Thursday, 1 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 47

_®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_


_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_


  _*NA*_

*_UMMI A'ISHA_*

    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _*Gaisuwa mai dunbin yawa gareku masoyan maryama sarauniya ina jida ku sannan ina alfahari daku....*_

   *_47_*

aishaummi.blogspot.com



~~~Duk karfin hali irin na shaddad wannan lokacin ji yayi ya kasa controlig din kanshi, idonshi cikeda wani irin duhu wanda ya hanashi ganin komai ya dubi dr muneerat,

"Tana ina?"

"Tana ciki.."

Bin bayanta yayi yana jan kafarsa domin bazai iya dagata ba, shi kuwa Dada yana nan tsaye awurin kamar an kafashi ya kasa koda motsi,

Tiryan tiryan shaddad yake biye da dr muneerat har zuwa dakin da maryama take lokacin har doctors din sunja farin kyalle sun lullubeta har fuska,

Jikinsa yana rawa hannunshi yana wani irin karkarwa ya yaye kyallen daga fuskarta, idanuwanta a lumshe amma kuma fuskarta dauke da murmushi kamar lokacin da tana raye, fadawa jikinta yayi ya fashe da kuka kamar ba namiji ba namijin ma soja,

"Dan Allah karki mutu maryama, kiyi hakuri kidawo muci gaba da rayuwarmu..."

Wani jirine ya debeshi daga nan ya zube awurin shikenan ya rasa hankalinsa bai sake sanin abinda yake faruwa ba, yana damke da takardar da maryama ta rubuta masa kam kam ya kasa sakinta ta fadi,

Kinkimarsa akayi akan wani gado aka nufi emergency dashi, koda Dada yaga haka sai ya kira driver yace yazo su dauki gawar su tafi da ita gida,

Haka kuwa akayi nan da nan aka fito musu da gawar maryama aka saka musu a mota suka nufi gidan Dada da ita, ahanya dada ya kirasu anty maijidda ya sanar musu, ai anty maijidda naji ta hau salati tana cewa,

"Wacce maryaman? Dazu fa ta kirani tace za ashiga dakin haihuwa da ita..". Nan ta kashe wayar jikinta yana rawa, tama rasa me zatayi dole sai samun wuri tayi ta zauna hawaye nabin kuncinta.

  Koda Dada suka je gida kafin wani dogon lokaci har gidan ya fara dinkewa da jama'a, su anty maijidda da anty zainab sunzo sannan su hajiya ma da yan uwan shaddad su anty babba sunzo, in banda koke koke babu abinda akeyi, babu mai rarrashin wani, wani karin abin tausayin ma sai da su baba ladi suka karaso itada nu'ayma nan nu'ayman ta rinka neman umminta tana kuka,

Cikin lokaci kankani aka yiwa maryama wanka aka shiryata, mutane sai zuwa suke daya bayan daya suna yi mata addu'a,

Shaddad kuwa sai da ya dauki fiyeda awa daya kafin hankalinsa ya dawo jikinsa, bude idonshi yayi nan take mutuwar maryama ta dawo masa cikin kwakwalwarsa ai zunbur ya mike ya fincike karin ruwan da ake yimasa ya fita jiri na daukarsa ba tare da ya saurari kiran da nurses din dake cikin emergency din suke yi masa ba,

Motar maryama da suka zo da ita ya shiga yafita daga asibitin aguje, yana driving yana kuka sannan har lokacin yana damke da wasikar da maryama ta rubuta masa,

Gidan Dada yaje anan yaga mutane sun fara taruwa wadanda zasu yimata salla,

"Me kuke yi anan? Maryama fa bata mutu ba, wallahi bata mutu ba, ku tafi, ku tafi, maryama tana raye..." Tamkar mahaukaci haka yake ta fada yana kuka hawaye nabin kumatunsa, cikin gidan ya shiga, yana shiga nu'ayma taso tazo ta rungumeshi tana kuka,

"Dady ka kaini wurin Ummi.."

"Mamana umminki tana raye bata mutuba, wallahi bata mutuba..,maryama ba zata taba mutuwa tabarni ba, waye ma yace ta mutu? Bata mutuba.."

Kowa binsa yake da kallon tausayi saboda ya zauce hankalinsa baya tare dashi,

Sakin nu'ayma yayi ya nufi falon Dada inda gawar maryama take, yana zuwa ya yaye lullubin da akayi mata ya dauketa gaba daya ya rungumeta ajikinsa yana kuka, takardar data rubuta masa ya warware yana sake karantawa rubutunta gashi nan mai kyau irin na likitoci kamar da computer aka rubuta bada hannu ba,

Sake damke takardar yayi yana wani irin kuka kamar ba soja ba,

"Maryama wallahi ina sonki, dan Allah kiyi hakuri ki dawo zan nuna miki irin soyayyar da nake yimiki, wallahi maryama ina sonki tun ranar farko dana fara ganinki, kiyi hakuri maryama nauyin baki nayi ban taba furta miki ba amma da ace zaki iya bude zuciyata to da kinga sonki mamaye acikinta,

Kiyi hakuri maryama, ina sonki, ina sonki, wallahi ina sonki, maryama ina sonki.."

Kamar a mafarki yaji taja wata irin doguwar ajiyar zuciya,nan zuciyarta taci gaba da aiki numfashinta ya dawo,

"Yawwa maryama dama nasan ba zaki mutu ki barni ba, sai da nafada musu baki mutuba amma suka ki yarda... Ni dama nasan ba zaki mutu yanzu ki barni ba.."

Ahankali take bude idonta tana kallonsa hawayen dake fita daga idonsa suna sauka akan fuskarta,

"Maryama wallahi ina sonki, ina sonki maryama, waye yace miki bana sonki, wallahi ina sonki..." Fashewa yayi da kuka ya rungumeta,

Su hajiya dake babban falo suna jin duk abinda yake faruwa su duk a tunaninsu shaddad zaucewa yayi dan haka hajiya ta mike ta nufi falon domin bashi baki da yimasa nasiha kan yayi hakuri ya karbi kaddara domin dukkan mai rai mamaci ne,

Tana shiga ta ganshi rungume da maryama ita kuma maryaman idonta a bude tana jijjiga masa kai alamun yabar kuka, ai hajiya komawa tayi da baya har tana yin tuntube,

"Bata mutu ba, wallahi ashe bata mutu ba" hajiya ta fada cikin razani,

Nan itama aka fara yi mata kallon ko tabi sahun shaddad dinne basu gama mamaki ba sai da suka ga shaddad ya fito dauke da maryama a hannunsa kamar wata jaririya zai mayar da ita asibiti saboda tanata yimasa nuni da cewar cikinta ciwo yake yi mata,

Mimmikewa tsaye sukai suna kallonsu saboda ganin maryaman idanuwanta a bude sannan tanata rirrike shaddad,

Nan kuma kowa ya shiga murna anty maijidda harda tsalle, taya juna murna aka shiga yi, shidai shaddad fita yayi da ita, su Dada na zaune suna jiran afito da ita ayi mata salla aje akaita makwancinta sai ga shaddad ya fito dauke da ita idanuwanta a bude tana kallon kowa,

"Dama nafada muku maryama bata mutu ba, wallahi bata mutu ba"

Sakata yayi a mota ya zagaya da gudu shima ya shiga ya finciki motar aguje ya koma asibiti da ita, kamar mahaukaci haka ya dawo, daukarta ya sakeyi bayan sunje asibitin ya nufi ciki da ita yana shiga yayi kicibus da dr muneerat nan ta nuna masa dakin da zai kaita, tare suka shiga ya kwantar da ita akan gado, yana makale da hannunta acikin nashi dr tafara dubata daga karshe tayi mata wata allura sannan ta daura mata drip,

Kafin wani lokaci har asibitin ya cika da yan uwa duk sun baro gida sun taho nan, shaddad yana zaune agefen gadon yana rikeda hannun maryama ahaka duk yan uwa suka shisshigo suka dubata suka fita,

Juyo da kanta tayi ta kalli shaddad saboda yanzu ta dawo cikin nutsuwarta sosai,

Cikin sauri ya daga kanshi yaje saitin fuskarta,tareda sake damke hannunta,

"Maryama kiyi hakuri wallahi ina sonki, idan bana sonki ai bazan zauna dake ba, tunda kika ga na zauna dake ai dan ina sonki ne...

Kiyi hakuri maryama dan Allah karki tafi ki barni ni kadai, wallahi idan babu ke nima bazan iya rayuwa ba,

Kiyi hakuri muci gaba da zama tare nikuma nayi alkawarin zan soki zan nuna miki soyayya fiyeda irin wacce kike nuna min.." Yana maganar ne hawaye yana bin kuncinsa,

"Kadaina kuka please.." Tafada ahankali,

Kifa kanshi yayi a kirjinta ya rungumeta, ita dinma rungumeshi tayi tana shafa sumar kanshi,

"Ina abinda muka haifa?"

Sai a lokacin shaddad ya tuna da batun jaririn domin shi tun lokacin da yaji mutuwar maryama bai kara bi takansa ba,

"Bari nasa akawo manashi ki ganshi.."

Fita yayi ya samu nurses din da ke zaune awaje yace akawo musu jaririnsu,

Komawa wurin maryama yayi ya zauna yakama hannunta ya rike cikin nashi,

Har aka kawo jaririn yana makale da ita, "ni babu ruwana dashi tunda ya wahalar min da matata har tayi dogon suma akace min ta mutu.."

Murmushi maryama tayi ta leka fuskar jaririn ta gani,

"Masha Allah, yaro mai kamada babanshi sak" tafada bayan ta koma ta kwanta,

"Nima ramawa nayi ai, last time mai kamada ke kika haifa shiyasa nima this time around na dage na samu mai kama dani"

Murmushi maryama tayi tana kallon shaddad wanda idanuwansa suke jajur har lokacin,

"Maryama kiyi min uzuri kibani dama irin damar da phertymah xarah tabawa jawad lokacin da ya rusa mata MARTABARTA,nikuma nayi miki alkawarin zan zama tafida bazan manta alkairinki agareni ba domin shi AlHERI DANKO NE, zaman da nayi dake na fuskanci kinada hakuri da juriya da kawaici fiyeda Aishan Abdulhakeem wadanda suka yi rayuwarsu karkashin inuwar BIYAYYAR IYAYE, kiyi min alfarma irin alfarmar da Ikhlas ta yiwa Lamido lokacin da yayi amfani da kalmar hausawa ta cewa RUWAN KASHE GOBARA basai mai kyau ba, idan kika bani dama zan yi amfani da SANADIN GATA na mayar dake WANI HASKE acikin rayuwarmu data yayanmu irin yadda jabir ya mayar da bahijja, sai na mayar dake tauraruwa fiyeda yanda Awwab ya mayar da nihal acikin KWARYA TABI KWARYA, insha Allah zaki kasance MACE GUDA DAYA TILO acikin birnin zuciyata tunda kin dade da daukar AURE a matsayin YAKIN MATA.."

"Kana sona..?"

Rufe mata baki yayi da hannunsa guda daya, "kidaina wannan tambayar, da bana sonki da bazan taba zama dake ba"

Matsawa yayi saitin kunnenta, "akwai wani lokaci guda daya wanda shi kadai ya isa ya sanar dake dunbin kaunar da nake yi miki..."

Murmushi maryama tayi ta lumshe idanuwanta tana mai sake jin wata irin zazzafar kaunar shaddad tana kwaranya acikin zuciyarta....


_masoya kuyi hakuri da wannan, gani nayi hankalinku ya tashi ne shiyasa na samu nayi muku wannan..._




*_Ummi A'isha_*

No comments:

Post a Comment