Thursday 1 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 24,25

[5/15, 10:04 AM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


   *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

    _Fatan alkairi ga duk masoyan littafin maryama sarauniya, masoya ina ganin sakonnninku kuma ina godiya, bazan iya zayyano sunayenku bane saboda yawanku amma sai dai duk wacce ta turo sakonta agareni mutukar ya riskeni to tana nan acikin zuciyata..._


   *_24_*


     ~~~Cikin lokaci kankani anty maijidda tasaka maryama awata islamiyya ta kudi wacce ake zuwa kullum da misalin karfe 10 nasafe a taso karfe 1 na rana,

Registration anty maijidda tayi mata har na naira dubu talatin sannan duk karshen term ana biyan dubu goma sha biyar amma kuma makarantar taci kudinta saboda akwai mazakuraren malamai masana wadanda suke koyarwa sannan duk dakikancin mutum cikin lokaci kadan zai kai matakin da akeso,

Dogon hijab har kasa ash colour shine uniform din makarantar dolen maryama haka ta burmashi ta tafi,

Tunda tafara zuwa makarantar kuma sai tazama busy koda yaushe bata da lokacin kanta gashi tana dawowa gida kuma anty maijidda zata fara dora mata wani sabon karatun, dan haka ba adauki wani dogon lokaci ba maryama tafara haddace azkar da hadisai marassa tsawo,

Yauma kamar kullum ta taso daga makaranta tana rikeda alqur'aninta tana kokarin karasawa wurin da ta ajiye motar da tazo da ita,

"Malama maryama..."

Juyawa tayi anan taga ya sayyadi dinsu ne malamin dake koyar dasu darasin alqur'ani,

"Ohh ni maryama nikuma da haka Allah ya jarrabeni wasu na sona nikuma ina son wani.."

"Ya sayyadi" tafada fuskarta babu yabo babu fallasa,

"Malama maryama kenan, wato nidai tun ranar da nafara tozali dake na yaba da kyakkyawar surar da Allah madaukakin sarki yayi miki..., ataikace dai maryama..., atakaice gaskiya kin kwanta min arai"

Murmushi tayi ta bude motar, "to ya sayyadi nagode madalla, yanzu sauri nake yi dan haka gobe ma karasa maganar"

"Ato a sauka lafiya malama maryama, Allah ya tsare"

Shiga motar tayi ta dauki hanyar gida tana yi tana tsaki saboda ita kullum burinta da addu'arta shine Allah ya hadata da shaddad amma maimakon su hadu sai haduwa take da wasu daban,

Kamar zata fashe da kuka haka ta shiga cikin gidan tana rikeda  kayan karatunta, a falo ta zube kayan sannan ta nemi wurin zama saboda yunwa takeji gashi ta gaji lis,

Anty maijidda ce ta fito daga cikin kitchen inda take shirya abincin rana,

"Yata andawo ne?"

Hamma tayi ta rufe bakinta sannan tayi magana "nadawo anty...."

"Angaji ko?"

Kai tadagawa anty maijidda tana jingina da jikin kujerar da take zaune,

"Ai naga alama tunda gashi nan ko magana bakya iyawa,bari nakawo mana abinci tunda na kammala.."

"Yawwa anty"

Cikin kitchen anty maijidda takoma taje ta zubo musu abincin data shirya jalop din shinkafa da taliya sai hadadden salad agefe da lemon kwakwa mai sanyi,

Tunda maryama ta zauna tafara cin abincin bata yi maganaba har saida tagama saboda yanzu tana dan iya cin abinci ba kamar da ba da sai ta wuni bata ci komaiba sai zallar tea empty,

Tashi tayi ta shiga daki tayi wanka tayi salla ta kwanta domin yin baccin rana amma kuma sai hakan ya gagareta maimakon ta runtsa ma sai tunanin abin sonta tafara yi dole babu yanda ta iya ta hakura ta tashi ta koma falo ta kunna kallo ta dauki wayarta ta kira Dada.

Yau tunda taje islamiyya taga wata bakuwar fuska a ajinsu wanda bata santa ba, yarinyar kyakkyawa da ita ya sayyadi yana yimata dori idan yafada itama ta fada ba karamin burgeta yarinyar tayiba saboda jin yanda take rero karatunta cikin kwarewa da iyawa gashi tsakiyar kur'ani ake biya mata kasancewar kowa dorinsa ake masa daban,

Sai da aka gama dorawa yarinyar sannan maryama taji ya sayyadi yace,

"Yawwa malama khairat Allah yabada Sa,a"

Juyawa yayi ga maryama "malama Maryam bismillah ko.."

