Friday 14 April 2017

RAMUWAR GAYYA.. 48

*_RAMUWAR GAYYA..._*💘

  _Love story 50,50_

  *_UMMI A'ISHA_*

          _with_

  *_PHERTYMERH XARAH_*

  48

Driving sawwam yake da hannu daya yayinda daya hannun kuma yake rike da hannun abar kaunarsa ummulkhairi,

"My lonely nasan jiya bakiyi bacci ba kamar nima yanda banyi ba ko?" Yace da ita yana murza yan yatsunta,

Idanuwanta ta lumshe ta sake kwantar da kanta ajikin kujerar da take zaune,

"Wallahi banyi bacci ba sawwam, ai nariga da nayi sabon da bazan iya bacciba sai tare dakai.."

Murmushi yayi ya dan kalleta kafin ya mayar da idanuwansa kan titi,

"To kuma my lonely ranar da kuka zama ku biyu yaya zakiyi?" Yace da ita cikin zolaya harda fakar idonta yayi mata gwalo kasancewar idonta arufe yake shiyasa bata ganshi ba,

"Mu biyu kuma? Ai ko yanzu ma mu biyune" tafada idonta har lokacin arufe yake,

"Ah wai ina nufin idan na kawo miki kanwa"

Murmushi tayi tafara zare hannunta daga cikin nashi,

"Nabar mata kai tun kafin tazo"

Dariya yayi ya juya ya kalleta,

"Tun da wuri haka har kin bada ni kyauta"

Shiru tayi masa fuskarta kunshe da murmushi,

"Ehhh" tabashi amsa,

"Kinga kiyi hakuri nifa da wasa nake, idan na karo miki wata kuma ina zan saka kaina"

Murmushi tasaki ta kalleshi, "wai har ka tsorata?"

"Ba dole ba, nasan idan kika yi fushi akwai ta inda zaki rama"

Murmushi tayi ta sake makale yatsunshi cikin nata,

"Kaine kake tunanin haka amma ni ban kawo wannan araina ba"

"Wallahi karya kike mugunta kike son yimin kisani hauka...."

Dariya tafara harda rike ciki, "amma dai kasan Mami tace kadaina matsa min ko? Ko kana son murasa babyn?"

"Kai kar kiyi min mummunan fata, kin san kuwa yanda nake ji da wannan babyn? Duk duniya nafi sonshi fiyeda komai... "

Da sauri ta kalleshi cikeda mamaki,

"Harda su mami da dad dani ko?" Tafada fuskarta ahade,

"Ohhh baby kin cika rigima, bafa haka nake nufiba, ai ke special one ce nafi son ki fiyeda babyn, su mami kuma ai matsayinsu daban ne.."

Sakin fuska tayi tana murmushi, "kai dai kawai kayi min wayo"

"Babu wani wayo my lonely"

Tsayawa sukayi sakamakon tsayar dasu da danja tayi, kiss yakai mata akumatu ya mika hannu zuwa kan cikinta,

"Wai sai yaushe cikin nan zai fitone, nifa na kosa naga yadan turo"

"Saboda ba ajikinka yake ba ko? Kai babu mai kallonka balle yace..."

Dariya yayi yaci gaba da driving har lokacin dariya yake,

"Balle ace me? Kowa yasan kece kikazo dakina ni banine nazo ba, waya saki kizo?"

Itama dariyar tayi ta kalleshi, "au haka kace?"

Kada kai yayi yana dariya,

"Ko ba haka bane?"

"Amma ai kaine kayi min wayo ka lallabani har nabika ko"

Hularshi ya cire ya fara shafa sumar kansa, fuskarshi dauke da murmushi,

"My lonely kenan, kemafa yarinya ce in banda haka dama tunda kika bini ai kin san dole sai nabaki ajiya..."

"Ni ka rabu dani bacci zanyi.."

"To nayi shiru yi baccinki"

Bata kara magana ba ta lumshe idanuwanta, ga mamakinsa mintina kadan sai yaji tayi bacci murmushi yayi yaci gaba da driving yana kallonta yasan cikin datake dauke dashi ne yake sata baccin,

Har suka shiga cikin garin kano bata tashiba bacci take yi sosai hannunta rikeda nashi,

Yana shiga cikin gidansu yayi packing ya fita, kofar barin da take yaje ya bude ya daukota kamar wata jaririya, a falo ya kwantar da ita akan doguwar kujera,

Kitchen ya leka kozai iya hada musu wani abu kafin ta tashi amma yakasa saboda shi bai iya dafa komai ba,

Cornflakes ya hada ya zauna agefenta yana sha, har yagama tana bacci, kayan jikinshi yaje ya rage yafito da iya gajeren wando,

"Sahibina..." Ummulkhair ta fada tana mika bayan ta bude idonta,

"My lonely kin tashi?"

"Yunwa nakeji sawwam..."

"Bari nazubo miki cornflakes nima shi nasha yanzu"

Batare da bata lokaci ba yaje ya hado mata cikin cup ya kawo mata, agefenta yazauna yafara bata tana sha har ta shanye tas,

Matsawa ya sakeyi jikinta sosai ya kama hannunta ya rike,

"Zo ki rakani bedroom dina kiga wani abu"

Murmushi tayi ta tsaida idonta bisa fuskarshi tana kallonsa,

"Kai da kace nice nake binka dakinka, ai bazan kara zuwa ba"

Kwantar da murya yayi yana kallonta cikin kalar tausayi,

"Da wasa fa nake yi miki ai kowa yasan nine na gayyaceki dakin nawa ba haka kawai kika zoba"

Far tayi da idonta ta dauke kanta, ganin haka yasashi tashi ya dauketa ya nufi hangar dakinshi.....

  Ramuwar baccin da basu samu sunyi ba adaren jiya shi sukayi, itace ta fara tashi, wanka tayi ta shirya ta shiga kitchen ta dora girki, tana cikin kitchen din tana aiki ya shigo,

"My lonely sannu da kokari"

"Yawwa sannu, katashi?"

Rungumeta yayi tabaya yana murmushi, "natashi saboda naji bakya kusa dani"

Tare suka karasa girkin, da daddare yace ta shirya suje gidan mami su gaishesu, ita dai duk kunya take ji saboda tahowar da sukayi itada sawwam suka baro su dad acan,

A kunyace tabishi suka shiga falon dad inda suke zaune itada dad suna kallon labarai a tashar aljazeera, akasa ta zauna tana gaida su mami,

"Dan gidan dady kuma haka akeyi sai ka dauko iyalinka ku taho ku barmu acan?" Dad yafada yana dariya,

"Dad batada lafiyane shiyasa muka taho" sawwam yace da dad yana satar kallon ummulkhair wacce ta sunkuyar da kanta kasa,

"To Allah yabata lafiya yarabata da abinda take dauke dashi lafiya"

Babu kunya taji sawwam ya amsa da "amin dad"

Kafin wani lokaci har Mami ta cika ummulkhair da kayan ciye ciye da na tande tande, shikuma sawwam sai diba yake yanaci Mami kuma sai fada take tana cewa ita bashi fa ta kawowa ba ummulkhair ta kawowa duk da haka bai yarda ba tare dashi aka cinye komai, dad yana kallonsu sai dariya yake yana cewa sawwam,

"Dan gidan dady kai baka koshi ne?"

"Dad nakoshi banbanci naga ana kokarin nuna min shiyasa nadage akaci komai dani"

"Ka karata dai" Mami tace tana dariya, ita dai ummulkhair tana zaune tana jinsu,

Lokacin da suka tashi tafiya har sun fito yaga mami ta biyosu da wani abu a hannunta acikin leda,

Matsawa yayi yana son yaji ko menene, nan mami ta koreshi, gaba yayi yana tuttura baki shi ala dole yayi fushi,

"Ungo wannan ummulkhair ki hada da madara da zuma kisha zai taimaka miki mutuka saboda naga wannan dan rawar kan bazai rinka saurara miki ba gashi kuma cikin jikinki baiyi kwariba shiyasa nasamo miki wannan insha Allah zai taimaka miki har lokacin da cikin zaiyi kwari" mami tafada tana mika mata kullin dake hannunta, karba ummulkhair tayi cikeda kunya amma har cikin ranta tana jin kaunar mami da sonta tamkar na uwar data haifeta saboda mami tana nuna mata soyayya tun kafin suyi aure da sawwam take sonta take kyautata mata har zuwa aurensu,

"To mami nagode"

"Haba haba ummulkhair babu komai Allah dai yabaki lafiya"

Karasawa wurin sawwam sukayi anan mami tasake ja masa kunne akan ya rinka kulawa sosai da ummulkhair sannan yarage wannan rawar kan, dariya kawai yayi aransa yana cewa,

"Wai mami sai tarinka cewa narage rawar kai, ni wallahi bazan iya hakuri ba"

Sallama suka yiwa mami suka tafi, lokacin da sukaje gida sai da ta kira abbanta suka gaisa nan yayita sanya mata albarka yana yimata kyakkyawar addu'a sannan daga karshe ya hadata da mama suka gaisa.

Sai da ummulkhair tayi hutu nasati daya sannan taci gaba da zuwa makaranta,kullum tare suke fita su dawo da sawwam,

Cikinta ya shiga wata na shida yanzu kam ya fito kowa yaganta yasan tana da juna biyu, murnar sawwam kasa boyuwa tayi domin kullum cikin kallon cikin yake yana lissafin haihuwa,tsiya kam ummulkhairi tashata awurin alawiyya lokacin da taga cikinta yafito,

"Wai har sawwam yayi miki me?"

"Abinda kika gani" ummulkhair tabata amsa tana harararta,

"Me idona yagani?" Alawiyya tasake tambayarta tana dariya,

"Ciki" ummulkhair tabata amsa,

"Tab wannan ai kune hadamammun, da yaushe kuka yi auren ma da har za asamu juna biyu?"

"Lissafa kiga, yau watanmu bakwai da aure watanmu shida da tarewa, haka shima cikin watanshi shida"

Dariya alawiyya tayi, "Allah ya kyauta muku aranar da kuka tare aranar kuka samu abunku"

"Amin, dama ai ba kallon juna mukaje yiba"

"Ai nagani, Allah yaraba lafiya"

"Amin" ummulkhair tace tareda mikewa saboda ta hango motar sawwam yana karasowa, tare sukaje wurinshi da alawiyya saboda zasu sauketa agida,

Kallon sawwam ummulkhair tayi bayan sun hau titi, "sahibi kaji abinda alawiyya tace? Wai mu hadamammu ne aranar da muka tare aranar muka samu baby"

Alawiyya ji tayi kamar kasa ta tsage ta shiga ciki dan kunya, sawwam kam murmushi yayi saboda yana jin dan nauyin alawiyyar amma shima yasan hakane idan ma ba aranar bane to dai acikin satinne,

Sai da suka sauke alawiyya sannan ya kalleta yana murmushi,

"Abinfa da kawarki tafada wallahi gaskiyane, may be a first night dinmu muka samu rabo"

Baki ta turo, "ai duk kaine"

"Naji, kuma ina son abina sannan har yanzu ina sake jin sabon son matata"

Murmushi tayi ta kwantar da kanta a kafadarshi tana murmushi.

  Lokacin data kammala exams sawwam hutu ya dauka domin yana son su fita outside shida ummulkhair kasancewar basuje honey moon ba,sallama suka yiwa yan uwa da abokan arziki suka lula kasar Brazil, ummulkhair taji dadin zamansu awannan kasa domin sawwam yabata kulawa ta musamman itada babyn dake jikinta, kullum cikin tattalinta yake babu bata lokaci jikinta yasake gogewa ya murje ta sake zama katuwa ga fari da ta kara,

Satinsu bakwai suka tarkato suka dawo gida domin mami kullum cikin waya take kan cewa su dawo domin cikin khairi yakusa shiga watan haihuwa, dawowarsu da kwana biyar sukaje bauchi suka gaida su mama, sun samu tarba sosai daga wurinsu abba da kowa dake gidan, wuni sukayi sawwam ya dauketa suka koma kano.

Tunda suka dawo babu abinda ummulkhair takeyi,komai sawwam ne keyi, lokacin da edd dinta yakusa cika mami tazo ta tafi da ita gidanta saboda tace bazata barsu daga ita sai sawwam agidan ba gashi dukkaninsu yarane ba gama hankali sukayi ba, ai sawwam kamar zaiyi kuka ganin mami ta dauke masa matarshi, shi dinma tattarawa yayi yabisu gidan mamin ya bude dakinshi nada ya tare,

Lokacin da ya shiga sashen mami samun ummulkhair yayi zaune afalo tana kallo tana shan fruits ita kuma mami tana kan kujera tana lissafa kayan da ta bayar order aka kawo mata,

"Lafiya? Daga ina?" Mami tace dashi,

"Mami nima fa nadawo nan gidan saboda wallahi can yayi min girma ni kadai"

Murmushi Mami tayi taci gaba da lissafinta, shikuma kusa da ummulkhair yaje ya zauna yana kallonta yanda cikinta yayi kato kamar yanzu zata haihu,

Tunda ya dawo gidan baya iya yin bacci kullum haka yake kwana yana juyi, yau kwanansu biyar agidan ganin haka yasashi tafiya dakin da mami tabawa ummulkhair, tana kwance tana bacci yaje kusa da ita ya kwanta,

Har asuba tayi bata san yana cikin dakinba sai da mami ta shigo dakin kasancewar duk farkon dare da karshensa tana zuwa tana dubata,

Mamakine Yakama mami saboda ganin sawwam da tayi acikin dakin,

"Kai sawwam, sawwam tashi katafi dakinka" mami tace dashi tana bubbugashi, afurgece ummulkhair ta juya nan taganshi yana bacci,

Gyara kwanciyarsa yayi yana cewa,

"Dan Allah Mami kibarni wallahi kasa bacci nakeyi idan bata nan"

Juyawa mami tayi ta fita ta rabu dashi, ita dai ummulkhair tagumi tayi tana kallonshi.

49

Koda gari ya waye tashi yayi yana hamma ya shiga toilet yafito yayi salla yana kallon ummulkhair wacce ke zaune gaban mirror tana shiryawa,

"Good morning my lonely" yafada yana kashe mata ido,

"Gaskiya ni karka kara zuwa, haka kawai zaka wani zo dan kasa mami ta zargi ko wani abun muke"

Tashi yayi yaje ya rungumeta ta baya,

"Na nawa kuma, ai mami tagama sanin muna yin wani abu dake tunda gaki nan dauke da katon ciki"

Hannu takai zata dakeshi ya rike hannun tareda kaishi bakinsa yafara kissing dinshi, babu zato Mami ta shiga cikin dakin,

"Sawwam me zan gani haka? Yanzun ma da take dauke da tsohon cikin ba zaka barta ta huta ba"

Saurin matsawa yayi yana murmushi, "mami bafa komai nayi mata ba itace tayi kokarin dukana shine na rike hannun"

"To naji zo ka fita"

Juyawa yayi yafita yana jin mami tana tambayar ummulkhair abinda take son adafa mata,

Tunda kwanakin haihuwar suka gabato sawwam ya daina fita office saboda yafi son khairi ta haihu agabansa yana nan amma haihuwa shiru har edd din ya wuce, fushi yayi ya shirya yayi tafiyarsa office,

Ummulkhair tana daki a kwance saboda tunda ta tashi take nakuda amma taki ta bari mami tagane, karfe 12 narana mami ta fuskanci nakuda take dan haka suka tafi asibiti suna zuwa babu jimawa ummulkhair ta haihu, ta samu baby boy dinta kato kyakkyawa mai kama da babanshi sak,

Tunda ta haihu tajita lafiya lau ta rabu da duk wani ciwo wanda ada yake damunta, wayarta ta dauka takira sawwam,

"Hello, sahibi kazo kaga babynka,tun dazu yana ta son ganin dad dinshi" tace da sawwam bayan taji ya daga wayar,

"My lonely bana son wasa fa" yafada cikin doki,

"Allah dagaske nake ko na mintsineshi yayi kuka kaji"

"No, no dan Allah karki mintsineshi kibari idan nazo ni sai ki mintsinenin"

Da saurinshi yaje ya shiga mota sai asibiti saboda dama yasan asibitin da mami take kaita, lokacin da yaje ya samu nurses sunata gwada mata yanda zata shayar da yaron, tsayawa yayi yana kallonsu kirjinta ko kadan bai canjaba yana nan kamar yadda yake da sai cika da ya sake yi,

Hadasu yayi ita da yaron ya rungume ko kunyar mami baiji ba, ita mami kam yau bakinta yaki rufuwa sai waya take yiwa yan uwa da kawayenta tana sanar dasu matar sawwam ta haihu,

Basu dauki dogon lokaci ba aka sallamesu suka tafi gida, tunda sawwam ya dauki jaririn ya rikeshi bai ajiyeba har sai da Mami tayi masa dagaske ta koreshi daga dakin saboda ganin yan barka har sun fara zuwa ganin jariri,

Koda dare ma yayi haka suka sha fama shi da mami saboda cewa yayi dole shi sai adakin zai kwana, korararshi mami tayi tace bazai kwana anan ba, sai kawai ya dauki jaririn,

"Ina kuma zakaje dashi" mami ta tambayeshi,

"Mami zantafi dakina dashi ne, ga yarki nan nabar miki nima na dauki dana saboda nasan akan tane zaki hanani kwana a dakin"

Abin dariya yabawa mami saboda ganin yanda ya dauki jaririn da net dinshi,

"Kawo shi nan shi dinma babu inda zakaje dashi kai kadai zaka tafi"

Fushi yayi ya bata jaririn ya fita amma bai hakura ba asubar fari sai gashi ya dawo bayan ya dawo daga masallaci,

Kullum yana manne adakin sai dai idan yaga baki sunzo sannan ne zai fita suna tafiya zai dawo da haka har ranar suna ta zagayo,

Saniya da raguna dad ya yanka sannan ya bawa jaririn sabuwar mota kirar kamfanin KIA, ga gida da ya mallaka masa wanda ke unguwar rijiyar zaki, anyi shagalin suna sosai yaro yaci suna Abdulrahman,mai jego ita da jaririnta sunyi kyau sosai tasha swiss les wanda mami ta dinka mata bayaga kunshi da lalle da aka yi mata,

Gidan mami cika yayi dam da al'umma nan manyan mata suka rinka cashewa ana zuba musu naira, har mangaruba tayi mutane basu bajeba, makida da mawaka kuwa ranar sun baje basirarsu, har bayan sallar isha aka kai ana budiri daga bisani kowa ya tafi gidansa cikeda kayan suna.

Tunda akayi suna kuma sawwam yafara damun mami da tambayar yaushe zasu koma gidansu shida khairi, ko kallonsa mami batayi bare ta amsa masa domin ita tabada himma wurin sake sabinta masa khairin sa yanda zai sake riketa da daraja,

Har akayi arba'in yaron yayi wayo mami bata bashi khairi ba wasa wasa har suka yi kwana 60,

Dakin khairi ya shiga ya isketa kwance ta dora andulrahman akan ruwan cikinta,

"My lonely yakamata fa ki tausaya min mukoma gida haka, wallahi zan iya shiga wani hali"

Kallonshi khairi tayi tasaka murmushi,

"Ni babu ruwana kaje ka sami mami ka fada mata"

"Haka kikace? Shikenan"

Juyawa yayi ya fita, tun daga lokacin yake fushi sam yaki dariya koda yaushe fuskarshi ahade,

Da daddare yana falo a zaune yana cin tuwo khairi ta sameshi zata fita zuwa kitchen, waya taji yana yi kasa kasa,

"Sorry ai nace miki ba ason raina bane amma kiyi hakuri zanzo may be gobe inyaso sai mu karasa maganar.."

Shiru taji yayi kafin yaci gaba,

"Ohh God! Ai nabaki hakuri, nawane kudin saloon din? Kibari idan nazo sai nabaki zan ma kaiki da kaina, ok thank you, abdulrahman zaiji,bye bye.."

Katse wayar yayi yaci gaba da cin tuwonshi, yana juyawa kuma sai yaga ummulkhair a tsaye tana kallonsa,

Batace dashi komai ba tawuce kitchen amma hankalinta yagama tashi da wayar da taji yana yi, kishine yafara taso mata saboda gani take kamar sawwam wani sabon auren zai sake yi rumtse idanuwanta tayi tana jin kishinsa har cikin ranta,

Dakin mami tawuce ta sameta akan dadduma tana lazimi, zama tayi har ta idar ta juyo tana tambayarta me take bukata,

Sunkuyar da kanta tayi ta daure tace "mami dan Allah kibarmu gobe mu koma gida, saboda wallahi sawwam yafara neman aure saboda wai naki komawa,ni ko bauchin ma nafasa zuwa idan mun koma daga baya yakaini"

Murmushi mami tayi tace "babu komai Allah ya kaimu goben sai ku tafi"

Tashi tayi tafita amma lokacin sawwam baya nan yatashi, dakinta takoma tafara harhada kayanta dana Abdul,

Washe gari mami ta kira sawwam tace yazo zasu tafi, shan kamshi yafara ya kalli khairi,

"Mami suyi zamansu basai sun koma ba"

Cikeda mamaki ummulkhair ta kalleshi sai kuma tafara kwalla,

"Mami kin gani ko wallahi aure zaiyi.."

"Aure kuma? Babu auren da ya isa yayi, shekarun nasa ma nawa suke da har zaiyi wani sabon auren, kai kana jina wallahi ko bayan raina ban yarda kayiwa wannan yarinyar kishiya ba"

"To" yafada yana hararar khairi,

"Kadai ji nafada maka, ummulkhair tashi ku tafi, Allah ya kiyaye hanya"

Tashi ummulkhair tayi suka fita nan sawwam ya debi kayansu yabi bayansu dashi, baba dan tsoho na ganinshi yafara washe baki yana yi masa kirari,

Murmushi kawai yayi baice komai ba yashiga motar suka tafi, ko acikin motar ma yaki kulata sai iya Abdul yake kallo yana yimasa wasa, har sukaje gida bai kulata ba,

Gidan ta gyara ta tsaftace tayiwa Abdul wanka tasake shiryashi, shikuwa sawwam tunda ya kawosu yafita bata sake ganin idonshi ba, sai da dare yayi bayan tayi wanka ta shirya cikin kayan bacci riga da wando light blue wandon iya cinya rigar kuma iya cibiyarta, tana falo zaune rikeda Abdul sai gashi ya shigo kallo daya yayi mata yaji hankalinsa na neman gushewa yabar jikinsa,

"My lonely bakiyi bacci ba? Taso muje ki kwanta.."

Kanta ta dauke, "sai yanzu zaka yimin magana?"

"Haba my one and only",

"Ni ba one and only dinka bace tunda kana shirin karo wani auren"

Zama yayi kusa da ita, "wallahi ni wacce kikaji muna waya ba budurwa tace ba budurwar suhaib ce sukayi fada akan zuwa saloon shine ta kirani take fada min nikuma nabata hakuri nace zan kaita saloon din kuma zan biya kudin, ki yarda dani wallahi babu wata bayan ke"

Kallonsa tayi anan taga har kwayar idonshi ta sauya, sai da yasake rarrashinta sannan ta tashi tabishi zuwa master room...

Sawwam da khairi suna gudanar da rayuwarsu cikin kaunar juna da hakuri da juna, bayan lokaci yadan shude ummulkhair ta kammala karatunta lokacin Abdul yanada watanni takwas a duniya, alokacin office din su sawwam suka turashi karatu kasar Turkish, cewa yayi bazai iya tafiya shi kadai ba sai da khairinshi da yaronshi dan haka anan suka hau shirye shiryen tafiya, sallama sukaje suka yiwa yan uwa sannan suka daga, to sai muce adawo lafiya.

   Alhamdulillah

Anan muka kawo karshen wannan littafi mai suna ramuwar gayya, Allah ya amfanar damu darasin dake ciki,

Sakon gaisuwa ga masoyanmu masu sonmu, masu son rubutunmu, Allah yabarmu tare muma muna sonku,sai mun hadu daku acikin labari nagaba.

*Kuna ranmu*

Anty maijidda musa
Khadija Sidi
Kdeey
Serdia lawal
Miss Aysher
Halamcy
Maryam kaumi
Hawy
Lilmeerahcute
Xuhura Ajiya
Maryam Ramat
RAZ

Masoyan Nada yawa uncountable......

Fatan alkairi ga members din groups dinmu,

Pherty novels 1&2&3

Duniyar makaranta 1&2

Ummi shatu

Pherty Xarah

RAMUWAR GAYYA.. 47

*RAMUWAR GAYYA......💘*

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

         &

*Ummy Aysher*

47

  Alhaji mukhtar yayi Saurin tsaidashi,

'karkaje ka raba wannan auren Abinda Allah ya rubuta ba Wanda ya isa ya hanashi, ko ba komai yarannan suna son junansu,

'idan mutum yayi ma ba dai dai ba, ka haqura kabarshi, ai *Alheri danqo* ne saka mashi da alherin kai kuma sai kaga kyakkyawar sakayya, kayi haquri kabarshi kabar komai ba komai ba abinda ya riga ya wuce ya tafi sai kubawa xuciyarku haquri amma Sam *Ramuwar gayya* bata dace da ku ba,

'kayi haquri yaya idan har nabar masu yarinyar sunci Lagona kenan, an karbemin budurwa an karbemin yarinya,

'Tun asali can ba matar ka bace, ai matar mutum kabarinsa, ya dubi yayan Ransa a bace,

*'Matar waye*? Sun dai ci amanata ne, kuma bawai ina son ta bane har ynxu kawai Ina so na rama abinda suka min ga yaron sune,

'Sam bai dace ba, Kada ka kuskura karaba wannan auren na khairi domin yaran suna son junansu, Kada ka shiga haqqinsu akan abinda basuda laifi akai, tunda baka jin magana kaje can kacigaba da gabar da kake da mahaifansa,

Abba ya sa Kai ya fice yana gunguni shi baiga abinda xai hanasa karbo yarinyarsa ba sai ya saketa,

Yana fita gidan motarsa ya shiga Ransa a bace kai tsaye Kano ya nufa, baisha wahalar neman gidan su mahaifin sawwam ba kasancewar yana da address ďin gidan.

Dad da Mami na xaune a falonsu lokacin suna tattauna Mgnr su Kan sawwam ne, yaga yaron ya daina xaman gida ina yake xuwa tunda ya bincika gurin aikinsa an tabbatar masa da lallai yana xuwa,

'Tace duk inda yake xuwa baxai wuce gurin abokansa ba kuma hakan yafi saboda xai rage damuwa sosai da kaďaici shi kaďai a ďaki,

'hakane ba laifi tunda yana xuwa gun aikinsa, sai a fara nema masa auren Rukayya kada abarshi haka ba mata,

Gaban mami ya faďi tun bata kai ga magana ba sai ga mai gadi ya shigo, ya gaidasu cikin girmamawa,

'Alhaji kana da baqo a waje, Dad ya dubesa,

'Waye shi,
'bai gayamin ba amma dattijo ne kamar irin mu,

'kaishi falon baqi... kodai shigo da shi nan ďin,

Maigadi ya fita da sauri bai jima ba sai gasu tare,

Suna haďa ido dad ya tashi da mamaki yana kallonsa, mami Kuwa kusan ruďewa tayi,

'me Kuma kaxo yi gidana?
'in banda ya'ta har akwai abinda xnxo yi a Wannan gidan naka,

Dad ya juya yana kallon mami data daburce kafin ya maida kallonsa garesa,

'wace ya'kuma, ko kayi batan kaine,
'wannan tambayar yaron ka ya dace kayiwa, ya'ta naxo abani a yau ďinnan, yaje ya sami guri ya xauna, jikin dad na soma rawa Ransa ya baci Kada xarginsa ya xama gsky sawwam yana tare da khairi ne,

A dai dai wannan lokacin khairi na kwance a jikin sawwam tayi matashi da cinyarsa,

'tashi mugani cikinnan ya qara girma, ta qara narkewa,

'wai kai kullum aka cema yake qara girma ne, kullum sai kace xaka duba kagani idan ya qara girma,

'tor shikenan gyara xn duba lafiyar cikin,

'yaushe Kuma ka xama likita bn sani ba,

'ni likitanki ne ai, barama kigani.... kafin tayi mgn ya kware rigar ya kara kunnensa a cikin yana saurare, kallonsa take cikin so da qauna kome yayi yana burgeta, sai ya dubeta da murmushi,

'kinji me yace....

Tayi far da ido cikin tsananin mamaki kafin tayi murmushi tana shafar fuskarsa,

'banda qarya sahibina, wata uku ne fa ko mutum bai xama ba,

Ya bata fuska alamar yayi fushi,

Tayi murmushi haďe da sumbatarsa a gefen kumatunsa,

'yi haquri gayamin inji, yaja hancinta yana kallonta da murmushi,

'baby abinci yake so abashi dan haka muje ďaki, ya soma qoqarin ďaukarta, taqi bari suna haka wayarsa ta soma ringing, yana ganin mamice ya sauke numfashi haďe da Kara wayar a kunnensa,

'kana ina ne?
'gida,
'kaxo ynxu tare da khairi,

Kafin yayi mgn ta tsinke Wayar, ya dubi khairi yana gayamata abinda mami tace,

'ko xa'a rabamu ne,
'bana tsammanin haka qila tayiwa dad bayanin komai kuma xai fahimce mu ne, tashi ki shirya,

Ta tashi a sanyaye ta nufi dakinta, duk shirinta ba kuxari a jikinta, hijab ta sanya fuskarta ba kwalliya ta fito, ya dubeta dai dai ya fito cikin nasa shirin,

'chab ina xaki bini a haka, sai kace wacce ke xaune cikin takura, yaja hannunta suka koma shi da kanshi yayi mata kwalliya harda Jan baki Kuma tayi kyau sosai, da kanta ta ďaura kallabi, yabata gyale yana kallonta tayi kyau sosai,

'Haba ko Kefa, xamu gaida surukai xakije da wannan shigar,

Ta rungumeshi tana murmushi kafin ta kai masa kiss yayi Saurin riqeta yana kissing ďinta sosai, sai da ya gaji dan kansa kana ya saketa,

Ga mamakinsa sai yaga ta turo bakinta a shagwabe,
'bai isheki bane? Ta make kafada tana nuna masa Jan baki akan mirrow,

Tayi murmushi haďe da shafa kansa,

'sorry dear, yaje ya ďauko ya qara sa mata kana suka fita daga gidan.

Tun a bakin gate gabanta yayi mummunan faďuwa ganin motar Abba, ta dubi sawwam dai dai lokacin da yake parking motarsa, ya kalleta yana faďin,

'menene naga duk kin tada hankalinki,
'motar Abba yaxo ya tafi dani ne, shima gabansa ya faďi,
'impossible, fito muje ba abinda xai faru, baxasu rabamu ba ina sonki,

Ta fito jikinta a sanyaye suka shiga gidan, nan Iyayen maxa suka hau faďa sosai kowa nayi kan yaronsa da faďa Kamar xasu dake so, kowane ransa a bace sai kumfar baki suke cikin tsananin fushi,

Khairi ce kawai ke kuka gurin, mami da sawwam kuwa bacin raine kwance a fuskarsu,

'ki tafi muje, kin gama xama dashi sai inga ynda xaixo ya qara ďaukarki,

Ga mamakinsu sai sukaga khairi taje gaban dad ta riqe qafafuwansa tana kuka,

'karka bari ya tafi dani, ina son sawwam dan Allah kada ku rabamu kabawa Abbana haquri,

A lokacin sai jikin dad yayi sanyi, tausayin yaran yakeji har cikin ransa, yayi shiru bai yi mgn ba,

Mami tace ba ynda xa'a raba aurensu, sawwam baxai saki khairi sai dai kaje da Ita tayi ta xama a gabanka, idan ta haihu ka maida mana yaron mu ka riqe yar'ka,

Sai sukaji mgnr wata iri banbarakwai  daga Abba har dad, khairi nada ciki kenan,

Abba yaxo a fusace ya fisgota, tana kuka take kallon dad aganinta shi kaďai xai iya cetonta,

'please dad.......

Abba sai janta yake, tayi saurin riqa hannu sawwam shima a ynxu hawaye yake, Abba ya juyo yana kallonsa,

'kai sake min yarinya bana son shashanci, ba musu sawwam ya saketa,

Tanaji tana gani Abba ya rabata da sawwam, ya sanyata a mota ya fice da sauri,

Sawwam ma ďakin sa ya nufa ransa a bace, ya bugo qofar ďakin ji kake gam kamar xai ballata....

'Dad yace duqawa wada baxai hana ya tashi ba, ni nayi masa laifi saboda ke, xnje na bashi haquri saboda yaran, suna matuqar son junansu,

'Mami tace sai muje tare a gobe kaga yarinyar nada ciki kar yaje ya salwantar dashi, munason cikin da farincikin sawwam,

'Nima haka nake tunani cewar dad.

Khairi Kuwa kuka take sosai acikin motar bai kulata ba har suka xo gidan, idanunta sunyi jawur luhu luhu da su,

Da gudu ta shiga cikin gida tana kuka, kukanta ya fito da mama daga kitchen anan ta sameta tsugunne riqe da cikinta sai amai take kwararawa kamar xata amayarda hanjin cikinta,

Mama sai sannu take mata cikin tausayawa yarinyar, taje ta kawo mata ruwa,

'sai dai ki mutu amma kin gama xama da wannan yaron cewar Abba yasa kai ya fice da sauri,

Khairi ta riqa ta tana kuka,
'mama ki taimakeni, mama kibashi haquri ya maidani inda sawwam,

Mama ta riqata suka shiga ďaki, yinin ranar komai bata ci ba har dare duk ynda mama tayi da Ita taqi taci komai, yayyunta maxa ma sai tausayamata suke suna rarrashinta taci taqi kasancewar ita kaďai ce Mace a gidan duk maxa ne shiyasa suke sonta,

Har goma na dare taqi taci komai, mama ta damu sosai sai taje ta gayawa Abba,

'ai ba'a fushi da abinci kibarta xata nemeshi dan Karan kanta ko dan cikin dake jikinta,

'cikine da Ita Alhaji? ta tambaya cike da mamaki,

'cikine da Ita wai injisu  Iyayen yaron, koma dai menene tagama aurensa, idan ta haihu xn kai masu abinda ta haifa shikenan,

Mama ta girgixa kanta kawai cike da takaici tabar ďakinsa wannan rayuwa dame tayi kama,

'ummu.. Ummu.. ta soma kiranta, can qasan maqoshinta taji ta amsa,

'tashi kici abinci ba dan niba sai dan abinda ke jikinki, bakisan xaman ki da yunwa xai iya janyo masa matsala ba, idan ya xube mijinki baxai ji daďi ba,

Khairi ta ďan dubeta tana share hawayen fuskarta,
'mama ni sawwam nake so,

'kici abinci tukunna xamuyi Mgnr,

'bana iya cin komai ynxu sai tea,
'shikenan bara na haďa maki,

Tea mai kauri ta haďa ta kawo mata ta bata,
'inbaki bread, ta girgixa kanta, biscuits fa, nan ma a'a, cake fa, ta yatsina fuska kafin ta girgixa kanta,

'haka xakisha ruwan tea bada komai ba ai baxai riqa cikin ki ba ummu,

'mama ya isa, tasa kai ta shanye tas, sai ga xufa na karyo mata sai wani ajiyar xuciya take, ta cire rigar jikinta,

'mama tace ko xakiyi wanka ne? Ta gyada Kai tana kallonta, mama da kanta ta haďa mata ruwan wanka taje tayi ta fito tana kallon maman dake xaman jiranta,

'mama bakuda ďan wake a gidannan?
'ďan wake ynxu ummu, Ina xn samu,

Khairi ta xauna tana yatsina fuska,
'mama kimin kona garin rogo ne kona flour,

Mama ta tashi tana faďin inaji kamar da akwai flour gidan bara na duba ingani, ni xama bai sameni ba tunda an haďa ni da lalurar Mai ciki ta fice....

Tana fita khairi ta dauki wayarta ta Kira Alhaji mukhtar cikin kuka take sanardashi duk abinda ya faru,

'kiyi shiru ki kwantar da hankalinki bai isa ya rabaki wannan auren ba, tunda ni har nayi masa mgn bai jiba Gobe xnxo da aminin babanmu nasan shi dole ya isa da shi,

Tayi godiya sosai xuciyarta fal da farinciki, ta kira wayar sawwam bata shiga sai ta ajiye wayar.

*

Washe garin ranar da sassafe Alhaji mukhtar yaxo gidan tare da wani dattijo aminin babansu suna kiransa da baffa,

Faďa sosai yayiwa Abba har sai da yayi danasanin abinda ya aikata,

Ana haka sai ga dad mami da sawwam,

Nan aka taru aka sasanta Iyayen bayan faďa da nasihohin da baffa yayi masu,

'a koda yaushe ka xama mai yafiya domin kaima a gurin Allah mai laifine,

Suka yafe juna tare da miqawa juna hannu suka gaisa haďe da rungume junansu cikin farin ciki, shekaru da yawa rabonsu da hakan,

Basu ankara da sawwam da khairi basa gidan ba sai da suka soma nemansu, tuni sun kama hanyar Kano sun bar Iyayen.......

*Pherty xarah*

        &

*Ummi shatu🏼*

My wattpad Phertymerh1

RAMUWAR GAYYA.. 46

Ramuwar gayya.. 46
*RAMUWAR GAYYA...*💘

_Love story 50,50_

*_Ummi A'isha_*
_with_
*_Phertymerh Xarah_*

46

K'arfe biyar da rabi sawwam yafarka,
ummulkhair ya kalla wacce ke kwance gefenshi
ta cure jikinta wuri guda,

Hannunshi yakai kan goshinta ya taba, duk zufa
ta tsatssafo mata kamar wacce take zaune
atsakiyar rana,

Tashi yayi ya shiga toilet ya tsaftace jikinsa
yafito, zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi
kamar kankara sai zallar farin ciki dake
wanzuwa acikinta marar yankewa,
Idonshi akan khairi ya dauko kayanshi yasaka,
gaban gadon yaje ya dagata ahankali ya gyara
mata kwanciyarta, fuskarta yabi da kallo yana
murmushi saboda baccinta take hani'an kamar
ta shekara batayi ba,

Sai da yabata wani zazzafan kiss a kumatunta
sannan yaja bargo ya lullubeta yafita masallaci.

Karfe shida da yan mintuna yadawo cikin dakin
amma har lokacin ummulkhair bata tashiba
asalima ko juyi bata yiba tana nan a yarda
yatafi yabarta,
Gefenta yaje ya kwanta ya dagota zuwa
jikinshi ya rungumeta,

"My lonely yau kin tabbatar da abinda nadade
ina fada miki cewar zan baki daddadar rayuwa
duk ranar da muka kasance tare,

Gashi yau Allah cikin jin kansa ya nuna mana
wannan lokacin, Allah yayi miki albarka
khairi,Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya
albarkacemu da 'yaya masu albarka,
Ina tsananin sonki ummulkhair and bazan taba
daina sonki ba har karshen rayuwata, babu
abinda zai rabani dake...."

Sharrr hawaye suka fara bin kumatunsa, ita dai
khairi kamar a mafarki take jin maganganunsa
kasancewar bacci take yi sosai,

Rungumeta yayi sosai ajikinshi har bacci ya
sake tafiya dashi bashi ya tashi ba sai da
misalin karfe tara saura,

Mamakine ya kamashi ganin har lokacin
ummulkhair bata tashiba, tashinta yafara yi
ahankali,
"My lonely..., my lonely rana tayi bakiyi salla
ba.."

Sake gyara kwanciyarta tayi ta juya baya, bai
hakura ba yasake komawa gefen datake yana
shafar fuskarta,

"Tashi mana yanmata na..."
"Um, um ka kyaleni"
"Sai yaushe zaki tashi to?"
"Yanzu..." Tabashi amsa har lokacin bata bude
idanuwanta ba,

Ganin bata da niyyar tashi yasashi kyaleta
yafita, motarshi ya dauka ya nufi gidansu,
lokacin da yashiga ko dakinsa bai shigaba ya
nufi falon Mami, tana cikin kitchen ita da mai
aikinta suna hada breakfast,

Daga bakin kofa ya tsaya yafara gaida mami,
kallo daya zaka yiwa fuskarsa ka fahimci irin
tsananin farin cikin da yake ciki,
"Sawwam har ka tashi?" Mami tace dashi tana
fara'a,

"Ehh wallahi Mami" yabata amsa yana sosa
keyarshi saboda yasan mami ta rigada ta
fahimci komai,
"Mami kawo natayaki..."
"To zo ka debi wannan flasks din ka kai kan
dining ka jera"

Da murmushi akan fuskarshi yakarasa cikin
kitchen din yafara diban flasks din yana kaiwa
kan dining, mami sai kallonshi take in banda
murmushi babu abinda yake yi shi kadai,
Girgiza kai Mami tayi ita dinma wani farin
cikine yake ratsata domin farin cikin sawwam
shine farin cikinta,

Tare suka kammala shirya breakfast din har dad
ya shigo cikin shirinsa na zuwa office,
Fuska dauke da fara'a da walwala sawwam ya
gaidashi, shi kansa dad din sai da yayi mamaki
saboda yajima baiga fara'ar sawwam haka ba,

Cikin farin ciki sukayi karin kumallon suka
kammala, lokacin da dad zai fita har farfajiyar
gida sawwam ya rakashi,
Yana ganin dad yafita yakoma wurin mami,
"Mami zanje natafi, nabar ummulkhair ita kadai"

Murmushi mami tayi tana harhada masa food
flasks acikin wani dan madaidaicin kwando,
"Lafiyarta dai kalau ko?"
"Mami lafiya lau take"
"To ka gaisheta dakyau, ga abincin"
Karba yayi yajuya ya fita yana fadin, "zata ji
mami".

Sawwam bai jima da fitaba ummulkhair ta
tashi, zama tayi tana kallon ko ina nacikin dakin
da kallo, take kuma abubuwan da suka faru
suka rinka dawo mata daya bayan daya,

Mikewa tayi ta lallaba ta shiga bathroom ta yi
wanka bayan ta gasa jikinta da ruwa mai zafi,

Fitowa tayi daure da towel ta nufi dakinta, kaya
tasaka riga da skirt na shadda kalar ruwan kwai,

Salla tayi sannan tayi musu addu'ar samun
zaman lafiya itada mijinta, tana idarwa ta mike
ta dan gyara fuskarta tafita falo,

Abincin da sawwam ya kawo mata jiya shi ta
ciro daga cikin fridge, ko dumamawa batayi ba
ta zauna taci ahaka saboda yunwa takeji,
Kan doguwar kujera takoma ta kwanta bayan ta
kammala cin abincin, bata jima da kwanciyar ba
sawwam ya shigo hannuwansa dauke da kaya,
Kayan ya ajiye akan center table yana kallonta,

"Ba zakizo kiyi min sannu da zuwa ba?"
Zaune ta tashi tana murmushi sai dai takasa
hada ido dashi,

"Sannu da zuwa..."
Kafada ya makale alamun bai yarda ba,
"Nidai sai kinzo kinyi min sannu da zuwa
sannan zan amsa"

Murmushi tayi idonta yana kallon kasa gashi
takasa tashi taje inda yake,karasawa yayi ya
zauna akusa da ita tareda kamo hannuwanta
yarike cikin nasa,
"Kin tashi?"kai ta daga masa,
"Kinsha bacci.."

Kallonsa tayi sai kuma tayi saurin kawar da
kwayar idonta kafin su hada ido dashi,
"Ga abinci mami ta bayar akawo miki, taso
muje nabaki"
Girgiza masa kai tayi, "na koshi"
"Me kikaci?"
"Abincin jiya"

Murmushi yayi ya tsaida idonshi akan fuskarta
ya lura duk maganar da take masa tana yine
idonta akasa batare data kalleshi ba yasan
kunyarsa takeji yanzu, niyyar tsokanarta yayi
yakai hannunshi kan zif din rigarta, cikin sauri ta
rike hannunsa tana kallonsa,

"Meya faru?" Yace da ita yana murmushi kasa
kasa,

"Babu komai"

"To zomuje ki kwanta ki huta"
Kai ta girgiza masa alamun a'a, murmushi yayi
ya shafi gefen fuskarta,

"My lonely matsoraciyace duk kinbi kin tsorata
daga jiya kadai, sannan wannan kunyar babu
inda zata kaiki garama ki cireta"

Bai barta tayi magana ba ya mikar da ita tsaye
yakamata zuwa bedroom dinta, kwantar da ita
yayi ya zauna agefenta yana yi mata tausa har
bacci ya dauketa yana ganin haka shima ya
kwanta akusa da ita.

Ranar dai tare suka wuni agida baije ko inaba
dama ko office bashida niyyar zuwa, sai da dare
yayi sannan suka fita tare, gari suka dan
kewaya sannan yadawo da ita gida ya koma
gidan mami, sai da yajira suka ci abincin dare
tareda dad,har sai da yaga dad din yashiga part
dinsa sannan yayiwa mami sallama zai tafi,

"Ka gaisheta, sannan dan Allah sawwam ka
kula da ita sosai kaji, kaga dai irin halaccin da
tayi maka"

"Insha Allah mami zan kiyaye"

Lokacin da yaje gidan yasamu har ummulkhair
ta yi shirin bacci ta kwanta adakinta,

"Badai har kinyi bacciba?" Yafada yana shafar
kumatunta,
"Nadai fara, kadawo?"

"Ehh nadawo, tunda kin kwanta bari naje nayi
wanka"

"To sai da safe" tafada tareda gyara
kwanciyarta,

"Wanne irin sai da safe? Ai zan dawo, ko yau
korata kike?"
Shiru tayi tana jinsa bata amsa ba, hannunta ya
kamo,

"Zo mutafi dakina"
Kafada ta makale,

"a'a"

"Wai yau abin tsoro nazama ne? Dakin nawa ma
tsoronshi kike?"
Sake kwanciya tayi tana turo baki,

"Zo mutafi maza my lonely dina..., Allah muna
zuwa baccinki zakiyi"

Da lallami da komai yasamu ta tashi tabishi
zuwa dakin nashi, wanka ya shiga ita kuma ta
hau kan gadonshi ta kwanta, kafin yafito daga
wankan har tayi bacci,murmushi yayi ya shirya
ya matsa kusa da ita ya rungumeta,

"Shine kikayi bacci kika barni baki jirani nazo
munyi hiraba"

"Indai wannan hirarce nayafe" yaji tabashi
amsa, murmushi yayi ya sake kankameta
tamkar zai mayar da ita cikin kirjinsa.

Ahaka har sukayi sati daya, kullum mami ce
take basu abinci shi dad ma sam bai san
sawwam baya kwana agidan ba saboda yana
ganinshi kamar da, sai dai wani lokacin idan ya
nemeshi cikin dare sai mami tace yayi bacci
saboda yasha maganin mura, sam dad bai taba
ganewa ba shiyasa hankalinsa ya kwanta
musamman ma da yaga shi kansa sawwam din
shima hankinsa ya kwanta.

Tunda ummulkhair tazo gidan yau kwana goma
kenan sai yau sawwam zai fita office amma da
kullum agida yake wuni suna soyayyarsu shida
khairi idan dare yayi kuma sufita su zagaya gari,

Yana kwance yana bacci ta shigo taci kwalliya
sosai, daga shi har ita har sunyi kiba a yan
kwanakin da suka dauka tare,
Bakinshi ta tsotsa da nata tana dariya,

"sahibi
kafasa fita aikin ne?"
Kamota yayi zuwa jikinsa ya rungumeta, "ban
gama baccin bane"

"To katashi kayi wanka ko ka makara"
Jin zata zame ta gudu yasashi bude idonshi,
"ina zakije?"

"To bakaine kaki tashiba"
Tashi yayi yana kallonta, "natashi, shikenan?"

Kai ta daga masa taja hannunshi, wanka ya
shiga ya fito ta shiryashi yafito fes dashi,
breakfast ta gabatar musu sukaci sai da ya
sammata soyayyarsa mai tsayawa arai sannan
ya mike domin fita, babu zato yaganta tafara
zubar da hawaye,
Rungumeta yayi yafara lallashinta,

"My lonely nima ba ason raina zan tafi nabarki
ba amma sai dai zanyi miki albishir guda daya,
kema acikin week dinnan zaki koma makaranta"
Tsalle tayi ta rungumeshi ta fara kissing dinshi
a wuyanshi,

"Nagode sahibina, Allah ya kiyaye hanya.."

"Shikenan kuka yakare..?" Yafada cikin tsokana,
murmushi tayi ta daga masa kai, bayanshi ta
dale, ahaka yafita tana goye abayanshi har sai
da yaje wurin motarshi sannan ta sauka tana
dariya, shima dariyar yake ya bude motar ya
shiga,

"Zan iya tafiya?" Ya tambayeta, kiss tayi masa a
baki tana dariya,

"Zaka iya tafiya Allah ya tsare min kai har ka
dawo"

"Amin my lonely, sai nadawo"

Tana tsaye tana kallonsa har yafice daga gidan,
ciki takoma duk sai taji gidan babu dadi saboda
sawwam baya nan ita sai yanzune ma tasan ta
shaku dashi ashe da shakuwar da sukayi a
makaranta ba shakuwa bace shirme ne,
yanzune suka shaku shakuwa irin ta zuciya da
zuciya, yanzune take sonshi soyayyar da Allah
ne kadai yasan adadinta,

Tana zaune tanata missing dinshi har yamma
tayi, ta idar da salla kenan taji sallamarshi,
fitowa tayi ta rungumeshi sosai tana
murna,kallonta yayi tayi kwalliya tayi kyau sosai
abinta,
Kugunta ya rike yana hada fuskarshi da tata,

"Kinyi bakuwa"
Saurin sakinshi tayi ta kalli bayanshi, alawiyya
tagani tsaye tana murmushi, da gudu ta tafi ta
rungumeta,

"Ashe tare kuke? Wallahi ban ganki ba"

"Dama taya zaki ganni" alawiyya tafada tana
dariya, zaunar da ita ummulkhairi tayi ta kawo
mata abinci, sannan taje ta gabatarwa da
sawwam shima nasa abincin,hannunta yaja ya
hadata da jikinsa,

"Nifa ke kadai nake bukata ba wani abincin ba"
ido ta kwalalo,

"Haba sawwam bakaga munyi bakuwa bane,
kabari mana tatafi"
Dariya abin yabashi saboda yanda yaga ta zaro
ido,

"To naji..." Cakulkul yafara yi mata tayi saurin
kwacewa tagudu tana dariya,
Wurin alawiyya takoma suka fara hirar yaushe
gamo,

"Khairi kinyi kyau wallahi kuma gashi kinyi kiba
abinki"

Dariya ummulkhair tayi,

"nikuma wallahi bana
ganin kibar, shima sawwam kullum sai ya
tsokaneni wai nayi kiba"

"Gaskiya kinyi kiba, shima sawwam din naga
yayi kiba, da alama kuna kulawa da junanku"

Dariya ummulkhair tayi suka cigaba da hirarsu
da alawiyya,har dare suna tare sai da akayi
sallar isha sannan sukaje itada sawwam suka
mayar da ita gida.

Acikin satin ummulkhair takoma makaranta
tafara zuwa lectures, kullum tare suke fita da
sawwam yasauketa sannan yawuce office,

Gidan mami kuwa tunda ta tare bata jeba
saboda suna tsoron kar dad yaganta, ganin haka
yasa ita mamin ta shiryo tazo, basu jima da
dawowa gidan ba suna kitchen tana girki
sawwam yana tayata saiga mami tazo, ko
sallamarta basuji ba saboda hira suke yi, tana
bashi labarin wasu yanmata da sukayi fada akan
saurayi a makaranta yau,

"Kema fa kin taba fada akaina" yafada cikeda
tsokana,

"Ai ko yanzu da kake mijina bazanyi fada
akanka ba balle da a matsayinka na saurayi"

Dariya yasaka

"wallahi karya kike, yanzu idan
nakawo miki budurwata da dambe zaki kamata"

"Haba dai sai kace wata gara.."

"Allah kina kishina sosai nasani, duk daren
duniya fa sai kin fada min kalmar so sannan
kike yin bacci, au ashefa wani lokacin bakya
sanin kina fada, jiyama dan bakiji abinda kika
fada bane ko kina son ji in fada miki?

"Banda sharri dai" tafada tana murmushi,

"Babu wani sharri, kedai kam nasan idan baniba
sai rijiya"

Kafin tabashi amsa ya lallabo ta bayanta ya
rungumeta yana yi mata rada,

"nima idan bake
ba sai rijiya, ki gama girkin nan muje kibani
tukwici.."

"Haka dai.." Tafada tana tureshi,

"Idan kika hanani wurin yanmata na zan tafi,
ohh Allah sarki khairina rannan da kika yimin
rowa nace zan je wurin yanmatana fa rudewa
kikayi harda kukanki kina cewa dan Allah
sawwam karkaje wallahi zina babu kyau, dan
Allah kar kaje su bata min kai..."

Ya karashe
maganar yana dariya,
Dariya itama tayi ta debi ruwan da take fere
dankali ta watsa masa,

"Kuna inane?" Suka jiyo muryar mami,

"Lahh mamice tazo, dan Allah dauko min
hijabina"

Kafada ya makale yana dariya, "sai dai kifito
haka"

Rikeshi taje yi ya goce ya gudu yana mata
dariya domin wata yar rigace kamar shimi iya
cinyarta kalarta pink,

"Mami sannu da zuwa"

sawwam yafada bayan
ya zauna akusa da mamin, kallonsa mami tayi
dagashi sai short nicker da riga mai gajeren
hannu,

"Yawwa sannu ina ummulkhairin?"

"Mami taki fitowa wai kunya take ji"

Zaninta dake kan kujera ya dauka ya mika mata
cikin kitchen din ya fito, dole haka ta daure
tafito, kallo daya mami tayi mata ta fahimci
tana dauke da juna biyu amma su dayake
yarane duk cikinsu babu wanda yasani,

"Mami sannu da zuwa" ummulkhair tafada
cikeda kunya,

"Yawwa sannu, aiki ake tayine?"

"Ehh mami"

Mikewa tayi ta shiga daki ta sako hijab tafito ta
kawowa mami kayan motsa baki,
Cike da kunya ta gaisar da mami, cikin fara'a
da kauna Mami ta amsa mata tana tambayar ta
babu wani abu ko,

"Babu komai mami" ta amsa cikin jin kunya,
shikuma sawwam dake kusa da ita sai
mintsininta yake tayadda Mami ba zata
ganiba,hannunshi ta buge ta mike ta canja wuri
tana harararsa,

Mami bata wani dadeba sosai tace tafiya zatayi
saboda dama ganinsu kawai tazo yi, tare suka
fito suka rakota, kallon sawwam tayi tace,

"Ina fata dai baka matsa mata ko? Kaga juna
biyu gareta idan kafiya matsa mata dayawa to
cikin zai iya zubewa..."

Dukkaninsu mamakine ya kamasu, ga kunya mai
nauyi data rufe khairi,

"Mami ciki kuma?" Yafada cikeda mamaki,

"Kai baka saniba ba ko saboda kana shirme,
juna biyu gareta mana, Allah dai yaraba lafiya"

"Wallahi mami bata gaya minba boye min tayi
sai yanzu nasani da kika fada"

"To Allah yaraba lafiya, kuma ku kula sosai
banda shiririta"

"To mami..."

Ita dai ummulkhair takasa magana sai sawwam
ne kadai ke amsawa, har mami tatafi bata bari
sun kara hada idoba,

Yana ganin fitar motar mami yaja hannunta
suka koma ciki,

"Shine kika boye min?"

"Wallahi nima fa ban san dashiba nidai kawai
nasan tunda nazo gidan nan banyi period ba"

Rungumeta yayi yana murmushi, nan kuma
yashiga tsokanarta....

"Maman yan biyu ce ko?"

"Yan uku" tafada tana turo baki,

"Idan ma hudu kika Haifa min wallahi ina so,
gaskiya ke hadamammiya ce har kinyi ciki, koda yake nagane
bakya son wata tazo tafiki samuna ko?"

Tureshi tashiga yi,

"ni kyaleni naje nakarasa
girkina"

Tashi yayi yabita yana murmushi, "mu karasa
tare dai tunda dama tare muka fara"

Tana jinshi ta rabu dashi sai murmushi da
takeyi aranta tana ta mamakin wai har sun kusa
samun baby ita da sawwam lallai abin babu
wuya awurin Allah...

***

"Yau zanje nagano yarinyar nan" mahaifin
khairi yafada yana gyara babbar rigarsa,
Mama dake tsaye kamar zata saka kuka tace

"Allah ya kiyaye hanya, kagaisheta"

"Zataji" shine kawai abinda yafada yasa
takalminsa yafice,binsa mama tayi da ido amma
duk zuciyarta babu dadi saboda rabata da yarta
da akayi,

Karfe 12 suka shiga garin gombe, kai tsaye
gidan dan uwansa suka wuce sunci Sa,a sun
sameshi agida bai fita ko inaba,
Saida suka gaisa aka dan jima sannan abban
khairi yadubi yayansa,

"Ina ita wannan yarinyar take?
Kallonsa yayansa yayi,

"wafa?"

"Ummulkhairi mana" yafada yana fara,a,

"Ai bata zoba"
"Haba yaya, nifa nakawo yarinyar da hannuna"

"To ai tun wannan turowar da kayi aka tafi da
ita shikenan rabonmu da ita"

"Ni? Da yaushe?" Baban ummulkhair yafada
cikin tashin hankali,

"Banfa gane abinda kake son fada min ba, kaine
fa ka aiko aka tafi da ita.."

"Yaya wallahi ban san wannan maganar ba..."

Tashi yayansa yayi ya leka cikin gida yana
kwallawa umma kira, tana zuwa yafara magana,

"Zoki jiye min wani abin al'ajabi, kinji wai
bashine yaturo aka tafi da khairi ba"

Shiga rudani umma tayi jikinta yana rawa,

"Alhaji ka gafarceni wallahi banyi haka dan in
bata maka ba, dan Allah kayi hakuri"

"Me kuma yafaru?" Alhaji mukhtar yafada
hankali tashe,

"Alhaji wallahi ba shine ya turo atafi da itaba
mijinta ne..."

Zunbur abba ya mike arazane,

"wai kuna nufin
khairi bata gidan nan? Tana ina?"

"Tana kano gidan mijinta tun kimanin watanni
uku baya da suka wuce"

Mamakine karara ya bayyana a fuskokinsu
amma shi abban khairi bayan mamakin ma
harda tashin hankali, ko takansu bai sake biba
ya saba babbar rigarsa yafita yana cewa,

"Wallahi yau ko ani ko a mahaifin wannan yaron,
bazan yarda ba sai sun sakar min yata, yata
bazata zauna dashi ba".....

Ummi Shatu