Thursday 1 June 2017

MARYAMA SARAUNIYA.. 26,27.28

[5/16, 8:01 AM] Ummi Shatu🏻: _®HASKE WRITERS ASSOCIATION (HWA)_

*_MARYAMA SARAUNIYA..!!_*



   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


    _*Gaisuwa mai dumbin yawa ga duk members na haske writers association, ina alfahari daku Allah yaci gaba da hada kanmu,wannan shafin nakune domin jin dadinku.*_

 
    *_26_*

   ~~~Jiki asanyaye maryama ta dauke idonta daga kan hoton tafita zuciyarta sai ambulo mata tarin tambayoyi take wanda bata da amsarsu, gashi lokaci guda kirjinta ya hau harbawa da sauri da sauri banda bugun da zuciyarta take dum dum saboda duk atunaninta nan gidan shaddad ne,

"To kodai shaddad yayi aure ne? Innalillahi amma da na shiga uku.."

Komawa falon baki suka yi suka zauna amma ita maryama duk ji take zaman ya gundureta babu abinda take kauna irin taganta agida,

"Khairat bari muje mu tafi ga wannan babu yawa.."

Mikewa tayi takama hannun A'isha idanuwanta har sunyi jajur,

"Kai adda Maryam daga zuwa sai tafiya?"

"Ehh khairat bana jin dadin jikina ne shiyasa"

"Ayya to Allah yabaki lafiya ashe gobe ma ba lallai kizo makaranta ba"

"Ehh sai yanda ta yiyu dai"

Daukar ledar kayan khairat tayi tanufi falon antynta tana kwalla mata kira,

"Anty zo ki tayani godiya kinga kayan da adda maryam ta kawo min.."

Fitowa matar tayi fuskarta dauke da murmushi,lokacin itama maryama har sun fito zasu tafi,

"Ahh duk wannan, maryama harda wahala haka? To angode madalla Allah yabar zumunci"

Ita dai maryama yaken dole kawai take tana amsawa daga nan suka fice daga gidan,

Har kofar gida antyn khairat tabisu tana yiwa maryama godiya,

"Adda Maryam angode madalla"

"Babu komai khairat"

Shine kawai abinda maryama tace ta tashi motar da suka zo da ita ta dauki titin da zai mayar dasu gida,

Ko kadan bata jin surutun da Aisha take yimata tana bata labari saboda gaba daya hankalinta ba ajikinta yake ba,

Koda sukaje gidama dakin da yake a mazaunin nata ta nufa taje tafada akan gado tana jin kamar kanta zai rabe gida biyu,

Ita anty maijidda ma bata san sun dawo ba saboda tana can baya wurinda samarin 'yayanta suke buga ball suda yaran makota tana kallo, har saida ta shigo ciki taga Aisha a falo tana kallo sannan tasan sun dawo,

"Yaushe kuka dawo ku kuma?"

"Yanzu muka dawo"

"To ina addar taku?"

"Tana daki"..

Dakinta kawai anty maijidda ta nufa saboda tayi tunanin ko kawai maryama ta shiga dakine domin ta huta shiyasa bata bi ta kanta ba.

Ita kuwa maryama tana can tana fama da ciwon zuciya gashi kirjinta sai wani irin zafi yake yimata, kanta kuwa kamar zai fita yabar gangar jikinta,

Dafe kan tayi tana numfashi da kyar kafin wani lokaci har numfashinta ya tsaya cak ya daina fita,

"Momy ara min wayarki zan kira dady nace masa ya taho min da laptop tunda waccan ta daina yi.." Faruk second born din anty maijidda ne yayi wannan maganar,

"Ni wayata bata nan Sadiq ya fita da ita sai dai ka aro ta addarku"

Dakin maryama faruk din ya nufa yana cewa, "ai momy kece kika hana dady ya bamu waya da yanzu kowa da tashi mun huta aro"

"Ba wanda za abawa waya sai yayi candy, jimin yaro da iyayi"


Shiga dakin faruk yayi  ya karasa wurin da maryama ke kife akan gado,

"Adda Maryam bani aron wayarki nakira dadynmu"

Jin shiru bata amsaba yasashi zuwa kusa da ita yafara bubbuga gefen da take kwance amma nan dinma shiru bata motsa ba, har ya juya zai fita yaji tayi wata irin jan zuciya mai mutukar karfi sai kuma yaji k'attt,kamar fitar rai, wata kara ya kwalla, take su anty maijidda suka taho aguje domin hatta ita dake zaune a falo sai da suka jiyo wannan k'att din,

Juyowa da ita anty maijidda tayi arude anan taga idanuwanta akakkafe ga shatin hawaye nan akan kuncinta amma kallo daya zaka yi mata ka fahimci cewar bata numfashi,

"Maryama.." Anty maijidda takira sunanta da karfi tana jijjigata,

"Nashiga uku, faruk kaga bata numfashi, ke A'isha meya sameta ahanyarku ta dawowa?"

"Momy kibar wannan maganar muje mu kaita asibiti" faruk yace yana kokarin ciccibar maryama, wani aiki sai maza, kasancewar namijine nan ya cirata ya dauketa, binsa da kallo anty maijidda tayi saboda kwata kwata shekarunsa basu fi sha biyar ba,

Ko mayafi babu ajikin ta tabisu tana salati sai A'isha ce ta bita da mayafin,

Wani clinic dake cikin unguwar suka kaita mai suna, Daula clinic, suna zuwa aka shiga da ita aka kaita emergency,

"Ikon Allah yanzu dama wannan shiga dakin da maryama tayi ba lafiya ba?" Anty maijidda tafada a diririce, duk tabi ta fita hayyacinta.

Bayan awowi uku ne suka samu shiga dakin da take, har ta dan wartsake amma da gani kasan tana cikin damuwa,

"Sannu maryama, wai meya sameki ne?"

Murmushin karfin hali tayi, "babu komai anty"

"A,a ai kuwa kowa yaganki yasan kinada damuwa"

Korar su faruk anty maijidda tayi yarage daga ita sai maryama ta titsiyeta, nan maryama ta sanar da ita,

"Kashh amma maryama kema dai kinyi rashin hakuri, shiyasa nace miki zaki samu shaddad amma sai kinyi hakuri sai kin jure, sannan ta yiyu shima shaddad baiyi aurenba kila nan gidan yan uwansa ne, ai a hikimance zaki ji duk wani bayani a bakin khairat tunda tanada surutu babu abinda bazata fada miki ba, kedai kawai kiyi hakuri kuma kiyi addu'a.."

Ko babu komai kalaman anty maijidda sun sanyaya mata ranta da zuciyarta domin kullum karfafa mata gwiwar cewar zata samu shaddad take, kuma itama ta daura aniyar yin duk wani yaki domin mallakarsa..



*_Ummi Shatu_*
[5/16, 8:01 AM] Ummi Shatu🏻: _®HWA_

_*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_


   *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


     _Dedicated to Maryam Qaumi_💕

 

    _Fatan alkairi agareku Hawwa (Hawy) & uwa tagari Halamcy.._


    _*27*_

  ~~~Gyara kwanciyarta tayi idanuwanta suna fitar da kwalla,

"Shikenan anty zan jarraba yadda kika ce"

"Yawwa maryama ko kefa amma da har zaki karaya tunda wuri, ai ba akaraya akan abinda ake so, yanzu ki kwantar da hankalinki kibi khairat ahankali har ta fayyace miki komai"

Haka anty maijidda taci gaba da lallabata tana bata shawarwari har na wani lokaci,basu suka bar wannan clinic dinba sai dare anty maijidda tana cike da tausayinta saboda ganin soyayya tana ta faman wahalar da ita.

Tunda suka dawo gida anty maijidda ta hada mata tea tasha tayi wanka ta kwanta dan haka da safe ras ta tashi sai ciwon kan dake damunta ganin haka yasa ranar bata samu zuwa islamiyya ba har sai washe gari,

Aranar ma kawai dai daurewa take yi amma bawai dan ta warke sumul ba,

Suna zaune a aji bayan angama yimusu dori ta kalli khairat wacce ta maida hankalinta kan alqur'anin dake gabanta tana ta faman maimaita wurinda ya sayyadi ya dora mata,

"Khairat nikuwa na tambayeki mana.."

"Allah yasa nasani adda Maryam" khairat tace bayan ta rufe alkur'anin dake ajiye agabanta,

"Am ranar da naje gidan nan naku naga hoton wani guy soja wanda kamar na sanshi.."

"Yaya Navy kika gani ko Yaya army?"

"Wani fari dai mai tabon salla agoshinsa ina jin indai ban manta ba sunanshi shaddad.."

"Ohh Yaya Navy, ai brother nane, a ina kika sanshi"

Murmushi maryama tayi,

"A Lagos"

"Kwarai ya taba zama a Lagos"

"To yanzu yana ina?"

"Yanzu yana Benue state"

"Yayi aure?"

"A,a amma dai yakusa wata yarinya yake so to kuma bata gama karatu ba"

Ajiyar zuciya maryama ta sauke saboda jin baiyi aureba,

"Wacce makarantar take yi?'

"Yarinyace fa yar secondary school sai yanzu ma ta shiga SS 1 fa, batafi 15 years ba"

Maganar ba karamin sukan zuciyar maryama tayiba amma haka ta daure,

"Ko zaki bani number dinshi zan kirashi amma kar kice masa kin bani, ko maganata ma kar kiyi masa"

"To adda maryam gashi"

Number dinshi khairat tabata tasaka acikin wayarta, tana dubashi a whatsapp taganshi sai dai da alamun yajima bai hau online ba fiyeda watanni hudu, amma ga hotonshi nan abakin wani rafi yana sanye cikin uniform dinshi na navy,

"Wannan antyn nawa da kika gani ita yake bi nikuma akwai wasu mutum biyu atsakaninmu amma dayan ya rasu"

"Allah sarki Allah ya jikanshi"

Haka suka yita hira har lokacin tashi yayi,

Cikeda murna maryama ta koma gida tasamu anty maijidda tabata labarin yanda sukayi da khairat,

"To yanzu dai kece zaki yimasa dabara irinta mata har hankalinsa yadawo kanki"

Cikin jin kunya da murna maryama ta tashi ta shige daki, number tashi ta kira cikin sa'a kuwa sai ta shiga, ta dan jima tana ringing kafin ya dauka,

Sallama yayi, "assalamu alaikum"

"Wa'alaikumussalam" ta amsa masa, duk da bai santa ba amma sai da ya lumshe idonshi saboda zakin muryarta,

"Shaddad ne?"

"Ehhh shine wake magana?"

"Wata baiwar Allah ce"

Shiru yayi yana sauraron daddadar muryarta, jin tayi shiru yasashi yin magana,

"Daga ina?"

"Daga wani gari"

Murmushi yayi wanda har saida tajishi acikin kunnenta,

"To ya akayi kika samu number ta?"

"Saboda nadamu dakai, kanada muhimmanci acikin rayuwata"

"To indai hakane maiyasa bazaki bayyana min kanki ba, meyasa zaki boye min ko ke wacece?"

"Zaka san ni wacece amma sai lokacin hakan yayi"

"To shikenan babu damuwa nagode"

Katse wayar tayi tana hamdala ga Allah saboda jin shaddad bai gwaleta ba, tasan insha Allah hakanta zata cimma ruwa.