Ita maryama ma sai taji kunya ta kamata saboda ganin ita ba wani nisa tayi acikin alkur'ani ba amma ga yarinya karama wacce bata wuce shekaru 25 ba ta kusa sauke alkur'ani,

Ahaka dai ta daure taje aka dora mata ta taso ta dawo ta zauna dama ita bata fiya shiga cikin yan ajinba saboda taga duk yarane ta girmesu ba sa'anninta bane,

Tana zaune ita kadai tana amsa wayar dr yazeed wannan yarinyar da aka kira da suna khairat tazo kusa da ita ta zauna tana murmushi,

Sallama tayi da dr yazeed ta juya wurin yarinyar,

"Adda maryam ina wuni..?"

Murmushin yake maryama tayi kafin ta amsa,

"Lafiya lau yagida"

"Lafiya lau, amma baki dade da fara zuwa makarantar nan ba ko saboda naga ban sanki ba, nima gida natafi shiyasa bana zuwa sai jiya nadawo, yan gidanmu duk suna Kaduna nan awurin yayata nake to shine last week muka tafi gida nida ita.."

Maryama dai sakin baki tayi tana ganin ikon Allah azuciyarta kuwa cewa take,

"Wannan yarinyar amma kinada surutu.."

"Kefa kema yar nan garince?"

Ta sake jiyo muryar khairat tana tambayarta,

"A,a nima zuwa nayi, a Lagos nake"

"Ohh Allah sarki nima kuwa ina son zuwa Lagos wallahi, amma dai ba canne asalin garinku ba?"

"Uhm.." Maryama tabata amsa a takaice saboda ita bata son yawan magana"

"Inane asalinku?"

"Jimeta.." Maryama tabata amsa cikeda kosawa,

"Ashe shiyasa naganki haka tubarkalla, Allah sarki"

Ita dai maryama shiru tayi mata tana binta da ido domin ita dai tunda tafara zuwa makarantar nan babu abinda yake hadata da yan ajin sai gaisuwa daga nan kuma bata shiga harkarsu saboda tana son taja girmanta..



*_Ummi A'isha_*🏻
[5/15, 10:04 AM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOC.(HWA)_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

    *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_


   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _*25*_

aishaummi.blogspot.com

  ~~~Zubawa yarinyar ido kawai maryama tayi tana ganin kokarinta yanda ta dage take tayi mata surutu kamar ba yaune ranar farko data fara ganinta ba, ita idan itace tayi wannan surutun ai sai kanta yayi ciwo,

"Adda maryam wacce makarantar kikeyi?"

Murmushine ya subucewa maryama saboda ita rabonta da makaranta ai tafi shekara biyar saboda tun tana 25 years tazama kwararriya kuma cikakkiyar likita,

"Ni ai najima da gamawa, yanzu bana zuwa school"

"Ohh Allah sarki nikam iya diploma nayi amma ana nema min admission a federal university dake Kaduna da zarar nasamu zan bar abuja nakoma can nafara zuwa makaranta"

"To Allah ya bada sa,a"

Ita dai yarinyar nan khairat haka kawai taji maryama ta burgeta saboda yanda take yin komai nata a nutse babu hayaniya gata yar gayu kyakkyawa fes da ita komai nata cikin jan aji,

Yayinda ita kuma maryama ta kosa da maganganun da khairat keyi mata saboda ita bata son hayaniya,alla alla take atashi ta tafi gida domin taji kanta yana neman ciwo,

Koda aka tashin ma biyota khairat din tayi har wurin motarta tana yimata zance,

"Adda maryam kibani phone number dinki mana saboda wani lokacin ko bazan samu damar zuwa ba sai in sanar dake"

Bata phone number din maryama tayi ta shiga mota ta wuce, tun daga kofar gida tasan yan makaranta sun dawo saboda yanda take jiwo hayaniyarsu,

Tana shiga kuwa ta gansu barbaje a falo suna ta faman cin abinci,

Yaran anty maijidda biyar duk maza dayace mace yar autar wadda yanzu take jss 1 a Nigerian Turkish school dake nan cikin birnin abuja,

"Ahh anty dama yau yan makaranta zasu dawo shine baki fada min ba?"

"Ina sone in baki surprise dama tun safe driver yatafi debosu"

Tasowa sukayi yaran dukansu suka rungumeta, itama rungumesu tayi saboda tana jin sonsu kamar ciki daya suka fito, zama tayi tana binsu da kallo daya bayan daya domin har yanayi suke yi da ita afusge, nan anty maijidda tafara tuna mata sunayensu domin duk sun giggirma shiyasa ma takasa banbancesu,

"Kinga sadiq nan ga faruk, ga haydar, ga usy nan ga kuma yanmata na nan aysha autata, ko autan mama" anty maijidda tafada tana dariya,

"Anty ai ke duk sunayen iyayena kika hada hadda fa sunan surikina baban shaddad"

"Shi din ya sunan baban nashi?"

"Sadiq wallahi"

"Ahh to kai sadiq kazama surikin adda maryama dan haka sai tafara girmamaka tun daga yanzu.."

Dariya maryama tayi tace "ai ko baki fada ba anty.."

Haka suka cigaba da barkwancinsu da raha itama ta shiga ta zauna suka fara cin abincin tare da ita domin ita bata san dadin yan uwaba tunda ta taso ita kadai take rayuwarta babu yaya babu kani, koda yamma tayi ma kwasarsu tayi suka fita yawo har anty maijidda basu suka dawoba sai daf da sallar magrib,

Agajiye suka dawo tana bawa anty maijidda labarin khairat yar islamiyarsu mai surutu, sai dariya suke anty maijidda nacewa,

"Kin hadu da aku kenan gashi ke kuma bakya son surutu"

"Ai anty wannan yarinyar tafi parrot..".

Haka rayuwar maryama taci gaba da kasancewa kullum bata fashin zuwa makaranta shiyasa sannu ahankali har tayi nisa a karatu, khairat kuwa koda yaushe a makaranta tana kusa da ita tana yimata zance shiyasa yanzu itama har ta saki jiki da ita tana biyeta suna hira, yauma kamar kullum bayan angama yimusu dorin karatu malamin ya fita maryama take cewa khairat,

"Khairat ina gayyatarki birthday dina gobe, ko baza abarki agida ba?"

"Za abarni mana anty, shekaru nawa zaki yi? Ko 26?"

Murmushi maryama tayi, "26 khairat ai sai dai yata kuma na 30 years zanyi"

Kwalalo ido khairat tayi amma bawai dan tayarda ba duk a zatonta maryama bata kai haka ba,

"To Allah ya kara nisan kwana zanzo"

Washe gari da yamma akayiwa gidan anty maijidda decoration aka shirya abubuwa duk da cewar ba wasu mutane akayi inviting ba iya maryama ne kawai sai yaran gidan sai ko khairat da tazo,ko ina maryama tayi binta take da kallo saboda yanda tayi kyau cikin blue din gown mai tsada wacce tasha stones ajiki,

Sosai suka taya maryama celebrating akaci aka sha sannan aka yanka cake, sai mangariba sannan khairat tatafi gida,wannan dalilin ne yasa washe gari itama maryama tace da anty maijidda zataje ta ziyarci khairat din ta kaimata ziyara tareda yimata bangajiya saboda zuwan da tayi mata jiya, duk da cewar yarinyar ba sa'arta bace amma tana son yin zumunci da ita,

Shiryawa sukayi ita da A'isha suka tafi, sai da ta biya ta wani store tayiwa khairat yar siyayya na kayan kwalliya da turare sannan suka je gidan wanda ke cikin unguwar mai tama,

Murnar da khairat tayi kamar zata yi hauka,cikin rawar jiki ta kaisu falon baki taje ta fara kokarin kawo musu kayan motsa baki, sai murna take ta kawo musu ruwa da lemo suka sha,

"Kuzo muje ku gaisa da antyn nawa to"

Fita sukayi zuwa wani falo inda matar ke zaune tana rubutu acikin wani littafi,da fara'arta ta karbesu suka gaisa suka tashi zasu fita, har sunkai bakin kofa kamar wadda aka cewa maryama juya sai ta jiyo nan idonta suka sauka kan hotonshi kato wanda ke manne ajikin bangon falon yana sanye cikin uniform dinshi na sojoji yayi kyau har ya gaji...

*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment