Thursday 1 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 48,49

[5/25, 9:20 PM] Ommee A'esherh: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_


*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

 
  _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _Wannan shafin nakune masoyan maryama sarauniya daku da takwarorinta gaba daya._


  *_48_*

aishaummi.blogspot.com

~~~Shaddad yana rike da hannun maryama gefe daya kuma jaririn sune kwance agefen maryaman, gaba daya shaddad ya kasa tashi ya matsa ko nan da can saboda gani yake yi idan ya fita kafin ya dawo maryama ta mutu,

Ko sallah ya kasa zuwa yayi yana nan zaune kusa da ita kwakume da hannunta, tun suna yin hira tare har ta dan fara yin bacci, zuruf ya mike yaje ya kara kunnensa ajikin kirjinta nan yajiyo bugun da zuciyarta take yi, duk da haka hankalinsa bai kwanta ba har sai da ya kai hannunshi saitin kofofin hancinta yaji numfashinta yan sauka akan hannun nashi sannan yakoma ya zauna ya zuba mata ido kamar lokacin ne yafara ganinta, hakurinta da juriyarta yake tunawa da irin soyayyar da take yi masa koda wasa bata son taga yayi fushi ransa ya baci, dai dai da rana daya bata taba fada masa kalmar da zata bata masa rai ba, sannan duk tawon lokacin da suka dauka tare bai taba shakar wani abu atareda ita sabanin kamshi ba,

Bude idanuwanta tayi tana yi masa murmushi,

"Navy baka tafi gida kayi wanka ba?"

"Jira nake naga kin bude idonki kin gama baccin tukunna..."

Murmushi ta sake yi ta runtse hannunshi cikin nata,

"Tunda natashi to kaje ka tafi"

Hannunta yakai kan bakinshi yayi kissing dinshi tukunna ya mike zai tafi,

Bude kofa akayi khairat ne da anty maijidda suka shigo hannunsu rikeda dan karamin basket wanda suka hadowa maryama kayan tea aciki,

Komawa shaddad yayi ya zauna,

"Yaya Navy bakayi salla ba fa.."

Khairat tace tana dariya, "navy ai yau yazama baby.."

Anty maijidda tafada itama tana dariya,

Karbar kayan yayi yana murmushi ya hadawa maryama tea rabin cup ya koma bakin gadon ya tadata zaune ya jinginata da jikin pillow yafara diba a spoon yana bata,

"Navy baka fifita ba da zafi tea din..."

"Yi hakuri bari na fifita miki"

Wani cup din ya sake dauka ya fifita mata tea din sannan yaci gaba da bata su anty maijidda da khairat suna tsaye suna kallon ikon Allah,

Daf da zata kammala shanyewa ta kauda kanta tea din ya zuba ajikin habarta,

"Barshi haka ya isheni.."

Babu kunya shaddad yasa harshensa ya lashe wanda ya zuba akan habar tata, anty maijidda da khairat sai ficewa suka yi daga cikin dakin,

"Zanje gida nayi wanka nayi salla sai in dawo..."

"Abinci fa? Kaci abinci kafin ka dawo dan Allah"

Kiss yayi mata akan lebenta, "to sai nadawo"

Fita yayi tabishi da kallo, ta glass din window din dakin take hangoshi har ya bacewa ganinta,

Murmushi tayi ta janyo jaririnsu tana kare masa kallo komai na yaron irin na shaddad ne sak babu banbanci,

Fitar shaddad ce tasa wadanda ke zaune awaje suka shisshigo cikin dakin suna yiwa maryama sannu,

Shaddad na fita gidanshi ya wuce acan ya iske su hajiya da su anty karama da anty zainab suna kitchen suna girke girke,

Ganinshi yasa Nu'aima zuwa ta rungumeshi tana murna,

"Dady wai Ummi ta siyo mana sabon baby boy?"

Dariya maganar nu'aima tabishi, riketa yayi yana dariya, "ehh mamana umminki ta yimiki kani, zamuje ki ganshi ko?"

Kaita wurin hajiya yayi ya juya zai tafi,

"Kai shaddad sai ka nemo wani sunan da zan rinka fada maka saboda bazan kara kiranka da mazaje ba.."

Dariya yayi saboda jin abinda hajiya tafada yasan tafadi hakane saboda ta ga irin kukan da yayi dazu,

Dakinsa ya shiga yaje yayi wanka yayi salla ya shirya cikin blue din jeans da jar riga mai gajeren hannu,

Yana kokarin fitowane suka yi kicibus da anty karama zata kawo masa abinci, kamar ba zai zauna yaci abincin ba sai ya zauna saboda rokon da maryama tayi masa dazu kafin ya bar wajenta, yanzu so yake shima ya nuna mata so da kauna irin wacce ba ataba nunawa wata ya mace ba,

Cokali uku yayi a abincin ya fita ya dauki nu'aima suka tafi asibitin, lokacin da yaje ya samu maryama azaune tana rike da jaririn akan cinyarta sai khairat kuma dake zaune akan wata farar kujera tana yiwa maryama hira,

"Ummi ina babyn da kika siyo mana?" Nu'aima ta fada tareda kokarin hawa kan gadon, shaddad ne ya dagata ya dorata akan gadon shima ya zauna akusa da maryama,

"Gashi mamana, kaga yaya nu'aima.."

Maryama tace tareda dora jaririn akan cinyar nu'aima,

"Yarinya karama sai manyance" khairat ta fada tana dariya,

"Bawani manyance itama ai yanmata ce yanzu da me kika fita?"

Maryama tafada tana dariya, kallon shaddad tayi wanda ya maida hankalinsa akan wayarshi dake hannunshi,

"Kaci abincin kuwa..?"

Gira ya daga mata yana murmushi,

"Ban yadda ba Navy"

Bakinshi ya kai kusa da hancinta,

"Shinshina kiji zakiji kamshin curry"

Maimakon ta shinshina din kamar yadda yace sai kawai ta cijeshi, tashi khairat tayi ta fita ta basu waje,

Riketa yayi yana kallonta ido cikin ido fuskarshi kumshe da murmushi,

"Kika cijeni?"

Lumshe masa idanuwanta tayi tana yi masa murmushi,

"Tsautsayi ne.." Tace dashi tana wasa da hannunshi,

"Idanma bada tsautayin kika yi ba nayi miki uzuri, ni duk abinda kika yimin koda na bacin raine to ki dauka raina bai baciba domin ina maraba da duk wani abu da zai zo gareni mutukar daga gareki yake"

Bude idanuwanta tayi akan kyakkyawar fuskarshi tana jin wani irin farin ciki yana ziyartar zuciyarta...


*_Ummi A'isha_*
[5/25, 9:20 PM] Ommee A'esherh: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

  _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _*49*_

~~~Hannunta tasa ta shafi gefen fuskarshi tana murmushi,

"Nagode navy, Allah ya barni dakai har ranar da zan daina numfash..."

Rufe mata baki yayi da hannunsa guda daya,

"Ki daina ambatar wannan kalmar saboda bana son jinta, tana hanani sukuni sannan tana rabani da nutsuwata, bana fatan mu rabu har abada.."

Murmushi tayi idonta cikeda kwalla duk kalaman da yake fada mata ji take kamar a mafarki ne ba agaske ba,

Girgiza mata kai yayi yafara goge mata kwallar da ke kokarin sauka daga idonta,

"To kuma menene zakiyi kuka..?"

Murmushi tayi ta lumshe masa idonta, nan shaddad yaci gaba da zama atare da ita har dare yayi, koda daddaren ma da anty maijidda tazo tace zata kwana awurin su maryaman shaddad cewa yayi a,a shine zai kwana awurinta, sai dakyar anty maijidda ta samu ta shawo kansa ya hakura,

Mannawa maryama kiss a kan goshinta yayi sannan yafita ita dai anty maijidda binsu da ido kawai take yi,

Washe gari kuwa da sassafe sai gashi dauke da kayan breakfast shi ko karyawar ma bai yiba haka ya taho, azaune ya samu maryama kusa da ita yaje ya zauna yana kallonta,

"Baby sannu ya jikin naki?"

Kallonshi tayi tai murmushi, "Navy kenan, ina kwana?"

Kashe mata ido guda daya yayi, "kema dai daga ganina kin san ba lafiya na kwana ba saboda rashinki.."

"Bani tea din.."

Sauka yayi daga kan gadon ya hada mata tea ya fara bata da haka har anty maijidda tazo ta iskesu ta dawo daga karbowa maryama magani,

Gaisheta shaddad yayi nan tafice ta basu wuri saboda yanzu taga tashen rashin kunya suke, sai da yagama bawa maryama tea din sannan yatafi gida domin yin wanka,

Haka shaddad yayita zirga zirga har aka sallami su maryama daga asibitin lokacin kwanansu hudu saura kwana uku suna,

Suna zuwa Gida suka tarar su hajiya dasu anty zainab da sauran dangi, an gyarewa maryama dakinta tsaf komai fes sai kamshin turaren wutar da aka kunna ne yake ta faman tashi agidan,

Dan zama maryama tayi ta shayar da jaririn sannan ta barwa su anty maijidda shi ta shiga daki saboda wanka take son tayi,

Tana shiga wankan shaddad ya shigo cikin bedroom din, motsinta da yaji acikin toilet ne ya fahimtar dashi cewar wanka take yi,

Kofar dakin ya sawa key yabita cikin toilet din, maryama sai ganinshi kawai tayi ya shigo yana balle botir din gaban rigarshi,

"Shaddad ya haka? Wanka fa nake yi"

"Nima wankan zanyi shine nazo muyi tare"

"Kai shaddad ka fiya rigima, nifa jego nake"

"Nasani ai, wankan kawai nake so muyi tare.."

"To idan su anty maijidda suka shigo fa"

"Babu mai shigowa ai na rufe kofar"

Tare suka yi wankan anty maijidda sai bugun kofar dakin takeyi saboda jaririn maryama yanata kuka, maryama ce taje ta bude kofar shikuma shaddad yana tsaye yana saka rigarshi, batare da anty maijidda ta shiga dakin ba tabawa maryama jaririn ta fita, wurin anty babba ta koma a inda suke zaune suna hirarsu,

"Nifa ana yin suna nima washe gari zan bar gidan nan.."

Anty maijidda tafada, "au wannan karon ba zaki taya yar taki zama ba?"

Inji anty babba,

"A'a wannan yaran ai yanzu sunfi karfina, tare suka yi wanka fa yanzu, ina zuwa suna fitowa shikuma gogan ko kunya ina ganinshi yana saka riga shiyasa ma ko dakin ban shiga ba"

Dariya anty babba tayi, "ashe baya yin surukar dake"

"Ai shiyasa zan tafi tun kafin yafito kiri kiri yace in tattara kayana in tafi"

  Sai da shaddad ya rikewa maryama jaririn ta shirya sannan ya bata shi ya fita, yana fita nu'aima ta shigo taje jikin maryama ta kwanta, shafa kanta maryama tafara yi tana jin tausayin yarinyar saboda yanda tayi ranar da zata haihu ba karamin tayar mata da hankali tayi ba,

Shaddad dakinsa yaje ya shirya yafita, tunda ya fita kuma bai dawo gidan ba sai da daddare, wasu na falo wasu kuma na dakin maryama yayinda wasu na daya dakin dake kusa da na maryama,

Ita maryama tana dakinta ita da khairat da anty maijidda da anty babba,

"Ni kam maryama nu'aima tayi shekara biyu ne?" Anty babba ta tambayi maryama,

"A'a Anty bata yi shekara biyu ba"

"Ni ai ban taba ganin likitar da tayi kunika ba sai maryama" anty maijidda taceda maryama tana dariya,

"To anty yaya zanyi ya hanani inyi planning yace ko aboye nayi bai saniba Allah ya isanshi.."

"Nima ai da wasa nake yimiki, kiyi haihuwarki wallahi muma ai duk kunikar muka yi shiyasa su hydar gasu nan duk Kansu daya"

Kafin maryama tayi magana shaddad ya shigo, anty babba ce ta tashi khairat tace taje ta kawo masa abinci, fita yayi yanata kallon maryama saboda yafi son ita takawo masa abincin ba khairat ba,

Koda khairat ta kai mishi abincin cewa yayi taje ta turo masa maryama, lokacin da khairat tazo ta fadi sakon anty babba cewa tayi maryama ba zataje ba sai anty maijidda tace abarta taje suje can su karata,

Tashi maryama tayi ta fita taje dakin shaddad, yana kwance akan gadonshi, agefenshi ta zauna tana kallonsa,

"Navy tashi kaci abincin mana"

Hannunta ya rike nan taji zazzabi ne ajikin nashi, zirga zirgar da yayita yine yanzu kuma take tambayarshi ga ciwon kai dake damunsa,

"Ya naji jikinka da zafi? Zazzabi kake yi?"
tashi zaune yayi ya kama hannayenta ya rike,

"Bani abincin naci sai ki bani magani nasha"

Murmushi tayi, "allura zanyi maka sai kafi jin dadi"

Bashi abincin tayi yaci tabashi ruwa yasha ya koma ya kwanta, tasan yana jin jiki amma sam baya son tagane saboda kar hankalinta ya tashi,

Fita tayi ta koma dakinta ta dauko allura da sirinji ta dawo, rub da ciki ta sameshi yayi ahankali tayi masa allurar,

"Washh.." Ya fada lokacin da yaji ta shigar da allurar cikin jikinshi,

"Da zafi ne?"

"Da zafi mana"

Zare allurar tayi tasa dan yatsanta tafara shafa wurin da tayi masa allurar,

Hannu yasa ya kwanto da ita jikinsa ya rungumeta,

"Dan Allah ki zauna mu kwana anan karki tafi"

"To kuma jaririn fa?"

"Zamuje mu daukoshi"

Murmushi tayi ta fara shafa kumatunsa, tana kallonshi idanuwanshi har sunyi ja saboda ciwon kai da zazzabin dake damunshi,

"Kayi hakuri dai ka kwanta kayi bacci saboda kaga akwai sirikai agidan namu su hajiya suna nan ga su anty babba da anty maijidda"

Hannunta ya rike sannan ya rike kanshi da daya hannun,

"Sannu Navy.." Tafada cikeda da tausayinsa saboda tun da taga yana yin haka to tasan yana jin jiki, tashi tayi ta shiga toilet dinshi ta debo ruwa a dan karamin baho tazo ta zauna abayanshi, rigarshi ta cire masa ta tsoma dan kwalinta aruwa ta fara matsewa tana goge masa goshinsa da jikinsa,

Ta jima tana yimasa haka har bacci ya daukeshi, sai da taga yayi nisa da bacci sannan ta fara kokarin tafiya, bakinshi ta yiwa kiss ta tashi zata tafi, hannunta taji ya rike ahankali kuma ya bude idonsa,

"Tafiya zakiyi ki barni baby?"

"A'a zuwa zanyi nadawo" sakinta yayi yana murmushi saboda bai san cewar wayo zata yi masa ba,

Sakin hannunta yayi ta tafi, yanda tabar su anty babba da anty maijidda haka tazo ta samesu suna hira khairat ce kawai tayi bacci,

Rigar bacci ta saka ta kwanta, har bacci yafara daukarta taji wayarta tana ruri, shaddad tagani mai kiran,

Tana dagawa taji yace, "baby najiki shiru.."

"Ya jikin naka navy?"

Lumshe idanuwanshi yayi yana jin dadin muryarta mai sanyi wacce take kara rura wutar sonta acikin zuciyarshi,

"Kinga ma wani zazzabin ne ya sake rufeni, zo kiyi min wata allurar"

Jin ya fadi haka yasata tashi da sauri ta fita tana rikeda wayar a kunnenta, a falo ta samu su anty maijidda sun maida dabar hirar tasu can sudai Allah ne kadai yasan lokacin baccinsu amma kowa sai yayi bacci ya barsu,

Dakin shaddad ta hara, tana yi masa magana a waya,

"Harda ciwon kan bai daina ba?"

"Shima bai daina ba.. Ba kiji ba kamar zai fita daga jikin.."

Daidai lokacin ta bude kofar dakin nashi ta shiga, a kwance ta sameshi yayi rub da ciki,

Zama tayi ta kwanta a bayanshi tana shafashi ahankali amma kuma sai taji jikin nasa sanyi kalau alamar babu zazzabin,

"Navy ai naji jikin naka babu zafi"

Murmushi kawai yayi baiyi magana ba ya mika hannunshi kan bed side drewar ya ajiye wayarshi ya kashe bedside lamp,

"Navy magana fa nake yi maka wallahi bacci nake ji"

"To kiyi baccinki mana"

Tashi tayi yayi saurin riketa,

"Dan Allah karki tafi"

"Nabar jariri adaki kar ya tashi yazo yana kuka"

Dakyar ta samu ta kwace ta koma dakinta taje ta kwanta saboda wani irin bacci take ji gashi ta gaji mutuka....


_*Ummi Shatu*_

No comments:

Post a Comment