Wurin anty maijidda takoma tafada mata yanda sukayi dashi,

"Ashema bashida wahalar kamawa indai kin dage nan da lokaci kankani zaki sameshi a hannunki wallahi"

Tun daga ranar maryama kullum saita kirashi awaya idan ya daga suka gaisa sai tace lafiyarshi ta kira taji banda text massages da take tura masa, nasafe daban, narana daban, na yamma daban, na dare daban,da yake yau da gobe sai Allah ko sati biyu ba ayiba yafara mayar mata da reply din massages din da take tura masa sannan shi dinma wani lokacin yana kiranta, shi dai bai san wacece ba amma muryarta tana bala'in yimasa dadi, da ya tambayeta sunanta sai tace sunanta Nana,

Kullum suna waya da ita tun bai damu da itaba har yazo yafara damuwa da ita idan bata kirashiba sai yaji duk yadamu,

Ahankali suka fara soyayya awaya, shidai bai san waceceba kuma yaji zuciyarsa ta aminta da ita,

Tana kwance tana baccin rana ya kirata, cikin yanayin bacci ta daga wayar,

"Hello Navy.."

"Nana ko bacci kikeyi natasheki?"

"Me kaji?"

"Naji muryarki ta canja ne"

Murmushi tayi, "bacci na danyi wallahi, nadawo daga islamiyya ne agajiye shine ina yin salla sai na kwanta"

"Ayya sannu, yau me aka koyo a makarantar?"

Murmushi tayi, "abubuwa da yawa ciki harda muhimmancin karbar kaddara kyakkyawa da mummuna"

"Wannan haka yake malama nana, har yau dai kinki turo min hotunanki naganki ko?"

"A'a ni baki nayiba"

"To me kikayi?"

"Nidai nafi son kazo kaganni face to face saboda kar kaganni a hoto kaga banyi maka ba"

"Babu wannan maganar, ai tundaga voice dinki naji kin yi min, kuma ko ya naganki zanci gaba da kulaki ahaka"

"Nidai fa sai kazo gaskiya.." Tafada cikin shagwaba,

"To shikenan tunda kince haka, zan samu lokaci na musamman nazo naganki, tunda kinyi min wayo kin hanani ganinki"

"Ba wayo bane ni nafi son kazo ne"

"Shikenan ai tunda nace zanzo amma sai nanda 2 months saboda yanzu aiki ya rikemu"

"Babu damuwa ina jiranka koma yaushe ne",

Haka suka cigaba da kasancewa a waya kullum sai dai kuma ita maryama kullum cikin fargaba take saboda bata san ya zata kasanceba idan har shaddad yazo yaganta amma anty maijidda tana kokarin kwantar mata da hankali da cewa ai yanzu idan yaganta bazai k'ita ba tunda ta nutsu ta zama irin macen da yake so, duk lokacin da anty maijidda tafadi haka sai taji hankalinta ya dan kwanta.

  Akwana atashi har sai da maryama da shaddad suka dauki kimanin watanni biyar suna soyewa awaya, kullum wuni suke suna hira, yauma kamar kullum bayan sallar isha tana kwance ya kirata,

"Kin fara bacci ne baby?"

"Idona biyu navy,me kakeyi yanzu?"

"Abinci nake ci, bude bakinki kema in sammiki"

Murmushi tayi, "to na bude.."

"To gashi nan tauna"

"Uhmmm wannan abinci amma badai dadiba.."

"Girkin hajiyata ne ai, albishirinki?"

"Goro" tafada tana daga kwance idonta a lumshe,

"Nazo Kaduna yau, gobe insha Allah zanzo abuja naganki..."

Zumbur ta mike daga kwancen da take jikinta yana rawa, sam bata son yazo idan yaga itace ya juya mata baya daga daddadar soyayyar da suke gudanarwa....


*_Ummi Shatu_*🏻
[5/16, 8:01 AM] Ummi Shatu🏻: _*MARYAMA SARAUNIYA..!!*_


   *_NA_*

*_UMMI AI'SHA_*


    _Dedicated to Maryam Qaumi_💕


    _*28*_

  ~~~Duk kokarinta na kar shaddad yagane rudun da ta shiga saida ya fahimta,

"Baby... Lafiya kuwa?"

"Lafiya lau mana, me kaji?"

"Ai najine kamar bakiyi murna da maganar zuwan nawa ba"

Murmushi ta kakaro tayi,

"Haba dai Navy kai kaji dadin danaji, tsabar dadi fa ji nayi kamar amafarki kake fada min shiyasa ma na burkice"

"Masha Allah, gobe iyanzu nasan nadade da ganinki,idanuwana sun jima da yin tozali da kyakkyawar fuskarki mai tsada.."

Shiru ita dai tayi tana jimamin wannan rana wacce Allah ne kadai yasan ayanda zata tsinci kanta,

"Yana ji kinyi shirune baby, Kodai baki shirya ganina yanzu ba nahakura?"

"Hmm ba haka bane Navy kawai dai ina tsoron abinda zaije yazo ne"

"Kamar me kenan?"

"Ina tsoron kar kaganni ka juya min baya, kamanta duk wadannan maganganun masu dadi da sanyaya rai da kake fada min, karka ganni ka tafi ka manta dani wannan shine abinda yake sakani cikin zulumi akoda yaushe, saboda idan har hakan takasance Allah ne kadai yasan makomata..."

"Ni bana son ki rinka furta irin wadannan maganganun, nariga da nafada miki babu wannan a tsakaninmu, bazan taba gudunki ba, idan ma tunani kike cewar idan naganki zanga bakiyi min ba to kidaina domin ni duk a irin kamar da naganki zanci gaba da sonki ahaka"

Kwallar idonta ta goge, "Allah yasa hakan takasance"

"Insha Allah hakance zata kasance baby, kidaina doubting akaina"

Sosai taji dadin kalamansa nan ta danji hankalinta ya kwanta,

Suna gama waya dashi ta tafi dakin anty maijidda wacce ke zaune tana goge kayan dadyn su A'isha,

Abakin gado ta zauna ta rafka tagumi ta juya tana kallon anty maijidda,

"Lafiya kuwa?"

"Anty Navy ne wai zai zo gobe, ina jin tsoro anty, kar yazo yaganni yagudu yabarni saboda ya tsaneni bai san cewar dani yake waya ba"

"Haba maryama ai maganar baya tawuce  maganar yanzu akeyi,sanin da yayi miki ada daban yake da wanda zaiyi miki ayanzu"

"Wallahi anty hankalina atashe yake"

"Ki kwantar da hankalinki insha Allah babu abinda zai faru"

Maganganu masu dadi anty maijidda tai ta fada mata har ta danji dama dama sannan takoma dakinta ta kwanta, yanda taga rana haka taga dare kwata kwata takasa bacci, sai sake sake da zuciyarta keyi akan haduwar da zasuyi da shaddad gobe bayan shekaru biyu da suka wuce rabonsu da ganin juna.

  Tunda asuba anty maijidda ta tasheta suna idar da salla suka shiga kitchen domin shirya abinda za a tarbi shaddad dashi,

Abinci kala kala aka yimasa da drinks masu dadi, ga hadin salad da pepe chicken agefe,

Karfe goma sha daya tuni sun kammala komai an shirya a falon baki,

Maryama na shirin shiga wanka kenan taji kiran shaddad ya shigo sai da gabanta yayi mummunar faduwa yau sunyi waya yafi sau goma dashi tun daga wayewar gari zuwa yanzu,

"Hello.."

"Nakaraso kofar gidan"

"Ok maigadi zai zo ya shigo dakai idan kayi hon, ni ban shirya bane yanzu zan shiga wanka"

"To ranki yadade afito lafiya.."

Kashe wayar tayi ta saki ajiyar zuciya, "yau dai za ayita takare ni maryama", tafada acikin zuciyarta,

