Tuesday 28 February 2017

RAMUWAR GAYYA.. 7

*RAMUWAR GAYYA..*💘


  _Love story 50,50_

  *_UMMI A'ISHA_*

          _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*

   *_7_*

*A*fusace ya juya yabi bayansu yana huci zuciyarsa na tafarfasa abinka da dogo taku kad'an yayi ya cimmusu,

Hijabinta ya fizgo afusace take hijabin ya yage daga wuya,

"Ke wai ke wacece? Me kike takama dashi da har zaki rinka shiga gonata..."

Abokanshi ne suka katseshi ta hanyar janyeshi daga wurin suna bashi hakuri,

"Haba 3 pointer kar ka biye mata mana, ai kai namiji ne me zai saka fada da mace, ai ba afada da mace..."

Har lokacin ummulkhair da alawiyya suna tsaye awurin hakama mutane duk sun jujjuyo suna kallonsu amma ko uffan ummulkhair bata ce ba in banda binsu sawwam da kallo babu abinda take gashi gabanta sai faman faduwa yake domin ba karamin tsorata da yanayinshi tayi ba ayanda fuskarshi ta nuna to yana iya dukanta a wannan lokacin sai dai Allah ya rufa mata asiri an ceceta bai samu damar dukanta ba,

Jan hannunta alawiyya tayi suka bar wurin domin har mutane sun fara cece kuce kowa yana fadin albarkacin bakinsa,

Wuyan hijabinta taja ta gyara domin duk yanzu yayi mata yawa sakamakon yagashin da sawwam yayi,

"Yanzu kin dai ga irin abinda naketa fada miki amma kika yi biris dani kika ki daukar shawarata,

Tun ba aje ko inaba kinga kin fara ganin abinda na jima ina guje miki, yanzu me amfanin haka agaban mutane ya yaga miki hijab dinki, kuma wallahi ma Allah ne yasoki da rahama da bai mammareki ba domin ya zuciya.."

Murmushi ummulkhair tayi,

"Ni kaina na tsorata dashi wallahi dan daga ganinsa kin san zaiyi zuciya sai dai fa amma naji dadi da ranshi ya baci dama ni burina shine yaji haushi sannan yaji kunya, to duk gashi hakan ta faru at the same time...."

"To nidai shawarata agareki akaro na karshe shine ki fita daga hanyarshi domin nasan shima ba hakura zaiyi da abinda kika yi masa ba, so idan ya rama ki rabu dashi shikenan kunyi 50,50.."

Sake murmushi ummulkhair tayi "insha Allah daga wannan karon zan rabu dashi bazan sake kulashi ba duk da nasan sai ya dau fansa akan abinda nayi masa.."

"Yawwa naji dadin wannan maganar taki, dan Allah kiyi kokarin kai zuciyarki nesa.."

"Insha Allah, bari naje hostel na canja hijab dinnan.."

Sakin hannun alawiyya tayi ta wuce zuwa hostel ta cire hijab dinta ta saka wani ta koma wurin alawiyya.

  Sawwam ba karamin haushin abinda ummulkhair tayi masa yaji ba gashi abokanshi sai faman tsokanarshi suke,

"Three pointer gashi nan a bayanka wooooohhhh"

Tun abin yana bashi takaici har ya dawo yana dariya, wuni suka yi acikin school din sai yamma sannan ya fita zuwa gida,

Yana shiga falon Mami ya isketa itada mahaifinshi akan dining table sai lokacin suke cin abincin rana,

Idonshi ya daga ya kalli agogon bangon dake sakale acikin falon, karfe 5 har da yan mintoci agogon ya nuna,

"Mami sai yanzu kuke cin abincin rana..?"

Karasawa yayi yaja kujera ya zauna akusa da dad dinshi,

"Dad barka da yamma"

Kallonshi mahaifin nashi yayi yana murmushi, farin ciki tsantsa bayyane akan fuskarsa gamida walwala domin yana mutukar kaunar tilon dan nashi,

"Sawwam barka dai, ya karatun?"

Sai da ya dan yamutsa fuskarshi sannan yace "alhamdulillah dad but akwai wahala gaskiya especially ma wannan semester din.."

Sai da dad din ya tura masa filet din abincin da yake ci gabanshi domin suci tare kasancewar koda wanne lokaci indai yana gida to tare suke cin abinci,

"Ai haka abin yake sawwam shi karatu aduk lokacin da yazo karshe to yafi bada wahala shiyasa kaji bahaushe yace idan aski yazo gaban goshi to yafi zafi.."

Spoon sawwam ya dauka yasa acikin abincin dad din ya fara diba yana ci yana murmushi,

"Dad to idan na kammala karatuna successfully wanne albishir zaka yimin..?"

"Sawwam kenan ai a wannan lokacin zan siyo maka new brand car, sannan zan baka makuden kudi domin kayi dukkan abinda kake son yi kaje duk kasar da kakeso, sannan ina nan ina yi maka ginin gidan da zaka zauna kai da matarka amma bazan kaika gidan ba har sai an kammala because inaso ne na baka mamaki..., and kafin wannan yanzu na biya mana umara dani dakai daga yanzu zuwa kowanne lokaci visa dinmu tana iya fitowa.."

"Woowww, thank you dad"

Sawwam yafada yana murmushin jin dadi,

"Nidai Alhaji aduk maganganunka babu abinda ya kayatar dani kamar maganar aurenshi da kayi,

Narasa me yake damun yaron nan har yau ya kasa fitar da matar aure shi ko budurwa ma ina jin bai taba yiba.."

Murmushi dad yayi yana kallon sawwam "dan gidan daddy ko tsoron yanmatan kake yine??" Dad ya fada cikin barkwanci,

Ajiye spoon din hannunshi yayi yafara shafa keyarsa yana sunkuyar da kai,

"Dad ba haka bane ni wallahi ban taba yin budurwa bane,kuma har yanzu banga wacce tayi min ba.."

"Amma tun yaushe nake kawo maka yanmata gidan nan akan ka duba ko zaku fahimci juna amma kaki, idan lissafawa za ayi yan matan da suka zo gidan nan sunfi su talatin.." Inji mom,

"To ya dai isa haka, idan anyi hakuri ai shi da kanshi watarana zai kawo mana wacce tayi masa ko sawwam?"

"Yes dad" sawwam yafada yana murmushi,

"Kai dama goyon bayansa ai nasan zakayi saboda baka son laifinsa"

Tashi mom tayi ta bar musu wurin ta koma cikin falo domin ita tana son sawwam yayi aure da wuri basai ya zauna dogon boko ba ita tafi son yayi aure a yan shekarun nan domin yanzu shekarunsa 27.

  Tun daga wannan rana sawwam bai sake ganin ummulkhairi ba duk da cewar kullum yana zuwa makarantar,

Yau kwananshi uku rabonshi da ita, acikin kwana na hudune suna zaune karkashin bishiya shida friends dinshi shikuma yana saman motarshi a zaune,

Wata yagani ta fito daga hostel tana sanye da hijab har kasa ta rufe fuskarta da bakin nikab, kallo daya yayi mata yaganeta duk da shi bai cika kallon mata ba musamman ma idan mace ta saka wannan abin a fuskarta, hakan ya bashi dariya dole sai da ya dan murmusa,

Ita dinma tun daga nesa take kallonshi yasha kananan kaya Riga t shirt milk colour mai dogon hannu da bakin jeans kamar koda yaushe fuskarsa saye cikin bakin glass...

Phertymah 1

2 comments:

  1. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  2. Great literally it's an amazing post I have ever seen please allow me to get your feed to keep up to date with your valuable quality posts. cash for cars ipswich

    ReplyDelete