Friday 23 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 42-46

[5/21, 8:48 PM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_


*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


  _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

   _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

_Gaisuwarku ta dabance, Benaxir Omar,Lubabatu m/tafsir,Khaleesat Hydar,Hafsat Bunza,Teemah cool & A'isha (maman Khadija)_


  *_42_*

aishaummi.blogspot.com

~~~Komawa tayi tai kwanciyarta saboda yau ta fadawa shaddad abinda ke cikinta, wunin ranar akwance tayi shi babu abinda ta iya tashi tayi har dare yayi, shirin bacci tayi ta sakawa kofarta key ta kwanta,

Kwananta uku agida bata fita ko ina har saida taji tafiyarta tafara komawa normal sannan ta fara zuwa aiki, ai shaddad kuwa na ganin haka yafara kaiwa dakinta ziyara duk daren duniya kullum cikin kokawa suke dakyar ya hakura ya rabuda ita ta huta na tsawon sati biyu, aranar da ta cika sati biyun aranar ya ritsata a daki,

Tana daure da towel ta gama shan tea kenan ya shigo,

"Lafiya?"

"Kinfi kowa sanin in lafiyarce ta kawoni ko kuma sabanin haka, zan cikawa mahaifiyata umarni ne"

"Kar kayiwa hajiya karya.."

"Nine makaryacin?" Ya tambayeta yana dosota, kafin tayi yunkurin tashi har ya take kafarta da tashi,

Daukarta yayi zuwa saman gadon, sanin irin bakar azabar da tasha rannan yasa yau bata bawa kanta wahala wajen biye masa suyi kokawa ba, rabuwa tayi dashi ya karaci sha'aninsa yayi abinda yake so sai dai kuma yau sai taji har tafi rannan shan wahala saboda dinkin dake jikinta, ji take kamar ana bin jikin dinkin ana farkewa,

Tana son tayi kuka amma bata son yaji ya samu damar rainata, sai da tasha mutukar wahala kafin ya kyaleta ashe barinta yayi ta huta,

"Yau na hadu da jarababben miji ni maryama nashiga uku, wannan gayen kasheni yake son yayi ne?" Ta fadi hakan acikin zuciyarta, juya kanta kawai take yi saboda azaba,

K'ankameshi tayi sosai kamar zata koma cikin cikinsa, yana son ya tafi ya koma dakinsa amma haka ya hakura saboda ta rirrikeshi kamar wacce take tsoron wani abu, ahaka suka kwana tana kankame dashi saida safiya tayi wurin karfe shida sannan tafara sakin doguwar ajiyar zuciya,ahankali tafara sassauta rikon da tayi mishi tana jan zuciya da haka har ta sakeshi gaba daya, shidai yana kwance yana kallonta, jin ta bar jikinsa ta koma gefe ta kwanta yasashi tashi ya shiga toilet dinta, in banda kamshi babu abinda bathroom din yake kamar ba ashiga ciki, yasan dama dole tayi tsafta saboda kasancewarta likita,

Tsaftace jikinsa yayi ya fito yana kallonta har lokacin tana kwance tana bacci taja bedsheet ta rufe rabin jikinta, dakinshi ya koma yayi salla ya kwanta.

  K'arfe bakwai da yan mintuna maryama ta samu dakyar ta tashi taje tayi wanka tazo tayi salla, wata doguwar shimi kawai ta zira takoma ta kwanta nan take jikinta yafara ciwo, samu tayi bacci ya dan dauketa,

Cikin bacci shaddad yaji ana bugun kofa, kamar a mafarki yake jin bugun, bude idonshi yayi ya tashi ya fita daga shi sai gajeren wando da t shirt ruwan toka,

Yana bude kofar yaga hajiyarshi ce itada khairat,

"Hajiya sannunku da zuwa.."

"Yawwa mazaje sannu"

Basu hanya yayi suka wuce ciki shikuma yana biye dasu a baya, tiryan tiryan khairat take tafiya har zuwa dakin maryama wacce ke kwance tana dafe da goshinta,

"A'a ko baku tashi bane?" Hajiya ta fada tana kallon shaddad,

"Ehh wallahi hajiya"

Cikin bacci maryama take jin maganganunsu ahankali ta bude idonta ganin hajiya da khairat yasa tafara kokarin tashi tana murmushi amma ta kasa, komawa tayi ta kwanta tana cije lebenta,

"Hajiya sannunku da zuwa, khairat yanzu kuka zo?"

Hajiya ce ta amsa da,

"Yawwa sannu maryama, daga gani ma bakya jin dadi, yi kwanciyarki basai kin tashi ba"

Juyawa tayi ga shaddad wanda ke tsaye abayanta, "mazaje wuce muje"

Fita suka yi daga dakin sai khairat ce ta zauna agefen gadon tana kallon maryama cikeda tausayawa,

Daya dakin da babu kowa hajiya ta shiga itada shaddad a bakin gadon dake cikin dakin ta zauna, shaddad ya durkusa ya fara gaisheta  maimakon ta amsa gaisuwar sai cewa tayi,

"Mazaje me kayiwa yar mutane ta kasa tashi..?"

Shiru yayi saboda jin tambayar da hajiya tayi masa, "to ni yanzu me zancewa hajiya?", yafadi acikin zuciyarsa kafin ya lalubo amsar da zai bata yasake jiyo muryarta,

"Bada kai nake magana ba? Kafada min abinda kayiwa yarinyar mutane ta kasa tashi"

"Hajiya ni babu abinda nayi mata"

"Shine nazo na sameta akwance tana son ta tashi amma ta kasa ahakan babu abinda kayi mata?, mazaje ka fita daga idona wallahi akan yarinyar nan zanci mutuncinka zan sassaba maka"

Shiru yayi amma kuma duk kunya ta kamashi saboda yasan hajiya tagane abinda yafaru shi da yasan zata zo yauma ai da hakan bata faruba,

"Ka rage wanan zafin ran naka akan iyalinka.."

"Hajiya dan Allah kiyi hakuri insha Allah bazan sake ba, dan Allah kiyi hakuri"

"Shikenan Allah yayi muku albarka, mun sameku lafiya?"

"Lafiya lau hajiya"

"Yau bazaka fita aikin bane?"

"Yanzu zan shirya natafi"

"To madalla, sai katashi kaje ka shirya ai tunda mu muna nan"

Tashi yayi ya fita ya shiga dakinsa ya fada wanka,

Su hajiya na fita maryama ta rike hannun khairat,

"Khairat taimaka min naje nayi wanka"

Riketa khairat tayi ta tashi ta shiga bathroom ta dade acikin ruwan zafi sannan tayi wanka ta fito, kafin ta fito har khairat ta gyara mata dakin ta koma kitchen ta dora musu abin karyawa, shiryawa tayi ta saka wani material dinkin riga da skirt ta fita dakin da hajiya take, cikin fara'a da kulawa hajiya ta amsa gaisuwarta suna gama gaisawa hajiya tace ta koma dakinta ta kwanta kafin khairat ta kammala abincin karyawa, tashi tayi tafita tana tafiya ahankali, zata shiga dakinta shikuma shaddad ya fito da uniform ajikinsa, cikin dakinta ta shige ba tareda ta kalleshi ba, kwanciya tayi tana tuna rayuwarsu da shaddad, yanata ikirarin baya sonta baya sonta amma kuma yafi kowa iya fada mata Kalmar so da kalmomin kauna adaren jiya da daren farkonsu, ko kuma dan ba acikin hankalinsa yakeba shiyasa baya sanin lokacin da yake fada oho,

Shigowar khairat ce ta katse mata tunaninta, zama tayi akusa da ita,

"Sannu adda maryam wai dama haka sojoji suke"

Kallonta maryama tayi, "yayanki mugu ne khairat, sam bashida tausayi.."

Dariya khairat tayi "kai adda maryam agaban nawa zaki rinka cewa yayana mugu ne?"

"Wallahi mugu ne na karshe, dan rainin hankali yanata ikirarin wai zai auri yarinya yar 18 to da ace ita ya aura yayiwa abinda yayi min da ina jin kasheta zaiyi, mugu kawai"

Dariya khairat tayi "adda maryam maida wukar, ki huce dan Allah, wai dama sai jiya akayi first night din?"

"Khairatu kenan wannan second night ne amma yafi first night wahala, first night dinmu sai da naje aka yimin dinki, to jiya yabi dinkin yaso farkeshi shiyasa nace miki yayan nan naki mugune"

Karaf sai a kunnen shaddad kalmar data fada ta karshe wai yayan nan naki mugune, shidai bai san akan me suke magana ba amma yasan maganarshi ake kuma dashi maryama take,

"Ke khairat wai baki gama hada abincin bane? Ina saurine fita nake son nayi"

Tashi khairat tayi da sauri tana fadin "sorry yaya Navy, wallahi mantawa nayi.."

Bin maryama da kallo yayi wacce ke kwance idanuwanta arufe, fita yayi yabi bayan khairat zuwa kitchen,

Titsiye khairat yayi wai sai ta fada masa me maryama take fada mata harda kiranshi da mugu,

"Yaya bafa maganarka ake yiba"

"Wallahi karya kike maganata kuke yi, me kuke cewa?"

"Nima namanta mema muke cewa Allah"

Rabuwa da ita yayi ya fita yakoma wurin hajiya ya zauna, kayan breakfast din khairat ta kinkima takaiwa hajiya nasu itada shaddad ita kuma itada maryama ta kai musu dakin da maryaman ke ciki,

Ruwan tea kawai maryama ta iya sha jin ta danji dama dama yasata tashi taje wurin hajiya ta zauna lokacin shaddad yafita.

  Khairat ce tayi komai agidan hatta abincin rana itace ta girka musu, ita maryama tana wurin hajiya suna hira, yamma likis shaddad ya dawo gidan komawa dakinta maryama tayi khairat ta bita tana dariya,

"Adda maryama nimafa ina son in auri soja"

"Ki aureshi yarinya ke zaki gane kurenki, sojoji jarababbun matane.."

"Hakane amma ai ke kinyi dace adda maryam, Yaya Navy baya shan komai koda sigari baya sha sannan babu ruwansa da matan banza, amma kinga shi yaya Yusuf yana shan sigari.."

"Yayanki kam nima na shaideshi anan sai dai akwaishi da mugunta"

"Ah adda maryam wannan kuma ai tsakaninku ne"

Haka suka cigaba da hirarsu har magriba tayi,

Ba karamin dadin zuwansu hajiya maryama tajiba, koda dare yayima tareda khairat suka yi kwanciyarsu, sannan kullum khairat ce take yin komai nagidan har saida maryama ta warware sannan suke yi tare, satinsu daya suka fara haramar tafiya, sha tara ta arziki maryama ta hada musu suka tafi amma kafin hajiya tatafi saida ta barwa shaddad sallahun lallai lallai blessing mai aikin maryama tadawo gidan saboda ta ringa ragewa maryama ayyuka,dolensa babu yadda zaiyi yace to,

Adaren ranar da su hajiya suka tafi ya hana maryama sakat, danma wannan karon bata sha wuya kamar wancan ba,

Kyaleta yayi yakoma dakinsa asuba nayi yasake dawo mata, ita dai takasa gane wannan jaraba irinta shaddad, babu yanda ta iya dole haka zata jure tunda tagamu da gamonta,

Washe gari blessing tazo da kayanta, nan maryama ta zaunar da ita ta gaya mata cewar banda zama a falo idan shaddad yana nan sannan ba itace zata rinka girkiba ita dakanta zatayi girkinta sannan banda shiga dakinta da na shaddad, ko me take bukata tabari idan tafito sai ta tambayeta saboda yanzu ba irin da bane lokacin da tana gida,

Maryama tayi hakane saboda tasan halin shaddad idan jarabarsa ta motsa da rana ma hanata sukuni yake,

Tunda blessing ta dawo gidan sai maryama ta samu saukin aikin da take yi lokaci kadan tayi kiba tayi kyau,

Tana kwance afalo sanye cikin english wears blessing ta fito hannunta rikeda maggi kala kala,

"Anty kinga wannan maggin kina sone ko in dauka.."

"Blessing karki matso nan da maggin nan tsaya daga nan bana son warinsa"

Tsayawa blessing tayi daga nesa tana nuna mata maggin daga karshe dai maryama tace ta dauka tabata saboda ya dan jima a ajiye a store,

Tana nan kwance shaddad ya fito yazo kusa da ita, ko bai fada ba tasan abinda yake nufi, gocewa tafara yi daga rikon da yake kokarin yimata saboda ita idan tana period kamar mai ciki take zama gashi sam bata son kowa yaje kusa da ita ko lokacin da tana gida daga blessing taje kusa da ita zata koreta amma idan normal take itace zata yi mata komai,

Tureshi ta shiga yi saboda bata son taji mutum ajikinta,

"Dan Allah ka matsa.."

Tunda yaji tafara fadin haka yagane period take saboda wancan watanma haka suka yi da ita daga ya matso kusa da ita zata fara cewa ya matsa, amma idan lafiya lau take ko sau nawa zaije kusa da ita bata k'i,

Tashi yayi ya fita amma gaba daya atakure yake saboda kwanakin da takeyi idan tana period sunyi masa yawa har tsawon kwana takwas,

Tunda yafita bai dawoba sai da daddare, tana falo ita kadai tana kallo domin ta kora blessing daki,kusa da ita shaddad yaje ya rungumeta, duk da yasan bata so tunda yanzu tana cikin wani irin yanayi,

"Kwanakin nan naki sunyi yawa, wai babu wani abu da zakisha ne ya rage kwanakin?"

"Babu.." Tafada atakaice daga nan bata sake magana ba amma acikin zuciyarta cewa take"babu abinda zansha bayan nasamu zan dan huta da jarabarka",

Rungumeta yayi sosai yana jujjuya kanshi a kirjinta da haka har bacci ya kwasheshi, tana daga inda take ta mika remote ta kashe tv din dake kunne tana aiki, ahaka suka kwana afalo har saida asuba tayi ya tashi sannan itama takoma daki, tausayinsa kuma ta danji dan haka ta sha wani magani wanda yake sa rushing sannan yake rage kwanaki, cikin kwana hudu ta gama....


*_Ummi A'isha_*
[5/21, 8:48 PM] Ummi Shat🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*


  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*




  _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


   *_43_*



~~~Tunda yaga alamun ta gama yaji ya kasa hakuri,

Blessing yaje ya aika kasuwa iyo siyayyar da babu gaira babu dalili, yana ganin ta fita yaje ya rufe gidan ya nufi dakin maryama, tana yin sallama daga sallar da take yana shiga, binsa da kallo tayi,gajeriyar addu'a kawai tayi ta shafa ta mike, riketa yayi ya nufi kan gado da ita, kallonshi kawai take saboda irin yanda jikinsa yake rawa kamar sun shekara basa tare,

K'arshen soyayya yana nuna mata aduk lokacin da suka kebe a matsayin ma'aurata, gaba daya mantawa yake da batun cewar baya sonta yayi ta nuna mata zallar so yana yimata kalaman soyayya,

Sun kwashe awanni acikin duniyar ma'aurata kafin shaddad ya hakura, rungumeshi tayi sosai tana ajiyar zuciya har na tsawon wani lokaci, tashi yayi ya fita zuwa dakinshi ya shiga wanka zuciyarsa cikeda farin ciki domin ya samu nutsuwa dari bisa dari,

Yana fitowa daga wanka ko gama shiryawa baiyi ba yaji anfara bugun kofa, ko ba afada masa ba yasan blessing ce ta dawo, tsaki yaja saboda shi gaskiya yana takura badan umarnin hajiya ne ba da tuni ya dade da korar blessing,

Rigarshi ya zira ya fita yaje ya bude mata kofar ya dawo dakinsa yaci gaba da shiryawa,

Maryama kam tana can tana baccin gajiya, ba ita ta tashiba sai da yamma, wanka tayi tasaka english wears jeans da t shirt ta fita falo,

Blessing ta gani zaune tana gyara alkama,

"Blessing wannan fa na meye?"

"Anty oga ne ya aikeni na siyo"

Murmushi maryama tayi ta nemi wuri ta zauna saboda tasan dalilin shaddad nayin aiken babu gaira babu dalili, kawai ya aiketa ne saboda ya samu ya hutawarshi, "shikenan sai muyi kunu da ita" tafada tana murmushi,

Haka da daddare ma bai iya hakuri ba har sai da ya ziyarci makwancin maryama, haka da asuba ma, ita dai maryama koda yaushe yazo bata gudunshi saboda son da take yimasa bazai bari ta barshi acikin matsala ba, soyayyar da take yi masa bazata bari ta iya hanashi kanta ba, sannan a iya wannan lokacin ne kawai yake nuna mata kauna da soyayya,

Kullum haka take dawainiya dashi da daddare da asuba daidai da rana daya bata taba nuna masa gajiyarta ko kuma taki amince masa ba, ita yanzu harma ta saba da lokutan da yake zuwar mata ta daina jin wahala,

Kullum shi kenan cikin cewar zai auro karamar yariya, idan taji haka sai dai tayi murmushi tace,

"Nidai na fada da karamar yarinya yar 16 wacce bata adana mutuncinta ba gara tsohuwa yar 30 wacce ta adana mutuncinta har takaishi gidan mijinta"

Anty maijidda ce ta bata shawarar cewar ta nemi islamiyya tashiga taci gaba da zuwa saboda ko babu komai zata rinka samun karuwa akan ilmin da take dashi ada,

Wata islamiyya ta shiga asabar da lahadi acan unguwar hausawa tsakinsu da unguwar da nisa amma haka take samu ta daure taje duk sati sannan babu laifi tana samun karuwa sosai.

Haka zamansu yaci gaba da tafiya tsakaninta da shaddad, tun farkon aurensu har yau shaddad bai taba furtawa maryama kalmar so ba sai a lokacin mu'amalar auratayyarsu kawai,

Yau kam da ciwon jiki tatashi gashi tana ta jin tashin zuciya da wani irin jiri, duk atunaninta malaria ce ta kamata amma da taji tanata yawan yin yunkurin amai sai ta zargi cikine, nan ta dauko abin gwaji ta gwada, tana gwadawa taga cikinne kuwa wata daya,

Maganin hana tashin zuciya ta balla tasha ta kwanta, yau kwata kwata ta kasa cin abinci sai tashin zuciya dake damunta da zazzabi zazzabi,

Ko office bata fitaba tana kwance agida ta aika blessing ta samo mata farar kasa tanata sha, yawu kuwa kamar anbude fanfo haka take ji yana cika mata baki,

Tana kwance a falo tana shan farar kasar shaddad ya shigo, tashi tayi ta shiga bedroom dinta ta shiga bathroom domin zubar da yawun da ya cika mata baki,

Dawowa tayi falon ta kwanta, girkin da blessing tayi gaba daya sai tayar mata da zuciya yake dan haka ta tashi daga falon ta koma dakinta ta kwanta, wata yar karamar robar man shafawarta da ya kusan karewa ta dauka take zuba yawun aciki saboda tagaji da wannan zirga zirgar zuwa bathroom din zubar da yawu,

Shaddad ne ya shigo cikin dakin yana yi mata magana,

"Hajiya ta kirani dazu tace kin tura musu sako ko?"

Sai da ta tofa yawu acikin robar dake hannunta sannan tayi magana,

"Ehh ai ba wani mai yawa bane.."

"Tace to ayi miki godiya tagode madalla"

Wani yawun ta sake zubarwa sannan ta amsa masa,

"Babu komai"

Tun da shaddad yaga haka ya fahimci cewar cikine da ita saboda yaga sai tofe tofen yawu take alhalin ada ba haka takeba,

Juyawa yayi ya fita zuciyarsa kunshe farin ciki, wurin lokacin sallar mangariba ya shiga dakin nata saboda yana son zai fita,

Zaune yaganta da wani magani ahannunta zata sha, cikin sauri yaje ya karbe maganin yafara dubawa _well women_ yaga anrubuta ajiki, nan yafara karanta rubutun dake jikin kwalin, hankalinsa ne ya kwanta saboda ganin maganin mai amfani ne ga jikin mata bamai cutarwa bane,

Fita yayi batare da yayi magana ba,nan ya tafi ya barta taci gaba da tofe tofen yawunta.......




*_Ummi A'isha_*🏻
[5/21, 8:48 PM] Ummi Shatu: _*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_


  _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

   _*44*_


~~~Duk da kasancewar bata jin dadin jikinta wannan bai hana shaddad zuwar mata ba, haka ta daure ta cije ta bashi hakkinshi acikin wannan daren, yana dawowa daga sallar asuba ya sake dawo mata,

Dan haka dasafe kasa tashi da wuri tayi sai wurin misalin karfe 9 sannan ta tashi tayi wanka ta fito,

Lokacin data fito tuni har shaddad ya jima da fita amma ya barwa blessing sako tafadawa maryama zai dawo yaci abinci anjima,

Zama tayi a falo ta fadawa blessing abinda zata dafa, ita kuma ta hada bakin tea tasha,

Bayan blessing ta kammala aikace aikacen gidan ne maryama ta aiketa kasuwa taje ta siyo mata ganda saboda ita take sha'awar ci,

Tana zaune ita kadai tana kallo gefe daya kuma robar tara yawunta ce sai budewa take tana tofawa shaddad ya shigo,

"Sannu da zuwa" tace dashi tana canja channel da remote a hannunta,

"Yawwa, angama abincin?"

"Gashi nan akan table"

Kan table din yaje ya zauna ya debi abincin ya fara ci, yana yi yana kallonta, motsi kadan sai ta yamutsa fuska ta bude roba ta tofa yawu, da haka har blessing ta dawo ta kawo danyar gandar data siyo mata,

Daukar gandar tayi tana sansanawa, da adane ta sansana ganda da amai zatayi amma ayanzu har wani kamshi take ji gandar tana yi mata maimakon karni,

"Blessing tuwo nake so, idan kika yimin tuwon sai kiyi miya da wannan gandar"

Yana jinta ta fadi haka acikin zuciyarsa yace, "keda kika tsani tuwo yanzu kuma shi kike so?"

Tun daga ranar kullum babu abinda take son ci sai tuwo, abubuwan da ada take son ci yanzu duk ta tsanesu musamman ma masu madara irinsu cornflakes, golden morn, viju milk, ziza, duk yanzu bata sha saboda amai suke sata.

Tana tsaka da wannan laulayin su anty maijidda suka zo itada anty zainab saboda rabonsu da ita tun bikinta watanni biyar da suka wuce,

Tana kwance adakinta tana faman shan farar kasa suka zo dama ranar shaddad baya nan sun tafi Ilorin duk tanata missing dinshi kuma bazai dawo ba sai wani satin,

Tashi tayi cikeda murna taje ta rungume anty maijidda, amma cikin hanzari ta saketa saboda kamshin humarar da tasaka ta tayar mata da zuciya, bathroom ta shiga tayi amai ta fito,

Anty zainab kallon anty maijidda tayi ta kuma kalli robar da maryama take tara yawu ga kuma farar kasanan cikin wata farar leda,

"Anty maijidda kin kusa samun jika sai kifara tanadin kayan baby"

Dariya anty maijidda tayi, "nima ai na fahimci hakan zainabu, Allah ya rabasu lafiya"

Fitowa maryama tayi daga cikin bathroom bayan ta gama aman,

"Wai anty maijidda wannan humrar taki amma da karfi take, koda yake nima tawa haka nake jinta yanzu shiyasa ma na daina shafawa ciwon kai take sakani da amai"

Murmushi anty maijidda tayi suka karasa bakin gadon suka zazzauna,

"Yata kenan ashe andace har an samu rabo"

Dauke kai maryama tayi cikin jin kunya, "anty ina daddy? Inasu haydar?"

Dariya anty zainab tayi "kinji yarinya taki zancen.."

Nan suka gaggaisa suka shiga hira, da Kansu su anty maijidda suka shiga kitchen suka yi girki sannan suka tukawa maryama tuwon shinkafa miyar agushi, ba karamin dadin zuwansu tajiba domin sun dauke mata kewar mijinta,

Kwanansu biyar saboda shaddad baya nan amma da ace yana nan da kwana biyu zasuyi, ana igobe zai dawo su anty maijidda suka tafi bayan sun zaunar da maryama sun yimata jawabai kala kala kan yanda ya kamata ta kula da mijinta yanzu Sannan kar ta rinka gudunshi,

Sai karfe 8 nadare su shaddad suka sauka, dayake garin garine na damina tuni har anfara ruwan sama, dan haka ajike ya dawo gidan yasa key ya bude ya shiga, ganin maryama tayi bacci ya kyaleta bai tasheta ba sai da asuba ya shiga dakinta, sai lokacin ma ita tasan ya dawo,

Tari tafara yi sosai saboda har ya goga mata murar da yazo da ita jiya, haka ta fito da safe hancinta yana yoyo ga uban tari da take, shi kanshi yasan shine silar wannan murar tata,

Kullum maryama tana gida bata fita aiki saboda laulayin dake damunta ko gidan Dada bata iya zuwa sai shine yake zuwa ya dubata duk bayan kwana biyu, sai da cikin ya danyi kwari ya shiga wata na shida sannan tafara fita,acikin wannan lokacin su shaddad aka turasu kasar burtaniya kuma ta ruwa zasu tafi, hankalin maryama ba karamin tashi yayiba, sallama shaddad yayi mata ya tafi,

Aranar da ya tafi kasa bacci tayi tanata sakar zuci wani lokacin har tunani take cewar kila fa sallamar kenan tsakaninta da shaddad ba lallai ya dawo ba, kuka tayi sosai wanda ta dade bata yi irinshi ba,

Kullum idan ta tashi daga aiki sai taje gidan dada shine yake kwantar mata da hankali yace karta damu ai babu wani abu shaddad zai dawo,

"Dada wata da watanni fa zasuyi acikin ruwa, tayaya zasuci abinci? Tayaya zasu sha ruwa? Tayaya zasuyi ibada?", haka take fada kullum tana kwalla,

"Kibar damun kanki daughter, insha Allah babu komai"

Kullum haka sukeyi da dada yayita rarrashinta yana nuna mata cewar shaddad zai dawo mata lafiya da yardar Allah.

  Haka ta hakura taci gaba da gudanar da al'amuranta amma kuma duk ranar da tunanin shaddad ya tunkudo ta to kwana take bata runtsaba gashi dama tunda ya tafi ko sau daya basuyi waya ba saboda babu dama tunda shi yana cikin ruwa,

Ita tausayinsa ma takeyi kullum tunaninta tayaya zaici abinci,tayaya zai sha ruwa alhalin yana cikin ruwa?.

  Akwana atashi babu wuya har shaddad yayi wata biyu da tafiya kullum cikin zuba idon dawowarshi take amma shiru, har suka kusa shiga wata na uku, nan hankalin maryama ya tashi,

Watansu uku cif ranar talata da daddare sai gashi ya dawo, nan maryama ta shiga hidima dashi masu karatu karfa kuga laifin maryama kun san shi so hana ganin laifine indai kana son mutum to kullum son dadada masa kake,

Duk inda ta wulga binta da kallo shaddad yake saboda cikinta ya tsufa saura yan kwanaki ya rage ya shiga wata na tara,

Duk da yaga yanda take takawa dakyar amma sai yakasa hakuri saboda sun jima basa tare, maryama baiwar Allah haka da tsohon cikin da komai tabashi hadin kai bata k'i ba domin ita aduniya duk abinda shaddad yake so zata iya bashi mutukar baifi karfinta ba,kwana biyu ya dauka kullum yana gida yana yimata naci baya fita ko ina,masu karatu duk fa wannan abun da yake faruwa har yau shaddad bai taba nunawa maryama cewar ya kamu da sonta ba bare ya furta mata,kwanansa biyar da dawowa ya shirya ya tafi Kaduna amma aranar ya dawo.

Sati biyu da dawowar shaddad maryama tafara nakuda, karama clinic suka tafi nan dr muneerat tace operation za ayi mata saboda kamar haihuwar zata yimata wahala sosai, babu bata lokaci aka shiga da ita aka yi mata aiki aka ciro baby girl katuwa mai kamar maryama sak,

Sai da maryama ta farfado sannan aka gyara babyn wata nurse taje ta Kira shaddad da Dada wadanda ke waje suna jira.....

*_Ummi A'isha_*
[5/21, 8:48 PM] Ummi Shat🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


  _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  _*45*_


~~~Zubawa shaddad ido maryama tayi tana son taga da wanne irin yanayi zai karbi babyn lokacin da suka shiga cikin dakin, fuskarshi da fara'a taga ya karasa gadon da babyn take ya dauketa yana ta kallonta, ita kuwa ko wurinda take bai kalla ba balle ta saka ran zaiyi mata sannu,

Wannan abu yayi mutukar bawa maryama haushi ganin ya nuna halin ko in kula akanta sai ta babyn sa yake,

"A tsaga jikin nawa afito maka da yar amma banida darajar da zaka cemin koda sannu?" Tafada acikin zuciyarta,

Ta wuri daya taji dadi taji bacin ranta ya tafi shine lokacin da Dada ya shigo shima bai nufi wurin kowa ba sai wurinta yaje yana ta yimata sannu yana tambayar ko da akwai wurinda yake yi mata ciwo?

Dadi taji azuciyarta tace "dadinta dai nima nawa uban yadamu dani.." Tafadi acikin zuciyarta,

Sai da Dada yaji cewar lafiya lau take sannan ya matsa wurin shaddad ya karbi babyn ya sanya mata albarka ya fita, zuba ido maryama tayi tana ta kallon shaddad yana kai kawo da yarshi akan kafadarshi,

Waya yayi kaduna ya sanarwa da hajiya haihuwar sannan ya kikkira yan uwa ya fada musu, murna hajiya ta shiga yi sosai kamar wannan ne karo na farko data fara samun jika nan tace khairat ta shirya ta tafi tunda dama acikin hutun semester take,

Ita kuwa maryama wayarta tasa blessing ta dauko mata ta kira anty maijidda ta fada mata ajiyar zuciya anty maijidda tayi ta shiga hamdala domin tunda cikin maryama ya shiga watan haihuwa bata iya bacci saboda fargaba,

Kashe wayar tayi ta kira anty zainab itama ta fada mata,

Har bacci ya kwasheta bata san lokacin da shaddad ya ajiye babyn daga hannunshi ba,

Sai yamma lis ta farka lokacin har khairat tazo daga kaduna sunje gida itada blessing sun hado mata kayan tea sun dawo,

Tashi tayi ta zauna aka miko mata babyn ta karbeta zata shayar da ita, kurawa kirjinta ido shaddad yayi yana kallonta har lokacin kamar bata haihuba kirjinta yake sai dai cika da ya kara amma babu alamun zubewa atare dasu,

Haka aka yita faman kaiwa da komowa a asibitin har aka sallamesu suka koma gida, aranar su anty maijidda suka zo lokacin kwanan maryama uku da haihuwa, tunda suka koma gida kuma dangi da yan uwa suke ta zuwa ganin jaririya, kwanansu hudu su hajiya suka zo ita da anty karama da matar yaya Yusuf hadiza,

Dan murna hajiya ji take kamar zata hadiye jaririyar, kiran shaddad tayi tace wanne suna za asawa jaririyar? Nan yace sunanta zai saka,

"Ita kuma maryaman fa? Kamata yayi asa sunan mahaifiyarta tunda ni ai kaga yan uwanka sun sassaka sunana dayawa"

"Hajiya ai sunanku daya da babartata itama.."

Fara'a hajiya tayi ta gutsiri goro,

"Ashe kai maryaman naka suna da yawa, to Allah ya rayata"

Tashi yayi ya fita a kitchen ya hango su khairat suna aiki ita ya kira yace taje ta turo masa maryama saboda yaga dakin acike yake, dakinsa ya wuce ya  tsaya yana jiranta,

Tana sanye cikin doguwar riga na atamfa ta shigo dakin, sai da yaji wani kamshi ya gauraye dakin lokacin data shigo kamar ba maijego ba,

"Gani.." Tafada saboda dama har lokacin a kule take dashi na rashin sannun da baiyi mata ba lokacin data haihu,

Zama tayi agefen gadonshi bata ko kalleshi ba, tunda yaga haka yasan fushi take dashi,

"Munyi magana da hajiyane akan sunan da za asawa jaririyar, sunanta maryama"

"Allah ya rayata.." Shine kawai abinda tace ta tashi zata tafi,

"To babu wani abu da kuke bukata?"

