Tuesday 28 February 2017

RAMUWAR GAYYA.. 9

*RAMUWAR GAYYA..*💘

_Love story 50,50_

   *_UMMI A'ISHA_*

          _With_

_*PHERTYMERH XARAH*_

  *_9_*

*D*riving yaci gaba dayi zuciyarshi tana hasko masa hoton ummulkhair lokacin da ta mareshi,

"Lallai yarinyar nan.." Yafadi hakan acikin zuciyarsa,

"Wai yanzu ni ta mara? Idan na kyaleta shikenan ta mari banza kenan...? Kai impossible wallahi,dole sai na rama wannan rashin mutumcin da tayi min.." Yafadi yana shafa sumar kanshi,

Da tunaninta ya samu ya isa gida, koda yaje gidan kin shiga wurin Mami yayi yawuce dakinshi saboda baya son taga shatin yan yatsun ummulkhair dake zane akan kuncinsa,

Wuni yayi acikin daki har sai da yamma tayi sannan yafito lokacin shatin dake fuskarsa ya dan goge.

  Ummulkhair hostel ta wuce kai tsaye taje ta bude dakinta ta shiga ta kwanta nan ta fara kuka sosai, ta rasa meyasa sam bata da juriya akan wulakancin sawwam, gashi dai ita kanta fadan nasu ya soma isarta amma bata son ta kyaleshi yayi nasara akanta, tafi son suyi tayi har shi da kansa ya gaji ya sallama mata,

K'arar da wayarta keyi ne ya katse mata kukan nata, babu shiri ta tashi ta dauki wayar bayan ta hadiye kukan da take yi saboda ganin mahaifinta ne me kiran,

Sakin fuskarta tayi suka gaisa tamkar babu abinda ke damuta, sai da ya jaddada mata cewar ta dage tayi abinda ya turota sannan ya hadata da mamanta suka gaisa, kasancewar yayunta duk suna gida lokacin suma sai da suka gaggaisa sannan suka yi sallama,

Hakuri tayi ta daina kukan taci gaba da abinda ke gabanta,koda suka hadu da alawiyya ma bata yarda ta sanar da ita fadansu da sawwam na jiya ba,sannan tun daga lokacin bata sake sakashi acikin idonta ba har tsawon kwana biyu, gashi kullum hijabi take sawa har kasa da nikab ta rufe fuskarta,

Sai dai shi sawwam duk inda ya hangota yana ganeta haka kawai ya rasa dalilin da yasa daga ya ganta zai san itace.

Tafe yake shida abokansa sun nufi filin kwallo wanda ke cikin makarantar, yasha jar riga mai gajeren hannu da wando jeans blue, kasancewar yammaci ne yasa ko ina ka hanga dalibai kake gani kowa yana sha'anin gabanshi, wasu na hira wasu na karatu,

Zaune ya hangota a kan wata kujerar karfe dake girke a kasan wata bishiya, tana sanye da blue din hijabi har kasa da nikab a fuskarta hannunta rikeda lecture note da alama karatu take yi, tabbas ya gane itace sai dai ita Sam bata zaci cewar ya ganeta ba,

"Hello guys, ku bani 2 minutes kuyi gaba zan taho, bari naje neman fad'a..."

Bai jira amsarsu ba juya ya nufi wurinta,kanta yana sunkuye tana duba lecture note dinta ya karasa wurin,

"Mtswwwwww" yaja dogon tsaki yana kallon kafarta,ba karamin kyau kafar tata tayi mishi ba domin faratanta gaba daya sunsha jan kunshi,

Bata ko daga kanta ta kalleshi ba taci gaba da karatunta,

"Ke...! Zuwa nayi na sanar dake kan ki shirya karbar rashin mutuncina ako wanne lokaci domin wallahi kinyi kadan ki mareni na rabu dake, tunda nazo duniya babu wanda ya taba marina sai ke..., to wallahi sai na shuka miki gonar rashin mutunci so get ready" yana kaiwa nan ya juya ya wuce yana fito da bakinshi,

Bayanshi tabi da kallo tayi murmushi, "ko me kake ji dashi to a shirye nake domin nima ina ji dashi" ta fada ahankali.

  Kwana uku da faruwar wannan al'amari ummulkhair suka nufi wurin yin photocopy itada alawiyya, sawwam yana kallonsu kuma duk da cewar ta lullube fuskarta to ya ganeta,

Gaba daya hankalinsu ya tattara kan lissafin adadin lecture notes din da za ayi musu gefe kuma wasu yanmata ne wurin su biyar suma suna jira ayi musu, daya daga cikin yanmatan ne wayarta ta fadi ba tare data sani ba kuma akayi Sa,a babu wanda ya gani, sunkuyawa sawwam yayi ya dauki wayar ya wuce, a kusa da ummulkhair ya tsaya yana yiwa mai shagon magana, sam bata luraba ya jefa mata wannan wayar acikin jakarta,

Juyawa yayi ya koma gefe can nesa ya jingina ya tsaya yana kallonsu, yana kallo wannan budurwar ta fara neman wayarta amma bata samu ba nan aka soma dube dube, wata wayar ta karba ta kira layinta take wayar ta dau kara daga cikin jakar ummulkhair wacce sam ita bata ma san abinda yake faruwa ba,

Kanta yanmatan suka iyo, "sannu barauniya daga zuwa shine zaki dauke mana waya? To Allah ya toni asirinki..."

Wata daga cikin yanmatan tafada, cikin rashin fahimta ummulkhair ta jiyo tana kallonta,

"Meya faru?" Alawiyya ta tambaya,

"Wayarmu ta sace gata nan tana kara acikin jakarta..." Kafin alawiyya ta sake magana har sun fusge jakar sun ciro wayar, daga alawiyya har ummulkhair kasa magana suka yi nan yanmatan suka hau zagin ummulkhair suka yi mata tatas mutane na tsaye suna kallonsu,

Jakarta ta dauka tana hawaye ta nufi hanyar barin wurin,

"Hy barauniya, ashe dama ke barauniya ce?? Even though kin saba satar kayan mutane...."

Taji magana daga bayanta tana juyawa taga sawwam ne yana yi mata murmushi...

Ummi Shatu
Pherty..

RAMUWAR GAYYA..8

*RAMUWAR GAYYA....*💘

_love story 50,50_

_Fertymerh Xarah_

              &

_Ummy Aysher_

*_8_*

    Kallon ta yake qasa qasa cikin yin observation masu yawa akanta, tana sanye da baqin hijab har qasa, ga wannan baqin abu tasanya a fuska, yanayin tafiyarta kaďai xaisa ya gane ta a duk inda ta shiga....

Ya dubi ďaya daga cikin abokansa cikin murmushi,

'Abdul dubi mutuniyar, ta canxa kamanni ko meyasa?

'saboda kai ne abokina, taji tsoro..... Suka kwashe da dariya harda tafawa dai dai lokacin ta xo ta gabansu, inda suke ma bata kalla ba kuma xuciyarta na bugawa dan tasan sarai ya gane ta tun daga lokacin da taga suna kallonta suna magana, Gashi ynxu sun yi mata dariyar dake qona mata rai....

Sawwam ya diro daga Saman Mota ya sha gabanta yana fadin,

'Dan Allah sister kije hostel ki taimaka ki kiramin budurwata...

Bata tanka ba illah qoqarin kauce masa da takeyi, ta gane yana son raina mata hankali Kamar bai gane taba, ya dubi su Abdul cikin ďaga murya ya soma mgn,

'Abokina taqi responding kodai yar shi'a ce?

'Ga alama ka gani a jikinta baqin hijab baqin niqab, in kuma tayi gardama abokina ta buďe har ciki mugani idan ba baqaqen kaya ne a jikinta ba....

'eh hakane kuma.. Sawwam ya faďa haďe da maido kallonsa gareta,

Xuciyarta tamkar ta faďo saboda baqin ciki ita suke dangantawa da shi'a Sannan har wai ta buďa masu jikinta Su gani, cikin bacin rai ta fisge niqab ďinta haďe da nuna sa da yatsa....

Ya xare ido haďe da bude bakinsa cikin tsananin mamaki ya juya yana kallon abokansa haďe da kashe masu ido ďaya,

Abdul ya tako yana faďin,
'abokina ashe itace, taji tsoro,

Mtsewwwwww taja dogon tsaki haďe da janye hannunta, ta juya batare da tayi mgn ba ta fice hakan ya Sanya sawwam riqo hijabinta,

Abinda yayi matuqar bata mamaki da ďaure mata kai, ko suna mata kallon yar iska ne? idanun mutane akansu, ta juyo a fusace haďe da kai masa Mari a fuska kafin ta sauke hannunta ji kake tas.. tas.. ya ďauke ta da lafiyayyun Mari har guda biyu tayi baya kamar xata faďi sai da taga shuďewar wasu mintoci kafin ganinta ya dawo dai dai, nan da nan hawaye na soma ambaliya a fuskarta,

Yana tsaye yana huci kamar wani namijin xaki, a yanda yakeji komai xai iya faruwa a Wannan lokacin tunda yake a rayuwa baa taba Marin sa ba, Waďanda suka haifesa ma basu taba gwada hakan ba, abokansa mutuwar tsaye sukayi yayin da kallon mutane na dawo garesu maxa da mata,

Ta sunkuya ta đauki niqab ďinta dake qasa, har lokacin bata daina hawaye ba, suna haďa ido bakinta yayi motsi ga bacin rai kwance akan fuskarta,

'Ban yafe ba, mugu axxalumi Allah xai sakamin, ta juya da sauri cikin yanayin tsoro tayi hanyar hostel,

Daga yanayin yanda take magana xaka karanci bitterness wato ďacin da Mgnr tayi mata Akan harshen ta, mgnr taso ta sanyashi dariya duk da yana cikin bacin rai...

'3 pointer wannan yarinyar mu barta kawai Kada ta janyo mana raini wataran a skul ďinnan girman mu xai faďi...

Idan mun barta kenan munji tsoronta, yamin dai dai da ya Rama Marin, amma baabaa Marin fa ya shige ka da alama cos ga yatsunta biyu nan a kuncinka, sawwam ya shafi fuskarsa Idanunsa jawur yama xaije da wannan fuskar gida haka, idan an tambayesa shikenan sai yace mace ta mare sa kome? ai *Girma ya faďi (takori)*, ya dube su,

'Son ta nake yi, if not because of the love sai na nuna mata ko waye sawwam a skul ďin nan, ban San Ina son ta ba sai ynxu dana kasa aiwatar da mummunan abu akan ta, xn iya raping ďin ta ba ruwana....

'So fa kace sawwam....
'of course ya faďa Kuma duk shegen dana ganta dashi a skul ďinnan sai ya raina kansa itama xn hana mata sukuni a skul ďinnan,

'Abdul yace ni har xnce Ayi inviting ďinta ta shigo cikin mu muxama 4-pointers...

'Nooooooo ya girgixa kansa,

Sai safa da marwa yake yi gurin, xuciyarsa a dagule take, suna gurin wasu mata biyu sun fito daga hostel sukaji suna faďin,

'Kinsan abu a skul nan da nan kowa xaiji amma ni naji daďin da ta maresa Ummi, yaron ya fiye girman Kai da izza, wadda aka Kira da Ummi ta juya tana kallon dayar

'Amma ance shima ya rama fa Pherty, ai wannan *ramuwar gayya* ce tunda har biyu yayi mata, ni naso naga wannan yarinyar tayi matuqar birgeni,

'nima ta birgeni xnje in nemeta a hostel mu qulla qawance,

Sawwam ya rude kenan Mgnr ta biye ko ina mace ta maresa har ta birge mutane, ai Kuwa baxai barta ba, ya rasa dame xai jefi matan can biyu da suka wuce suna tsegumi sai ya ciro ďayan takalmin sa ya jefa masu sai akan keyar Ummi suka juyo da mamaki ganin ko Waye, ai Kuwa suna ganinsa suka falla da gudu....

A harxuqe ya shiga motarsa bai bi takan abokansa ba ya fita daga Skul ďin,

Driving yake kamar Wanda xai tashi sama, kwayar idanunta yake gani cike da hawaye da yanda bakinta yayi motsi a Wannan lokacin har xuwa Marin da tayi masa..... yayi firgigit kamar da gaske ďin Marin sa tayi abin Marin ya tsaya masa sosai a rai....

_Ban yafe ba, mugu axxalumi Allah xai sakamin._

Pherty...
     &
Shatu....

RAMUWAR GAYYA.. 7

*RAMUWAR GAYYA..*💘

  _Love story 50,50_

  *_UMMI A'ISHA_*

          _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*

   *_7_*

*A*fusace ya juya yabi bayansu yana huci zuciyarsa na tafarfasa abinka da dogo taku kad'an yayi ya cimmusu,

Hijabinta ya fizgo afusace take hijabin ya yage daga wuya,

"Ke wai ke wacece? Me kike takama dashi da har zaki rinka shiga gonata..."

Abokanshi ne suka katseshi ta hanyar janyeshi daga wurin suna bashi hakuri,

"Haba 3 pointer kar ka biye mata mana, ai kai namiji ne me zai saka fada da mace, ai ba afada da mace..."

Har lokacin ummulkhair da alawiyya suna tsaye awurin hakama mutane duk sun jujjuyo suna kallonsu amma ko uffan ummulkhair bata ce ba in banda binsu sawwam da kallo babu abinda take gashi gabanta sai faman faduwa yake domin ba karamin tsorata da yanayinshi tayi ba ayanda fuskarshi ta nuna to yana iya dukanta a wannan lokacin sai dai Allah ya rufa mata asiri an ceceta bai samu damar dukanta ba,

Jan hannunta alawiyya tayi suka bar wurin domin har mutane sun fara cece kuce kowa yana fadin albarkacin bakinsa,

Wuyan hijabinta taja ta gyara domin duk yanzu yayi mata yawa sakamakon yagashin da sawwam yayi,

"Yanzu kin dai ga irin abinda naketa fada miki amma kika yi biris dani kika ki daukar shawarata,

Tun ba aje ko inaba kinga kin fara ganin abinda na jima ina guje miki, yanzu me amfanin haka agaban mutane ya yaga miki hijab dinki, kuma wallahi ma Allah ne yasoki da rahama da bai mammareki ba domin ya zuciya.."

Murmushi ummulkhair tayi,

"Ni kaina na tsorata dashi wallahi dan daga ganinsa kin san zaiyi zuciya sai dai fa amma naji dadi da ranshi ya baci dama ni burina shine yaji haushi sannan yaji kunya, to duk gashi hakan ta faru at the same time...."

"To nidai shawarata agareki akaro na karshe shine ki fita daga hanyarshi domin nasan shima ba hakura zaiyi da abinda kika yi masa ba, so idan ya rama ki rabu dashi shikenan kunyi 50,50.."

Sake murmushi ummulkhair tayi "insha Allah daga wannan karon zan rabu dashi bazan sake kulashi ba duk da nasan sai ya dau fansa akan abinda nayi masa.."

"Yawwa naji dadin wannan maganar taki, dan Allah kiyi kokarin kai zuciyarki nesa.."

"Insha Allah, bari naje hostel na canja hijab dinnan.."

Sakin hannun alawiyya tayi ta wuce zuwa hostel ta cire hijab dinta ta saka wani ta koma wurin alawiyya.

  Sawwam ba karamin haushin abinda ummulkhair tayi masa yaji ba gashi abokanshi sai faman tsokanarshi suke,

"Three pointer gashi nan a bayanka wooooohhhh"

Tun abin yana bashi takaici har ya dawo yana dariya, wuni suka yi acikin school din sai yamma sannan ya fita zuwa gida,

Yana shiga falon Mami ya isketa itada mahaifinshi akan dining table sai lokacin suke cin abincin rana,

Idonshi ya daga ya kalli agogon bangon dake sakale acikin falon, karfe 5 har da yan mintoci agogon ya nuna,

"Mami sai yanzu kuke cin abincin rana..?"

Karasawa yayi yaja kujera ya zauna akusa da dad dinshi,

"Dad barka da yamma"

Kallonshi mahaifin nashi yayi yana murmushi, farin ciki tsantsa bayyane akan fuskarsa gamida walwala domin yana mutukar kaunar tilon dan nashi,

"Sawwam barka dai, ya karatun?"

Sai da ya dan yamutsa fuskarshi sannan yace "alhamdulillah dad but akwai wahala gaskiya especially ma wannan semester din.."

Sai da dad din ya tura masa filet din abincin da yake ci gabanshi domin suci tare kasancewar koda wanne lokaci indai yana gida to tare suke cin abinci,

"Ai haka abin yake sawwam shi karatu aduk lokacin da yazo karshe to yafi bada wahala shiyasa kaji bahaushe yace idan aski yazo gaban goshi to yafi zafi.."

Spoon sawwam ya dauka yasa acikin abincin dad din ya fara diba yana ci yana murmushi,

"Dad to idan na kammala karatuna successfully wanne albishir zaka yimin..?"

"Sawwam kenan ai a wannan lokacin zan siyo maka new brand car, sannan zan baka makuden kudi domin kayi dukkan abinda kake son yi kaje duk kasar da kakeso, sannan ina nan ina yi maka ginin gidan da zaka zauna kai da matarka amma bazan kaika gidan ba har sai an kammala because inaso ne na baka mamaki..., and kafin wannan yanzu na biya mana umara dani dakai daga yanzu zuwa kowanne lokaci visa dinmu tana iya fitowa.."

"Woowww, thank you dad"

Sawwam yafada yana murmushin jin dadi,

"Nidai Alhaji aduk maganganunka babu abinda ya kayatar dani kamar maganar aurenshi da kayi,

Narasa me yake damun yaron nan har yau ya kasa fitar da matar aure shi ko budurwa ma ina jin bai taba yiba.."

Murmushi dad yayi yana kallon sawwam "dan gidan daddy ko tsoron yanmatan kake yine??" Dad ya fada cikin barkwanci,

Ajiye spoon din hannunshi yayi yafara shafa keyarsa yana sunkuyar da kai,

"Dad ba haka bane ni wallahi ban taba yin budurwa bane,kuma har yanzu banga wacce tayi min ba.."

"Amma tun yaushe nake kawo maka yanmata gidan nan akan ka duba ko zaku fahimci juna amma kaki, idan lissafawa za ayi yan matan da suka zo gidan nan sunfi su talatin.." Inji mom,

"To ya dai isa haka, idan anyi hakuri ai shi da kanshi watarana zai kawo mana wacce tayi masa ko sawwam?"

"Yes dad" sawwam yafada yana murmushi,

"Kai dama goyon bayansa ai nasan zakayi saboda baka son laifinsa"

Tashi mom tayi ta bar musu wurin ta koma cikin falo domin ita tana son sawwam yayi aure da wuri basai ya zauna dogon boko ba ita tafi son yayi aure a yan shekarun nan domin yanzu shekarunsa 27.

  Tun daga wannan rana sawwam bai sake ganin ummulkhairi ba duk da cewar kullum yana zuwa makarantar,

Yau kwananshi uku rabonshi da ita, acikin kwana na hudune suna zaune karkashin bishiya shida friends dinshi shikuma yana saman motarshi a zaune,

Wata yagani ta fito daga hostel tana sanye da hijab har kasa ta rufe fuskarta da bakin nikab, kallo daya yayi mata yaganeta duk da shi bai cika kallon mata ba musamman ma idan mace ta saka wannan abin a fuskarta, hakan ya bashi dariya dole sai da ya dan murmusa,

Ita dinma tun daga nesa take kallonshi yasha kananan kaya Riga t shirt milk colour mai dogon hannu da bakin jeans kamar koda yaushe fuskarsa saye cikin bakin glass...

Phertymah 1

Thursday 9 February 2017

RAMUWAR GAYYA.. 6

*RAMUWAR GAYYA...*💘

_love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

            &

*Ummy Aysher*

*6*

  Fuskarsa da murmushi ya shiga kasancewar yau cikin nishaďi yake jin kansa, ita kanta Mami ta fahimci haka lokacin da ya xauna kusa da ita yana qarewa yarinyar dake mata tausa kallo,

Hakan Kuwa ya Sanya Mami jin daďi a zatonta xaice yarinyar tayi masa ne,

Yau da alama kana cikin farin ciki sawwam ko miye dalili? Yayi murmushi a Karo na biyu,

'ba komai, ina cikin farin ciki ne Mami, yau me xn samu a gidan, ya ďan yatsina fuska...

'your favorite nasa Rukayya ta girka ma,

'Wacece Rukayya? Ya tambaya fuskarsa a yatsine,

Rukayya yar gidan hajiya luba, nan da nan ya sauya fuskarsa haďe da maida madubinsa a idanuwansa,

Rukayya na xaune idanunta a kansa sosai ya tafi da imaninta yayi matuqar yi mata kwarjini, batare da ya tanka ba ya fice

Mami ta lura da yanayinsa bataji daďi ba, toilet ya nufa shower ya sakarwa kansa Idanunsa a lumshe, surarta yake gani a idanuwansa, baisan meyasa yarinyar ta tsaya masa a rai ba,

Ya gama shirinsa kenan sai ga Mami ta shigo fuskarta ba walwala,

Na rasa gane me kake nufi sawwam, Kada ka Bari fushina ya sauka akan ka,

Da akayi me Mami? Ya tambaya Idanunsa akanta cikin rashin fahimta,

Yarinyar dake xaune a falo, kada kace bakasan saboda kai ta xo ba,

'Saboda ni ta xo, banfa Santa ba Mami...

'ai nasan Baka Santa ba shiyasa nace taxo dan ku fahimci juna itace matar dana xaba ma ka aura ai kaganta kyakkyawa ce, ya ware Idanunsa sosai Akanta cikin mamaki,

'Mami nifa namiji ne idan ita xa'a xaba mata mijin aure ni baxaa xaba min macen aure ba, gsky ni batamin ba ta fiye kallo da yawa, ko aurenta nayi haka xata xauna tayi ta kallon abokaina a falo, ni bana son ta Mami,

'kada ka raina min wayo, da yaushe da yaushe take kallon ka Bari mahaifinka yaxo xan sanardashi, ai dole ta Kalle ka taga mijin da xata aura, ya soma kallon jikinsa ta madubi...

'Mami ko makauniya tasan nayi, Kedai kibarta bana sonta, idan dole sai nayi aure ki canxa min da wata ko ki Bari na xabi wacce nakeso da kaina...

'Tace kana nufin duk matan dana ke kawo ma ba wacce tayi ma? Ya gyada kansa, ta girgixa kanta kawai ta juya ta fice....

2 days~~

Sawwam tun daga ranar bai qara ganin ummulkhairi ba, baisan dalilin daya sa ya damu daya ganta ba,

Akwai lokacin da xuciyarsa ta takurasa da tunaninta shi kaďai a ďaki, idan ya rumtse ido surarta yake gani da kururuwarta a kunnensa lokacin da taji tsoro, meyiwuwa tayi fushine dashi, sai me ya furta da qarfi bayan ya xira hannayensa cikin sumar kanshi dake cike kamar xaka kitse ta saboda cika da tsawo,

At school.....

Yana Saman motarsa tare da abokansa, Idanunsa boye cikin baqin glass duk matan dake wucewa Idanunsa akansu, Alawiyya yakeson gani ya tambayeta khairi...

Mtseww wai me ke damuna ne ya faďa bayan ya cire glass ďin idonsa, ya diro daga Saman motarsa ,guys muje muci abinci....

Ummulkhairi da Alawiyya tsaye lokacin da taga su sawwam sun nufi gurin cin abinci,

'Gashi can xaije kixo muje dan Allah,

'khairi na xata kin bar mgnr nan ne tun bayan kwana biyu da suka wuce, kinga shima ya kyaleki kema ki barshi kiyi abinda ke gabanki,

'Wlhy baxan barshi ba, idan na barshi yaci bulus kenan Ina tsoronsa,

'karki manta Kefa Macece....

'Mtseww kixo muje dan Allah,

Sun rigashi isa gurin saboda yanayin tafiyarsa ta izza, tuni ta dade da haďa masa plan rana kawai take jira Kuma gata,

Tana xuwa tayiwa Mai abincin mgn kafin ta sami guri ta xauna itakam Alawiyya jikinta sai kyarma yake bataso abu yana hadata da 3pointer saboda rashin mutuncinsa,

Suna xaune ya shigo, mutane suka soma tashi xasu bar gurin sanin halinsa,

Da hannu ya tsaidasu haďe da masu nuni da su xauna Su cigaba da cin abincin su, suka sami guri suka xauna ko kaďan baiga su khairi ba,

Suna kallo aka wuce da abincinsa kamar yanda ta umurta,

Ya cire glass ďinsa, with full confidence ba tunanin komai ya buďe plate ďin dake rufe, budewar keda wuya frog ya fira sai a fuskarsa, cike da tsoro ya saki ihu bayan ya tashi tsaye, frog ďin ya faďi qasa, mutanen dake gurin suka đauki dariya bama kamar abokansa da har kasa suka Kai gun dariya,

'wannan plan ne aka haďa mashi, tor amma Waye? Gashi har ya jimasa ciwo a fuska, ya juya a fusace ya nufi inda Mai abinci anan Idanunsa sukayi toxali da ummulkhairi, suna haďa ido ta ďauki wata irin dariya taja hannun Alawiya ta gabansa suka wuce tana fadin,

'qawata ashe haka kike da tsoro, na ďauka ba abinda xai tsorataki anan duniya, sai gashi qaramin kwaro yasanya kinyi ihun dana firgita mutane ya janyo hankalinsu akanki, gwanda ni Macece ansan mata da tsoron qadangare, maza fa? Cikin dauriya Alawiyya tace

'qawata ba kowane namijine matsoraci ba, kinsan wani Iskanci a baki ne kawai, maxan ma suna suka tara wani abun kamar mace.... Suka sa kai suka fice suna dariya harda tafa hannaye,

Shi da abokansa kallonsu suke hr suka fice, bacin rai ne kwance a fuskarsa kallo ďaya xaka masa ka fahimci haka, ya juya yana kallon mutanen dake gurin shi ake kallo aga wane action xai ďauka, Ransa a bace ya juya yabi bayansu....

Phertymerh1

Ummy Aysher

RAMUWAR GAYYA.. 5

*RAMUWAR GAYYA...*💘

_Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

        _With_

_*PHERYMER XARAH*_

  *_5_*

*B*atare data sake magana ba ta dauki kayanta ta fice daga cikin hall din ta nufi hanyar hostel,

Sawwam ta gani atsaye ajikin wata bishiyar dogon yaro shida wasu dalibai sai faman murmusawa yake yi,

Bata sake duban inda yake ba ta wuce amma sai taji ya biyota yana mata magana,

"Dama na fada miki indai kikace zaki yi sa'insa da ni to wallahi ina mutukar tausaya miki saboda wuya zaki sha, ni dinnan da kika ganni bani da mutunci muddin aka shiga gonata, ko babu komai nasan yau kin fara gane halina da kuma ko ni waye,

Shawara daya Zan baki shine ki fita daga hanyata domin duk wanda ya taboni wallahi ya tabo gidan rina..."

Gabanta yasha dan haka babu shiri taja ta tsaya, glass din fuskarshi ya zare yana murmushi,

"Ke kadai ce macen da ta taba kokarin raina mini hankali duk cikin makarantar nan dan haka ina gargadinki and this is the last waning da zan baki karki sake garajen shiga hanyata, idan kunne yaji..."

Murmushi ya sake yi ya juya ya mayar da glass dinshi fuskarshi yayi tafiyarshi, juyawa tayi tabi bayanshi da kallo,

Ringing din da wayarta keyi ne ya dawo da ita cikin nutsuwarta, cikin gaggawa ta daga wayar saboda ganin sunan mahaifinta ajikin screen din wayar,

Gaisawa suka yi ya sake gargadinta akan ta dage ta aiwatar da abinda ya turata banda wasa, sun dan jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama ta katse wayar ta tunkari hostel.

Tana shiga dakinta ta cire hijabinta tana karkadewa domin gani take kamar har yanzu kadangaren yana jiki gashi sai ta rinka jin kamar tafiyar kadangaren a jikinta,

Alawiyya ce ta biyota tana zaune sai gata ta shigo,

"Wai ummulkhair meyasa kike da taurin kaine..?"

"Da nayi me fa?" Ummulkhair ta tambayeta tana kallon fuskarta,

"Dama sai da na fada miki ki rabu da wannan gayen ba abokin fadan ki bane amma kika ki yarda to gashi yanzu kin gani tun ba aje ko inaba kin fara kwasar kashinki a hannu, nidai shawarar da zan baki itace tunda kin jarraba kinga ba zaki ci riba ba to ki sallama masa ki rabu dashi, ko me zai ce miki ki kyaleshi ki tura masa aniyarsa saboda idan fadan nan naku yaci gaba da faruwa to wallahi komai yana iya faruw..."

Ummulkhair ce tayi saurin katseta gamida mikewa tsaye hawaye na malala daga idanuwanta,

"Haba alawiyya, yanzu ni kika dorawa laifi? Shin bakiga abinda shi yayi min ba? Haba alawiyya ta yaya zaki tsammaci hakuri daga gareni,

Tayaya zaki zaci rashin mayar da martani daga gareni? Wallahi bazan kyaleshi ba sai dai idan shi ya gaji ya kyaleni, fada dani dashi yanzu muka fara so ki barmu muci gaba dayi har muzo gab'ar da marar juriya zai hakura ya sallamawa dan uwanshi.."

"Haba ummulkhair yanzu ashe bazan fada miki kiji ba? Karfa ki manta duk abinda yaje yazo daga karshe kece zaki ji kunya domin kece mace shi namiji ne kin san kuwa duk abinda namiji yayi shi ado ne agareshi.."

"Banda wannan karon, a wannan karon bazai taba zama ado agareshi ba..."

Ummulkhair ta mayarwa da alawiyya amsa har lokacin hawaye yana fita daga idanuwanta,

"Ummulkhair kiyi hakuri ki kyale yaron nan saboda a makarantar nan kowa sonshi yake, mutane da yawa suna girmama shi saboda kokarinshi wasu kuma suna girmama shi saboda tsabar kwarjininshi ke ko ma badan haka ba ana girmama shi saboda kyawunshi.."

"Ahakan? Mtswwwww" ummulkhair tace tareda jan wani dogon tsaki,

"Ke dama nasan tsananin gabar dake tsakaninku ba zata taba barinki kiga wadannan abubuwan da na lissafa miki ba amma ke kanki kin san yayi babu karya, ke dinma ina kyautata zaton soyayyar sa ce acikin zuciyarki shiyasa kiketa wannan..."

"Ubangiji Allah ya rufa asiri, wallahi babu abinda zanyi da wannan gajarabul din yaron.."

Dariya alawiyya ta fashe da ita wacce bata shirya ba,

"Duk abunki dai sawwam yafi karfin a kirashi da gaja, ko hasadun iza hasadi bazai kusheshi ba, kedai yanzu na gane tsakaninki dashi, sai anjima"

Jakarta ta saba ta fice tabar ummulkhair tsaye sororo tana kallonta.

  Yau cike da farin ciki sawwam yaja motarsa zuwa gida, tuki yake yana bin wakar da ya kunna ta larabci,

Horn yayi baba dan tsoho yazo ya bude masa,

"Barka da dawowa magaji..."

"Baba dan tsoho nace maka dan Allah ka daina kirana da sunan nan, wallahi gaba daya sunan nan baiyi min ba"

"Sawwam ai magajin da kaji ina ce maka saboda kaine magajin Alhaji, ehh kaine magajin masu gida..."

Murmushi sawwam yayi ya fito daga cikin motarsa bayan ya ajiyeta a muhallinta,

"To baba nidai kaci gaba da kirana da sawwam din abar magajin nan.."

"To, to, to uban gidana ai duk yanda kace haka za ayi.."

Naira Dubu daya sawwam ya ciro ya mika masa yawuce cikin gida cikeda farin cikin abinda yayiwa ummulkhair,

Yana shiga falo ya iske mami zaune gefenta kuma wata farar budurwa ce take mammatsa mata kafafunta,

"Mami mai yanmata yau kuma ko wa aka samo?" Ya fadi hakan acikin ransa saboda yasan duk yadda akayi shi aka kawowa yagani ko Allah zai sa ya kyasa....

Ummi Shatu

RAMUWAR GAYYA..4

*RAMUWAR GAYYA...💘*

_Love story 50,50_

*FERTYMERH XARAH*

            _with_

*_UMMI A'ISHA_*

4

*W*ani irin malalacin murmushi ya saki marar fitar da sauti, ya shafi sumar kansa haďe da lumshe idanuwansa cikin farin ciki,

Baba ďan tsoho ya dubesa,

'ya akayi ne sawwam meyasa kake tambaya?

Ya tashi yana faďin ba komai, aikin gida ne aka bamu a makaranta, kafin baba tsoho yayi mgn tuni ya fice cikin jin daďi,

San da ya koma cikin gidan ya sami har lokacin yan matan suna xaune a falo suna kallo, yaja qaramin tsaki...

Waďannan ko mayu ne yakamata su bar mana gida, yasa kai yayi shigewarsa ďakinsa batare da ya qara kallonsu ba....

_At hostel...._

Ummukhairi xaune da tulin takardu a hannunta tana dubawa, dogon tsaki taja xuciyarta a cunkushe hr lokacin tana cikin bacin rai,

Alawiyya ta juyo tana kallonta bayan ta xubo indomie a plate ta nufeta,

'ke ummu Wlhy ki Kama kanki, Kada Kice xaki sanyawa xuciyarki taurin kai sawwam ba irin maxan da kike tunani bane, kowa anan Skul tsoronsa yake....

'Mtseww idan kowa na tsoronsa ni bana tsoronsa, maganinsa xanyi..

'Tace kiyi maganinsa kada ki tsaya kiyi karatu Abinda iyayenki suka turo ki kenan,

Tayi shiru data tuna alqawarinta da mahaifinta, bata qara mgn ba ta janye takardun gabanta ta matso suna cin indomie.

Washe gari bayan sun gama shirinsu suka nufi cikin Skul,

Tun a bakin gate suka tsinkayo sawwam da mutanensa suna tsaye shi yana kan mota Idanunsa sanye da baqin glass ta ciki ya xuba mata idanuwa yana kallonta sosai,

Alawiyya tace dan Allah khairi karki kulasu kibarsu kiyi sha'anin gabanki, kinga da alama fitina suke nema ke mace ce bai kamata ki biye masu ba,

Shikenan ta faďa a hankali ta ďauke kanta gefe batare da ta kalli inda suke xaune ba,

A hankali sawwam ya diro kan motarsa haďe da xare glass ďin idonsa yana kallonta da guntun murmushi alamar dani kike xancen...

Suna xuwa dab dasu suka kece da wata mahaukaciyar dariya suna nuna su da yatsa hakan yasa khairi ta soma kallon jikinta taga me suke ma dariya bata gane komai ba, Alawiyya Kuma tuni ta San halinsu shiyasa bata damu ba,

Ganin yanda khairi ke kallon jikinta duk ta tsargu yasanyasu kwashewa da wata dariya harda riqe ciki, banda sawwam Dake tsaye fuskarsa ba walwala yana kallonsu yaji daďin wannan wulaqancin da suka mata Dan tuni hankalin mutane ya dawo kansu....

Alawiyya taja hannunta tana fadin nace karki kulasu, Bafa Abinda suke ma dariya dan kawai kiji haushi ne....

Sosai taji haushi ta juya tana kallon sawwam, tsaki taja tana masa kallon cike da tsana kafin ta wuce...

A class suna xaune in group suna solving wani assignment da xasuyi submitting bada jimawa ba,

Su da yawa ne a hall ďin sai dai kowa da grup ďinsa kamar yanda lecturer ďin yayi dividing ďinsu,

Bata San yanda akayi ba sai jin tayi kamar abu na tafiya Saman hijab ďinta, dubawar da xatayi taga wani shirgegen qadangare qaton gaske kansa jawur, sauran matan dake gurin suka lura suka soma ihu suna watsewa,

ita kanta a tsorace take idanunta sun firfito ta saki qara sosai haďe da cire hijab ďin jikinta ta qanqame guri ďaya,

Hankalin mutanen dake hall ďin ya dawo kanta, harda hawayenta,

Tana sanye da Doguwar riga blue shape ďinta sosai ya fito sawwam na tsaye yana kallonta,

Alawiyya taje da sauri ta rufa mata hijab ďin, ta qanqameta tana kuka sosai,

Sawwam da mutanensa suka đauki dariya a hankali taji yana faďin _"ramuwar gayya,_ inbanda abinki yarinya wake shiga hurumina ya xauna lfy....."

Shiru ummulkhair tayi tana kallonsa hawaye sai faman kwaranya suke yi acikin idonta gashi har lokacin jikinta in banda rawa babu abinda yake yi tamkar mazari,

Duk da halin da take ciki hakan bai hanata yi masa murmushin mugunta ba wato in kasan wata to baka san wata ba,

Mazan ajinsu ne suka taru suka dauki hijabin nata suka zazzageshi suka cire kadangaren suka fitar dashi, nan ta karba ta saka har lokacin a tsorace take, tana ganin sawwam ya dago mata hannu alamun bye bye sannan ya saka bakin glass dinsa ya juya yabar wurin fuskarsa dauke da murmushi,

Tattare littattafanta ta fara yi tana yi tana share hawayen fuskarta domin ba karamin kunya yau taji ba saboda idan akwai abinda tafi tsana a rayuwarta to shine namiji ya ganta babu hijab a jikinta amma yau gashi wannan sakaran gayen yasa maza masu yawa sun ga kirar jikinta ba tareda lullub'i ba........

Ummi Shatu....

My wattpad Phertymerh1

RAMUWAR GAYYA.. 3

*RAMUWAR GAYYA...*💘

_Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

        _With_

_*PHERTYMAH XARAH*_

  *_3_*

    *H*annun ummulkhairi alawiyya ta kama suka fara kokarin barin admin block suka nufo cikin makaranta,

"To yanzu ina za muje?" Ummulkhairi tace da alawiyya,

"Muje kawai mu samu wuri mu zauna mu huta kafin lokacin shiga lecture yayi"

"Ok to muje"

Tafe suke suna hira cikeda annashuwa har suka je karkashin wata bishiyar mangoro wacce aka girka wata bakar doguwar kujerar karfe a wurin domin hutawa, zama suka yi bisa kujerar alawiyya ta fara koyawa ummulkhair abubuwan da aka danyi lokacin da bata nan, sun shafe fiye da mintuna goma sha biyar awurin suna tattaunawa sai ga wannan gayen na dazu shida wasu mutum biyu har shi na uku,

"Ke baki san nan wurin wajen da nake zama bane?? Dalla malamai ku tashi ku bawa mutane wuri.."

Ko kallonshi ummulkhair bata yi ba taci gaba da latsa wayar dake rike a hannunta,

"Ke tun ranar da nafara ganinki na lura kema fa yar rainin wayoce, agidanku ba akoya miki bawa babba girmansa bane?"

Nan dinma shiru tayi kuma da alama bata da niyyar tanka mishi kamar yadda ya zata,alawiyya ce ta fara harhada littattafanta tana sakawa acikin jaka,

"Ummulkhair tashi mu tafi"

Sai a lokacin ummulkhair din tayi magana,

"Ina zamu tafi? Shi har ya isa yazo ya tashe mu daga nan? Babu inda za muje har sai lokacin da muka yi niyya yayi sai dai idan shine zai yita tsayuwar jiranmu.."

"K'arya kike yarinya ke baki isa na tsaya ina jiranki ba God forbid"

Murmushi ummulkhair tayi "ehh ai da yake kujerar daga gidanku ka daukota ka kawo nan shiyasa zaka hana kowa zama awurin sai kai",

"Ummulkhair dan Allah ki rabu dasu kizo mu tafi"

Alawiyya tace da ita bayan ta kama hannunta tana kokarin mikar da ita tsaye,

"Ke wallahi idan baki bar wurin nan sai kinyi nadamar yin haka.." Yafada yana huci,

"Idan har ni banyi nadama ba to kuwa kai zaka yi nadama, nonsense kawai.." Ummulkhair ta fada cikeda jin haushi domin ita haushi yake bata,

"Ke ni kika cewa nonsense? Ni kika zaga? Ke har kin isa ki zageni?" Ya fada cikin daga murya tareda zabura yayi kanta zai daketa,cikin zafin nama abokanshi suka rikeshi suna bashi hakuri,

"Dan Allah ku sakeni na koya mata hankali.."

"Ku sakeshi dan Allah in yaso naga abinda zai yimin, kai ka isa ka dakeni ka zauna lafiya? Wallahi baka isaba domin ni yanzu babu wanda ya isa ya dakeni sai ruwan sama..."

"Wai ku sakeni mana bakwa jin irin maganar da yarinyar nan take fada min?" Ya sake fada a zuciya,

Abokan nashi basu sakeshi ba sai hakuri da suke bashi ita kuma ummulkhair sai fama da ita alawiyya take yi akan ta tashi su tafi subar wurin domin mutane har sun fara taruwa amma fur ummulkhair taki tashi tace babu uban wanda ya isa ya tayar da ita daga wurin,

"Ke ni kike zagi..?"

"An zageka din kai dan gidan uban waye da ba za azageka ba?"

Wata kara ya saki take ya kwace daga rikon da abokan nashi suka yi masa ya nufi kanta gadan gadan, aguje suka sha gabansa suka tattareshi, ganin haka yasa alawiyya jan ummulkhair ta karfi suka bar wurin yayinda sawwam in banda huci babu abinda yake yi,

Lokaci kadan idonshi ya kada yayi jawur ranshi in yayi dubu to ya baci saboda zagin da ummulkhair tayi mishi agaban bainar jama'a,

"Wallahi sai na koyawa yarinyar nan hankali domin babu macen da ta taba zagina sai ita..."

Fusgewa yayi ransa a bace yabar wurin ya nufi wurinda motarsa ke ajiye,

Yana zuwa ya shiga ya yi mata key azuciye ya fita daga cikin makarantar bayan ya tayar da kura wacce kai in ba sani kayi ba zakace sansanin yakine,

Yanayin yanda yake tukin ma kana gani kasan ransa a bace yake, ji kake k'uuuuuuu ya taka wani wawan mahaukacin burki sakamakon tsayarsu da danja tayi,

Duk mutanen wurin sai da suka razana saboda sunyi zaton wani aka kade, shi kuwa gogan sai furzar da numfashi mai dumi yake yana shafa sumar kansa alamun ransa ya gama baci,

Kamar zai tashi sama haka yayi lokacin da danja ta basu hannu, da wannan gudun na masifa ya isa gidansu dake unguwar Sharada phase 2,

Wani tangamemen gida ya shiga bayan yayi horn mai gadi ya bude masa, yana yin packing ya fito a fusace ya shiga cikin gidan, falon mahaifiyarshi ya shiga kamar zai ci tuntube saboda bacin rai,

Zaune ya sameta itada wasu yanmata guda biyu kyawawa suna kallon Indian film awata tasha (zee world),

Tsallakesu yayi saboda bai sansu ba yawuce cikin bedroom dinta,tunda ganinshi mahaifiyarshi ta gane yana cikin bacin rai dan haka tayi gaggawar binshi cikin dakin,

A tsaye ta sameshi ya dunkule hannunshi sai naushin iska yake yi yana cewa "ohh my God..."

Saurin karasawa gareshi tayi ta rikeshi "sawwam me ya farune?" Mahaifiyarshi ta tambayeshi cukin kulawa,

"Mami wallahi a school ne aka bata min rai..."

Kama hannunshi tayi ta zaunar dashi a bakin gado itama ta zauna tana murmushi,

"Sawwam sau nawa zan fada maka cewar duk inda mutum ya tsinci kansa to dole sai yayi hakuri,kofa da wa zaka zauna dole sai kayi hakuri, kayita hakuri kaji..." Mami ta fada tana Shafa kanshi,

"Shikenan Mami naji kuma zanyi hakurin"

Mikewa yayi amma har lokacin ranshi a bace yake mutuka,

"Ga baki can a falo 'yayan hajiya rahama ne ta turosu ka duba koda wacce zaka ga tayi maka acikinsu.."

Murmushin yake yayi domin idan har da sabo to ya saba kusan kowanne lokaci kawayen Mami sukan turo yaransu yanmata wai ya duba ko zai ga wacce tayi masa,

"Mami dan Allah nidai mubar wannan maganar.."

Kafin Mami tayi magana har ya fice daga cikin dakin, ko kallon yanmatan bai yi ba ya wuce abinshi, dakinsa ya shiga ya fada toilet ya sakarwa kanshi ruwa yayi wanka ya fito har lokacin bai daina hango fuskar ummulkhair tana zaginsa ba,

Kananan kaya yasa ya fita zuwa wurin mai gadinsu domin dama kusan kowanne lokaci idan yana gida can yake zuwa suyita hira,

Yau dinma zaman yayi suka fara hira baba dan tsoho yana bashi labari mai saka nishadi,

"Yawwa baba dan tsoho dama ina son tambayarka wai dan Allah me mata suka fi jin tsoro ne?"

Dariya baba dan tsoho yayi sannan yace,

"Ai sawwam babu abinda mata suka fi tsoro sama da kadangare komai kankantarsa kuwa, duk mace zaka sameta tana tsoron kadangare..."

🅿herty novels📚
Duniyar makaranta

RAMUWAR GAYYA..2

*RAMUWAR GAYYA...!*💘

   _Love story 50,50_

_*UMMI A'ISHA*_

       _with_

*_PHERTYMAH XARAH_*

  *_2_*

~~~ Sallama ta yiwa samarin tareda cewa "dan Allah tamabaya nake, inane wurinda yan level 1 suke lectures?"

"Ke, yauma dawowa kikayi? Wai ke mu sa'anninki ne?" Wani saurayi ya fada sai da suka hada ido sannan ta gane ashe shine saurayin jiya,

"Kuyi hakuri" tafada atsorace zata juya ta tafi,

"Ina zakije? Zo nan" taji yafada da karfi,

Dawowa tayi ta tsaya, "wanne course kike karantawa?"

"Mathematics" ta bashi amsa,

"Ya sunanki?"

"Ummulkhairi" ta sake bashi amsa,

"Ungo jeki ki siyo min lemo, kuma indai baki kawo min ba kika gudu to zan nemoki duk inda kika shiga"

1000 ya zaro ya bata ta karba ta wuce,

Capteria ta nufa acan ta siyo masa lemon ta dawo duk hankalinta atashe yake domin bata san dalili ba kawai tsoronshi taji tana yi,gashi bata san cewa a jami'a kowa gashin kansa yake ci babu sawa babu hanawa ba, tayi zaton irin secondary school ne akwai seniority,

Wurin da suke ta karasa takai masa lemon,

"Ke wayasa ki siyo min fanta? Saboda ke villager ce ko? Karbi ki je ki canjo"

Hakuri tafara bashi "dan Allah kayi hakuri dan Allah"

Fashewa da dariya taji abokannshi sunyi sannan ga dalibai sun zagayesu suna yi mata dariya kun san jami'a komai abin kallo be kuma abin dariya ne, nutsewa ne kawai batayi ba dan kunya, kudin da lemon ta cilla masa ta juya idonta duk ya ciko da kwalla,

Wata tagani sanye da hijab nan budurwar ta kamo hannunta,

"Yar uwa me yakaiki wurinsu wadancan yaran marassa mutunci?"

Kwallar idonta ta goge tace "wallahi ban sansu ba daga zuwa tambayarsu wurin lecture dinmu shikenan fa harda aikena"

"Yi hakuri to share hawayenki, wanne department kike?"

"Mathematics"

"Level 1?"

Kai ta daga mata alamun ehh,

"Ayya department dinmu daya dake amma gaskiya naji dadi saboda dama ni kadai ce mace kullum atakure nake dama kuma ance mu biyune mata wadanda muka nemi course din"

Murmushi ummulkhairi tayi "kin san ai maths bashida farin jini majority din dalibai sun tsaneshi saboda akwai caja brain, nima fa da ban iyaba lokacin da ina primary school sai da naje secondary school sannan nadage na iya daga karshe har quiz nake zuwa na maths"

Dariya budurwar tayi "ah lallai ashe daya muke, wallahi nima yanzu bazan iya theory ba saboda tsananin sabon da nayi da lissafi"

"Koni gaskiya yanzu bazan iya theory ba nafi ganewa in zauna inyita Tarawa da debewa" ummulkhairi ta bata amsa,

"Allah Sarki ya sunanki?"

"Sunana ummulkhairi"

"Ayya nikuma sunana alawiyya"

"To inane wurin lectures din?" Ummulkhair ta tambayeta,

"Canne new side fa, ai abun namu muhimmi ne dan yau ma bamu da lecture sai 12"

Zaro ido ummulkhair tayi "kai amma akwai damuwa wallahi ni ai nayi tunanin tun 8 ake fara lectures din"

Hannunta alawiyya ta kama tana murmushi, "zo muje admin block kiga time table dinmu saboda nima bani dashi"

"Yawwa to muje"

Tafiya suke suna shan hirarsu tamkar dama can sun san juna ko kuma sun dade suna kawance, har suka karasa admin block din wurinda aka kafe time table na kowanne department,

Biro da dan karamin memo ummulkhair ta ciro ta fara kwafar musu time table din tana murmushi,

"Alawiyya wai wannan gayen na dazu wanene?"

"Meyasa kike son sanin waye shi?" Alawiyya ta tambayeta tana kallon fuskarta,

"Kawai ina son sanine domin inada wani buri akanshi" ummulkhair tace da ita tana rubutu ajikin memo dinta,

"Buri? Wanne irin buri ummulkhair? Ko dai kin kyasa ne?"

Murmushi ummulkhair tayi wanda har biro hannunta yana kokarin subucewa ya fadi kasa,

"Ko kadan bai yimin ba saboda na fuskanci dan rainin hankaline"

"Hmmm ummulkhair kenan ai duk makarantar nan kowa yasan three pointer saboda tsabagen kwakwalwarsa, yana ja fiyeda yadda bakya tunani shiyasa ma kika ga yana rashin mutuncinsa son ransa saboda yaga yanada ilimi, ni kaina yaron yana burgeni domin yasan abinda yake yi yana zama yayi karatu kuma bai taba samun carryover ba tun farawarsa har kawo yanzu, haka ake son mutum bawai yazama dan iskaba amma brain empty, shikam wannan gayen ya iya wulakanci amma kuma yasan me yake yi sannan yanda kika gansun nan shida friends dinshi to haka suke duk school dinnan kowa yasan basa kula yanmata."

"Alawiyya kenan nifa duk wannan yabon da kika dage kina yi akanshi ba burgeni zaiyi ba"

"Dama nasan bazai taba burgeki ba ummulkhair tunda three pointer yasaki kuka, amma kisani ni ina fada miki ne abinda na sani agame dashi, sunanshi na asali *SAWWAM MUSTAPHA* ance shi kadai mahaifanshi suka haifa gidansu yana nan a unguwar sharada phase 2, kamar yanda na fada miki yaron nan yana ja domin baya wasa da karatu, shine president na makarantar nan domin lokacin da akayi zabe dalibai duk shi suka zaba"

"Yayi kyau" ummulkhair ta fada tana kokarin saka biro dinta da memo acikin jaka.

🅿herty novels📚

Duniyar makaranta

RAMUWAR GAYYA.. 1

*RAMUWAR GAYYA...*💘

   _Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

       _with_

*_PHERTYMAH XARAH_*

*_1_*

_Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai...._

~~~"Wannan shine abinda nake son kiyi kamar yadda nafada miki abaya, hakika ummulkhair nadade ina burin Allah ya bani ya mace domin wannan burin nawa ya cika amma Allah bai baniba sai yanzu, ina fata zaki dage ki zama silar cikar Burina kamar yadda nadade ina fata,

Idan kikayi haka kin gama yimin komai kuma zanyi alfahari dake sannan koda na mutu to zan mutune da farin cikin abinda kika yimin, ina fata zaki mayar da hankali kan abinda natura ki sannan banda kula kawayen banza da samari barkatai idan kikayi haka to lallai ranki zai baci, Allah yayi miki albarka ya baki nasara"

Idonta fal da kwalla ta dago tana duban mahaifin nata wanda ke kishingide akan kujera fuskarsa cikeda walwala da annuri,

"Abba nayi maka alkawari zan zama silar cikar burinka kamar yadda ka dade kana fata sannan zanyi abinda ka turani batare da an samu kuskure ba"

Sai alokacin mahaifiyarta dake zaune agefe tayi magana itama idonta dauke da kwalla,

"Yanzu Alhaji abinda kayi ka kyauta kenan? Ka dauki yarinya karama yar shekara 22 katurata har nan da garin Kano kawai dan kanada buri acikin ranka kuma ka dage sai burin nan ya cika.."

Katseta yayi ta hanyar cewa "ya isa haka hajiya fati, ai dai 'ya tawace ko? To ki barni na zabar mata abinda naga yafi cancanta da ita, tun shekaru 30 da suka wuce nake burin Allah ya mallaka min ya mace amma bai baniba sai yanzu, yayunta duk samarine maza d'ai d'ai har hudu, to yanzu tunda lokaci yazo dama ta samu ai sai ayi amfani da ita"

"Gaskiya Alhaji nidai ban goyi bayan ka tura min yarinya wata uwa duniya har kano ba kawai dan kana son cikar burinka"

"Mama kiyi hakuri babu komai insha Allah bazan yi abinda duniya zatayi Allah wadai dani ba, zan kare kimar gidan nan da mutuncinsa abinda abba ya tura ni shi zanyi bazan taba yin wani abuba sabanin haka" ummulkair ta fada tana share hawayen idonta,

"Allah yabada sa'a yayi miki albarka, maza ki tashi kije kar kuyi dare, Allah ya kiyaye hanya" mahaifinta yace da ita,

"Ummulkair Allah yabaki sa'a" mahaifiyarta tafada tana goge hawayen dake kwarara akan idonta,

Tashi tayi taja katuwar jakar kayanta (trolley) tafita tana share hawayen idonta,

Awaje ta iske yayanta wanda take bi yana jiranta, kayan ya karba ya saka acikin Mota ta shiga ta zauna suka lula,

Tunani take yi aranta domin wannan shine karo na farko da zataje garin kano kanon ma wai jami'ar bayero,

"Allah kabani sa'a" tafada acikin ranta tana kallon hanyar da zata fitarsu daga garin bauchi zuwa kanon dabo.

  Tafiyar awa ukuce ta kaisu cikin kano lokacin karfe 3:30 na yamma atsakiyar makarantar kusa da hostel din da aka tanada domin mata yayanta ya ajiyeta yafara kokarin fito mata da kayayyakinta,

Tana ganinsa ya juya zai tafi take tasa kuka kamar yarinya ko saurarenta baiyi ba yayi tafiyarsa kasancewarsu sako da sako,

Kayanta tafara dauka tana kaiwa cikin hostel kofar dakin da aka bata, sai da tagama kwashewa tsaf sannan ta shigar da kayan cikin dakin wanda ya kasance nata ita daya domin bata son kazanta wannan dalilin ne yasa zata yi zamanta ita kadai,

Shisshirya kayan tayi ta mike akan gadonta ta kwanta ga wata irin yunwa da takeji gashi babu wanda tasani,

"Gaskiya bazan iya girki yanzu ba bari kawai naje na siyo abinci awaje" tafada acikin zuciyarta, mikewa tayi taja hijabinta tasa ta dauki yar karamar jakar hannunta ta fita,

Babu inda tasani dan haka taketa waige waige gashi ranar weekend ne makarantar babu dalibai da yawa,

Wani shago ta hango dan haka ta nufi can, wasu samari guda uku tagani suna zaune akofar shagon,

"Dan Allah me da me ake sayarwa anan?" Tafada tana kallonsu,

Shiru suka yi mata babu wanda ya tanka,

"Bayin Allah magana fa nake yi muku"

"Ke bar nan" wani saurayi acikinsu yafada fari dogo mai saje,

"Ba zaki bar nan ba sai nataso?" Yasake fada yana kallonta,

Da sauri tafara kokarin barin wurin har tana hadawa da gudu, dariya suka saka gaba dayansu tareda Tafawa,

"Sai 3 pointer" suka fada suna ihu,

Hostel takoma tana tunanin to shi wannan waye a makarantar? Itadai bakuwa ce bata da masaniyar ko waye shi, dambun naman da  mamanta ta yi mata ta dauko tafara ci da biredi har ta koshi,

Zama tayi jugum tana jin hayaniyar mutane har dare yayi, atsorace ta kwanta adakin bayan ta kulle, baccine ya dauketa sakamakon gajiyar da tayi.

  Tun asuba ta tashi tayi salla ta dauko alqur'aninta ta bude ta karanta har gari yayi haske,bucket ta dauka taje ta debo ruwa ta wuce bathroom tayi wanka ta zo ta shirya,

Ruwan zafi ta jona a heater ta hada tea ta saka kayanta riga da zani da katon hijab taja dakinta ta kulle ta fita,

Koda ta fita ganin makarantar tayi acike sabanin jiya da babu mutane da yawa,

"Yau ake yinta" tafada azuciyarta sakamakon bata san takamaimai wurin da zata samu yan ajinsu ba kuma babu wanda tasani aciki,

Wasu samari ta hango su hudu asaman wata mota daya daga cikinsu ya bata baya yana sanye da kananan kaya yana taje sumar kanshi da cumb,

"Ohh samarin jami'a kenan" tafada aranta tareda dosar wurin da samarin suke.

🅿herty novels

RUWAN KASHE GOBARA.. 78-End

[2/2, 3:14 PM] Itz Ummi A'isha🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

    _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

aishaummi.blogspot.com

  _*78*_

~~~Daren ranar sam lamido bai samu damar yin bacci ba saboda tsananin farin cikin da yake ciki, koda ya idar da salla zuwa yayi kusa da abdallah ya zauna ya zuba masa ido yana kallonshi,

Sai daf da sallar asuba sannan lamido ya dan samu bacci ya daukeshi kwata kwata baccin da yayi baifi na minti talatin ba ya tashi yayi sallar asuba, yana nan zaune har gari ya waye wurin karfe 7 abdallah ya tashi, kamashi lamido yayi yana kallon fuskar yaron mai dauke da beautiful point irin nashi,

"Abdallah ka tashi? To maza muje kayi alwala kazo kayi salla kaji"

"To daddy" abdalla ya amsa masa yana sake makaleshi, tare suka shiga cikin bathroom din abdallah yayi alwala sannan suka dawo tsakiyar dakin yayi salla,

"Abdallah kayi mana addu'a nida momynka kaji"

"To daddy zanyi muku"

"Yawwa abdalla, Allah yayi maka albarka" lamido yafada yana murmushi, suna nan acikin bedroom dinshi a zaune ikhlas ta shigo saboda tana son taje ta yiwa abdallah wanka, k'in koda kallonta lamido yayi saboda jiya taki amsa gayyatarshi,

"Abdallah zo muje nayi maka wanka ko" ta fada tana murmushi domin ta lura da shariyar da lamido ya fara yi mata,

"Abban sadiq ina kwana?" Sai da ya juyar da kanshi sannan ya amsa mata da "lafiya" daga haka bai kara cewa komai ba ya koma saman gadonshi ya kwanta,

Jan hannun abdallah ikhlas tayi tana murmushi, dakinta suka koma tayi masa wanka ta shiryashi cikin bakar riga da brown din wando nan tayiwa sadiq ma shima ta shiryashi sannan itama ta shiga tayi ta fito, kwalliya ta zauna ta tsara cikin wani blue din material mai zanen flower ajiki, abdallah na zaune yana rike da sadiq yana yi masa wasa,

"Anty zanje wurin daddy.."  Inji abdallah,

"Tashi kaje yana dakinshi, bani sadiq din" karbar sadiq tayi shikuma abdallah ya tafi wurin lamido yana kwance kamar me yin bacci dan haka abdallah yaje bayanshi ya kwanta ya nanuk'a cikin jikinshi ya rungumeshi,rungumeshi shima lamido yayi yana jin tamkar ya mayar dashi cikin cikinsa saboda tsananin so.

Sai da misalin karfe 9 sannan suka hallara akan table domin yin karin kumallo, lamido daukar abdalla yayi ya dorashi asaman cinyarsa ya soma bashi abincin,

Suna ci suna nishadi har suka kammala, suna gamawa lamido ya dauki abdallah suka nufi gidan innah, innahn bata sashenta tana sashen baffa dan haka yabisu can, suna zaune suna tattaunawa bayan sun kammala yin breakfast,

Suna shiga innah ta zabura ta tashi zaune tana kallonsu ita duk a tunaninta ma haydar ne dan marigayi,

"Lamido waye wannan?" Innah ta jefo masa wannan tambayar tana bin abdallah da kallo,

"Innah abdallah ne d'ana.."

Ba innah ba hatta Baffa sai da ya zabura ya tashi daga kishingiden da yake,

"Lamido wanne d'a kuma?" Baffa ya tambayeshi, zama lamido yayi yana murmushi ya dora abdalla akan cinyarsa,

"Baffa wannan yaron d'anane, ikhlas ce mahaifiyarshi..." Nan lamido ya kwashe labarin komai ya sanarwa dasu innah,

K'walla innah ta fara yi wacce ta kasance k'wallar farin ciki,

"Lallai Allah shine gagara misali.." Innah ta fada cikin murna,

"Wannan haka yake domin kuwa gashi munga zahiri da idonmu, Allah ya raya yaronnan cikin kyakkyawar rayuwa, hakika da ace mutane zasu rinka daukar kaddara su daina zubar da ciki da jefar da yara to da ba asamu bata gari dayawa daga cikin yara masu tasowa ba, ya kamata mutane su ringa rungumar yaran da aka samesu bata hanyar aure ba domin ba laifinsu bane,basu da wani hakki saboda basu san ta yanda akayi aka haifesu ba, mudai insha allahu zamu rike wannan yaron irin rikon da har ya girma bazai taba sanin cewar shi ba dan halak bane sai dai idan har ku iyayensa kune kuka yi ra'ayi kuka sanar dashi" baffa ya kammala jawabin yana mikawa abdallah hannu,

"Zo nan abdallah zo mu gaisa"

Tashi abdallah yayi yaje wurin baffa ya zauna,

"Yawwa zaka zauna anan ko?"

"A'a daddy na zanbi" abdallag ya bashi amsa,

Dariya dukkaninsu suka yi cikeda farin ciki, su lamido sun jima agidan har sai da 12 na rana yayi sannan suka tafi wurin bash, lokacin da bash yaga abdallah kuma yaji cewar wai dan lamido ne ba karamin murna yayi ba yace,

"Shege on top ashe kai ka dade da ajiye mai yi maka addu'a ni ka bari acikin matsala"

Dariya lamido yayi "kaima ka kusa ai domin wallahi bash rayuwar aure da dad'i musamman ma idan kayi dace da mace ta gari wacce ta iya kulawa da miji, idan kana da mata komai sai dai ayi maka, kaga ni yanzu komai yimin ake yi tun daga kan wanka, shafa mai, sa kaya, babu abinda nake yi gashi uwa uba....!". Shiru yayi bai karasa maganar ba sakamakon ganin abdallah yana kallonshi,

"Allah ya shiryeka.." Bash yace dashi yana dariya,

"Gaskiya ai na fada maka bash wallahi ka dage ka shiga daga ciki tun kafin hunturun nan ya dawo ya tarar da kai..."

"To gani nan dai kawai, amma wannan yaron babu ta inda ya barka wallahi, photocopy dinkane sak..."

"Dagaske muna yin kama?" Lamido ya tambayeshi cikeda tsokana,

"Ai da gani babu tambaya duk wanda ya ganshi ya ganka yasan danka ne, kai ko? Kai mugun jarababbe ne tsabar jaraba ma dan kamarka ya biyo"

"Ya isheka haka bash.." Lamido yace da bash yana dariya, tashi bash yayi suka fita tare da lamido da abdallah wanda tunda suka fita basu suka koma gida ba sai da yamma tayi,

A falo ya iskesu dukkaninsu sun kammala cin abinci suna hira, zama yayi da alamun gajiya a tare dashi shi kuma abdallah ya nufi wurin ikhlas yaje ya fara kokarin shiga jikinta,

Sannu da zuwa suka yiwa lamido sannan ihsan ta mike taje ta fara shirya masa table shida abdallah,

"Bari nayi wanka sai nazo naci abincin" lamido yafada tareda mikewa ya nufi sashensa, ihsan ce ta dawo ta zauna tana yiwa abdallah magana,

"Abdallah ina da ina kuka je ne?"

"Gidansu daddy da... Da gidansu uncle"

"Iye ashe ka gaisa da su innah ko?" Fadila ta fadi tana murmushi, itama ikhlas murmushin take yi saboda tana jin dadin irin yadda su ihsan ke kula abdallah babu kyamata,

Suna nan zazzaune har lamido ya fito yayi wanka yasaka green din t shirt da bakin wando iya gwiwa, table ya hau ya zauna domin cin abinci, da gudu abdallah yaje ya haye cinyarshi suka soma cin abincin tare,

Ikhlas na zaune tana kallonsu tana ganin yadda lamido yake bawa abdallah abincin sunata faman dariya, suna kammalawa suka sake fita shikenan ikhlas bata sake yin ido hudu dasu ba sai da karfe 9 na dare yayi.

  Dakinta lamido ya shiga bayan yakai abdallah dakinshi ya kwantar dashi, tana kwance ta gama yin shirin bacci cikin milk colour din rigar bacci,

"Abban sadiq ya kamata fa ka daina irin wannan shigar saboda yanzu ka girma.."

Murmushi yayi ya juya ya fita ba tare da yace da ita komai ba saboda dama zuwa yayi yaga kyakkyawar fuskarta kafin ya kwanta bacci.

  Washe gari tunda safe su ihsan itada fadila suka samu lamido a dakinshi suka sanar masa cewar zasu cigaba da zama dashi koda bazai haihun ba domin dama saboda Allah suke sonsa kuma abinda ya sameshi kaddara ce daga Allah wacce babu wanda ya wuce ta sameshi, ba karamin murna lamido yayi ba har sai da yayi hawaye saboda tsananin murna nan yayita saka musu albarka tareda addu'ar Allah yaci gaba da zaunar dasu lafiya.

  Acikin satin duk lamido ya zauna agidane babu inda yake fita kullum yana tareda iyalinsa, wata makaranta mai tsada yaje ya saka abdallah sannan ya siyo masa dukkan abubuwan da zai bukata a matsayinsa na dalibi, ga kayan wasa da ya siyo masa kamar babu gobe banda su biscuit, chocolate, juice, da sauran kayan zaki irin na yara,

Lokacin da ya dawo daga kaishi school din a falo suka tarar da ikhlas tana yanka cabbage,

"Anty daddy na yace yanzu sunana Abdallah Usman, yanzu ba abdallah Hussain bane sunana"

Kallonshi ikhlas tayi tana murmushi ita kwata kwata ma bata san sunan lamido na gaskiya Usman ba sai yau gaskiya fa shiyasa yake da zuciya da fushi ashe sunan mazaje gareshi,

"To abdallah Allah ya bada sa'a" ta fada tana kallon lamido kasa kasa domin tunda abdallah yazo gidannan nan kullum lamido daukarshi yake yi zuwa dakinshi su kwana tare.

*_79_*

~~~Acikin satin abdallah ya fara zuwa school wanda kullum lamido ne yake kaishi yake zuwa ya daukoshi idan an tashi ya dawo dashi gida, komai yawan aiki a office haka yake tsallakeshi da zarar lokacin tashinsu abdallah yayi,

Haka rayuwa taci gaba da tafiya har abdallah yayi sati uku da dawowa gidan, yau tunda sassafe ikhlas ta samu ta tashi ta shiryawa abdalla abincinshi na tafiya school sannan tayi masa wanka, tana tsaka da shiryashi lamido ya shigo daga shi sai jar t shirt da blue din wando three quarter,

"Good morning daddy" abdallah yace da Lamido yana murnar ganinshi,

"Morning my sweet boy" lamido ya bashi amsa cikin fara'a,

"Abban sadiq yanzu abinda kakeyi ka kyauta kenan?" Ikhlas tace da lamido tana kokarin sakawa abdallah riga,

"Me nayi kuma?" Ya tambayeta yana mai zuba mata manyan idanuwanshi,

"Tunda abdallah yazo gidan nan ka daina kwana adakin kowa kullum sai dai ka daukeshi ka kaishi dakinka ku kwana tare"

"Gani nayi bakuda bukata ta shiyasa, tun ranar da ya dawo ai nace miki ki rakani dakina mu kwana kika k'i basai in kyaleki ba lokacin da kika bukaceni sai ki nemeni..."

Shiru tayi masa saboda abdallah yana wurin, tsallaketa yayi yaje ya dauki sadiq wanda ya tashi daga bacci ya dan fara kuka, jijjigashi ya fara yi yana rarrashinshi,

"Saddiquna.." Sadiq najin maganar lamido ya daina kukan ya bude idonshi yana dariya.

"Tunda kina son in baki hakkinki sai ki shirya kafin na dawo.."

Ya fada yana kallonta, "wanne hakki kuma? Ni azumi ma nake yi" ta bashi amsa tana harararshi,

"Azumi? Azumin me? Wallahi gara ma ki hada tea mai kauri kisha kafin na dawo idan ba haka ba kuma kece zaki sha wuya.."

Kallonshi ta sakeyi cikeda mamaki, "hmm zancen kakeso"

"Kema kina so kuma wallahi yau dai kam sai na kashe kishin ruwata"

Sake kallonshi tayi "abdallah dai yana jin duk abinda kake cewa"

Kwantar da sadiq yayi ya kama hannun abdallah, "kisha tea dinfa kafin na dawo"

Bai jira amsarta ba ya fita rikeda hannun abdallah, baifi minti 20 ba ya dawo lokacin ta fito daga wanka tana goge jikinta da dan karamin towel,

Wayarshi ce ta fara kara da kamar bazai daga ba ganin xahar ce amma sai ya daga ya kara a kunnensa tareda matsawa kusa da ikhlas ya rike towel din hannunta,

"Hello xahar" ya fadi ahankali gamida kaiwa ikhlas kiss a kuncinta, kokarin zamewa daga jikinsa ta fara dan haka yayi saurin rikota nan ta fara kokarin kwacewa turata saman gado yayi yana dariya,

"Xahar ina zuwa zan kiraki anjima"

Tun kafin ta bashi amsa ya ajiye wayar  yabi ikhlas suka ci gaba da kokawar da suka fara, xahar har lokacin tana makale da wayar tana jinsu har sai da taji abin yana neman wuce saninta sannan tayi maza ta kashe wayar tana hawaye tun daga wannan lokacin tayiwa kanta alkawarin cire lamido daga cikin zuciyarta domin ta fahimci akwai wacce yake so.

Sai da komai ya lafa sannan ikhlas ta tayar masa da boren abinda ke tsakaninsa da xahar, rungumeta yayi yana shafar gashin kanta,

"Pretty na karki sakawa kanki damuwa ni babu auren da zan sake yi,ita wannan xahar dinma so nake yi na hadasu da bash ya aureta tunda kinga shima ya fara aiki a kamfanina amma ya kika gani?"

Sake rungumeshi ikhlas tayi ta yi masa kiss a baki tace "hakan yayi daidai abban sadiq, indai kayi haka to zaka samu lada mai tarin yawa"

"Allah yasa ta sanadiyyar wannan hadin auren da zanyi su abdallah su samu kani nan bada jimawa ba"

Murmushi tayi ta riko hannunshi "ni ai nagama haihuwa.."

"Sauranki tara domin guda goma nake son ki haifa min"

Makale kafada tayi tana murmushi "Idan na sake yin guda biyu ma nayi kokari"

"Sai na kawo amarya ta karasa miki ko..?"

Duka ta kai mishi a kirji tana dariya, kare dukan ya shiga yi ya hada hannuwanta dakyar ya ciccibeta ya nufi bathroom da ita.

_Gaisuwa mai tarin yawa ga ummu fahad & matar officer_

*_Ummi Shatu_*
[2/2, 3:14 PM] Itz Ummi A'isha: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_

*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

   _Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_

_*80*_

~~~Kamar yadda lamido ya kudiri niyyar hada auren bash da xahar hakance ta faru domin bash bai k'i ba haka itama xahar bata musa ba domin ta fuskanci shi lamido sam hankalinsa baya gareta yana ga wata ta daban, babu dogon bayani soyayya ta kullu tsakanin bash da xahar nan aka sanya ranar biki wata uku masu zuwa.

  Akwana atashi haka rayuwa taci gaba da gudana agidan lamido cikin jin dadi da kwanciyar hankali, a lokacin lamido ya shirya musu tafiya zariya shida ikhlas da abdallah batare da ya sanarwa da ita ikhlas dinba domin yana son ya sasanta tsakaninta da abbanta,shiryawa suka yi suka tafi su hudu dashi da ita da abdallah da sadiq,

Tun akan hanyarsu yake bata hakuri sannan yaci gaba da yimata nasihar cewar ba a fushi da mahaifa, duk abinda suka yiwa mutum to haka zai daure yayi musu biyayya,shiru kawai tayi tana sauraronshi domin ita kanta tasan tayi dacen miji mai kaunarta mai kaunar dukkan danginta bama yan uwanta ba duk wanda ya danganceta to lamido yana kaunarshi,

Kasancewar da wuri suka tafi yasa suka isa zariya da wuri, hotel suka je ya kama musu sai da suka ci abinci suka huta sannan suka tasamma gidan abbanta, kamar yanda gidan yake ada yanzun ma haka yake sai dai kuma babu jami'an tsaro kamar da nan ikhlas tafara tunanin to Kodai su abban sun tashi ne?

Da wannan tunanin acikin ranta suka karasa cikin gidan nan suka ganshi tamkar babu kowa aciki amma koda suka karasa shiga sai suka iske goggo kakar ikhlas a tsaye tana rikeda babban fo na yin fitsari ai suna hada ido da ikhlas ta saki fo din ta fashe da kuka mai ban tausayi,

Sakin baki ikhlas tayi tana kallonta yayinda lamido ya razana ya fara tambayar goggo abinda ya faru, kasa basu amsa goggo tayi illah wucewa da tayi cikin daki tana sharar kwalla nan suka mara mata baya suna shiga suka ga abbansu ikhlas kwance barin jikinshi a shanye duk ya rame yayi baki,

Cikin rudu ikhlas ta ajiye sadiq idonta fal da kwalla,

"Goggo meya samu abban?"

"Ikhlas ki yafe mana, hakika abinda mukai mukune keda mahaifiyarki yake bibiyarmu, tun bayan tafiyarki babu jimawa mahaifinki ya yanke jiki ya fadi sakamakon bai yi nasara a zabe ba tun daga wannan lokacin ya haduda lalurar shanyewar barin jiki ita kuma nafi ta hura masa wuta akan cewar dole sai ya saketa nan ya saketa saki daya ta tattare dukkan kudadensa ta gudu, yanzu gashi bamu da komai gidan nan ma da muke ciki mun sashi a kasuwa sayar dashi zamu yi..."

Goggo ta karasa maganar tana kuka,

"Allah sarki ki daina kuka goggo insha Allah zai samu lafiya" lamido yace da goggo, ahankali baban ikhlas ya bude idonsa yana kallonsu yana ganin ikhlas ya fara kwalla,

"Ikhlas ce?.." Ya fadi maganarshi a shawude bakinsa a karkace,

"Ehh nice abba" ikhlas ta bashi amsa tareda matsawa kusa dashi,

"Ikhlas ki yafe min kinji,nasan ban karbi kaddarar da Allah ya aiko min ba nasaki kin zubar da ciki gashi zaben ma ban ciba"

"Abba ai nadade da yafe maka sannan bayan tafiyata na haihu har nayi aure na sake haihuwa"

"Kin haihu? Ina yaran?"

Matso dasu abdallah tayi ta nuna masa su nan ya kamo abdallah da hannunshi mai lafiya,

"Yanzu wannan shine yaron da kika tafi da cikinsa? Lallai Allah shine gagara misali babu shakka bamu isa mun hana kaddarar ubangiji ba, Allah ya rayasu yayi musu albarka.."

"Amin abba" suka amsa gaba dayansu, tashi ikhlas tayi ta ajiye mayafinta ta soma gyara gidan domin ko ina a hargitse yake babu bata lokaci ta kalkale ko ina shi kansa abban nata sai da ta dafa ruwa tayi masa wanka ta debo wasu daga cikin kayanshi ta wanke masa,

Tunda suka zo har dare yayi bata hutaba aiki kawai take yi har karfe 9 na dare, sallama lamido yayi musu ya tafi hotel tare da abdallah, kwanansu uku agidan suna jinyarsa acikin kwana na hudune lamido yazo musu da maganar cewar zai fitar da abba kasar waje domin sama masa lafiya, kuka awurin goggo kamar wacce akayiwa mutuwa domin yau ta yarda ranar wuya sai naka amma ranar dadi kuwa sai dai bare,babu bata lokaci aka fitar da abba kasar chairo, nan su ikhlas suka tattara suka koma gida saboda makarantar abdallah.

  Rayuwarsu haka taci gaba da tafiya kullum lamido hankalinsa yana kan ikhlas bashida wani buri wanda ya wuce ya kyautata mata ita da yaranta ko hira suka hadu suna yi gaba dayansu dasu fadila to yafi mayar da hankalinsa kan ikhlas wani lokacin har kunya yake sakata ji saboda su Kansu su ihsan din har sun fahimci yafi ji da ita acikinsu,

Yauma suna kitchen suna aikin girkin abincin dare ita da ihsan fadila kuma tana falo tana yiwa abdallah home work, lamido ne ya dawo daga office yasha suit bakake wadanda suka karbeshi,

Kitchen din ya shiga ya samesu suna aiki,ihsan yaje ya mannawa kiss a kumatu yace "sannu da aiki my ihsan" ya wuceta ya nufi wurin ikhlas wacce take tsaye ta juya baya tana yanka alayyahu,

Ta bayanta ya tsaya ya rungumeta yadora kansa akan kafadarta,

"Barka da aiki pretty na...."

"Abban sadiq sannu da zuwa" tace dashi tana kokarin tureshi daga jikinta,

"Zo muje kiyi min wanka.." Ya rada mata a kunnenta,

"Aiki fa nake yi" ta bashi amsa,

"Wallahi kizo mu tafi tun kafin na daukeki"

"Kai abban sadiq gaskiya ka cika rigima"

"Ehh na yarda" ya fada yana shafa cikinta,

"To sai ka bari na karasa ai"

Yana nan tsaye yana rungume da ita har ta karasa yanka alayyahun yaja hannunta suka fita ita duk ya gama sata ta tsargu saboda ga ihsan nan a cikin kitchen din a falo kuma ga fadila nan,sai take ganin kamar ba zasuji dadiba duk da cewar ranar girkinta ne,

Dakinshi suka shiga, suna shiga ya jata jikinsa ya rungumeta, dauke kanta tayi ta fara kokarin cire masa kayan jikinshi,

"Haba pretty ki saki fuskarki mana irin wannan tsare gida haka..." Yace da ita yana lakuce mata hanci,

"Ni wallahi abban sadiq..."

Tun kafin tayi magana yayi sama da ita zuwa kan gadonshi,

"Dama tunda naga kanata wannan mammanne min din nasan abinda kake so kenan.." Tace dashi fuskarta a tsuke,

"To meye na bata ran kuma? Ba hakkina bane?"

Kawar da kanta tayi "nidai gaskiya ka daina yimin haka saboda zaka sa su ihsan su rinka jin babu dadi.."

"Wai me nayi ne ?" Ya sake tambayarta,

"Ya za ayi ace kullum sai muna tare dasu sai ka rinka zuwa kana kawoni dakinka bayan kuma duk lokacin da nazo bana komawa akan lokaci kuma nasan suna gane abinda ya faru tunda su ba yara bane"

"Dan Allah ni ki kyaleni nayi abinda zai fissheni.."

"Akan me zan kyaleka ka rinka yin rashin adalci? Duk ranar girkina baka barina acikinsu, da safe da rana da yamma da daddare, ko abincin rana fa kazo ci baka tafiya yanda kazo sai ka kawoni nan kuma saboda iya cin fuska sai ka sake sauya kaya, gaskiya wannan cin fuskar ya isa haka"

"Kin gama?" Ya tambayeta,

"Nagama" ta mayar masa da amsa,

"To wannan maganganun naki dai ba hanani abinda nayi niyyar yi zai yi ba"

Bai barta ta sake magana ba ya fara nuna mata soyayya bayan ya rufe mata baki da nashi, sai bayan sallar magrib sannan suka fito daga sashen nasa ita dai ikhlas duk kunyar hada ido dasu fadila take yi domin tasan ko waye ake yi masa haka dole bazai ji dadiba amma shi lamido babu ruwanshi ko kunya ba yaji wani lokacin ma sai suna zaune suna hira koda rana ko yamma sai yazo ya kira ikhlas kuma da zarar ta tafi shikenan bazasu dawo akan lokaci ba,

Dakinta ta koma ta shirya tayi salla ta fita, su fadila suna zazzaune suna cin tuwon shinkafa suna kallo, ko a fuskarsu bata ga alamun damuwa ba amma tasan acikin zuciyarsu akwai damuwar, zama tayi acikinsu tasa hannu suka ci gaba da cin abincin tare har lamido ya shigo sai faman kamshin turare yake budadawa da sun hada ido da ikhlas sai yayi mata gwalo.

Watan mahaifinta 3 akasar chairo ya dawo gida ya warke ras nan ikhlas ta shirya ta tafi tayi masa sannu da zuwa, yayunta ma sai da tayi musu waya ta sanar musu da abinda ya faru nan suka taho dubashi bayan ammi ta babbasu baki,lokacin da suka zo kuka abbansu ya shiga yi yana neman gafararsu tareda rokonsu akan su daure su shawo kan mahaifiyarsu ta dawo gareshi,da kyar ammi ta amince da komen nan kowa ya shiga murna, satin ikhlas daya ta koma yola domin bikin bash yazo, tana komawa suka sha bikin bash da amaryarsa xahar,

Bikin bash da sati biyu ammi ta koma gidan abbansu ikhlas bayan an daura musu aure, kudi mai yawa lamido ya bawa abbanta akan yayi jari yaci gaba da kasuwancinshi kamar yadda yake yi a baya.

  Rayuwarsu rayuwace mai dadi kowa yana jin dadin zaman gidan kullum cikin farin ciki suke gashi duk su ukun kansu ahade yake babu fada babu gaba kamar ba kishiyoyi ba,lokacin dasu abdallah suka samu Hutu alokacin lamido ya biyawa fadila da ihsan da abdallah umarah, iya shida ikhlas ne kawai da sadiq bai biya musu ba dalilinsa nayin haka kuwa shine baya son ikhlas tayi nisa dashi, tanaji tana gani su ikhlas suka tafi suka barta,

Zama tayi tai tagumi duk ranta ajagule,lamido ne ya biyota cikin dakin yana murmushi,

"Pretty na.."

Harararshi tayi ta kawar da kanta "ni ai babu abinda zakace min wallahi"

Zama yayi ya dauketa ya dorata akan cinyarshi,

"Kiyi hakuri dama nayi hakane saboda mu samu mu sake musha soyayyarmu kafin su dawo"

Makale kafadarta tayi tana harararshi,

"Haba pretty na, yimin murmushi nagani.."

Dolenta babu yadda ta iya haka ta biyeshi suka fara gudanar da soyayya mai wuyar fassarawa,

Tunda su fadila suka tafi babu abinda suke yi agida domin aikinma ba kullum lamido yake fita ba soyayya kawai yake gwadawa prettynshi,

Ita kanta ikhlas tasan sunyi daddadar rayuwa da lamido acikin kwanakin domin ya nuna mata ita kadaice mace guda daya tilo acikin zuciyarshi.

  Dawowarsu ihsan da watanni hudu shima lamido ya biyawa prettynshi dashi kanshi umarar nan suka tattara suka tafi dama lokacin ta yaye sadiq domin shekarunshi biyu cif, tunda sukaje kasa mai tsarki soyayya kawai suke yi da ibada ikhlas kam ta dage da yiwa lamido addu'a akan Allah ya basu haihuwa duk da abinda likitoci suka fada gameda lamido amma tasan fadar likitoci ba fadar Allah bace kuma Allah yakan iya nuna ikonshi akowanne lokaci, satinsu uku suka tattaro suka dawo,

Allah maji rokon bayinsa dawowarsu babu jimawa ikhlas ta soma zazzabi koda sukaje asibiti aka gano tana dauke da juna biyu, nan gida ya gauraye da murna, cikinta yanada wata biyar itama fadila ta soma nata laulayin, babu jimawa itama ihsan ta fara nata, wai ai murna awurin lamido ba acewa komai saboda ganin abin yake kamar a mafarki lallai Allah shine gwanin iya kyauta,shiryawa yayi ya koma umarah yaje yayi addu'a ya nunawa ubangiji godiyarsa,

Nan ya shiga riritasu ya samo musu masu aiki yanzu babu abinda suke yi agidan sai hidimarsa ikhlas kuwa idan abinda yafi mayen karfe to lamido ya zame mata domin wannan cikin da take dauke dashi manne mata yasa lamido ya sake yi, cikinta yana cika wata Tara daidai ta haifo santaleliyar yarinyarta mai kama da lamido sak nanfa lamido ya dau murna ya shiga nunawa jaririyar gata da ita kanta ikhlas din ranar suna yarinya taci sunan innarshi wato A'isha suna kiranta da humaira.

Duk wanda yaga humaira yasan yar gatace sosai kusan kullum tana cikin kwalliya gata kamarta daya da abbanta, su fadila da ihsan kusan tare suka haihu domin tsakaninsu kwana biyune kowacce ta samu da namiji, rana daya aka hada akayi suna yaran sukaci sunan Aliyu da umar.

  Lamido yanzu kam hankalinshi ya kwanta yayi kyau yayi fes domin babu wanda zai ganshi yace yanada mata biyu bare uku,

Watan humaira goma sha daya ikhlas ta tashi da zazzabi, shima lamido zazzabin yake yi dan haka yace taje asibiti, tunda taje gwajin farko akace tana da juna biyu,

Hankalinta atashe ta shiga gidan ta nufi dakin lamido yana kwance shida humaira ya lulluba da bargo, bude idonshi yayi yana kallon ikhlas,

Takardar test din da akayi mata ta ajiye masa akan hannunshi,

"Gashi nan daga zuwa sunce cikine dani ni dama nasan wannan zazzabin da kake tayi ba a banza ba"

Murmushi yayi ya lumshe idonsa, "to meye na fushin kuma? Ba kece kika hana zuciyata sakat ba, kece kika hanani son kowacce mace sai ke daya shiyasa kullum nake manne dake.. Allah ya raba lafiya, sai ki yaye Humairaa saboda karta sha ciki ko.."

Tashi tayi ta fita ta zumburo baki,fitowa yayi daga cikin bargon ya fita ya bita, tana zaune a gefen gadonta tana tsotsar goba, zama yayi ajikinta ya rungumeta yana cewa,

"Godiya ta tabbata ga Allah kwanan nan sai haihuwa aketa yi mana kinga xahar din bash itama ta kusa sauke yan biyunta,gaki kema kila yan biyun ne, saura fadila da ihsan"

Murmushi ikhlas tayi ta sake shiga jikinshi sosai,

"Ai gara ayita zube maka 'yayan ko ka tsufa da wuri in huta da amarya..."

Dariya yayi mata yaja hancinta, "tsufa? Ai ko na tsufa zan iya auro yarinya budurwa.."

Dagowa tayi ta kalleshi ganin irin kallon da tayi masa ya sashi rikicewa ya fara inda inda,

"Pretty da wasa fa nake yi miki, haba dai aure,wallahi da wasa nake"

"Kaji tsoro kenan?",tace dashi tana murmushi,

"Ehh naji, ai kin san tsoro wajibine..."

"Kaifa mai sunan mazaje ne bai kamata ka zama mai tsoro ba"

  Murmushi yayi ya rungumeta yana shakar daddadan kamshin turaren dake fita daga cikin jikinta,

"Allah dai yayi miki albarka pretty hakika kin zama wani bangare na rayuwata... I love you"

Murmushi tayi ta rungumeshi itama "i love you too abban sadiq..."

Rungume juna sukayi suna dariya...!

  ALHAMDULILLAH!

Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki wanda cikin amincewarsa da yardarsa na kammala wannan littafi mai suna ruwan kashe gobara, ina addu'ar Allah yasa ya amfanar damu baki daya.

  SADAUKARWA
Na sadaukar dashi gareki k'awata mai sona mai kaunata KHADIJA SIDI,ubangiji Allah yasa albarka acikin rayuwarki.

TUKWICI
Na bayar da ruwan kashe gobara tukwici babba agareku,

NANA HAFSAT (miss Xoxo)

SADIYA L BALA

ANISA A RIMI

A'ISHA (E'eshmal)

HAJJA (Maman Ihsan)

GAISUWA MAI YAWA

Gareki uwar dakina HAWWA M JABO,

INA JI DAKE..
Aminyar arziki KAUSAR LUV,Allah ya barmu tare

INA ALFARI DAKU
Hawwa jidda Aliyu
Besty na phertymah Xarah

KUNA RAINA

Fido Sodangi k'awata
Ummi Hambali
Batool Mamman
Momy sady Jegal
Baby lilmeerahcute
Mimi Bee
Anty bebeelo
Xarah bb
Aisha Dansabo
Teemah cool
Hafsat Bunxa
Humaira Zaria
Khaleesat haydar
Maman Ihsan
Stylish bich

KUN CANCANCI YABO
Big Aunties
Anty jamila moh (maman bobo)

Anty Adama (maman fatima)

Anty sis (maman sultan)

Anty Maijidda musa (maman twins)

Anty zubaida (maman ansar)

Anty Naseeba (maman Sadeeq)

Nagode da soyayyarku agareni ina addu'ar Allah ya raya muku zuri'arku yabarku da mazajenku, ya kara musu arzikin da zasu kawo muku abokan zama nagari......

Gaisuwar fatan alkairi agareku masoyana masu karanta rubutuna suna yimin addu'a ako yaushe, hakika ina alfahari daku kuma ina sonku fiyeda yadda kuke sona, duk wata masoyiyar ummi A'isha to ina gaisheta aduk inda take wannan gaisuwar taku ce, sai mun hadu cikin littafi nagaba mai suna RAMUWAR GAYYA.. Wanda zamu rubuta nida besty na phertymah Xarah, karku bari abaku labari,taku ahar kullum UMMI A'ISHA.

*_Ummi Shatu_*