Thursday 9 February 2017

RUWAN KASHE GOBARA.. 77

*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_

  _*NA*_

_*UMMI A'ISHA*_

   _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

aishaummi.blogspot.com

  *_77_*


~~~Jin maganar ikhlas yayi kamar acikin mafarki, yasan kawai ta fad'i hakane saboda tana son ta kwantar masa da hankali tunda ga yaran yan uwanshi nan suma a matsayin 'yayanshi suke sai dai ai duk kusancinsu dashi bai kai na wanda ya haifa gudan jininshi ba,

Rungumeta ya sake yi yaci gaba da kukan da yake yi,

"Pretty nasan kin fadi hakane saboda kawai kina son kwanciyar hankalina kina son zuciyata tayi sanyi amma ki sani wannan radadin dake cikin zuciyata yanzu bazai taba gogewa ba har na koma ga mahaliccina.."

Murmushi ikhlas tayi ta fara goge hawayen dake sintiri akan kumatunta,

"Abban sadiq abinda na fada maka gaskiyane amma ba zaka gane hakan ba har sai nan da wani lokaci, ka jirani ina zuwa"

Tashi tayi ta fita daga bedroom dinshi ta nufi nata tana zuwa ta dauki wayarta tafara kiran yaya Hussain duk kuwa da cewa gabanta sai faman faduwa yake domin tasan dakyar idan yaya hussain zai yarda ya dawo musu da abdallah sai dai kuma ai wata bukatar tafi wata domin yanzu lamido abin tausayine gashi matashi mai jini ajika kyakkyawa amma Allah ya jarrabeshi da lalura a matsayinshi na d'a namiji,

"Assalamu alaikum" ta jiyo muryar yaya Hussain ta cikin wayar yana yi mata sallama, hanzarin amsawa tayi ta hanyar cewa,

"Wa alaikumussalam, yaya hussain ina yini..?"

"Lafiya lau ikhlas yagida,ya sadiq?"

"Lafiya lau yaya, yasu anty farida?"

"Lafiya lau" ya bata amsa, shiru yaji tayi ta kasa magana saboda gaba daya bata sanma ta inda zata soma yi masa zancen tana son abdallah ya dawo hannunta ba duba da irin halaccin da yayi mata, ya zamewa abdallah uba, ya zama gatansa alokacin da bashi da wani gata sai na Allah,

"Ikhlas lafiya? Kodai wani abune ya faru?" Ta jiyo muryar yaya Hussain yana sake tambayarta,

"A'a yaya, dama dai ba wani abu bane..."

"Ikhlas kiyi magana mana, idan baki fada min damuwarki ba wa kike dashi wanda zaki fadawa bayan nida hassan?"

Daurewa tayi dakyar tace,

"Am yaya dama accident din da abban sadiq yayine ya samu matsala doctors sunce yanzu bazai sake haihuwa ba to kuma ya shiga damuwa sosai shine nace ko zaka dan bamu aron abdallah na dan wani lokaci?"

Murmushi yaya Hussain yayi mai dan sauti,

"Haba ikhlas dama akan wannan ne zaki tsaya inda inda, ni nayi tsammanin ko wani abune ya sake faruwa ai, zan baku abdallah bama aroba kyauta,ai abdallah dankune idan har na hanaku shi to banyi muku adalciba shi kansa yaron shima banyi masa adalci ba, insha Allahu yau dinnan zan aiko akawo muku shi amma dan Allah ku kula da tarbiyarsa sosai, kuma duk karshen term ku rinka kawo mana shi hutu duk da cewar nasan na shaku da shi hakama farida domin tana jinsa tamkar dan data haifa na cikinta amma hakan bazai hanani dawo muku da danku ba kamar yadda kuka nema...!"

K'wallar idonshi ya fara sharewa domin yayi mutukar sabo da abdallah, ita kanta ikhlas sai da taji wani iri amma bata zaci yaya Hussain zai basu abdallah cikin sauki haka ba,

"Mun gode yaya Hussain ubangiji Allah yayi maka sakayya da gidan aljannah"

"Amin ikhlas, anjima za akawoshi"

Yana gama fadin haka k'it ya katse wayar, tashi tayi duk jikinta yayi sanyi ta fita, fadila ta gani cikin shirin tafiya makaranta, sallama suka yi ta wuce dakin lamido, tareda ihsan ta samesu ihsan na zaune akan kafofinshi suna dariya amma da alama ita dinma ihsan din fita zata yi,

Juyawa tayi zata koma yayi saurin dakatar da ita,

"Zo mana yanmata na..."

Dawowa tayi da baya ta jiyo amma ta kasa kallon wurin da suke,

"Tunda ga maman sadiq tazo to sai ta dora daga inda na tsaya ni natafi sai na dawo" ihsan tace dashi tareda manna masa kiss a kumatunshi,tashi tayi ta zo ta wuce ta gefen ikhlas ta fita tana murmushi.

Ahankali ikhlas ta nufi gefen gadon taje ta zauna,

"Ai ba zama zakiyi ba ko ba kiji abinda ihsan ta fada miki ba? Kafafuna nake son a daddanna min.." Yace da ita yana kashe mata ido,

Daddanna mishi kafarshi ta fara yi ahankali shikuma sai faman lumlumshe idanuwa yake yi yana murmushi, kneel down tayi agefen gadon taci gaba da mammatsa mishi kafarshi,

Ahankali ya bude idanuwanshi wadanda suka yi ja ya kalleta,

"Pretty bar matsar kafar nan kizo kiji wani abu..."

Kafada ta makale tafara kokarin tashi zata gudu sai dai amma kafin ta tashin tuni shi ya rigata tashi kafin ta ankara sai jinta tayi kwance cikin fadeden kirjinshi,

"Wato da guduwa zaki yi ko?" Ya fada bayan ya hada fuskarshi da tata,

"Abban sadiq....!"

"Shhhhh" yace da ita tareda dora dan yatsanshi akan lips dinshi,

"Kina tsammanin yau zan kyaleki ne? Wallahi nima yau sai kin biyani bashina dake kanki kamar yadda na biyaki naki bashin rannan..."

"To kuma ai..."

Saurin katseta yayi, "da sanina yau na zauna agida babu inda zanje saboda ina son in baki lokaci sosai, kinga su ihsan ma basa nan"

Bai barta ta kara furta koda kalma daya ba ya dauketa akan kafadarshi.

Kamar yadda yace mata hakan ce ta kasance domin har azahar suna tare dakyar ya kyaleta ta fito ta shiga kitchen tayi musu girki kasancewar yanzu an daidaita ita dasu fadila kowa ranar girkinta gaba daya gidan zata rinka yi,

Taliya da macaroni ta dafa jalop ta hada da dankali ta hada zobo wanda yasha kayan hadi,akan dining ta shirya abincin ta nufi dakin lamido, yana kwance ya dora sadiq akan ruwan cikinshi yana jijjigashi,

Zama tayi ta karbi sadiq ta daga rigarta ta fara kokarin shayar dashi,tashi zaune lamido yayi ya rike hannunta,

"Yanzu kin daina boye min ko?.." Ya fada cikin tsokana, murmushi tayi ta rufe fuskarta da daya hannunta,

"Yanzu ai babu sauran boye boye domin ko da dinma da kike bobboye min na rigada na gani"

"Yaushe?"

"Lokacin da kina bacci" ya bata amsa yana yi mata dariya,

"Ka tashi kaje kayi salla dai kafin ka makara"

"Ke nake jira ai gimbiya.."

Ji tayi ya matsa da karfi take sadiq ya kware ya fara tari,

"Kagani ko? Ka sakashi ya kware"

"Sorry yarona, laifin mamanka ne"

Murmushi tayi ba tare da ta bashi amsa ba domin tasan neman magana ne kawai.

  Misalin karfe 8:30 mai gadi ya shigo yace ikhlas tayi baki lokacin suna zazzaune dukkaninsu a falo suna kallo, hijabinta ta dauka ta fita tana zuwa taga abokin yaya Hussain ne da abdallah, rungumeta abdalla yayi yana murna, kallonshi ta tsaya yi domin ya sake girma a yan kwanakin nan da bata ganshi ba gashi kamarshi da lamido ta sake bayyana komai nashi iri dayane da na lamido sak,

Katuwar trolley din abdalla ta dauka taja suka bi ta kofar baya suka shiga cikin gidan,ta falon lamido suka bi zuwa bedroom dinta, abakin gado ta zaunar da abdallah tace ya zauna tana zuwa,

Falo ta koma wurinsu fadila ta dauki sadiq, da ido tayiwa lamido nuni da ya biyota, tana tafiya ko minti biyu ba ayiba ya tashi yabi bayanta, bedroom dinta ya shiga amma tun daga falo yake jiyo magana irinta yaro,

"Anty yanzu anan zan zauna ko?, uncle Hussain yace bazan koma gidanshi ba sai dai ina zuwa hutu"

"Ehh abdallah yanzu kaima ka dawo wurin abbanka"

"Anty ina abban nawa?"

Daidai lokacin lamido ya shiga cikin dakin, ganin yaro yayi wanda zai kai shekara 7 a duniya yasha jeans baki da farar yar t shirt amma baya hango fuskarshi kasancewar yaron ya bashi baya,

"Abdalla ga abban naka nan maza jeka wurinshi ka gaisheshi.."

Ta fada tana yiwa abdallah nuni da lamido, da gudu abdallah ya nufi lamido yaje ya rungumeshi yana murna, kusan suman tsaye lamido yayi, dago fuskar yaron yayi yana kallonshi take zuciyarshi ta shiga bugawa da karfi saboda ganin kamar da yaron yayi dashi tamkar shine lokacin da yana yaro,

"Pretty....waye... Wannan?"  Ya tambayi ikhlas cikin rawar murya,

"Abban sadiq yaronka ne, gudan jininka ne" ikhlas ta fada tana share kwallar da ta ciko idonta,

Jan hannun abdallah lamido yayi har zuwa wurin da ikhlas take, akusa da ita ya zauna yaja abdallah jikinshi ya rungumeshi tsam,

"Pretty ban fahimci abinda kike nufi ba, me kike son sanar dani?"

"Abban sadiq abdallah danmu ne nida kai.."

Cikin sauri ya juya ya kalleta sai kuma ya dago abdallah daga jikinshi yana kallonshi daga sama har kasa, tabbas sunyi kama da yaron mutuka to amma ta yaya suka samu wannan yaron? Wannan tambayar itace ya gagara nemo amsarta acikin kwakwalwarshi,

"Daddy ina yini... Anty tace kaine daddy na, zaka rinka kaini school ko? Duk abokai na daddynsu ne yake kaisu school nine kadai uncle Hussain yake kaiwa.." Muryar abdallah ta dawo dashi,

Rungumeshi lamido yayi yana shafa kansa duk tausayin yaron yagama mamaye zuciyarshi sannan ga wani son yaron da yake shigarsa kota ina domin ji yake a duniya bai taba son wani abuba kamar yanda yake son abdallah,

"Ehh abdallah insha Allahu kaima daga yau zaka fara ganin gata irin wanda kowanne uba yake nunawa danshi, daga yau kaima nine zan rinka kaika school da duk wurinda kake so..."

Rungumeshi abdallah ya sake yi yana murna "i love you daddy..."

Wasu hawayene suka shiga zarya a kumatun lamido, "i love you too my boy.." Lamido yafada cikin hawaye,
Zamewa abdallah yayi daga jikin lamido ya nufi trolley din kayanshi yaje ya bude ya ciro lollypop ya kawowa lamido,

"Daddy ga sweet na kawo maka"

Karbar lollypop din lamido yayi yana murmushi, barewa yayi ya saka a bakinshi ya soma tsotsa sannan ya cire ya sakawa abdallah a baki yana murmushi,

Ita dai ikhlas tana zaune tana kallonsu hawaye sai bin kumatunta suke yi na tausayin lamido da abdallah,

"Pretty kar dai fyaden da nayi mik...." Ikhlas ce tayi saurin rufe masa baki da hannunta bata barshi ya karasa abinda yayi niyyar fada ba, girgiza masa kai ta shiga yi saboda bata son abdallah yaji,

Mikewa lamido yayi ya sunkuci abdalla ya fita ya nufi falo, mamakine ya kama su fadila saboda ganinshi da suka yi dauke da yaro,

Zama yayi ya dora abdallah akan cinyarshi yana murmushi, "abdallah baka gaida su anty ba"

"Anty ina wuni, anty ina wuni?",abdallah yace dasu yana kwantar da kanshi ajikin kirjin lamido,

"Fadila, ihsan ga yarona abdallah,nida ikhlas ne iyayenshi amma bata hanyar aure muka sameshi ba, dalilin da yasa kuka ji na fada muku wannan maganar kai tsaye shine saboda bana son kujita awani wuri ko a bakin wani ba niba kunga idan hakan ta kasance zaku ga kamar na rufe muku wani sirri wanda ni kaina nasan dole sai ya bayyana watarana, amma ina son ku sani kaddara ce tayi sanadiyyar da har muka haifi wannan yaron sannan wani nufine na ubangiji wanda shine kadai yasan abinda yake nufi da haka tunda gashi yanzu ya jarrabeni da lalurar da may be har nabar duniya bazan iya sake samun d'a ba"

Ya karasa maganar yana goge kwallar idonshi,daga fadila har ihsan duk sai da suka razana da jin kalamanshi,

"Ba zaka sake haihuwa ba fa kace?" Fadila ta tambayeshi arude,

"Hakane fadila domin haka likitoci sukace, na boye muku ne saboda bana son hankalinku ya tashi amma yanzu ya zama dole na sanar daku saboda bana son na cutar daku domin kunga ku har yanzu yarane daga ke har ihsan babu wacce ta haura 25 ikhlas ma ta girmeku sosai, dan haka kuna bukatar haihuwa so idan har kunga bazaku iya zama dani babu haihuwa ba zan sawwake muku zamu rabu cikin farin ciki da girmama juna saboda ni yanzu kunga naga gudan jinina kuma nasan kuna da bukatar ganin naku gudan jinin dan haka na baku kwana biyu kowaccenku tayi tunani inyaso idan ta yanke shawara sai ta sanar dani.."

Yana kaiwa nan ya mike kwalla cike a idonshi ya kama hannun abdallah suka yi ciki, daga ihsan har fadila suman zaune suka yi saboda jin wai lamido bazai haihu ba, sannan zahiri duk wanda yaga abdallah to yaga danshi saboda tsananin kamar da suke yi,to su yanzu menene mafita agaresu?

Dakin ikhlas lamido ya shiga yana rikeda hannun abdallah, har lokacin tana zaune a inda suka tafi suka barta amma ta daina kukan da take yi dazu, zama Lamido yayi ya kwantar da abdallah ajikinshi,

"Abdallah zakaci abinci..?" Yace da abdallah yana Shafa kanshi, girgiza kai abdallah yayi

"Daddy na koshi munci abinci tareda abokin uncle, bacci nake ji"

Kwantar dashi Lamido yayi ya dora kanshi akan cinyarshi ya juya yana kallon ikhlas,

"Pretty ki wayar min da kai agameda abdallah dan Allah"

"Abban sadiq lokacin da kayi min fyade nasamu ciki lokacin, ashe har rabo ya shiga batare da kowa ya sani ba har sai da na koma gidan mahaifina...." Nan ta kwashe labarin komai ta sanar dashi da irin wahalar da tasha wajen zubar da cikin abdallah da korarta da mahaifinta yayi daga gidansa har komawarta Maiduguri wurin mahaifiyarta har kawo lokacin data haifi abdallah,

Tashi lamido yayi ya koma kusa da ita ya rungumeta yana jin tausayinta yana ratsata,

"Allah sarki pretty, hakika ni mutumne mai babban laifi agareki, nayi miki fyade, nayi miki cikin shege, na rabaki da mahaifinki sannan na jefa rayuwarki cikin kunci, wahala, da damuwa,tabbas na cancanci dukkan wani horo daga gareki komai girmansa, nasan wannan abin da nayi miki ba zai taba barin zuciyarki ta soni ba.."

Jin saukar hawayenshi akan wuyanta ya sata dagoshi tana murmushi, ido ta zuba mishi tana kallon kyakkyawar fuskarshi mai sanyaya zuciyar duk wani ma'abocin kallonta, hannuwanshi ta kama ta rike cikin nata tana matsasu ahankali,

"Waye yace maka bana sonka?? Nafara sonka tun ranar dana fara ganinka a hoton bikinmu nida marigayi,kar ka kara tunanin wai bana sonka, ina tsananin sonka handsome"

Zuba mata ido shima yayi yana kallonta wani irin shauki yana ratsa zuciyarsa domin bai taba zaton irin wannan soyayyar daga gareta ba sakamakon laifin da yayi mata,

Idonshi ta bushe mishi da iskar bakinta, "meye kake kallona?" Ta tambayeshi tana kallon idanuwanshi, bai iya bata amsa ba illa kallonta da yaci gaba dayi hakan ya sata kaiwa bakinshi kiss,

"Ikhlas kiyi hakuri ki yafe min abinda nayi miki dan Allah, hakika naji dadi da wannan cikin bai zube ba da ace ya zube da yanzu bamu samu abdallah ba da shikenan bani da d'a a duniya.."

"Ya isa abban sadiq, ni na dade da yafe maka, karma ka sake yimin wannan maganar dan Allah"

Murmushi ya soma yi ya matsa tsakiyarsu abdallah da sadiq ya kwanta ya sasu a tsakiya,

"Ban ganeba, ya naga kazo ka kwanta anan? Yau fa ba ranar kwanana bane, kwanan ihsan ne ko ka manta ne?" Ikhlas tace dashi,

Tashi yayi tareda jan dan karamin tsaki domin shi yama manta da batun wani ba kwanan ta bane,

"Kizo muje dakina mu kwana, su ihsan akwai abinda nake son mu tattauna dasu kafin naci gaba da ziyartar dakunansu"

Make kafada ikhlas tayi, "a'a babu ruwana, kaje kawai"

"Ba zakije ba?" Ya tambayeta yana kallon ta,

"Uhmm" ta bashi amsa, tashi yayi cikeda jin haushi ya sunkuya ya dauki abdallah ya fita, binshi tayi da kallo tana murmushi saboda ganin har yayi fushi akan taki binshi dakinshi amma shine bai saniba ita dinma bata bukatar tayi bacci ba tare dashi ba domin akwai wani sirri na musamman dake tattare da yin bacci tareda lamido, murmushi ta sakeyi akaro na biyu ta tashi ta sauya kayan jikinta izuwa kayan bacci ta haye gado ta kwanta.

Lamido kai tsaye dakinshi ya shiga ya kwantar da abdallah a tsakiyar gadonshi  ya shiga wanka, kayan bacci yasa yaje ya kwanta ya zubawa abdallah ido yana kallonshi kusan komai na yaron irin nashine sak babu banbanci, rungumeshi yayi yana dokin gari ya waye domin yaje yakaiwa su innah shi suganshi sannan ya nunawa bash shi,kasa bacci yayi sai faman juyi yake daga karshe ya tashi ya shiga bathroom ya dauro alwala yazo ya tada salla.

_Gaisuwa mai tarin yawa ga masoyan ruwan kashe gobara, na gaisheku aduk inda kuke...!_

*_Ummi Shatu_*

No comments:

Post a Comment