"Babu" tafada tareda karasa ficewa, tun daga nan take shareshi taci gaba da hidimarta, har gida mai saloon tazo tayi mata ta gyara mata yalo yalon gashinta sannan aka yi mata jan lalle wannan kam khairat ce tayi mata saboda dama ta iya sosai,

Kyawun da maryama tayi kai idan ka ganta ba zakace itace ta haihu ba shiyasa duk inda tayi idon shaddad akanta yana lasar lebe, shaddad yayi kokari sosai wurin yi mata kayan kece raini ita da jaririyar,

Manyan raguna guda biyu ya siyo ma jaririyar, ranar suna aka yankasu aka radawa jaririya suna MARYAMA zasu rinka kiranta da Nu'aima,

Anyi hidima iya hidima awannan sunan, Dada mahaifin maryama gida guda ya mallakawa jaririyar, su hajiya da sauran dangi duk basu tafiba sai bayan suna da kwana biyu,

Yanzu gidan daga anty maijidda sai khairat ne kadai sai ko blessing da take zaune agidan tana tayasu ayyuka,

Tun maryama na share shaddad har ta dawo ta hakura ta rabu dashi amma bawai dan ta manta abinda yayi mata ba, ita kuwa anty maijidda maida hankali tayi wurin gyara maryama sosai,daga maryaman har nu'aima sunyi bulbul sunyi kiba sunyi kyau abinsu, ana igobe zasu cika kwana arba'in anty maijidda ta tattara ta tafi abuja gidanta tabar khairat awurin maryama saboda ta rinka tayata rainon nu'aima, ranar da suka cika 40 shaddad bai daga kafa ba dama tunda ya kyalla ido yaga khairat adakin maryama take kwana ya kira maryaman yace khairat ta koma daya dakin da kwana,

Yar gidan jiya suka koma koda yaushe baya barinta ta huta daga dare har asuba samun hutunta da ranane kadai, yanzun ma kuma sai da ya sake maimaita mata cewar indai tayi planing a boye Allah ya isanshi bai yafeba,

Haka suka cigaba da gudanar da rayuwarsu har sukayi wata biyu lokacin khairat ta koma Kaduna saboda school, sha tara ta arziki maryama ta hada mata sannan tabada sako mai girma tace akaiwa hajiya,

Khairat bata jima da tafiya ba shaddad ya shirya ya tafi Kaduna ashe zance yatafi wurin budurwarshi Amira saboda yanzu tayi candy, sai da yagama zancenshi sannan ya tafi gidan hajiya, tsabar zance yayi dadi wai har number din maryama ya bawa yarinya akan zata kirata su gaisa,

Duk lokaci zuwa lokaci yake zuwa Kaduna yanzu saboda Amira, ita maryama bata saniba, idan yana gida kullum yana makale da yarshi nu'aima hatta bacci tare suke yi, bikin blessing ne ya taso nan maryama ta hada mata sha tara ta arziki ta sallameta ta tafi garinsu, yanzu gidan yadawo sai su uku kacal, kullum da nu'aima maryama take zuwa aiki idan taje da ita kuwa bata sake ganinta sai idan tatashi zata dawo gida sannan ne zataje ta nemota su koma gida,

Tana tsaka da aiki acikin kitchen taji an kirata awaya, bakuwar number tagani ana kiranta awaya,

Dagawa tayi tun kafin tayi magana taji ance,

"Sannu amarya yar shekara 30 yanzu ke ko kunya bakiji ba kika dage kika auri yaro sa'anki, bayan kin san yadade yana sona tun ina jss 3 yake sona kuma har yanzu bai daina sona ba..."

Kashe wayar maryama tayi saboda ita bata iya fada ba, duk da ta kashe wayar Amira bata hakura ba sai da ta sake turo mata da text massage,

Haushi iya haushi maryama tajishi amma bata ko nunawa shaddad ba duk da tasan shine zai fadawa budurwar tasa cewar shekarunta 30 lokacin da ya aureta,

Cikin satin suka shirya suka tafi Kaduna gaida hajiya, ina ka saka ina ka ajiye haka hajiya tayiwa su maryama, shi kuma shaddad ya tafi wurin Amira saboda yana son ya turo ayi maganar aurensu da ita....



*_Ummi A'isha_*
[5/21, 8:48 PM] Ummi Shatu🏻: *_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

  _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

  *_46_*


~~~Amma koda yaje yayiwa Amira maganar sai tace masa ita makaranta zatayi ba yanzu zata yi aure ba,

"Amira kin san dai na dade ina sonki kuma hajiya ta matsa akan ayi ayi maza ai auren nan.."

Budar bakin Amira sai cewa tayi, "kuma ni ina ruwana da wata hajiya, ai ba itace zata yimaka auren ba da zata bi ta uzzura maka.."

Tunda tafadi haka yaji ransa yabaci sannan yaji yarinyar tafara fice masa arai saboda sam bata da kunya gata dai yarinya karama dan ko khairat da take kanwarsa ta biyu ta girme mata nesa ba kusa ba amma sai ta rinka fada masa bakar magana, duk da yasan harda yarinta acikin tsarin nata amma harda rashin kunya da rashin ganin girman nagaba, ta inda yake sarawa maryama kenan sam bata son bacin ranshi gashi tana mutukar kaunar mahaifiyarshi da yan uwanshi sannan duk abinda ya fada mata bata iya yimasa musu kuma duk tsanani baya magana ta mayar masa ko lokacin da yake yimata wulakancin nan farkon aurensu shiru take yi bata ramawa gashi dai ahaife ba girmanta yayiba amma tana bashi girma da daraja a matsayinshi na mijinta,

Cikeda bacin rai yabar wurin Amira ya koma gidan hajiya, kwanansu biyu suka koma Lagos bayan hajiya ta samowa maryama wata yar dattijuwa mai suna baba lami wacce zata zauna da maryama ta rinka tayata yan aikace aikacen gida saboda yanzu bata da mai aiki ita kuma hajiya ko kadan bata son taga maryama na shan wahala,

Komawa Kaduna suka yi suka cigaba da gudanar da rayuwarsu, nu'aima babu laifi ta girma tayi wayo sosai, shi kuwa shaddad dole yanzu ya hakura da maganar Amira musamman ma da yaga text massage din data turowa maryama awayar maryaman nan yasake jinjinawa maryama wurin hakuri da dauriya domin ba duk macece zata iya wannan ba da wata matarce Allah ne kadai yasan tashin hankalin da zasuyi da ita amma ita maryama ko nuna masa bata yiba, sannan baya ga haka ma tunda tafara jami'a ta hadu da wani guy ya ke hure mata kunne, yanzu kwata kwata ta juyawa shaddad baya, ganin haka yasa shaddad hakura ya kyaleta saboda dama hajiyarsu da sauran yan uwanshi ba son aurensa da Amira suke ba.

Watan nu'aima tara maryama ta fara laulayin wani cikin danma nu'aiman mai saurin girma ce sannan tunda maryama likitan yarace tana taimaka mata da wasu sinadirai masu gina jikin yara shiyasa ta taso cikin koshin lafiya dama kuma ba damuwa tayi da shan mama ba shiyasa maryama ta yayeta,

"Zo Mamana, ummice ta yaye ki ko ta hanaki shan abincinki, yi hakuri zamuje in siyo miki bobo.."

Tana ganin shaddad ya dauketa suka fita yawo, haka tayita laulayinta wannan karonma kamar lokacin da tayi na nu'aima, amma yanzu tunda bana farko bane ta ji dan dama dama, shiyasa ma ko hutu bata dauka ba a office har saida azumi yazo lokacin cikinta yana wata bakwai shine ta dauki hutu saboda tana son su tafi umarah itada nu'aima,

Shaddad bai hanata ba tunda da kudinta ta biya, nan aka gama musu dukkan shirye shiryen da ya kamata suka tafi,

Kullum suna waya da shaddad, satinsu uku acan suka dawo, nan shaddad ya karbesu da farin ciki domin yayi missing din matarshi sosai,

Gidan Dada maryama takai nu'aima saboda kullum sai ta rinka cemata zataje wurin dada tunda ta kaita bata daukota ba sai da zasu tafi Kaduna salla,

Kamar koda yaushe wannan zuwanma taji dadin yanda su hajiya suka karbeta kowa kamar zai hadiyeta dan so, sai da akayi salla da sati daya sannan suka koma Lagos,

Kwanci tashi da haka har watan haihuwar maryama ya cika, ranar da edd dinta ya cika aranar ta tashi da nakuda,shaddad ne ya dawo daga office ya kaita asibitin, wannan karon ma cs din za ayi mata, yana ganin lokacin da aka zo za awuce da ita nu'aima taje gaban gadon tana kuka,

"Ummi zaki dawo ko? Dan Allah Ummi karki tafi"

Jin abinda nu'aima take fada ne ya karyarwa da maryama zuciya har taji kwalla tana kokarin sauko mata batare da ta shirya ba,

Shi kansa shaddad sai yaji jikinsa yayi sanyi sosai, zuwa yayi ya kamo hannun nu'aima batare da ya iya kallon wurinda maryama take ba,

Yana nan atsaye har nu'aima tayi bacci akan kafadarsa, gida ya koma ya mayar da ita wurin baba lami ya sake dawowa asibitin,

Shida dadane a reception suna jira, can nurse tazo tace anciro jaririn suzo su ganshi, duk murnar da shaddad yake yi na zai samu karuwa amma sai yaji wannan lokacin ya nemi farin cikin ya rasa,

Wurin jaririn sukaje suka ganshi tubarakalla kato dashi mai kama da shaddad fitik, nan aka shirya yaron aka ajiyeshi acikin gadonshi,

Maryama kam awa da awanni bata farfado ba dan haka hankalin doctors din ya tashi sosai nan suka rufu akanta domin ceto numfashinta sai dai amma ina basu da wannan ikon daga karshe dai dole suka hakura domin tuni rai yayi halinsa maryama ta rigamu gidan gaskiya,

Dr muneerat ce ta fito jikinta yana rawa taje wajen su Dada amma sai ta kasa fada musu rasuwar maryama,

"Dr ta farfado ne?" Dada ya tambaya, girgiza kai dr muneera tayi,

"Yallabai sai dai muyi hakuri mu karbi kaddarar da Allah ya aiko mana.."

Hawaye suna bin kuncinta ta mikawa shaddad wata farar takarda,

"Gashi itace ta rubuta kafin ayi mata aikin.."

Karba yayi hannunsa yana rawa ji yake kamar mafarki yake yi, cikin rawar jiki ya warware takardar yafara karantawa,

"Mijina dan Allah idan nayi maka laifi ka yafe min, Allah ya hadamu a aljanna sannan dan Allah ka taimaka ko gawata ne ka fada mata Kalmar so duk da nasan ba ka sona, amma ka sani ni ina tsananin sonka son da ban san adadinsa ba, Allah ya raya mana yaranmu..."

Ai shaddad yana gama karantawa yaji kamar zai zube awurin saboda hajijiyar data fara daukarshi idanuwanshi suka rufe baya ganin komai sai duhu....

  _Gaisuwa ga masoyana masu sona, ina mai baku hakuri sakamakon bana baku amsa da wuri idan kun yimin magana wallahi abinne yafi karfina shiyasa, sakonninku da yawa bazai yiyu in amsa a lokaci guda ba,nagode da kaunarku gareni, ummi shatu luvs u too.._




_*Ummi A'isha*_

No comments:

Post a Comment