Friday 14 April 2017

RAMUWAR GAYYA.. 48

*_RAMUWAR GAYYA..._*💘




  _Love story 50,50_

  *_UMMI A'ISHA_*

          _with_

  *_PHERTYMERH XARAH_*


  48

Driving sawwam yake da hannu daya yayinda daya hannun kuma yake rike da hannun abar kaunarsa ummulkhairi,

"My lonely nasan jiya bakiyi bacci ba kamar nima yanda banyi ba ko?" Yace da ita yana murza yan yatsunta,

Idanuwanta ta lumshe ta sake kwantar da kanta ajikin kujerar da take zaune,

"Wallahi banyi bacci ba sawwam, ai nariga da nayi sabon da bazan iya bacciba sai tare dakai.."

Murmushi yayi ya dan kalleta kafin ya mayar da idanuwansa kan titi,

"To kuma my lonely ranar da kuka zama ku biyu yaya zakiyi?" Yace da ita cikin zolaya harda fakar idonta yayi mata gwalo kasancewar idonta arufe yake shiyasa bata ganshi ba,

"Mu biyu kuma? Ai ko yanzu ma mu biyune" tafada idonta har lokacin arufe yake,

"Ah wai ina nufin idan na kawo miki kanwa"

Murmushi tayi tafara zare hannunta daga cikin nashi,

"Nabar mata kai tun kafin tazo"

Dariya yayi ya juya ya kalleta,

"Tun da wuri haka har kin bada ni kyauta"

Shiru tayi masa fuskarta kunshe da murmushi,

"Ehhh" tabashi amsa,

"Kinga kiyi hakuri nifa da wasa nake, idan na karo miki wata kuma ina zan saka kaina"

Murmushi tasaki ta kalleshi, "wai har ka tsorata?"

"Ba dole ba, nasan idan kika yi fushi akwai ta inda zaki rama"

Murmushi tayi ta sake makale yatsunshi cikin nata,

"Kaine kake tunanin haka amma ni ban kawo wannan araina ba"

"Wallahi karya kike mugunta kike son yimin kisani hauka...."

Dariya tafara harda rike ciki, "amma dai kasan Mami tace kadaina matsa min ko? Ko kana son murasa babyn?"

"Kai kar kiyi min mummunan fata, kin san kuwa yanda nake ji da wannan babyn? Duk duniya nafi sonshi fiyeda komai... "

Da sauri ta kalleshi cikeda mamaki,

"Harda su mami da dad dani ko?" Tafada fuskarta ahade,

"Ohhh baby kin cika rigima, bafa haka nake nufiba, ai ke special one ce nafi son ki fiyeda babyn, su mami kuma ai matsayinsu daban ne.."

Sakin fuska tayi tana murmushi, "kai dai kawai kayi min wayo"

"Babu wani wayo my lonely"

Tsayawa sukayi sakamakon tsayar dasu da danja tayi, kiss yakai mata akumatu ya mika hannu zuwa kan cikinta,

"Wai sai yaushe cikin nan zai fitone, nifa na kosa naga yadan turo"

"Saboda ba ajikinka yake ba ko? Kai babu mai kallonka balle yace..."

Dariya yayi yaci gaba da driving har lokacin dariya yake,

"Balle ace me? Kowa yasan kece kikazo dakina ni banine nazo ba, waya saki kizo?"

Itama dariyar tayi ta kalleshi, "au haka kace?"

Kada kai yayi yana dariya,

"Ko ba haka bane?"

"Amma ai kaine kayi min wayo ka lallabani har nabika ko"

Hularshi ya cire ya fara shafa sumar kansa, fuskarshi dauke da murmushi,

"My lonely kenan, kemafa yarinya ce in banda haka dama tunda kika bini ai kin san dole sai nabaki ajiya..."

"Ni ka rabu dani bacci zanyi.."

"To nayi shiru yi baccinki"

Bata kara magana ba ta lumshe idanuwanta, ga mamakinsa mintina kadan sai yaji tayi bacci murmushi yayi yaci gaba da driving yana kallonta yasan cikin datake dauke dashi ne yake sata baccin,

Har suka shiga cikin garin kano bata tashiba bacci take yi sosai hannunta rikeda nashi,

Yana shiga cikin gidansu yayi packing ya fita, kofar barin da take yaje ya bude ya daukota kamar wata jaririya, a falo ya kwantar da ita akan doguwar kujera,

Kitchen ya leka kozai iya hada musu wani abu kafin ta tashi amma yakasa saboda shi bai iya dafa komai ba,

Cornflakes ya hada ya zauna agefenta yana sha, har yagama tana bacci, kayan jikinshi yaje ya rage yafito da iya gajeren wando,

"Sahibina..." Ummulkhair ta fada tana mika bayan ta bude idonta,

"My lonely kin tashi?"

"Yunwa nakeji sawwam..."

"Bari nazubo miki cornflakes nima shi nasha yanzu"

Batare da bata lokaci ba yaje ya hado mata cikin cup ya kawo mata, agefenta yazauna yafara bata tana sha har ta shanye tas,

Matsawa ya sakeyi jikinta sosai ya kama hannunta ya rike,

"Zo ki rakani bedroom dina kiga wani abu"

Murmushi tayi ta tsaida idonta bisa fuskarshi tana kallonsa,

"Kai da kace nice nake binka dakinka, ai bazan kara zuwa ba"

Kwantar da murya yayi yana kallonta cikin kalar tausayi,

"Da wasa fa nake yi miki ai kowa yasan nine na gayyaceki dakin nawa ba haka kawai kika zoba"

Far tayi da idonta ta dauke kanta, ganin haka yasashi tashi ya dauketa ya nufi hangar dakinshi.....

  Ramuwar baccin da basu samu sunyi ba adaren jiya shi sukayi, itace ta fara tashi, wanka tayi ta shirya ta shiga kitchen ta dora girki, tana cikin kitchen din tana aiki ya shigo,

"My lonely sannu da kokari"

"Yawwa sannu, katashi?"

Rungumeta yayi tabaya yana murmushi, "natashi saboda naji bakya kusa dani"

Tare suka karasa girkin, da daddare yace ta shirya suje gidan mami su gaishesu, ita dai duk kunya take ji saboda tahowar da sukayi itada sawwam suka baro su dad acan,

A kunyace tabishi suka shiga falon dad inda suke zaune itada dad suna kallon labarai a tashar aljazeera, akasa ta zauna tana gaida su mami,

"Dan gidan dady kuma haka akeyi sai ka dauko iyalinka ku taho ku barmu acan?" Dad yafada yana dariya,

"Dad batada lafiyane shiyasa muka taho" sawwam yace da dad yana satar kallon ummulkhair wacce ta sunkuyar da kanta kasa,

"To Allah yabata lafiya yarabata da abinda take dauke dashi lafiya"

Babu kunya taji sawwam ya amsa da "amin dad"

Kafin wani lokaci har Mami ta cika ummulkhair da kayan ciye ciye da na tande tande, shikuma sawwam sai diba yake yanaci Mami kuma sai fada take tana cewa ita bashi fa ta kawowa ba ummulkhair ta kawowa duk da haka bai yarda ba tare dashi aka cinye komai, dad yana kallonsu sai dariya yake yana cewa sawwam,

"Dan gidan dady kai baka koshi ne?"

"Dad nakoshi banbanci naga ana kokarin nuna min shiyasa nadage akaci komai dani"

"Ka karata dai" Mami tace tana dariya, ita dai ummulkhair tana zaune tana jinsu,

Lokacin da suka tashi tafiya har sun fito yaga mami ta biyosu da wani abu a hannunta acikin leda,

Matsawa yayi yana son yaji ko menene, nan mami ta koreshi, gaba yayi yana tuttura baki shi ala dole yayi fushi,

"Ungo wannan ummulkhair ki hada da madara da zuma kisha zai taimaka miki mutuka saboda naga wannan dan rawar kan bazai rinka saurara miki ba gashi kuma cikin jikinki baiyi kwariba shiyasa nasamo miki wannan insha Allah zai taimaka miki har lokacin da cikin zaiyi kwari" mami tafada tana mika mata kullin dake hannunta, karba ummulkhair tayi cikeda kunya amma har cikin ranta tana jin kaunar mami da sonta tamkar na uwar data haifeta saboda mami tana nuna mata soyayya tun kafin suyi aure da sawwam take sonta take kyautata mata har zuwa aurensu,

"To mami nagode"

"Haba haba ummulkhair babu komai Allah dai yabaki lafiya"

Karasawa wurin sawwam sukayi anan mami tasake ja masa kunne akan ya rinka kulawa sosai da ummulkhair sannan yarage wannan rawar kan, dariya kawai yayi aransa yana cewa,

"Wai mami sai tarinka cewa narage rawar kai, ni wallahi bazan iya hakuri ba"

Sallama suka yiwa mami suka tafi, lokacin da sukaje gida sai da ta kira abbanta suka gaisa nan yayita sanya mata albarka yana yimata kyakkyawar addu'a sannan daga karshe ya hadata da mama suka gaisa.

Sai da ummulkhair tayi hutu nasati daya sannan taci gaba da zuwa makaranta,kullum tare suke fita su dawo da sawwam,

Cikinta ya shiga wata na shida yanzu kam ya fito kowa yaganta yasan tana da juna biyu, murnar sawwam kasa boyuwa tayi domin kullum cikin kallon cikin yake yana lissafin haihuwa,tsiya kam ummulkhairi tashata awurin alawiyya lokacin da taga cikinta yafito,

"Wai har sawwam yayi miki me?"

"Abinda kika gani" ummulkhair tabata amsa tana harararta,

"Me idona yagani?" Alawiyya tasake tambayarta tana dariya,

"Ciki" ummulkhair tabata amsa,

"Tab wannan ai kune hadamammun, da yaushe kuka yi auren ma da har za asamu juna biyu?"

"Lissafa kiga, yau watanmu bakwai da aure watanmu shida da tarewa, haka shima cikin watanshi shida"

Dariya alawiyya tayi, "Allah ya kyauta muku aranar da kuka tare aranar kuka samu abunku"

"Amin, dama ai ba kallon juna mukaje yiba"

"Ai nagani, Allah yaraba lafiya"

"Amin" ummulkhair tace tareda mikewa saboda ta hango motar sawwam yana karasowa, tare sukaje wurinshi da alawiyya saboda zasu sauketa agida,

Kallon sawwam ummulkhair tayi bayan sun hau titi, "sahibi kaji abinda alawiyya tace? Wai mu hadamammu ne aranar da muka tare aranar muka samu baby"

Alawiyya ji tayi kamar kasa ta tsage ta shiga ciki dan kunya, sawwam kam murmushi yayi saboda yana jin dan nauyin alawiyyar amma shima yasan hakane idan ma ba aranar bane to dai acikin satinne,

Sai da suka sauke alawiyya sannan ya kalleta yana murmushi,

"Abinfa da kawarki tafada wallahi gaskiyane, may be a first night dinmu muka samu rabo"

Baki ta turo, "ai duk kaine"

"Naji, kuma ina son abina sannan har yanzu ina sake jin sabon son matata"

Murmushi tayi ta kwantar da kanta a kafadarshi tana murmushi.

  Lokacin data kammala exams sawwam hutu ya dauka domin yana son su fita outside shida ummulkhair kasancewar basuje honey moon ba,sallama suka yiwa yan uwa da abokan arziki suka lula kasar Brazil, ummulkhair taji dadin zamansu awannan kasa domin sawwam yabata kulawa ta musamman itada babyn dake jikinta, kullum cikin tattalinta yake babu bata lokaci jikinta yasake gogewa ya murje ta sake zama katuwa ga fari da ta kara,

Satinsu bakwai suka tarkato suka dawo gida domin mami kullum cikin waya take kan cewa su dawo domin cikin khairi yakusa shiga watan haihuwa, dawowarsu da kwana biyar sukaje bauchi suka gaida su mama, sun samu tarba sosai daga wurinsu abba da kowa dake gidan, wuni sukayi sawwam ya dauketa suka koma kano.

Tunda suka dawo babu abinda ummulkhair takeyi,komai sawwam ne keyi, lokacin da edd dinta yakusa cika mami tazo ta tafi da ita gidanta saboda tace bazata barsu daga ita sai sawwam agidan ba gashi dukkaninsu yarane ba gama hankali sukayi ba, ai sawwam kamar zaiyi kuka ganin mami ta dauke masa matarshi, shi dinma tattarawa yayi yabisu gidan mamin ya bude dakinshi nada ya tare,

Lokacin da ya shiga sashen mami samun ummulkhair yayi zaune afalo tana kallo tana shan fruits ita kuma mami tana kan kujera tana lissafa kayan da ta bayar order aka kawo mata,

"Lafiya? Daga ina?" Mami tace dashi,

"Mami nima fa nadawo nan gidan saboda wallahi can yayi min girma ni kadai"

Murmushi Mami tayi taci gaba da lissafinta, shikuma kusa da ummulkhair yaje ya zauna yana kallonta yanda cikinta yayi kato kamar yanzu zata haihu,

Tunda ya dawo gidan baya iya yin bacci kullum haka yake kwana yana juyi, yau kwanansu biyar agidan ganin haka yasashi tafiya dakin da mami tabawa ummulkhair, tana kwance tana bacci yaje kusa da ita ya kwanta,

Har asuba tayi bata san yana cikin dakinba sai da mami ta shigo dakin kasancewar duk farkon dare da karshensa tana zuwa tana dubata,

Mamakine Yakama mami saboda ganin sawwam da tayi acikin dakin,

"Kai sawwam, sawwam tashi katafi dakinka" mami tace dashi tana bubbugashi, afurgece ummulkhair ta juya nan taganshi yana bacci,

Gyara kwanciyarsa yayi yana cewa,

"Dan Allah Mami kibarni wallahi kasa bacci nakeyi idan bata nan"

Juyawa mami tayi ta fita ta rabu dashi, ita dai ummulkhair tagumi tayi tana kallonshi.

49

Koda gari ya waye tashi yayi yana hamma ya shiga toilet yafito yayi salla yana kallon ummulkhair wacce ke zaune gaban mirror tana shiryawa,

"Good morning my lonely" yafada yana kashe mata ido,

"Gaskiya ni karka kara zuwa, haka kawai zaka wani zo dan kasa mami ta zargi ko wani abun muke"

Tashi yayi yaje ya rungumeta ta baya,

"Na nawa kuma, ai mami tagama sanin muna yin wani abu dake tunda gaki nan dauke da katon ciki"

Hannu takai zata dakeshi ya rike hannun tareda kaishi bakinsa yafara kissing dinshi, babu zato Mami ta shiga cikin dakin,

"Sawwam me zan gani haka? Yanzun ma da take dauke da tsohon cikin ba zaka barta ta huta ba"

Saurin matsawa yayi yana murmushi, "mami bafa komai nayi mata ba itace tayi kokarin dukana shine na rike hannun"

"To naji zo ka fita"

Juyawa yayi yafita yana jin mami tana tambayar ummulkhair abinda take son adafa mata,

Tunda kwanakin haihuwar suka gabato sawwam ya daina fita office saboda yafi son khairi ta haihu agabansa yana nan amma haihuwa shiru har edd din ya wuce, fushi yayi ya shirya yayi tafiyarsa office,

Ummulkhair tana daki a kwance saboda tunda ta tashi take nakuda amma taki ta bari mami tagane, karfe 12 narana mami ta fuskanci nakuda take dan haka suka tafi asibiti suna zuwa babu jimawa ummulkhair ta haihu, ta samu baby boy dinta kato kyakkyawa mai kama da babanshi sak,

Tunda ta haihu tajita lafiya lau ta rabu da duk wani ciwo wanda ada yake damunta, wayarta ta dauka takira sawwam,

"Hello, sahibi kazo kaga babynka,tun dazu yana ta son ganin dad dinshi" tace da sawwam bayan taji ya daga wayar,

"My lonely bana son wasa fa" yafada cikin doki,

"Allah dagaske nake ko na mintsineshi yayi kuka kaji"

"No, no dan Allah karki mintsineshi kibari idan nazo ni sai ki mintsinenin"

Da saurinshi yaje ya shiga mota sai asibiti saboda dama yasan asibitin da mami take kaita, lokacin da yaje ya samu nurses sunata gwada mata yanda zata shayar da yaron, tsayawa yayi yana kallonsu kirjinta ko kadan bai canjaba yana nan kamar yadda yake da sai cika da ya sake yi,

Hadasu yayi ita da yaron ya rungume ko kunyar mami baiji ba, ita mami kam yau bakinta yaki rufuwa sai waya take yiwa yan uwa da kawayenta tana sanar dasu matar sawwam ta haihu,

Basu dauki dogon lokaci ba aka sallamesu suka tafi gida, tunda sawwam ya dauki jaririn ya rikeshi bai ajiyeba har sai da Mami tayi masa dagaske ta koreshi daga dakin saboda ganin yan barka har sun fara zuwa ganin jariri,

Koda dare ma yayi haka suka sha fama shi da mami saboda cewa yayi dole shi sai adakin zai kwana, korararshi mami tayi tace bazai kwana anan ba, sai kawai ya dauki jaririn,

"Ina kuma zakaje dashi" mami ta tambayeshi,

"Mami zantafi dakina dashi ne, ga yarki nan nabar miki nima na dauki dana saboda nasan akan tane zaki hanani kwana a dakin"

Abin dariya yabawa mami saboda ganin yanda ya dauki jaririn da net dinshi,

"Kawo shi nan shi dinma babu inda zakaje dashi kai kadai zaka tafi"

Fushi yayi ya bata jaririn ya fita amma bai hakura ba asubar fari sai gashi ya dawo bayan ya dawo daga masallaci,

Kullum yana manne adakin sai dai idan yaga baki sunzo sannan ne zai fita suna tafiya zai dawo da haka har ranar suna ta zagayo,

Saniya da raguna dad ya yanka sannan ya bawa jaririn sabuwar mota kirar kamfanin KIA, ga gida da ya mallaka masa wanda ke unguwar rijiyar zaki, anyi shagalin suna sosai yaro yaci suna Abdulrahman,mai jego ita da jaririnta sunyi kyau sosai tasha swiss les wanda mami ta dinka mata bayaga kunshi da lalle da aka yi mata,

Gidan mami cika yayi dam da al'umma nan manyan mata suka rinka cashewa ana zuba musu naira, har mangaruba tayi mutane basu bajeba, makida da mawaka kuwa ranar sun baje basirarsu, har bayan sallar isha aka kai ana budiri daga bisani kowa ya tafi gidansa cikeda kayan suna.

Tunda akayi suna kuma sawwam yafara damun mami da tambayar yaushe zasu koma gidansu shida khairi, ko kallonsa mami batayi bare ta amsa masa domin ita tabada himma wurin sake sabinta masa khairin sa yanda zai sake riketa da daraja,

Har akayi arba'in yaron yayi wayo mami bata bashi khairi ba wasa wasa har suka yi kwana 60,

Dakin khairi ya shiga ya isketa kwance ta dora andulrahman akan ruwan cikinta,

"My lonely yakamata fa ki tausaya min mukoma gida haka, wallahi zan iya shiga wani hali"

Kallonshi khairi tayi tasaka murmushi,

"Ni babu ruwana kaje ka sami mami ka fada mata"

"Haka kikace? Shikenan"

Juyawa yayi ya fita, tun daga lokacin yake fushi sam yaki dariya koda yaushe fuskarshi ahade,

Da daddare yana falo a zaune yana cin tuwo khairi ta sameshi zata fita zuwa kitchen, waya taji yana yi kasa kasa,

"Sorry ai nace miki ba ason raina bane amma kiyi hakuri zanzo may be gobe inyaso sai mu karasa maganar.."

Shiru taji yayi kafin yaci gaba,

"Ohh God! Ai nabaki hakuri, nawane kudin saloon din? Kibari idan nazo sai nabaki zan ma kaiki da kaina, ok thank you, abdulrahman zaiji,bye bye.."

Katse wayar yayi yaci gaba da cin tuwonshi, yana juyawa kuma sai yaga ummulkhair a tsaye tana kallonsa,

Batace dashi komai ba tawuce kitchen amma hankalinta yagama tashi da wayar da taji yana yi, kishine yafara taso mata saboda gani take kamar sawwam wani sabon auren zai sake yi rumtse idanuwanta tayi tana jin kishinsa har cikin ranta,

Dakin mami tawuce ta sameta akan dadduma tana lazimi, zama tayi har ta idar ta juyo tana tambayarta me take bukata,

Sunkuyar da kanta tayi ta daure tace "mami dan Allah kibarmu gobe mu koma gida, saboda wallahi sawwam yafara neman aure saboda wai naki komawa,ni ko bauchin ma nafasa zuwa idan mun koma daga baya yakaini"

Murmushi mami tayi tace "babu komai Allah ya kaimu goben sai ku tafi"

Tashi tayi tafita amma lokacin sawwam baya nan yatashi, dakinta takoma tafara harhada kayanta dana Abdul,

Washe gari mami ta kira sawwam tace yazo zasu tafi, shan kamshi yafara ya kalli khairi,

"Mami suyi zamansu basai sun koma ba"

Cikeda mamaki ummulkhair ta kalleshi sai kuma tafara kwalla,

"Mami kin gani ko wallahi aure zaiyi.."

"Aure kuma? Babu auren da ya isa yayi, shekarun nasa ma nawa suke da har zaiyi wani sabon auren, kai kana jina wallahi ko bayan raina ban yarda kayiwa wannan yarinyar kishiya ba"

"To" yafada yana hararar khairi,

"Kadai ji nafada maka, ummulkhair tashi ku tafi, Allah ya kiyaye hanya"

Tashi ummulkhair tayi suka fita nan sawwam ya debi kayansu yabi bayansu dashi, baba dan tsoho na ganinshi yafara washe baki yana yi masa kirari,

Murmushi kawai yayi baice komai ba yashiga motar suka tafi, ko acikin motar ma yaki kulata sai iya Abdul yake kallo yana yimasa wasa, har sukaje gida bai kulata ba,

Gidan ta gyara ta tsaftace tayiwa Abdul wanka tasake shiryashi, shikuwa sawwam tunda ya kawosu yafita bata sake ganin idonshi ba, sai da dare yayi bayan tayi wanka ta shirya cikin kayan bacci riga da wando light blue wandon iya cinya rigar kuma iya cibiyarta, tana falo zaune rikeda Abdul sai gashi ya shigo kallo daya yayi mata yaji hankalinsa na neman gushewa yabar jikinsa,

"My lonely bakiyi bacci ba? Taso muje ki kwanta.."

Kanta ta dauke, "sai yanzu zaka yimin magana?"

"Haba my one and only",

"Ni ba one and only dinka bace tunda kana shirin karo wani auren"

Zama yayi kusa da ita, "wallahi ni wacce kikaji muna waya ba budurwa tace ba budurwar suhaib ce sukayi fada akan zuwa saloon shine ta kirani take fada min nikuma nabata hakuri nace zan kaita saloon din kuma zan biya kudin, ki yarda dani wallahi babu wata bayan ke"

Kallonsa tayi anan taga har kwayar idonshi ta sauya, sai da yasake rarrashinta sannan ta tashi tabishi zuwa master room...

Sawwam da khairi suna gudanar da rayuwarsu cikin kaunar juna da hakuri da juna, bayan lokaci yadan shude ummulkhair ta kammala karatunta lokacin Abdul yanada watanni takwas a duniya, alokacin office din su sawwam suka turashi karatu kasar Turkish, cewa yayi bazai iya tafiya shi kadai ba sai da khairinshi da yaronshi dan haka anan suka hau shirye shiryen tafiya, sallama sukaje suka yiwa yan uwa sannan suka daga, to sai muce adawo lafiya.

   Alhamdulillah

Anan muka kawo karshen wannan littafi mai suna ramuwar gayya, Allah ya amfanar damu darasin dake ciki,

Sakon gaisuwa ga masoyanmu masu sonmu, masu son rubutunmu, Allah yabarmu tare muma muna sonku,sai mun hadu daku acikin labari nagaba.

*Kuna ranmu*

Anty maijidda musa
Khadija Sidi
Kdeey
Serdia lawal
Miss Aysher
Halamcy
Maryam kaumi
Hawy
Lilmeerahcute
Xuhura Ajiya
Maryam Ramat
RAZ

Masoyan Nada yawa uncountable......

Fatan alkairi ga members din groups dinmu,

Pherty novels 1&2&3

Duniyar makaranta 1&2




Ummi shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment