tana mai kankameshi,ahankali yasa tattausan hannunshi ya dagota ya kwantar da ita ajikinshi gamida shafar kanta har bacci ya saceshi.

Tun kiran sallar farko ya tashi ya gyara mata kwanciyarta ya lullubeta yaje yayi alwala yafita masallaci,

Har k'arfe 6:30 bai dawo gidan ba alokacin goodness ta farka tunda taga dakin wayam tasan bai dawo daga masallaci ba, sashenta taje tayi wanka da ruwan dumi ta shirya cikin dan karamin wando tied iya gwiwarta da yar riga fara mai hannun shimi,

Sashen jabir tayi maza ta koma ta gyara masa cikin bedroom dinshi ta gyara falo har lokacin bai dawo ba domin wani lokacin har sai rana tafito yayi sallar walaha sannan yake dawowa,

Part dinta ta koma bayan ta kammala gyara sashen jabir, kitchen ta shiga ta dora abin karin kumallo,

Dankali da kwai ta soya sannan tayi farfesun hatta ta dafa tea da kayan kamshi,

Sai da ta gama shirya komai sannan ta nufi sashen jabir tasan lokacin kila ya dawo,

Akan doguwar kujerar falonshi ta ganoshi yana kwance da doguwar jallabiya fara ajikinshi, yanda yayi kwanciyar ba karamin kyau taga yayi mata ba domin ya harde duka hannuwanshi guda biyu akirjinshi idanuwanshi alumshe amma fuskarshi dauke da murmushi kamar wanda yake ido biyu,

Ahankali ta sadada ta je inda yake kwancen, hannuwanshi ta warware ahankali ta budesu tashiga cikin jikinsa ta kwanta duk da tanada masaniyar kujerar tayi musu kadan, matsuwa tayi sosai ajikinshi tana mai kallon kyakkyawar fuskarshi,

Kanta ta kwantar akirjinshi tana mai shafa kyakkyawan sajensa,

Hancinshi taja sannan ta dora dan yatsanta akan lebenshi na kasa, "ohh abbu badai kyau ba, Kanada kyau sosai, shiyasa al'amin shima ya zama mai kyau"

Kanta ta cusa acikin kirjinshi tana shakar kamshinsa mai dadi,bakinta tasa ta ringa jan botir din gaban rigarsa har sai da ta bubbudesu duka da hakorinta nan ta tura kanta cikin rigarshi tana sinsinar kirjinshi, ta dade ahaka har jabir ya farka, ganinta yayi tana makale dashi gashi duk ta bubbude masa botiran jikin rigarsa da bakinta,kallonta yayi yanda suke kwancen nan kamar wasu hanta da jini,fuskarta yafara karewa kallo yana kokarin gyara mata kwanciyarta acikin jikinshi,

Da saninta tayi wani juyi zata fada kasa,cikin sauri ya tarota ya rungumeta,

Bude idonta tayi dama ba bacci take ba tana jinsa,

"Dama ai rigimace tasaki zuwa ki kwanta anan tunda kin san wurin yayi mana kadan, ke kadai ma wurin kadan zaiyi miki balle mu biyu" ya fada yana kallon idanuwanta,

"Yanzu wannan wurinne yayi mana kadan abbu?" Ta tambayeshi tana kallonshi itama,

"Ehh tunda saura kadan yanzu kisha k'asa, ba dan natashi ba da sai dai kijiki akasa"

"Abbu duk lokacin daka tashi magana sai kace ni katuwa ce bayan banga ta inda nafika kiba ba"

"Haba yarinya, kinfini mana"

"Ta ina?"

Hannunshi yadora akan cinyarta,

"Wannan cinyar taki guda daya tayi ahada nawa duka biyu"

Hannunshi ta rike saboda sai taji kamar tafiyar tsutsa yake yi mata acinyar tata,

"Sannan kuma waye yace miki ki bude min botiran rigata?"

"Yi hakuri abbu bari in rufe maka dama can ba laifina bane, hakorina ne ya bude"

Hannuwanta ya rike, "yanda kika bude da baki to yanzunma da bakin zaki rufe"

"Yi hakuri abbu bazan iyaba"

Bakinta tasa tafara kokarin wai sai ta balle botiran amma ta kasa,

"Abbu bari naje na kawo maka abinci, tun dazu nagama"

Sauka tayi daga kan kujerar ta fita da gudu, binta da kallo jabir yayi yana girgiza kai, wato yarinyar nan yarinyace danya sharaf bata da maraba da yar 14 komai nata na yara take yi,

Tashi yayi yaje yayi brush ya fito lokacin har goodness ta kawo abincin tana zuba masa,

Akasa ya zauna yafara ci yana kurbar tea din,

"Abbu insa hannu nima muci tare?" Dagowa yayi ya kalleta tana tsotsar dan yatsanta wanda ta yanke jiya,

"Uhm" yafada atakaice saboda wani lokacin shi baya son surutu,

Cokali tasa tafara ci tanayi tana satar kallon bakinshi wanda yake motsi mul mul lokacin da yake taunar dankalin,

Ya rigata kammalawa dan haka tashi yayi ya shiga cikin dakinsa ya janyo jakar kayan da yazo mata dashi, anesa da ita ya zauna ya fara kokarin bude jakar,

Da sauri ta ajiye spoon din hannunta tadawo kusa dashi ta zauna tana murmushi,

"Ungo sakonki inji danki al'amin" mika mata chocolate yayi acikin wani babban kawali,

Cikeda doki da murna ta karba, "nagode, Allah Sarki al'amin dina"

Yana kallonta ta bude chocolate din tafara sha ya yi tunanin abin na wasane sai yaga sha kawai take babu kakkautawa kafin ya farga har tasha guda biyar tana kokarin bude ta shida,

Hannunta yakama  yarike wadda take da niyyar budewar,

"Ke bakya gajiya da shan zakine? Wannan kayan zakin da kikesha sune suke sakaki rushing dinnan idan kina period, kar nasake ganin kinsha wannan chocolate din, mayarta cikin kwalin ki bani nan"

Langabar da kanta tayi cikin sigar shagwaba tace "ayya abbu kabarni nasha wannan din, daga ita bazan sake shan wata ba"

"Bazafa kisha ba, bani nan" fusgewa yayi ya mayar cikin kwalin ya rufe ya ajiye akusa dashi,

Wasu kananan kaya masu kyau ya shiga futo mata dasu yana mika mata,

"Woww..!" Shine kawai abinda take furtawa,

Bra din da ya siyo mata ya ciro, "ungo wannan idan kuma sunyi miki kadan shikenan"

Karba tayi duk kaloline masu kyau kuma manya irin size dinta,

"Haba abbu wannan ai sunyi min yawa, wanne irin kadan?"

"Wadannan abubuwanne suka yi miki yawa?" Ya tambayeta yana satar kallon kirjinta, dago kanta tayi daga sunkuyen da yake tana kallon kayan, caraf suka hada ido, dauke kansa yayi duk sai yaji yar kunya ta rufeshi saboda yadda goodness ta kamashi yana kallon kirjinta,

Lips dinta ta cije ta zuba masa ido kamar zata cinyeshi,shikuma sai basarwa yake yaki sake kallonta,

Sunfi minti biyar ahaka tana kallonsa shikuma yana kallon wani wuri, juyowa yayi suka sake hada ido har lokacin tana cije da lips dinta fuskarta dauke da murmushi,

"Lafiya? Ki duba sauran kayan mana, wannan kuma idan sunyi miki kadan ki bayar kawai"

Murmushi tayi aranta tace "dama fa sai da ka gama karewa kirjina kallo kasan size dina sannan ka siyo min wannan braziers din idan ba haka ba ya akayi kasan size dina"

Kallonta ya sake yi jin bata yi magana ba,

"Abbu wlh wannan ba zasu yi min kadan ba"

Mikewa tayi da bra daya a hannunta tashiga bedroom dinshi bata jima ba sai gata ta fito,

"Abbu kaga tayi min daidai"

Juyawa yayi yaganta daga ita sai bra din, kuma tayi mata cif cif, dama shi bai kawo cewar zata yi mata yawa ba yafi zaton  kada zata yi mata,

Kansa ya dauke daga kallonta,

"Nagani,tunda tayi dai dai shikenan"

Dakinsa ta koma ta sako rigarta, ta dawo wurinshi inda yake zaune yana nazarin cikar halitta irin tata.

Agabanshi ta zauna ta cigaba da dudduba sauran kayan dake cikin akwatin,wasu hadaddun turarruruka tagani wadanda daga gani masu tsadane nagaske,

"Bani wannan turaren nawane ba naki ba" yafada tareda mika mata hannu,

"Abbu bani ka siyowa ba?",ta tambayeshi a shagwabance,

"Ehh, nawane saboda me karfine, kinga ai bai kamata kisaka turaren maza ba saboda duk inda kikaje sai anji kamshinki kuma hakan haramunne"

Mika masa tayi, tafara kokarin mayar da kayan cikin jakar,

"Abbu dan Allah ka barni naje gidan anty bilkisu anjima, kaina ya cika da yawa saloon yake so" tafada tana shagwabe fuskarta,

"Saloon dinne har sai kinje gidan anty bilkisu?"

Kai ta daga masa batare da tayi magana ba,

"Indai wannan ne dalilin kadai to basai kinje ba"

"Abbu kagani fa" hular kanta ta cire, nan yaga gashin kan nata cukus kamar me amma baza asata asahun marassa gashi ba,

"Koni ai zan iya yimiki saloon din tunda ina yiwa ummu ma, badai saka relexer bane kawai?"

"Abbu relexer Kadai?"

"Akwai hand drayer ta ummu sai in dauko miki"

Jakar kayan ta dauka tafita ta nufi sashenta tana dariyar yadda za ayi jabir yayi mata shamfo,

Abincin rana ta dora ta dafa shinkafa da miya sannan tayi lemon kankana wanda ta hada da ayaba da apple tasaka madarar ruwa ta dan zuba sugar kadan,

Lokacin data gama komai tatafi wurin jabir domin ya saka mata relexer din, a dakinshi ta iskeshi yana kwance akan gado da wani littafin addini a hannunshi yana karantawa,

Ajikinshi ta kwanta, "abbu nagama aiki kazo ka shafa min relexer din"

Littafin hannunshi ya ajiye yana kallonta, "da wanne relexer kike amfani?"

"Abbu soft and beautiful ne"

Wayarshi ya dauka ya kira driver yace ya taho masa da relexer,

Tana nan kwance ajikinsa har driver din ya dawo, da kanshi ya fita yaje ya karbo ya dawo,

Tun awurin tajewa aka fara samun matsala domin rike hannunshi tayi "washh abbu wlh da zafi bani na taje da kaina"

Sakar mata cumb din yayi tagama tajeshi da kanta sannan ya fara raba mata shi gida uku,

"Abbu kasaka leda a hannunka karka ji ciwo"

"No basai nasaka ba"

Tana zaune akasa shikuma yana kan kujera yana shafa mata har yagama amma duk ya yayyabe mata goshinta da keyarta sosai da relexer din,

Tashi tayi taje gaban mirror ta gyara fuskarta ta dan goge na goshin nata, shi kuma jabir ya shiga bathroom ya wanke hannunsa, fitowa yayi ya koma falo ya kunna tv,

Tun relexer din baifi minti goma ba ta fito tazo wurinshi, "abbu zo muje ka wanke min, yafara yimin zafi"

Dago idonshi yayi ya kalleta "daga sakawa sai wankewa? Ki bari yayi 30 minutes kamar yadda suka rubuta ajiki"

Zama tayi kusa dashi tana jijjiga hannuwanshi, "abbu zai kona min kai, wlh da zafi"

"To bari idan ya kara 25 minutes sai in wanke miki"

Tashi tayi tana yarfe hannunta ta shiga bedroom dinshi, kallo yayita binta dashi har ta shige,

Dakyar ta bari yayi 20 minutes tazo tasaka shi agaba sukaje bathroom yafara wanke mata, wata uwar kara ta cillara,

"Wohhhhh abbu goshina, wayyo goshina,abbu wlh na kone"

Da kokawa da komai yake wanke mata kan daga karshe ta rirrike hannunshi,

"Nidai ka bari zan karasa wankewa da kaina"

Fita yayi ya barta ta dan lallaba kan ta wankeshi sama sama, duk kayan jikinta ya jijjike dama jabir ba iya saka relexer din da yayi asalima ita ummu al'amin bata shanfo iyakacinta kawai ta wanke gashinta,

Agefen gado ta sameshi zaune yana jiran fitowarta,

Rigarta ta kwaye ta fara goge goshinta da cikin kunnenta hakan ya bashi damar ganin jikinta hatta jar bra din dake jikinta sai da yagani,

"Abbu wlhi duk na kone agoshina da ta keya na",tafada idonta rau rau da kwalla,

"Ayya sorry binti, zo nagani"

Gabanshi taje ta tsugunna yafara ganin goshin nata hakika gashi nan kam duk ta kokkone wurin yayi alama,

"Sorry binti, zanje masallaci in dawo"

"Abbu har lokacin sallar yayi?"

"Ehh ke ai bayi kike ba shiyasa zaki ga lokaci yayi saurin yi"

Bathroom ya shiga yayinda ita kuma ta jawo towel dinshi ta daura ta fara kiciniyar cire kayan jikinta, tana tsaye daure da towel din yafito ya wuceta ya tafi masallaci.

Bangarenta ta koma ta shiga wanka ta sake wanke gashinta wanda keta yi mata radadi,

Kwalliya tayi ta shirya tsaf cikin riga da skirt yan kanti masu kwalliyar beza ajiki,

Kanta abude ta dauki abincin jabir tatafi part dinsa lokacin ya dawo daga sallar,

"Abbu wlh har yanzu wurinnan radadi yake yimin, nidai basai nayi amfani da hand drayer din ba, nafasa"

Abincin tafara zuba masa tana kallonshi,

"Zai daina zuwa anjima, gashinki yanada karfine, ni matar da zan aura gashinta mai laushine sosai kuma bata saka relexer"

Dagowa tayi ta kalleshi tareda kicincine fuskarta amma batace komai ba, ta gefen idonshi ya kalleta yana dan murmushi, salon yanda take kishinta yana burgeshi,

Abincin ta ajiye masa ba tareda tayi magana ba, mikewa tayi zata tafi saida taje har bakin kofa ya kirata,

"Binti zo nan"

Dawowa tayi tazo ta tsugunna agabanshi amma har lokacin taki kallon fuskarshi,

Kallonta yayi sosai yana mamakinta domin kishinta yawane dashi duk tabi ta damu daga fadar haka,

"Dubo kan drewar adakina akwai wasu littattafai da nake koyawa al'amin karatu ki debosu duka"

Mikewa tayi taje ta kwaso littattafan ta kawo masa,

Guda daya daga ciki ya dauka ya mika mata "wannan littafin akdari ne, shi zan rinka koya miki, bari na gama sai muyi"

Har lokacin taki kallon fuskarshi sannan taki magana, littattafan tafara dubawa acikin ranta tana tunanin kenan duk littattafan al'amin ya kwaso mata wanda yake koya masa,

Wani mai hoto ajiki ta bude tana gani, babu zato taga hoton zaki ajiki yana bin wani mutum da gudu, dariya tayi bata shirya ba,

"Abbu kagani" ta juya masa littafin, murmushi yayi yana cin abincinshi, kallon hoton tai tayi tana dariya har ya gama, hadadden lemon kankanar da ta hada musu ya zage ya shanye sai dan kadan ya rage wanda baifi rabin cup ba,

"Abbu shine ka shanye lemon ni baka rage min ba" tafada tana zumbura bakinta,

Wal yayi da manyan idanuwanshi wanda suka fi na cwt Kausar girma "au dama baki sha ba? Yi hakuri ai ban saniba"

Jikinshi ta matsa tana tuttura baki, nan yafara koya mata karatun har suka dauki tsawon lokaci,sai yamma sannan yayi wanka ya fita, tunda ya fice kuma bai dawo gidan ba sai da daddare,

Tana dakinta tana ninke kayanta ya shigo,

"Binti zanje unguwa in dawo"

Kallonsa tayi yasha shadda mai mutakar kyalli sai maiko take yi kalarta dark brown, yasha hula sai faman kamshi yake yi,

Rau rau tayi da idanuwanta tana tabe fuska kamar zatayi kuka "abbu zan bika dan Allah" amma duk atunaninta wurin budurwar da yake ta fada mata zaije,

"Yanzu idan naje dake fada zaki hadani da budurwata dan haka kiyi zamanki naje nadawo"

Tashi tayi taje ta rirrikeshi, "abbu wlh bazan zauna ba sai nabika" kuka tafara mai hawaye da dan sauti kadan,

Sakin baki yayi yana kallonta cikeda mamaki, ya fahimci sam bata da wahalar kuka abu kadanne yake sakata kuka,

"To yi shiru amma kiyi min alkawai idan munje amota zaki zauna ba zakice sai kin bini cikin gidan ba"

"Abbu nayi alqawari"

"To sake kayanki mu tafi"

Har lokacin tana rirrike dashi, dakyar ta cikashi ta fara binkito after dress dinta, agurguje tasaka tabishi suka fita,

Ko acikin mota ma shiru tayi tana mai jin haushin kanta biyoshin da tayi bayan kuma wurin budurwarsa yace zaije, idonta ta rufe taci magani ta bata rai har sukaje inda zasu bata bude idonta ba,

"Binti ina zuwa" yafada lokacin da yake kokarin fita daga cikin motar, bata bashi amsa ba kuma bata bude idonta ba har ya fice din,

Tadade zuciyarta tana kuna tana jin haushin koma wacece mijinta yake so,

Ahankali ta bude idonta ta kalli wurin kamar amafarki sai tagansu akofar gidansu ashe gidansu zaije shiyasa ya hanata shiga, wani farin ciki taji aranta take bakin cikinta ya yaye,

Tana nan tana jiransa har yafito shida papa,akofar gidan suka yi sallama yazo ya shiga motar yayinda mal idi driver ya bude boot yafara jidar kayan dake ciki yana shigar dasu cikin gidan,

Jikin jabir ta matsa ta kama hannunshi ta rike cikin nata tana murmushi, "kin gama fushin?" Ya tambayeta yana jujjuya hannunta acikin nashi,

"Abbu ba kai bane kace wurin budurwarka zakaje ba" ta fada tana kallon fuskarshi,

"Wurin baba nazo saboda rabona dashi tun cikin azumi lokacin da nazo yi masa sannu da shan ruwa ana saura biyu natafi umarah"

Kanta ta daga gabanta yana faduwa domin tunowa da tayi har yau fa mamanta bata san ta musulunta ba, tabbas tasan akwai drama agaba.

    Suna komawa gida ta shiga sashenta tayi wanka ta tsuke cikin kayan baccinta farare tas riga yar karama da wando iya gwiwa,

Turaren shifax ta shafa tatafi dakin jabir wanda ke gaban mirror yana gyara sajensa, ta cikin mirror din ya ganota tana shigowa kanta babu dankwali tana ta barbaza gashin kanta,

"Abbu gashin nan nawa gobe sai naje ansake wanke min akusa da gidan anty Bilkisu"

Juyowa yayi yana kallonta ba karamin kyau tayi ba cikin kayan baccin dake jikinta,

"Meyasa zaki saka fararen kaya bayan kina d'iga?"

"Abbu gobe zanje awanke min kaina wlh bai fitaba"

Ta kawar da maganar da yayi mata ta farko,domin kunya yake bata,

"Allah ya kaimu"

Kan gadon ta hau ta kwanta yayinda shima ya kwanta agefen gadon,"abbu duk wannan wurin Zaka barmin? Gaskiya yayi min yawa,yayi min girma"

Matsawa tayi ta kunnaceshi ta kwanta agefenshi,hannunshi ta dora akan gaban gashin goshinta,

"Abbu kajifa inda duk nabi na kone"

Wurin yafara shafawa da hannunshi, daga karshe ya dago kan nata ya dora akan kirjinshi yaci gaba da yimata lalube acikin gashin kanta,

"Abbu Idan nayi bacci kayi min addu'a pls"

"Kema ya kamata ki koya saboda ki rinka yi da kanki"

Idonta alumshe ta lalubo hannunshi daya ta rike cikin nata, "abbu har yanzu surori hudu kawai na iya daga fatiha, sai kul a'uzu bi rabbil falaq, nass,sai kulhuwallahu ahad"

"Ina sane da hakan binti amma zan fara yi miki dori daga yanzun nan sannan indai baki maida hankali kin iya ba zaneki zanyi"

Murmushi tayi ta sake gyara kanta akan kirjinshi, "abbu duka?"

"Ehh duka" yabata amsa yana cigaba da shafar kanta

"Abbu kofa al'amin ban taba gani ka daka ba amma shine ni zaka dakeni"

"Ai al'amin baya wasa da karatu shiyasa bana dukanshi amma ke indai kika yi wasa zaneki zan rinka yi"

Kanta ta daga tana kallon fuskarshi acikin hasken dakin,

"Abbu dama ance Ku mazan hausawa dukan matanku kuke yi, gaku kunyi suna wurin yiwa mata kishiya sannan kuma babu wuya kunyi saki"

  Maganarta dariya ta bawa jabir domin tunda take dashi bata taba ganinshi yana dariya harda kyakyatawa ba sai yau,

Sai da yayi dariyarsa da yawa sannan ya matsa hannunta dake cikin nashi,

"Binti da wasa nake yi miki fa, taya zan dakeki? Sannan waye yace miki mazan hausawa suna dukan matansu? Jahili ne zai daki matarsa amma ba mai koyi da annabi ba, mutukar mutum da annabi yake koyi ai bazai rinka dukan iyalinshi ba domin zaluncin yayi yawa, sannan mata amana ne awurin mazajensu"

Fuskarta ya shafo yana murmushi,

"Binti duk laifin da kika yimin komai girmansa bazan taba dukanki ba, ai babu tsari ace miji yana dukan matarsa domin ba baiwa bace, ko dabbace aka ajiye maka ai bai kamata kana dukanta ba bare yar adam wacce ta zamanto wani bangare na rayuwarka, amma wasu mazan saboda tsananin zalunci koda yaushe acikin dukan matansu suke wani abin haushinma wani har agaban yaransu yake dukan matar wani kuma agaban makota, agaskiya wannan baya daga cikin koyarwar annabi,domin annabi kullum cikin nishadi da kyautatawa iyalan gidanshi yake"

"Abbu to kuma sakin fa? Mazanku suna da yawan saki"

"Binti saki halal ne amma Allah baya sonshi domin duk lokacin da akayi shi sai al'arshi ya girgiza, kuma wani sakinma rashin hakuri ne yake kawoshi, ki kwantar da hankalinki indai nine insha Allahu bazan taba sakinki ba zan zauna dake har karshen rayuwata"

Wani farin cikine ya lullubeta wanda har sai da tayi mishi kiss akan kirjinsa ba tare da ta saniba,

"Abbu to kuma kishiyar fa?"

Ta tambayeshi tana murza yan yatsunshi,

"Aure ai Allah ne ya bamu dama yace mu auri mata har guda hudu"

"To yan gata"

Haka kawai ta fada ta tashi daga cikin jikinshi ta koma can karshen gadon ta kwanta,

"Binti" ya kira sunanta yana murmushi shidai ya kasa gane wanne irin kishine da ita, shiru bata amsa ba hakan yasa shi kashe hasken dakin,

Minti biyar atsakani taji wani abu ya garya mata cizo akan fatar idonta daya, zumbur ta tashi tana sosa wurin,

"Abbu..!"

Shiru shima yayi mata wato shima ya rama yanda tayi masa dazu,

"Abbu..!" Tasake kiransa tana sosa wurin, wani cizon taji kwaron ya sake yi mata awuyanta,

"Abbu, wayyo idona, abbu kunama ta cijeni" tafada gamida fashewa da kuka, cikin Sauri jabir ya tashi ya kunna fitilar dakin ya matsa wurinta,

"Kunama?" Tashi mugani, tana tashi sai ga cinnaka ya fado wani kato dashi bakikkirin,

Kasheshi yayi yana dan murmushi "wannan yarinya da rangwanta kike wai cinnakane kunama"

Yafadi acikin mind dinshi,

Komawa yayi zai kwanta, rarrafawa tayi tabishi tana kuka, "abbu idona, kaga har akan idona ya cijeni"

Hannu ya mika ya kwantota jikinshi,

"Sorry binti" yafada yana dan bubbuga bayanta,

"Abbu ka sosa min pls"

Dan yatsanshi ya dora asaman idonta yafara sosa mata wurin,

"Abbu har yanzu da zafi, ka sosa min"

Sosa wuyanta take tayi shikuma yana mulmula mata saman idonta da yatsanshi,

Ta dade tana yi masa rikici har bacci ya dauketa sai alokacin hannun jabir ya huta, murmushi kawai yake yi na darun binti,

Addu'a yayi musu ya kashe wutar dakin yaja bargo ya rufesu.

  Washe gari tun wurin 10 tagama shirinta tsaf driver ya kaita gidan yayarta bilkisu saboda tana son wanke gashinta,agida ta tafi tabar jabir domin har yanzu bai koma office ba,

Ba karamin murna anty Bilkisu tayi data ganta ba,

Nan ta shiga hidima da ita duk da cewar mijinta ba mai kudi bane amma akwai rufin asiri da wadatar zuci,

Nan suka shiga tattaunawa musamman ma maganar mahaifiyarsu wacce har wannan lokacin bata san goodness tabar addinin kiristanci ba,

Sun dade suna tattaunawa sannan suka gangaro kan zamantakewar auren jabir da goodness, kamar kullum yauma lecture anty bilkisu ta zage tayi mata mai taken "ki zama karuwar mijinki tun kafin wata ta zama karuwarsa awaje?"

Lecture din ta shigi goodness sosai amma bata yarda anty Bilkisu ta gane cewar har yanzu babu abinda ya shiga tsakaninta da jabir ba domin tasan wannan wani babban sirrine atsakaninsu wanda ko uwar data haifeta bazata taba iya sanar da itaba shiyasa take ganin kokarin matan auren da suke zama agidan biki ko gidan suna,suna bayar da labarin abinda ya gudana tsakaninsu da mazajensu, wata ko menene mijinta yayi mata to sai ta fadawa kawarta musamman ma amare dan wasu amaren adaren da aka kaisu gidan miji da safe sai sun kira kawayensu awaya sun zayyane musu tsaf abinda ya faru komai sai sun fadawa kawaye tamkar agabansu aka aikata, yakamata arinka kiyaye wannan sirrin,

Sai da anty bilkisu ta gama dorata akan network sannan ta tashi ta shiga gidan gyaran gashin, wanke mata aka sake yi ta shiga drayer aka gyara mata gashinta tsaf, tuni gashin yayi baki wuluk yayi kyau ya dau kyalli,

Gidan anty Bilkisu ta koma sai da ta jima agidan sannan ta kira wayar jabir lokacin yana kwance afalonshi yana waya da ummu,

Waiting call tagani har wayar ta tsinke, bari tayi aka yi kamar minti biyu nanma data sake kira har lokacin waiting call, wayar ta zubawa ido aranta tana tunanin to dawa abbu yake waya kodai da budurwar tasa yake hira?

Wani kishine ya mamaye zuciyarta, yafi minti 20 suna waya da Ummu da al'amin sai da yagama sannan yaga missed called din yar darun tasa,

"Binti rikici, yau zansha daru kenan" yafadi hakan azuciyarshi lokacin da yake kara wayar akunnenshi domin kiranta,

Ai kuwa tana dauka ta buntsure baki kamar yana kallonta,

"Abbu sai yanzu ka gama wayar?"

"Binti da matata nayi waya" yafada da niyyar zolayarta,

"Nasani ai, nagama tun dazu driver kawai nake jira"

"Zai zo ya daukoki yanzun nan binti, tana gaisheki"

"Bana amsawa" abinda ta fada kenan ta tsinke wayar.

     Lokacin data koma gida afalo ta iske jabir yana yan karance karancenshi kamar yadda ya saba,

Daf dashi taje ta zauna tareda zame hijabin kanta,

"Abbu ka gani"

Gashin nata yabi da kallo, ba karamin kyau yayi masa ba gashi sai wani irin kamshi yake mai dadi,

"Nagani binti, yayi kyau"

Kan cinyarsa ta dora kanta, "abbu dora min karatun"

Tana kwance acinyarsa ya fara dora mata suratul nasri, aya biyu yayita maimaita mata har lokacin fitarshi yayi, part dinta takoma ta mike akan gadonta.

    Misalin karfe _9:30_ nadare ta shiga kitchen ta dafawa jabir shayin na'a na'a, shiryawa tayi cikin kayan bacci orange colour marassa duhu, riga da wando masu laushi,

_Bedroom_ dinshi ta shiga ta sameshi yanata faman aiki a laptop dinshi, kan gadon ta hau ta kwanta akusa dashi bayan ta ajiye masa tea flask din agefenshi shi,

"Binti kafin kiyi bacci ki karanto min abinda na koya miki dazu"

"To abbu" cinyarshi ta dafa da hannunta ta soma karanta masa har ta gama,

Kur tayi masa da ido tana kallonsa shikuma yanata aikinsa na amsawa mutane tambayoyinsu akan abinda ya shafi addini,

Cikin sanyayyiyar muryarshi wacce tafi ta *Pherty Xarah* sanyi yace da ita,

"Binti taso kiga wani abu"

Tashi tayi takai dubanta ga laptop din tashi, anan ta hango sako daga wata mata tana tambayarsa kamar haka: _Assalam malam shekarata 5 da aure yanzu haka inada yara guda biyu, malam tambayata itace shin dagaske ne duk lokacin da miji ya ziyarci shimfidar matarsa sai tayi wanka? Dagaske ne idan shi yayi wankan ita basai tayi ba? Malam idan dagaske ne ana yin wankan to ya ake yinshi? Menene siffar wankan? Sako daga wata baiwar Allah_

Kallon fuskarshi goodness tayi duk da cewa ita bata dade acikin musulunci ba to amma ta dan fuskanci wani abu kadan akan sakon nan,

Rufe laptop din yayi ranshi abace ya ajiyeta akan drewar ya kwanta, kan kirjinshi taje ta kwantar da kanta tana kallon fuskarsa,

"Abbu menene? Meye ya bata maka rai?"

Cikin raunananniyar muryarsa wacce ta haduda bacin rai yafara magana cikin sanyinshi,

"Haba binti abinne ya bata min rai saboda wannan matar mijinta ya cuceta ya ci amanarta, narasa meyasa wasu mazan basuda tunani, acikin addini fa tilasne miji ya koyar da matarsa ilimi idan kuma bashida ilimin da zai iya koyar da ita ko kuma bashida lokacin koya mata to wajibine yasamo wanda zai koyar da ita ko kuma ya samar mata makaranta taje ta koyo, domin an yarjewa mutum yatafi neman ilmi har kasar birnin sin sannan duk wanda yake kan hanyar neman ilmi to yana kan tafarkin Allah inji annabin rahma sallallahu alai wasallam,ki gaya min ta yadda mutum zai bautawa ubangijinsa cikin jahilci? Ai Allah ma cewa yayi ku sanni kafin ku bauta min, wannan yana nufin mutum yaje ya nemi ilimin sanin dukkan hukunci abubuwan da suka shafi addini kafin ya gabatar da bautar ubangiji, ya kamata ace duk namijin da yayi aure to kafin wani abu ya shiga tsakaninsa da matar ya sanar da ita yanda zata bautawa ubangijinta, amma mace tana tare da mijinta tsawon shekaru amma bata san wani abu wai shi wankan janaba ba, bare wankan haida, da wankan biki da sauran wanka wadanda sukeda muhimmanci, kai Allah ya sawwaka"

Hannunshi ta rike "abbu yanzu nima idan nagama wannan abun sai nayi wanka?"

Kanta ya shafa "binti sai kinyi wanka da zarar wannan jinin ya dauke miki, sannan duk lokacin da miji ya ziyarci shimfidar matarsa to wajibi ne yayi wanka duk da nasha amsa tambayoyin mutane akan wai idan miji yayi wani abu da matarshi fiyeda sau daya to wai wankan ma fiyeda daya zai yi, wannan ba gaskiya bane, ko sau nawa mutum ya kula matarshi to idan ya tashi yin wanka sau daya zaiyi haka itama wajibi ne agareta tayi wankan"

Ita dai duk bayanan nan na jabir jinsu kawai take amma bata san inda suka dosa ba,

"Abbu yanzu duk kyan da gashin nan yayi haka zan wankeshi?"

"Ehh binti, dole ne, domin haida tana wajabta wanka kamar yadda fitar sparm yake wajabta wanka, sannan mutukar mutum ya ziyarci matarsa to ko bai fitar da sparm ba to wajibine sai anyi wanka,kin gane?"

Kai ta girgiza alamar a'a,

"Misali idan nayi miki wani abu har kika fitar da wani abu to tsarki zakiyi sannan ki sake alwala amma idan nayi rayuwar aure dake ko baki fitar dashi ba to dole sai kinyi wanka"

Kanta ta cusa acikin kirjinshi tana mai  tsananin jin kunyarshi,

"Shi maniyyi wajabta wanka yake amma fitar maziyyi shi hukuncinsa tsarkine,misali kamar idan na tabaki sai kikaji wani abu aranki na nishadi har kika fitar da wani Abu to idan kinyi alwala before na taba kin to alwalarki ta karye sai kin yi tsarki kin sake wata, haka idan bana nan sai kikayi tunanina har kikaji wani abu gameda ni to nanma alwalarki ta karye, amma kuma muddin nayi rayuwa dake irinta mata da miji to ko baki ji komai ba dole sai kinyi wanka, kin fahinta?"

Kanta ta sake cusawa atsakiyar kirjinshi bata bashi amsaba, shima bai zaci amsar daga gareta ba dan yasan kunya takeji duk da cewa shima daurewa kawai yayi ya sanar da ita saboda yasan hakkinsa ne yanzu ya koyar da ita duk abinda ya shafi addini musamman ma irin wadannan abubuwan wadanda babu wanda zai iya runtse ido ya koyar da ita dole sai shi.

  "Kodai practical za ayi sai kifi ganewa?" Ya rada mata acikin kunnenta yana wani malalacin murmushi.








_masu karatu yau kam ga wani haske nan da yawa Sai kuma kun jini nanda bayan sati biyu, saura kuma su oh oh ayi mafarkin goodness da jabir, Luv u all_








_*Ummi Shatu*_🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [10/5, 3:41 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*

   *_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*

       _Gaisuwa mai yawa gareki anty maijidda, nagode da kulawarki_

_96-100_

~~~Gashin kanta ya shafa yana murmushi, "tambayarki fa nake yi, nace ko nayi miki practically sai kifi ganewa?"

Shiru tayi masa ta sake cusa kanta atsakiyar kirjinshi duk kunya ta gama baibayeta,

"Hmm binti tunda kika yi shiru nasan kin fi son ayi practical din, bari afara yanzu"

Kankameshi tayi taki dago kanta amma hankalinta har ya dan fara tashi, wannan ranar ta yau tazo mata zuwa irin na bazata saboda bata zaci zuwanta ba,

"Dago kanki kiji binti" ya fada cikin muryarshi mai mutukar sanyi,dakyar ta iya dago kanta amma har lokacin idanuwanta arufe suke,

Juyi yayi da ita,ahankali ya dora bakinshi kan nata akaro nafarko, kamar a mafarki taji ya fara kissing din bakinta da dan mitsitsin bakinshi wanda ta jima tana kwadayin samu,

Wani farin ciki mai hadeda nishadi ne ya fara ziyartar babban dan yatsanta na kafa har ya haura zuwa cikin kwakwalwarta,

Wasu abubuwa ya shiga yi mata wanda sirrinsu ne babu ruwan ummi Shatu, sun jima ahaka suna jiyar da junansu farin ciki domin sun shafe fiyeda minti 30 acikin wannan yanayi,

Dakyar ta iya hakura ta saki dan karamin bakinshi wanda take jin zakinsa fiyeda sweet, acikin jikinshi ya kwantar da ita yasaka hannayenshi ya zagayeta yana murmushi,

"Binti..!" Ya kira sunanta ahankali,

Bata amsa ba shiru tayi ta kwanta luf ajikinshi tana fitar da numfashi ahankali,

"Binti, kina jina?"

"Uhm" ta fada atakaice,

"Menene uhm? Ki bude baki kimin magana"

Kanta ta soma boyewa acikin jikinsa tana murmushin farin ciki,

Hancinta ya lalubo yaja "saura kadan ki cinye min bakina yau" yafada cikin zolaya,

"Am sorry" tafada akunyace,

"Ban hakura ba"

"Haba abbu kar kayi fushi dani mana"

Hannunta ya laluba ya rike cikin nashi ya fara jan yatsunta yana kissing din goshinta hadida sinsinar gashin kanta me dadin kamshi,

"Kinga wannan abinda nayi miki yanzu? To hukuncinsa tsarkine da sake alwala,domin duk abinda yake fita ta sanadiyyar karamar sha'awa to hukuncinsa alwalane amma duk wani abu wanda babbar sha'awa ta sashi fita to shikuma wanka za ayi masa"

Har lokacin dai bata iya yin magana ba domin kunyace mai nauyi lullube da ita amma yau tana jinta itama wata macece mai daraja awurin jabir,

"Nasan yanzu kin gane abinda nake son in sanar dake abu dayane baki ganeba shima zaki gane nan da wani lokaci"

Gashin kanta yaci gaba da shafa tareda yi mata addu'a ya shafe mata jikinta bayan ya gyara mata kwanciyarta ajikinshi, ta jima tana tunanin yanayin da suka kasance dazu itada jabir har bacci ya dauketa batare data sani ba,

Jin alamun tayi bacci ya sanya jabir tashi ya zameta daga jikinsa ya kwantar da ita,

Ya lullubeta da bargo ya shiga bathroom alwala ya dauro yaje ya tsaya ya fara sallar nafila kamar yadda ya saba ako wanne dare,sai wurin k'arfe 3 nadare sannan yayi addu'a ya tashi yakoma kan gadon ya kwanta bayan ya jingina jikinsa dana goodness.

K'arfe 8 daidai ta farka tana mika tareda yin hamma kamar wacce ta shekara bata ci abinci ba, da hanzarinta ta tashi tafita zuwa part dinta, agurguje tayi wanka tayi brush ta fito,

Jikinta ta shafe da turare mai kamshi sannan ta saka wata bakar doguwar riga iya gwiwa mai siririn hannu,

Gashin kanta kawai ta taje ta gyara ta fita zuwa kitchen ba tareda tayi kwalliya ba,

Bread ta dauka tafara ci da guntun farfesun da tayi jiya, sai da tayi nak sannan ta daga idanuwanta ta kalli window, jabir ta hango tsaye ajikin window din bedroom dinsa yana kallonta,

Wata gagarumar kunya taji ta kamata kasancewar tuno abinda ya faru jiya da tayi, gashi kuma yanzu ya ganta tana lauma,

Tana nan tsaye tana hada masa breakfast har ta kammala shima yana gaban window din atsaye yana kallonta, har saida yaga fitarta sannan ya matsa daga wurin ya nufi falonshi, yana fitowa tana shigowa,

Bata iya kallonshi ba illa kanta dake kasa tana kallon kasan falon hannunta dauke da farantin silba,

Ahankali ya taka ya karasa har gabanta ya mika hannunshi ya dora kan nata yarike farantin tareda janta zuwa kan dining table, ahankali ta ajiye farantin amma har lokacin hannunsa yana dafe da nata,

Bakinta har wani nauyi yayi mata yau takasa magana domin kunyarsa take ji, idanuwanshi masu mutukar girma ya zuba mata yana kallonta up and down saboda tayi kyau sosai kamar irin black American dinnan haka yaganta,
 
Duk tagama tsarguwa da kallon da yake yi mata, ahankali tace,

"Abbu ina kwana?"

Hannunsa yasa ya dago kanta yana kallon fuskarta,

"Binti ban gane wannan sussunkuyar da kan da kike yi ba, meke faruwa?"

Shiru tayi bata amsaba, hakan da tayi yasashi jan hannunta suka koma cikin falo,Zaunarda ita yayi yana murmushi "yawwa kar namanta yankan farce zanyi domin yana daya yana daya daga cikin sunnonin ranar juma'a"

abin yanke farce ya dauko ya fara yanke faratansa, dana hannun damansa ya fara, yatsan da ake nune dashi shi yafara yankewa saida yakai har kan dan kurinsa sannan yakoma ya yanke babban dan yatsanshi na karshe,

Tana zaune tana kallonsa har ya yanke na daya hannun wato hannun hagun sannan yakoma kan kafarsa ta dama yafara yankewa daga kan karamin dan yatsanshi har zuwa babban, kafar hagun dinma haka taga yayi,

Murmushi tayi acikin ranta tana nazarin rayuwa irinta musulmi komai acikin tsari yake babu baragada,

"Binti wai yau lafiyarki kuwa? Sam kinki yimin magana sai kallona kike"

Fuskarta ta rufe da tafukan hannunta "abbu period dina ya rikice nakasa ganewa,wancan yin nayi kwana 4 yanzu kuma kaga har kwana 5"

Yan yatsunta ya kamo, "rikicewar period kusan mafi akasarin mata suna fama dashi to amma abubuwa guda ukune suke haddasa shi nafarko ciwon sanyi idan yakama mace har takai matakin da zataga wani farin ruwa yana fita ajikinta ko kuma tana jin kaikayi ko kuraje to hakan yana hassadar da rikicewar period, abu na biyu kuma shine samun matsala acikin mahaifa, kamar fitar k'ari ko kuma wani ciwo dai acikin mahaifar, abu na karshe kuma shine rashin kwanciyar hankali, to ke ban san wannene matsalarki ba, abu mafi sauki dai shine kawai kije asibiti kiga likita"

Murmushi tayi tana kallonsa aranta tana cewa "gaka nan babban likitan da zanga" saboda abubuwan nan da ya zayyano mata tamkar wani likita haka taga ya zama,

"Abbu nidai kawai ka siyo min magani"

"Shikenan tunda ba zakije asibitin ba"

Dan yatsanta ta cusa acikin kunnenta tasoma sosa kunnenta,

"Abbu ka sosa min kunnena dan Allah" tafada cikin shagwaba,

"Jeki dakina ki dauko abin goge kunnen to"

Da saurinta ta tashi ta garzaya ta shiga bedroom dinshi ta dauko abin goge kunnen akan mirror dinsa ta kawo masa,

Bajewa tayi ajikinsa ta dora kanta akan cinyar sa yafara goge mata kunnen ta,

Sun dade ahaka har tsawon wani lokaci kafin ta tashi taje ta kwaso masa kayan karin kumallonsa ta kawo masa inda yake zaune,

"Abbu ba yanzu zaka fitaba ko?" Ta tambayeshi tana kallon fuskarsa wadda shikuma abincin gabanshi yake kallo,

"Yanzun nan zanyi wanka in fita,meya faru?"

Matsawa tayi kusa dashi, "abbu fita zakayi ka barni? Dan Allah ka tafi dani abbu" tana gama fadin haka sai hawaye sharrrrrr!

Juyawa yayi ya kalleta, "menene abin kuka binti? Ai masallaci zanje da sai mutafi tare"

Hannunta ya kamo ya rike cikin nashi, "abbu bana son katafi ka barni"

"Kiyi hakuri binti ai idan natafi ma zan dawo kinji"

Kai ta daga tana sake makale hannunsa cikin nata,

Tana nan tare dashi har ya kammala cin abincin yaje ya dauko littafi mai tsarki yadawo kusa da ita ya zauna, kwanciya ta sake yi ajikinsa yayinda shikuma ya bude alqur'anin yafara karanta suratul kahfi domin dacewa da hasken juma'ah,

Tana jin ya kammala karatun tafara sosa saman idonta har wurin ya dan fara kumbura idon yayi ja,

"Abbu kaga wurin da wannan kunamar ta cijeni shekaran jiya har yanzu bai warkeba"
Tashi zaune tayi tana nuna masa,

"Abbu zafi, sosa min"

Babu zato taji harshensa akan wurin yana juyawa,

"Abbu...!" Hannunsa yasa ya rufe mata bakinta yaci gaba da lasar fatar idonta da harshensa,

Ya jima yana yimata haka kafin ya tsaya ya kurawa gashin kanta ido wanda yayi masa kyau ainun,

"Binti bari naje nayi wanka, fita nake son yi"

Tashi tayi daga jikinsa ta matsa gefe, cikin bedroom dinshi ya shiga yayinda ita kuma ta rakashi da ido,

Tv ta kunna ta fara kallon African magic, har jabir ya fito ya sameta, kamshine yafara ziyartar hancinta hakan ya sanyata juyawa ta kalleshi, kamar kullum komai fari yasaka tun daga yadin jikinsa har takalmin kafarsa,

"Wowww...!" Tafada cikin zuciyarta,

"Abbu kayi kyau" tafada gamida tashi ta karasa gabansa ta tsaya tana kallonsa,

Hannunsa yasa ya fara shafa wurin da ya kumbura asaman idonta,hakan ya sata lumshe idanuwanta,

Kamar daga sama taji bakinsa kan nata yana tsotsar lips dinta,

Sunfi Minti biyar ahaka sannan yasaki bakin nata ahankali,

"Binti sai nadawo ko?"

Hannunsa ta kamo idonta cikeda kwalla, "abbu zaka tafi da farin cikina zaka barmin damuwa" tafada ahankali,

Hannuwan nata shima ya riko,

"Binti kinga yau juma'a zanje nayiwa mutane huduba kuma akwai gurin da nake son zuwa kafin lokacin masallacin yayi"

Dagowa tayi ta kalleshi yayinda kwallar da ta taru a idonta ta zubo kan kumatunta,

"Abbu wurin budurwar taka zakaje?" Tayi masa tambayar da ita kanta bata san lokacin da tayiba,

Lallausan murmushi yayi yasa hannunsa duka biyu akan kumatunta yafara share mata hawayen dake kan fuskar tata,

"Ni ba wurin macema zanje ba wurin namiji ne, wani dan kasuwa ne ya shirya wani dan kwarya kwaryar wa'azi domin fadakar da yan uwansa yan kasuwa akan illar tauye mudu da cin riba"

Murmushi tayi  tadafe hannayensa dake kan kumatunta,

"Me zaka tafi ka barmin wanda zan rinka yi kafin kadawo?"

"Binti kiyita yiwa annabi salati tunda kinga yau juma'ah annabi kuma yace mu yawaita yimasa salati musamman ma ranar juma'a domin salatin da muke yimasa yana zuwa gareshi shiyasa annabi yace duk wanda ya yawaita salati agareshi to ranar gobe alqiyama zai samu cetonshi, idan kuma hakan bai samuba to kiyita fadin subhanalli wabi hamdihi, subhanallahil azim, domin annabi yace kalmomine masu saukin fada akan harshe sannan masu soyuwa awurin Allah kuma masu nauyi akan sikeli ranar auna ayyukan bayi"

Wani dadi taji ya ratsata agaskiya mutum mai ilmi yanada dadin zama sannan komai nashi akan tsari yake ita ta dade da fahimtar haka,

"Abbu to karka dade pls" hannunsa ta sauke daga kumatunta tafara murza yatsunshi, hatta hannun nashi kamshin turare yake zubawa,

"Binti bari mana karki karya min alwala ta ko kin manta abinda nafada miki jiya?"

Sakin hannunshi tayi tajuya cikeda kunya,

"Yanzu abbu dan wannan abun sai ya bata maka alwala"

Tafada bayan ta juya masa baya,

"Ehh mana binti, sai nadawo kinji"

"Ka kula da kanka abbu, Allah ya dawo min dakai gida lafiya"

Ba karamin dadin addu'ar da tayi masa yaji ba,

"Nagode binti"

Fita yayi ya tafi saboda yaga idan yaci gaba da tsaiwa awurinta zai dade bai tafiba, gaban window taje ta tsaya tana kallonsa lokacin da yake kokarin shiga cikin motarsa,

Har saida taga fitarsa daga gidan sannan tabar jikin window din tashiga bedroom dinshi tafara gyarashi tanayi tana yiwa annabi salati domin kwadayin samun rabon da taji jabir yace ana samu muddin aka dimanci yiwa annabi salati musamman ma aranar juma'a.

Gyara sashen jabir tayi tatas ta fesheshi da air freshener mai dadi sannan ta kulle ta dauki kwanukan data kawo masa breakfast ta fita zuwa sashenta,

"Oh Allah Sarki abbu" tafada tana dan murmushi akan fuskarta,

Sai da ta kammala gyaran sashenta ko ina yayi tsaf tsaf sannan ta zauna zaman kallo,

Tana nan zaune taji kiran mamansu ya shigo cikin wayarta wanda har sai da taji gabanta ya fadi domin bata san abinda zata fadawa ma ba,

Dakyar ta iya dauka jikinta har wani rawa yake yi, wata uwar tsawa taji ma ta daka mata da karfi sannan cikin zafin rai tafara magana,

"Goodness kinci amanata kin saba alqawarin da kika yimin tun farko, amma kisani sai na dauki mataki akanki"

Ido goodness ta zazzaro gamida toshe bakinta da hannuwanta, shikenan yanzu ma tasan ta musulunta saura kawai ta jirayi dan karamin yakin da zai afku, ta raya hakan acikin ranta,

Cikin tsawar data fi ta farko ma tace,

"Bakya jin abinda nake fada ne? Kiyi min magana tun kafin nazo har cikin gidan ki inci mutuncinki"

"Ma am so sorry pls, wallahi ba yin kaina bane kawai *wani haske* ne ya fado cikin rayuwata,amma kiyi hakuri ma"

"Ki rufe min baki munafuka, da ai cewa kikayi zaki rinka zuwa church din duk ranar Sunday amma yanzu gashi kin daina zuwa"

Wani sanyi taji ganin har yanzu 'ma' bata san ta musulunta ba,

"Ma zanzo, banida lafiya ne shiyasa nake zuwa church din bayan gidana amma idan nawarke zan zo"

"Saura idan kin warke ki k'i zuwa"

Tana gama fadin haka ta yanke wayar, tagumi goodness tayi tana tunanin gashi yanzu akan rashin zuwa church kadai ma tana fada to inaga idan taji ta karbi addinin gaskiya, ta jima tana tunani aranta Kafin ta tashi ta shiga kitchen,

Jalop din cous cous tayi wanda yasha kayan lambu aciki in banda kamshi babu abinda ke tashi, dan kadan ta zuba ta koma falo ta zauna, wayarta ta jawo ta shiga kiran jabir,

Cikin sanyin muryarshi taji yafara yi mata magana "amincin Allah ya tabbata agareki yake wannan yarinya"

Murmushi tayi mai dan sauti "abbu ba zaka dawo gida kaci abinci ba?"

"Binti ai ban gama abinda nake yi ba, ko zan dawo gidan nan ina jin sai dare"

Kamar zata fashe da kuka tace "Allah ya kaimu, Allah ya dawo dakai lfy"

"Binti karfa kiyi kuka kinji, pls kar kibari hawayenki su zuba"

Kwallar data cicciko idonta tayi kokarin maidawa, "to abbu" tafada ashagwabance,

"Yawwa binti shagwababbiya" yace da ita yana murmushi, itama maganar tasa murmushin tasakata,

Zare wayar tayi daga kunnenta tana tunanin jabir green snake ne under the green grass, saboda babu wanda zaiyi tsammanin haka yake domin shi din wani shiru shiru ne kamar ruwa sam bashida hayaniya gashi ko magana bai fiya zagewa yayiba ashe soyayya ce tsububu acikinsa,

Tunda ta kammala cin abincin ta kwanta tafara shakar bacci sai 5 ta tashi,

Wanka tayi taci kwalliya cikin riga da wando wadanda suka kamata sosai suka bayyanar da surar jikinta afili,

Part din jabir takoma ta zauna afalonsa ta dauki daya daga cikin littafin da yake koya mata tafara bitarsa, tana nan zaune har 7 tayi amma jabir shiru bai dawo ba,

8:30 tana nan a inda take azaune dif taji an dauke wuta atsorace ta tashi zata fita takoma sashenta domin acan tabaro wayarta, tana zuwa bakin kofa taji anbude kofar alamun za ashigo, babu tsammani tajita ajikin mutum, wata uwar kara tasaka mai firgitarwa,

Bakinta ya toshe da hannunsa hadida sake rungumeta acikin kirjinsa,

"Haba binti irin wannan kara haka ai sai ki kashe min dodon kunne" yarada mata acikin kunnenta, ajiyar zuciya ta saki mai karfi,kamar wacce zata yi kuka tafara magana,

"To ai abbu kaine baka yi magana ba shiyasa ban zata kai bane"

"Binti nadauka kina wajenki shiyasa ban zaci kina nan ba, amma dai ki daure ki rage tsoron nan pls"

Haske ne ya gauraye dakin sakamakon injin da aka kunna, kanta ya dago yana mai kallon jikinta ita dai ahar kullum cikin kananan kaya take,

Hannunta ya kama suka koma cikin falon,

"Binti idan mutum ya tsorata addu'a yake yi ba ihu ba kinji"

Kai ta daga masa tana kallonsa "abbu nakawo maka abinci ko? Tun safe baka kara cin abinci ba"

"To binti kawo min amma bari nayi wanka kafin ki dawo"

Cikin bedroom dinshi ya shiga ita kuma tafita zuwa sashenta.

Abincin ta hado masa ta dauko acikin dan madaidaicin kwando ta dawo sashensa, afalo ta dire kayan ta shiga cikin bedroom din daidai lokacin shikuma yafito daga bathroom daga shi sai gajeren wando ja,

Hannuwanta biyu tasaka ta rufe fuskarta gamida juya masa baya,

"Yi hakuri abbu ban san cewar baka gama ba da bazan shigo ba"

Kusa da ita yaje ya juyo da ita, "bude idonki binti, ai ya halatta ki ganni acikin ko wanne irin yanayi kamar yadda nima zan iya ganinki acikin kowanne irin hali,wanda ba muharraminki ba shine ya haramta ki gani acikin irin wannan lokacin"

Ahankali ta bude idonta amma kasa take kallo ta kasa dagowa ta kalleshi, shidai kunyarta tana burgeshi domin bata iya kallonsa indai babu kaya ajikinsa,

Hannunta yaja yakaita gefen gado ya zaunar da ita ya karasa gaban mirror yafara shiryawa, man touch me nacikin wani gwangwani yayi amfani dashi ya shafe jikinsa sannan yafeshe ko ina najikinsa da turare bayan ya taje sajensa zuwa dan madaidaicin gemunsa,

Kayan bacci ya dauko dark blue yasaka amma har lokacin goodness idonta akasa yake bata iya kallonsa ba har sai da ya gama,

Falo suka koma ta zuba mishi abincin yafara ci,

"Ungo" ya debo acikin spoon tareda mika mata, matsawa tayi ta dafa kafarsa ta bude bakinta ya saka mata, hakika tana jin dadin irin kulawar da jabir yake bata,

Haka yaci gaba da ci itama yana bata har ya gama, alokacin ya tuna da cewar ya shigo mata da kayan dadi amma ya ajiye a babban falo,

"Binti jeki falon farko akwai abinda nasiyo ki dauko akan kujera"

Tashi tayi tafita tana juyi domin ko ina nata motsi yake,

Kawo masa tayi ta ajiye, kayan marmarine kankana da apple sai tsire gasasshe wanda yasha tumatir da albasa,

Kankanar da apple din ta dauka taje kitchen dinta tayi blending dinsu tazuba masa madara da suga ta kawo masa,

"Wai ni binti menene wannan ne kiketa bani?" Ya tambayeta yana kallonta duk da cewar yasan ko menene kuma yasan amfaninsa,

"Abbu lemo ne"

"To meye amfaninsa?"

"Abbu yana kara lafiya"

"Da me kuma?"

Shiru tayi cikeda kunya fata take aranta Allah dai yasa bai ganota ba,

"Kin dage sai abu kiketa dura min binti alhalin ke kuma raguwace,gashi kullum cikin period kike, ki barni haka kar kisa naje matakin da sai na kwanta agadon asibiti"

Jikinshi ta shiga ta kankameshi ta boye kanta acikin kirjinsa tana dariya,

"Kai dan Allah abbu"

Tafada cikin shagwaba,

"Ai gaskiyace binti"

Lemon ya tsiyaya ya fara sha yana bata itama, tsiren ya bude ya dauko yanka daya yasaka mata abaki ai tana cinyewa tafara tsalle ajikinsa tana huhhura bakinta,

"Menene?"

"Abbu yaji" harshenta ta turo waje wai yasha iska yadaina yi mata yajin,

Bata ankara ba kawai sai ji tayi jabir ya cafki harshen nata yafara yi mata maganin yajin da take ji, ya jima yana yi mata wani salo mai nauyin fada kafin ya saki bakinta yana yi mata dariya,

Tsiren yake taunawa har sai ya tsotse shi sannan sai ya saka mata acikin bakinta, mamaki da farin ciki fal cikin zuciyarta saboda ganin jabir yagama sakewa da ita yanzu,

"Abbu da ace haka sauran maza suke yin rayuwar aure da matansu to da kowacce mace ta dawwama agidanta tare da mijinta har abada, da baza su rinka samun sabani mai yawa ba"

Murmushi jabir yayi yaja karan hancinta,

"Hakika maza da yawa basa zama su karanci mace kafin su aureta, kawai auren akeyi ake zama, zama irin na kai da kafa, yawancin mutane basa binciken wacce irin rayuwa annabi ya gudanar tare da iyalinsa, annabi ya kasance yana wasa da iyalinsa yana cin abinci dasu har wanka annabi yana yi tareda matarsa nana A'isha Allah ya kara mata yarda tace muna yin wanka tare da annabi har hannuwanmu suna haduwa acikin kwaryar ruwan da muke yin wankan da ita, kinga kenan ya kamata kowanne miji ya kasance mai wasa da raha acikin iyalinsa anfi son miji ya dauki matarsa a matsayin abokiya,duk wadannan hadisan zan koya miki su insha Allah domin suna nan acikin zadizzaujaini"

Fuskarta ta rufe "kuma abbu muma zamu yi wankan tare?" Ta tambayeshi tana boye fuskarta,

"Sosai ma, ko kina so mufara practical daga yanzu?"

Kai ta girgiza "a'a abbu ba yau ba"

Murmushi yayi yana kokarin cire hannuwanta wanda ta boye fuskarta aciki,

"Yanzu karatu zan dora miki cigaban najiya, karanto naji"

"Abbu alqur'ani yanada girma, ayoyinsa sunada yawa surorinsa kuma sunada tsawo nikam har na karaya nasan bazan iya haddace koda rabinsa ba"

Tausayinta yaji har cikin ransa, hannunta yakamo yasake matso da ita jikinshi sosai "binti alqur'ani yanada sauki wurin karantawa, duk yawan nan nashi Allah yace zai saukakawa duk Wanda yaso karantashi, shiyasa babban abin kunyane ga duk wani musulmi wanda bai iya karatun alqur'ani ba, sai kiga mutum ya iya karatun hausa, ya iya karatun turanci amma bai iya karatun alqur'ani ba, yakamata mu dawo cikin hayyacinmu domin babu hanyar samun lada acikin sauki kamar karatun alqur'ani domin indai kana karantashi to duk harafi daya da zaka furta zaka samu lada goma, bafa kalma daya ba harafi daya kinga kuwa ai garabasar takai garabasa"

Kwantar da kanta tayi ajikin kirjinsa "gaskiya kam abbu, nima Allah ya taimakeni in iya karantashi domin na samu nadace da falalar da wadanda suke karantashi suke samu"

"Amin binti insha Allah zaki iya domin karantashi akwai falala mai yawan gaske shiyasa akalla koda shafi dayane arana yana dakyau mutum ya rinka karantawa"

Kwantar da kanta tayi akan cinyarshi yafara koya mata karatun, yana fada tana fada yana shafa gashin kanta har yagama dora mata karashen surar da yafara koyar da ita jiya,

Tashi tayi bayan sun kammala karatun tatafi sashenta domin yin shirin bacci, wanka ta silla ta shafe ko ina na jikinta da turaren white musk, sannan ta fesa body fantasy mai dadin kamshi,

Wata doguwar rigar bacci ta dauko acikin kayan da ummu al'amin ta aiko mata dasu,rigar doguwace mai budadden kirji kalarta kalar ruwan zuma, bata da nauyi ko kadan sai dan karan santsi,

Sashen jabir ta nufa bayan tagama kulle nata sashen,

Tana shiga dakinsa ta sameshi akishingide akan gado yana waya, sai da zuciyarta tayi rawa saboda jin yadda yake yin wayar, bazata iya tantancewa koda ummu yake wayar ba ko kuma da budurwarsa,

Kamar ta koma sashenta take ji domin zuciyarta wani irin bugu taji tana yi mata kamar zata fito daga cikin kirjinta,

Tafi minti goma kwance tana jinsa yana wayar jin bashida niyyar gamawa alokacin ya sanyata tashi ta fita daga dakin, sashenta ta koma ta kwanta adakinta tareda rungume katotuwar teddy dinta, sai kuma tafara kuka wanda bata san ko namenene ba,

Wani irin zafi takeji acikin ranta, ta dade ahaka har jabir ya shigo ya sameta, tun daga kofar dakin yake jiyo shasshekar kukanta har ya karaso kan gadon,

"Binti" ya kira sunanta ahankali,

Shiru tayi ta daina kukan sai dai har lokacin hawaye basu daina bin kumatunta ba,

Ahankali ya dago da ita ya zubawa fuskarta manyan idanuwansa,

"Binti meya faru?" Ya tambayeta muryarsa asanyaye,

Shiru tayi masa tafara share hawayen fuskarta,

"Binti wayar da kikaji inayi ce ta sakaki kuka?"

Nanma shirun tayi taci gaba da goge fuskarta,

"Da ummun al'amin nake yin wayar fa, kiyi hakuri kinji, binti kina da kishi da yawa amma akwai addu'ar da zan baki wacce zata sanyaya miki kishinki,kina so in fada miki?" Ya tambayeta yana kokarin kamo hannuwanta, (jabir idan ka tashi bayar da addu'ar ka fadeta afili domin masu so sunada yawa ciki harda ummi A'isha),

Kanta ta daga masa duk ranta babu dadi,

"Tashi muje ki kwanta kinji"

Kafada ta make tana kokarin kwanciya "ni yau anan zan kwana"

Murmushi yayi ya murza hannunta, "binti kefa rigimammiya ce, kina son nima na kwana anan ne yau?"

"Kai kayi tafiyarka dakinka kaje ka kwana" tafada tana turo baki domin haushinsa take ji haka kawai,

Rankwafawa yayi saitin fuskarta wanda har tana iya jiyo fitar numfashinsa wanda yake sauka akan kumatunta,

"Yau bakya jin tsorone da zaki kwana ke daya?"

"Yeah" tafada atakaice gamida kokarin juya masa baya, batayi zatoba taji ya dauketa cancak yana kokarin sauka da ita daga kan gadon, zillewa ta fara yi tana tutturo baki,

"Nidai ka ajiyeni natafi da kafata"

Direta yayi yaja hannunta suka fita, shine ya tsaya ya rufe mata part din nata sannan suka wuce,

Tana gaba tana doddoka kafa shikuma yana baya biye da ita har suka shiga cikin bedroom dinshi,

Can karshen gadon taje ta kwanta ta juya kanta ta kalli bango, murmushi yayi ya matsa kusa da ita,aranshi yana tunanin hali irin na mata kwata kwata ba a iya musu domin ita kanta ummu al'amin complain take yi masa wai ya rage bata kulawa ba kamar da ba saboda ya sake aure alhalin itace bata sani ba shi har yanzu ma babu abinda ya hadashi da amaryar, wannan dalilinne ya sashi fara kwantar mata da hankali yana bata hakuri har goodness ta shigo ta sameshi to ashe itanma nata borin yana gaba,

Yan yatsun kafarta ya kama yafara jansu daya bayan daya ahankali,

"Binti fushi kike yi dani ko? Ki fada min abinda nayi miki sai in baki hakuri"

Idanuwanta ta rufe kamar meyin bacci, tashi yayi yana kallonta,

"Kici gaba da yimin shiru idan ina yi miki magana, shekaran jiyama ai hakkina ne yasa wannan kwaron ya cijeki, yauma idan da rabon zai cijeki shikenan"

Fitila yaje ya kashe, ai goodness najin haka tayi maza ta matsa kusa da barin da yake kwanciya, yana zuwa yajita kwance awurin, murmushi yayi ya kwanta agefenta ya lalubo hannuwanta ya hada ya rike cikin nashi,

"Abbu kayi hakuri bazan sakeba"

"Na hakura binti, karma ki sake bani hakuri akan wannan maganar"

Kanta yafara shafawa yana sinsinar daddadan kamshin turaren da jikinta ke futarwa so yake ya gane kowanne irin turare ne amma ya kasa, haka yaci gaba da sinsinarta har bacci ya daukesu bayan yayi musu addu'o'in neman tsari.

***

Washe gari da safe misalin karfe 10 tana falonshi zaune kusa dashi taji yana waya kan akawo masa kayan abinci wadanda zai rabawa makotansu sadaka, girgiza kai tayi agaskiya jabir dan aljanna ne domin yana kare hakkin duk wanda yake tare dashi ta raya hakan acikin zuciyarta,

Hannunta taji yana matsawa ashe har ya kammala wayar batare da tasani ba saboda ta tafi duniyar tunani,

"Binti tunanin me kikeyi ne?"

"Abbu babu komai kawai dai ina tunanin irin yadda kake kyautatawa kowane duk wanda zama ya hadaka dashi ciki kuwa harda makotanka"

Murmushi yayi mai yalwa "binti kenan ai makoci yanada babban hakki akan makocinsa domin annabi ya kasance yana yiwa sahabbai nasiha akan girman makoci, bai gushe ba har saida sahabbai suka tsammaci annabi zaice makoci zai iya gadon makocinsa, shi makoci ai abin tambayane ranar gobe alqiyama shiyasa ake son ka kyautata musu akoda yaushe domin acikin alqur'ani mai girma akwai inda Allah ya ambaci cewar abawa makoci hakkinsa, haka kuma annabi yace : _imanin dayanku bazai cikaba har sai yasowa makocinsa abinda yake sowa kansa, awani hadisin kuma yace duk wanda yayi imani da Allah da ranar karshe to kada ya cutar da makocinsa,cikin wani hadisin kuma yace Duk wanda makocinsa bai amince da amanarsa ba to bazai shiga aljannah ba_,amma mutane basa bawa makota hakkinsu, yanzu mutane sun kasance masu son kawunansu masu cutar da makotansu, alhalin da akwai matar da tashiga wuta bayan tana kwana tana salla kuma tana wuni da azumi abakinta amma lokacin data rasu sai annabi yace tana gidan wuta saboda tana cutar da makotanta"

Zaro ido goodness tayi ita dai idan jabir yana bata ire iren wadannan labaran har bata son ya daina domin dadi suke yi mata,

"Abbu ka sake koya min yadda ake yin wankan nan, anjima zanje inyi"

"To muslima" yafada da niyyar tsokanarta, batace komai ba illa dan murmushi da tayi,

"Farko dai ana so ka tanadi ruwanka mai tsarki wanda bai canja kala ba sannan kuma bai canja dandano ba, sai ki tsiyayi ruwan ki wanke hannuwanki sau uku sannan sai kiyi tsarki ki tabbatar kin wanke ko ina inda kike tunanin jinin ya taba, daga nan sai kiyi alwala amma sau daya daya ba sau ukuba sai dai ba zaki wanke kafafunki ba a iya shafar kunnuwa zaki tsaya, daga nan sai ki wanke gashin kanki sau uku amma ga ita mace anfi son ruwan ya ratsa har can karkashin gashinta, ana son ko ina ya samu, sai ki wanke fuskarki zuwa wuyanki shima sau uku daga nan sai ki wanke barinki nadama wasu malaman sunce daga kafada zuwa saman mazaunai za a wanke na barin dama sannan akoma barin hagu ayi haka sai asake dawowa barin dama awanke daga kan mazaunai zuwa agara sannan akoma bangaren hagu nanma awanke duk sau uku uku sai a game dukkan jiki da ruwa awanke kafafuwa wato karashen alwalar da aka faro daga farko, amma wasu malaman kuma sunce idan anzo wanke barin dama to daga kafada zuwa agara ne za awanke sau uku sannan sai akoma barin hagu shima ayi masa haka sai kuma agame dukkan jiki da ruwa sai awanke kafafuwa amma yana dakyau arinka tsettsefe yan yatsu domin ruwa bai cika shiga wurinba sosai, wannan shine siffar wankan,sannan basai lallai an tsefe gashin kai ba malamai sunce ko gashin kan mace akitse yake to zata iya yin wankan ahaka kawai dai abin bukata shine ta tabbatar ta kwarara ruwa agashin kanta yanda ruwan zai tabo har can karkashin gashin, amma ga macen data gama al'ada to yana dakyau tayi amfani da turaren almiski da ganyen magarya domin tsaftace jikinta hakan sunnace domin Nana A'isha ta kasance tana aikata hakan duk lokacin data kammala jinin al'ada haka kuma idan kinyi wankan ne kafin faduwar rana to sallar azahar da la'asar suna kanki idan kuma sai bayan faduwar rana kikayi to wajibine ki sallaci sallar mangariba da isha'i"

"Nagode abbu bari natashi naje nagani amma indai banga jininba ai shikenan ko?"

Kai ya girgiza mata yana jan dan yatsanta guda daya,

"Har wannan mai kalar ruwan kasa kasan ko kuma yelo dinnan shima indai kin ganshi to zaki bashi hukuncin jinin al'ada ne domin jinin ne yake saba kala akarshen al'adar, domin fadin Nana A'isha uwar mumunai Allah ya kara mata yarda tace sun kasance suna daukar wannan ruwan mai fatsi fatsi a matsayin jinin al'alda mutukar suka ganshi alokacin al'adarsu haka kuma basa yin wanka har sai sunga farin ruwa mai kamar farar kasa ya bayyana"

Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi domin jabir tako ina yayi kuma yasan abubuwa da dama wadanda suka shafi mata kai kace su ya karanta ma gaba daya,

"To bari naje nadawo" tafada tareda tashi ta tafi part dinta, binta yayi da murmushi yana mai jin wani yanayi agame da ita.

  Kullum suna tare yana koya mata karatun alqur'ani ko kuma yana bata kissar annabi Muhammad (S.A.W) domin littafin sira ya samo mata yake koyar da ita akowanne dare, amma har yanzu bashida niyyar kulata irin kulawar da miji yake yiwa matarsa domin so yake yaga ta fahinci addini sosai sannan ta sake sakewa dashi gudun kar yaje ko har yanzu tana tsoronshi yasan hakan zai iya haifar mata da illa.

Yau ta kama ranar Monday dan haka da azuminsa ya tashi, ita goodness bata saniba dan haka taje ta shiryo masa breakfast mai lafiya,

Acikin bedroom dinshi ta tarar dashi yana kwance gashi kuma yau zai koma office, daga shi sai dogon wandon bacci ko riga babu ajikinsa,

Gaban gadon taje tayi kneel down agabanshi ta saitinshi ta soma mika masa littafin larabcin dake hanunta,

"Abbu tuna min sunan wadannan abubuwan namanta"

Karbar littafin yayi,

"Yadun hannu, rajlun kafa, uzunun kunne, ainun ido, anfun hanci, fammun baki"

Littafin ya mika mata yana gyara kwanciyarsa,

"Yawwa abbu nagane, yadun hannu ko?" Sai takamo hannunsa takama sannan tasaki,

"Um rajlun kuma kafa ko?" Kafarsa takoma takama ta shafi tafin kafarsa,

"Sai uznun kunne, abbu wannan?" Kunnensa ta kamo tana tambayarsa, kai ya daga mata yana kallonta gaba daya wani iri yake ji,

"Abbu ainun kuma ido ko?" Ji yayi tana shafar idonshi daya, kafin ya farga har ta cafko hancinsa,

"Anfun kuma hanci, yehhh gashi abbu dama Kanada dogon hanci"

Hannunta ya rike, "binti ki bari mana, azumifa nake yi"

Dariya tayi "Allah abbu yau bazan bariba tunda Kaine kace min duk karatun duniya in andorawa mutum to da practical yafi tafiya"

Kafin ya lalubo amsar da zai bata ta haye jikinsa tana cewa "fammun baki" caraf ta cafki bakinsa cikin nata, hmmm su malam jabir koya lafiyar wannan azumi? Umm pherty Xarah ko kinada amsa ne kibani?

      _Gaisuwa babba gareku masoya masu karanta wannan littafin na wani haske._








_*Ummi Shatu*_🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [10/9, 8:01 AM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*

    _*NA*_
_*UMMI A'ISHA*_

_101-105_

            _Assalamu alaikum masoya masu karanta littafin wani haske kuyi hakuri da rashin ganin posting akan lokaci wannan ya farune ta sanadiyyar wasu hidimomi da suka hau kaina sannan kuma kun san wannan littafin abubuwan da suke cikinsa sun shafi bincike da nazari shiyasa zakuga wani lokacin nadade banyi posting ba, yanzunma korafe korafenku naji shiyasa kawai na rubuto muku abinda ya sawwaka amma da a manufata zan kawo muku matsaloline wadanda mata suke fuskanta musamman ma ta fuskar auratayya tsakanininsu da mazajensu da kuma hanyoyin warwaresu to amma jin korafin naku yayi yawa yasa na ajiye wannan batun agefe saboda naji wasu na cewa ummi ta fiya jan rai akan wannan book din, to kuyi hakuri wlh ba jan rai bane yanayin rubutun ne haka, sannan kuma wata baiwar Allah tace ya kamata yanzu adaina kiran tauraruwar littafin da goodness tunda ta musulunta ana kiranta da bahijjanta, dan haka yanzu bahijja zakuji ina ambata, wannan Shafin nabayar dashi kyauta ga duk wata masoyiyar wani haske._


~~~Duk iya kokarinshi na ganin ya hanata aikata abinda tayi niyya kasawa yayi dolenshi haka ya rabuda ita taci gaba da yin yanda take so da bakinsa, rungumeshi tayi tana murmushi,

"Abbu yau bazakaje office ba ko?" Ta tambayeshi tana shafar sajensa, bude idonshi yayi yana kallonta kafin ya bata amsa wayarsa dake ajiye akan bedside drewar tafara vibration, hannu ya mika ya dauko ya duba mai kiran nasa,secretary dinsa ne na office dinsa dan haka yayi saurin dagawa domin yasan tunda ya kirashi to muhimmin abu zai sanar dashi,

Asanyayenshi ya daga wayar bayan sun gaisa yake sanar dashi bakin da zasu zo wurinshi anjima domin tattaunawa akan wata kwangila da zasu samu, wayar ya kashe yana tunanin dole yayi saurin fita zuwa office before bakin nasa su zo,

"Dagani naje nayi wanka" yace da ita yana kallon yar kyakkyawar jar rigar dake jikinta mai yalo yalo marar nauyi,

"Abbu kana yin azumin ko? Bayan kuma na yi maka breakfast, ni wlh bazan yarda ba" tafada cikeda shagwaba,

"Binti ai nafasa yin azumin tunda kin rigada kin bata min shi, idan nayi wanka yanzu zanci duk abinda kika girka min"

Wani tsalle ta daka ajikinsa tana murna, "yawwa abbu ko kaifa"

Murmushi yayi ya tashi zaune har lokacin tana kan cinyarsa azaune, kallo yabita dashi acikin zuciyarsa yana cewa "ai kuwa zaki sani tunda kika karya min azumina"

Hannunshi ta kama tana kallon fuskarshi "abbu inje in hada maka ruwan wankan"

"Uhm" yafada ahankali, wani tsalle ta dira ta sauka ta nufi toilet din yayinda shikuma yabita da kallo har yanzu akwai kuruciya da yarinta a tattare da ita,

Tana ciki tana sirka masa ruwan zafin data tara acikin wani babban baho ya turo kofa ya shigo cikin bathroom din, juyawa tayi ta kalleshi sai ta ganshi da dan gajeren wando, da saurinta ta juya wadda har tana kokarin fadawa cikin bahon ruwan zafin bata sani ba,

Da saurinshi ya rikota ta fada jikinshi ya riketa,

"Binti wannan gangancin fa? Saura kadan ki fada cikin ruwan zafi" yafada ahankali yana rikeda ita,

"Abbu gashinan kayi wankan, bari naje na gyara maka dakinka kafin ka fito" tafada tana mai sake rufe idanuwanta,

"Kitsaya binti, ai tare zamu yi wankan yau, ko bakya son ki samu lada?" Bude idonta tafara yi cikin sauri tareda yunkurin raba jikinta da nasa,

"Abbu kayi hakuri dan Allah, nidai wlh bazan iyaba kunyarka nakeji"

Dan murmushi yayi mai kayatarwa gamida dafa bangon bathroom din da hannuwanshi yayi mata runfa tana jingine ajikin bango tana neman hanyar guduwa,

"Ai kema wasa kike yi yarinya, ki karya min azumin nawa sannan kuma kice ba za muyi wanka tare ba, binti ladafa zaki samu domin babu abinda yafi kyautatawa miji saurin samun lada, duk umarnin da na baki muddin kika bishi to lada zaki samu, idan kika yimin wani abu wanda ya sani farin ciki shima lada zaki samu..!"

"Abbu wlh zaka makara a office gashi ana can anata jiranka"

Kallonta yayi yana sake bude manyan idanuwansa yana kallonta, fuskarta ya zubawa ido yana kallonta amma ita takasa kallonshi idonta yana kasa,

"Binti kinga, dago idonki ki kalleni"

Kasa dagowa tayi har lokacin kasa take kallo, hancinta ya lakuce "wannan yarinyar kin fiya wayo da yawa"

Ruwan da yake zuba acikin bahonne yafara zuba akasa domin bahon tuni ya dade da cika,

"Tunda kin ki yin abinda nasaki shikenan bari nayi ni daya kafin amaryata tazo munayi tare"

Juyawa yayi yaje gaban fanfon yafara kashe ruwan da yake zuba,

Ahankali bahijja ta bude kofar bathroom din tafita, agaban mirror ta tsaya tana tunani aranta, tunanin maganar da jabir ya fada mata yanzu take yi indai kuwa hakane amma da tasan sunanta gawa domin ayanda take jin zuciyarta gani take yi indai ya kara aure yanzu to babu makawa mutuwa zata yi, lallai Ummu al'amin tayi kokari gamida juriya data iya barinta ta zama kishiyarta,

Bata taba sanin kishi yanada daci ba sai yanzu da take auren jabir, kasa gyara dakin tayi tana tsaye har lokacin tana juya maganar da jabir yafada mata acikin kwanyarta, har jabir yayi wankan ya fito ya sameta tsaye agaban mirror wadda ita bata ma san yafito daga wankan ba,

Kafadunta ya dafa da duka hannuwanshi guda biyu sai alokacin ta dawo hayyacinta a sanadiyyar sanyin ruwan da taji ajikinta,

"Me kike tunani ne binti?"

Fuskarta ta shagwabe ta turo baki tana son yin kwalla,

"Abbu ba kaine ba kace...!"

Sai kuma tayi shiru,

"Nace me? Fadi inji, me nace?" Ya tambayeta yana kokarin juyo da ita,

"Kaine kace wai, wai, wai...!"

Hawayen idonta ne suka silalo kan kuncinta, hakan yasashi bude baki yana kallonta cikeda mamaki domin bai san abinda yafaru ba,

"Binti me nace? Yi shiru ki fada min kinji"

Kamar ya zugata sai tafashe da kuka tareda fadawa kirjinsa, rungumeta yayi ya fara shafa gashin kanta,

"Binti idan baki fada min ba wa zaki fadawa wanda yafini? Ni yafi cancanta da ki sanarwa da dukkan damuwarki"

"Abbu kaine kace wai idan amaryarka tazo, wai, wai, wai tare zaku nayin wanka" tana gama fadin haka ta boye fuskarta acikin kirjinsa, dariya sosai maganarta ta bawa jabir domin shi yayi tsammanin wani abune muhimmi tunda yaga harda kuka tayi,

"Yanzu binti wannan maganar kike yiwa kuka? Ohhh, nifa nayi zaton wani abune babba yasaki kuka, kishiyar kike yiwa kuka? So kike ta rainaki tun kafin tazo kenan"

"Abbu dagaske kake?"

Kanta ya shafa yana murmushi wanda har hakoransa sai da suka fito, kanta ya dago yana kallonta,

"Wasa ne binti, bada gaske nake yi ba dawasa ne amma indai bakya bani kyakkyawar kulawa to zan yimiki abinda bakya so, indai bazaki rinka bani farin cikiba to zanyi miki kishiya"

"Abbu dan Allah kayi hakuri Allah bazan sakeba" tafada idonta narai narai tana kokarin sake yin wani hawayen,

"Shikenan nahakura, karki sake yin kuka kinji, maza kije ki kawo min breakfast din kafin na shirya"

Sakinta yayi yana yi mata lallausan murmushi, fita tayi tabarshi yafara shiryawa ita kuma ta nufi sashenta, kwanuka masu tsafta ta dauko ta zubo masa doya da kwan data soya masa ga dan farfesun kayan ciki agefe sannan ga custard powder data dama sai tea wanda yasha kayan kamshi aciki,

Kinkimar kayan tayi ta kai masa falonshi ta ajiye sannan tabishi cikin dakin, lokacin data shiga har ya gama shiryawa cikin wani bakin danyen boyel mai kyau dakin gaba daya ya gauraye da kamshin turarensa mai dadi na special oud.

Acan wurin da ya kebe domin gudanar da ibadarsa ta hangoshi yana sallar walaha, tsayawa tayi ta zuba masa ido tana kallon shi hakika yayi mata kyau domin gayunshi ya burgeta mutuka, tun daga hular kansa har agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa duk kalar kayansa ne, tana nan tsaye tasaka zaren gabar rigarta abakinta tana wasa dashi har ya idar yayi addu'a yatashi ya nufo inda take tsaye tana jiransa, gabanta ya karaso ya tsaya, hannunsa yasa yana kokarin zare zaren dake bakinta tana wasa dashi da hakorinta,

"Binti abin riga kike ci? Kalleki kamar wata baby"

Kallonsa tayi tana murmushi "abbu kayi kyau sosai"

"Nagode binti, yau yarintar ce ta motsa?" Yafada yana lakuce hancinta,

Murmushi tayi taja hannunsa tana kallonsa, "abbu muje kayi breakfast, bana son ka makara azuwa office"

Bin bayanta yayi har suka isa wurin da takalmansa ke jere reras, wani bakin takalmi ta dauko masa na fata half cover mai kyau, ajiye mishi tayi agabansa,

Falo suka nufa bayan yasaka takalmin, akan kujera ya zauna ta jawo masa dan karamin stool ta ajiye masa abincin akai tana kallonsa,

"Binti wannan girkin naki ai sai yasa kunnena ya cire" yafada daidai lokacin da yafara cin doyar data soya masa,

"Abbu banda tsokana fa" tafada tana murmushi,

"Babu wani tsokana binti, abincin yayi dadi gashi naga harda wani koko koko, kunu kunu kika hada min"

Murmushi tayi tana tafa hannunta "lah jama'a kunji abbu bai san custard powder ba, amma abbu idan akaji dariya za ayi maka"

"To ai gashinan kin fara yimin dariyar"

Hannunsa ta riko na hagu, "abbu bari na gyara maka agogonka"

Agogon ta kunce ta sake daura masa tana murmushi koda ta gama daura masa bata saki hannun nasa ba yan yatsunta tafara ja tana lankwasa masa su suna kara kas kas,

"Binti kema kin iya mugunta ko?"

"Abbu me nayi maka? Daga gyara?"

Mikewa yayi yana murmushi aranshi yana burin wani lokaci da yake hasashen zuwansa a daren yau,

"Bari naje binti"

"Abbu, Allah ya kiyaye hanya, Allah ya bada sa'a" tafada tana kallonsa

"Amin binti" yafada tareda jan hancinta saboda ganin idonta ya fara kokarin kawo kwalla,

"Meyasa bakya gajiya da kuka ne? Ki rage saurin kuka idan ba haka ba zaki haifi yaro ruwa ruwa"

Dariya ce ta subuce mata bata shirya ba "abbu nida ko cikin banyi ba har zaka fara yimin maganar yaro" tafada tana yi masa murmushi,

"Saurin me kikeyi binti? Zakiyi ai soon"

Murmushi tayi har lokacin tana rikeda hannunsa "abbu ka taho min da chocolate"

"Muga bakin kwadayin shan chocolate?"

Bakin ta bude tana turo masa dan yagani, kiss ya manna mata akan lips dinta duka yana murmushi,

Sakinsa tayi ta juya tana murmushin itama, fita yayi yana mai jin babu dadi acikin ranshi dalilin nisantar ta da zaiyi,

Tana labe tana lekenshi har yabar gidan, kan kujera ta fada ta kwanta tana tunanin hali irin na jabir.

Tunda ya tafi yabarta taketa kirkirar ayyuka domin bata son zama kurum saboda idan ta zauna tasan kadaicine zai dameta gashi kuma tunda jabir yafita take tunaninshi acikin zuciyarta,

Babu irin aikin da bata yi ba domin ganin ta ragewa kanta lokaci, kananan kayan jabir duk ta tattare da jallabiyoyinshi da kayan baccinshi duk ta wanke, bayan ta gama taje ta dora girki, tuwon shinkafa miyar agushi tayi tahada lemonta na kwakwa da madara kamar yadda ta saba,

Wayar jabir tafara kira lokacin misalin karfe 1:30 narana, yana tsaka da aiki a office sai rubuce rubuce yake gashi files tuli guda akan teburinsa kasancewar ya dade baya office din shiyasa ayyuka suka tarar masa,

Agajiye ya daga wayar yana murmushi aranshi kuma yana tunanin ko yanzu da wacce rigimar ta bullo kuma,

"Binti ya akayi?"

Fuska ta shagwabe kamar yana kallonta, "abbu sai yaushe zaka dawo?"

"Binti aiki yayi min yawa, sai 5 zan tashi may be ma yau sai nayi over time saboda inada ayyuka dayawa"

"Abbu kar kayi over time dan Allah, kadawo 5 din"

"Kina son ganina ne binti?"

"Ehh abbu"

"Me zaki bani?"

"Abbu sai kadawo dai, yanzu dai ka turo min mal idi driver"

"Ina zaki aikeshi?"

"Wurinka abbu, dan Allah karka manta"

"Bazan manta ba"

"Yawwa abbu nagode, ayi aiki lafiya"

Wayar ta tsinke tana jin wani irin dadi acikin ranta,

Shima jabir wayar ya ajiye yana murmushi ko me zata aiko masa kuma oho,

Lokacin da mal idi driver yazo dama tuni ta gama harhada masa kayan acikin kwando babba, komai da zai bukata ta zuba kama tun daga filet da cokula da cups da tissue domin goge hannu, dan haka yana zuwa bashi kawai tayi takoma sashenta,

Lokacin da sakon ya riski jabir ba karamin mamaki yayi ba, domin abincine wanda akalla mutane biyar zasu ci ya ishesu gashi harda hadadden lemon kwakwa,dadine yake ratsashi tako ina dama meeting zasuyi shida directors dinsa Wanda duk lokacin da sukayi meeting din abincin sayarwa ake siyo musu amma shi baya ci saboda gaskiya yanada tsananin kyankyami,

Wannan abincin da bahijja ta aika musu shi sukaci sukayi kat Suna santi kowa sai yabawa yake yi, shikuwa jin bahijja yake har acikin zuciyarsa saboda yasan ta damu dashi sannan tana kiyaye duk wani abu wanda zai sakashi cikin damuwa, ranar har  6yakai a office sai 6:30 ya nufi gida, duk ya gama kosawa burinsa kawai yaje gida yayi ido hudu da ita.

Tana falonta tana kallon wani American film ya shiga yana gyara babbar rigarsa,

Tashi tayi tana murnar ganinsa yayinda shikuma yayi mutuwar tsaye yana kallon kyakkyawar shigar da tayi domin wata rigace orange colour mai wasu fararen duwatsu ajiki, iya cinya rigar take sannan bata da babban hannu, hannunta dan karamine, ga wani wando baki fela tasaka, kanta ta daura bakin dan kwali,

Gabansa taje ta tsaya tana kallonsa,

"Abbu sannu da zuwa"

Hannu ya mika ya kamo nata hannun yajata ya hadata da barin jikinshi ya nufi sashensa da ita,

"Yawwa binti ya gida? Natafi nabarki ke daya ko?"

Daga kai tayi "abbu ai gobe sai nabika"

Murmushi yayi yana mai tuno al'amin dinshi domin shima kusan kullum haka yake cewa sai ya bishi office lokuta da dama sai yayi masa dabara sannan zai samu ya zare jikinsa ya fita,

Har cikin falonshi ta rakashi tana shakar kamshin jikinsa, cikin bedroom dinsa ya shiga yayi wanka ya fito yayi shirin masallaci, gaba daya kamshine ke tashi daga jikinsa,

Har inda take yaje ya kamo hannunta ya yatasheta daga zaunen da take ya rike yan yatsunta yana kallon kwayar idonta, sunkuyar da kanta tayi ta kasa kallonsa,dago habarta yayi yakai bakinsa kan goshinta yayi mata kiss,yana murmushi,

"Binti zanje masallaci kinji? Sai nadawo"

Kai ta daga masa sannan ahankali tace "adawo lafiya abbu".

Fita salla yayi ita kuma ta koma sashenta tayi tata sallar, anan ta zauna tafara yin azkar irin wanda jabir ya koya mata, dab da sallar isha ta tashi takoma sashensa tana sanye da zumbulelen hijabi mai hannu wanda ya saukar mata har kafafunta domin yanzu jabir ya kawo mata hijabai manya kala daban daban.

Asashensa tayi sallar isha, tana idarwa tafara karanta hadisin da ya koyar da ita adaren jiya wanda aka karbo daga baban hurairata Allah ya kara masa yarda wanda annabi Muhammad sallallahu alaihi wassalam yake cewa "yaku mutane ku yada sallama, kubayar da sadaka, kuyi sallar dare alokacin da mutane suke bacci, idan kukayi haka hakika zaku shiga aljanna da aminci"

Shigowar jabir ce ta katse mata tilawar karatun da takeyi, kafadunta ya kama ya mikar da ita tsaye,

"Tashi muyi salla binti"

"Abbu ni nayi sallata yanzun nan na idar"

Dan malalacin murmushi yayi mata "binti wannan ai daban, wannan ta nafila ce zamuyi, sannan ina son ki dage ki rinka yin sallar shafa'i da wutr domin tanada tsananin falala mai tarin yawa"

"Abbu zan rinka yi kaga shikenan basai nayi ta tsakar dareba irin wacce kake yi"

"Waya fada miki? Koda ace kinyi shafa'i da wutr to zaki iya tashi da daddare kisake yin sallolin nafilarki kuma zakiyi shafa'i,wutr ne kawai bazaki yiba domin sau daya ake yinsa idan mutum ya sake to yazama shafa'i, nasan mutane da dama suna son tashi yin sallar dare to amma idan har sukayi shafa'i da wutr sai su zaci Cewar shikenan babu damar yin wata sallar tunda sun rufe da wutr to ba haka bane mutum zai iya yin wasu sallolin acikin dare koda kuwa yayi shafa'i da wutr kawai dai ba ason ya sake yin wutr ne domin wanda yayi afarko ya wadatar"

Kai ta kada masa tafara gyara masa abin sallar yanda zai ishesu,

Limanci yayi yajasu sallar suka gudanar da sallolin nafila wanda hadda shafa'i da wutr, addu'o'i sosai jabir yayi musu wadanda ba zasu faduba,

Bayan ya shafane ya jiyo yana kallonta, "binti idan kin idar akwai kaya acikin babban falo kije ki dauko, ina fata dai bakiyi wani girkin ba? Saboda yau naga kinsha aiki da yawa"

Addu'ar ta shafa tana kokarin cire hijabin jikinta "hmm abbu banyi ba dama yanzu nake tunanin dafa mana indomie"

"To na hutar dake basai kin dafa ba"

Hijab din ta ajiye ta fita taje ta shigo da kayan da yazo musu dashi,

Kaza dukekiya ta gani guda biyu gasassu ga chocolates dinta kala kala sannan ga kayan marmari suma daban daban,

Baje kayan tayi tana kallon jabir "abbu yau ka hutar dani nagode da yanzu sai nasake shiga kitchen"

Yan yatsunta ya kamo "babu komai binti, ai naga sakonki ya sameni har office, me yasa kika bini dashi har can?"

"Bana son ka zauna da yunwane shiyasa kuma nasan kai ba cin abinci zakayi ba haka zaka wuni da yunwa nikuma bana son haka"

"Nagode binti, ga abinci nan kici nakine ke daya"

Idanuwanta ta ware "abbu wannan sunyi min yawa, bazan iya cinyesu ba"

Kankana ya dauka yakai bakinsa "ni kinga iya abinda nake sha'awa kawai, ita kadai zansha"

"Abbu kazar fa?"

"Takice yarinya, kici kayanki kinji"

Kai ta girgiza tafara yagar kazar tana ci har taci rabi nan taji tafara koshi,

"Abbu yau zaka doramin karatu ko sai gobe?"

"Duk yanda kikeso binti, amma karatunmu na yau daban yake dana ko wacce rana, karatun yau na musamman ne"

Cigaba tayi da shan chocolate dinta domin bata fahimci inda maganar tasa ta dosa ba, har ta kammala yana zaune yana kallonta, kanta ta dora asaman cinyarsa,

"Washh abbu cikina nakoshi da yawa"

Kanta ya fara shafawa yana yi mata lalube acikin gashinta

"Kinyi irin koshin da ba aso mutum yayi, annabi yace idan dayanku zaici abinci to ya raba cikinsa gida uku, kashi daya abinci kashi daya ruwa, kashi dayan kuma iska saboda gudun kada ya cutar da jikinsa"

Zaune ta tashi "hmm abbu komai dai a musulunci ana bashi hakkinsa, Allah abbu musulmai sunji dadin rayuwarsu"

"Tashi muje nasaki aiki a kitchen"

Tashi yayi yaja hannunta suka fita zuwa kitchen, shayin na'a na'a ta dafa masa da kayan kamshi sannan suka dawo sashensa, tana kwance akan cinyarsa akan doguwar kujera shikuma yana shan shayinsa ga tv kuma yana kallo,

Wayarshi ce tafara kara, yana dubawa yaga ummu ce,

"Ummu al'amin kin dawone daga siyayyar?"

Tana jin ya ambaci sunan ummu tafara kokarin mikewa, cup din shayin ya ajiye ya riketa ya mayar da ita jikinsa yaci gaba da wayarshi daga karshe sukayi sallama yana tambayarta al'amin tace yayi bacci tun jimawa,

Wayar ya kashe yana kallon bahijja bayan sunyi sallamar da ummu,

"Abbu bacci, zanje nayi wanka" tafada tana mutsusstuka idonta,

"Bari nagama nakaiki kiyi" bata sake magana ba ta zauna tana jiransa, kasancewar komai nashi cikin sanyi yake yinsa shiyasa ya dade bai gamaba,

Yana gamawa ya kama hannunta zuwa cikin bedroom dinsa,

"Ki shiga kiyi wankan" ya nuna mata bathroom dinsa,

"Abbu brush dina da kayan baccina fa"

"Duk zan baki binti, ai na tanadar miki komai saboda zuwan wannan ranar"

Sabon brush ya dauko ya mika mata hadeda babban towel sabo fil,

Karba tayi ta shiga bathroom din amma duk tana cikeda mamaki da al'ajabi,

"Binti yau bazaki bar kofar bathroom din abude ba? Ko yau babu tsoro?" Yafada cikin tsokana,

Batayi magana ba tasaka key ta kulle kofar, mayukan wanka ta gani masu kamshi dayawa kala kala, duk sai da tayi amfani dasu ta wanke jikinta tas sannan tayi brush ta tsaftace bakinta bayan ta shaftace jikinta da shaving stick, hatta bayan kunnuwanta sai da ta tsaftacesu kasancewar wurine dake rike kazanta dan haka dole sai ana kulawa dashi,

Sai da ta dauki tsawon lokaci tana gyara jikinta sannan ta fito duk a tsure take da jabir sai muzurai take yi.

Acikin dakin tasameshi kishingide agefen gado yana kallonta, irin kallon da yake binta yasata jin kunya,

"Abbu nafito" tafada adirirce,

"Ga rigar baccinki nan kishirya sai kisa"

Towel din jikinta ta gyara,

"Abbu to ka fita daga dakin"

"Tofa, wata sabuwa" tashi yayi yana kallonta yafita ya koma falo, gaban mirror ta karasa ta fara shafe jikinta da man shafawarsa na touch me mai dadin kamshi, turarurrukansa ta fara dubawa har ta samo wani guda daya mai suna taibah, shi ta dauka ta feshe jikinta dashi sannan ta feshe rigar baccinta,

Bathroom ta koma ta tsaya tafara duba rigar, tabbas rigar ta hadu sai dai kuma zatasha kunya yau domin rigar za a iya kiranta da shararatu, banbancinta da gidan sauro kawai ita rigace amma net shine yanayinta,

Rigar bata bukatar bra domin akwai ajiki sannan tanada dan karamin pant,kalarta pink colour,

Daurewa tayi tasaka rigar, tana gama sakawa ta juya tafara kallon jikinta ajikin mirror din cikin bayin, tayi kyau iya kyau abunka da yar duma duma sai kace oh oh, jin alamun za a bude kofar yasata saurin janyo towel ta lullube jikinta, jabir ne ya leko ya jawota waje,

"Haba binti me kika sake komawa yi acikin bathroom kuma?"

Towel din yafara ja yayinda ita kuma ta rike kam, dakyar ya janye towel din hakan ya sata saurin rufe fuskarta da tafukan hannayenta,

"Masha Allah, binti irin wannan kyau haka?"

Sake damke idonta tayi tana doddoka kafafunta akasa,

"To jeki ki kwanta kinji"

Hannunta ya kama ya rakata har inda ta saba kwanciya ya saketa ya juya, cikin bathroom din shima ya shiga yayi wanka bayan ya tsaftace kowanne lungu na jikinsa,

Fitowa yayi yanata faman kamshi, gaban mirror yaje ya fara shafe jikinsa da mayuka masu kamshi,
Kayan baccinshi ya dauko yasaka ya karasa gefenta ya kwanta gamida janta jikinsa,

"Binti ko har kinyi baccine bayan ba muyi hira ba yau?" Yarada mata ahankali yana wasa da zip din rigarta, tana jinsa tayi shiru tayi luf,

"Nasan idonki biyu, jiyo kiji"

Yafada ahankali, jin shiru yasashi jiyo da ita tana fuskantarsa, cakulkuli yafara yi mata cikin sauri ta rike hannunsa bayan tafara  dariya,

"Abbu kabari dan Allah"

"Au dama kina jina shine kikayi min shiru?"

"Bazan karaba yi hakuri abbu"

"Yawuce binti, shikenan saura karatunmu da muka fara rannan ko?"

Bata iya yin magana ba hakan ya sashi kashe wutar dakin bayan ya lalubi bakinta cikin nashi.

***

K'arfe 8 daidai ta bude idonta, dakin shiru babu motsin komai aciki,sama ta daga kanta take kallo take abubuwan da abbu yayi mata suka fara dawo mata, hawayen farin ciki tafara yi fuskarta dauke da murmushi domin wannan rana ta jiya da yau ranakune masu mutukar muhimmanci acikin rayuwarta,

Dakyar ta juya jikinta daga barin da take kwance nan taga tsakiyar gadon tamkar an yanka kaza,

"Hmmmmm abbu kenan" shine abinda kawai tafada ahankali tafara kokarin tashi, lallabawa tayi ta shiga toilet tana dingisawa, ruwan zafi ta tara mai mutukar zafi amma bata saka dettol aciki ba kasancewar ta taba jin wani likita yana bayani kan illolin dettol ajikin mace shiyasa ba ason ayi sit bath dashi amma babu laifi ayi wanka dashi ko kuma awanke kaya domin yana da karfi yana kashe bacteria kowacce iri ciki harda mai amfani da marar amfani, gishiri kawai ta zuba acikin ruwan zafin ta shiga ta zauna domin shi gishiri har maganin kaikayin dake damun mutum yake yi haka kuma yana riga kafin ciwon cutar sanyi,

Ta dade acikin ruwan har sai da ya huce sannan tafita tayi wanka tayi brush amma duk agaggauce take yin wadannan abubuwan saboda bata son jabir ya shigo ya isketa bata shirya ba kuma haka ya kamata ga kowacce mace domin lokacin da aka tashi daga bacci agaskiya lokacine dake bayyanar da munin mutum kasancewar daga bacci aka tashi zaka samu wata ma launin fuskarta ya sauya idonta yayi ja wata harda kwantsa, sannan ita kanta yanayin fuskar wani iri yake zama har sai anyi wanka,

Fitowa tayi daga cikin bayin tayi maza tafara bincikar kayan sawarsa, wata farar t shirt ta zaro mai layi layi ajiki mai dogon hannu da maballaye ajiki, cikin sauri ta saka rigar sannan ta zaro jeans blue shima tasaka sai dai kayan tsayinsu yayi mata yawa kasancewar jabir dogone ajin farko,

Hijabinta ta dauka tayi salla tana idarwa tayi musu addu'o'i musamman ma kan samun zuri'a tagari duk da cewar jiya taji jabir ya dade yana yi musu wannan addu'ar lokacin da abubuwa zasu faru,

Cire hijabin tayi ta tashi bayan ta kammala addu'ar,gashin kanta taje gaban mirror ta fara tajewa amma kuma sai kamshin man datayi amfani dashi wurin wankewa yake, domin ita ba zata iya kwarawa kanta ruwa kawai tabarshi ahaka ba har sai tasaka man wanke gashi ta wankeshi domin idan aka zubawa gashi ruwa kawai aka kyaleshi to zakaji yana wani irin tashi marar dadi har maigida yaji babu dadi,

Cure gashin tayi ta daureshi ta nufi hanyar fita, akofa sukayi kicibus da jabir yana kokarin shigowa yasha wando iya gwiwa da yar shirt dinshi bashida banbanci da samari irin yan makarantar nan,

Da sauri ta juya masa baya tayi niyyar komawa cikin dakin, a tsakiyar dakin ta tsaya tana karewa royal bed dinsa kallo wanda yake a hargutse,

Jinsa tayi ta bayanta ya rungumeta ya zagayeta da hannayenshi gamida ziro kansa ta kan kafadarta,

"Binti kin tashi?" Yafada acikin rada,

"Abbu good morning"

"Morning bintin abbu, how was your night?"

Shiru tayi tana yamutsa fuskarta,acikin ranta ta tace "too harsh"

"Binti ba zaki amsa ba?"

Jiyo da ita yayi sai ta rufe idonta sai ga hawaye sharrr sun fara zuba akan idonta,

Baki bude ya kalleta dama a banza ma tana yin kuka inaga yanzu da dalili ya samu,

"Kiyi hakuri binti kinji, nine ko? Yi hakuri"

Hadata yayi da jikinsa yafara rarrashinta har ya samu ta daina hawayen, hanmunta ya kama ya zaunar da ita akan wani dan karamin stool yaje yafara gyara mata gadon, kallonshi kawai take yanda yake da sanyin nan to komai ma nashi a sanyaye yake gudanarwa dan haka ya zame mata dole ta nemo mafita duk da tasan ba ita kadai bace mai irin wannan matsalar ba mata da dama suna fuskantarta,

Hannun nata ya sake kamawa ya rakata kan gadon ta kwanta, agefenta ya zauna ya fara jan yan yatsun kafarta, da haka ya ware ya fara yi mata tausa ajikinta, kamar wacce take jira sai bacci, zama yayi yana kallonta acikin ranshi yana tunanin irin banbancin dake tsakaninta da ummu domin yagane akwai banbance banbance masu tarin yawa bawai kasancewarta budurwa kawai ba ko a ta fannin ni'ima ni'imarta tasha banban data ummu, kodan ita bahijjan tana shan kayan marmari ne da sauran abubuwan datake hadawa da kanta,

Haka yayita yan tunane tunanensa yana zaune yana kallonta, drewar din gefen gadonshi ya bude yafara bincike har ya binciko abinda yake nema, wani dan kyakkyawan zobe ne na gold mai kyau, dan yatsanta na hagu ya kamata ya saka mata zoben, ya kwanta agefenta yana makale da hannunta,

Sun jima suna baccin kafin jabir ya tashi yana kallon bahijja wacce keta faman baccinta tana fitar da numfashi ahankali, ahankali yafara kokarin zare hannunsa daga cikin nata, yana gama zarewa ta tashi firgigit,sai kuma tafara kallonsu shida ita, sunkuyar da kanta tayi tana kallon kayan jikinta,

"Abbu kagani kayanka sunyi min yawa ko"

Murmushi jabir yayi ya matsa kusa da ita "amma ai sunyi miki kyau binti"

Kallonshi tayi tana tuna wani abu acikin ranta wanda ita kadai tasan ko me take tunawa,

"Abbu yunwa nakeji" tafada tana turo baki,

"Zakici abinci yanzun nan binti, ai nasan bakya wasa da abinci shiyasa kike da karfi sosai kusan ma kinfini karfin"

"Haba abbu wanne karfi nafika? Tayaya kasan haka alhalin nida ba dambe muka yi dakai ba"

Sakin hannunta yayi yana murmushi tare da kokarin sauka daga kan gadon yana cewa "dambe na nawa kuma binti"

Falo ya fita ya shigo mata da kayan Karin kumallon da ya shirya mata shida kansa, akasa ya ajiye mata ya kamota ya sauko da ita,

Kazar jiya taga ya dumama mata sannan ya soya mata kwai ya dan soya mata dankali da plantain, sai ruwan tea, "yau zanci girkin maza kenan" tafada aranta,

Dankalin taci da plantain din tasha tea ta tashi tana mik'a, "abbu natafi dakina sai ka taho"

Kafin ya dago yayi mata magana har takai bakin kofa hakan ya sashi yin shiru, fita tayi ta koma dakinta tana zuwa tafada gado ta janyo katuwar teddy dinta ta rungume sai alokacin duk abubuwan da suka wakana tsakaninta da jabir suka fara dawo mata, idanuwanta ta lumshe tana jin wani irin farin ciki har cikin ranta, tana nan kwance har jabir ya shigo kunnensa makale da waya yana magana amma daga yanda ta fuskanta da al'amin yake wayar domin ta jiyoshi yana cewa

"Al'amin antyn naka ai sai kayi mata sannu saboda bata dan jin dadi"

Wayar ya mika mata yana shirin zama akusa da ita gamida zare teddy din dake makale ajikinta,

"Ni ni nidai lafiya ta kalau" tafada tana turo baki, dan yatsan da ya saka mata zobe ya kamo yafara ja yana cewa "yanzu ni zaki rinka rungumewa ba teddy ba binti, wayar ta kara a kunnenta tafara magana,

"Al'amin, yakake?"

"Anty fine" yanda yayi maganar sai taji tamkar mahaifinsa, sama sama ta biyeshi suka danyi shirmensu da suka saba amma yau bata bari sunyi nisa ba saboda wani iri takeji ajikinta sannan gashi gabanta sai faman faduwa yake yi,

"Abbu bazaka fita bane office?" Ta tambayeshi bayan ta ajiye wayar,

"Yau ina gidan nan tare dake binti, ko bakya son in zauna natafi?"

Kanta ta kwantar ajikin kafadarsa, "inaso mana abbu amma tunda natashi nake jin gabana yana faduwa"

"Kina yin wasa da addu'a binti, bakya son yin addu'a"

"Abbu wlh inayi"

Kafin ya sake yin magana wayarta tafara kara, cikin hanzari ta daukota tana duba sunan wanda yake kiran.









_*Ummi Shatu*_🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [10/11, 11:33 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*

  *_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*



_106-110_



~~~Sunan yayarta anty Bilkisu ta gani, cikin hanzari ta kara wayar akunnenta jikinta har rawa yake yi, suna gaisawa yayar tata take sanar da ita cewar suna asibiti an kwantar da ma,

Cikin rawar baki ta tambayeta wanne asibiti ne, tana fada mata ta ajiye wayar tana hawaye, janta jikinshi jabir yayi yafara shafar bayanta yana tambayarta,

"Binti waye bashida lafiya?"

Cikin kuka tace "ma ce"

Hawayen dake sauka akan fuskarta ya soma share mata amma yana jin tausayinta ga wata irin zazzafar soyayyarta har acikin jinin jikinsa zuwa bargonsa, yasan yanzu dole ta shiga damuwa saboda fushin mahaifiyarta da zata fuskanta,

" kukan ya isa haka binti, kiyi shiru kinji, ko bakya son nabarki kije?"

Kai ta girgiza cikin kuka tayi magana "ina so"

"To kiyi shiru ki shirya muje"

Idonta har lokacin taf da kwalla take kallonsa "abbu jikina ciwo yake yimin gashi duk yayi tsami"

"Am sorry binti, ki daure kinji"

Ahankali ta janye jikinta daga nashi ta tashi taje gaban drewar din kayanta ta bude, wata blue din doguwar riga ta zaro ta jiyo tana kallonsa ya gane abinda take nufi, ganin yana zaune yana kallonta yasata fita taje dayan bedroom din ta sako rigar ta dawo, binta yayi da murmushi agaskiya bahijja akwai shirme in banda haka to maganar boye boye kuma ai takare a tsakaninsu,

K'aton hijabi ta saka kalar ruwan madara duk wadannan abubuwan tana yinsune kamar kazar da kwai ya fashewa aciki domin sam yau bata da kuzari dakyar take motsa jikinta,

Mikewa yayi yaja hannunta suka fita zuwa sashensa, afalo ta zauna taki binshi cikin dakin, tana nan zaune ya fito cikin farin boyel da hula ga wani mayen kamshi da yake tashi daga jikinsa wanda yake barazanar tarwatsa numfashinta,

"Tashi muje" shine kawai abinda ya fada, tashi tayi tabi bayansa suka fita har suka karasa tsakar gidan bata yi magana ba tana biye dashi yana kiran driver,

Abaya dukkaninsu suka zauna driver yaja motar suka bar harabar gidan suka nufi Nakowa clinic, jikinta jabir ya matsa ya kamo yan yatsunta ya fara murza zoben da ya sanya mata,

"Binti bakiga kyautar da na bakiba shine babu ko godiya?" Yayi hakane domin ya dan sanyaya mata zuciyarta, aikuwa murmushin yak'e tayi tana kallon kyakkyawar fuskarsa,

"Ni kyautar da nabaka godiyar kayi min?" Tafada cikeda kunya,

"Wacce kyauta kika bani binti?" Ya tambayeta yana ware idanuwansa akan fuskarta,

"Nima namanta tunda kaima ka manta" tace dashi tana tutturo bakinta,

"Idan baki daina turo min bakin nan ba idan na kamashi sai kin fadawa yan garinku"

"Abbu okene kenan, kasan mu canne garinmu" tafada tana murmushi,

Jin alamun tsayawar motar ya dawo dasu cikin hayyacinsu sai alokacin suka san sun karaso asibitin, hakika haka ya kamata kowanne miji ya kasance ya rinka mantar da matarsa duk wani bacin rai ta hanyar maye gurbin bakin cikinta da farin ciki amma wani maimakon haka saima kara mata bacin ran zaiyi.

Hannunta ya kama suka fita suka tasamma cikin asibitin, tun daga nesa ta hango papa da yayarta suna tsattsaye duk hankulansu atashe,

Jin jikinta tayi ya sake yin sanyi, koda suka karasa wurinsu kasa magana tayi sai jabir ne yafara tambayar halin da ma din take ciki da kuma abinda ya faru,

"Tun jiya da mangariba muke nan amma har yanzu bata farfado ba, yanke jiki tayi ta fadi sakamakon jin muna maganar musuluntar da bahijja tayi nida Bilkisu, ashe lokacin ta dawo gidan daga church tana ji ta kwalla kara ta zube awurin, yanzu doctor yace zuciyarta bugawa tayi watakila ma sai sunyi mata aiki"

Babansu ya fada cikeda alhini, fuskarsa dauke da damuwa,

"Allah yabata lafiya, Allah ya tashi kafadunta" jabir yafada yana mai jin tausayinsu, ita kam bahijja tana daga tsaye tana faman hawaye,

Anty Bilkisu ce ta taso tazo inda take ta kama hannunta taje ta zaunar da ita akan dogon bencin da aka tanada awurin domin masu zaman jinya, baki suka fara bata dukkaninsu har ta samu ta daina kukan da take yi,

Suna nan zaune suna jiran tsammani domin kosu bilkisun da suka kwana awurinta basu samu ganinta ba balle bahijja da tazo yanzu, amma ga doctor nan da sauran nurses sunata kai kawo zuwa dakin da ma din take kwance aciki.

Har azahar jabir yana asibitin sai wurin karfe biyu narana sannan yatafi da niyyar zai dawo anjima, suna fita shida driver yaje cikin gari ya bayar aka karbo abinci awani restaurant yabayar aka kai musu bayan driver ya ajiyeshi agida, shi yau kwata kwata ma baici abinci ba tunda ya tashi da safe dama zama da yunwa sabonshi ne domin a office haka yake wuni har yamma baici komai ba shiyasa yake yawan yin azumi,

Kasancewar duk suna cikin damuwa babu wanda ya samu damar cin abincin da aka kai musu, suna nan zaune sunyi jungum jungum dr yafito yace musu ta farfado zasu iya shiga su ganta,

Tashi sukayi da hanzari dukkaninsu suka fada dakin da ma take ciki suna shiga suka sameta kwance idanuwanta abude tana kallon kofa, tana ganin bahijja ta mayar da idonta ta rufe ruf tana mai jin wani irin daci acikin ranta,

Duk wanda yayi mata sannu tana daga masa kai amma koda bahijja tayi mata sai taki kulawa, nan hankalin bahijja ya tashi dama wannan ranar ta yau ta dade tana jin tsoron zuwanta saboda tasan ma zata tsaneta zata kyamaceta uwa uba zata raba hanya da ita,

Wuri suka samu suka zazzauna acikin dakin har la'asar tayi lokacin jabir ya dawo asibitin suna dakin ya shiga ya samesu, wani kololon bakin cikine ya ziyarci ma, aranta tana tunanin yanzu shikenan wannan yaron yayi nasara akanta ya musuluntar da bahijja duk da dadewar da tayi tana dorata akan addinin kiristanci, runtse idanuwanta tayi saboda bata son ganin fuskarsa ko kadan,

Kwata kwata taki amsa sannun da jabir yake yi mata, gaban papa ya karasa ya dan russuna ya zaro kudi daga cikin aljihunsa rafa daya ya bashi domin yin hidimar siyan magunguna sannan ga kaya iri iri da driver ya fara shigowa dasu irin wadanda marar lafiya zai bukata,

Godiya da addu'a jabir yashata agun papa ga albarka da yayita saka masa da addu'ar Allah ya bashi yara nagari, duk da nauyin da yakeji sai da ya amsa da amin yana kallon bahijja kasa kasa, itama dago idonta tayi ta kalleshi tana mai jin mamakin amin din da yace.

K'arfe 10:30 babansu yace tabi mijinta su tafi shida Bilkisu ne zasu zauna a asibitin inyaso gobe ta dawo da safe, bata so hakanba amma haka tafita duk ranta a hargitsi domin ta shiga damuwa sakamakon ganin fushin da ma take yi da ita,

Tun acikin mota jabir ya fara rarrashinta saboda shima ya fuskanci akwai matsala, akan cinyarshi ta kwantar da kanta tana hawaye amma bata bari ya sani ba, kanta ya soma shafawa yana cewa

"Me kike sha'awar ci muje in siya miki?"

Girgiza kai tayi alamun babu komai "to ai naga kema baki ci abincin ba kodai sai nayi miki dura idan munje gida?"

Kafada ta mak'e tana girgiza kanta.

Suna zuwa gida sashenta ta wuce taje tayi wanka tasaka kayan bacci amma har lokacin ranta babu dadi, wayarta ce tafara kara tana dubawa taga jabir ne yake kiranta,

Asanyaye ta daga wayar, "binti me kikeyi ne najiki shiru?"

"Abbu kabarni na kwana adakina yau" tafada idanuwanta cikeda kwalwa,

"To zan barki amma kafin kiyi baccin kizo ki karbi wani abu"

Kashe wayar tayi ta tashi tafita ta nufi part dinsa, acikin bedroom dinshi ta sameshi zaune shima da kayan baccin ajikinsa yana gauraya wani abu acikin Kofi, kusa dashi ta karasa ta zauna,

"Gani abbu"

"Naganki ai binti, zauna mana nagama"

Cup din ya kai saitin bakinta,"ungo sha malt ne da peak saboda naga baki ci abinci ba, jibi har kinyi kashin wuya yau kadai"

Hannunshi yakai yafara shafar wuyanta yana kallon fuskarta, bude baki tayi ta runtse ido takama cup din tafara shan maltina din, kadan ta rage aciki,

"Wannan kuma ni kika barwa?"

Yafada kanshi akasa dagowar da zaiyi yaganta tana kokarin yin kuka,

"Wai wannan kukan na menene?" Yace da ita bayan ya dauketa cak ya dorata kan cinyarsa,

"Abbu ma tana fushi dani ko amsa sannun da nayi mata bata yi ba" kukane ya subuce mata, rasa yanda zaiyi mata yayi hakan ya sanyashi kwantar da ita agefen gadon yashiga jikinta yasa dan mitsitsin bakinshi cikin nata yafara shan bakinta.

Yajima yana yi mata wasu abubuwa na kwantar da hankali kafin ya kwantar da ita akan jikinsa ya dora kanta asaman kirjinsa yana shafar gadon bayanta ahankali,

"Kinyi wanka da ruwan dumi kuwa?" Ya tambayeta yana kissing din hannunta,

"Abbu nayi amma har yanzu dai banji daidai ba"

"Sorry kinji, zaki warware"

Hannunshi ta makale acikin nata tana matsawa,

"Abbu ma ko kallona yau batayi ba"

Gashin kanta yafara shafawa,

"Babu komai binti insha Allah wata rana zata gane gaskiya itama, ko baki da labarin kissar annabi ibrahim wanda mahaifinsa ya kasance mai bautar gumaka, alhalin shi kuma yana matsayin annabin Allah"

Sake shigewa cikin jikinsa tayi tana kara kankameshi sosai kamar wanda take tsoron yatafi ya barta,

"Haka Allah yake ikonsa abbu,shi annabi ibrahim gashi annabin Allah amma kuma mahaifinsa yana karyata abinda yazo dashi"

Dan yatsanta yafara murzawa cikin nashi,

"Kuma kinga har tallar gumaka mahaifinsa yake bashi amma bai taba bujirewa umarninsa ba, haka yake dauka yatafi tallen gashi kuma gunkin da ake sassakawa agidansu annabi ibrahim yafi na kowanne gida kyau, kullum yiwa mahaifinsa nasiha yake kan kar ya biyewa shaidan yana bautar wanin Allah,kuma daidai da rana daya bai taba sabawa umarnin mahaifinsa ba domin su iyaye ko wanne irine wajibi ne ayi musu biyaya,duk nasihar da annabi ibrahim yayiwa mahaifinsa bai saurareshi ba, kinsan mutum baya shiryar da wani, shiriya ta Allah ce"

Juyi tayi atsakiyar jikinsa takai hannunta daya ta shafo fuskarsa,

"Abbu bacci, kaci gaba da bani labarin idan kaji shiru kuma shikenan nayi bacci"

Sunbatar goshinta yayi yana murmushi, "ai kuwa ba za ayi haka ba, nima gara kawai nayi shirun tunda na fuskanci wayo kike kokarin yimin"

"A'a abbu bafa wayo bane"

Kanta yaci gaba da shafawa yana bata labarin har bacci ya dauketa, rungumeta yayi sosai acikin jikinsa yana tuno lokuta da dama wadanda suka kasance atare.

Washe gari da sassafe ta tashi ta shirya abin karyawa harda wanda zata kai asibiti, tare suka tafi da jabir sai da ya shiga ya duba jikin ma sannan yayi musu sallama ya wuce office, yauma kamar jiya ma bata kulata ba har lokacin tafiyarta yayi tatafi, ahaka har sai da akayi sati daya lokacin har sauki yafara samuwa awurin ma amma sam taki kula bahijja domin ko gaisuwarta bata amsawa,

Arana ta bakwai ce ma ta tsigaleta tatas tace kuma ko mutuwa tayi bata yarda taje inda gawarta take ba sannan ba ita ba ita har duniya ta tashi,

Da kuka bahijja tafita taje ta zauna awata runfa taci gaba da kukanta, anty bilkisu ce ta biyota tazo tafara bata baki tana cewa tayi hakuri sannan ta kara da cewa

"Karki saka damuwa acikin ranki domin ba ason mace mai juna biyu ta rinka damuwa hakan zai iya shafar har abinda ke cikin cikinta"

Murmushi tayi wanda bata shirya yinsa ba saboda jin maganar anty Bilkisu,

"Tab ni tunda naje gidanma sau daya akayi wani abu" tafada acikin zuciyarta ashe afili tayi maganar batare data saniba, cikin takaici anty bilkisu ta kalleta,

"Ashe dama duk abubuwan dana dade ina sanar miki baya shiga kunnuwanki,ke kuwa me kika zauna yi? Me kika tsinana agidan? Sau daya? Amma wlh kin bani kunya, banyi zaton sakalcinki da asarancinki yakai haka ba"

Hawayen idonta ta goge ta kalli anty bilkisu "to anty ya zanyi? Shi abbu ayanda na fahinceshi bashida yawan bukatar mace"

Girgiza kai anty bilkisu tayi cikeda bacin rai, "shine ke kuma kika barshi ahaka? Bari kiji ya kamata ki tashi atsaye ki bawa mijinki gudunmawa da kulawa ta musamman, bai kamata ki zuba masa ido kice wai har sai lokacin da yaji bukatarki ya nemeki ba, yanzu wannan ba shine wayewaba, akwai dabaru da salo wanda ya kamata ki koya musamman ma yanzu da kika fuskanci mijinki ko wanne irine, dama maza masu sanyin nan ai haka suke basuda yawan bukatar mace gasu da saurin biyan bukatarsu, dan haka wlh kece ya kamata ki zauna ku fuskanci juna ki gyarashi, ta hanyar yi masa kwalliya mai daukar hankali da sauran abubuwan da zasu jawo miki ra'ayinsa gareki, sannan ina son ki riki ruwan zafi domin duk macen da take amfani da ruwan zafi to tana dauke da wata ni'ima ta musamman, asalima ruwan sanyi bashida wani amfani ajikin ya mace, ita mace anfi son koda wanne lokaci ta kasance cikin dumi shiyasa yin lalle na asali yake da amfani domin shi yafi komai dawowa da mace dumin jikinta sannan kuma yana kewayawa har cikin jinin jikinta yana wanke mata kwayoyin cuta musamman ma cutukan dake cikin mara, idan kina son ki gane haka to ki gwada yin lalle ki kwana dashi, da safe idan kinje yin fitsari ki kula sosai zaki ga fitsarin ya sauya kala yayi kalar lallen sannan kuma har warin lallen zakiji fitsarin yanayi"

Kai ta daga tana kallon anty bilkisu wacce ta dage tana koro mata bayani,

"Ni anty duk banida bukatar wadannan kawai nidai burina abbu ya sauya daga wannan sanyin nashi, wlh yanda kika ganshin nan yana tafiya ahankali to acanma hakan yakeyi"

"To kin San ya zakiyi? Gaskiya zama zakuyi kuyi magana ku fuskanci juna keda shi, wannan ba matsalar da zakiyi shiru bace domin kanki zaki cuta,kedai kawai ki tabbatar kina gyara jikinki, ki yawaita shan kanumfari domin yana gyara mace kuma yana hana fitsarinta yin zarni, duk macen datake amfani da kanumfari to zaka ji tana wani kamshi har fitsarinta kamshin kanumfarin zakaji yana yi, haka kuma shan kunun alkama da zuma da madara yana gyarawa mace jikinta sosai da sosai sannan yana saukar mata da wasu sinadirai ajikinta, shi kansa shan ruwan zafi wani abune mai mutukar amfani ajikin mace daga mace har namiji anfi son susha ruwan zafi lokacin da zasu gudanar da mu'amular auratayya"

"Nagode Anty, insha Allahu zan kiyaye, amma ni kunshin zan gwada yi nagani"

"Hakan yanada kyau sister ki gwada kiga"

Suna nan zaune suna tattaunawa har la'asar tayi lis,  5 jabir yazo asibitin, shima dakyar ma ta iya amsa gaisuwarsa amma daga nan bata kara yi masa magana,

Awaje papa ya tare bahijja yayi mata nasiha ya bata hakuri akan abinda mamanta take yimata yanzu, sai da ya kwantar mata da hankali sannan suka tafi gida ita da jabir.

Duk da tana tsoron halin da ta tsinci kanta aciki a hannun abbu rannan hakan bai hanata shirya kanta awannan daren  ba domin wanka ta silla ta caba ado tasha wata rikitacciyar rigar bacci ruwan toka mai mutukar santsi, gaban rigar abude yake hakama bayanta, turarruka masu dadi tabi jikinta dasu ta shafa ta dauki kamshi tako ina, kwalliyar da tayiwa fuskarta kuwa tamkar mai shirin zuwa dinner,

Afalo ta iske jabir yana zaune yana waya da matarsa, ganin shigowar bahijja yasashi yaji ya fara rudewa, hannu ya mika mata yaci gaba da yin wayar, ahankali cikin tafiyar jan hankali ta karasa jikinsa ta zauna tana murmushi,

Sinsinar jikinta yafara yi yana shakar kamshin jikinta, sallama yayiwa ummu al'amin ya kashe wayar yana yiwa bahijja wani irin kallo na musamman,

"Muje ki kwanta ko binti" yafada cikin muryarsa wacce taji tasake yin sanyi,

"Abbu tun yanzu?" Tafada tana kada masa idanuwanta,

"Ehhh, zo muje"tashi yayi yaja hannunta suka shiga cikin dakin nasa,

Yauma kamar rannan babu canji hakan yasata niyyar zama dashi domin su fuskanci juna kamar yadda yayarta tabata shawara, wannan shine abinda ummu al'amin takasa tabarshi acikin ranta gashi har yau bata samu waraka ba.

Kwanan ma 10 a asibiti aka sallameta bayan dr ya dorata akan magani wanda zata runka sha domin samin sauki,

Kayansu suka harhada suka tafi gida koda sukaje gidanma ma taki sakin fuska musamman ma ga bahijja sai dai harara take aika mata amma baya ga haka taki cemata komai, har bayan sallar isha suna gidan itada yayarta,

Jabirne yazo daukarta yayi mata waya yace tafito su tafi, sallama tayiwa ma amma ko kallonta bata yiba hakan yasata fita duk ranta babu dadi, atsakar gida ta iske papa cikin faran faran suka yi sallama fita inda jabir ke jiranta, yau shi kadai ne ko driver baizo dashi ba, yayi wanka yasha t shirt da jeans yayi kyau sosai kamar bashi ba,

Zama tayi akujerar dake gefensa tana kallonsa cikeda so, "abbu wannan kyaun fa?"

Hannunta ya kama yana murmushi, "daga zance nake shiyasa"

Ido ta tsura masa tana kallon dan mitsitsin bakinshi,

"Abbu zansha chocolate"

"Banida chocolate acikin motar nan sai dai agida"

"Da akwai abbu" ta bashi amsa tana mai matsawa jikinsa,

"To dauki a inda kika ganta" yafada yana murmushi, ahankali takai bakinta kan nashi tahada,

"Ga chocolate nan awurinka kuma sai kace min babu"

Girgiza kai yayi "Allah yabaki hakuri ai ban san wannan kike nufi ba"

"Shi nake nufi abbu, ai yafi chocholate ma dadi"

Kallonta yayi da manyan idanuwansa, "dagaske?"

"Um dagaske mana, sai dai abbu meyasa baka jimawa...?" Sai kuma tayi shiru bata karasa ba,

"Bana jimawa ame?"

Ya tambayeta yana matso da ita jikinsa,

"Abbu baka da zafine gashi kuma bukatarka bata da yawa, shine nace ko akwai matsala ne?" Tafada tareda rufe fuskarta,sai yanzu ya gano inda bayanin nata ya dosa, murmushi yayi,

"Eh akwai matsala amma ai akwai hanyoyin gyarawa, bari muje gida akwai wani littafi da wani shehun malami ya rubuta domin warware irin wannan matsalar, kinga kenan sai ki daura damarar kawo sauyi duk da nidai babu wata matsala, ahakan nan da kika ganni to wlh banida damuwa, amma tunda ke jarababbiya ce sai ingyara saboda ke" ya karasa maganar cikeda zolaya,

"Abbu nice jarababbiyar? Menayi na jaraba?" Ta tambayeshi,

"Binti wasa nake yi miki ai koni banida damuwa to yana da kyau naduba naga ke wanne irin yanayi kike ciki saboda gudun kada na cutar dake domin annabi Muhammad yace gamsar da juna yana daga cikin tushen aure, bai yiyuwa narinka barinki acikin damuwa nikuma alhalin na nishadantu domin a tsarin halitta ta bil'adama mace tafi namiji karfin sha'awa, sha'awar mace ta ninka ta namiji kinga kuwa indai hakane to mata da dama suna cikin wani hali domin suna fuskantar matsala ata fuskar rayuwar auratayya, amma dai bari muje gida"

Dan murmushi tayi batace komai ba har ya tashi motar suka harba titi, hannunta guda daya ya kamo ya rike, cikin gari suka shiga domin yana son ya dan yimata siyayyar kayan makulashe,

Tunda suka shiga ta wuraren da mutane suke suka fara ganin mabarata da almajirai jere atiti suna bara sai kace ba dare ba, wurin da yake ajiye kudi ya bude ya zaro yan ishirin ishirin ya dora mata kudin akan hannunta,

"Ungo binti rinka mika musu sadaka"

Kallonsa tayi tafara mika musu ta gilashin motar,

"Allah yabaka lada abbu"

"Amin amma ba sadakata bace takice binti domin yana da kyau ki yawaita yin sadaka"

Juyowa tayi ta kalleshi bayan ta gama mimmikawa almajiran sadakar,

"Saboda kasancewata bakuwa acikin addinin musulunci?"

Murmushi yayi ya lakuto hancinta "kar kiyi min fassarar abinda bashi nake nufiba, ai sadaka akan kowa abune mai kyau domin annabi ya kwadaitar damu cewa mu kare kanmu daga wuta koda da tsagin dabino ne ta hanyar bayar dashi sadaka, kuma bayan haka ma ai ku mata annabi ya ce ku yawaita bayar da sadaka acikin hadisin da aka karbo daga abdullahi dan mas'ud Allah ya kara masa yarda cewar manzon Allah (S. A. W) yace: _yaku taron mata, ku yawaita bayar da sadaka, domin mafi yawanku yan wutane, sai wata mata tace meyasa mukafi yawa awuta? Sai annabi yace saboda kuna yawaita la'anta sannan kuna kafurcewa abokan zamanku"_ jin haka sai matan dake wurin suka fara ciccire dan kunnayensu da awarwaronsu da abun hannunsu suna hadawa domin abayar da sadakar."

Cigaba da kallonsa bahijja tayi tana jin wani karfin imani yana shigarta har acikin ranta,

"Lallai abbu indai hakane kam amma mata muna cikin fargaba, duk da cewa adunkule kabani hadisin ba awarware ba, kace muna yawaita la'anta sannan kuma muna kafurcewa abokan zama, to kamar yaya?"

Hannunta ya ajiye akan cinyarshi yakarya kan motar suka dauki titin da zai sadasu da _Batool suya spot and soft drinks_,

"Ehh binti yawancin mata gaskiya kunada yawan maganganu marassa dadi, mafi yawa daga cikinku zaginku yafi salatinku yawa, ina nufin wata sai kasamu tayi zagi sau hamsin arana amma batayiwa annabi salati koda sau daya ba, abu kadan sai zagi idan yaro yayi ba daidai ba zagi idan tana yin wani abu ta samu kuskure zagi, idan yan wuta suka dauke zagi,komai zagi,a maimakon zagin nan gara kuna yin addu'a domin annabi yace _addu'a'uh huwa ibadahu, hakika addu'a ita ibada ce_, sannan kuma ku mata agaskiya kuna da manta alkairi dayawa daga cikinku bakwa godewa mazajenku, wata zaka samu mijinta kullum yana kyautata mata amma rana daya idan yayi mata kuskure sai kiji tace me kataba yimin? Ta manta duk alherin da yayi mata abaya, sannan wata kuma miji zai hanata abu amma bazata hanuba sai tayi to irin wadannan abubuwan da kuke ganinsu kamar kanana ne to sune suke kaiku wuta shiyasa annabi yace ku yawaita bayar da sadaka saboda ko lokacin da annabi yaje isra'i da mi'iraji da aka nuna masa wuta mata yagani cike aciki ana yi musu nau'o'in azaba iri iri alokacin hankalin annabi ya tashi sosai har yake tambayar mala'ika jibrilu wanne laifi wadannan matan suka yi ake yimusu irin wannan azaba haka"

Cinyarshi ta kankame wanda sanadiyyar hakan tasa jabir sakin sitiyarin motar dakyar ya iya saita kan motar ya taka burki domin sun karaso wurin da za suyi siyayyar,

"Binti ya kike nema ki sa muyi accident?"

Fuska ta shagwabe, "abbu na tsorata ne da abinda naji ka fada dan Allah ka sanar dani laifukan da matan nan suka aikata domin nima kar nashiga sahunsu, ka fadamin dan na kiyaye"

Hannuwansa yasa ya tallafi kumatunta yana kallon kwayar idonta wanda yake hango tsantsar kaunarshi da soyayyarshi aciki, hakika ya dade da sanin bahijja tana sonsa so nagaskiya kuma shima yanzu yana jinta acikin ranshi irin jin da bai taba ji ba akan wata mace,

"Insha Allahu binti bakya daga cikin irin wadannan matan amma kibari nadawo zan sanar dake irin laifin da wasu daga cikinsu suka yi har Allah yasakasu acikin azabarsa"

Asanyaye ta shafa hannunshi dake ajiye akan kumatumta, wani kiss ya ajiye mata akan goshinta ya saketa ya fita, bayanshi tabi da kallo tana faman murmushi yau dinnan yayi kyau over cikin farar t shirt din dake jikinsa mai dogon hannu da bakin trouser hadadde,

Fresh milk ya siyo musu roba biyu da gasasshiyar kaza sai kankana da tufa da manyan chocolate guda biyar, motar ya dawo ya zauna ya dorawa bahijja kayan akan cinyarta yana yi mata wani hatsabibin kallo wanda shi kadai yasan fassararshi,

Motar yayiwa key yafara tuki ahankali domin wanda yake tafiya ahankali ma zai iya zuwa ya wucesu,

Chocolate daya ta dauka ta bare ta gutsiri rabi ta mikawa jabir rabin ta hanyar kai masa ita kusa da bakinshi, juyowa yayi ya kalleta bayan ya bude dan karamin bakinshi,

"Wai abbu tayaya spoon yake shiga wannan bakin naka ne?" Ta tambayeshi tana saka masa chocolate din acikin bakinsa,

"Kina son in baki amsa? To ta yanda bakinki yake shiga cikin nawa"

Murmushi tayi tana jin wani farin ciki acikin zuciyarta,

"Kina jina binti? Acikin wutar jahannama annabi yace yaga wasu mataye suna kuka suna bakin ciki suna kira ba amsa musu ba sannan suna kaskantar da kai ba a gafarta musu ba, sai ya tambayi su wanene? Sai mala'ika jibrilu yace masa sune masu yin ado ba dan mazajensu ba, sannan yaga wasu mata akansu akwai wanduna na wuta awuyansu kuma akwai sarkoki da mari mari na wuta sukuma sune masu wulakanta mazajensu wacce dayarsu tana cewa mijinta mummuna mai wari mai mummunar fuska, sannan yaga wasu mata fuskokinsu sun kone harshensu sun zazzago akan kirjinsu sukuma sune masu cewa mazajensu kasakeni batare da wani dalili ba,

Sannan yaga wadansu mataye wanda aka ratayesu da gashinsu kwakwalwarsu tana tafarfasa kamar yadda tukwanen karfe suke tafasa akan wuta sune wadanda basa rufe gashinsu ga mazajen da ba muharramansu ba, sannan yaga wasu mataye an shafe jikinsu kuma yayi baki kamar kwalta sukuma sune masu runa gashin Kansu kuma suke sauya halittar Allah,

Haka kuma yaga wasu mataye an dauresu da gashinsu a jikin bishiyar zakuum ana kwara ruwan zafi akansu sai namansu ta kone daya tambayeshi suwanene sai mala'ika jibrilu yace sune matan da suke shan magani har sai sun kashe yayan dake cikinsu saboda tsoron ciyar dasu da shayar dasu da tufatar dasu,

Agaskiya mata kuna aikata laifuka daban daban shiyasa kukafi maza yawa acikin wuta amma indai kuji tsoron Allah kun tuba to Allah mai yawan gafara ne kuma yana karbar tuban bayinsa mutukar bawan bai kai gargarar mutuwa ba, Allah yagafarta mana gaba dayanmu"

Hannunsa ta rike tana shirin yin kwalla "abbu shanfon nan da nakeyi shima haramun ne?"

Kai ya girgiza mata "ai shi adone, ita kuma mace an yarje mata dukkanin kayan ado kawai dai abinda ya haramta shine wurin yin shanfon ba aso wacce ba musulma ba taga gashinki amma indai wurin yar uwarki musulma kikaje bakiyi laifi ba duk da cewa wasu malaman suna ganin shi kansa yin shanfon haramun ne amma wasu kuma sun bada fatawar cewar ya halatta to koma dai menene sabanin malamai rahama ne"

Kanta ta kwantar agefen kafardarsa ta rirrike dantsen hannunshi da hannunta, bata iya kara cewa komai ba har suka kusa zuwa gida amma har lokacin tana makale dashi.

K'arfe 10 da mintuna suka shiga gida, part dinsa suka wuce tahada musu abinda zasu ci na kayan da suka shigo dashi suna cin abinci yana bata abaki har suka kammala, fresh milk dinma shine ya shayar da ita, bahijja uwar son jiki ajikinsa ta rabu ta ishisshire har suka gama suka koma kan fruit nanma shine ya yanyanka ya rinka saka mata abaki har taji ta koshi,

Tashi tayi taje dakinta ta debo kayan baccinta ta dawo wurinshi,

"Abbu anan yauma zanyi wanka" tace dashi tareda zama ajikinshi,

"To binti idanma wankan ni kike so inyi miki ai sai nayi miki"

Dariya ta saka tana make kafada "a'a nidai dakaina zanyi"

Tashi tayi ta shige cikin dakinsa tashiga wanka, bata jimaba ta fito ta shirya tasaka rigar baccinta ta haye gadonshi ta kwanta tana jiran shigowarsa,

Ta dan jima da kwanciya kafin ya shigo, kayan jikinsa ya rage ya shiga wanka duk tana kallonsa, bayan ya gama shiryawa ne yafara binciko littafin da yayi mata maganarsa dazu, dakyar ya samoshi domin tun lokacin da yake saurayi ya ajiye littafin bai sake budashi ba har yayi aure sai yau zai karantashi ta sanadiyyar binti kuma littafin yanada mutukar amfani domin marubucin littafin yayi kokari sosai wurin kawo matsalolin da ma'aurata suke fuskanta fuskar rayuwar auratayya domin matsalar mu'amular aure ba matsalace wadda mace zata ja bakinta tayi shiru ba, daga mace har namiji duk wanda baya samun gamsuwa daga wurin dan uwansa to dole arinka samun matsala komai dadin zama kuwa, shiyasa yana dakyau azauna afuskanci juna ba abin kunya bane dan mace bata samun biyan bukatar ta fadawa mijinta, domin idan tayi shiru ma kanta zata zalunta domin bata da wani wanda zai iya yimata wani abu bayaga mijinta amma saboda dayawa daga cikin mata bamuda wayewa tafuskar mu'amular aure shiyasa muke samun matsala da mazajenmu kuma kashi 50 a cikin dari na Ma'aurata kawai suna rayuwar aurene amma ba wai dan ana jin dadin rayuwar ba saboda kwata kwata kowa baya samun gamsuwa domin tun asali bamu san irin kulawar da namiji yake bukata ba, bamu san wanne abune namiji yafi so ba, bamu san wanne yanayi yakamata mu kasance tare dashi ba,shiyasa muka taso cikin rashin wayewa aharkar rayuwar auratayya gashi ko aure muka tashi yi babu Wanda zai iya zaunar da yarinya yayi mata huduba akan yadda zata kula da mijinta shiyasa ake yawan samun matsala agidan auren,

Littafin ya dauka mai taken guzurin amare da yanmata ya nufi inda bahijja ke kwance tana kallonsa, akusa da ita ya zauna yafara yi mata magana kasa kasa.

"Binti kitashi muyi karatun"

Juyi tayi tadora kanta akan cinyarsa,"abbu kayi ahaka ai inaji"

Pillow yaja yatasa jikinsa dashi sannan ya bude littafin yafara karanto mata yana fassarawa;

"Babi nafarko, yana da kyau ga ma'aurata su kasance sunyi amfani da madara ko wani abu wanda yake kara sinadari ajiki kafin suyi yunkurin kasancewa da juna, yin wanka,brush da shaving da amfani da abu mai kamshi shima yana taimakawa asamu kyakkyawar mu'amula, baya kyautuwa azowa juna cikin datti ko rashin tsafta haka yakamata ace kowanne lokaci ana rage gashin jiki domin hakan yana taimakawa kwarai, sannan kuma yayin gudanar da wannan mu'amular anfi son asamu wuri mai mutukar dumi, idan ma da wata na'ura mai fitar da sanyi kamar air condition ko fanka to duk akashesu,haka kuma anfi son koda ace ruwa mutum zai sha awannan lokacin to yasha ruwan zafi ba nasanyi ba,

Sai matsalar da yawancin Ma'aurata suke fuskanta ta fuskar rayuwar aure akwai da yawa daga cikin maza wadanda rayuwar auren bata damesu ba wasu kuma zaka samu koda ace suna kula matan to basa daukar lokaci atare dasu hakan zaisa matan su cutu domin kamar an tabosu ne kuma sai aka kyalesu, to wannan babbar matsalace kuma yawanci rashin kwanciyar hankali shike haifar da irin wannan ko kuma idan mutum baya samun hutu kullum yana cikin zirga zirga ko aikin office kodai wani abu wanda ya ke hanashi zama ya huta to irin wannan baya barin miji ya iya bawa matarsa kyakkyawar kulawar da take bukata, idan hakan ya faru to yana dakyau ma'aurata su gudanar da wasanni sosai ta hanyar yiwa junansu wasu abubuwa wadanda zasuji kamar zasu biya bukatarsu,to alokacin sai su gabatar da rayuwar aure,

Akwai kuma dayawa acikin maza masu fama da karancin sinadari ajikinsu to ke uwar gida sai kiyi kokari wurin hada lemo wanda zakiyi amfani da kankana Zuma, madara, kwakwa,tufa da dabino, idan ana yawan shan irin wadannan abubuwan to za asamu wadataccen abunda ake bukata, koda kuwa ita matarce take fama da karancin to itama zata iya shan wannan abun ko kuma ta samu zogale ta rinka sha da madara amma kuma arinka kwantar da hankali ana rage damuwa domin damuwa tana daukewa mace ni'imarta, kuma idan mace tana cikin fushi ko mijin yana cikin fushi to idan akayi mu'amular aure alokacin ba lallaine a iya biyawa juna bukata ba,

Abu nagaba shine idan mace ta kasance itama bata samun biyan bukatarta dalilin mijin yanada saurin biyan bukatar kansa, to duk dai hanyar dayace shine a tabbatar anyi wasanni sosai da juna sannan kuma idan shi mijin baya yawan bukatarki to ke ba zama zakiyi har sai ranar da ya nemeki ba kamata yayi ki zauna ki gyara jikinki kiyi duk wata kwalliya wacce kika san zata dauki hankalinsa sannan kuma ki kasance kullum atare dashi ako wanne lokaci"

Littafin ya rufe ya sunkuya yana leka idanuwanta wadanda ta rufesu kamar me bacci,

"Nasan ba bacci kikeyi ba binti" yafada yana shafar gashin kanta,

"Abbu har safiya tayine?" Tafada tana mika,

"A'a mantawa kikayi, azahar ce tayi, nasan duk kinji abinda nafada, oya dagani naje nayi alwala nazo na kwanta"

Tashi tayi tana mutsuttsuka idonta ita alalle mai yin bacci bata ji abinda yafada ba, kallonta yayi yana murmushi amma har azuciyarsa bai ga laifinta ba akan sanar masa abinda ke ranta da tayi domin zaman aure zamane na fuskantar juna,

Bathroom ya shiga ya yi alwala ya fito yadawo inda take zaune tana jiran fitowarsa,

"Abbu kullum baka bacci har sai ka dauro alwala"

Akusa da ita ya zauna tareda jawota jikinsa ya rungumeta,

"Binti yin alwala kafin kwanciya bacci abune mai mutukar muhimmanci domin tana bawa mutum kariya har gari ya waye, kema kinayi kinji ?",yafada tareda shafa kanta, jikinta ta janye ta tashi,

"Abbu bari naje nayi yanzu" sauka tayi daga kan gadon ta shiga toilet tayi alwala tafito ta dawo wurinshi ta kwanta ajikinshi tana shafa masa ruwan dake hannunta afuskarsa,

"Bari mana binti ko baki san sanyi nakeji ba?"

Kiss ta kaiwa bakinsa tana dariya "abbu wannan bakin naka ina sonsa, nadade ina sonsa acikin raina"

"To gashi nan nabar miki shi yi duk abinda kike so dashi"

Saitin kanshi ta matsa tafara laluben bakin nashi.

***

Kullum tana hanyar zuwa gidan ma duk da cewar ma din ta warware amma har lokacin bata daina zuwaba, amma fa babu sakin fuska tsakaninta da ma domin ko ta gaisheta bata amsawa, kusan duk ranar da taje gidan da kuka take dawowa sai dai jabir ne zai zauna yayita rarrashinta da kalamai masu sanyi,

Yanzu kam tana jin dadin yanda jabir ya ware yake gudanar da al'amuransa cikin kuzari da hanzari duk da dai har yanzu ita bawai ta gama sabawa bane,

Kullum cikin kwalliya take gashi jabir ya kawo mata dunkuna kala 5 na atamfa da lesuka, yau dai kam ta shirya yimasa kwalliyar hausawa domin kullum cikin kananan kaya yake ganinta,

Bayan kammala aikin gida da tayi, wanka tayi ta shirya tayi kwalliya sosai jan bakine eye shadow, jagira, mascara duk sai da tasakasu a fuskarta, wata jar atamfa mai adon koren ganye ajiki ta dauko tasaka, dinkin riga da skirt ne, daram kayan suka zauna ajikinta nan kyakkyawar kirarta ta bayyana das, dan kwali ta daura tayishi kamar fanka ta feshe jikinta da turare,

Fitowarta tayi daidai da dawowar jabir gidan, fita tayi tatafi wurinshi domin yi masa welcome,

Yana fitowa daga mota tana karasowa, tsayawa yayi ya zuba mata ido saboda ba karamin kyau tayi ba,

"Ranka ya dade ina za asaka maka wannan kayan" yajiyo muryar mal idi driver yana yi masa magana, juyawa yayi yaganshi hannunshi rike da files masu yawa wadanda ya taho dasu gida domin gudanar da aiki, kafin yayi magana bahijja har tazo zata giftashi tana cewa,

"Mal idi mikosu nan"

Cikin sauri jabir ya rikota yasata acikin jikinshi yafara rufeta da babbar rigarshi,

"Mal idi kaimin su kofar falo ka ajiye za ashiga dasu" yace dashi gamida jan bahijja suka nufi sashenta, ta kofar baya yabi dasu sai alokacin ya budeta daga lullubar da yayi mata da babbar rigarshi,

Dago kanta yayi daga cikin kirjinshi yana kallonta "binti waye yasaki kifito haka ana kallemin ke?" Ya tambayeta yana dora dan yatsanshi daya akan lips dinta,

"Abbu sannu da zuwa fa naje yi maka"

"To karki kara bakya ganin cewar bani kadai bane?"

Kallonshi tayi da mamaki "abbu shifa mal idi ko yaganni ba wani abu bane"

Kallon jikinta yayi duk hips dinta da kirjinta sun bayyana cikin kayan data saka domin sun fito radau,

"Waye yafada miki? Allah cewa yayi kar ki bayyanar da adonki ga kowa sai ni sai ko wanda yake muharraminki"

"To abbu bazan sakeba"

Jan hannunta yayi har lokacin tana rabe ajikinsa yayi part dinsa da ita.

    _Gaisuwa mai yawa gareku Hawy na & AG tawa ni daya._


*_Ummi Shatu_*🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [10/15, 2:21 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*

  _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

_111-115_


        _Sak'on gaisuwa gareki Batool Mamman masoyiyar wani haske, na gaisheki sosai_



~~~A tsakiyar falonshi sukayi burki, kallo sosai jabir yake binta dashi saboda ba karamin kyau tayi ba gashi sai kamshine mai dadi yake tashi daga jikinta,

Kafadunta ya dafa yana yi mata murmushi na musamman,

"Binti kinyi kyau sosai.." Yafada yana sinsinar wuyanta,

"Abbu nagode, kaima kayi kyau din ai"

Rike hannuwanshi tayi tana faman sunkuyar da kanta, "binti menene hakan? Me hakan yake nufi?"

Dagowa tayi ta kalleshi, "abbu muje kayi wanka"

Hannunshi tafara ja tana tafiya, binta yayi har cikin bedroom dinshi, hularshi ta cire ta nufi drewar domin adanawa, tana ajiyewa ta dawo inda yake tafara kokarin cire masa babbar rigar jikinshi, yana tsaye yana aikin kallonta duk wani motsinta akan idonshi ne har ta gama cire masa kayan ta barshi dagashi sai farar vest da gajeren wando blue,

"Bari nazuba maka ruwan wankan abbu"

Binta yayi har cikin toilet din tana hada masa ruwan yana ta bayanta atsaye sai da ta kammala cika wani katon baho da ruwa sannan ta jiyo gareshi,

"Abbu gashi" tana gama fada tafara kokarin fita, hannunta ya riko da tausassan hannunshi,

"Kar ki tafi binti, ki tsaya ki karasa ladanki"

Hannunta tafara kokarin zamewa daga nashi tana mammake kafadarta, cikin shagwaba tafara magana,

"Nidai abbu nayi wanka na dazu, dan Allah ka bar min kwalliyata kar ka bata min"

Janta yayi da karfi yayi mata masauki acikin kirjinshi "tsaya kiji bintina, kawo kunnenki nafada miki wani abu"

"Nidai a'a, abbu wlh kazama marar hakuri yanzu, gaskiya gobe kayi azumi"

"Babu azumin da zanyi, kuma ai kece kika sani nazama marar hakurin"

Daukarta yayi cak ya ajiyeta cikin bahon wankan.

Daukota yayi ya ajiyeta agefen gado yana yi mata dariya "binti da kikace bakya so, ashe dama gulma ce kinma fini so"

Fuskarta ta rufe da tafin hannunta,"abbu kabari ko inyi maka kuka"

Murmushi yayi yaje ya dauko lotion yazo inda take "yi hakuri kar kiyi pls"

Ajiyar zuciya ta saki daidai lokacin da yafara warware towel din jikinta domin shafa mata mai,

Agurguje ya shiryata shima ya shirya dama yanzu tanada kaya ajiyayyu acikin dakinsa kusan ma duk abubuwan da zata bukata ta ajiyesu adakin,

Hannunta yakama zuwa falo domin saura kadan lokacin sallar mangarib yayi, sai alokacin suka tuna da files din dake ajiye akofar falon

"Binti kina sani ina mantuwa fa" yafada yana jan hancinta,

Hannunshi ta rike "nidai kar ka dora min laifi abbu"

Tana manne ajikinsa sukaje suka dauko files din suka shigo dashi, zama tayi akan cinyarsa tareda kwantar da kanta ajikin kirjinsa,

"Zaki barni na iya yin aikin nan kuwa? Yace da ita yana shafar kanta,

"Zan barka mana abbu"

"To dagani naje masallaci nadawo" kiss tayi masa akan kumatunsa kafin ta dagashi tana kallonsa, masallaci ya fita ita kuma ta koma sashenta, sai da yayi har sallar isha sannan ya dawo gidan nan ya iske bahijja ta sake caba ado tasha kwalliya sosai cikin leshi yellow mai stones ajiki,

Zama tayi ajikinsa suka fara mikawa junansu sakonnin soyayya masu nauyin gaske, sun dade suna nunawa junansu soyayya kafin su hau dining table suka ciyar da junansu,

Falo suka dawo jabir yafara ayyukansa amma kuma duk hankalinsa yana kan bahijja motsi kadan sai ya kalleta dakyar ya samu ya duba files guda biyar daga nan ya rufe babin aikin ya bude babin soyayya shida bintinsa.

      Misalin karfe 10 suna kwance adakinshi yana rike da hannunta yana da wasa dashi ya fara tambayarta akan littafin da yafara koyar da ita na akdari,

"Menene farkon abinda ke wajaba akan baligi?"

Juyi tayi akan kirjinshi kafin ta bashi amsa "farkon abinda yake wajaba akan baligi shine ya inganta imaninsa sannan yasan da wanne abune zai gyara farillan ainihinsa dashi"

Sake tambayarta yayi "kamar da wanne abune zai inganta farillan ainihinsa dashi?"

"Abbu kamar hukunce hukuncen sallah, dana tsarki, dana azumi"

Sake rungumeta yayi yana yimata sumba akan goshinta, "yarinya ashe kina gane karatun da nake dora miki, wannan hukunce hukunce ya wajaba akan dukkan baligi ya sansu kuma yayi aiki dasu domin kowacce ibada ana son mutum yasan hukunce hukuncen da suka shafeta kafin ya gabatar da ita, misali salla, ana son baligi yasan abubuwan da suke warwareta da wadanda suke gyarata kamar kabli da ba'adi, hakama tsarki, azumi shima yakamata baligi yasan abubuwan da suke batashi da kuma abunda mai azumi ya kamata ya nisanta domin akwai abubuwa da dama da suke warware azumi wadanda bamu daukesu a matsayin manyan laifuffuka ba kamar giba yi da wani, kazafi da karya"

"Abbu menene giba?" Ta tambayeshi tana dago kanta domin kallon fuskarsa,

"Binti baki san giba ba? Giba itace gulma, zancen wani, annamimanci, fadin abu marar kyau ga wani wanda baya nan amma annabi ya siffatanta giba da cin naman mutum domin wani lokaci suna zaune da sahabbai sai yace dasu _"shin dayanku yana iya cin naman dan uwansa? Sai sahabbai sukace tayaya dayanmu zai ci naman dan uwansa ya rasulillah? Sai annabi yace duk wanda yayi zancen dan uwansa baya nan yafadi mummunan abu akansa yaci mutuncinsa to kamar yana yankan naman jikinsa yana cine"_,kinga kuwa indai hakane ya zama dole mu rinka kame harshenmu domin shine yafi komai hatsari atattare damu shiyasa alokacin sahabbai akwai sahabin da yake zuba duwatsu acikin bakinsa saboda kar yafadi wata magana wacce ta kaucewa shari'a,shiyasa sai kiga sahabi yayi kwana uku baiyi magana ba yana ta juya maganar acikin zuciyarshi yana tunanin shin ya fadeta ko yayi shiru, akwai wania sahabi wanda ya nemida annabi yayi masa nasiha sai annabi ya zaro harshensa ya nuna masa yace kaji tsoron wannan domin yana halakarwa,amma mu ya muke ayanzu? Bamu dauki gulma da annamimanci amatsayin laifi ba gashi mun iya cin mutuncin junanmu bayan kuma acikin wani hadisi annabi yace _"'duk wanda yaci mutuncin dan uwansa to Allah zaici mutuncin fuskarsa da wuta aranar alqiyama"'_ bafa wai dan uwa najini ba a'a dan uwa musulmi domin musulmi dan uwan musulmi ne haka annabi yafada, shiyasa yana da kyau mutane su rinka sauraron malamai saboda su gane illar gulma da annamimanci da k'azafi domin dukkaninsu laifuka ne masu nauyin gaske shi kansa mai yin annamimancin ma annabi cewa yayi _"'La yadkulil jannatu nammamun, wato annamimi bazai shiga aljannaba"'_ wannan hadisin daga wurin huzaifa dan yamani aka karbo shi,bukhari da muslim kuma suka rawaitoshi"
"Abbu Allah ya rabamu da sharrin harshe"

"Amin binti, kina jin bacci ko wata hirar za muyi?"

Idanuwanta ta rufe da tafin hanunta "abbu sai kanata sani ina jin kunya"

Murmushi yayi ya zare hannun nata daga fuskarta, "hakanma da lada binti domin kunya wani yanki ne daga cikin yanki na imani"

"To nidai bacci zanyi kayi min addu'a"

"To shikenan Allah ya kaimu gobe da asuba sai kiyi biyan bashi"

Shiru tayi tai lakwas ajikinsa yafara karanto mata addu'o'in kwanciya bacci yana tofa mata ajikinta.

  Washe gari da safe bayan ya shirya domin zuwa office ya riko hannun bahijja wacce tasha gayu cikin farar atamfarta mai zanen hannu ajiki,

"Binti ki hada min kayana anjima zanyi tafiya, zanje Kaduna wani conference"

Yatsunshi ta riko ta makalkaleshi,

"Abbu tare zamu tafi ko?"

Kai ya girgiza mata "a'a batare zamuje ba, ai kinga hotel ne bazan iya zuwa dake hotel ba, kiyi hakuri kinji kwana 3 kawai zanyi"

Daru tasa masa tafara doddoka kafafunta akasa tana kuka kamar wata yar karamar yarinya,

"Nidai abbu sai nabika, kuma shikenan ni kadai zaka bari, nidai bazan yarda ba, tare zamu tafi" tana fada tana kuka, kallo kawai yake binta dashi dama haka ya guda shiyasa yaki sanar mata da maganar tafiyar tun jiya saboda yasan zaisha rikici da shagwaba iri iri,

Binta yayi inda take tsaye ta juya masa baya tana kuka, ahankali ya rungumeta ta baya yafara kissing din wuyanta, juyo da ita yayi ya zubawa fuskarta ido, kuka take yi sosai kamar wacce aka yiwa mutuwa,

"Kiyi shiru binti, kwana ukune fa"

Idonta ta runtse wasu sabbin hawayen suka sake iyo ambaliya akan Kumatunta,

"Dan Allah abbu kar ka tafi ka barni"

Rungumeta ya sakeyi ajikinsa "to binti, shikenan amma dai ki hada min kayan bari naje office nadawo, ba lallai ne ma nayi tafiyar ba amma dai kihada min kayan kinji"

Kai ta daga masa tafara share hawayen kan fuskarta, dakyar ya iya rarrashinta ta tsaida kukan sannan ta rakashi tsakar gida tadawo tafara hada mishi kayan nan dinma tanayi tana hawaye har ta kammala.

Karfe 3 nayamma ya dawo gidan lokacin tana sashenta tana gyara style din dayan bedroom dinta tana canja salon jeren cikin dakin domin abune mai kyau uwar gida ta rinka sauyawa dakinta fasalin jerensa daga lokaci zuwa lokaci,

Ahankali ya sadada yaje inda take tsaye da pillow ahannunta tana gyarashi acikin rigarsa, ta bayanta ya tsaya yakai hannu ya toshe mata baki,

Mutsu mutsu ta fara yi tana ihun da ba a ji, kokawa take yi iya karfinta tana kokarin kwatar jikinta sai kuma tafara jin kamshin turarensa ahankali yana ziyartar hancinta,

Sakinta yayi yana yi mata dariya,

"Ke matsoraciya ce binti"

Kallonsa tayi sai kawai ta dauki pillow tafara kai masa duka

"Abbu kayi mugun bani tsoro wlh, nazata gardine ya shigo min gidan"

"Yi hakuri bintina, babu wanda ya shigo miki, nine nan"

Dukan ya shiga karewa da hannunsa har yayi nasarar kwace pillow din yajata ya hadata da jikinsa ya rungume,

"Abbu zakayi tafiyar ko ka fasa?"

"Binti kibari kibani abinci naci mana tukunna"

Hannunshi takama suka tasamma part dinshi inda ta shirya masa abinci mai rai da motsi, white rice with stew sai hadin salad,

Suna ci tana yi masa hira har suka kammala, zancen tafiyarshi ya fara yi mata anan tasake tayar masa da wani darun, kuka ta saka masa,

Janta yayi jikinsa yafara lashe fuskarta yana shanye hawayen da take yi, wata irin zazzafar soyayya yashiga nuna mata dolenta tayi shiru ta daina kukan,

Daukarta yayi yakaita cikin dakinshi ya ajiyeta akan tangamemen gadonshi yashiga nuna mata so.

Ajikinshi ya kwantar da ita yafara yi mata tausa adukkan bangarorin jikinta,iska yafara hura mata acikin kunnenta yana yimata kalamai masu dadi dan haka lokaci kankani bacci yayi awon gaba da ita.

Kwantar da ita yayi yatashi ahankali ya nufi toilet yayi wanka ya fito, cikin sauri sauri yayi shirinsa yasaka kayanshi ya debi dukkan muhimman abubuwanshi ya karasa Inda take kwance rungume da pillow ita ala dole shi ta rungume, sunkuyawa yayi ya kai bakinshi kan nata yayi mata kiss, yasake yi mata wani agoshinta sannan kumatunta sai nakarshe a tsakiyar kirjinta,

Jakarshi ya dauka yafita domin ya kusa makara saboda jirgin 4:30 zaibi zuwa Kaduna yanzu kuma gashi 4 harda yan mintuna ga baiyi salla ba.

Yana tafe yana waiwayenta har yafice daga cikin dakin, sai da ya tsaya a masallaci yayi salla sannan driver ya tafi kaishi airport, gaba daya jinsa yake yi babu dadi saboda zai tafi yabar bintinshi wacce yanzu yana jinta acikin ransa fiyeda yanda yake jin kanshi,kamar ya kirata awaya sai kuma ya rabuda ita yaga gwanda ya barta har sai ya sauka agarin Kaduna tukunna.

   Bahijja kuwa tunda jabir yatafi yabarta take ta bacci kamar wacce jabir ya durawa maganin bacci, ba ita ta iya tashi ba sai wurin karfe 5:30, ahankali tafara bude idonta, ganinta tayi rungume da pillow amadadin jabir, ahankali ta tashi zaune sai kuma ta shagwabe fuska tafara kuka tana kiran

"Abbu...!"  Ta kira sunanshi cikin shagwaba da kuka,

"Abbu...!" Jin shiru bai amsaba yasata tashi ta jawo towel dinshi ta daura ta leka cikin bathroom amma wayam baya ciki,

Fitowa tayi tana tafiya tana kuka tana kiransa, falo ta duba nanma baya nan, dakinshi ta sake dawowa ganin babu jakar data hada masa kayan tafiyarshi ya tabbatar mata da wayo yayi mata yai tafiyarsa,

Da kukanta ta shiga toilet tayi wanka tafito gashi ko salla bata yiba gashi jabir yau ya tara mata gajiya ba kadanba gashi baya nan, daurewa tayi ta daina kukan ta shirya tayi salla ta zauna tafara tasbihi har 6 tayi, alokacin taji kiran jabir awayarta,

Daukar wayar tayi bayan tafara kuka "abbu...!"

Jin muryarta ya tabbatar wa da jabir kuka take yi,

"Binti kukanne har yanzu baki daina ba?"

"Abbu shine ka tafi ka barni, kayi min wayo kasani bacci kafin natashi ka gudu"

  Dan sansanyan murmushi jabir yayi yana mai tuno kyakkyawar fuskarta da dukkan kyakkyawar surarta wacce take tsumashi acikin kowanne irin yanayi,

"Ba gudu nayi na barki ba binti na, kiyi hakuri kinji, ba dadewa fa zanyi ba"

"Nidai bazan hakura ba sai dai idan ba zaka sake tafiya ka barni ba"

  Kiss yayi mata ta cikin wayar "bazan sake ba binti wannan ma dan babu yanda zanyi ne amma bazan sakeba,i promised you my binti, ga sako nan naturo miki"

Murmushin itama tayi ta fara mayar masa da martanin kiss din da yayi mata,

"Binti kiyi hakuri ki bari haka kar kisa nakasa bacci"

Fuskarta tasoma gogewa sannan ahankali ta furta "abbu dan Allah kar ka kalli yanmata"

Dariya tasashi yi batare da ya shirya ba "binti ni ina ma zanga yanmata? Ina daki babu inda zanje daga daki sai ko dakin taron da zamu gudanar da conference din, ki kwantar da hankalinki kinji, daga ke babu kari kece yar auta awurina"

Tamkar yayi mata bishara da gidan aljanna haka taji, "abbu to yaushe zaka dawo?"

"Haba binti anyita nanata magana dayane? 3 days zanyi babu yawa"

Rufe idonta tayi tana tunanin yau ko a ina zata kwana,

"To abbu Allah ya kaimu"

"Amin binti, anjima zan kiraki kinji"

Kashe wayar tayi tana tunaninshi acikin zuciyarta.

Daren ranar bata iya bacci ba dakinta taje ta kwanta amma tunanin abbunta ya dameta, zaune ta tashi ta zubawa kan gadon ido tana nazari,

tattarawa tayi takoma dakin jabir ta kwanta amma kuma sam ta kasa baccin da zarar ta rufe idonta babu abinda take gani sai yanayin da suke kasancewa tare ako wanne lokacin bacci,idan kuma ta bude idonta sai ta rinka ganin kamar zata ganshi ne,

Daukar wayarta tayi tasoma laluben wayar jabir amma fuskarta sharkaf take da hawaye ohh bahijja irin wannan kuka haka sai kace pherty,

Jabir na daukar wayar yaji shasshekar kukanta "abbu nakasa bacci"

"Yi hakuri binti, kiyi alwala kiyi sallar nafila kinji, ko kin fara hutu?"

"Kai abbu yaushe nafara hutun naga dazuma kafin katafi kasan ina salla"

Murmushi yayi "ai tambayace binti, nasani ko nadace kwallona ya shiga raga"

"Kai abbu" tafada cikeda kunya,

"Ke binti" ya kwaikwayi maganarta, hakan da yayi ne yabata dariya,

Dariya take yi tana kyakyatawa kamar ba itace take kuka yanzu ba,

"Abbu ai al'amin ya ishemu"

"A'a binti al'amin dan ummu ne kema ki daure ki dage ki samu ki haifi naki,ko bakya son ki haifi mai kama da ni? Nafi son kema ki haihu ki zama mama"

Hannunta tasa ta toshe bakinta tana murmushi, cikin dabara ya samu ya rabata da damuwar da ta shiga, sun dade suna hira har tafara gyangyadi, addu'ar bacci yayi mata ta shafa ta kwanta taci gaba dayin wayar dashi yana bata labari mai dadi, shirun da yajine ya tabbatar masa da cewar tayi bacci, wayar ya kashe yana murmushi.

Kullum suna makale awaya dashi har yayi kwana ukun, aranar da zai dawo taje gidan kitso aka yarfo mata kananan kitso masu kyau harda wanda aka zubo mata shi gaban goshinta aka tufke mata shi,

Rasa inda zata saka kanta tayi dan tsananin murna, alla alla takeyi kawai ya dawo ta ganshi saboda tayi missing dinshi ba kadan ba.

  Karfe 2:30 ya sauka amma baije gida ba office yawuce tunda ya sanar da ita saukarsa taji kamar tayi tsuntsuwa taje ta daukoshi, jin yatafi office yasata kasa hakuri har saida ta aika masa da lafiyayyen girkin da tayi masa. Sai da yasha aiki a office har 5 tayi sannan ya tashi ya nufi gida,

Yana zuwa gidan sashen bahijja yafara shiga amma ko ina ya duba bata nan dan haka ya fita ya nufi nasa sashen, tunda ya shiga falon yake shakar kamshi mai dadi yana tashi afalon,

Jakarshi ya ajiye ya tasamma cikin bedroom dinshi, abin mamaki nanma bata ciki juyawa yayi zai fita amma aranshi yana tunanin to ina bahijja ta tafi, jinta yayi dalaf ta daleshi tana murna,

"Oyoyo abbuna"

Makaleta yayi ya nufi gaban mirror ya tsaya yana hangota ta cikin mudubin, wata kwalliya tasha tayi kyau sosai tayi kwalliya sosai cikin yar bingilar pink din rigarta da bakin wando matsattse,

Birkitota yayi yafara kallon kitson kanta yana shafashi,

"Waye yayi miki wannan kitson? Yayi kyau"

"Nagode abbu, agidan kitsone can baya"

"To zan bada tukwici yanzun nan"

Bata ankaraba taji yayi sama da ita bai direta ako inaba sai akan makeken gadonshi.

Basu iya barin junansu ba sai daf da sallar magrib, daukarta yayi zuwa bathroom yayi mata wanka yayi mata alwala ya dawo da ita cikin dakin, ita dai duk kunya ta gama rufeta,

"Daga dawowa ko gaisawa ba muyi ba kika rikitani da soyayyarki" yafada cikin tsokana yana kokarin daura mata towel,

"Ayya abbu ai laifinka ne ba nawa ba" rufe fuskarta tayi bayan tagama maganar,

"Nagode miki sosai kuma naji dadi Allah ya yi miki albarka binti"

"Amin abbu, nagode"

Shiryawa yayi agurguje ya saka jallabiya kalar ruwan toka ya tafi masallaci bayan ya shiryata itama.

Haka rayuwa taci gaba da kasance musu cikin farin ciki da annashuwa gashi kullum cikin kyautatawa junansu suke, ita dai bahijja bata da damuwar komai sai ta mahaifiyarta domin kullum abin sake tabarbarewa yake babu sauki saima gaba da yakeyi, duk lokacin da taje gidan bata samun sakin fuska awurin ma sai ko wurin mahaifinta.

   Cikin wannan yanayine jabir yayi musu shirin zuwa madina domin suyi umarah sannan su ziyarci su ummu al'amin saboda rabonsa dasu yanzu ankusa shekara saura yan watanni,

Lokacin da bahijja taji wannan albishir din ba karamin murna tayi ba anan suka shiga yin shirin tafiya bayan duk abinda zasu bukata natafiya ya kammalu, sai da suka je suka yiwa dukkan wand yacancanta sallama sannan suka daga kowannensu zuciyarsa dauke da murna musamman ma bahijja.

Acikin jirgi ajikin jabir ta lafe ta makaleshi gam tana muzurai sai aikin hararar wata mata take yi wacce ke gefen jabir azaune tana satar kallonshi,

"Abbu jiyo da fuskarka nan" tafada gamida saka hannunta ta jiyo da fuskarshi zuwa kusa da tata,

"Menene binti?" Ya tambayeta yana dora idanuwansa kan nata,

"Gani nayine sai kallonka ake tayi kai kadai sai kace babu wani namiji anan sai kai daya" tafadi hakan cikeda kishi,

"Binti dadina dake kishi, kinada kishi sosai tun kafin kisan abinda ake yiwa kishin,bare yanzu da kika sani"

Idonta ta sauke ta kwantar da kanta akan kafadarshi tana murmushi, hirarsu suka ci gaba dayi har Allah ya saukesu acikin madina,

Lokacin da suka fito suka hango al'amin da ummunshi tsaye suna jiran isowarsu, kallon kallo aka fara yi tun daga nesa tsakanin ummu da bahijja,

Hannunta rike cikin na jabir tasha bakar doguwar Arabian gown sannan ta yane kanta da bakin mayafin rigar, ba karamin kyau ta sake yi ba,

Ita dinma bahijjan shigar da ummun tayi take kallo domin bakar doguwar riga irinta larabawa tasaka da dan karamin hijab, hannunta rikeda na al'amin, ko ba a fadawa Ummu ba tasan bahijja ta musulunta domin ta tabbatar da ace bata musulunta ba to da babu abinda zai saka jabir yazo da ita,

Ahankali suke tafiya har suka karasa inda su ummu ke tsaye, da gudu al'amin ya fusge yaje ya rungume bahijja yana murna, ita dinma rungumeshi tayi ta dagashi ta saba akafadarta duk kuwa da cewar yanzu ya dan kara girma,

Dukkaninsu daga ummun har jabir tsayawa suka yi suna kallon al'amin da bahijja saboda yadda suka manta dasu sai dariya suke yi suna kara rungume juna,

"Anty ashe dama kema zaki zo? Anty kema kina salla yanzu ko?"

Al'amin ya tambayeta yana rungumeta,

"Ehh al'amin, me kakeci hakane naga ka sake zama kato?"

"Anty shinkafa kaza kema idan kina so ummu na zata dafa miki ta iya sosai"

Dariya tayi ta saukeshi kasa,"ohh al'amin ashe har yanzu dai kana nan da labarin nan ko?"

"Kuzo mu karasa gidan tukunna" muryar ummu ta katsesu kafin al'amin yabada amsa, tare suka jera suka nufi wurin da zasu samu taxi suhau,

Ganin yanda ummu ta shige jikin jabir tana yi masa rada suna dariya yasanya bahijja jin wani kololon bakin ciki yataho ya tokareta akirji, ita kam badai zafin kishiba musamman ma akan jabir,

Suna tsaye abakin titi tana rike da al'amin da yar trolley dinta tana kallon yanda jabir yasakala hannunshi tabayan ummu ya karata jikinshi sai rade rade suke yi suna dariya, duk ji tayi tsayuwar ta isheta alla alla take su samu taxi su isa gida dan ta daina ganin wannan abun haushin,

Sun dade atsaye kafin suka samu taxi, jabir ne ya shiga gaba sukuma suna baya azaune har lokacin al'amin yana manne da ita,

Tafiyar da batafi ta mintuna 20 bace takaisu kofar gidan da ummu take, nan suka firfito ita dai bahijja kallon garin kawai take tabbas wannan gari mai ni'ima ne domin iskar dake kadawa ma aciki daban take da sauran iskar dake kadawa aduniya, jabir ne ya biya mai taxi din sannan suka dunguma zuwa cikin gidan,

A falo suka yada zango inda ummu ta shisshirya musu kayan tarba kala kala, abincin larabawa tayi musu iri iri wani kuma ta siyo musu a restaurant,

Bin dan madaidaicin gidan bahijja take yi da kallo aranta tana tunanin gaskiya indai mutum yana zaune awannan wurin babu abinda zai dameshi shiyasa ummu da al'amin sukayi fes dasu gashi al'amin larabci abakinsa kamar sudais,

Abincin ummu ta fara zuzzuba musu, tana cewa,

"Antyn al'amin anzo lafiya? Ya mutanen gida?"

"Lafiya lau maman al'amin, kowa lafiya" bahijja tabata amsa tana gyarawa al'amin zama ajikinta,

Acikin babban faranti ummu ta zuba musu abincin dukkaninsu suka hadu suka fara ci ita dai bahijja duk jinta take atakure saboda yadda taga ummu sai rawar jiki take da ganin jabir, hakan yasata niyyar suna gama cin abincin nan zata nemi da anuna mata wurin zamanta domin ta tafi tabasu wuri,

Kallonsu take yi kasa kasa yanda ummu take manne dashi ta dora hannunta akan nashi tana wasa dashi gashi ko acikin kwanon abincin ma sai tsokanarshi take yi tana daukar spoon dinshi wai adole sai dai suci da spoon daya ita dashi,

Duk jin zaman tayi ya gundureta dan haka ta mike ta koma saman kujera ta zauna akujerar da tasan bazata cigaba da hangosu ba, al'amin ne ya biyota ya dale jikinta suka ci gaba da labarinsu.

Murmushi tayi takama hannuwan al'amin ta rirrike "al'amin kaga yanda ka zama kato kuwa? Sai kace irin kajin agric dinnan"

Dariya yayi yana jan mayafinta "hakama ummu na take cewa kullum"

Su jabir sun dade agaban kwanon abincin shida ummu suna dan taba soyayya,tashi jabir yayi yana kallon wurinda bahijja suke,

"Binti muje nakaiki masaukinki saboda ki samu kiyi wanka ki huta"

Yafada yana shafa sumar kanshi, kallonsa ta juyo tayi dama ta gaji da wannan zaman takurar dan haka batare da tace dashi komai ba ta tashi tana rike da hannun al'amin,

"Abu al'amin bari nazo muje mu kaita"

"To amma ki dan daukowa al'amin kayanshi koda guda 3 ne sai su zauna tare ya tayata hira" yafada yana kamo dayan hannun al'amin din,

"Al'amin ni bazaka kulani bane sai iya antynka zaka kula?"

Rungumeshi al'amin yayi yana cewa "abbu zan kulaka mana,ai tare zamuje da anty ko?"

Kafin jabir ya bashi amsa Ummu har tafito hannunta rikeda wata yar karamar jaka mai kyalkyali wacce ta zubowa al'amin kayansa aciki,

Dukkaninsu suka dunguma zuwa hotel din da za a kamawa bahijja daki domin gidan da ummu take ciki daki dayane sai falo da toilet da kitchen dama gidane na yan makaranta,

Wani hotel sukaje jabir ya biya kudin dakin ya karbi key suka dunguma zuwa dakin, sai da suka shigar dasu har ciki suka dudduba yanda tsarin dakin yake sannan suka yi musu sallama zasu tafi, ko jiyowa bahijja bata yi ba ayanda take ta juya musu baya tana ninke zanin gadon da suka samu acikin dakin domin shinfida nata,bata ko jiyoba tace su gaida gida domin bata ma son ta juya ta gansu saboda taga tun ahanya acikin mota suke wani shisshigewa junansu kamar wasu sabbin shiga,

"Abbu mu anan zamu kwana nida anty ko?"

"Ehh al'amin, bye bye ko"

Al'amin bai ko damuba saima daga musu hannu da yafara yana yi musu bye bye,

"Binti babu wani abu ko?"

"Babu" tafada atakaice, jan hannunshi ummu tayi suka fice daga cikin dakin suka tafi,zama bahijja tayi agefen gadon ta dafe goshinta kafin wani lokaci har hawaye sun fara sintiri akan kuncinta, al'amin ne yaje kusa da ita yana leka fuskarta,

"Anty bakida lafiya?"

Kai ta daga masa tayi sauri tafara share hawayen fuskarta, "idona ne yake ciwo al'amin"

"Sannu anty, ki fadawa abbuna ya kawo miki magani"

Kai ta sake daga masa amma bata kara magana ba domin ita kadai tasan yanda takeji acikin zuciyarta.

Dakyar ta iya tashi ta karasa gyara kan gadon ta tube ta shiga toilet tayi wanka amma acikin toilet dinma ta dan jima tana sharar hawaye sannan ta yi alwala tafito tadawo cikin dakin amma al'amin baya ciki, falo ta leka anan ta hangoshi ya kunna tv ya kwanta yana kallo,

Simple make up tayi tazira riga kalar ruwan madara marar nauyi doguwa tayi salla ta kwanta domin kanta ciwo taji yana yi mata saboda kukan da tayi,

Baccine yayi nasarar daukarta har lokacin sallar magrib yayi, sai alokacin ta iya tashi tana jin jikinta yana yi mata wani ciwo marar dadi ga kanta shima kamar zai fashe dan azaba.


  _Masu karatu mu hadu ashafi nagaba domin jin karshen labarin wani haske, nagode sosai da kulawarku_



*_Ummi A'isha_*🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [10/19, 4:35 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*

 

   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

_116-120_



~~~Ahankali cikin sanyin jiki ta sauko daga kan gadon tafara tafiya ahankali ta shiga bathroom, alwala tayi ta fito tana tafiya tana hada hanya saboda duhun da take gani agabanta sakamakon rufe mata idanuwanta da ciwon kan dake damunta yayi,

Azaune tayi sallar tana idarwa ta kwanta awurin tana rike da kanta saboda jinsa take kamar zai fice daga jikinta,

Al'amin ne ya shigo cikin dakin yana faman kwala mata kira,

"Anty zo muje muyi kallon tom and jerry...!"

Ganinta kwance tana hawaye yasashi yin shiru ya karasa kusa da ita,

"Anty har yanzu bakida lafiya?"

Kai ta daga masa sannan ta bude bakinta dakyar tace "al'amin anyi salla fa, ka bar kallon nan kaje kayi salla"

Hannunta ya kamo yana kallon "nayi sallar ai anty yanzun nan nadawo daga masallaci"

Zama yayi ra'as agabanta yana kallonta, "anty ki yiwa abbu na waya ya kawo miki magani"

Kasancewar bata son surutu yau yasata daga masa kai, wayar ta yaje ya dauko mata ya kawo mata sai alokacin ma tagane ashe kiran bazai yiyu ba,

"Al'amin bazan samu abbu awaya ba sai dai mubari har sai lokacin da ya gama abinda yake yi yazo"

Tana fadar maganar ne cikeda damuwa domin hawayene ke bin kumatunta,rike hannunta al'amin yayi yana girgizashi,

"Anty inyi miki addu'ar kamun kai?"

Kai ta daga masa, hannunsa yasa ya rike kan nata ya fara yi mata addu'a tana jinsa yayi bisimillah kafa uku sannan yafara karanto mata "As'alul lahil azim rabbil arshil azim an yashfiki" itama sau uku yana yi yana tofa mata a goshinta,

Babu laifi ta dan ji sausauci kam amma kuma ciwon da zuciyarta take yi mata ahalin yanzu ji take kamar tacireta ta yar,

Tana nan kawance al'amin akusa da ita suka fara jin bugun kofa, murna al'amin ya shiga yi "anty watakila abbuna ne yadawo"

Dagudu yaje ya bude kofa, ma'aikatan hotel din yagani masu bi daki daki suna raba abinci, nasu suka mika masa suka juya sukayi gaba,

Jikinsa asanyaye ya nufi wurin bahijja wacce duk tana jiyosu shida masu rabon abincin,

"Anty ba abbu bane, masu raba abincine"

"Al'amin ajiye abincin a falo bana son ganinshi,dama nasan ba abbu bane domin abbu bazai taba iya tunawa damu a wannan lokacin ba"

Tana maganar tana goge hawayen fuskarta, tashi tayi ta gabatar da sallar isha sannan tasake kwanciya a inda tayi sallar, kwanciyarta keda wuya wani naunauyan bacci yace muje zuwa,shi kansa al'amin shima baici abincin ba yana dawowa daga salla yayi kwanciyarsa a falo akan doguwar kujera.

Misalin karfe 2 nadare ta tashi daga naunauyan baccin da ya dauketa, bude idonta tayi tafara tuno jabir acikin kwakwalwarta, yanzu tasan yana can tare da ummu al'amin suna shan soyayyarsu,

Zaune ta tashi tayi tagumi tana karewa dakin da take ciki kallo, hakika kishi abune mai nauyin gaske wanda indai mutum baiyi takatsantsan ba zai iya halaka shi ta raya hakan acikin zuciyarta domin ita yanzu ji take ko kadan bata kaunar ganin fuskar jabir, haushinsa take ji sosai babu laifin tsaye babu na zaune,

Tana nan zaune tana karanta wasikar jaki zuciyarta ta shawarceta da taje tayi alwala tazo tayi salla ko dan koyi da jabir domin haka taga yana yi akowanne dare kai kusan ma baccinsa kullum ragagge ne bashida yawa, tsayuwar darensa tafi baccinsa yawa domin ko sunyi bacci tare to tsakiyar dare sai ya tashi yayi sallar nafilar da ta zame masa jiki,

Tashi tayi tafara bin jikin bango har ta shiga toilet din tayi alwala ta fito tazo kan abun salla, zata tada kabbara kenan taji motsi a falo, ahankali taje ta leka abun mamaki al'amin tagani shima yana tsaye yana sallar,

"Kyan da ya gaji ubansa" tafada ahankali gamida komawa cikin dakin tana tunanin babu ta inda al'amin yabar abbunshi a fannin dabi'u da halayya,

Salla tayi rak'a hudu domin kasala take ji ajikinta sosai, zama tayi tafara yiwa kanta da mijinta addu'a sannan tafara addu'ar Allah ya ganar da mahaifiyarta gaskiya itama tabi addinin da farin jakada masoyinmu na hakika annabi Muhammad yazo dashi.

Kan gado ta koma ta kwanta ta rungume pillow aranta tana tuna da agida ne da jabir zata rungume ba pillow ba amma yanzu gashi jabir dinma yayi mata wahalar gani balle har ta rabu jikinshi, shiru tayi tafara kiran sunayen Allah acikin zuciyarta amma yau tana ganin daren yayi mata tsawo da yawa ko dan bata tare da abin sonta ne, kasa komawa bacci tayi har asuba tayi ta tashi tai salla ta sake komawa ta kwanta. Har gari yayi haske idonta biyu, tana ganin al'amin yazo ya shiga toilet yayi wanka ya fito ya fara shafa mai ajikinsa,

"Inye ashe boy din nawa ya girma tunda yanzu ya iya wanka da kanshi" tafada tana kallonsa tana murmushi,

Juyowa yayi yana shafa mai akansa da fuskarsa "sabahul khair anty"

"Yau babu sch ne my boy?"

"Anty bama yin karatu ranar alhamis da juma'a, mu shine weekend dinmu"

Murmushi tayi tana kallonsa "hakan yayi kyau my boy, nima so nake natashi nayi wanka amma jikina duk a mace yake wallahi"

"Ki daure anty"

"To al'amin bari natashi" tafada tare da tashi ahankali ta shiga bathroom, bata wani jima ba tafito tana daure da towel, muryar al'amin ta jiyo daga falo yana cewa,

"Anty idan kin gama ga abinci an kawo"

"To al'amin" tafada tareda fara goge jikinta, mai ta dauko ta zauna agefen gado tafara shafawa,

Kamar a mafarki ta fara jiyo kamshin turaren gogan nata yana ziyartar hancinta ahankali ta daga kanta ta kalli kofar dakin,abbunta ta hango tsaye ya sha farar shadda riga da wando dinkin boda kansa ko hula babu ya zira hannayensa cikin aljihunsa,

Kicin kicin tayi da fuska ta bata rai, idonta ta dauke daga kallonshi ta mayar kan man shafawarta taci gaba da shafe jikinta dashi, ahankali ya tako ya karaso inda take yana murmushi,

Zama yayi agefenta daf da ita domin har tana jiyo jikinsa yana gogar nata, mai ta lukuto zata shafa yayi saurin rike hannunta,

"Haba binti yau ba zaki gaishe da abbun naki ba alhalin ba tare muka kwana ba, kawo na shafa miki man"

Batare da ta jiyo ta kalleshi ba ta bashi amsa "mantawa nayi, ashe fa ba tare muka kwana ba, ina kwana, mai kuma ka barmin kayana zan shafa"

Tunda tafara wannan bayanin ya zubawa fuskarta ido anan yagano kishi tsababa dankare akan fuskar tata hakan ya sashi yin murmushi,

"Binti me nayi mikine? Fushin nan naki na menene?"

"Ni me aka yimin da zanyi fushi? Ni babu wani fushi da nake yi"

Jikinta ya karasa shiga ya rungumeta, "idan ma wani laifin nayi miki to kiyi hakuri"

Man ya dauka ya fara shafa mata abayanta, bata yi magana ba har ya gama, yana jiyo da ita yaga kuka take, duk iya kokarinta na taga ta danne kishin dake azalzalar zuciyarta amma takasa dole sai da ya fahimta,

"Kiyi hakuri binti, jiya bakiyi bacci ba ko? Nima banyi baccin ba amma kiyi hakuri kinji, 3 weeks za muyi sai mu koma muci gaba da kwana tare, amma anan dinma gobe tare zamu kwana"

Da sauri ta kalleshi yana rike da hannunta yana kallon fuskarta, girgiza kai tayi

"Nidai indai nice na yafe ka zauna awurin ummun al'amin" azuciyarta kuwa tunani  indai haka ta faru amma da ta cika marar hakuri da kawaici,

"A'a binti karfa ki cuci kanki ki fadi gaskiyarki"

"Kaji abbun nan, da karya nafada?",ta fada tana zumburo masa baki, kiss yakai mata akan bakin nata ta zille tana dariya,

"Binti ba zaki bari in baki good morning massage ba?" Yafada yana dan miskilin murmushi kamarsa,

"Abbu naki wayon" ta fada tana make kafada,janta yayi zuwa jikinshi,

"Binti fada min gaskiya jiya kinyi barci?"

Kai ta daga "nayi mana, me zai hanani bacci abbu?"

Fuskarta ya dago yana kallon idanuwanta, "binti karfa ki koyi karya domin karya babban laifi ce indai mutum yana karya to bazai gushe ba har sai mala'iku sun rubuta sunansa acikin littafi na makaryata, haka kuma idan mutum shima yana kwatanta gaskiya to bazai gushe ba har sai mala'iku sun rubuta sunansa acikin masu gaskiya, daga ganin idon nan naki bakiyi bacci ba, kar ki boye min binti fada min gaskiya, kinyi bacci jiya?"

Kanta ta kwace ta sunkuyar dashi kasa ta girgiza kai "abbu kasawa nayi, ban san dalili ba"

Kumatunta ya dafa da hannuwanshi masu laushi,"ni nasan abinda ya hanaki binti, kishine, amma akwai mafita, ki rinka yawaita fadin la ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin, ba ke kadai ba duk wata mace da take jin zuciyarta acushe muddin ta riki wannan tasbihin da yardar Allah zata samu saukin damuwarta"

"Nagode abbu" tafada idonta fal da kwalla,

"To kukan ya isa haka kinji, maza kiyi shiru, yau ba zaki sha chocolate din taki ba?"

Ya tambayeta yana jan hancinta, dago idonta tayi ta kalleshi cikeda kunya,

"Abbu kaga" ta nuna masa wani wuri, juyar da idonsa yayi, kafin ya juyo gareta har tayi digirgire ta taka kafafunsa takai bakinta kan nasa,

Ta jima tana tsotsar chocolate dinta kafin ta hakura tana kallonshi,

"Abbu wallahi kaima dogone sosai, kalli fa duk tsayin nan nawa a kafadar ka natsaya"

Kugunta ya rike yana murmushi, "ke dama ai ba doguwa bace, gajeriya ce"

Murmushin itama tayi ta rike hannuwanshi, "ahakan? Wallahi nima inada tsayi"

Sakinta yayi ya nufi jakar kayanta domin ciro mata wanda zata sa, tana daga tsaye tana gyara fuskarta sai aikin murmushi takeyi ita Kadai domin idan akwai abinda ta tsana to bai wuce rashin jabir akusa da ita ba, ita kanta takasa gane wanne irin so take yi masa,

Wata blue din doguwar riga arabian gown ya ciro mata sannan ya fara zabo mata inner wears, duk suma blue colour ya cicciro mata saboda yaga haka take yi idan ta tashi saka kaya,

Niyyar tsokanarta yayi yace "gaskiya binti kema fa katuwace sosai, jibi wadannan abubuwan da kike sawa"

Daga inda take ta turo baki "haka dai ka gani kake so"

Murmushinsa mai sanyi yayi ya taso da kayan ahunnunsa ya nufota, "ni dama bafa wani abu nace ba, ungo juyo nafara saka miki kinga mafi sauri"

Sunkuyawa yayi yana ware mata pant din, "abbu tsaya, na b'ule sai na nemo pad"

Dagowa yayi daga duk'en da yake yafara kallonta, "wai binti  anya kuwa lafiyarki kalau? Nifa wannan abin naki yafara bani tsoro, ace ba zakiyi kwana 15 ba sai kinyi wannan abun"

"Nidai, nidai abbu lafiyata kalau" tafada cikeda shagwaba tana tutturo baki, wurin jakar tata ya koma ya ciro mata pad din ya kawo mata,

"Gashi nan sai ki saka danni ba sanin yadda ake yi nayi ba"

Kafa tafara bugawa akasa "abbu kaine zaka saka Allah"

"Oh binti yanmatan rigima, ya na iya, bani"

Taimaka mata yayi ta shirya sai dariya take tana murna, shi kansa jabir wani farin ciki yaji yana shigarshi domin kullum bashida burin da ya wuce na yaga bintinshi cikin walwala, hannunta ya kama suka fita falo inda al'amin yake zaune yana kallo bayan yagama cin abinci,

"Al'amin ummunka fa ta shirya muku breakfast mai dadi gashi kuma ka zauna anan ka cika cikinka da na yan hotel" jabir ya fada yana mika masa hannu,

"Abbu anty na bata da lafiya jiya ko bacci bata yiba idonta ne yake ciwo gashi yayi ja kuma yanata kuka"

Juyawa jabir yayi ya kalleta yana kashe mata idonshi daya,

"Ai nabata magani al'amin, kaga ai yanzu idon ya daina kukan ko?"

Kai al'amin ya daga, hannunshi jabir ya kama suka fice daga cikin dakin bahijja tana biye dasu abaya, taxi suka tare suka shiga suka tasamma gidan ummu,

Lokacin da suka shiga ummun tana cikin daki tana shiryawa domin fitowarta kenan daga wanka kasancewar tunda ta tashi tafada kitchen domin hada hadar shirya musu abin karyawa tunda jabir yace mata har su bahijjan ma anan zasu zo su karya,

Labule ummun ta dan bude ta leko tana yi musu sannu da zuwa kafin ta koma cikin dakin,zama suka yi shikuma jabir ya nufi cikin dakin,

Su bahijja na nan afalo a zaune itada al'amin duk zaman ya isheta ga uwar yunwa da takeji tasan jabir tsayawa yayi ya taimakawa ummun al'amin ta shirya kamar yadda itama yayi mata, wani kishine yaketa taso mata amma tana danneshi tana ta nanata adu'ar da ya sanar da ita dazu, suna nan azaune sai gasu jabir sun fito ummu tana makale dashi sai kace masu shirin zuwa dinner,

Dauke kai daga kallonsu bahijja tayi aranta tana tunanin wai ko kunyar al'amin basa ji, ita sau lokuta da dama bata iya yin wani abun saboda al'amin domin ta fuskanci wayone dashi ba kadan ba amma su ko ajikinsu sai dai ta fahinci kamar wani abun ummun tanayi ne dan ita,

"Bisimillah ga abinci fa" tajiyo muryar ummu tana yi mata magana,

Tashi tayi taje ta zauna a inda suke, kusa da al'amin ta matsa ta zauna suka fara bawa cikinsu hakkinsa, kamar jiya yauma Ummu da jabir sai soyayya suke aikawa da jununsa acikin kwanon abincin hakan yasa bahijja jin gaba daya abincin ma ya fice mata arai, cakular abincin taci gaba dayi da spoon tana ci kadan kadan ammafa bawai dan tana so ba kawai dai bata son su ganota ne,

Sun jima suna dan taba soyayyarsu kafin jabir ya mike ya fita zuwa toilet domin wanko bakinshi kasancewar abincin akwai tafarnuwa aciki, bayanshi ummu tabi zuwa cikin dakin,

Inda al'amin yake zaune yana hada abin yin game dinshi na puzzle ta nufa ta fara tayashi suna jerawa, suna yi yana bata labarin abokanshi da yayi,tuni ta manta da batun su jabir sai dariya take yi itada al'amin wani lokacin ma idan hirar tayi dadi sai ta bashi hannu su tafa.

"Lallai hira tayi dadi" suka jiyo muryar jabir abayansu, atare suka juya suna kallonsa yana tsaye da aswaki abakinshi yanayi,

"Abbu kaga anty ma ta iya hada puzzle"

"Ai al'amin kaida antyn nan naka ban san wanda yafi wani daru ba shiyasa taku tazo daya"

Kallonsa bahijja tayi tana murmushi, "lallai abbu nice mai darun" yanda tayi maganar cikin shagwaba ya sanya ummu al'amin tsayawa kallonta,

"To yanzu dai ku tsaya kun san dalilin da yasa nayi brush sannan nazo nake yin aswakin nan?"

Kai bahijja ta girgiza shikuma al'amin yace "lah abbu"

"To saboda wannan tafarnuwar da naci ne, mala'ikun rahma basa zuwa kusa da mutumin da yaci danyar albasa ko kuma tafarnuwa shiyasa alokacin manzon Allah annabi yace duk wanda yaci tafarnuwa ko albasa to kar yazo mana masallaci domin annabi baya sonta ko kadan amma kuma yana kaunar zuma sosai"

"Mun gode abbu" al'amin yafada yana dariya, inda suke jabir yaje ya zauna yafara tayasu aikin shirmen da suke yi yayinda ita kuma ummu ta mike adoguwar kujera ta kwanta tana hangosu daga inda take har tasamu bacci ya dauketa.

Suna nan zaune sunata buga game din da al'amin da jabir ganin jabir zai yi wining din al'amin ya sanya bahijja shigar masa suka cigaba dayi tare itada jabir har ummu ta tashi daga baccin da takeyi ta shiga kitchen ta fara aiki, binta bahijja tayi ta tayata har suka kammala.

K'arfe 4 suka fita mike kafa, ita ummu tana rikeda hannun jabir kamar wanine zai kwace mata shi ita kuma bahijja tana makale da na al'amin, har dare yayi suna cikin gari domin bude ido sai da dare ya danyi sosai sannan su jabir suka raka su bahijja masaukinsu,

Yauma kamar jiya bahijja kasa bacci tayi amma ta dan sassautawa zuciyarta wannan ne ma ya sanyata niyyar yin watsi da tunanin jabir da ummu ta rungumi ibadar da tazo yi domin samun dacewa saboda taji jabir yace duk wanda yayi umarah kuma ya kyautata to kamar ya rayu tare da annabi ne, ta dukufa sosai wurin yiwa mahaifiyarta addu'a akan itama Allah ya ganar da ita gaskiya yasa ta samu *wani haske* acikin rayuwarta.

Yanzu kullum a masallaci suke wuni suna sallolin nafila da karatun alqur'ani da sauran nau'o'in ibada har kwanakin suka shude domin yanzu har sun fara shirye shiryen komawa Nigeria kasarmu ta gado,

Ana saura kwana uku su tafi jabir ya dauki ummu da bahijja sukaje wani makeken supermarket domin yin siyayya, cemusu yayi kowaccensu ta dauki abunda take so, hakan yasa bahijja nutsawa cikin supermarket din ta shiga boutique inda ake sayar da kayan sakawa na maza, gajerun wando da kayan shan iska ta fara diba,duk wani abu da tagani na maza wanda ya burgeta sai ta daukawa jabir dama haka ya kamata duk abinda mace taga ya burgeta to kamata yayi ta saiwa mijinta yayi mata kwalliya dashi,kayan data daukawa kanta kadanne sai yan gidansu data daddaukawa abubuwan da ba arasa ba, lokacin da sukaje wurin biyan kudin kayan kallonta Ummu ta tsaya tana yi tana ganin ikon Allah yarinya karama wacce batafi sa'ar kanwar kanwarta ba tazo tana neman mallake mata miji,

Jidar kayansu suka yi suka nufi gida, masaukinsu bahijja suka fara zuwa ganin kayan sunyi mata yawa yasa jabir daukar mata wani ya tayata suka shigar dashi dakinta,

Tsayawa tayi tana kallonsa duk zuciyarta babu dadi domin agaskiya tana bukatar mijinta kasancewar yau wurin kwanaki 22 kenan rabonta dashi,

"Binti sai da safe?" Yafada bayan ya riko hannayenta,

Shiru tayi masa bata bashi amsa ba amma acan kasan cikin zuciyarta wani irin kololon bakin ciki takeji,

"Bari naje binti kinga Ummu tana jirana"

Hakan da yafada ne yasake tunzurata, hannunta ta fusge ta juya masa baya,

"Binti....!"

Yakira sunanta yana kallonta cikeda mamaki, shiru bata amsaba,

"Binti ni ne nake kiranki amma kika kyaleni?"

Nanma shirun ta sake yi ganin haka yasashi juyawa yafita ya nufi wurin ummu inda itama ta cika tayi fam tana jiran dawowarsa, dauke kanta tayi bata ko kalleshi ba lokacin da ya shigo cikin taxi din har sukaje gida bata ce masa ko uffan ba har suka fita daga taxi din suka shiga cikin gidan,

Sai alokacin tayi magana "ai nazata acan yau zaka kwana" tafada cikin kufula,

Kallonta yayi zuciyarsa cikeda mamaki wato sudai mata sam ba a iya musu duk hakurinka watarana sai sun kaika bango indai akan kishine,

"Ban ganeba" yafada yana kokarin cire rigar jikinsa,

"Dama ai bazaka ganeba" tafada gamida figar jakar kayanta tanufi cikin dakinta, bin bayanta yayi yashiga toilet yayi wanka yafito, itama toilet din tashiga tayi wankan tafito ta shirya tana gamawa tazo inda jabir yake kwance ta kwanta ta juya masa baya.

Juyo da ita yayi yafara rarrashinta "haba ummu al'amin, bai kamata muyi irin wannan rabuwar ba dake, antyn al'amin fa batafi matsayin kanwarki ba dan Allah kar ki daga hankalinki akanta"

"To ai abu al'amin gani nayine kamar kafi sonta shiyasa"

Sakata yayi acikin jikinsa yana murmushi "haba ummu bai dace kiyi irin wannan tunanin ba, koda ace zanso wata mace to bayanki zata bi"

Sai da taji haka sannan ta iya jin sanyi aranta tabar wannan zancen takoma fagen soyayya kuma.

Ita kuwa bahijja jabir yana fita tazauna dabas agefen gado zuciyarta cikeda damuwa gashi taga kamar alamun fushi yayi mata,

Rasa inda zata tsoma ranta taji dadi tayi, kukan nan dai data saba yauma shi tayi ta share ta kwanta tafara tuna jabir acikin zuciyarta.

Tun daga ranar jabir bai zo mata ba sai ana igobe zasu tafi da yamma sai gashi yasha kyau cikin yadi kalar ruwan madara, lokacin data ganshi cewa tayi acikin zuciyarta,

"Kai gaskiya abbu kanada kyau kullum yaro kake dawowa"

"Al'amin me ya samu idon naka naga kanata sosawa" ta jiyoshi yana yiwa al'amin magana, daki ta shiga batafi minti 1 da shigaba taji shigowarshi yana dosar inda take tsaye yana zuwa ya rungumeta ta baya,

"Binti badai fushi kike yiwa abbu ba?"

Jin yanda ya kanannadeta yasata kasa yin kwakkwaran motsi,

"Binti" yakira sunanta cikin rada,

"Na'am, bayan kaine katafi kaki dawowa" tafada ashagwabance,

Hannunsa yakai ya rufe bakinta "to ai gani yanzu nazo, kiyi hakuri kinji bintina"

Kalar rarrashin da yasoma yimata ne ya sanyata hakura dan dolenta ba tareda ta shirya ba.

  Washe gari misalin karfe 2 suka isa airport domin tafiya, ummu tana rikeda jabir taki sakinshi sai wani kankameshi take yi hakan yasa bahijja acikin ranta cewa "to ku zauna kar ya tafi mana"

Dakyar suka rabu itama bahijjan dakyar ta iya banbare al'amin ajikinta yana kuka tana kuka har suka shiga jirgi, jabir ne ya kwantar da ita agefen jikinsa ya soma rarrashinta daga karshe ya bige da tsokanarta,

"Shiyasa nace miki ki dage ki haifi naki saboda irin wannan amma kin kasa kullum ke kenan acikin yoyo kamar wata agwagwa"

Dariya yasata wacce batayi niyya ba "abbu kana bani dariya"

"Burina kenan binti ko kina son nabaki kuka?"

Kai ta girgiza, suna ta hira shida ita har jirginsu ya tashi suka tasamma kasar Nigeria.

Karfe 3:30 suka sauka mal idi driver yaje ya daukesu ya karasa dasu gida, sashen jabir suka fara shiga nan taga duk kura tako ina, kayan hannunta ta ajiye ta tatafi part dinta nan dinma ba acewa komai domin shima ya hada kura sosai, kayan jikinta ta rage tafito daga ita sai yar body hug green wacce ajiki aka rubuta _its all about me_ da manyan haruffa sai dan short din wandonta jeans baki iya gwiwarta,

Sashen jabir ta koma tana dauke da kayan aiki, lokacin da ta shiga yana tsaye afalo yakasa koda zama ma saboda kurar da take ciki,

"Abbu atsaye kake sai kace soja?" Tafada tareda yin dariya,

"Ehh yau dai kam nazama soja da alama"

"To ai kai ba zaka iya soja ba" tafada lokacin da tagama nade center carpet din da yake shinfide afalon domin fara shara,

"Saboda ni ba namiji bane?" Ya tambayeta yana nannade kafar wandonshi bayan ya cire rigar jikinshi,

"Haba abbu har ka fassarani? Ni ba haka zance ba"

"To me zakice?" Ya tambayeta yana jan rigarta ta baya,

"Abbu wlh kai kam da lawyer kafi dacewa"

"Saboda me?"

"Saboda iya tambayarka"

Murmushi yayi ya dauki mopper, tana shara shikuma yana yin mopping,

"Kinga kuwa yawan tambayoyi babu kyau domin abinda mutanen farko suka yi kenan Allah ya halakar dasu"

"Tambayar?" Ta tambayeshi bayan ta mike tsaye tana rike bayanta,

"Kwarai kuwa, ai mutanen farko akwai su da tambaya musamman ma mutanen annabi musa, a zamaninsa ansamu wani mutum ya mutu to kuma mutane suna zargin ko wanine ya kashe shi amma suna son su tabbatar sai suka tafi wajen annabi Musa sukace ya rokar musu ubangijinsa kan ya fada musu wanda ya kashe wannan mutumin, sai annabi musa yace Allah ya ce su samu saniya su yanka, daga nan sai suka shiga tambayoyi marassa dalili, wacce irin saniya? Wacce kala? A ina zamu samota? Awurin wa take?  Daga karshe sai da suka sha wahala sosai kafin su samu saniyar nan saboda yawan kwakwarsu amma da ace tun farko da aka ce musu su samu saniya sun samo basu yi wadannan tambayoyin ba da shikenan bukatarsu ta biya acikin sauki, shiyasa annabi yace da sahabbai acikin wani hadisi, kashedinku da yawan tambayoyi domin abinda ya halakar da wadanda suka gabaceku shine yawan tambayoyinsu da sabawa annabawansu, idan na haneku da wani abu kubarshi, idan kuma na umarceku da wani aiki to ku zo dashi gwargwadon iko"

"To ai abbu kai ba irin tambayoyin mutanen farko kakeyi ba, irin na mutanen yanzu kake yi"

"Kar kiyi min cuwa cuwa dai yanmata"

Kiss tazo tayi masa akumatu ta wuce cikin bedroom dinsa domin sharowa,

Har akayi kiran sallar la'asar sunata aikin, alwala jabir yayi ya tafi salla ita kuma taci gaba da aikin har tagama gyaran dakin nasa tsaf ta kunna turaren wuta na tsinke samfarin touch me nan dakin ya kaure da daddadan kamshin, tana shigar masa da kayansa wanda yazo dashi cikin dakin ya dawo daga sallar,

"Abbu har kadawo?"

"Nadawo, ke kinyi sallar ne?"

Kai ta girgiza "wallahi banyi ba dama so nake nakarasa wannan aikin"

Kusa da ita ya matsa ya tsaya adaf da ita tana dagowa tajita ajikinsa, kafadunta ya dafa "binti duk abinda mutum yake yi to zarar an kira salla ko kuma lokacin salla yayi bari akeyi aje ayi sallar sai adawo aci gaba bawai atsaya har sai an karasa abinda ake yiba, antambayi manzon Allah wanne aikine yafi lada yafi soyuwa awurin Allah? Sai annabi yace   _"'as salatu fi waqtiha, ma'ana yin salla akan lokacinta"'_, dan haka duk abinda kikeyi da zarar lokacin salla yayi to ki hakura har sai kinyi salla,mata dayawa acikinku kunada wannan sakacin"

Itama tasa kafadar ta dafa tana kallon dan mitsitsin bakinshi mai kyau "abbu shiyasa nake son zama dakai, aduk lokacin da muke tare kana yawaita sammin ilimin da ubangiji ya hore maka, bazan iya kwatanta irin son da nake yi maka acikin raina ba" kwalla ya gani tana kokarin kwaranyowa daga idonta,

Hannunshi yasa yafara kokarin share mata kwallar,

"To kuma menene abin yin kuka? Haba binti meye abin kuka, duk wanda kake so to zaka tashi tare dashi aranar karshe, mutum yana tashine tareda wanda yake so inji annabi Muhammad (S.A.W) shiyasa ake son duk wanda zaka so zaka kaunata to ya kasance nagari domin tare za atasheku, yanzu dai kije kiyi sallar kar nasake tsayar dake"

Ganin tana tsaye taki yin gaba taki baya ya sanyashi nannade hannun rigarshi ya dauketa ya shiga toilet da ita, alwalar ya dauro mata ya fito da ita akafadarsa sai da suka zo tsakiyar dakin sannan ya ajiyeta tanata faman dariya,

"Ashe abbuna yanada karfi"

"Ai binti bama ke kadai ba har ku biyu zan iya dauka keda cikinki wata tara"

"Abbu dagaske?"

"Dagaske mana yarinya"

Doguwar riga ta zira tana murmushi, salla ta tayar shikuma ya fita falo domin yana son yin waya da uwar gidanshi.

Tunda ta idar da sallar ta mike akan abun sallar domin ta gaji iya gajiya, tana nan akwance jabir ya shigo "a'a binti kin gama gyaran naki part dinne?"

"Abbu ba yau ba,yanzu nadawo dakinka kafin nagyara nawa"

Akusa da ita yaje ya zauna,

"Sannu binti na ai kinyi aiki, bari nayi miki tausa"

Kanta ta mayar kan cinyarsa yafara matsa mata dukkanin gabobin jikinta.

***

   Kwanansu 3 da dawowa jabir ya koma office amma sai da yasha rigimar bahijja kafin ta barshi ya tafi hakan ya sanyashi niyyar sakata awata makarantar islamiyya wacce ake zuwa kullum daga karfe 10 nasafe zuwa 12,ai kuwa ba karamin murna tayi ba duk da cewar shima yana koyar da ita agida haka ko wani aiki aka basu a makarantar idan ta dawo gida shine yake koyar da ita, basu dade da dawowa ba tayi fari fau da ita ga kiba da tafara hadawa kasancewar yanzu bata da damuwa sai ta mamanta wacce har yau taki sakar mata fuska domin ko tsarabar data kai mata ma lokacin data dawo daga umarah kin karba tayi wannan abu yana damunta mutuka sai dai kullum jabir yana yi mata nasiha kuma yana nuna mata muhimmamcin yin hakuri adukkan lamura.

Yau ta kama ranar juma'a, tunda taga jabir yana kokarin fita ta marairece masa,

"Abbu pop corn nake son ci"

"Dame kuma?" Ya tambayeta yana kallonta,

"Abbu da umbrella (fruit)"

"Kalli bakinki na kwadayi, hmm binti kiga yanda kike kiba amma ni sai rama kike sakani, ni kike tsotsewa  ke kina kiba ko?"

"Abbu bakace to ba"

"Binti nace to, shikenan?"

"uhm" tafada tana turo baki,

"Rigimammiya kawai" yafada tareda lakuce mata hanci yana murmushi,

Rakashi tayi ya shiga mota ya tafi office ta dawo falonta ta kwanta tana jiran akawo mata sakon da tayi domin wadannan abubuwan guda biyu yanzu su take kaunar samu.

Tunda aka kawo mata guggurun shi ta wuni tanaci sam ta kasa cin abinci, har jabir ya dawo ya tarar da ita da guggurunta ahannu tana kwance tana kallo tana diba tana ci, washe gari kuwa tunda ta idar da sallar asuba tafada kitchen, hijab dinta kawai ta cire ta shiga kitchen tafara aikin kosan da ta tashi da sha'awar ci,

Kasancewar dan kadan zata yi yasanyata markada waken a blender, kayan hadi ta saka masa sosai ta dora mai tafara soyawa ga kuma yajinta a ajiye agefe dan haka tana tsamewa take cinyewa, jabir ne yadawo daga masallaci dan lokacin har 6 tayi da yan mintuna, ta window din dakinsa ya hangota a kitchen dan haka ya fita ya bita cikin kitchen din yana shiga ya ganta tana cin kosan sai dandanar yaji take yi gashi kosan sai uban tiriri ne yake tashi daga cikinsa kasantuwar lokacin ta tsameshi,

Yana daga bakin kofa yana kallonta wanda ita bata ma san ya dawoba,

"Duk yanda akayi al'amin ya samu kani ko kanwa kenan" yafada acikin zuciyarshi yana murmushi,

Cikin kitchen din ya karasa ya tsaya ata bayanta, "binti ya kike cin abu tun yana kan wuta?"

"Abbu yafi dadine da zafin" tafada tana yarfe hannunta saboda zafin kosan gashi kuma so take takaishi bakinta,

"To kawo in tayaki"

Gefe ta matsa ta tsaya yaci gaba da soya mata yana tsame mata tana ci har yakare, ko d'aya jabir baici ba duk ita ta cinye kayanta,

Hannunta Yakama bayan ya kashe risho din,

"To zomuje ki bani ladan aikin da nayi miki"

"Kai abbu ashe dama ba dan Allah kayi min ba"

Murmushi yayi yana gyara mata igiyar da take daure gaban rigar baccinta wacce ta kasance riga da wando pink colour,

"Dan Allah nayi bintu amma kuma akwai niyya"

Bin bayanshi tayi tana bubbuga kafarta "shi abbun nan wayone dashi Allah"

Yana jinta sarai kawai kyaleta yayi har suka shiga dakin baccinshi.

  Wunin ranar bata huta ba saboda dambun shinkafa taji tana ra'ayin yi ta inda ta samu sauki tana da zogale agidan ashuke, haka tatashi aikin dambun, jabir tabawa gyaran zogalen ya karba ya zuge mata shi taje ta dora nan da nan gidan ya hade da kamshin dambun wanda nasan yanzu har yawun masu kwadayi irina ya tsinke,

Yana falonsa yana karanta wani littafin fiqhu wanda wani shehun malami ya rubuta ta shigo hannunta dauke da farantin abinci,

"Abbu ga dambun na kawo mana"

Agabanshi ta ajiye ta bude flask din ta zuba musu "har kin gama binti?"

Bata iya bashi amsaba ta gambada yaji ta tsulala mai acikin dambun tafara ci, kallonta ya tsaya yi yana murmushi,

"Bintina wannan cikin naki akwai kwadayi"

"Ciki kuma abbu?"

"Ehh mana binti, yaushe rabonki da bakonki?"

Dambun ta diba takai bakinta ta kalleshi tace "tun a madina"

"To kin gani, kema kin kusa samun babynki,shikenan nima na huta da bayar da pad"

Bata kara magana ba taci gaba da cin dambunta kafin daga bisani shima ya saka hannunshi acikin kwanon.

Yanzu kullum ita kenan a kayan kwalama bata iya yin normal girki na yau da kullum sai dai na kwadayi yau ma da niyyar yin meat fie ta tashi, zama tayi ta dage tana buga fulawarta wacce ta kwaba tafara murzawa da kwalbar lemu, tana gamawa taje tafara suya dama ita indai abin soyawa ne to tana daga tsaye take cinye kayanta,

Tana suya tana ci har taji ta koshi, sauran ta diba ta ajiyewa jabir wanda yana can a office yana aiki amma lokaci zuwa lokaci yana kiranta awaya yaji halin da take ciki,

Koda ya dawo gida kuwa rigima ta saka masa ita tuwo take so kuma tuwon ma na dawa miyar kuka,

Ido ya zuba mata yana kallonta, "binti tuwo?"

"Ehh abbu, wallahi yunwa nakeji"

Daukarta yayi suka tafi gidan malam amma acan dinma babu tuwon dawar sai na masara dakyar aka samo mata ma makwafta suka dawo gida.

Da safe kuwa bata barshi yayi baccin safeba tashinsa taje tafara yi,

Kansa ta hau ta zauna tafara jijjigashi,

"Abbu katashi muje ka fafe min gwangwani yau alala zanci"

Bude idonshi yayi ya riketa, "alale zakuci yau binti?"

Kai ta daga "ehh abbu yau alale zanci"

"Za kuci dai keda babynki"

Tashi yayi suka fita tare zuwa corridor dinta inda ta tara masa gwangwaneyen peak kanana,

"Binti meyasa ba zakiyi na leda ba yafi sauki wannan wahalar da kanki zakiyi"

"Abbu nidai bana son na leda, wallahi na gwangwani nake so" ashagwabe tayi maganar gashi ta rakwarkwabe fuska tana shirin yimasa kuka,

"To ya isa kar kiyi kuka zan fafe miki"

Zama yayi yafara fafe mata yana jin tausayinta har acikin ransa domin yanzu ita abar tausayice saboda lalurar da take dauke da ita na juna biyun dake jikinta, shiyasa kullum yake bata abinda take so kuma ako wanne lokaci cikin bata kulawa yake dai dai da rana daya bai taba jin ya gaji da yarintarta ko kuma shirmenta ba domin yasan har yanzu ita yarinyace saboda shekarunta har yau ba zasu wuce 25 ba kuma a ka'ida mata basa yin hankali na hakika har sai sunkai 35 alokacinne suke tantance baki da fari shiyasa ma acikin alqur'ani Allah ya ambaci matan aljanna wato hurul aini da cewar matasane masu hankali malamai sunce anan ana nufin yan shekara 35 ne, koma dai menene dama dole miji sai yana yin hakuri da matarsa saboda hankalinsu da nutsuwarsu ba daya bace,

Yanata yan tunane tunanenshi yana fafe mata gwangwanin ita kuma tana gyara wakenta domin akai mata markade,

"Abbu yanzu fa nan da shekaru 20 kazama tsoho ko" tafada tana dariya,

"Ai maza basa tsufa binti kece dai kika tsufa lokacin, nikuma lokacin zan auro yarinya Yar 18"

Waken ta bari ta koma kusa dashi "abbu dagaske kake yi?"

Kallonta yayi yanda duk ta rirrikeshi ta cukwikuyeshi tana kallonsa tareda hayewa jikinshi,

"Dagaske mana" yabata amsa yana tara mata gwangwanayen wuri guda, babu zato yaji tasaka masa kuka,

"Kai binti ai lokacin kema fa kin girma kilama kinyi auren babbar yarki"

Kukan ta daina ta rufe fuskarta, "kuma dan nayi auren yata shine zaka auro min sa'arta?"

"Ehh mana ai hakan yafi lada" yafada yana janye hannuwanta,

"Tam shikenan Allah ya kaimu lokacin idan ka aurota yayana zan saka suyi mata duka" tana gama fadin haka tatashi daga kusa dashi ta dauki bokitin wakenta takoma cikin kitchen, dariya sosai jabir yayi saboda jin abinda ta fada,

Lafiyayyen alalenta tayi yasha manja da alayyahu _(nasan pherty Xarah uwar kwadayi har yawunki ya tsinke, to kwalelenki, ga Batool Mamman canma na hangota tana lasar lebe to kema kwalelenki)_, yaji ta dauka roba guda ta koma falonta inda jabir yake yana hira da al'amin a waya,

"Ga antyn naka sarkin kwadayi"

Bata wayar yayi ya dauke robar yajin data dauko,

Duk hankalinta ya kasu kashi kashi dan haka agurguje ta yiwa al'amin sallama ta riko hannun jabir "abbu bani yajin, wallahi idan babu yaji bana jin dadin abincin"

"Kullum ke kenan acin yaji, yajifa bashida wani amfani ajikin dan adam"

Magiya tasaka masa, dan kadan ya zuba mata suka fara cin alalen tare, kullum haka yake biye mata yaci abinda ta girka na kwadayi ita kanta tasan jabir namiji ne wanda yasan hakkin mace domin tunda ta samu cikin nan ta daina dafa abinci kullum sai kayan kwadayi daga wainar fulawa sai dan malele, alala, dambu, dan wake da sauransu amma bai taba kin cin abinda ta girka ba, ko kuma yin korafi, sam bai taba yiba.

  Yammacine na ranar litinin tana zaune afalon jabir tana shan kafi kaza wanda yasha kifi da albasa tsabar kwadayi ma harda attaruhu tasa asuyar, tasha kwalliya sosai cikin leshi ja da adon baki ajiki,

Jabir ne ya turo kofa ya shigo bakinsa dauke da sallama,

Inda take ya karaso yana kallonta hadida aika mata da wani zazzafan sako ta cikin kwayar idonsa,

"Binti me kikesha ne haka?" Ya tambayeta bayan ya kamo hannunta,

"Abbu kafi tsire ne"

"Binti bakya tsoron yasaki gudawa? Wannan abun ai daga ganinsa zai batawa mutum cikinsa ko ba kuli kuli bane?"

"Abbu shine amma fa da dadi sha kaji"

Hannunta ya saki ya mike yana girgiza kansa "haba binti nikuwa yaushe zansha wannan abun? Kema dan akwai daliline"

Dakinshi ya wuce yana jiyota tana cewa "wallahi abbu akwai dadi saboda har wani zaki zakin maggi yake yi"

Murmushi yayi ya wucewarsa cikin daki, minti kadan ya fara kwalla mata kira cikin sanyayyiyar muryarshi, sanin bazata jiyoshi ba yasashi tashi ya leka falon, har yanzu tana zaune inda ya barta tana shan kafi kazarta,

"Binti zo"

Mikewa tayi ta tashi sai kuma taji wani irin ciwo ya murde mata cikinta da mararta,

Rike cikin tayi tana salati "wash abbu" shine kawai abinda ta iya fada jini yafara bin kafarta.



_Masu karatu kuyi min afuwa naso kammala book dinnan awannan shafin amma hakan bai samu ba, gaisuwa mai tarin yawa gareki khadija magaji bk da dukkan masoyan wani haske_


*_Ummi Shatu_*
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [10/22, 9:21 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*

   *_NA_*
*_UMMI A'ISHA_*

_121-125_




~~~Durkushewa tayi awurin tana rike da cikinta yayinda jini yake gudu ajikinta yana bin kafarta kamar an bude fanfo,

Da sauri jabir ya karaso inda take yana tambayarta,

"Binti menene? Me ya sameki?" Sai alokacin idonshi yakai kan jinin da yake bin kafafunta,

"Innalillahi" yafada arazane, dasauri ya saketa ya nufi dakinsa domin dauko rigarsa, yana tafiya yana saka rigar ko hula bai tsaya dauka ba, hijabinta daya hango akan kujera ya dauko ko saka mata baiyi ba ya dauketa irin daukar da ake yiwa jarirai,

Yana dauke da ita ya nufi tsakar gida da ita, kamashi tayi ta rikeshi gam numfashinta yana kai kawo yana fita dakyar,

Tunda mai gadi ya hangoshi ya tabbatar babu lafiya dan haka yayi maza ya fara kwalawa mal idi driver kira, shima a sukwane ya zaburo yazo ya shiga motar ya figesu mai gadi ya hangame musu gate suka fita,

_Nasara clinic_ shine asibitin da suka nufa, har lokacin bahijja murkususu take yi ajikin jabir tana sake kankameshi abin gwanin ban tausayi,

Suna zuwa asibitin jabir ya sake daukarta ya nufi ciki da ita yana shiga wata nurse ta garo gadon da ake saka marassa lafiya ya dorata akai aka garata suka doshi wani daki _(antenatal)_ ,jabir binsu kawai yake yi yana yiwa bahijja addu'a acikin zuciyarsa, dole a waje ya tsaya aka shiga da bahijja cikin dakin.

Yana nan tsaye yana kai komo awurin yama rasa abinyi kwata kwata shi kawai ta lafiyar bintinshi yake yi domin bai san acikin wanne hali take ba ahalin yanzu,

Wurin minti talatin yana tsaye a inda yake wani kyakkyawan likita ya fito dan gayu dashi mai mutukar kyau da iyayi  (saurayin adda Benazir), hannu ya bashi suka gaisa kafin yajashi zuwa cikin office dinshi yana goge gumin dake fita ajikin goshinsa,

Bayan sun zauna ne dr din ya dubi jabir cikeda damuwa akan fuskarsa yafara jawabi kamar haka,

"Dafarko dai ranka ya dade ina mai baka hakuri sakamakon munyi iya kokarinmu na ganin mun ceto ranta da lafiyar abinda ke cikinta amma unfortunately abin ya gagara...!"

Kallonsa jabir yayi wanda idanuwanshi suka sauya kala daga fari zuwa ja,

"Dr ban fahimci abinda kake nufi ba"

"Abinda nake nufi anan shine madam dinka ta samu miscarriage, tarasa cikin dake jikinta"

Cikin damuwa jabir yadafe kumatunsa da hannunsa guda daya acikin ranshi yana karanta addu'a domin samun sassauci,

"To dr menene musabbabin faruwar hakan, menene ya haifar da hakan?"

Wadannan sune jerin tambayoyin da jabir ya jerowa likitan alokaci guda,

"Ehh to gaskiya shine abinda muka kasa fahimta, har yanzu bamu gano abinda ya haddasa mata wannan miscarriage dinba saboda ahalin yanzu ta lafiyarta muke yi sannan kuma kasancewar ta zubar da jini da yawa to tana bukatar akara mata jini, da ruwa"

"Shikenan dr, thank you"

Tashi jabir yayi yana mika masa hannu domin yin musabaha, fita yayi ya tafi wurin mal idi driver suka koma gida ya dauko kudin da za ayi amfani dashi domin da saboda tsabar rudewa ko kudin ma bai samu ya dauko ba,

Asibitin suka dawo alokacin har ansamo jinin da yayi daidai dana bahijja ana kara mata, wata takarda aka bashi wacce ke dauke da jeren magungunan da ake bukata hakan yasashi nufar pharmacy domin siyo duk magunan da ake bukata,

Yana waje yana jira bai samu ganinta ba har mangaruba tayi, salla yaje yayi ya dawo yana zuwa ya samu dr din yana fitowa daga dakin da bahijja take anan yake sanar dashi cewar zai iya shiga ya ganta,

Jiki asanyaye jabir yasaka kai ya shiga cikin dakin, hangota yayi kwance hannunta daya makale da abin karin ruwa ana kara mata, dayan hannun kuma ta dafe cikinta dashi daga gani kuka take yi,

Gefen gadon ya karasa ya zauna akusa da ita yakai hannunshi kan goshinta yana shafawa,

"Binti na sannu..!"

Bude idonta tayi hawaye yana sauka daga idanuwan nata ta kalleshi,

"Abbu shikenan cikin ya zube ko?"

Duk da yana cikin damuwar shima amma sai da yayi murmushin karfin hali yaci gaba da shafa goshinta zuwa gashin kanta,

"Babu komai binti kar ki damu, wannan wata jarrabawa ce daga wurin Allah, watakila samun babyn ayanzu bashine alkairi agaremu ba shiyasa Allah ya hanamu ya kwace abunshi cikin sauki"

Idonta ta runtse wasu hawayen suna gudu akan kumatunta,

"Abbu yanzu shikenan na rasa wannan cikin? Wannan wacce irin...!"

Sauri yayi ya rufe mata baki da hannunshi,

"Haba binti ita jarrabawa akan mumuni ai tazama wajibi, mutum indai mai imani ne Allah baya taba barinsa kara zube domin Allah cewa yayi _"'Ashe mutane sunyi zaton abarsu suce munyi imani alhalin ba za a jarrabesu ba? Kuma lalle mun jarrabi wadanda ke gabaninsu domin lalle Allah yasan wadanda sukayi gaskiya kuma lallai yasan makaryata"' (suratul ankabut aya ta 3)_ dan haka wannan abun jarrabace daga wurin Allah binti, mutukar kayi imani to dolene sai Allah ya jarrabeka shiyasa acikin suratul bakara sura ta biyu aya ta _155-157_ Allah subhanahu wata'ala yake cewa:

_Kuma lalle ne muna jarrabarku da wani abu guda daga tsoro, da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da 'yayan itace, kuma kayi bushara ga masu hakuri, wadanda suke idan wata masifa ta samesu sai suce lalle ne mu ga Allah muke kuma lalle ne mu zuwa gareshi masu komawa ne, Allah yace wadannan akwai albarku akansu daga ubangijinsu da wata rahama kuma wadannan sune shiryayyu"'_

Kinga bai kamata ki rinka irin wadannan maganganun ba, addu'a ya kamata kiyi domin shi lamarin mumini akwai abin sha'awa da ban mamaki inji annabi Muhammad acikin wani hadisi haka yafada yace saboda idan wata musifa ta samu mumini sai yayi hakuri ya dogara ga Allah sai Allah ya canja masa da abinda yafi zama alkairi agareshi, idan kuma wani abin farin ciki ya sameshi sai yayi farin ciki ya godewa Allah hakan sai ya sake zama alkairi agareshi, hakika babu mai samun irin wannan garabasar face mumini"

Hannun jabir ta riko da dayan hannunta wanda bashine wanda ake yi mata karin ruwan ba, "abbu nahakura, wallahi nahakura, Allah ya bani ladan jarrabawar da yayi min, Allah yasa hakan shine yafi zama alkairi agareni, agareka da kuma rayuwarmu gaba daya"

Kissing din goshinta yayi yana murmushi "amin binti,haka ya kamata dukkan musulmi ya zama wurin rungumar kaddarar da ubangiji ya aiko masa da ita"

"Abbu marata tana yimin ciwo ga wani irin fitsari da nakeji"

Kanta ya shafa yana yi mata sannu, ya dade azaune awurinta har sai da yaga bacci yayi awon gaba da ita sannan ya tashi ya fita,abincin da zata ci yaje ya samo mata da sauran tarkace irin wanda marar lafiya zai nema.

  Kwananta uku a asibitin jabir yana kulawa da ita amma koda wasa bai fadawa kowa abinda ya faru ba, hatta gidansu bai sanar musu ba, haka itama gidansu bai fada ba, Ummu al'amin kuwa kusan kullum sai sunyi waya amma bai taba sanar da ita rashin lafiyar ba,

Yanzu taji sauki sosai ta dawo normal bayan likitoci sunyi mata wankin ciki, ganin ta warware taji sauki yasa aka sallamesu zuwa gida amma har lokacin basu san makasudin zubewar cikin ba shi dama jabir baya son yawan bincike domin yasan koma menene dai to Allah ne ya shiryo faruwar hakan.

Suna komawa gida ta shiga aikace aikace kasancewar jikinta ya warware sosai,

Tana kitchen tana goge goge jabir ya shigo daga shi sai wando baki iya gwiwarsa da farar t shirt mai gajeren hannu,

"Binti sarkin aiki, daga dawowa kuma sai afara da aiki?"

"To abbu idan nabari waye zai yimin?"

Ta bayanta yaje ya shiga jikinta ya rungumeta,

"Kibari anjima zan tayaki kiyi,amma yanzu kizo muje in nuna miki wani abu"

Make kafada tayi tana murmushi

"nidai abbu basai ka nuna min ba,Allah nasan wayo zaka yimin" ta karasa maganar cikeda shagwaba,

"Binti bakya son babyn ne? Naga harda kuka kikayi lokacin da wancan cikin ya zube, ko bakya son kiyiwa al'amin kani?"

"Gaskiya nidai abbu, nidai, nidai....!"

Juyo da ita yayi ya dauketa akafadarshi ya fita da ita yana kwaiwayonta,

"Nidai, nidai, nidai binti" dariya tafara kyakyatawa batare da ta shirya ba.

  Rayuwa taci gaba da tafiya musu cikin son juna da yarda da amincewa da junansu da kuma zaman lafiya mai dorewa, har yanzu jabir yana koyar da ita abubuwan da suka shafi addini, gashi kullum tana zuwa makarantar islamiyya inda take kara samun wani karatun,

Kimanin wata uku da yin barinta tasake samun wani juna biyun nan aka koma gidan jiya aka fara laulayi da kwadayi,

Karfe uku na dare ta farka daga baccin da take yi, ido ta bude tafara neman jabir, acan wurin da ya kebe domin sallarshi ta hangoshi yana karatun alqur'ani, juyawa tayi tana fuskantarsa, alqur'anin ya rufe ya taso zuwa inda take kwance,

Agefenta ya zauna ya riko hannunta yana shafa kyawawan kananan kitson dake kanta,

"Abbu gobe ko fate faten tsaki zanyi da wake da alayyahu"

Tafada tana kallonsa, shima kallonta yayi yana murmushi,

"Fate fate? Nikuma me zaki yimin?" Ya tambayeta yana jan hannun rigar baccinta guda daya,

"Abbu kaima shi zaka sha" tace dashi bayan ta rike hannunshi,

"Wallahi abbu ko idan ka tsinka min hannun rigata ba yarda zanyi ba" tafada tana turo masa baki,

"Me zakiyi binti? Ramawa zakiyi?"

Dariya tayi ta riko hannunshi duka cikin nata, "hanaka fate fatena zanyi"

Dariya yayi ya dagota kacokan ya dorata ajikinshi, "to yanzu ba zaki koma baccin ba?"

"Abbu muyi hira ni nagama bacci"

"To ai ni kin san irin hirata indai irin wannan lokacin ne" ya rada mata acikin kunnenta,

Sumar kanshi tafara shafawa "abbu wallahi indai na haifo baby marar gashi to kaine"

"Kedai binti, ni ai duk Sati sati nake yin aski da ace bana aski da tuni yanzu sumata tafi taki yawa"

"Hum um" tafada cikin shagwaba,

Bakinshi yakai saitin nata tagoce tana cewa "um um abbu"

"Ehh binti" yace da ita yana murmushi,

Kwanciya tayi ajikinshi suka ci gaba da nunawa junansu so.

  Washe gari da safe kitchen ta shiga ta shirya fate faten tsakinta takoma dakinta ta zauna atsakiyar gadonta tafara sha, dakin nata jabir ya biyota ya sameta tazuboshi a filet tanata sha da cokali,

"Binti tsabar rowa shine zaki gudo nan ki zauna"

"Ba rowa bace abbu"

"To menene?" Ya tambayeta yana kokarin hawa kan gadon,

"Gashi abbu musha"

Hannu yasa yafara diba yana ci,

"Binti bakin nan naki ya iya kwadayi tun jimawa"

"Kaima ai kwadayayyen ne abbu" tafada tana murmushi,

"Naji, nayarda"

Sai da suka koshi dam sannan yashirya domin tafiya office, part din bahijja ya shiga domin yi mata sallama, daure da towel ya ganta ta fito daga wanka tana kokarin karasawa gaban mirror,

"Binti nafito, sai nadawo?"

Juyowa tayi tana kallonsa yasha black din dafaffen boyel da hularshi yayi kyau sosai,

"Abbu kayi kyau, adawo lfy, Allah ya baka sa'a ya saka maka albarka adukkan al'amuranka"

Gareta ya karasa ya rungumeta yayi mata kiss agoshi sannan ya amsa da,

"Amin bintina,Allah yayi miki albarka, me zaki dafa da rana?"

"Fate fatena zansha yana nan dayawa na ajiye"

Hannunta ya kama ya rike yan yatsunta, "to shikenan nima ki rage min kinji"

Kai ta daga, sakinta yayi ya juya yafita yana murmushi, itama da murmushin ya tafi yabarta akan fuskarta tana mai jin wani sabon sonsa yana sake shigarta.

K'arfe 8 nadare yana kwance adakinsa akan gadonshi gabanshi da laptop yana lallatsawa bahijja ta shigo hannunta dauke da hijab jikinta kuma riga da wando ne yan kanti,

"Abbu gari da sugar nake son sha, kazo ka rakani muje mu siyo tare"

Juyawa yayi ya kalleta, "gari?" Ya tambayeta,

"Uhm abbu"

Laptop din ya rufe ya tashi zaune, yana karewa jikinta kallo,

"Muje, amma binti yau kuma ki rasa abinda zakisha sai gari da sugar?"

Hannunshi ta rike bayan tasaka hijabinta suka fara tafiya,

"Amma dai abbu ai ba laifina bane"

Ganin ta rakwarbabe masa fuska yasashi fara rarrashinta, suna tafe suna hira har sukaje wani shago abayan layinsu, tsayar da ita yayi ya karasa da kanshi shagon ya siyo mata garin kwano daya ya dawo suka koma gida,

Suna zuwa ta dauko Kofi ta diba ta zuba ruwa tasa sugar da madara tafara sha jabir yana zaune yana kallonta, bata iya yi masa maganaba har sai da ta kammala shanye garinta tukunna,baki ta turo masa,

"Abbu kuma meye kaketa kallona?"

Jikinshi ya matso da ita "binti wannan cikin naki ya saki kinyi kyau ne, matsalarshi daya ya mayar dake lazy mai dankaren kwadayi"

Kwantar da kanta tayi akan kirjinshi tana dariya, "shi kuma abbu gashi yanzu ya zama wani kala"

Hancinta yaja yana murmushi.

Kullum haka take fama da kayan kwadayi, yau wainar fulawa tayi ita ta wuni tana ci har dare,

Tsakar dare tana tsaka da bacci ciwon ciki ya tadata daga baccin kafin wani lokaci har jini yafara zuba daga jikinta,

Fitowar jabir kenan daga bathroom ya iyo alwala yazo ya risketa acikin wannan halin ba tare da bata lokaci ba yacire mata yar rigar baccin da take jikinta ya saka mata kaya ya dauketa yafita da ita lokacin har ta fita hayyacinta,kasancewar darene mal idi driver baya nan dan haka da kanshi yayi driving ya kaita asibiti suna zuwa aka karbeta likitoci suka fara kiciniyar hana cikin dake jikinta fita sai dai kaddara ta riga fata domin kafin wani lokaci har cikin ya karasa zubewa,

Bahijja tasha wuya sosai azubewar wannan cikin amma jabir sai kwantar mata da hankali yake yi yana bata hakuri sannan yana nuna mata cewar ta rungumi wannan jarrabawar da Allah ya aiko mata da ita domin doctors din sunce bawata matsala ce da itaba kawai dai kaddara ce,

A wannan karon ma jabir bai sanarwa da kowa ba har aka sallamesu a asibitin suka koma gida, komawarsu kuma keda wuya bahijja tafara yi masa kuka mai cin rai,

Hakurin dai yaci gaba da bata har ta hakura itama ta dangana kamar yadda taga shima yayi ita kam har mamaki jabir yake bata domin bata taba ganin mutum mai tawakkali irinshi ba, duk abinda Allah ya aiko masa karbarsa yake yi da hannu bibbiyu, bai taba nunawa Allah gajiyawarshi akan wannan jarrabawar ba, ganin haka ya sanyata itama daukar kaddarar suka ci gaba da zamansu cikin aminci da kaunar juna.

  Bayan faruwar haka babu dadewa ta sake samun wani cikin amma kuma wannan tun yana wata daya da yan satittika shima ya zube tunda sukaje asibiti aka bata gado dr din ya kira jabir office dinshi yafara yi masa jawabi kamar haka:

"Agaskiya ayanda muke zargi matarka tana shan magungunan zubar da cikine in banda haka yaza ayi ace tayita samun miscarriage har sau uku, gaskiya kasaka ido sosai akanta sannan ka dauki matakin da ya dace"

Jabir jin jikinsa yayi ya mutu yayi sanyi amma kuma acan kasan zuciyarshi wani irin tafarfasa yaji tanayi ga wani uban bacin rai da ya ziyarceshi lokaci guda.

Shiru kawai yayi yaci gaba da sauraron bayanin da dr din yake yi masa,

"Yanzu gobe idan Allah ya kaimu zamu iya sallamarku ku koma gida amma gaskiya kasaka ido sosai akan matarka domin duk yadda akayi itace ke zubar da cikin da take samu"

Tashi jabir yayi batare da yace komai ba ya mikawa dr din hannu ya fita ya nufi resumption domin bazai iya shiga dakin da bahijja take ba lokacin saboda bacin ran da yake tare dashi,

Tunani kawai yake yi aranshi me yake yiwa yarinyar nan da har ya sata kin hada jini dashi, shin me yake tare dashi da har take kyamar jininshi, sanin bashida amsar wadannan tambayoyin ya sanyashi mikewa yafara zagaya farfajiyar wurin,

Har gari ya waye bai samu nutsuwa ba yana nan dauke da takaicin abinda likitan nan ya sanar dashi,

Sai da ya danne zuciyarsa sannan ya shiga dakin da bahijja take kwance duk ta dan rame daga daren jiya zuwa yau kadai, bai iya yi mata magana ba asalima ya kasa koda kallon fuskarta,

"Abbu zan sha tea" shine abinda ya jiyota tana fada cikin kasalalliyar murya,

Bai bata amsa ba ya juya ya fita, minti kadan sai gashi ya dawo hannunsa dauke da kayan shayi da tea flask domin ya tura akawo musu dama,

Zama yayi ya hada mata tea din ya mika mata, dakyar ta iya tashi ta kafa kai tafara sha,

Har tagama jabir baiyi mata magana ba,

"Abbu kace su sallameni mu tafi gida, bana son wannan wankin cikin wallahi da wahala"

Tafada tana ajiye cup din dake hannunta,

"Dama wannan time din sunce ba zasu yi miki ba amma ai bai kamata ki tsorata ba tunda kece kika jawowa kanki" yace da ita tareda mikewa ya fice, Gida yayi tafiyarshi batare da ya sanar mata ba,

Mamakine ya kamata sosai saboda jin abinda ya fada, sam takasa fahimtar inda zancen nashi ya dosa, tana nan zaune har dr ya shigo ya sake dubata ya bata sallama, shiru shiru babu jabir sai da rana tayi sannan mal idi driver yazo ya dauketa yakaita gida, ba karamin mamaki tajiba lokacin da taje gidan ta tarar jabir baya nan yayi tafiyarshi office,

Duk da jikinta babu kwari haka ta daure ta gyara gidan tayi girki amma koda jabir ya dawo bata samu fuska awurinshi ba, abincin ta kai masa amma yanda ta ajiye masa haka ya tashi ya barshi yayi wanka ya ficewarsa,

Duk tabi ta damu da sauyin da tafara gani daga gareshi,tana zaune tana nazarin abinda ya fara faruwa agareta tsakaninta da jabir har ya dawo misalin karfe 9:30,bai kulata ba ya wucewarsa cikin daki yayi wanka yayi shirin bacci ya kwanta, jin shiru bai fitoba ya sanyata binshi cikin dakin,

"Abbu bakada lafiyane?" Ta tambayeshi tana kokarin zuwa kusa da ita,

"Kar ki zauna min adaki, kikoma dakinki bana son damuwa" yafada ahankali yana kokarin juya mata baya,

Kuka tafara "abbu dan Allah idan wani abun nayi maka kayi hakuri, abbu dan Allah kafada min laifin da nayi maka, wallahi bazan iya kwana ni daya adakina ba"

Jin kukan da take yi masa yake yi har acikin ranshi, shi kansa yana tunanin ta yanda zai iya ganin wannan daren ba tare da bintinshi ba amma kuma radadin ciwon abinda tayi masa shine bazai barshi ya iya kwana da ita adaki daya ba ayau,

"Ki tashi ki fice min" yafada cikin tsawar da bata taba sanin ya iyata ba, cikin rawar jiki ta mike ta fita tana tafe tana kuka wanda har yana iya jiyota,

Dakinta ta koma ta kwanta taci gaba da kukanta ga wani azababben sabon son jabir da taji yana shigarta, shima abangaren jabir din kukanta kawai yake jiyowa acikin kunnensa tana rokonshi kan ya sanar da ita laifin da tayi masa wani irin tausayinta yaji har acikin ranshi, dukkaninsu ranar babu wanda ya iya yin bacci acikinsu, bahijja kuwa kwana tayi tana kuka har gari ya waye, mamakin canjawar jabir kawai take yi,

Tana dakinta da misalin karfe 10:30 ta jiyo alamun fitarsa zuwa office ba tare da ya koda kalli sashenta ba, lokacin da ya dawo ma haka wasa wasa sai da suka yi kwana biyar ahaka akwana na shidane ta kuduri niyyar sai anyita ta kare ranar domin itama yanzu ta shirya rayuwarta ita daya ba tare dashi ba domin gani take kamar ko dan yaga tana sonshi ne shiyasa yayi mata haka,

Tana falonta zaune tana jiran dawowarsa har taji shigowarsa batayi kasa a gwiwa ba ta nufi sashensa, acikin dakinshi ta sameshi yana kokarin cire kayan jikinshi,

"Zuwa nayi yau ka fada min abinda yake ranka, idan zama danine baka ra'ayi yanzu ka sanar min ko ka sawwake min"

Bai jiyo ya kalleta ba yace "ke kar ki saka min ciwon kai pls, ki fitar min daga dakin nan kingane?"

"Akan me zan fita bayan baka sanar min da abinda kake nufi dani ba"

"Duk abinda kike tunani shi nake nufi"

"To meye nufinka, nabar maka gidanka kenan?"

"Yanda kika zaba" yafada tareda shigewa cikin bathroom,

Bin bayanshi tayi da kallo ta hadiye kukan da yazo mata,

"To sai me dan nabar maka gidanka? Zan barshi yanzun nan saboda basai lalle dashi zanyi rayuwa ba, idan dan saboda kaga ina sonka ne yasa kayi min haka to kasani nima yanzu nadaina sonka, zanyi rayuwa ba tare da kai ba"

Tana kaiwa nan ta juya tafita tanufi dakinta tana hawaye tana zuwa tafara harhada kayanta acikin katuwar akwatinta, hijabi ta zira taja jakarta domin ji take yi itama yanzu tana iya fitar dashi daga ranta saboda dama tun asali bashi ya ganta yana soba itace taganshi taji tana sonsa su kuma maza dama haka halinsu yake indai kaine ka nuna kana sonsu to babu irin wulakancin da bazaka gani ba,shiyasa duk tsawon lokacin da suka dauka atare bai taba furta mata kalmar so ko kauna ba, akwatinta taja tafita daga gidan me gadi yana tambayarta ko lafiya amma bata bi takansa ba tayi gaba,

Jabir yana tsaye agaban window yana kallonta har tafice, duk da yana jin haushin abinda tayi masa amma yaji rashin dadin tafiyarta domin ganinta kawai wani abune awurinshi wanda yake jinsa har cikin ransa,labulen ya saki ya koma cikin dakinsa ya zauna ya dafe kansa yana tuna irin daddadar rayuwar da suka gudanar tare da ita,hakika yanzu ya yarda bahijja wani tsagi ce na rayuwarsa kuma bazai taba jin dadin rayuwarshi ba sai tana kusa dashi.

Tsayar da kukan da take yi tayi lokacin da zata shiga gidansu,

Iya papa tasamu domin ma tatafi church,tunda babanta yaganta yasan babu lafiya dan haka ya tsayarta yafara tambayarta, bata iya sanar dashi ba kawai dai tace jabir dinne yace tadawo gida,

Shiru mahaifinta yayi yana tunanin anya kuwa jabir zai iya yin haka, akwatinta ta dauka ta nufi dakinta nada tasaka aciki, kokari tayi ta danne duk wani tunanin jabir wanda yake kokarin hanata sukuni,

Tana falo azaune tana lazimi ga Nigerian film ta kunna tana kallo ma ta shigo hannunta rikeda bible,

"Welcome ma" tafada tana kallon maman nata,

"Ah goodness me kika zo yi? Ba nahanaki zuwa gidan nan ba indai wurina ne ba?" Ma tafada cikin fada,

"Ma mijinane yace nadawo gida" tafada idonta cikeda kwalla,

"Ah goodness wannan shine abinda nayita fada miki but you refuse my advice that time, tun farko sai da nafada miki karki Auri hausa man but kika ki ji, yanzu gashi kinje ya koroki gida"

Zama ma tayi ta ajiye bible dinta ta kalli bahijja "my daughter yanzu wannan abunda ya faru to abun farin cikine agareki sannan kuma damace agunki wacce zaki bar wancan addinin ki tuba kidawo addininmu nagaskiya"

Girgiza kai bahijja tayi "ma ai ni narigada nabar wannan addinin har abada, addinin musulunci addini ne nagaskiya,sannan kuma shi addinin *Wani haske* ne ga kowa da kowa, amma kuma wannan ba shine yake nufin suma masu addinin basa aikata kuskure ba, yanzu 'ma' akwai mutanen da kika taba gani masu tsarin komai na rayuwa samada musulmai? Yanzu 'ma' bakya mamakin yanda Allah ya tsaya ya shirya sama ya shirya kasa? Allah shi kadaine ya halicci sammai da kassai acikin kwanaki shida ba tare da taimakon kowa ba,

Shine wanda ya daidaita akan al'arshinsa yana kallon kowa kuma yana jiransa a madakata, wallahi ma addinin musulunci shine addini na gaskiya kuma shine addinin da yake dauke da abin al'ajabi iri iri domin Allah shine ya tsara addinin ba mutum ne ya tsarashi ba, addinin musulunci shine addinin da Allah ya halicce mutune domin su kasance acikinsa ta hanyar bauta masa shi kadai ba tareda kowa ba, ma shigata addinin musulunci naga abubuwa daban daban naban mamaki wanda addinin kiristanci bai bayar da koda rabinsa ba, asali Allah ya halicci mutum da aljan ne domin su bauta masa, annabi Isah ba kowa bane face bawan Allah, halittar Allah kamar kowa sai dai Allah ya aikoshi zuwa ga mutane domin ya kirasu zuwa ga bautar Allah shiyasa Allah ya azurtashi da mu'ujuza ta warkar da marassa lafiya musamman ma kutare da makafi wannan ne yasa mabiya addinin kiristanci suka gajeshi suna bude asibitoci suna bawa mutane magani na rashin lafiyarsu"

Shiru ma tayi tana kallon yar tata amma fa duk jikinta yagama yin sanyi sai dai bata jin zata iya barin addinin datake kai,

Mikewa tayi ta shiga dakinta batare da tayi magana ba hakan yasa bahijja daga hannu tana addu'ar Allah yasa itama ma ta amshi Kalmar shahada.

   Daren ranar kasa bacci tayi tunanin abbunta kawai take yi gashi dan jaraba takasa mantawa da kyakkyawan yanayin da kullum suke kasancewa aciki kamar yadda shima jabir din yana can yana tunaninta acikin ranshi gashi gidan gaba daya yanzu jinsa yake ya zame masa wani shiru kamar makabarta,

Alwala ta dauro tazo tafara sallar dare domin takasa yin baccin, ta dade acikin sujjadarta tana rokon Allah kan ya daidaita tsakaninta da mijinta ya kawo zaman lafiya mai dorewa atsakaninsu.

Babu laifi yanzu ta samu sakin fuska awurin ma domin har suna zama suyi hira hakan da ta samu yasata cigaba da yiwa ma nasiha akan addinin musulunci saboda ta fuskanci yanzu tafara yin sanyi,

Kullum ita kenan acikin ibada,sallolin nafila irinsu walaha ga azumin litinin da alhamis da take yi, satinta biyu da dawowa gida ta tashi da wani azababben ciwon ciki wanda take jin kamar mutuwa zatayi tabar duniyar,

Mota babanta ya samo suka kinkimeta shida 'ma' suka sakata aciki suka nufi asibiti da ita, 'ma' sai kuka take yi tana rirriketa,

_Dr Tafida females & children's care hospital_ suka kaita, ana shigar da ita dakin da za a dubata 'ma' tafashe da wani sabon kuka tana leka dakin,

Mintuna kadan da shigar da ita wata likita mace tafito tana kiran mahaifan bahijja, binta suka yi zuwa wani office,

"Am ina mijinta? Muna son zai yi mana signing saboda theatre zamu yi mata"

"Baya nan sai dai ni, ni mahaifinta ne?" Papa ya ce da likitar wacce take kyakkyawa mai mutukar fara'a,

"No mijinta muke so yayi signing din" tafada tana Ciro wani file agabanta,

"Bari anemoshi, bari akirashi"

Fita papa yayi ya fara neman jabir awaya amma dakyar ya sameshi, yana dauka ya sanar da shi abinda yake faruwa,

Arikice jabir yabar aikin da yake yi ya taho asibitin dama sam baya cikin nutsuwarshi aikinma kawai yinsa yake amma bawai dan dadi ba sanin idan ya zauna agida kewa da kadaicin bintinshi ne zai dameshi shiyasa yake zuwa office din,

Yana zuwa ya samu papa yana tsaye yana jiransa, jagora yayi masa zuwa office din dr hanfa, tare da mijinta dr tafida suka sameta suna tattauna matsalar bahijja,

"Kaine mijinta?" Dr hanfa ta tambayeshi,

"Ehh nine" jabir yabata amsa,

"Ok zo muje to" dr tafida yafada tare da fita, bin bayanshi jabir yayi zuwa office dinsa,

"Wato ita wannan matar taka nayi scanning nagano tana dauke da wani k'ari acikin mahaifarta wanda indai wannan k'arin yana nan to bazai taba barinta ta haihu ba, duk lokacin data samu ciki to zubewa zai rinka yi, gashi har k'arin ya fara girma"

Wani yanayine ya zuyarci jabir naban mamaki,

"Dr ban gane abinda kake son fada ba"

"Ina nufin yanzu dole sai mun yiwa matarka theatre mun cire mata k'arin dake mahaifarta domin shine yake sanya mata ciwon ciki dana mara wanda wannan ciwon zafinsa zai rinka sanya mata yin miscarriage, shiyasa muke cewa mata da zarar sun fara fama da rikicewar al'ada to su zo asibiti domin hakan yana haifar musu da matsala"

Turo masa wani file yayi anan jabir yayi signing yatashi ya fita lokacin tuni har anwuce da bahijja zuwa dakin da za ayi mata aikin,

"Allah sarki bintina na hukuntaki akan laifin da ba nakiba, Allah yasa ayi miki aikin nan acikin nasara afito dake nikuma nayi alqawarin baki kulawar da tafi wacce nabaki ada" yafadi hakan acikin zuciyarshi,

Suna tsaye awurin 'ma' sai kuka take tana zagaye wurin takasa zama, shi kansa jabir ya kasa zaman domin rabonshi da bintinshi tun sati biyu da suka wuce, hakika yasan ya hukuntata da hukunci mafi tsauri agaresu shida ita,wani irin zazzafan tausayinta yaji yana ratsashi da wata irin sabuwar soyayyarta wacce bazata fasaltu ba.

Karfe  3 daidai dr tafida yafito daga theatre din da yashiga yiwa bahijja yana rikeda hannun matarsa dr hanfa wacce suke tafe tana goge masa zufar dake tsattsafowa agaban goshinsa domin jin cikakken labarin wadannan ma'auratan likitocin duba littafin ummi Aisha _(Alheri dankone)_,

Cikin hanzari ma da papa da jabir suka doshesu domin jin halinda bahijja ke ciki.

   _Ina cigiyar safiyya ummu Abdoul, idan sak'ona ya riskeki my regards to you!_







_*Ummi Shatu*_🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [10/26, 8:43 PM] Ummi A'isha🏻: *WANI HASKE*

  _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

_126-130_

_(second to the last page)_


~~~Kowannensu fuskarsa dauke da alamun tambaya suke kallon dr tafida,

"Dr ya akayi? Wanne hali binti take ciki yanzu? Anyi nasarar cire karin daga mahaifarta?"

Wadannan sune jerin gwanon tambayoyin da jabir ya zayyanowa dr tafida alokaci guda,

"Dr kafada mana halin da my daughter take ciki" ma tafada cikin tashin hankali,

"Duk ku kwantar da hankalinku patient dina tana nan lafiya, anyi aiki cikin nasara amma sai nanda 4 sannan zata farfado"

Sai alokacin dukkaninsu suka samu nutsuwa, wata sanyayyiyar ajiyar zuciya jabir yayi domin hankalinsa da ba karamin tashi yayi ba gani yake kamar ya rabu da bintinshi kenan har abada,

Masallaci yatafi yaje yayi salla ya fito daga nan kasuwa suka wuce bayan ya biya ta bank ya ciri kudi,

Kayan dubiya irin wadanda wanda aka yiwa tiyata zai iya ci  ya sissiyo mata da sauran kayayyaki marassa nauyi,

Sai da yakoma asibitin ya kaiwa su 'ma' kayan  ya biya kudin aikin da aka yiwa bahijjan da kudin magungunan da za abata sannan yatafi gida domin yin wanka,

Agaggauce yayi wanka ya shirya ya fito tsaf cikin farin yadi mai laushi shara shara wanda ya bayyanar da farar vest din da yasaka, kamar yadda ya saba komai nasa fari yasaka tun daga kan agogonshi har zuwa takalmin kafarsa hularshi ce kawai light blue mai ratsin fari ajiki, turaren _Special oud_ da _muqalatul shaikha_ yayi amfani dasu ya feshe jikinsa dasu,

Lokacin da ya koma asibitin misalin karfe 5:30 na yamma yasan yanzu dai bintinshi ta farfado, da Anty Bilkisu yayi clash ahanya hannunta dauke da flask din abinci,

Ganin 'ma' da papa suna dakin da bahijjan ke ciki ya sakashi kin shiga domin shi mutumne mai alkunya da kara,yafi minti 10 atsaye awaje yana jiran fitowarsu,yana nan tsaye har papa ya fito ya sameshi,

"A'a malam jabiru ya kake tsaye anan? Ka karasa ciki mana ai ta farfado"

Papa yace dashi yana murmushi fuskarsa cikeda annashuwa,

"Allah ya kara bata lafiya" jabir yafada yana kokarin shiga cikin dakin,

"Amin, amin" papa ya amsa yakara gaba,

Kofar dakin ya bude ya shiga idonshi fes akan gadon da bahijja ke kwance mamanta tana gaban gadon tana tattare mata rigar da tasaka mata sannan tana kokarin gyara mata zanin jikinta gudun kar ya rinka gogar wurin da aka yi mata aikin,

Anty Bilkisu ce ta tura masa kujera ya zauna yana gaisar dasu, bahijja najinshi yana magana cikin wannan sanyin muryar tashi kamar marar laka ajiki,

Dauke kanta tayi tayadda ma ba zasu iya hada ido ba, ganin yadda take cikinta awaje, kasan cikinta awaje yasa jabir jin wani irin kishi yana taso mishi, yanzu shikenan wani ya kalle masa cikin bintinshi da mararta,

Fita anty bilkisu tayi 'ma' itama ta mara mata baya, suna ficewa ya tashi daga kan kujerar da yake ya nufi gadon da bahijja take kwance,

"Sannu bintina, ya jikin naki?" Yafada ahankali cikin sanyin muryarshi bayan ya rankwafar da kanshi kusa da fuskarta,

Idan gadon da take kai yayi magana to itama tayi magana, shiru tayi masa ta rabu dashi amma kuma yanda ya kusanto jikinshi da nata yasata cikin wani irin wahalallen yanayi ga wani kamshi mai dadi wanda yake fita daga jikinsa duk ya cika mata hanci,

"Binti...!" Yakira sunanta bayan ya kai hannunshi kan nata ya dafe,

"Binti duk fushin ne haka zaisa ki k'i yimin magana? Haba bintina"

Har lokacin bata tanka masa ba asalima runtse idanuwanta tayi dama kuma fuskarta ba saitin da yake take kallo ba,

Tana jinsa yana murza yan yatsun hannunta da nashi amma tayi biris dashi domin itama ta dau alwashin sai ta rama abinda yayi mata sai ta wahalar dashi tayadda dakanshi sai ya furta yana sonta,domin duk iya zamansu bai taba sanar da ita wannan kalmar ba,

"Bintina yanzu haka doctors dinnan suka gane min surar jikinki, suka kalle min halittarki"

Nanma shiru tayi bata tanka masa ba, babu zato taji ya sunkuya ya fara yiwa wuyanta da saman kirjinta zafafan kiss, sake runtse idonta tayi domin rabon da taji wannan yanayi tun kafin su samu sabani dashi, tana jinshi ya dage yanata sinsinar jikinta musamman ma wuyanta amma har lokacin taki ta kulashi.

Jin alamun za bude kofa ya sanyashi matsawa daga gareta ya tsaya agaban gadon,

Anty Bilkisu ce ta shigo itada wata nurse wacce take dauke da magungunan bahijja,

Yana tsaye yana jinsu nurse din tagama karanta dokokin abubuwan da za a iya bawa bahijjan ayanzu taci,

Juyawa suka yi suka fita yayinda ita kuma 'ma' ta shigo cikin dakin, gaba daya jabir nauyin 'ma' yake ji dan haka ya juya yafita daga cikin dakin sai da bahijja taji fitarsa sannan ta iya jiyo da kanta tana kallon mamanta amma har acikin ranta wani irin son jabir ne taji yana sake zagaya jinin jikinta.

Misalin k'arfe 10 jabir ya leka cikin dakin yayi musu sallama cewar zai tafi gida,tunda bahijja taji maganarshi ta kawar da kanta ta rufe idanuwanta, murmushi yayi ya fita yana mai jinjina fushi irin na bahijja in banda abinta waye yake fushi da mijinsa irin haka,

Koda yaje gida ma kasa bacci yayi sai tunane tunanenta da ya addabi ruhinsa, sanin wannan tunanin bazai barshi ya runtsa ba ya sanyashi tashi ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito yafara gudanar da ibada.

Washe gari da safe da misalin karfe 9 ya shirya ya fita domin zuwa asibitin, lokacin da yashiga dakin iya bahijja da anty Bilkisu yagani domin dama tun jiya da daddare mamansu da papa suka tafi gida iya bilkisu aka bari awurinta,

Azaune yaganta ta jingina da pillow anty bilkisu tana hada mata tea dan kadan acikin cup, batare data kalleshi ba ta amshi cup din tea din ta fara kurba ahankali,

"Baban al'amin tunda kazo to bari naje gida nadawo, dama su mama nake jira amma tunda kazo shikenan"

Anty Bilkisu tafada sannan tafara tattare kwanukan abincin da aka kawo musu domin tafiya dashi,

"To babu damuwa sai kin dawo" jabir yabata amsa yana latsa wayarshi,

Bahijja kam bata so haka ba amma babu yadda ta iya sannan badan bata son agane tsakaninsu da jabir ba da ta cewa anty bilkisu kar tatafi,

Fita anty bilkisun tayi tana fadin "nima ba zama zanyi ba,yanzun nan zan dawo wanka kawai zan iyo"

Tashi jabir yayi ya nufi gadon yana kara waya akunnenshi,

"Ummu al'amin ga antyn al'amin din"

Tajishi ya fada tareda zama akusa da ita ya kara mata wayar akunnenta yana rada mata ahankali cewar "ga uwar gidanki zata gaisheki"

Bata ko jiyo ta kalleshi ba tafara magana ahankali irinta marassa lafiya, kallonta kawai jabir yake yanda ta dauke kanta taki koda kallon gefen da yake ita ala dole fushi take yi dashi,

Wurinda aka yanka ajikinta ya kalla, "binti me dan tumbi" yafada aranshi domin tana da tumbi kadan, yana rike da wayar akunnenta tagama magana da ummu suka fara da al'amin,

"My boy nayi missing dinka, yaushe zaka dawo ne?"

Bai jiyo amsar da al'amin yabata ba yaji tace,

"I luv u too my boy"

Janye kunnenta tayi alamun tagama wayar, rufe wayar yayi yasaka acikin aljihunsa yajiyo yana kallonta amma ita kam sam taki kallon koda sashen da yake ma,

Kurbar tea dinta taci gaba dayi har ta shanye tafara kiciniyar komawa ta kwanta amma ta kasa, yana zaune akusa da ita yana kallonta sai kokarin kwanciya take amma kuma abin ya gagara,

"Binti kice na kwantar dake mana, kodan yanzu kin daina yimin magana ko?"

Yace da ita tareda kai hannuwanshi ya taimaka mata ya kwantar da ita, sai bata rai take tasha kunu ta bata rai, shi abin natama dariya yake bashi,

Jikinta ya matsa, hannu tasa ta tureshi ba tareda ta kalleshi ba tace,

"Kabari kar ka fama min ciwo na"

Asaman kirjinta ya dora kanshi yamika hannunshi daya ya kamo nata,

"Binti banida bakin da zan baki hakuri amma dai kiyi hakurin, kisani ni bana daya daga cikin mutanen da basa aikata kuskure, binti duk mutum tara yake bai cika goma ba shiyasa baya iya tsallake kuskure, annabi ne kawai mutumin da ya cika sama da goma akomai amma mu sauran mutane dukkaninmu masu aikata kuskure ne, binti ni ba waliyyi bane, ba ma'asumi bane ba kuma masanin gaibu bane, kisani duk ilimin mutum duk tsoron Allahnshi to yanada tawaya awani wurin shiyasa dole sai muna yiwa junanmu uzuri,

Bama ni ba kowanne mutum arayuwar nan dole sai ana yi masa uzuri domin komai kirkinsa da kamewarshi to wata rana sai yayi kuskure dan haka ina mai sake baki hakuri akan abinda ya faru saboda ba laifina bane ni banida masaniyar dalilin zubewar cikinki, dr ne ya sanar dani cewa kina amfani da kwayoyin zubar da cikine shiyasa kiketa samun miscarriage dinnan, but now tunda nagane gaskiya shikenan yawuce kuma kin san duk namijin da zai ji matarshi tana aikata irin wannan to dolene ransa ya baci..!"

Yanda yafara bayaninshi har ya diga aya bahijja bata ce mishi uffan ba asalima ayanda take dazu yanzun ma haka take, amma taji mamaki mutuka wai da jabir yace mata dr ne yace itace take zubar da cikin datake samu, wasu zafafan hawayene suka zubo mata domin ita anata tunanin ya za ace tana aikata wannan abun bayan bata taba haihuwa ba, gara shi jabir yanada yaro amma kuma duk da haka yana son yasake samun wani to inaga ita wacce bata da kowa,

Dago kanshi yayi yana kallonta duk jin ranshi yake yi ya sosu saboda ganin yanda take hawaye gashi ranta abace, hannu yakai yafara shafe hawayen nata,

"Menene abin kuka kuma? Ba nariga da nabaki hakuri ba? Haba binti kina so hankalina yatashi ne?"

Bata bude idonta ba amma dai ta daina kukan sai dai har yanzu fuskarta babu walwala, shidai jabir ya rasa abinda yarinyar nan ta taka domin sam taki yi masa magana sannan taki koda kallonsa,

Suna nan ahaka har nurse ta shigo dauke da spirit domin gogewa bahijja wurin da aka yi mata aikin,

Yana zaune agefenta nurse din tafara aikinta, runtse ido kawai bahijja take yi amma fa tana jin zafin yana ratsata har cikin jijiyar jikinta, hannunta ya sake kamowa,

"Da zafine binti?"

Gudun kada ta badashi agaban nurse din ya sata daga masa kai amma batayi magana ba,

"Ayya sorry bintina" yace da ita ahankali, jin yanda yake wasa da hannunta yasata mantawa da zafin spirit din da take ji asalima bata san lokacin da nurse ta kammala ta fita ba,

Dawowar anty Bilkisu ce ta sanya jabir yi musu sallama yatafi, sai da yatafi sannan bahijja tajiyo da kanta, tunda yatafi ahanya yafara tunanin bahijja "lallai yarinyar nan ta iya fushi" yafada aranshi yana murmushi domin tunowa da yayi yanda taki ko kallonsa har yagama zamansa yatafi.

Har sukayi sati daya a asibitin bai samu kan bahijja ba domin kullum idan yaje bata rai take ta murtuke fuska sannan ta kawar da kanta tayanda bazasu ga fuskokin juna ba, yana son yaganta yayi magana da ita amma babu hali kasancewar kullum anty Bilkisu da 'ma' suna dakin,

Kwanansu 9 aka sallamesu amma fa ba karamin dawainiya jabir yasha ba lokacin da suna asibitin nan, daga office ya tura musu driver ya daukesu domin kaisu gida nan kuma bahijja tace ita ba gidan jabir za akaita ba gidansu za akaita,

Mamansu ce ta rarrasheta tace tabari dai su fara zuwa gidan nata tukunna, kwanciya tayi ajikin mamanta tana mai jin wani irin sanyi acikin ranta domin yanzu ta fahinci kwata kwata maman nata bata son bacin ranta.

Tunda suka koma gida wanka kawai tayi tasaka wata yar karamar riga iya cibiya pink colour da yar karamar mini skirt baka,

A falo ta kwanta yayinda anty bilkisu ta ke can tana yi mata yan aikace aikace, tea ta tashi tahada ta fara sha kenan jabir ya shigo kuma da alama ba lokacin ya dawo ba saboda taganshi kanshi babu hula sannan kuma takalmin kafarshi slippers ne,

Kallonta ya tsaya yi yanda tayi kyau sosai cikin kananan kayan da tasaka,

"Bintina me zaki bani nacine? Yunwa nakeji"

Bata amsa masa ba har anty bilkisu ta shigo ta riski maganarshi,juyawa anty bilkisu tayi tafita bayan tayi masa sannu da zuwa Jim kadan sai gata da food flasks guda biyu,

"Ungo kai masa abincin"

Kallon jabir tayi ta kalli anty bilkisu sai kawai ta mike tana zumbura baki ta karba tayi gaba, bin bayanta yayi yana murmushi "yan darun kwana biyu akusa suke" yafada acikin zuciyarshi,

Yanda ta zallake tana tafiya har dariya abin yaso bashi, tana shiga falonshi shima yana shiga, a kasa ta ajiye flasks din ta jiyo zata fice yayi saurin riko hannunta,

"Binti wai wannan fushin har yau baki huce bane?"

Kanta ta kawar batare da tayi magana ba,

"Kiyi min magana ko na matse bakinki yanzu"

"Kar ka matsa cewar sai nayi magana saboda maganata ba zatayi maka dadiba" tafada gamida fusge hannunta ta cire zoben da ya saka mata takama hannunshi ta dora masa atafin hannunshi,

"Ga abunka nan bana so"

Wucewa tayi ta gefenshi yana kallonta bai hanata ba, fita tayi takoma sashenta taci gaba da harkokinta.

Bayan sallar magrib tana zaune asaman gadonta sai gashi ya shigo sanye da jallabiya ruwan toka, har tsakiyar gadon yabita ya tsura mata ido,

"Binti karfa ki zama daya daga cikin mutanen nan wadanda basa yafiya idan aka yi musu laifi"

Juyowa tayi ta dubeshi tasake dauke kanta,

"Ungo zobenki domin ni bana daya daga cikin wadanda suke yin kyauta suna kwacewa domin annabi yace duk wanda yake kyauta yana kwacewa to kamar karene yayi amai sannan ya koma ya lashe amansa"

Hannunta Yakama yasake saka mata zoben yana kallon fuskarta,

"Binti kina son yau na mutsuttsuke wannan dinkin da aka yi miki? Kiyi min magana naji"

Shiru bata bashi amsa ba, maganar anty bilkisu yajiyo a falo sam bai san tana nan ba,tashi yayi yafita, haka suka ci gaba da zama har anty tagama kwana biyun da zata yi mata tayi tafiyarta dama jabir kyaleta kawai yayi yana jiran yaga tafiyar anty bilkisu.

   Karfe 4 yau yadawo daga office, ta kofar baya yabi ya shiga part dinta daga shi sai vest da dogon wandon farin yadin dake jikinsa,

Adakinta ya sameta tana kwance ruf da ciki,amma ba bacci take yiba idonta biyu,

Juyata yayi yana cewa "binti babu kyau irin wannan kwanciyar dan Allah ki daina"

Jin bata amsaba yasashi niyyar daukarta sai kuma yafasa yana cewa "ashe fa bamu taba barin tarihi adakin nan ba ko? Bari yau mu bari"

Tana jinshi amma bata yi tsammanin dagaske yake yiba, jikinta ya shiga yafara aika mata da wasu zafafan sakonni, da dai taga dagaske yake sai tafara kuka,

"Abbu kar wurin dinkina ya farke kayan cikina su fito"

Dariya yayi ya rungumeta yana shafar kanta,

"Bazai farke ba binti kinji".

Bayan komai ya wakana ne bahijja,

  Cikin sigar shagwaba tafara magana, "abbu yanzu ka kyauta min kenan?"

"Ai nabaki hakuri binti, shiyasa ma yanzu nasake baki wani hakurin saboda naga kamar akan kin rasa cikinki ne kike fushi dani"

Girgiza kai tayi "abbu baka sona, baka taba cewa kana sona ba" takarasa maganar tana hawaye,

"Au wannan shine kadai? Wlhi ina sonki binti ina yimiki irin son da bana yiwa kaina"

Koba komai taji sanyi acikin ranta saboda jin maganarshi, daukarta yayi zuwa toilet yayi mata wanka ya fito da ita ya zauna ya shiryata yasaka mata wasu kananan kaya riga da wando, ko masallaci bai iya fitaba agida ya zauna yajasu salla, lokacin bacci yanayi ya shiryata cikin kayan baccinta yar yaloluwar rigar bacci yeluwa iya gwiwa, daukarta yayi zuwa sashensa ya kwantar da ita agefen gado, kusa da ita yaje ya kwanta bayan shima ya shirya, kalamai masu dadi ya shiga yi mata, Kalmar i love you kuwa tajita babu adadi har tayi bacci bata san lokacin da yadaina fadi ba.

   Mata da miji dama sai Allah domin sun shirya sun dinke sunci gaba da zamansu lafiya fiyeda da, zaman da bahijjan ta danyi agida lokacin da suka samu sabani da jabir yabawa mamanta damar fuskantarta sosai wanda har taji itama yanzu tana burin kasancewa cikin addinin islama, hakan ba karamin dadi yayiwa kowa ba, awurin jabir ta karbi Kalmar shahada sannan ta amshi sabon suna wato A'isha, wannan abuda yafaru ya kara sakawa bahijja imani domin yanzu tagane sau da dama abubuwan da suke faruwa arayuwarmu marassa dadi to hanyace kuma ta samun wani babban rabon acikin rayuwarmu domin lokacin da suka samu sabani da jabir ta shiga cikin tashin hankali sosai ashe mabudin alherine agareta bata saniba.

  Yau takama ranar laraba tana kitchen tana aikin kayan kwadayinta jabir ya dawo daga office ya shigo ya isketa tana soya yar gullisuwa,

Abayanta ya tsaya "binti yau kuma me akeyi haka"

"Abbu Yar gullisuwa nakeyi"

Murmushi yayi ya leka cikin kaskon man, "dadina dake duk hanyar kwadayi kin santa binti, da alama nasake baki wani sabon babyn ko?"

"Nidai abbu kabari gaskiya" tafada ashagwabance, juyawa yayi yafita yana yi mata dariya.

Tun daga ranar ya zamana kullum ita kenan cikin hade haden kayan makulashe,yau kam salak ta yanka ta yanka masa tumatur da albasa da dafaffen kwai tasaka maggi da man gyada tafara ci,

Shigowar jabir ne ya katse mata laumar da ta dage tanayi,

"Abbu ga salad"

Akan kujera ya zauna yana kallonta, tacika sosai domin kirjinta yasake cika gashi hips dinta shima yasake budewa sosai,

"A'a binti nagode ci kayanki" yace da ita yana murmushi,

"To abbu ka samo min lalo, anjima tuwon amala zanyi miyar lalo sai in saka masa man shanu da garin yaji"

"Binti ina zan samo miki wani lalo yanzu?"

"Agidan malam za asamu"

"To naji ya isa, zan samo mikin"

Cin salak dinta taci gaba dayi yayinda shi kuma yana zaune yana kallonta, kullum kwadayinta sake karuwa yake domin bata da aiki sai shan tsami gaye, alawar madara, goba mai tsami da makamantansu amma tunda take neman kayan kwadayinta jabir bai taba kin samo mata ba duk abinda take so samomata yake domin har tambayarta yake idan zai fita yau kuma me ake kwadayi ita kam sai dai tayi murmushi tafada masa.

Lokaci yaci gaba da tafiya har cikin nata yafito domin yanzu watanshi 7 duk tabi ta dan kunkumbura, alokacin su ummu al'amin suka fara shirin zuwa gida,

Ana saura kwana biyu su dawo bahijja tafara kwasar kayayyakinta dake cikin dakin jabir domin dama rabi tana dakinta ne rabi tana dakinsa,cike da damuwa tashiga toilet dinsa ta kwaso inner wears dinta dake shanye wanda jabir ya wanke mata,

Kayan kwalliyarta dake kan mirror dinshi tafara tattarewa ranta acinkushe,shima kansa jabir din yana cikin damuwa domin yanzune ya kamata ya bata kulawa ta musamman domin cikin dake jikinta gashi yanzu bata yin minti 30 sai taci abinci shiyasa kullum da daddare sai ya tashi ya hada mata abinci taci koda kuwa cornflakes ne da madara. Ganin ta shiga damuwa yasashi kwantar mata da hankali har ta dan ji sassauci aranta.

Ana igobe ranar da su Ummu al'amin zasu dawo yan uwan ummun suka zo domin gyara mata sashenta, wannan shine karo nafarko da bahijja taga wani wanda ya danganci ummu al'amin.

Duk da tsohon cikin dake jikinta hakan bai hanata shiga kitchen ta dora musu girki ba, tuwon shinkafa tayi musu miyar agushi,

Dauka tayi ta kai musu tasamesu sunata faman aikace aikace domin babu laifi wurin yahada uban datti,

Zama tayi bayan ta ajiye musu abincin, tana nan wurinsu tana dan tattaya su aikin wata daga cikinsu ta zame tafadi "washhh ni jikar mutun hudu" wacce ta zame din tafada tana rike kunkuminta,

"Kijita maimakon kiyi salati zaki wani ce haka sai kace wata sabuwar tuba" wata daga cikinsu tafada, take bahijja taji ranta ya sosu, tun kafin abin yayi yawa ta mike dakyar tafita daga part din ta nufi nata, sam bata ma san cewar jabir ya dawo gidanba,dakinta ta Shiga tana hawaye "wai shin meyasa wasu mutanen suke yiwa wadanda suka karbi musulunci isgili?" Ta tambayi kanta,

Gaban mudubinta takarasa tana kuka domin abin ya bata mata rai, jabir yana daya dakin nata ya jiyo motsinta, binta yayi yaje ya tsaya abayanta tareda jiyo da ita ganin tana kuka yasanya kwakwalwarshi gano abinda yafaru,

"Binti keda yan uwan ummu al'amin ne ko?"

Girgiza kai tayi alamar a'a,

"Kar kiyi min karya binti nasan sune suka saka ki kuka kila cemiki sukayi ke ba asalin musulma bace"

Kwantar da kanta tayi akafadarshi tana goge hawayen fuskarta,

"Kar wannan ya dameki kinji bintina, kema yanzu bakida banbanci dasu wadanda aka haifa acikin addinin, banbancinku kawai wanda yafi tsoron Allah to shine yafi daraja awurin Allah, ko bakida labarin wani mutum wanda za atafi yaki yazo wurin manzon Allah yace ya musulunta, annabi yabashi kalmar shahada yace idan andawo daga yaki zaiyi sauran abubuwan da suka wajaba akansa, lokacin da akaje yakin sai mutumin ya rasu acan da aka dawo sai annabi yake tambayar yana ina akace ai ya rasu sai annabi yace yana aljanna, kinji wani ikon Allah ya shiga aljanna batare da yayiwa Allah salla ba, baiyi azumi ba, baiyi zakka ba, amma mu yanzu nawane daga cikinmu zasu shiga wuta bayan suna salla suna azumi? Kar wannan yadameki kinji bintina, zo muje kiga dinkunanki da na karbo miki saboda zakifi sakewa acikinsu duk bubu nasa aka yi miki"

Murmushi tayi tabi bayanshi yana rike da hannunta har zuwa dayan bedroom dinta.

Ranar da su ummu al'amin zasu dawo bahijja tasha aiki domin tun 9 ta shiga kitchen tafara yi musu kayan saukarsu girki kala kala tayi musu da lemuka masu dadi da kamshi,

Kasancewar saukar rana sukayi ana kiran sallar azahar suka shigo gidan, murna wurin bahijja ba a magana lokacin da sukayi ido biyu da al'amin, ganinshi tayi yasake girma ya zama saurayi,ummu al'amin kuwa ido ta zubawa bahijja aranta tana tunanin cewa ashe badan sun zo ba da sai dai suji haihuwa,

Al'amin ne ya tayata ta gabatar musu da girke girken data tanadar musu, basu fi minti biyar da zuwaba jabir ya taho daga office nan gida ya kancame da murna, ummu tana nanike da jabir duk inda yayi ita kam dama bahijja aranta ta kudiri  niyyar basu kwana 7 kyauta dan haka sashenta ta koma bayan sun gama gaggaisawa, bata sake ganin jabir ba sai da yamma nan dinma tareda ummu suka shigo da al'amin lokacin tana kwance afalo sannu suka yimata suka fice suka barta ita da al'amin suna hirarsu.

  Daren ranar bata samu bacci ba domin dama jabir ne yake yi mata dabara yake kwantar da ita ajikinshi ta yanda ba zasu takura ba ita da babyn, yadda taga rana haka taga dare, asuba tanayi tayi salla ta shiga kitchen ta shirya musu abin karyawa, harda su dambun kifi da albasa da attaruhu ga wani irin hadadden hadi da tayiwa dankalin hausa ta sarrafashi _(masu karatu babu space da nakawo muku yadda ta sarrafa wannan dankalin)_, dakinta ta koma tayi wanka tashirya cikin doguwar riga yar kanti ta koma falo ta zauna.

  Sai misalin karfe 9 da yan mintuna jabir ya shigo sashen nata tana zaune tasaka katon cikinta agaba tana cin taliya da manja mai da yaji,

Tausayinta yaji ya kamashi ganin yanda kafufunta suka dan kunbura gashi daga ganin idonta yasan bata samu bacci ba daren jiya yau kuma ta tashi sassafe tayi musu hidima,agabanta ya zauna yana kallonta ita kuma ta dauke kanta,

"Morning binti, me kike ci ne?"

"Morning" tafada atakaice cikin kishi,

Murmushi yayi "sorry my binti, meyasa bakiyi bacci ya isheki ba? Kalli yanda kafafunki suka kunbura"

Bata bashi amsaba taci gaba da cin taliyarta har tagama, mikewa yayi ya shiga kitchen ya dauko ruwa da sabulu yazo ya wanke mata hannunta ya mayar ya dawo ya dauketa ya nufi dakinta da ita, kwantar da ita yayi ya soma daddanna mata kafafuwanta yana cewa,

"Kar ki sake wahalar da kanki wurin yimana girki, kawai ki yi wanda zakici tunda kin gama yin nauyi yanzu, sannan ki dage da addu'a ki rinka rokon Allah yasa ki haihu lafiya kuma tun yanzu kifara yiwa abinda zaki haifa addu'a domin wannan yana daya daga cikin hakkokin'yaya akan iyaye wato yi musu addu'a tun suna cikin ciki, kuma ki yawaita fadin ya hayyu ya k'ayyum birahmatka astangis akoda yaushe ako wanne lokaci domin samun rahma daga wurin Allah, sannan kowacce safiya kafin kici komai kifara diban ruwa a cup dan kadan idan kuma kinada zamzam to kiyi amfani dashi ki karanta ya hayyu ya k'ayyum birahmatika astangis sau bakwai sai kiyi bisimilla kisha, sai abu nagaba shine yawaita sadaka wannan sune abubuwan da duk wata mai ciki ya kamata ta rik'e musamman ma lokacin da cikin ya girma"

Tana kwance tana jinshi amma bata iya bashi amsa ba saboda baccin da ya hau kanta, babu jimawa bacci ya dauketa, gyara mata kwanciyar yayi ya fita yabarta.

  Daren ranar kuwa tana zaune atsakiyar gado tanata addu'a sai ga jabir ya shigo agogo ta kalla karfe 2 nadare, zama yayi agefenta ya kamo hannunta,

"Abbu me kazo yi? Idan ummun al'amin ta tashi taga ka taho nan ai sai ta zargi wani abu"

Bakinta ya rufe mata da hannunsa "binti ko annabi ai yana ziyartar iyalanshi ba aranar girkinsu ba, nasan dama bakiyi bacci ba why?"

Ido ta mutsuttsuka "abinci zanci"

Tashi yayi yaje ya hado mata Golden morn da madara cikin cup ya kawo mata,akusa da ita ya zauna yasoma bata abaki tana sha,

"Abbu gaskiya wannan babyn naka da mugun cin abinci yake motsi kadan sai inji yunwa"

Murmushi yayi yakai spoon din bakinta "to ai binti dama yanzu komai naki ya karu jinki ankara miki, ganinki ma ankara shi sannan uwa uba shakar numfashinki ma duk ya karu saboda bake kadai bace, duk abinda zakiyi yanzu na mutane biyu zaki"

Fuska ta shagwabe "to abbu kace ya rage cin abinci gaskiya"

"To kai baby ka rage cin abinci da yawa" yafada bayan ya kara kunnenshi ajikin cikin nata, sai da yagama bata abincin tayi dam ya lallabata ta kwanta sannan ya tafi ya barta.

  Washe gari da yamma bayan ya dawo daga office yayi wanka ya nufi part dinta lokacin da ya shiga tana kwance afalo daga ita sai daurin kirji tana shan iska ga al'amin yana tsaye tasakashi yana taka mata tafin kafarta, tafin hannunta da kafarshi,wani irin tausayinta ne ya ziyarci jabir,

"Al'amin jeka wurin ummunka" yace da al'amin yana mika masa hannu domin yin musabaha,shima al'amin din hannu ya mika masa suka gaisa yana cewa "assalamu alaikum abbu"

Fita al'amin yayi shikuma jabir ya fara dan taka mata kafar tata ahankali da kafarshi,

"Abbu yunwa, bani abincina a kitchen" tafada tana kokarin tashi,

Kitchen yaje ya zubo mata jalop din macaroni da kifi wanda ta girka ya kawo mata sai kuma ya tarar da ita tana kuka hawaye sai bin kumatunta yake,

"Binti lafiya"

"Abbu wallahi kacewa babynka ya daina naushina, kullum sai yayita naushina, Allah nima zan rama idan bai daina ba" tafada tana kuka,

Abin dariya yaso yabawa jabir amma sai ya guntse dariyarshi "yi hakuri kar ki rama yunwa yake jine shiyasa yake naushinki"

"Babu wani yunwa kofa kwanciya nayi ta gefen nan sai ya fara naushina idan nasaka rigar da ta dan kamani nanma sai ya yita naushina, Allah ka yi masa magana"

Abincin ya ajiye yamatsa kusa da cikin nata yana murmushi "babyn abbu stop biting your mom kaji, kabarta da dawainiyar da take yi da abbunka ma ya isheta"

Dago kanshi yayi, "basai kin ramaba nayi masa magana zai daina, amma takura shi kikeyi binti shiyasa, kidaina saka kayan da suka matseki wannan bubu din da nakawo miki tun jimawa su zaki rinka sakawa"

Baki ta zumburo ta dauki spoon tafara diban abincin tana ci, karba yayi yaci gaba da bata.

  Tana koshi ya dauketa zuwa dakinta ya ajiyeta akan gado "binti kin kara nauyi da yawa, ki shirya gobe awurinki zan kwana"

Zabura tayi ta tashi tana zare ido "abbu nayafe, kayi zamanka awurin ummu har sai bayan na haihu, nidai kawai kubani aron al'amin mu rinka kwana tare"

"A'a binti idan ke kin yafe to ni ban yafe ba"

"Nidai abbu a'a" tafada tana tuttura baki,

"Saboda yanzu kin gaji dani ko?"

"Nidai abbu ka kawo min al'amin"

"Allah babu al'amin din da za akawo miki kinji nace Allah nidin dai da bakya so nine abokin kwananki agobe"

Komawa tayi ta kwanta tana tuttura masa baki sai kunkuni take "shi abbun nan wallahi wayone dashi kullum kullum sai yayita yimin wayo"  yana jiyota tana kunkunin amma baya iya jin abinda take fada, cigaba da mammatsa mata jikinta yayi yana cewa

"Idan Allah ya saukeki lafiya zan sanar dake wasu hakkoki wadanda suka rataya akanki binti na".


  _Masu karatu kusake hakuri mu hadu a page nagaba inda zamuji karshen labarin da yardar Allah, gaisuwa mai tarin yawa gareku dinbin masoyana masu karanta wannan labarin hakika ina alfahari daku._



*_Ummi A'isha_*🏻
[11/24, 7:53 PM] Ummi A'isha🏻: [11/1, 8:18 AM] Ummi A'isha: *WANI HASKE..!*

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

_131-135_

       

~~~Bata ce dashi komai ba saboda ita yanzu ta kanta take yi domin alla alla take ta rabuda wannan cikin dake jikinta lafiya,

"Binti bakice komai ba ko natafi?" Ya tambayeta bayan ya zauna akusa da kafafunta yana jan yan yatsunta,

"Kafin katafi abbu ka hada min ruwa zanyi wanka" tace dashi tanata faman tutturo masa baki saboda abinda taji yafada dazu,

"Binti menene na fushin ne? Shi al'amin din idan nakawoshi me zai iya yimiki? Nikuwa kinga ko babu komai da daddare zan tashi na hada miki abincinki kici"

"Abbu nikam ka hada min ruwan wanka Allah zafi nake ji"

Mikewa jabir yayi ya shiga toilet dinta ya tara mata ruwan wanka a katon baho ya dawo ya taimaka mata zuwa cikin bathroom din, wankan ya tayata ya rakata dakinta ta zauna abakin gado,cikeda tausayawa jabir yake kallonta domin cikin nata ba karamin girma yayi ba sai kace wacce zata haifi 'yan biyu alhalin kuma a asibiti ance yaro dayane,

Mai ya mika mata ya nufi wurin kayan sawarta ya ciro mata wata koriyar atamfa mai hoton cokali ajiki wadda tasha dinkin bubu,

Ba wata kwalliya mai yawa tayi ba powder kawai ta shafa tasaka kwalli domin kwalli yana da mutukar amfani agun'ya mace yana daya daga cikin abubuwan da yake dawowa da mace martabarta a matsayinta na ya mace shiyasa ko ba zatayi wata kwalliya da yawaba to takan saka kwalli,

Turarruka kala kala ta fesa ta saka doguwar bubu din da jabir ya dauko mata, juyowa yayi yana kallonta bayan ya ajiye mata kayan kwalliyarta agaban mirror dinta,

"Kinyi kyau sosai bintina"

"Nagode abbu amma ni yanzu wanne kyau zanyi da wannan katon cikin" tafada fuskarta ashagwabe,

"Duk da haka kinyi kyau binti"

Hannunshi ta kama suka dauki hanyar falo, "abbu a asibiti ance na rinka exercise amma banda yin shara"

Akan kujera ta zauna shikuma yana daga tsaye yana kallonta,

"Kibar sharar to al'amin zai rinka yi miki sannan aikin ma ba kowanne zaki nayi ba"

"To abbu" tafada tana gyara zamanta akan kujerar, kallonta kawai jabir yake cikeda tausayawa domin ba karamin kumbura tayi ba kullum kunburin sake karuwa yake yi, yar kwallar tausayinta ce ta taru agefen idonshi amma bai bari ta gani ba,

"Binti bari naje salla nadawo ko? Idan nadawo za muje kiga gari"

Murna tafara yi tana dariya "yawwa abbu sai ka dawo"

Kissing din goshinta yayi ya juya ya fita domin zuwa masallaci.

    Ana idar da sallar isha ya dawo gida, agurguje ya shiga dakin ummu ya tarar ta shirya masa abincin dare,kadan yaci, yana ci suna hira har ya kammala ya fita zuwa wurin bahijja,

A falo ya samesu itada al'amin ta baje tana cin tuwon biskin masarar da ummu al'amin ta kawo mata miyar taushe sai kamshin man shanune ke tashi,shi kuma al'amin yana kallon wa'azi atashar manara tv,

"Abbu kazo adaidai" tace dashi tana side hannunta,

Agabanta jabir ya tsugunna yana kallonta,

"Kuma meyasa ba zaki sude kwanon ba? Ki sudeshi binti sai ki samu cikakken lada,ko baki san haka annabi yake yi ba? Nana A'isha tace annabi ya kasance idan yaci abinci yana sude kwanon har sai kwanon ya zamana kamar an wankeshi"

Murmushi tayi ta dauki kwanon ta fara sudeshi itama "Allah ya saka da alkairi abbu"

Mikewa yayi yaje inda fridge yake ya dauko mata ruwa ya tsiyayo a cup ya dawo inda take ya mika mata, kwanon data gama cin abincin ya dauka yakai kitchen ya dawo ya mika mata hannunshi ta kama ya tayar da ita tsaye,

Kallo tabishi dashi yanda yayi kyau sosai cikin bakin trouser da doguwar farar jallabiya ga yar karamar hularta itama fara yasaka sai kace wani balarabe,

Waigawa tayi ta kalli al'amin wanda hankalinsa gaba daya ya tattara akan wa'azin da yake kallo,

"Al'amin bani hijab dina adaki pls"

Tashi al'amin yayi ya shiga dakinta kafin ya fito ta kalli jabir "abbu sunkuyo kaji" tafada ahankali, kasancewar yafita tsayi ba kadan ba ya sanyashi kawo fuskarshi saitin tata,

Kiss tayi masa akan lips dinshi, "abbu kayi kyau ne adaren nan"

Murmushi yayi ya riko hannunta, "hakama budurwa ta tace"

Kallonsa tayi ta dan bata rai "a ina taganka?"

"Gidansu naje" yace da ita yana kallon cikin idonta,

"Yayi kyau" tafada tana kokarin kwace hannunta, daidai lokacin al'amin ya fito hannunshi rikeda zunbulelen hijab dinta, karba tayi ta saka suka dunguma suka fita,

Ahankali suke tafiya akafa shida al'amin sun sakata a tsakiya yana rikeda hannunta amma fa tafiya kadan zata zauna ta huta da haka har suka yi yar tafiya mai nisa.

Basu suka dawo gida ba sai 9:30 nadare suna zuwa tsakar gida ta tsaya ta rike kunkuminta,

"Wash abbu bayana"

Daukarta jabir yayi zuwa part dinta al'amin yana tsaye yana kallonsu yana dariya,

"Abbu da anty ashe kun jima da shiryawa" yafada aranshi tareda juyawa ya nufi part din ummunshi.

Suna shiga jabir bai direta ako inaba sai a dakinta akan gadonta,

"Abbu yunwa bani abinci, amma banda abu mai madara, akwai guntun tuwona a cikin kitchen"

Kitchen din yaje ya dauko mata tuwon ya kawo mata yabata taci yakaita tayi wanka ta fito ta saka doguwar rigar baccinta ta kwanta, kasancewar ta gaji mintuna kadan bacci yayi awon gaba da ita, lullubeta jabir yayi yaje fuskarta yayiwa bakinta kiss yafita bayan ya kashe mata wutar dakin.

    Washe gari tunda misalin karge 4 tafara shirye shiryen karbar jabir domin yace yau itace dashi dole babu yadda ta iya haka ta daure ta fada kitchen tayi masa girki na alfarma tayi wanka ta shirya ta danyi make up sama sama tasaka doguwar riga ta atamfa pink colour,

Ganin tanata zaune shiru gashi babu al'amin yau yatafi wurin jaddi wato kakanshi kamar yadda yake kiran Malam din, kayan jabir ta hado tafita corridor dinta tafara wankewa, kasancewar harda su jeans ya sa duk ta jijjike gashi ta jijjika corridor din ma,

Tana tsaka da shanyar kayan jabir ya shigo,

"Binti me kike yi?"

"Abbu wanki nayi maka na kayanka a asibiti ne akace idan muna yin aiki haihuwa zata fi zuwa mana da sauki"

Hannunta jabir ya kama zuwa cikin falonta "kiga yanda kika jika jikinki, wannan kayan ai sunyi miki nauyi binti, jeki ki sauya kayan jikinki kin ga duk sun jike, ai ba sai lallai wanki ba, ko hidima dani ma zai kawo miki nakuda mai sauki"

Kafada ta make "naki wayon"

Juyawa tayi zuwa cikin dakinta shikuma ya koma corridor din domin gyarawa gashi kayanma duk basu wankuba kasancewar sunyi nauyi da yawa.

Corridor din ya gyara tsaf sannan yabita dakinta, lokacin da ya shiga tana daure da zani tana kokarin saka riga, gabanta ya karasa yakai hannunshi ya dafa cikinta yana murmushi,

"Babyn abbu yau ba a naushin ne?" Ya fada cikeda tsokana yana kallon idanuwan bahijja,

"Ai wlhi abbu shiyasa manzon Allah yace abi uwa kafin yace abi uba saboda mata sunfi maza shan wahala awurin hidimar yara"

Rigar ya karba ya saka mata yana cewa "babu komai binti sakamakon ku yana wurin Allah"

Gefen gado taje ta zauna bayan ya gama saka mata rigar, kusa da ita ya matsa ya dan duka ya dafe gwiwowinsa yana kallonta,

"Muje ki rakani nayi wanka binti"

Mikewa tayi dakyar "nidai abbu shiyasa nace nayafe kace kai baka yafeba, nidai gaskiya...!"

Ta bayanta ya rungumeta, "haba binti bakya son Allah ya baki lada ne?"

"Ina so" tafada cikin shagwaba,

"Yawwa binti ko kefa, maza muje ki rakani"

Binshi tayi amma dakyar take iya tafiya da haka har suka shiga sashen shi, toilet ta wuce kai tsaye ta hada masa ruwa tafito ta iskeshi daga shi sai gajeren wando yana kallon sumar kanshi a mirror,

"Abbu kaima fa dan gayune kullum kai kenan cikin kallon mudubi kamar wata mace"

Murmushi yayi ya juyo yana kallonta,

"Annabi ma ai dan gayune binti shiyasa indai mutum da shi yake koyi to ya kamata shima ya zama dan gayu ba kazami ba"

Hannunshi ta kama "hakane Malam"

"Oh yau kuma sunan da kika bani kenan binti na"

Tare suka shiga toilet din ta zage ta wankeshi tas suka fito tana rikeda dan karamin towel tana tsane masa jikinshi,

Mai ta shafa masa ta taje masa sumar kanshi da sajenshi da gemunshi mai mutukar kyau,

Kayan da zai saka ta ciro masa bayan ta feshe shi da turarruka masu dadi,

Falonta suka koma taje ta hada masa abincin data girka masa mai mutukar dadi, suna nan tare har lokacin salla yayi sai sannan yafita zuwa masallaci.

Rayuwa mai dadi suka ci gaba da gudanarwa har cikin bahijja ya shiga wata na tara, tunda watan haihuwarta ya kama ta dage da addu'a kan Allah ya sauketa lafiya shima jabir ba abarshi abaya ba kullum cikin yin sadaka yake da addu'o'i domin Allah ya sauki bahijjansa lafiya.

Ranar laraba da daddare haihuwa tace salamu alaikum, bahijja tana tsaka da bacci taji ciwo ya turnuketa dolenta ta tashi babu shiri, jabir dake kwance kusa da ita tafara tashi,

"Abbu, abbu bayana, abbu cikina,abbu marata..!"

Tashi jabir yayi yai maza ya taimaka mata suka fita, ganin tana tafiya dakyar ya sanyashi daukarta ya saka acikin mota, harda dan gudunshi yaje ya taso ummu al'amin,

Lokacin da suka isa asibitin karfe 3:30 nadare nan aka karbi bahijja aka nufi maternity da ita,

Tunda aka shiga da ita jabir yarasa nutsuwarsa hankalinsa gaba daya ya gama tashi, ba karamin wahala bahijja take sha ba amma haihuwa shiru tun ana sa rai har aka fara jiran tsammani,

Har asuba tayi bahijja bata haihu ba gashi likitocin sunce zata iya haihuwa da kanta, gaba daya jabir ya shiga damuwa kallo daya zaka yi masa kasan baya cikin kwanciyar hankali,

Har aka wuni haihuwa shiru, jabir na zaune bai san lokacin da kwalla ta tarar masa ba a idanuwanshi, tausayin bahijja yake ji sosai, har yamma tayi babu haihuwa sai bayan sallar isha sannan Allah yayi ikonshi bahijja ta haifo katuwar jaririyarta jajur da ita mai mutukar kama da jabir, kasancewar jininta ya hau sosai ya sa aka yi mata allurar bacci domin ta samu hutu,

Su jabir suna zaune shida ummu al'amin aka sanar musu da cewar ta haihu, hamdala jabir ya shiga yi amma acan karkashin zuciyarshi kuma wani irin tausayin bahijja yakeji marar misaltuwa,

Suna nan suna jira jabir sai waya yake yana sanarwa da yan uwa haihuwar aka fito da bahijja zuwa postnatal lokacin misalin karfe 11 daidai nadare,

Ummu al'amin ce ta fara shiga dakin ta yiwa bahijja sannu ta dauki jaririyar tana kallonta kamarsu daya sak da al'amin dinta lokacin da ta haifeshi lallai jabir jininsa yanada karfi sosai ta raya aranta,

Ajiye jaririyar tayi ta zubawa bahijja abinci tafara ci domin shi jabir yana can wurin hidimar biyan kudaden da asibitin take bukata awurinsu,

Fita ummu tayi domin tafiya gida saboda taji jabir yace yayar bahijja zata zo lokacin,

  Bata jima da tafiya ba jabir ya shiga dakin fuskarsa dauke da farin ciki mai yawan gaske, kusa da bahijja yaje ya zauna yana kallonta cikeda tausayawa,hannunta ya kamo ya rike cikin nashi,

"Sannu _*BAHIJJA*_ hakika nasan kinsha wahala, Allah ubangiji yasa sanadiyyar wannan wahalar da kika shiga yayi miki sakamako da gidan aljanna"

Kallonsa bahijja tayi domin tunda take dashi bata taba jin ya kira sunanta ba sai yau gashi ya iya fadin sunan domin har wani jan sunan yayi,

"Amin abbu" ta amsa mishi ahankali,

"Yanzu inane yake miki ciwo?"

Girgiza masa kai tayi "abbu ga babyn baka dauketa ba"

  Sai alokacin ya tashi yaje inda babyn take tasha kayan sanyi pink colour masu digon fari ajiki, an saka mata hula da safa duk kalar kayan, yarinyar ya zubawa ido yana murmushi sai fito da harshe take tana lasar lips dinta,

"Wannan babyn mai kwadayi ce irin mamanta kalli yadda take lasar lebe" yafada cikeda zolaya,kiran salla yayiwa jaririyar akunnenta na dama sannan ya koma na hagu nanma yayi mata,yayi mata huduba, zam zam da dabino ya ciro daga cikin aljihunsa ya disa mata abaki sannan ya tauna dabinon ya kai bakinshi kan nata ya fara lasa mata, dayake babyn mai kwadayi ce nan tafara shan ruwan dabinon,

Kallonsu bahijja tayi shida babyn "amma kuma komai nata irin na abbunta ne"

Kallon bakinshi tayi ta kalli bakin yarinyar "lahh abbu harfa bakinku iri daya ne"

Kafin ya bata amsa su mamanta da anty Bilkisu sun shigo harda papa, nan jabir ya basu jaririyar ya fita,a reception ya haduda mahaifinshi da sauran matan gidansu suma suna kokarin shigowa, bai bisu dakinba yawuce,

Wurin 12:30 yadawo asibitin lokacin babu kowa sai anty bilkisu jaririyar ya dauka yayi kan gadon da bahijja ke kwance da ita, kallonshi kawai bahijja take saboda yayi wanka yayi fes cikin farar shadda babu hula akanshi.

Wani irin kyau taga yayi mata sosai  domin yafito kamar dan saurayi das dashi,

Agefenta ya zauna yana gyarawa babyn zama ajikinshi,

"Al'amin yayi nacin sai ya biyoni amma ban taho dashi ba saboda dare yayi, sai gobe zai zo yaga kanwarshi"

"Abbu dama ka taho min dashi"

Kallonta yayi yakai hannunshi kan kafafuwanta yafara dannawa ahankali, "binti har yanzu fa akunbure kike"

"Bp dina ne bai sauka ba abbu sai nan da wani lokaci"

"To Allah ya baki lafiya ya raya baby ya kawo kannenta kwana kusa"

Juya baya tayi tana cewa "hum um, ni yanzu sai na dade ban sake haihuwa ba abbu, nasha wahala dayawa"

Murmushi jabir yayi yana kallonta yadda ta juya baya "nima zan so ki huta din amma kuma hakan ba mai yiyuwa bane, kinga ummun al'amin har yau itama bata sake haihuwa ba mutane har cewa suke yi wai nine bana son haihuwa"

Juyowa bahijja tayi "abbu mutane dama ai ba a iya musu sai dai kawai mutum ya toshe kunnuwansa domin duk yanda yake sai sun yi korafi akanshi"

Hira suka ci gaba dayi har wurin daya saura sai da bacci ya dauketa sannan jabir ya ajiye babyn ya tafi gida, haka yan uwa da abokan arziki suketa zarya zuwa asibitin ganin baby, wasu ma bahijja ba saninsu tayi ba,wasu daliban jabir ne wasu kuma ma'aikatanshi, kai bahijja taga jama'a daga karshe ma dr din hanawa yayi arinka shiga dakin da take domin har yau jininta bai sauka ba shiyasa yace akyaleta ta huta.

  Ana saura kwana biyu suna aka sallamesu zuwa gida, anan wata sabuwar hidimar ta tashi, tunda suka koma gida kuma jama'a suke kai kawo, tana daki zaune da babyn a hannunta tanata kukan huda kunnen da aka yi mata domin da a asibitin ba ayi mata ba, ita kanta bahijja ji take kamar itama tayi kukan saboda tausayin yarinyar,

Jabir ne ya shiga dakin ganin baby na kuka ya karbeta yana cewa "meya samu babyn abbu take kuka?"

"Kunne aka huda mata"

"Ina fata ba huda biyu aka yi mata ba?" Yafada yana duban kunnen jaririyar,

"Kai abbu idan biyune menene?"

"Ban so ne abarta idan ta girma in tanada ra'ayi sai tayi da kanta"

Lebenshi ya sawa babyn abaki ya fara jijjigata yana rarrashinta har tayi shiru, shidai tunda babyn nan tazo duniya yake kallonta domin komai nata irin nashine, yanzun ma anyi mata ado cikin blue din kaya riga da wando harda safa da hula tana nade cikin farin towel,

"Zo muje malam ne ya zo ganinku"

Hijab bahijja ta dauka suka fita zuwa sashen jabir inda malam yake, daukar yarinyar yayi yaita yi mata addu'a yana sakawa bahijja albarka.

  Ana saura daya suna mai lalle tazo tayiwa bahijja hadadden kunshi baki da ja sannan aka yi mata kitso kananu three step mai 7,7,shi kam jabir lokacin yana can yana yi musu shirye shiryen walimar da za agudanar ranar sunan, al'amin kam koda wanne lokaci yana nanuke da yar jaririyar kamar zai hadiyeta.

Sai dare sannan jabir ya samu ya shigo gidan, part dinshi yaje ya kira ummu ta hada mishi ruwan wanka ta gabatar mishi da abinci yaci sannan ya kira bahijja,

Yana bakin gadonshi azaune lokacin ummu ta tafi bahijja ta shigo tana sanye da blue din t shirt da bakin skirt na jeans, hannunta dauke da jaririyar,

Kallonta jabir ya tsaya yi ganin yadda tayi kyau, gashi tasha kunshi da kitso, babyn ya karba yana shafar hannun bahijja,

"Kunshin nan yayi kyau binti"

"Nagode abbu" tafada cikin fara'a,

Jikinshi ya jata yahada ta da nashi yaci gaba da shafar kitson kanta da kunshin dake hannunta,

"Binti har yau baki tambayi sunan babynki ba"

"To ai abbu kai nake jira ka fada min"

Murmushi yayi yakama jelar kitsonta guda daya, "sunanta _Bahijja_ mai sunanki kika haifa"

Ya rada mata acikin kunnenta, dago da kanta tayi ta kalleshi "dagaske abbu?"

Sai da yayi kissing din hannunta sannan yabata amsa "dagaske binti, yanzu me zaki kirata dashi?"

"Abbu ni dama imtisal zan nace mata"

"Imtisal? Binti kin san ma'anar imtisal din?"

Girgiza kai tayi alamun a'a,

"To imtisal yana nufin kwatance kwatance ko misalce misalce, kina son arinka kwatanta abubuwa akan yarki?"

Nanma kai ta girgiza "indai hakane to ki hakura da kiranta da wannan sunan, nidama a niyyata mu kirata da *_TASLEEM_* sunan tasleem sunane mai kyau domin yana nufin wanda ya mika wuya, kinga idan kin sake haihuwa idan namiji ne sai mu kirashi da aslam ko?"

Murmushi tayi batare da tayi magana ba,yan yatsunta ya kama yafara ja yana murzasu ahankali,

"Binti kisani yanzu wani nauyi yahau kanki, wannan yarinyar da kika haifa wata amana ce Allah ya baki dan haka ki kula mutuka wurin ganin rayuwarta ta inganta, yanzu lokaci yayi wanda zaki san irin abubuwan da zaki runka yi agaban yarki domin idan ta tashi dake zata yi koyi, duk wata dabi'a taki to ita yarki zata dauka dan haka sai kinyi takatsan tsan sosai wurin sanin irin maganganun da zaki rinka furtawa idan ranki ya baci da kuma idan kina cikin halin farin ciki, sannan ki yawaita yi mata addu'a kan Allah ya shiryar da ita yasa mata imani acikin zuciyarta domin hakkin iyaye ne yiwa yayansu addu'a, yanzu gobe za ayi mata aski da safe"

Baki bahijja ta zumbura "nidai ba za ayi mata aski ba abbu"

Kanta ya shafa yana murmushi "binti yin hakan sauke wani hakkine da ya rataya awuyanmu, annabi yace hakkin yaya akan iyayensu sun hadar da yi musu addu'a tun suna ciki, idan aka haifesu kuma to hakki nafarko shine yi musu kiran salla a kunnensu sannan ayi musu huduba da suna mai kyau domin suna yana da tasiri sosai akan mutum amma ku matan yanzu kowanne suna kiran yaranku kuke dashi indai yayi muku dadi,

to tsaya kiji wani mutum yazo ya samu manzon Allah duk kayan mutumin a yayyage da alamun wahala da tsanani atare dashi, sai annabi ya tambayeshi sunanshi sai ya fada sai annabi yace dole ne kasha wahala arayuwa domin fassarar sunanka tana nufin matalauci, marar arzuki mai shan wahala, dan haka yanzu zaka canja suna ka koma wani domin suna yana da mutukar tasiri ga mutum, to kinga indai hakane to dole ku rinka sanin ma'anar suna kafin ku sakawa yaro, sai abu nagaba shine bawa yaro zam zam da dabino ko zuma lokacin da aka haifeshi wannan ma sunna ce,

sannan ranar suna ana son ayiwa jariri ko jaririya aski idan angama za abayar da sadaka kwatankwacin nauyin gashin da aka aske, hakika yin aski itama wata sunnarce amma mata dayawa bakwa son ayi wa yaranku wannan askin indai matane to wannan gashin datti ne, daudar mahaifa ce asketa shine mafi a'ala,

sai hakki nagaba shine yankawa jariri rago idan namiji ne rago biyu idan kuma macece rago daya wannan shine yazo abisa koyarwar manzon Allah amma babu laifi ga wadanda suke da wadata su yanka fiyeda haka, abu nagaba acikin hakkin yara akan iyayensu shine basu tarbiya da kula da tarbiyarsu tun suna cikin tsumma har kawo lokacin da zasu girma su mallaki hankalin kansu, ya kamata iyaye su rinka koyar da yaransu saukakan kalmomi tun suna kanana irinsu alhamdulillah, bisimillahir rahamanur rahim, masha Allah, astagfurullah,

sannan ki sani duk abinda kike yi to yaronki yana lura dake kuma dake zaiyi koyi a dukkan al'amuransa idan ya tashi zai tashine da dabi'unki yanda kike reacting idan ranki ya baci, yanda kike reacting idan abin farin ciki ya sameki da dukkan abubuwan da kikeyi agaban idonshi shiyasa idan ranki ya baci to anfi son kiyi addu'a idan abin farin cikine ya samu nanma kiyi addu'a sai yaronki yataso cikin tarbiya mai kyau.

Sannan alokacin da yaro ya fara tasowa to yana dakyau iyaye su jashi ajiki su bashi kulawa su sakar masa fuska su rinka zama tare dashi suna tattaunawa suna sanar dashi hakkin Allah akanshi da kuma tsoratar dashi da azabar Allah to irin hakane zakiga ko yaro yataso to zai tasone da shakuwa mai karfi tsakaninsa da iyayensa sannan baya iya sanar da kowa damuwarsa sai iyayensa amma indai bamu ja yayanmu ajiki ba to maimakon su sanar damu sai dai suje su sanar da wasu awaje ko su sanar da kawayensu saboda mu suna jin kunyar fada mana bayan kuma iyaye su suka fi cancanta da zama aminan yayansu na kut da kut domin babu mai rufawa da asirinsa sama da iyaye, ke kanki shaidace akaina nida al'amin nadaukeshi tamkar wani abokina shiyasa ya taso bashida wasu abokai sai ni tun yana yaro nakan zaunar dashi nayi wasa dashi muci abinci tare muje salla tare shiyasa ya taso da dukkanin irin halayena da dabi'una sannan baya iya boyemin damuwarsa ko sirrinsa, ko mafarki al'amin yayi sai ya fada min har takai akwai lokacin da nasanar dashi cewa zaiyi mafarki, mafarkin  balaga nafada masa cewar duk lokacin da yayi wannan mafarkin to ya girma ya zama cikakken namiji wanda zai iya yiwa mace abinda zata haihu kuma yanzu anbude masa littafin rubuta ayyukansa na alkairi da sharri nayi masa nasihohi masu ratsa jiki, to haka ake son iyaye su zama domin su kansu yayan suna samun sassaukar rayuwa"

  Gaba daya jikin bahijja yagama yin sanyi, "nagode abbu Allah yasaka maka da alkairi yayi maka sakamako da gidan aljanna"

Jaririyar ta karba ta tashi zata fita idonta taf da kwalla, bin bayanta jabir yayi ya rakata har kofar falonta sannan ya juya ya koma sashensa,

  Koda bahijja ta kwanta bacci sai takasa tanata tunanin maganganun da jabir ya sanar da ita lallai indai hakane to tarbiyar yara is not easy sai dai ahada da addu'a.

  Washe gari aka radawa yarinya suna bahijja tasleem, tuni mai jego da baby sun shirya cikin kaya na alfarma, anyi girke girke da toye toye danma jabir ya hana taron suna yace walima kawai za aje ayi a central mosque nacikin garin,

Karfe uku nidai ummi A'isha muka bazama nida aminiyata *Cwt Kausar Luv* muka nufi inda za agudanar da walimar abakin gate muka ci karo da bestynah *Phertymah Xarah* itada kawayenta Sadiya berry da Miss Aysha, nan muka rankaya zuwa ciki, yanda wurin ya cika dam da al'umma yasa bana iya hango kowa ganin haka nai ta maza nakutsa ciki nan nayi arangama da kawata *Khadija Sidi* gilashinta na ara nasa a idanuna take nafara hango mutane radau nan naga marubuta kamar dansu aka shirya walimar, gefena nadama nafara dubawa nan na hango  Lubabatu mai Tafsiri itada Benaxir Omar sai handamar dambu suke, gefensu kuma Maman Shakur ce itada bestynta kuma kawata Humaira sukuma sunata shan kunun aya kowaccensu ta rike roba hurhudu, jan hannun Kausar da pherty nayi muka kara gaba tsayawa nayi ina kallon ikon Allah domin Jidda Aliyu na hango itada Rash Kardam sai wawar alala da dambu suke gasu Anka da Ummu abrar agefensu sukuma suna shan zobo can bayansu kuma S A Aziz ce da stylish bch da zeebeels, da ummu adnan da Aneeluv, ga Anisa didi da Ummu sabreena da baby Lilmeerahcute da khadija chafe sai faman daukar selfie suke ana son asamu na dorawa akan dp,

Bayana na waiwaya nan na hango kannena su Mimi bee da Autar hajiya da Afra mai yar bincike da Futhahatul khair da Kdeey yan matan junior sunsha jar atamfa iri daya mai hoton jaririyar ajiki "ohh wadannan yara da shisshigi kuke ko a ina kuka samo wannan atamfar" nafada azuciyata na kara gaba domin nan nabar su cwt Kausar da besty pherty domin su samar mana take away saboda kar mu koma gida a zero,

Wurin da nahango kawayena na nufa Fiddausi Sodangi itace agaba sai kwasar dambu take duk ta bata fuskarta da maiko ga takwarorina zagaye da ita suna hanbadar jalop A'isha Dansabo da A'isha A Gambo da A'isha Munay da Aisha chuchun gaye ko waccensu ta ajiye mayafinta agefe, daga bayansu kuma Xarah BB ce da takwararta Pherty BB da Teemah Cool sai Hafsa Bunza su dinma ba abarsu abaya ba wurin wawason dambu da lemon kwalba, "yaufa an samu na bati dole ayi cin keta" nafada nawucesu domin basu ganni ba kasancewar idonsu yana kan kwanon da suke wawaso,gaba dasu kadan na hango dotar ubbe da Jidda samusa,da E'eeshmal da amrah ga billy a giro sai wawaso suke yi adaron shinkafa duk kayansu ya baci da maiko,karawa gaba nayi ina dariya har nazo kujerar karshe nan naga ummi adnan da Qurratul ayn da basma erlele sun zage sun takarkace sai zukar kunun gyada suke dukkaninsu hankalinsu yana kan kular kunun dake gabansu gashi duk sun diddisa kunun ajikin kayansu, "masha Allah" nace na nemi wuri na zauna ina zare idanu.

Bayan anci ansha anyi kat ne mai jego bahijja ta shigo taci gayu cikin wani orange colour din leshi tasha katon mayafi tana rikeda jaririyarta tasleem wacce tasha ado cikin riga da skirt yan kanti jajaye masha Allah jaririya kam katuwa ce,

Malamar da zatayi wa'azi ce ta shigo wato malama safiyya Ummu Abdoul, anan ta gabatarwa da mata lecture mai taken *Tarbiyyar yara a musulunci* malamar tayi namijin kokari mutuka wurin fadakar da mata yanda ya kamata su kula da tarbiyar yaransu tun daga haihuwa har zuwa girmansu da lokacin da ya kamata afara raba musu makwanci,

Walimar ta kayatar mutuka amma duk nacin masu naci basu samu ganin jabir ba domin baizo wurin ba yana can shima yana tasa hidimar.

Karfe 6 daidai aka tashi daga walimar kowa ya kama gabansa, su bahijja na komawa gida tayi wanka da ruwa mai zafi ta fito daure da towel yayinda anty Bilkisu tana zaune tana yiwa tasleem wanka, ko jabir bata nema ba tasaka rigar baccinta ta kwanta nan bacci ya dauketa,

Jinta shiru da jabir yayi yasashi binta dakinta bacci ya sameta tanayi ga tasleem agefenta ta kunna musu air condition,

"Binti angaji kenan" yafada ahankali bayan yayi musu kiss ita da babyn akumatu, a.c din ya kashe musu ya fita zuwa part dinshi.

  Haka bahijja taci gaba da rainon jaririyarta gashi anty Bilkisu ta dage wurin shiryata domin gabaruwa ta samo mata take tafasa mata tana zama aciki ga wani hadadden tsumi na sassaken baure wanda ake dafashi da kayan kamshi irinsu citta da kanumfari da zuma da ta dage wurin hada mata, daga bahijjan har babyn duk sunyi bulbul dasu sunyi kyau gwanin sha'awa, ranar da suka yi 40 aranar anty Bilkisu tatafi bayan jabir ya hada mata goma ta arziki.

  Nan fa jabir da bahijja aka bude sabon babin soyayya domin tattarasu yayi ita da tasleem zuwa dakinshi inda ya basu kulawa ta musamman, har tafita daga girki kullum jabir cikin tattalinsu yake dama kuma da rana tasleem din hannun al'amin da ummunshi take wuni.

  Haka rayuwa taci gaba taci gaba da gudana agaresu cikin jin dadi, yanzu watan tasleem biyu, misalin karfe 2 nadare tasleem sai kuka take tsalawa bahijja domin yan kwanakin kukan dare take yi,

Tana zaune ta rasa yadda zata yi mata gashi ba ranar girkinta bane domin idan ranar girkinta ne baccinta takesha tabar jabir da raino, jabir ne ya shigo yana sanye da kayan bacci,

"Meya sameta" ya tambayeta yana kokarin daukar tasleem,

"Abbu haka kawai rigima dai" tafada kamar tayi kuka,

Daukar tasleem yayi yafara jijjigata yana lallashinta sanin yagama da hidimar ummu al'amin ya sashi fita da tasleem din zuwa bedroom dinsa, kwanciya yayi ya dorata asaman kirjinsa yana jijjigata ahaka suka yi bacci shi da ita, ita kam bahijja dama tun kafin jabir yafita daga dakinta ma tayi kwanciyarta amma tana jin soyayyarshi tana karuwa acikin jinin jikinta domin tasan jabir nadaban ne acikin maza saboda samun namiji wanda zai yi irin abinda jabir yake yi ba abune mai sauki ba.

   Washe gari kuwa tunda jabir ya fita tasleem take yi mata kuka gashi jikinta yayi zafi dau, zama bahijja tayi tai tagumi tana kuka takasa aikata komai har la'asar tayi,

  Dawowar jabir kenan ya shiga sashenta nan ya samesu suna kuka itada tasleem,

"Binti menene"

Tasleem din ta mika masa tana hawaye,

"Ina jin bata da lafiya tunda katafi take min kuka gashi babu abinda nayi agidan"

Jin jikin tasleem da zafi yasashi fita domin kaita asibiti sai alokacin bahijja tasamu tayi ayyukanta tashiga wanka tafito tayi kwalliya,

Tana daura dan kwalinta jabir ya shigo dauke da tasleem akafadarshi tana bacci,kwantar da ita yayi ya nufi bahijja,

"Binti zazzabi ke damunta da ciwon ciki amma dr ya dubata ya bata magani"

Tasowa tayi ta shiga jikinsa tana murmushi "sannu abbu mun gode"

Fuskarta ya lukuce "ba godiyarki nake bukata ba kulawarki nake bukata"

Kanta ta cusa akirjinsa "abbu ina jin tsoro"

"Name?"

"Ciki" tafada ahankali,

"Ai bazan baki yanzu ba sai kin yaye tasleem"

Bude baki tayi tana kallonshi da niyyar yin magana, bakinshi ya hada da nata ya dauketa zuwa dayan bedroom dinta yana cewa, "kin kusa ki dauki dawainiyata ma ke daya domin su al'amin nanda 3 weeks zasu koma.

Tana kwance ajikinshi tana ta faman zuba masa shagwaba,

"Abbu nidai ka samo min yar aiki wacce zata rinka yimin rainon tasleem, akwai wata Xarah ta iya raino sosai"

Sake rungumeta yayi sosai ajikinshi, "kiyi hakuri binti kiyi dukkan ayyukan gidanki da kanki sai Allah ya baki sakamako mai kyau"

Sake kankame juna suka yi suna dariya.

BAYAN SHEKARA 20

*

  Wata mata na hango tana sanye da katon hijabi har kasa awani wawakeken fili wanda mata suka cikashi tana yi musu wa'azi, ta kwashe fiyeda awanni 3 tana yi musu wa'azin kafin ta kammala ta rufe da addu'a,

Wurin motarta ta nufa ta bude ta shiga tana murmushi akusa da wani saurayi ta zauna wanda kallo daya zaka yi masa ka gane jabir ne sak "dan autan abbu yau kai kadai ka taho"

Murmushi shima saurayin yayi "ammun yau ban samu yan rakiya ba duk sunki
rakoni sunce awurin abbu zasu zauna"

"Kace yau gidan namu acike yake da yan jikoki" tafada tana dariya,

"Ai kuwa dai ammun"

"Allah dai yayi muku albarka abdul halim" tace dashi tana murmushi, tafiya kadan ta sadasu da gidansu, nan suka shiga tun kafin tafito wasu kyawawan kananan yara kimanin su 10 suka taho suka rungumeta suna "jaddati oyoyo"

Rungumesu tayi suka shiga cikin falonta inda jabir ke zaune da wasu yaran yana koya musu alifun ba'un,

"Abbu yau haka gidan namu ya zama?"

Dagowa yayi ya kalleta "ga masu gyara gida nan sun zo yau"

Cikin dakinta ta wuce ta zauna tana hamdala acikin ranta domin hakika jabir ya zama *_WANI HASKE_* acikin rayuwarta domin ta sanadinshi duk danginta dake okene sunzo sun musulunta awurin jabir gashi yara 9 Allah ya azurtasu da samu ita dashi tun daga kan tasleem, abdullah, abdulrahman, abdulrahim, abdul hamid,abdul rashid, abdul gani, abdul malik sai dan autansu abdul halim,gashi yanzu harda jikoki suke dasu wurin su goma sha biyar,

Shigowar jabir ce ta katse mata tunanin da take yi,

"Yanmatan abbu ki shirya danki al'amin ya biya mana umarah"

Yafada yana zama akusa da ita,

"Allah saka masa da alkairi, shima Allah ya bashi masu yi masa" tafada idonta narai narai,

"Kar kiyi min kuka, nidai yanzu kulawa nake son kibani domin nakada wadancan jikokin naki zuwa gidan zoo suda uncle dinsu abdul halim"

Murmushi tayi ta kwantar da kanta ajikinshi "abbu baka gajiya dani, ban taba ganin sauyin fuska atattare dakai ba"

Hannunta ya kama ya rike cikin nasa,

"Binti duk auran da aka ginashi akarkashin koyarwar ma'aiki to haka yake kasancewa, shiyasa annabi yace maza su auri mace mai addini domin itace matar da kullum tana tsufa tana sake rike addininta, maimakon kaji tana fita daga ranka sai dai kaji tana sake shiga cikin ranka, sannan duk soyayyar da aka yita saboda Allah to tana dorewa"

Hannunshi ta matsa "nidai nayi sa'a, ina addu'a Allah yabarni dakai har lokacin da zan koma gareshi"

"Kizo muje mu kula da junanmu kidaina yi min maganar rabuwa"

Yace da ita gamida daukarta zuwa special room.

*ALHAMDULILLAH*

Anan nakawo karshen littafin wani haske ina addu'ar Allah yatara mu acikin ladan ya yafe mana kuskuren dake ciki, duk wacce ta karanta wani haske taji dadinshi to ta taimaka tayiwa ummi A'isha addu'a akan Allah ya biya mata bukatarta.

 
  *SADAUKARWA*

Na sadaukar da wani haske gareki kawata *BAHIJJA BEBEELO* (marubuciyar D'a na kowane) dake da dukkan masoyan littafin wani haske, Allah ya raya miki yarinyarki iman, nagode kwarai da kaunarki agareni.

*TUKWICI NE*
agareki bestyna *PHERTYMAH XARAH* (marubuciyar littafin matar sadiq),Allah yakara dankon zumunci agaremu.

*DOMINKU NE*
Masoyana masu yi min fatan alkairi akoda yaushe.

*JINJINA GAREKI*

Uwar dakina *HAUWA M JABO* nagode da kulawarki.

*KINA RAINA*
Aminiyata mai share min kukana *CWT KAUSAR LUV*, hakika kinfi karfin kawa agareni, ke ta dabance awurina ina kaunarki kawata, Allah yabarmu tare,tabbas banda kamarki.

*FATAN ALKHAIRI*
Gareki tawan kawata *KHADIJA SIDI* nayaba miki sosai hakika ke ta musamman ce agareni.

Gaisuwa ta musamman gareku masoya yan uwana marubuta, ina addu'ar Allah ya kara muku basira da hazaka, yaci gaba da taimakonku acikin al'amuranku, ya kara muku baiwa mai amfani,ya baku lada aduk inda kuka yi daidai, ya yafe muku a inda kuka yi kuskure.

Gaisuwa mai dunbin yawa gareku masoya wadanda suke karanta rubutuna suna yimin fatan alkairi akoda yaushe, nagode muku sosai ina kaunarku mutuka kuma ina addu'ar Allah yabar zumuncin dake tsakaninmu, duk wanda yake kaunar ummi A'isha ko kuma yake kaunar rubutunta ko yaji tana burgeshi ko yaji yana sonta to UMMI A'ISHA loves you too, sai mun hadu acikin labari nagaba da yardar mai sama Rabbi Azimu.



_*Ummi Shatu*_