Friday 23 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. END

_®HWA_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

  _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _Wannan Shafin nakune Besty phertymah Xarah keda Cwt Kausar luv (aminiya ta kwarai)_

   _*52*_

~~~Tunda taje asibitin suke waya da shaddad tana waya tana duba patients dinta, duk wanda ya shiga office din zaiji tana magana kasa kasa ga earpiece makale akunnenta, har tagama duba patients din ta nufi round har lokacin suna tare awaya itada shaddad tana fada masa dakin yara zataje round,

Su Kansu basu san tsawon lokacin da suka dauka tare awayar ba, kullum haka suke shafe lokuta masu tsawo suna waya idan suna gida kuwa suna manne da junansu,

Akwana atashi babu wuya har an kammala ginin asibitin maryama furnitures ne kawai ba azuba ba aciki, daukar shaddad tayi ta kaishi yaga asibitin, ya sanya mata albarka suka dawo gida,

Kwana biyu baya Dada yayi mata waya yasanar mata ya siyo mata furnitures din daga kasar India shine gudun mawarsa, lokaci kankani aka yiwa asibitin fenti aka zuba masa komai da komai aka rubuta suna asama MARSHANN HOSPITAL,wato Maryam, shaddad, nu'aima & nu,aim,

Cikin yan kwanakin aka shirya walimar bude asibitin, duk yan uwa da abokan arziki sun halarci walimar, sannan ga wani babban gida kato da yake cikin asibitin wanda yasha kayan alatun more rayuwa aciki shikuma gidan maryama ne wanda ta gina musu zasu koma idan har shaddad ya yarda, lokacin data fada masa murmushi yayi yace,

"Shikenan nayarda tunda dan kwali yaja hula.." Murmushi maryama tayi ta manna masa kiss a gefen kumatunsa, nan da nan suka yi packing din kayansu suka koma sabon gidan, maryama ta debi ma'aikata da yawa kowacce lalura ta yara akwai likitanta, sannan duk da haka tana zuwa asibitin da take aiki tana ganin patients gashi kuma state university suma sunyi inviting dinta kan taje ta rinka yin lecturing acan a matsayin contract, nan abubuwa suka taru suka cakude mata danma dai business dinsu itada anty maijidda ba komai take yiba anty maijidda dince take fita dubai ta shigo musu da kaya,

Duk wannan ayyukan basu hana maryama kulawa da mijinta ba, bashi kulawa take yi sosai sannan har lokacin bata da mai aiki balle mai raino, ita dashi ne suke yin komai na aikin gidan, sai idan zata fita office ne take daukar su nu'aima ta kaisu gidan Dada kafin shekara ta zagayo su saka nu'aima a makaranta,

Agajiye lis ta dawo Gida saboda sai da tafara zuwa office tayi aiki sannan ta wuce university tayi lectures har guda biyu daga nan ta dawo asibitinta taga patients sannan taje gidan Dada ta dauko yara ta nufi gidanta,

Wanka tayiwa yaran ta shiryasu ta dora girki tabasu suka ci suka kwanta bacci har lokacin bata yaye nu'aim ba domin watanshi goma sha daya,

Wanka da ruwa mai zafi itama tayi ta fito nan taga shaddad kwance agefen gadonta,

"Yaushe ka shigo mijina? Allah sarki daga gani kaima ka gaji"

Janta jikinsa yayi ya rungumeta,

"To ya zanyi tunda na zama mijin hajiya.."

Murmushi tayi tana kallonsa tana ji yana shirin rabata da towel din dake daure ajikinta,

"Kayi hakuri idan har nagaza a kulawar da nake baka, yanzu fada min awurin da na gaza sai na rage ayyukana ko nadaina zuwa office ko nadaina lecturing na zauna na baka kulawa"

"Ni baki gaza ba ako ina baby, aikin mace ko kasuwanci dama bashine abin kyamatar ba abin kyamatar shine ta fifita aikinta ko kasuwancinta fiyeda kulawa da mijinta nidai ni kika fi fifitawa akan komai kuma nasan baki gaza ta ko ina ba sai dai har yau kin kasa bawa nu'aim kani"

Rungumeshi tayi tana murmushi, "wai ai bari nayi idan ka auro yar 18 years sai ta basu kanin.."

Rufe mata baki yayi, "ai ni yanzu babu wacce zan sake aurowa domin ke Allah ne ya zaba min ke yabani, da atunanina bazaki soniba bazaki girmamani ba bazaki girmama yan uwana ba, nazata karamar yarinya ita zan iya juyawa ita zata fi bani girma, ashe abin ba haka yakeba ke din duk da tsananin kyawunki da ilminki da dukiyarki da shekarunki hakan bai hanaki girmamani da yimin biyayya ba, lallai Allah shine tsarkakken sarki, hakika Maryam ke wata sashe ce babba na rayuwata, kuma naji dadi da rayuwarki tayi kamantacceniya da wani hadisi na manzon Allah wanda yace ka bibiyarwa mummuna da kyakkyawa sai kyakkyawan ya shafe mummunan daka aikata a baya, tabbas wannan magana haka take idan mutum yayi abu marar kyau to ya kamata ya aikata abu mai kyau agaba to sai yasamu kyakkyawan sakamako,

Godiya ga Allah wanda ya kyautata rayauwarki da halittarki sannan ya mallaka min ke a lokacin da ban zata ba"

Soyayya ya shiga gwada mata bai bari ta sake yin magana ba.

  Cikin satin shaddad yazowa maryama da labarin cewar anturasu kasar Canada zasu tafi ta ruwa, ganin maryama kawai yayi idonta fal da kwalla,

"Navy yanzu irin tafiyar nan da ka taba yi zaka sakeyi ka tafi kabarni?"

Rungumeta yayi yana dariya, "wasa fa nake yi miki, wasu aka tura amma banda ni aciki"

Rungumeshi tayi cikeda farin ciki, acikin kwanaki biyu kacal ta biya musu kudin ziyartar kasashe biyu, zasuje India medical check up domin kafarta tana dan ciwo kuma tana son aduba musu lafiyar yaransu daga nan sai su wuce madina umarah,

Shi shaddad ma bai san ta biya musu ba sai da visa din ta fito nan suka tattara suka tafi yana mai cikeda farin ciki da saka mata albarka saboda kudinta sam bai rufe mata ido ba, duk abinda ya kamata na harkokin gida da dangi yimasa take babu rowa bare kyashi,

Rayuwa mai dadi suka gudanar awadannan kasashen tun a india ta yaye nu'aim daga can suka wuce umarah, sati uku a kasa mai tsarki suka yi suka dawo Nigeria, suna dawowa aka kawo kayan auren khairat kanwar shaddad nan maryama ta zage tayi mata kayan kitchen hadaddu duk wani abu na amfanin kitchen babu wanda bata siyaba takanas tayi order aka kawo mata daga kasar waje,

Sai da ta kashe kudi sama da dubu dari biyar a siyayyar kayan khairat, tun ana saura sati shida bikin sukaje suka kai kayan Kaduna itada shaddad, lokacin da sukaje tana cewa hjiya shaddad ne ya siyi kayan shikuma yana cewa itace daga karshe dai har hajiya tagane itace ta siya taita sanya mata albarka.

  Lokacin bikin ma itace ta zama amara kirjin biki idan ba sani kayiba zaka zaci kanwarta uwa daya uba daya ake aure saboda duk abinda aka nema zata cire kudi ta siyo daga ance babu kaza zata dauki kudi ta siyo, _(chaii Mata mu tashi mu nemi kudi kodan taimakon mazajenmu, arzikin mace yana sawa asamu zaman lafiya saboda rokon miji bani kaza bani kaza zai ragu kuma in mun samu kudin banda yiwa miji rowa dan Allah, kar muce yaci kudinsa muci namu, ahadu aci gaba daya shine zaman tare..)_

Rayuwarsu maryama da yan yaransu guda biyu haka taci gaba da tafiya cikin farin ciki har yaran sun fara zuwa makaranta, amma daga su maryama bata sake samun wani cikin ba, shaddad ya samu karin girma yazama canal, muna yimusu fatan cigaba arayuwarsu....

    Alhamdulillah!!

Anan littafin maryama ya kammala bawai dan ya kare ba sai dai kawai gajiya da nayi sannan kuma masu karatu nasan kun kosa kuga an kammala maryama queen, Allah ya yafe mana kuskuren dake ciki ya tara mu acikin ladan tare.

*SADAUKRWA*

Sadaukarwar littafin gaba daya takice kawata kuma aminiya ta jini, MARYAMA QAUMI GAIDAM, ina alfahari dake Allah yabarmu tare har abada.

*TUKWICI*
Tukiwcine agareku,

ANTY MAIJIDDA MUSA

AUTAR HAJIYA

ANTY ZAINABU (Anty sis)

KHAIRAT DANDAWAKI

Da dukkan masoyan Ummi Shatu.

Fatan alkairi ga yarana masu albarka MUHAMMAD (Sultan) &NANA A'ISHA,Allah ya raya minku cikin imani da aminci.

Jinjina ga dunbin masoya na wadanda suke kaunata suna bibiyar rubutuna sannan suna yimin fatan alkairi akoda yaushe, nima ina alfahari daku sannan banida kamarku saboda kun zama ni nima na zama ku da bazarku nake dancing, ina yimana addu'ar yin ibada cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya karbi ibadunmu ya amsa mana addu'o'inmu sannan ya biya mana bukatunmu, sai mun hadu acikin littafi nagaba mai suna MIJINA SIRRINA, wanda zaizo muku bayan salla da yardar Allah, Ummi Shatu ta gaisheku kyauta,duk wani masoyin Ummi Shatu to itama tana kaunarshi.

*_Ummi Shatu_*

MARYAMA SARAUNIYA.. 50,51

[5/25, 9:20 PM] Ommee A'esherh: _*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

     _Sako ga autar hajiya, in banda abinki auta ai ni ban hanaki mijina ba,matsalar kawai yace daga ni babu k'ari.._

     _*50*_

~~~Ko minti biyu batayi da kwanciya ba taji shigowarshi, tsugunnawa yayi a saitin kanta ya dafata yana bin kyakkyawar rigar baccinta da kallo,

"Bacci zakiyi?"

Kai ta daga masa saboda idanuwanta har rufewa suke yi saboda tsabar bacci, "to yi addu'a"

"Nayi" ta bashi amsa batare data bude idonta ba,yana tsugunnen har bacci yayi gaba da maryama,ya jima yana tsugunne yana kallonta yana ta faman shafa kyakkyawan sajen dake fuskarta wanda ya tafi ya lullube goshinta, ya jima ahaka kafin ya tashi ya fita, lokacin da ya fita har su anty maijidda sunyi bacci itada anty babba.

   Washe gari ya kama saura kwana biyu suna, tun sassafe maryama tayi wanka ta shirya saboda yau za ayi mata kunshi da saloon, wani leshi ta saka baki mai adon ja ajiki, kyawun da tayi ba kadan bane, gashi tako ina kamshi ne yake fita daga jikinta,

Tana rikeda jaririnta a hannu tace da anty maijidda,

"Anty bari nakai boy ya duba dadynshi yayi masa sannu bashida lafiya"

"Sai kun dawo"

Anty maijidda tafada tana kallon anty babba domin jiya da daddare sunga lokacin da taje dakin shaddad sannan shima sunga lokacin da yasake binta dakinta,

Fita tayi da jaririn akan kafadarta ta shiga dakin shaddad, yana tsaye agaban mirriro yana zira rigarshi, bakar t shirt mai dogon hannu, jaririn ta kwantar taje gaban shaddad ta tsaya tafara balle mishi botir din jikin rigar tana murmushi,

"Ya jikin?"

Hannuwanshi yasaka gaba daya ya zagayeta ya rungumeta,

"Da sauki,ina nu'aima?"

"Tana can tanata bacci bata tashi ba"

"Da ace ta tashi da ta rakani kasuwa, ina son inje in siyo muku duk abubuwan da suka kamata, gashi ma dai banida kudi wallahi.."

Jan hancinshi maryama tayi, "nima kuma ina son zaka kaini saloon anjima idan khairat ta gama yimin kunshi kuma dole zaka biya kudin kunshi da na saloon"

Fuskarshi ya hada da tata yana murmushi,tareda jan hancinta, "ai ko baki fada ba ma dole na nabiya domin matata aka gyara min tasake yin kyau"

Murmushi tayi taja shi suka karasa bakin gado ta dauki jaririn ta dorashi akan cinyarshi, "gashi dama gaisheka yazo yayi"

Tana bashi jaririn ta fita zuwa dakinta bata jima ba sai gata ta dawo rikeda ATM card dinta a hannu, zama tayi a kusa dashi ta mika mishi ATM card din,

"Naji kana cewa baka da kudi, gashi kaje ka ciri duk yanda zaiyi maka.."

Kallonta yayi sai kuma yayi murmushi ya jijjiga kansa,

"Bazan karbi kudinki ba baby, kudin wurina zai isa na siyo muku komai da komai"

Fuska ta bata ta mika masa hannu alamar ya bata jaririn, hanata jaririn yayi ya kwantar dashi agefe yana cewa,

"Muhammad kwanta anan inje in rarrashi mamanka mai daru.."

Sai lokacin tasan Muhammad zai radawa jaririn domin har yau basuyi maganar sunan da zai sakawa yaron ba.

Kusa da ita ya matsa yasa hannuwanshi guda biyu ya tallafe kumatunta,

"Baby menene nayin fushin? Kin san dai bana son bacin ranki.."

Sake daure fuska tayi, "ai dama nadade da sanin baka daukeni a matsayin abokiyar zama ba, baka daukeni a matsayin sirrinka ba, sannan ni ka daina kirana da wani baby, budurwarka da kakeso yar 18 years wacce har kabata number ta dan ta kirani tayi min rashin kunya ita ya kamata ka kira da baby"

Murmushi yayi sai kawai taji ya rungumeta,

"Allah yabaki hakuri, wallahi ke sirrina ce saboda akwai sirrin dake tsakaninmu wanda duk duniya babu wanda ya sanshi sai ubangijin da ya haliccemu, kuma ni ban bawa Amira number ki dan ta kiraki taci miki mutunci ba.."

"To ya akayi tasan shekarata 30 lokacin da ka aureni indai ba kaine ka fada mata ba.."

"Ni nafada mata amma bawai da wani abu nafada ba, haba baby tayaya zanje naci mutuncin iyalina awurin wacce ba iyalina ba? Nifa kawai cewa tayi tana so ku gaisa shine nabata number ki, anan take tambayata wai ta girmeki ko kin girmeta shine nace kin girmeta shekarunmu daya dake... Dan Allah kiyi hakuri"

Shiru tayi domin dama ta dade da hakura amma mamaki takeyi sosai wai yau itace shaddad yake bawa hakuri,

"Kin hakura? Uhm baby nah..?"

Dagowa da kanta tayi tana kallonshi shima itan yake kallo,

"Na hakura amma sai ka tafi da ATM card din nan ka ciri kudin siyayyar da zaka iyo mana"

"Baby bana son in rinka taba miki kudinki.."

"To ai ba tambayata kayiba, nice nayi niyya na baka, haba shaddad nifa kafi haka awurina wallahi duk abinda nake dashi zan iya mallaka maka, nasan abinda kake jin tsoro baka son inyi maka gori watarana, to ka kwantar da hankalinka bazan taba goranta maka ba domin mun zama daya, account dinma da babu wani kudi mai yawa aciki duk ginin asibiti ya lashe kudin..."

Sake rungumeta yayi cikeda kauna, "gashi kuma mijinki talaka ne balle ya kara miki wasu kudin ki karasa ginin.."

Dariya tayi tana shakar kamshin turaren active man dake fita daga jikinshi,

"Ina son mijina ahaka komai babunshi, da mai kudi da talaka duk daga Allah suke"

"Nagode baby Allah yayi miki albarka ya albarkaci rayuwarki data yaranki"

Dadine ya ratsata sakamakon addu'ar da taji yayi mata, sakinshi tayi tana kallonsa,

"Zanje saloon saboda wacce take zuwa tayi min agida tatafi garinsu"

"To idan kin shirya sai ki fada min in kaiki"

"Tom, bari nakawo maka breakfast.."

Daukar jaririnta tayi ta fita shaddad yabita da kallo cikeda so da tausayawa irin na masoya,tana fita suka yi kicibus da anty maijidda,

"Nazata ai acan zaku zauna keda jaririn" anty maijidda ta fada tareda karbar jaririn tayi gaba saboda tun dazu yan barka suka zo, kitchen maryama ta wuce ta karbowa shaddad breakfast takoma takai masa,

Zama tayi tafara bashi shima yana bata har suka koshi, tare suka fito tana rikeda farantin kwanukan da suka ci abincin, a falo yasamu su hajiya ya gaisheta sannan ya dauki nu'aima wadda ke zaune tana shan tea.

Zama maryama tayi khairat ta zana mata jan lalle mai kyau, sai da yayi jajur sannan aka cire, nan ta je ta sake yin wanka tana jiran shaddad ya dawo ya kaita wurin saloon domin ya fita da motar tata,

Shaddad bai dawo gidanba sai da mangariba, siyayya ce ya iyo mai yawan gaske duk abinda za a bukata saboda shagalin suna ya siyo shi sannan ya siyo raguna biyu manya,

Shigar musu da kayayyakin da ya siyo yayi cikin kitchen ya wuce dakinsa, mintuna kadan ya fito ya shiga dakin maryama yace ta fito ya kaita saloon din,

Anty maijidda sai fada take tana cewa ahakura da wannan saloon din, ko kwana 7 da haihuwa bata yiba amma har zata fita, hajiya ce tace abarta taje ai yanzu zasu dawo, nan maryama ta dauki hijab ta fita tana tafiya ahankali saboda har lokacin bata gama warwarewa ba,

A mota ta samu shaddad ta shiga,kallonta ya tsaya yi kafin yakamo hannayenta masu taushi wadanda suka sha jan lalle yafara gani,kissing din tafin hannunta yashiga yi dakyar ya saketa ya tashi motar suka tafi cikin gari,

Wani shagon saloon ya kaita ta shiga  tabarshi acikin mota yana jiranta,

Tafi minti 40 kafin ta fito bayan angama yi mata gyaran gashin, zama tayi tana kallon shaddad,

"Allah sarki mijina yi hakuri yau sai wahalar dakai nake yi naki barinka ka huta"

Haske ya kunna acikin motar yana kallonta,

"Karki damu baby ai kinfi haka, muga gyaran kan da akayi miki"

Bude mishi tayi yagani maryama badai gashi ba, domin gashinta har kafadarta yake bakikkirin mai laushi,shafa gashin yayi,

"Nidai nayi dace duk wani abu mai kyau wanda ake bukata awurin mace matata ta mallakeshi, shiyasa babu ruwana da sha'awar na matan waje saboda nasan nima ina dashi agida na"

Murmushi maryama tayi ta mayar da dan kwalinta ta daura ta lulluba hijab dinta ajikinta,

"Banda zuga dai navy.."

"Ba zuga bace baby gaskiya ne, wallahi kina da duk wani abu wanda yake sakani farin ciki shiyasa lokacin da na tafi burtaniya idan kewarki ta dameni surarki kawai nake tunowa sai naji hankalina ya kwanta nasamu nutsuwa, gashi awurin akwai mata kala kala dayake wurin boda ne amma ni ko kadan basu taba burgeni ba saboda nasan inada wacce tafisu acan gida tana jirana ni kadai"

Murmushi maryama tayi ta shafi kumatunsa, "Allah sarki navy ashe dai kaima kayi missing dina wannan lokacin duk da baka sona sannan kana zargina da kula wasu maza awaje"

"Nifa dama najima ina sonki baby, kawai zafin kishine yake damuna idan natuno yanda naganku keda wannan yaron naziru a office dinki yana gyara belt din wandonshi, da yanda kike zuwa guest house wurin manyan mutane sai naga kamar ko akwai abinda suka taba amfana dashi daga jikinki amma ni bana zarginki ko kodan shiyasa ma da nayi tafiyar nan hankalina bai tashiba saboda nasan zaki kula min da kanki.."

"Lokacin da kaga naz yana gyara belt din wandonshi wallahi nice nayi masa fada saboda sai kaga bai daura belt ba kawai yabarta haka wandonshi yana faman sabulewa shine nayi masa magana to yana cikin gyarawa kai kuma ka leko, alh bashir kuma da nake zuwa wurinshi shine yayi min cuku cukun siyan wannan filin da nake gina asibiti na.."

Rungumeta shaddad yayi yana shinshina kanta yana shakar kamshin saloon din da akayi mata,

"Shiyasa annabi (S.A.W) acikin wani hadisi yace kabar abinda kake kokwantonsa izuwa ga wanda baka kokwantonsa, duk yanda ka kai ga ganin mutum mai laifine awurin Allah to karka kuskura ka yanke masa hukunci har sai ka ganshi ido da ido yana aikata laifin, nidai dama nadade da sanin cewar matata tawace ni daya.."

Kwace jikinta tayi tana murmushin dole amma azuciyarta tausayinshi take ji sannan dama tun jimawa ta fahimci cewar yanada tsananin kishi akanta saboda lokacin da basa shiri ya taba ganin text massage awayarta wanda dr fahad ya turo mata cewar yana nan yana jiranta bazaiyi aure ba har ranar da boko haram zasu kashe sojan mijinta sai ya aureta, masifar da shaddad yayi lokacin ba kadan bace har fahad din ya kira awaya agabanta yace masa to ko ya mutu shi bai isa ya auri matarsa ba,koda ma ya aureta to shi bai taka matsayin da ya takaba domin a bazawara ya aureta shikuwa tun tana budurwa yayi rayuwa da ita,

"Wai tunanin me kike yi?" Maganar shaddad ta dawo da ita cikin hayyacinta,

"Tunani nake nabar jaririna agida"

Murmushi yayi yafara driving, "naga alama dai kina ji da wannan jaririn"

"Yana kama da kaine shiyasa naji yafi shiga raina akan nu'aima"

"Nikuma kinga nafi son nu'aima saboda komai nata irin nakine sannan bata wahalar min dake kinyi dogon suma har ana tunanin kin mutu ba.."

Dariya maryama tayi tana kallonsa, cikeda farin ciki suka koma gida.....

*_Ummi Shatu_*
[5/25, 9:20 PM] Ommee A'esherh: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_

_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_

   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _Gaisuwa ga yan haske writers association, Afra bhai,Asmy b Aliyu, Ayusher mohd,Billy galadanchi,faxy fation, Phertymah Xarah,Hajja ce,Kausar luv, Khaleesat hydar,Lilmeerah cute,miss Xoxo,miss billy,Maman Shakur,maman Khadija,Nana diso,Nuceey love, Queen Mimi, Rash kardam and rest....,Allah yakara hada kanmu ina alfahari daku..._

    _*51*_

aishaummi.blogspot.com

~~~Ahaka ranar suna tazo aka gudanar dashi cikin farin ciki da nishadi, yaro yaci suna Muhammad amma zasu kirash da nu'aim,

Aranar da akayi sunan mutane suka fara bajewa basu zauna ba kamar lokacin sunan nu'aima, iya hajiya da anty maijidda ne kawai suka zauna sai anty babba da khairat saboda yan aikace aikacen da za ayi washe garin suna amma su dinma aranar suka ce zasu tafi da zarar sun gama aikin saboda shaddad kiri kiri yanzu yake nuna musu so yake su tafi subarshi daga shi sai matarshi da yaranshi,

Hakance kuwa ta faru washe gari tunda asussuba su anty maijidda suka tashi suka gama soye soyen nama suka gyara gidan sannan suka yi girki, karfe goma na safe har sun gama dukkan abubuwan da zasuyi,

Waya shaddad yayiwa maryama yace yana kiranta, tashi tayi ta fita nan anty maijidda tabita da kallo tace,

"Idanma kunyi hakuri yanzu zamu tafi mu bar muku gidanku"

Dariya anty babba tayi, "ai yaron nan jarababbe ne wallahi daga gani baya barinta ta huta"

"Itama ai dama ta dade da sanin irin mijin data aura dan tun kafin ayi bikin na kora mata jawabi"

Dariya anty babba tasake yi, "to mudai ai yau zamu basu sarari suga filin gidansu"

Maryama na shiga dakin shaddad ta sameshi kishingide agefen gado nu'aima kuma tana jikinsa tana bacci,

"Baby kin san meye? Har baba lami karta zauna tabi su hajiya su tafi Kaduna idan da yiyuwar ta dawo zanje na dawo da ita"

"Haba mazaje har baba lamin ma tafiya zata yi? Aikin zai yimin yawa fa ga yara ga kula dakai sannan ga hidimar gida..."

Mika hannu yayi ya kamota zuwa jikinsa,

"Kema mazajen zaki kirani dashi kamar hajiya?"

Murmushi tayi,  tafara wasa da zobunan gold din dake sanye a yan yatsun hannunta,nu'aima ya gyarawa kwanciyarta ya tashi zaune yana kallon fuskarta, ba karamin kyau tayi ba sannan ga barima ta gold akan hancinta,

Hannunshi yakai kan barimar yafara juyata acikin kofar bular dake kan hancinta, ba karamin kyau hudar hancin tayi mata ba saboda komai tayi yimata kyau yake,

"Idan baba lami tatafi ai gani, zan rinka yimiki duk aikin da kika sani.."

Murmushi tayi ta kalleshii, "karfa ka sake magana daga baya"

"Bazan sakeba.."

Yafada tareda kai bakinshi kan nata,kallonshi tayi tana kokarin tashi, "ka fito fa saboda may be sun gama shiryawa"

Fita tayi ta koma wurinsu anty maijidda wadanda suka kammala shirin tafiya,

"Uhm hajiya dadyn nu'aima yace baba lami ma basai ta zauna ba.."

Kallon anty babba anty maijidda tayi suka hada ido tareda saka dariya a lokaci guda,

"Danme zata tafi, idan ta tafi waye zai rinka tayaki sauran ayyukan gidan?"

Hajiya tafada cikin fada,

"Hajiya babu komai nima zanyi ai"

Fadin haka da maryama tayi yasa hajiya fahimtar cewar itama maryaman tafi son baba lami din tatafi,

"To shikenan sai mu tafi ai inyaso duk lokacin da kuka bukaci yar aikin na samo muku wata"

Shaddad ne ya shigo cikin dakin yana kallon su hajiya, "hajiya idan kun shirya muje na kaiku tasha.."

"Ah mun shirya, ku tashi mu tafi"

Kallon maryama khairat tayi, "adda maryama sai mun sake dawowa suna next year tunda na nu'aima ma last year muka zo gashi yanzu this year mun zo na nu'aim"

Dariya anty babba tayi, "ai kuwa dai wata shekarar ma muna tafe"

Ita dai maryama bata cemusu komai ba saboda hajiya na wurin, drewar din gadonta taje ta dauko kudi sabbi yan 200 rafa guda ta bawa shaddad, "gashi idan ka kaisu kabasu susha ruwa ahanya"

"Ke babu kudin da zamu sake karba duk, wannan hidimar da kikayi mana har sai kin kara da kudi?"

Hajiya tafada bayan ta tashi  tana yafa mayafinta,

"Hajiya danma ban nuna miki kayan data baniba masu kyau wallahi har kala biyar kuma duk bata sakasu sosai ba sai munje gida zaki gani.." Khairat tafada tana murna,

"To angode Allah dai yasaka da alkairi yayi miki albarka maryama, Allah ya raya miki yaranki"

Tafiya suka yi bayan ta rakasu waje, sai da taga tafiyarsu sannan ta koma cikin gidan,wanka ta shiga tayi ta fito ta shirya ta tsuke sosai cikin riga da wando English wears, rigar pink colour ce mai budadden kirji agaban rigar an rubuta, _love makes heart to beat sweeter.._,sai matsattsen bakin wando wanda ya bayyanar da hips dinta sosai,

Tana tsaye gaban mirror tana taje gashin kanta shaddad ya shigo, tsayawa yayi yana kallonta ta jikin mudubin domin indai ba sani kayiba to idan kaga maryama bazaka taba zaton ta haihu ba,

Zuwa yayi ya rungumeta ya dora kansa akan kafadarta yana kallonta ta jikin mudubin,

"Kinyi kyau sosai.."

Kiss yayi mata a kumatu ya karbi pink colour ribom din hannunta ya daure mata gashin nata yajata suka fita zuwa falo, kwanciya sukayi acikin kujera suka fara yiwa junansu hira irin ta masoya, har shi kanshi shaddad sai da yayi mamakin maryama saboda yanda ta dage tana ta yimasa labarai kala kala wanda ta sani,

Sai da suka fara jiyo kukan nu'aim sannan suka bazama sukaje kai masa agaji.

  Cikin farin ciki da kaunar juna sukayi wunin wannan ranar shaddad kuwa yana gida babu inda yaje, har 12 suka kai suna kallon wani American film a tashar MBC action,

Kashe komai shaddad yayi suka nufi dakinsa, wanka maryama ta shiga yabita cikin toilet din dole sai tare suka yi suka fito suka shirya cikin kayan bacci suka kwanta bayan sun saka nu'aim da nu'aima a tsakiya.

  Karfe 9 nasafe maryama ta tashi nan taga kan gadon babu kowa sai ita kadai, fita tayi nan ta ga ko ina na gidan agyare tsaf anshare anyi mopping dinshi ga turaren wuta yana tashi, hatta nu'aima da nu'aim shaddad yayi musu wanka ya hadawa nu'aima tea tana sha, shi kuma yana kitchen yana soya chips da kwai,

Dakinta ta fada nan dinma ashare agoge sai kamshi yake, hatta toilet din an wankeshi sannan ya tara mata ruwan da zatayi wanka dashi, wanka tayi tana cikeda farin ciki ta fito ta shirya cikin wata hadaddiyar doguwar riga ja mai dan karamin hannu, gashinta kawai ta daure ta fita saboda yunwar da take ji,

Shaddad yana shirya table ta karasa wurinsa,

"Sannu navy gaskiya kasha aiki"

Murmushi yayi, "karki damu baby ai kinfi haka agareni, ni bawanki ne saboda kasancewarki SARAUNIYA,zanyi dukkanin iyawata saboda ganin na hutar dake baki wahala ba"

Kujera ya ja mata ta zauna ya zuba mata breakfast din, tare suka ci suna ciyar da junansu har suka kammala.

  Tun daga ranar kullum kafin maryama ta tashi daga bacci shaddad ya tashi ya gyara gidan sannan ya shirya musu breakfast yayiwa su nu'aima wanka.

  Yau ma tun kafin ta tashi ya gyara gidan yayiwa su nu'aima wanka yana tsaka da shiryata yana yimata kwalliya maryama ta fito ta shiga wanka har ta fito su shaddad basu gama kwalliyar ba, kwalliya tayi ta shirya ta saka wani blue din materia riga da skirt sun kamata sosai saboda yar kibar data kara yi,

"Sweetheart kinyi kyau.." Haka shaddad yaketa fadawa nu'aima bayan ya gama yimata kwalliyar yasaka mata riga yar kanti baka doguwa,

Fushi maryama tayi ta fita tabarsu a dakin ta koma falo ta fara karyawa tana rikeda nu'aim, binta falon shaddad yayi yana murmushi yaje ya rungumeta,

"Menene abin fushin saboda nacewa daughter dina tayi kyau ke ban fada miki ba? Ai ke ba fada zanyi da bakiba nuna miki zanyi ki gani"

Kafin tayi magana ya kama lips dinta sun jima ahaka yana nuna mata yanda tayi kyau din sai da kyar tasamu ta kwace bakinta,

"Gaskiya kadaina wannan aikin gidan, ai idan wani yazo yagani sai ace na mallakewa hajiya d'a na mayar dashi mijin tace.."

Hancinta ya dan ja yafara shafa barimar dake kai, "nifa kafin kice kika mayar dani ba mijin tace ba, kafin kice na aikata duk abinda kike so.."

Kullum da safe sai shaddad yayi mata komai sannan yake tafiya office, haka suka kasance kullum, gashi idan yadawo gida sai yayi ado yasha turare ya tura nu'aima ta kirata wai yazo hira, kamar wasu saurayi da budurwa haka zata shirya ta fito falo hirar,

Yauma da misalin karfe 8 nadare hirar yazo ya tura nu'aima ta kirata,

"Kije kice bana nan.."

Dariya yayi ya kirata awaya, "yau kuma har dasu karyar ba anan?"

Kwantar da nu'aima tayi akusa da nu'aim ta fita, yana zaune yana kallo a tv sai kamshin turaren precious yake yi yana sanye da wandon sojoji da wata t shirt tasu,

Akusa dashi ta zauna ta kwantar da kanta kan kafadarshi ta rikeshi,

"Yau fa ni bacci nake ji"

Kanta ya fara shafawa daga karshe ya dawo da ita kan cinyarshi ya rungumeta,

"To muyi hirar ahaka har kiyi baccin"

Hira yake yi mata tun tana cemasa "uhm" har yaji shiru, sai da yagama kallonshi sannan ya dauketa a kafadarshi ya kaita daki, dakinshi ya koma yasaka kayan bacci ya dawo dakinta ya kwanta ajikinta ya rungumeta.

   Rayuwa mai dadi suke yi har ranar da su maryama suka cika kwana 40 cif da haihuwa, ai ranar taga hidima awurin shaddad, sallah sukayi raka'a biyu ya dauketa zuwa toilet suka yi wanka, wata kyakkyawar night gown mai zanen butterfly ajiki ya saka mata ya dauketa zuwa dakinshi wanda ya gyarashi ya shimfida wani bedsheet pink and blue colour tsakiyarshi kuma zanen wani katon butterfly ne,

Shafa hoton butterfly din tafara tana murmushi, wani farantin silver shaddad ya hawo mata dashi kan gadon wanda yake dauke da gasasshiyar kaza da fresh milk da fruits,

Tashi zaune tayi tana kallonsa tana jin soyayyarshi tana karuwa acikin zuciyarta, fresh milk din kawai ta dauka tasha sai fruit din shima ba kowanne ba apple da water milon kawai tasha ta tashi zataje wanke bakinta, riketa yayi bayan ya ajiye farantin a kasa,

"Kibarni nima nasamu sauran dake bakinki mana.." Bai barta tayi magana ba yafara tsotsar bakinta, wata soyayya mai sanyi yafara nuna mata cikin nutsuwa da so,

  Yau kam maryama ta yarda cewar shaddad yana sonta dari bisa dari kuma natane ita kadai, soyayyar da ya nuna mata bazata misaltu ba amma karshen kauna ya nuna mata tamkar zai hadiyeta dan so, wani bacci mai dadi mai cikeda nutsuwa tayi bata iya tashi ba sai 7 nasafe, tana bude idonta taga shaddad agaban mudubi yana shiryawa da alama fita zaiyi saboda umifom ne ajikinsa, ta cikin mudubi ya hangota ya sakar mata murmushi, juyawa yayi yana kallonta,

"Makararriya..."

Murmushi tayi ta tashi yayi saurin zuwa ya dauketa kamar wata jaririya, jikin maryama mai kyaune babu wanda zai kalleta ya tsammaci tafi shekara 22 shiyasa shaddad baya jin wahalar daukarta, cikin toilet ya kaita,

"Sorry baby, nine ko? Gashi zan fita yanzun nan.."

"Kaje babu komai sai kadawo"

Kissing dinta yayi agoshi ya fita, wanka maryama tayi ta fito tayi salla ta fita, yau ma babu inda bai gyaraba hatta su nu'aima ya shiryasu tana zaune a falo tana kallon carton,

  Satinsu biyu suna shan soyayya suka shirya suka tafi kaduna sukayi kwana uku daga can suka wuce abuja suka yi kwana biyu, kayan gyaran jiki anty maijidda ta tattarawa maryama ta bata tana cewa "naga wannan mijin naki bita zaizai ne"

Dariya maryama tayi, "ni anty ai wadannan kayan basu dameni ba well women kawai nakesha kuma shima har gyara mace yake shiyasa yawancin matan manya shi suke sha"

"To koma dai menene idan kana da kyau ka kara da wanka dan haka dole ki kara da wadannan".

  Kwana biyu sukayi suka koma Lagos, washe gari maryama ta koma office ta fara zuwa aiki, gidan Dada takai nu'aima da nu'aim ta ajiyesu saboda yanzu dada babu inda yake zuwa yana gida.

_*Ummi A'isha*_

MARYAMA SARAUNIYA.. 42-46

[5/21, 8:48 PM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

  _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

_Gaisuwarku ta dabance, Benaxir Omar,Lubabatu m/tafsir,Khaleesat Hydar,Hafsat Bunza,Teemah cool & A'isha (maman Khadija)_

  *_42_*

aishaummi.blogspot.com

~~~Komawa tayi tai kwanciyarta saboda yau ta fadawa shaddad abinda ke cikinta, wunin ranar akwance tayi shi babu abinda ta iya tashi tayi har dare yayi, shirin bacci tayi ta sakawa kofarta key ta kwanta,

Kwananta uku agida bata fita ko ina har saida taji tafiyarta tafara komawa normal sannan ta fara zuwa aiki, ai shaddad kuwa na ganin haka yafara kaiwa dakinta ziyara duk daren duniya kullum cikin kokawa suke dakyar ya hakura ya rabuda ita ta huta na tsawon sati biyu, aranar da ta cika sati biyun aranar ya ritsata a daki,

Tana daure da towel ta gama shan tea kenan ya shigo,

"Lafiya?"

"Kinfi kowa sanin in lafiyarce ta kawoni ko kuma sabanin haka, zan cikawa mahaifiyata umarni ne"

"Kar kayiwa hajiya karya.."

"Nine makaryacin?" Ya tambayeta yana dosota, kafin tayi yunkurin tashi har ya take kafarta da tashi,

Daukarta yayi zuwa saman gadon, sanin irin bakar azabar da tasha rannan yasa yau bata bawa kanta wahala wajen biye masa suyi kokawa ba, rabuwa tayi dashi ya karaci sha'aninsa yayi abinda yake so sai dai kuma yau sai taji har tafi rannan shan wahala saboda dinkin dake jikinta, ji take kamar ana bin jikin dinkin ana farkewa,

Tana son tayi kuka amma bata son yaji ya samu damar rainata, sai da tasha mutukar wahala kafin ya kyaleta ashe barinta yayi ta huta,

"Yau na hadu da jarababben miji ni maryama nashiga uku, wannan gayen kasheni yake son yayi ne?" Ta fadi hakan acikin zuciyarta, juya kanta kawai take yi saboda azaba,

K'ankameshi tayi sosai kamar zata koma cikin cikinsa, yana son ya tafi ya koma dakinsa amma haka ya hakura saboda ta rirrikeshi kamar wacce take tsoron wani abu, ahaka suka kwana tana kankame dashi saida safiya tayi wurin karfe shida sannan tafara sakin doguwar ajiyar zuciya,ahankali tafara sassauta rikon da tayi mishi tana jan zuciya da haka har ta sakeshi gaba daya, shidai yana kwance yana kallonta, jin ta bar jikinsa ta koma gefe ta kwanta yasashi tashi ya shiga toilet dinta, in banda kamshi babu abinda bathroom din yake kamar ba ashiga ciki, yasan dama dole tayi tsafta saboda kasancewarta likita,

Tsaftace jikinsa yayi ya fito yana kallonta har lokacin tana kwance tana bacci taja bedsheet ta rufe rabin jikinta, dakinshi ya koma yayi salla ya kwanta.

  K'arfe bakwai da yan mintuna maryama ta samu dakyar ta tashi taje tayi wanka tazo tayi salla, wata doguwar shimi kawai ta zira takoma ta kwanta nan take jikinta yafara ciwo, samu tayi bacci ya dan dauketa,

Cikin bacci shaddad yaji ana bugun kofa, kamar a mafarki yake jin bugun, bude idonshi yayi ya tashi ya fita daga shi sai gajeren wando da t shirt ruwan toka,

Yana bude kofar yaga hajiyarshi ce itada khairat,

"Hajiya sannunku da zuwa.."

"Yawwa mazaje sannu"

Basu hanya yayi suka wuce ciki shikuma yana biye dasu a baya, tiryan tiryan khairat take tafiya har zuwa dakin maryama wacce ke kwance tana dafe da goshinta,

"A'a ko baku tashi bane?" Hajiya ta fada tana kallon shaddad,

"Ehh wallahi hajiya"

Cikin bacci maryama take jin maganganunsu ahankali ta bude idonta ganin hajiya da khairat yasa tafara kokarin tashi tana murmushi amma ta kasa, komawa tayi ta kwanta tana cije lebenta,

"Hajiya sannunku da zuwa, khairat yanzu kuka zo?"

Hajiya ce ta amsa da,

"Yawwa sannu maryama, daga gani ma bakya jin dadi, yi kwanciyarki basai kin tashi ba"

Juyawa tayi ga shaddad wanda ke tsaye abayanta, "mazaje wuce muje"

Fita suka yi daga dakin sai khairat ce ta zauna agefen gadon tana kallon maryama cikeda tausayawa,

Daya dakin da babu kowa hajiya ta shiga itada shaddad a bakin gadon dake cikin dakin ta zauna, shaddad ya durkusa ya fara gaisheta  maimakon ta amsa gaisuwar sai cewa tayi,

"Mazaje me kayiwa yar mutane ta kasa tashi..?"

Shiru yayi saboda jin tambayar da hajiya tayi masa, "to ni yanzu me zancewa hajiya?", yafadi acikin zuciyarsa kafin ya lalubo amsar da zai bata yasake jiyo muryarta,

"Bada kai nake magana ba? Kafada min abinda kayiwa yarinyar mutane ta kasa tashi"

"Hajiya ni babu abinda nayi mata"

"Shine nazo na sameta akwance tana son ta tashi amma ta kasa ahakan babu abinda kayi mata?, mazaje ka fita daga idona wallahi akan yarinyar nan zanci mutuncinka zan sassaba maka"

Shiru yayi amma kuma duk kunya ta kamashi saboda yasan hajiya tagane abinda yafaru shi da yasan zata zo yauma ai da hakan bata faruba,

"Ka rage wanan zafin ran naka akan iyalinka.."

"Hajiya dan Allah kiyi hakuri insha Allah bazan sake ba, dan Allah kiyi hakuri"

"Shikenan Allah yayi muku albarka, mun sameku lafiya?"

"Lafiya lau hajiya"

"Yau bazaka fita aikin bane?"

"Yanzu zan shirya natafi"

"To madalla, sai katashi kaje ka shirya ai tunda mu muna nan"

Tashi yayi ya fita ya shiga dakinsa ya fada wanka,

Su hajiya na fita maryama ta rike hannun khairat,

"Khairat taimaka min naje nayi wanka"

Riketa khairat tayi ta tashi ta shiga bathroom ta dade acikin ruwan zafi sannan tayi wanka ta fito, kafin ta fito har khairat ta gyara mata dakin ta koma kitchen ta dora musu abin karyawa, shiryawa tayi ta saka wani material dinkin riga da skirt ta fita dakin da hajiya take, cikin fara'a da kulawa hajiya ta amsa gaisuwarta suna gama gaisawa hajiya tace ta koma dakinta ta kwanta kafin khairat ta kammala abincin karyawa, tashi tayi tafita tana tafiya ahankali, zata shiga dakinta shikuma shaddad ya fito da uniform ajikinsa, cikin dakinta ta shige ba tareda ta kalleshi ba, kwanciya tayi tana tuna rayuwarsu da shaddad, yanata ikirarin baya sonta baya sonta amma kuma yafi kowa iya fada mata Kalmar so da kalmomin kauna adaren jiya da daren farkonsu, ko kuma dan ba acikin hankalinsa yakeba shiyasa baya sanin lokacin da yake fada oho,

Shigowar khairat ce ta katse mata tunaninta, zama tayi akusa da ita,

"Sannu adda maryam wai dama haka sojoji suke"

Kallonta maryama tayi, "yayanki mugu ne khairat, sam bashida tausayi.."

Dariya khairat tayi "kai adda maryam agaban nawa zaki rinka cewa yayana mugu ne?"

"Wallahi mugu ne na karshe, dan rainin hankali yanata ikirarin wai zai auri yarinya yar 18 to da ace ita ya aura yayiwa abinda yayi min da ina jin kasheta zaiyi, mugu kawai"

Dariya khairat tayi "adda maryam maida wukar, ki huce dan Allah, wai dama sai jiya akayi first night din?"

"Khairatu kenan wannan second night ne amma yafi first night wahala, first night dinmu sai da naje aka yimin dinki, to jiya yabi dinkin yaso farkeshi shiyasa nace miki yayan nan naki mugune"

Karaf sai a kunnen shaddad kalmar data fada ta karshe wai yayan nan naki mugune, shidai bai san akan me suke magana ba amma yasan maganarshi ake kuma dashi maryama take,

"Ke khairat wai baki gama hada abincin bane? Ina saurine fita nake son nayi"

Tashi khairat tayi da sauri tana fadin "sorry yaya Navy, wallahi mantawa nayi.."

Bin maryama da kallo yayi wacce ke kwance idanuwanta arufe, fita yayi yabi bayan khairat zuwa kitchen,

Titsiye khairat yayi wai sai ta fada masa me maryama take fada mata harda kiranshi da mugu,

"Yaya bafa maganarka ake yiba"

"Wallahi karya kike maganata kuke yi, me kuke cewa?"

"Nima namanta mema muke cewa Allah"

Rabuwa da ita yayi ya fita yakoma wurin hajiya ya zauna, kayan breakfast din khairat ta kinkima takaiwa hajiya nasu itada shaddad ita kuma itada maryama ta kai musu dakin da maryaman ke ciki,

Ruwan tea kawai maryama ta iya sha jin ta danji dama dama yasata tashi taje wurin hajiya ta zauna lokacin shaddad yafita.

  Khairat ce tayi komai agidan hatta abincin rana itace ta girka musu, ita maryama tana wurin hajiya suna hira, yamma likis shaddad ya dawo gidan komawa dakinta maryama tayi khairat ta bita tana dariya,

"Adda maryama nimafa ina son in auri soja"

"Ki aureshi yarinya ke zaki gane kurenki, sojoji jarababbun matane.."

"Hakane amma ai ke kinyi dace adda maryam, Yaya Navy baya shan komai koda sigari baya sha sannan babu ruwansa da matan banza, amma kinga shi yaya Yusuf yana shan sigari.."

"Yayanki kam nima na shaideshi anan sai dai akwaishi da mugunta"

"Ah adda maryam wannan kuma ai tsakaninku ne"

Haka suka cigaba da hirarsu har magriba tayi,

Ba karamin dadin zuwansu hajiya maryama tajiba, koda dare yayima tareda khairat suka yi kwanciyarsu, sannan kullum khairat ce take yin komai nagidan har saida maryama ta warware sannan suke yi tare, satinsu daya suka fara haramar tafiya, sha tara ta arziki maryama ta hada musu suka tafi amma kafin hajiya tatafi saida ta barwa shaddad sallahun lallai lallai blessing mai aikin maryama tadawo gidan saboda ta ringa ragewa maryama ayyuka,dolensa babu yadda zaiyi yace to,

Adaren ranar da su hajiya suka tafi ya hana maryama sakat, danma wannan karon bata sha wuya kamar wancan ba,

Kyaleta yayi yakoma dakinsa asuba nayi yasake dawo mata, ita dai takasa gane wannan jaraba irinta shaddad, babu yanda ta iya dole haka zata jure tunda tagamu da gamonta,

Washe gari blessing tazo da kayanta, nan maryama ta zaunar da ita ta gaya mata cewar banda zama a falo idan shaddad yana nan sannan ba itace zata rinka girkiba ita dakanta zatayi girkinta sannan banda shiga dakinta da na shaddad, ko me take bukata tabari idan tafito sai ta tambayeta saboda yanzu ba irin da bane lokacin da tana gida,

Maryama tayi hakane saboda tasan halin shaddad idan jarabarsa ta motsa da rana ma hanata sukuni yake,

Tunda blessing ta dawo gidan sai maryama ta samu saukin aikin da take yi lokaci kadan tayi kiba tayi kyau,

Tana kwance afalo sanye cikin english wears blessing ta fito hannunta rikeda maggi kala kala,

"Anty kinga wannan maggin kina sone ko in dauka.."

"Blessing karki matso nan da maggin nan tsaya daga nan bana son warinsa"

Tsayawa blessing tayi daga nesa tana nuna mata maggin daga karshe dai maryama tace ta dauka tabata saboda ya dan jima a ajiye a store,

Tana nan kwance shaddad ya fito yazo kusa da ita, ko bai fada ba tasan abinda yake nufi, gocewa tafara yi daga rikon da yake kokarin yimata saboda ita idan tana period kamar mai ciki take zama gashi sam bata son kowa yaje kusa da ita ko lokacin da tana gida daga blessing taje kusa da ita zata koreta amma idan normal take itace zata yi mata komai,

Tureshi ta shiga yi saboda bata son taji mutum ajikinta,

"Dan Allah ka matsa.."

Tunda yaji tafara fadin haka yagane period take saboda wancan watanma haka suka yi da ita daga ya matso kusa da ita zata fara cewa ya matsa, amma idan lafiya lau take ko sau nawa zaije kusa da ita bata k'i,

Tashi yayi ya fita amma gaba daya atakure yake saboda kwanakin da takeyi idan tana period sunyi masa yawa har tsawon kwana takwas,

Tunda yafita bai dawoba sai da daddare, tana falo ita kadai tana kallo domin ta kora blessing daki,kusa da ita shaddad yaje ya rungumeta, duk da yasan bata so tunda yanzu tana cikin wani irin yanayi,

"Kwanakin nan naki sunyi yawa, wai babu wani abu da zakisha ne ya rage kwanakin?"

"Babu.." Tafada atakaice daga nan bata sake magana ba amma acikin zuciyarta cewa take"babu abinda zansha bayan nasamu zan dan huta da jarabarka",

Rungumeta yayi sosai yana jujjuya kanshi a kirjinta da haka har bacci ya kwasheshi, tana daga inda take ta mika remote ta kashe tv din dake kunne tana aiki, ahaka suka kwana afalo har saida asuba tayi ya tashi sannan itama takoma daki, tausayinsa kuma ta danji dan haka ta sha wani magani wanda yake sa rushing sannan yake rage kwanaki, cikin kwana hudu ta gama....

*_Ummi A'isha_*
[5/21, 8:48 PM] Ummi Shat🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

  _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   *_43_*

~~~Tunda yaga alamun ta gama yaji ya kasa hakuri,

Blessing yaje ya aika kasuwa iyo siyayyar da babu gaira babu dalili, yana ganin ta fita yaje ya rufe gidan ya nufi dakin maryama, tana yin sallama daga sallar da take yana shiga, binsa da kallo tayi,gajeriyar addu'a kawai tayi ta shafa ta mike, riketa yayi ya nufi kan gado da ita, kallonshi kawai take saboda irin yanda jikinsa yake rawa kamar sun shekara basa tare,

K'arshen soyayya yana nuna mata aduk lokacin da suka kebe a matsayin ma'aurata, gaba daya mantawa yake da batun cewar baya sonta yayi ta nuna mata zallar so yana yimata kalaman soyayya,

Sun kwashe awanni acikin duniyar ma'aurata kafin shaddad ya hakura, rungumeshi tayi sosai tana ajiyar zuciya har na tsawon wani lokaci, tashi yayi ya fita zuwa dakinshi ya shiga wanka zuciyarsa cikeda farin ciki domin ya samu nutsuwa dari bisa dari,

Yana fitowa daga wanka ko gama shiryawa baiyi ba yaji anfara bugun kofa, ko ba afada masa ba yasan blessing ce ta dawo, tsaki yaja saboda shi gaskiya yana takura badan umarnin hajiya ne ba da tuni ya dade da korar blessing,

Rigarshi ya zira ya fita yaje ya bude mata kofar ya dawo dakinsa yaci gaba da shiryawa,

Maryama kam tana can tana baccin gajiya, ba ita ta tashiba sai da yamma, wanka tayi tasaka english wears jeans da t shirt ta fita falo,

Blessing ta gani zaune tana gyara alkama,

"Blessing wannan fa na meye?"

"Anty oga ne ya aikeni na siyo"

Murmushi maryama tayi ta nemi wuri ta zauna saboda tasan dalilin shaddad nayin aiken babu gaira babu dalili, kawai ya aiketa ne saboda ya samu ya hutawarshi, "shikenan sai muyi kunu da ita" tafada tana murmushi,

Haka da daddare ma bai iya hakuri ba har sai da ya ziyarci makwancin maryama, haka da asuba ma, ita dai maryama koda yaushe yazo bata gudunshi saboda son da take yimasa bazai bari ta barshi acikin matsala ba, soyayyar da take yi masa bazata bari ta iya hanashi kanta ba, sannan a iya wannan lokacin ne kawai yake nuna mata kauna da soyayya,

Kullum haka take dawainiya dashi da daddare da asuba daidai da rana daya bata taba nuna masa gajiyarta ko kuma taki amince masa ba, ita yanzu harma ta saba da lokutan da yake zuwar mata ta daina jin wahala,

Kullum shi kenan cikin cewar zai auro karamar yariya, idan taji haka sai dai tayi murmushi tace,

"Nidai na fada da karamar yarinya yar 16 wacce bata adana mutuncinta ba gara tsohuwa yar 30 wacce ta adana mutuncinta har takaishi gidan mijinta"

Anty maijidda ce ta bata shawarar cewar ta nemi islamiyya tashiga taci gaba da zuwa saboda ko babu komai zata rinka samun karuwa akan ilmin da take dashi ada,

Wata islamiyya ta shiga asabar da lahadi acan unguwar hausawa tsakinsu da unguwar da nisa amma haka take samu ta daure taje duk sati sannan babu laifi tana samun karuwa sosai.

Haka zamansu yaci gaba da tafiya tsakaninta da shaddad, tun farkon aurensu har yau shaddad bai taba furtawa maryama kalmar so ba sai a lokacin mu'amalar auratayyarsu kawai,

Yau kam da ciwon jiki tatashi gashi tana ta jin tashin zuciya da wani irin jiri, duk atunaninta malaria ce ta kamata amma da taji tanata yawan yin yunkurin amai sai ta zargi cikine, nan ta dauko abin gwaji ta gwada, tana gwadawa taga cikinne kuwa wata daya,

Maganin hana tashin zuciya ta balla tasha ta kwanta, yau kwata kwata ta kasa cin abinci sai tashin zuciya dake damunta da zazzabi zazzabi,

Ko office bata fitaba tana kwance agida ta aika blessing ta samo mata farar kasa tanata sha, yawu kuwa kamar anbude fanfo haka take ji yana cika mata baki,

Tana kwance a falo tana shan farar kasar shaddad ya shigo, tashi tayi ta shiga bedroom dinta ta shiga bathroom domin zubar da yawun da ya cika mata baki,

Dawowa tayi falon ta kwanta, girkin da blessing tayi gaba daya sai tayar mata da zuciya yake dan haka ta tashi daga falon ta koma dakinta ta kwanta, wata yar karamar robar man shafawarta da ya kusan karewa ta dauka take zuba yawun aciki saboda tagaji da wannan zirga zirgar zuwa bathroom din zubar da yawu,

Shaddad ne ya shigo cikin dakin yana yi mata magana,

"Hajiya ta kirani dazu tace kin tura musu sako ko?"

Sai da ta tofa yawu acikin robar dake hannunta sannan tayi magana,

"Ehh ai ba wani mai yawa bane.."

"Tace to ayi miki godiya tagode madalla"

Wani yawun ta sake zubarwa sannan ta amsa masa,

"Babu komai"

Tun da shaddad yaga haka ya fahimci cewar cikine da ita saboda yaga sai tofe tofen yawu take alhalin ada ba haka takeba,

Juyawa yayi ya fita zuciyarsa kunshe farin ciki, wurin lokacin sallar mangariba ya shiga dakin nata saboda yana son zai fita,

Zaune yaganta da wani magani ahannunta zata sha, cikin sauri yaje ya karbe maganin yafara dubawa _well women_ yaga anrubuta ajiki, nan yafara karanta rubutun dake jikin kwalin, hankalinsa ne ya kwanta saboda ganin maganin mai amfani ne ga jikin mata bamai cutarwa bane,

Fita yayi batare da yayi magana ba,nan ya tafi ya barta taci gaba da tofe tofen yawunta.......

*_Ummi A'isha_*🏻
[5/21, 8:48 PM] Ummi Shatu: _*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_

  _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _*44*_

~~~Duk da kasancewar bata jin dadin jikinta wannan bai hana shaddad zuwar mata ba, haka ta daure ta cije ta bashi hakkinshi acikin wannan daren, yana dawowa daga sallar asuba ya sake dawo mata,

Dan haka dasafe kasa tashi da wuri tayi sai wurin misalin karfe 9 sannan ta tashi tayi wanka ta fito,

Lokacin data fito tuni har shaddad ya jima da fita amma ya barwa blessing sako tafadawa maryama zai dawo yaci abinci anjima,

Zama tayi a falo ta fadawa blessing abinda zata dafa, ita kuma ta hada bakin tea tasha,

Bayan blessing ta kammala aikace aikacen gidan ne maryama ta aiketa kasuwa taje ta siyo mata ganda saboda ita take sha'awar ci,

Tana zaune ita kadai tana kallo gefe daya kuma robar tara yawunta ce sai budewa take tana tofawa shaddad ya shigo,

"Sannu da zuwa" tace dashi tana canja channel da remote a hannunta,

"Yawwa, angama abincin?"

"Gashi nan akan table"

Kan table din yaje ya zauna ya debi abincin ya fara ci, yana yi yana kallonta, motsi kadan sai ta yamutsa fuska ta bude roba ta tofa yawu, da haka har blessing ta dawo ta kawo danyar gandar data siyo mata,

Daukar gandar tayi tana sansanawa, da adane ta sansana ganda da amai zatayi amma ayanzu har wani kamshi take ji gandar tana yi mata maimakon karni,

"Blessing tuwo nake so, idan kika yimin tuwon sai kiyi miya da wannan gandar"

Yana jinta ta fadi haka acikin zuciyarsa yace, "keda kika tsani tuwo yanzu kuma shi kike so?"

Tun daga ranar kullum babu abinda take son ci sai tuwo, abubuwan da ada take son ci yanzu duk ta tsanesu musamman ma masu madara irinsu cornflakes, golden morn, viju milk, ziza, duk yanzu bata sha saboda amai suke sata.

Tana tsaka da wannan laulayin su anty maijidda suka zo itada anty zainab saboda rabonsu da ita tun bikinta watanni biyar da suka wuce,

Tana kwance adakinta tana faman shan farar kasa suka zo dama ranar shaddad baya nan sun tafi Ilorin duk tanata missing dinshi kuma bazai dawo ba sai wani satin,

Tashi tayi cikeda murna taje ta rungume anty maijidda, amma cikin hanzari ta saketa saboda kamshin humarar da tasaka ta tayar mata da zuciya, bathroom ta shiga tayi amai ta fito,

Anty zainab kallon anty maijidda tayi ta kuma kalli robar da maryama take tara yawu ga kuma farar kasanan cikin wata farar leda,

"Anty maijidda kin kusa samun jika sai kifara tanadin kayan baby"

Dariya anty maijidda tayi, "nima ai na fahimci hakan zainabu, Allah ya rabasu lafiya"

Fitowa maryama tayi daga cikin bathroom bayan ta gama aman,

"Wai anty maijidda wannan humrar taki amma da karfi take, koda yake nima tawa haka nake jinta yanzu shiyasa ma na daina shafawa ciwon kai take sakani da amai"

Murmushi anty maijidda tayi suka karasa bakin gadon suka zazzauna,

"Yata kenan ashe andace har an samu rabo"

Dauke kai maryama tayi cikin jin kunya, "anty ina daddy? Inasu haydar?"

Dariya anty zainab tayi "kinji yarinya taki zancen.."

Nan suka gaggaisa suka shiga hira, da Kansu su anty maijidda suka shiga kitchen suka yi girki sannan suka tukawa maryama tuwon shinkafa miyar agushi, ba karamin dadin zuwansu tajiba domin sun dauke mata kewar mijinta,

Kwanansu biyar saboda shaddad baya nan amma da ace yana nan da kwana biyu zasuyi, ana igobe zai dawo su anty maijidda suka tafi bayan sun zaunar da maryama sun yimata jawabai kala kala kan yanda ya kamata ta kula da mijinta yanzu Sannan kar ta rinka gudunshi,

Sai karfe 8 nadare su shaddad suka sauka, dayake garin garine na damina tuni har anfara ruwan sama, dan haka ajike ya dawo gidan yasa key ya bude ya shiga, ganin maryama tayi bacci ya kyaleta bai tasheta ba sai da asuba ya shiga dakinta, sai lokacin ma ita tasan ya dawo,

Tari tafara yi sosai saboda har ya goga mata murar da yazo da ita jiya, haka ta fito da safe hancinta yana yoyo ga uban tari da take, shi kanshi yasan shine silar wannan murar tata,

Kullum maryama tana gida bata fita aiki saboda laulayin dake damunta ko gidan Dada bata iya zuwa sai shine yake zuwa ya dubata duk bayan kwana biyu, sai da cikin ya danyi kwari ya shiga wata na shida sannan tafara fita,acikin wannan lokacin su shaddad aka turasu kasar burtaniya kuma ta ruwa zasu tafi, hankalin maryama ba karamin tashi yayiba, sallama shaddad yayi mata ya tafi,

Aranar da ya tafi kasa bacci tayi tanata sakar zuci wani lokacin har tunani take cewar kila fa sallamar kenan tsakaninta da shaddad ba lallai ya dawo ba, kuka tayi sosai wanda ta dade bata yi irinshi ba,

Kullum idan ta tashi daga aiki sai taje gidan dada shine yake kwantar mata da hankali yace karta damu ai babu wani abu shaddad zai dawo,

"Dada wata da watanni fa zasuyi acikin ruwa, tayaya zasuci abinci? Tayaya zasu sha ruwa? Tayaya zasuyi ibada?", haka take fada kullum tana kwalla,

"Kibar damun kanki daughter, insha Allah babu komai"

Kullum haka sukeyi da dada yayita rarrashinta yana nuna mata cewar shaddad zai dawo mata lafiya da yardar Allah.

  Haka ta hakura taci gaba da gudanar da al'amuranta amma kuma duk ranar da tunanin shaddad ya tunkudo ta to kwana take bata runtsaba gashi dama tunda ya tafi ko sau daya basuyi waya ba saboda babu dama tunda shi yana cikin ruwa,

Ita tausayinsa ma takeyi kullum tunaninta tayaya zaici abinci,tayaya zai sha ruwa alhalin yana cikin ruwa?.

  Akwana atashi babu wuya har shaddad yayi wata biyu da tafiya kullum cikin zuba idon dawowarshi take amma shiru, har suka kusa shiga wata na uku, nan hankalin maryama ya tashi,

Watansu uku cif ranar talata da daddare sai gashi ya dawo, nan maryama ta shiga hidima dashi masu karatu karfa kuga laifin maryama kun san shi so hana ganin laifine indai kana son mutum to kullum son dadada masa kake,

Duk inda ta wulga binta da kallo shaddad yake saboda cikinta ya tsufa saura yan kwanaki ya rage ya shiga wata na tara,

Duk da yaga yanda take takawa dakyar amma sai yakasa hakuri saboda sun jima basa tare, maryama baiwar Allah haka da tsohon cikin da komai tabashi hadin kai bata k'i ba domin ita aduniya duk abinda shaddad yake so zata iya bashi mutukar baifi karfinta ba,kwana biyu ya dauka kullum yana gida yana yimata naci baya fita ko ina,masu karatu duk fa wannan abun da yake faruwa har yau shaddad bai taba nunawa maryama cewar ya kamu da sonta ba bare ya furta mata,kwanansa biyar da dawowa ya shirya ya tafi Kaduna amma aranar ya dawo.

Sati biyu da dawowar shaddad maryama tafara nakuda, karama clinic suka tafi nan dr muneerat tace operation za ayi mata saboda kamar haihuwar zata yimata wahala sosai, babu bata lokaci aka shiga da ita aka yi mata aiki aka ciro baby girl katuwa mai kamar maryama sak,

Sai da maryama ta farfado sannan aka gyara babyn wata nurse taje ta Kira shaddad da Dada wadanda ke waje suna jira.....

  _*45*_

~~~Zubawa shaddad ido maryama tayi tana son taga da wanne irin yanayi zai karbi babyn lokacin da suka shiga cikin dakin, fuskarshi da fara'a taga ya karasa gadon da babyn take ya dauketa yana ta kallonta, ita kuwa ko wurinda take bai kalla ba balle ta saka ran zaiyi mata sannu,

Wannan abu yayi mutukar bawa maryama haushi ganin ya nuna halin ko in kula akanta sai ta babyn sa yake,

"A tsaga jikin nawa afito maka da yar amma banida darajar da zaka cemin koda sannu?" Tafada acikin zuciyarta,

Ta wuri daya taji dadi taji bacin ranta ya tafi shine lokacin da Dada ya shigo shima bai nufi wurin kowa ba sai wurinta yaje yana ta yimata sannu yana tambayar ko da akwai wurinda yake yi mata ciwo?

Dadi taji azuciyarta tace "dadinta dai nima nawa uban yadamu dani.." Tafadi acikin zuciyarta,

Sai da Dada yaji cewar lafiya lau take sannan ya matsa wurin shaddad ya karbi babyn ya sanya mata albarka ya fita, zuba ido maryama tayi tana ta kallon shaddad yana kai kawo da yarshi akan kafadarshi,

Waya yayi kaduna ya sanarwa da hajiya haihuwar sannan ya kikkira yan uwa ya fada musu, murna hajiya ta shiga yi sosai kamar wannan ne karo na farko data fara samun jika nan tace khairat ta shirya ta tafi tunda dama acikin hutun semester take,

Ita kuwa maryama wayarta tasa blessing ta dauko mata ta kira anty maijidda ta fada mata ajiyar zuciya anty maijidda tayi ta shiga hamdala domin tunda cikin maryama ya shiga watan haihuwa bata iya bacci saboda fargaba,

Kashe wayar tayi ta kira anty zainab itama ta fada mata,

Har bacci ya kwasheta bata san lokacin da shaddad ya ajiye babyn daga hannunshi ba,

Sai yamma lis ta farka lokacin har khairat tazo daga kaduna sunje gida itada blessing sun hado mata kayan tea sun dawo,

Tashi tayi ta zauna aka miko mata babyn ta karbeta zata shayar da ita, kurawa kirjinta ido shaddad yayi yana kallonta har lokacin kamar bata haihuba kirjinta yake sai dai cika da ya kara amma babu alamun zubewa atare dasu,

Haka aka yita faman kaiwa da komowa a asibitin har aka sallamesu suka koma gida, aranar su anty maijidda suka zo lokacin kwanan maryama uku da haihuwa, tunda suka koma gida kuma dangi da yan uwa suke ta zuwa ganin jaririya, kwanansu hudu su hajiya suka zo ita da anty karama da matar yaya Yusuf hadiza,

Dan murna hajiya ji take kamar zata hadiye jaririyar, kiran shaddad tayi tace wanne suna za asawa jaririyar? Nan yace sunanta zai saka,

"Ita kuma maryaman fa? Kamata yayi asa sunan mahaifiyarta tunda ni ai kaga yan uwanka sun sassaka sunana dayawa"

"Hajiya ai sunanku daya da babartata itama.."

Fara'a hajiya tayi ta gutsiri goro,

"Ashe kai maryaman naka suna da yawa, to Allah ya rayata"

Tashi yayi ya fita a kitchen ya hango su khairat suna aiki ita ya kira yace taje ta turo masa maryama saboda yaga dakin acike yake, dakinsa ya wuce ya  tsaya yana jiranta,

Tana sanye cikin doguwar riga na atamfa ta shigo dakin, sai da yaji wani kamshi ya gauraye dakin lokacin data shigo kamar ba maijego ba,

"Gani.." Tafada saboda dama har lokacin a kule take dashi na rashin sannun da baiyi mata ba lokacin data haihu,

Zama tayi agefen gadonshi bata ko kalleshi ba, tunda yaga haka yasan fushi take dashi,

"Munyi magana da hajiyane akan sunan da za asawa jaririyar, sunanta maryama"

"Allah ya rayata.." Shine kawai abinda tace ta tashi zata tafi,

"To babu wani abu da kuke bukata?"

"Babu" tafada tareda karasa ficewa, tun daga nan take shareshi taci gaba da hidimarta, har gida mai saloon tazo tayi mata ta gyara mata yalo yalon gashinta sannan aka yi mata jan lalle wannan kam khairat ce tayi mata saboda dama ta iya sosai,

Kyawun da maryama tayi kai idan ka ganta ba zakace itace ta haihu ba shiyasa duk inda tayi idon shaddad akanta yana lasar lebe, shaddad yayi kokari sosai wurin yi mata kayan kece raini ita da jaririyar,

Manyan raguna guda biyu ya siyo ma jaririyar, ranar suna aka yankasu aka radawa jaririya suna MARYAMA zasu rinka kiranta da Nu'aima,

Anyi hidima iya hidima awannan sunan, Dada mahaifin maryama gida guda ya mallakawa jaririyar, su hajiya da sauran dangi duk basu tafiba sai bayan suna da kwana biyu,

Yanzu gidan daga anty maijidda sai khairat ne kadai sai ko blessing da take zaune agidan tana tayasu ayyuka,

Tun maryama na share shaddad har ta dawo ta hakura ta rabu dashi amma bawai dan ta manta abinda yayi mata ba, ita kuwa anty maijidda maida hankali tayi wurin gyara maryama sosai,daga maryaman har nu'aima sunyi bulbul sunyi kiba sunyi kyau abinsu, ana igobe zasu cika kwana arba'in anty maijidda ta tattara ta tafi abuja gidanta tabar khairat awurin maryama saboda ta rinka tayata rainon nu'aima, ranar da suka cika 40 shaddad bai daga kafa ba dama tunda ya kyalla ido yaga khairat adakin maryama take kwana ya kira maryaman yace khairat ta koma daya dakin da kwana,

Yar gidan jiya suka koma koda yaushe baya barinta ta huta daga dare har asuba samun hutunta da ranane kadai, yanzun ma kuma sai da ya sake maimaita mata cewar indai tayi planing a boye Allah ya isanshi bai yafeba,

Haka suka cigaba da gudanar da rayuwarsu har sukayi wata biyu lokacin khairat ta koma Kaduna saboda school, sha tara ta arziki maryama ta hada mata sannan tabada sako mai girma tace akaiwa hajiya,

Khairat bata jima da tafiya ba shaddad ya shirya ya tafi Kaduna ashe zance yatafi wurin budurwarshi Amira saboda yanzu tayi candy, sai da yagama zancenshi sannan ya tafi gidan hajiya, tsabar zance yayi dadi wai har number din maryama ya bawa yarinya akan zata kirata su gaisa,

Duk lokaci zuwa lokaci yake zuwa Kaduna yanzu saboda Amira, ita maryama bata saniba, idan yana gida kullum yana makale da yarshi nu'aima hatta bacci tare suke yi, bikin blessing ne ya taso nan maryama ta hada mata sha tara ta arziki ta sallameta ta tafi garinsu, yanzu gidan yadawo sai su uku kacal, kullum da nu'aima maryama take zuwa aiki idan taje da ita kuwa bata sake ganinta sai idan tatashi zata dawo gida sannan ne zataje ta nemota su koma gida,

Tana tsaka da aiki acikin kitchen taji an kirata awaya, bakuwar number tagani ana kiranta awaya,

Dagawa tayi tun kafin tayi magana taji ance,

"Sannu amarya yar shekara 30 yanzu ke ko kunya bakiji ba kika dage kika auri yaro sa'anki, bayan kin san yadade yana sona tun ina jss 3 yake sona kuma har yanzu bai daina sona ba..."

Kashe wayar maryama tayi saboda ita bata iya fada ba, duk da ta kashe wayar Amira bata hakura ba sai da ta sake turo mata da text massage,

Haushi iya haushi maryama tajishi amma bata ko nunawa shaddad ba duk da tasan shine zai fadawa budurwar tasa cewar shekarunta 30 lokacin da ya aureta,

Cikin satin suka shirya suka tafi Kaduna gaida hajiya, ina ka saka ina ka ajiye haka hajiya tayiwa su maryama, shi kuma shaddad ya tafi wurin Amira saboda yana son ya turo ayi maganar aurensu da ita....

*_Ummi A'isha_*
[5/21, 8:48 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

  _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  *_46_*

~~~Amma koda yaje yayiwa Amira maganar sai tace masa ita makaranta zatayi ba yanzu zata yi aure ba,

"Amira kin san dai na dade ina sonki kuma hajiya ta matsa akan ayi ayi maza ai auren nan.."

Budar bakin Amira sai cewa tayi, "kuma ni ina ruwana da wata hajiya, ai ba itace zata yimaka auren ba da zata bi ta uzzura maka.."

Tunda tafadi haka yaji ransa yabaci sannan yaji yarinyar tafara fice masa arai saboda sam bata da kunya gata dai yarinya karama dan ko khairat da take kanwarsa ta biyu ta girme mata nesa ba kusa ba amma sai ta rinka fada masa bakar magana, duk da yasan harda yarinta acikin tsarin nata amma harda rashin kunya da rashin ganin girman nagaba, ta inda yake sarawa maryama kenan sam bata son bacin ranshi gashi tana mutukar kaunar mahaifiyarshi da yan uwanshi sannan duk abinda ya fada mata bata iya yimasa musu kuma duk tsanani baya magana ta mayar masa ko lokacin da yake yimata wulakancin nan farkon aurensu shiru take yi bata ramawa gashi dai ahaife ba girmanta yayiba amma tana bashi girma da daraja a matsayinshi na mijinta,

Cikeda bacin rai yabar wurin Amira ya koma gidan hajiya, kwanansu biyu suka koma Lagos bayan hajiya ta samowa maryama wata yar dattijuwa mai suna baba lami wacce zata zauna da maryama ta rinka tayata yan aikace aikacen gida saboda yanzu bata da mai aiki ita kuma hajiya ko kadan bata son taga maryama na shan wahala,

Komawa Kaduna suka yi suka cigaba da gudanar da rayuwarsu, nu'aima babu laifi ta girma tayi wayo sosai, shi kuwa shaddad dole yanzu ya hakura da maganar Amira musamman ma da yaga text massage din data turowa maryama awayar maryaman nan yasake jinjinawa maryama wurin hakuri da dauriya domin ba duk macece zata iya wannan ba da wata matarce Allah ne kadai yasan tashin hankalin da zasuyi da ita amma ita maryama ko nuna masa bata yiba, sannan baya ga haka ma tunda tafara jami'a ta hadu da wani guy ya ke hure mata kunne, yanzu kwata kwata ta juyawa shaddad baya, ganin haka yasa shaddad hakura ya kyaleta saboda dama hajiyarsu da sauran yan uwanshi ba son aurensa da Amira suke ba.

Watan nu'aima tara maryama ta fara laulayin wani cikin danma nu'aiman mai saurin girma ce sannan tunda maryama likitan yarace tana taimaka mata da wasu sinadirai masu gina jikin yara shiyasa ta taso cikin koshin lafiya dama kuma ba damuwa tayi da shan mama ba shiyasa maryama ta yayeta,

"Zo Mamana, ummice ta yaye ki ko ta hanaki shan abincinki, yi hakuri zamuje in siyo miki bobo.."

Tana ganin shaddad ya dauketa suka fita yawo, haka tayita laulayinta wannan karonma kamar lokacin da tayi na nu'aima, amma yanzu tunda bana farko bane ta ji dan dama dama, shiyasa ma ko hutu bata dauka ba a office har saida azumi yazo lokacin cikinta yana wata bakwai shine ta dauki hutu saboda tana son su tafi umarah itada nu'aima,

Shaddad bai hanata ba tunda da kudinta ta biya, nan aka gama musu dukkan shirye shiryen da ya kamata suka tafi,

Kullum suna waya da shaddad, satinsu uku acan suka dawo, nan shaddad ya karbesu da farin ciki domin yayi missing din matarshi sosai,

Gidan Dada maryama takai nu'aima saboda kullum sai ta rinka cemata zataje wurin dada tunda ta kaita bata daukota ba sai da zasu tafi Kaduna salla,

Kamar koda yaushe wannan zuwanma taji dadin yanda su hajiya suka karbeta kowa kamar zai hadiyeta dan so, sai da akayi salla da sati daya sannan suka koma Lagos,

Kwanci tashi da haka har watan haihuwar maryama ya cika, ranar da edd dinta ya cika aranar ta tashi da nakuda,shaddad ne ya dawo daga office ya kaita asibitin, wannan karon ma cs din za ayi mata, yana ganin lokacin da aka zo za awuce da ita nu'aima taje gaban gadon tana kuka,

"Ummi zaki dawo ko? Dan Allah Ummi karki tafi"

Jin abinda nu'aima take fada ne ya karyarwa da maryama zuciya har taji kwalla tana kokarin sauko mata batare da ta shirya ba,

Shi kansa shaddad sai yaji jikinsa yayi sanyi sosai, zuwa yayi ya kamo hannun nu'aima batare da ya iya kallon wurinda maryama take ba,

Yana nan atsaye har nu'aima tayi bacci akan kafadarsa, gida ya koma ya mayar da ita wurin baba lami ya sake dawowa asibitin,

Shida dadane a reception suna jira, can nurse tazo tace anciro jaririn suzo su ganshi, duk murnar da shaddad yake yi na zai samu karuwa amma sai yaji wannan lokacin ya nemi farin cikin ya rasa,

Wurin jaririn sukaje suka ganshi tubarakalla kato dashi mai kama da shaddad fitik, nan aka shirya yaron aka ajiyeshi acikin gadonshi,

Maryama kam awa da awanni bata farfado ba dan haka hankalin doctors din ya tashi sosai nan suka rufu akanta domin ceto numfashinta sai dai amma ina basu da wannan ikon daga karshe dai dole suka hakura domin tuni rai yayi halinsa maryama ta rigamu gidan gaskiya,

Dr muneerat ce ta fito jikinta yana rawa taje wajen su Dada amma sai ta kasa fada musu rasuwar maryama,

"Dr ta farfado ne?" Dada ya tambaya, girgiza kai dr muneera tayi,

"Yallabai sai dai muyi hakuri mu karbi kaddarar da Allah ya aiko mana.."

Hawaye suna bin kuncinta ta mikawa shaddad wata farar takarda,

"Gashi itace ta rubuta kafin ayi mata aikin.."

Karba yayi hannunsa yana rawa ji yake kamar mafarki yake yi, cikin rawar jiki ya warware takardar yafara karantawa,

"Mijina dan Allah idan nayi maka laifi ka yafe min, Allah ya hadamu a aljanna sannan dan Allah ka taimaka ko gawata ne ka fada mata Kalmar so duk da nasan ba ka sona, amma ka sani ni ina tsananin sonka son da ban san adadinsa ba, Allah ya raya mana yaranmu..."

Ai shaddad yana gama karantawa yaji kamar zai zube awurin saboda hajijiyar data fara daukarshi idanuwanshi suka rufe baya ganin komai sai duhu....

  _Gaisuwa ga masoyana masu sona, ina mai baku hakuri sakamakon bana baku amsa da wuri idan kun yimin magana wallahi abinne yafi karfina shiyasa, sakonninku da yawa bazai yiyu in amsa a lokaci guda ba,nagode da kaunarku gareni, ummi shatu luvs u too.._