Jikinta asanyaye ta tashi ta leka falo, "anty ya karaso"

"Ato sannunsa da zuwa, meye haka duk jikinki asanyaye, dan Allah ki saki jikinki kiyi kiyi ki shirya kifita"

Ciki ta koma ta shiga wanka har lokacin jikinta asanyaye yake, wanka tayi tafito ta zauna ta shirya, kwalliya tayi sosai da sosai tasha jan janbaki tazana jagira dama kun san maryama badai iya kwalliya ba,

Jar wata doguwar riga hadaddiya tasaka ta yane kanta da madaidaicin mayafi kashka shima kalarsa ja,babu karya tayi kyau iya kyau kuma ta fito a maryamanta,

"Wowww my daughter kin dauku fa, kinyi kyau ba karya.., Allah yabada nasara sai kin dawo"

Anty maijidda tace da ita cikeda karfafa mata gwiwa, fita maryama tayi gabanta yana faman faduwa ta nufi falon baki inda shaddad ke zaune yasha wani hadadden bakin yadi lallausa wanda yayi mutukar yimasa kyau,

Agogon azurfa ya daura yasa bakar hula,

Hango fuskarshi maryama tayi lokacin data je kofar falon, cikin sanyayyiyar muryarta tayi masa sallama ta shiga, cikin fara'a da shaukin kauna ya amsa mata hannunshi rikeda cup yana kurbar juice,

"Barka da fitowa sarauni...."

Zumbur ya mike ya ajiye cup din hannunshi saboda ganin fuskarta,

"Meya kawoki nan?" Yafada cikin tsawa wanda har sai da bangon falon ya amsa,

"Please shaddad kar muyi haka dakai, karka manta cewar kayi min alkawarin cewar bazaka gujeni ba aduk yanayin daka ganni.."

"Wai dama kina nufin kece Nana..?" Yafada yana nunata da yatsa,

"Tabbas nice shaddad..."

"To bani hanya inwuce, wallahi da ace cewar nasan kece da babu abinda zai kawoni nan.."

"Navy karka manta da alkawarin..."

"Wanne alkawari? Alkawarin da nayishi cikin rashin sani?, me zanyi dake, ko matan duniya sun kare kina zaton zan aureki? In aureki ince na auri wa? Ko kin manta da cewar nafi kowa sanin wacece ke, nafi kowa sanin halinki,ke mazinaciyace, marar kamun kai, jahila marar ilmin addini, marar tarbiya, mai kula maza, mai zuwa club, mai shan kayan maye, marar girmama mutane, idan kin manta to natuna miki, daga karshe ina son kiyi nesa dani saboda natsaneki tsanar da bata da adadi..."

Idanuwanta ne suka kada sukayi ja kamar yadda nasa idanuwan suma suka rine sukayi ja,

"Shaddad idan har kayi min haka baka yimin adalciba, idan har ban kasance dakaiba wallahi ina iya..."

"Wallahi indai sai kin kasance danine zaki rayu to sai dai ki mutu saboda bazan taba auren mace irinki ba.."

Yana kaiwa nan ya ketareta ya wuce zuciyarsa tana faman tafarfasa, ransa abace yafita ya shiga motarsa ya figeta,

Durkushewa maryama tayi awurin tana wani irin kuka mai cin rai, kokartawa tayi ta tashi ta nufi cikin gida, tana shiga falo taje tafada jikin anty maijidda tana wani irin numfarfashi,

"Anty...anty wallahi yabarni, yatafi..,anty yatafi,yace bazai aure ni ba,.... Anty mutuwa zanyi.."

Tana kaiwa nan ta sankame numfashinta ya tsaya cak, zuciyarta ta daina bugawa numfashinta ya daina fita, idanuwanta suka kakkafe....


  _Gaisuwa mai yawa ga yan uwa najini, Hajja (mom ihsan) & Halimatus Sadiya (stylish)_


*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment