Thursday 9 February 2017

RUWAN KASHE GOBARA...! 76

*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_

   *_NA_*

_*UMMI A'ISHA*_

  
    _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

  aishaummi.blogspot.com

  *_76_*

~~~Cikin d'aki ikhlas ta koma ta kwanta akan gadonta ta rungume sadiq tana tuna Lamido da daddadar rayuwar da suka gudanar acikin kwanaki biyun nan sai dai kuma duk jikinta jinsa take ya gama yin sanyi gashi zuciyarta sai harbawa take yi da sauri,

Lumshe idanuwanta tayi tana jin kamar ta kira lamido tace masa ya fasa yin tafiyar nan saboda hankalinta bai kwanta ba,

Tana nan kwance sai juyi take yi tana tunaninshi da zarar ta rufe idonta babu abinda take gani sai kyakkyawar fuskarshi yana yi mata murmushi, bude idonta tayi ta kalli sadiq wanda ke kwance yana bacci, sake lumshe idonta tayi tana ci gaba da tunanin lamido, duk abubuwan da suka faru tsakaninsu da irin soyayyar da yake nuna mata idan sun kebe su biyu sai da duk kwalwalwarta ta tariyo mata su, fuskarta dauke da murmushi bacci ya saceta.

Abangaren lamido kuwa driving yake yi amma tunaninsa yana ga ikhlas domin duk wani motsin zuciyarshi itace kwata kwata bai san wanne irin so yake yi mata ba a rayuwarshi,

Murmushi ya saki ya shafi sajenshi domin tunota da yayi da rakin da take nuna mishi idan suna tare hadida shagwabarta da take yi mishi,

"I love you pretty" ya fada ahankali tareda daukar wayarshi wacce ke faman ruri,

"Hello bash.."

"On top ya akayi ne..."

"Ka ganni a hanya bash idan naje zan kiraka"

"To asauka lfy amma wallahi ba girmanka bane zuwa abuja a mota kamata yayi ka tafi by flight.."

"Ina son tsayawa awurin budurwata ne a Kaduna shiyasa"

Dariya bash yayi yace "wannan maganar kamar a kunnen ikhlas, sai na fada mata idan naje gidan anjima"

"Wohhhh, bash kar ka fada mata dan Allah, ka rufa min asiri wallahi idan ikhlas taji na kad'e tsaf... Wallahi ikhlas ta wuce yanda kake tunani akan kishina"

Dariya bash ya sake yi "ka godewa Allah domin ya baka mata kyawawa tamkar jera maka matan duniya akayi gaba dayansu ka zauna ka zabo kyawawan ciki.."

"Kai bash bari fa, nidai dan Allah karka fada mata kodan nasan maganinka bari ma na kirata yanzu before kaje gidan"

Katse wayar yayi ya fara kiran ikhlas wacce keta faman bacci,

Cikin bacci ta jawo wayar ta dauka ta kara a kunnenta,

"Pretty..." Ya fadi ahankali,

"Washh, abban sadiq ko har ka sauka ne.."

Murmushi yayi ya sake gyara wayar a mazauninta,

"Wai bacci kikeyi ne.."

"Uhmmmm" ta bashi amsa,

"Baccin jiya bai isheki bane?" Ya fada cikin tsokana,

"Uhmm" ta sake bashi amsa,

"Haba?"

Juyi tayi da wayar a kunnenta ta rungume pillow,

"Ba kai bane ka hanani..."

Murmushi yayi mai dan sauti, "to kiyi hakuri nan gaba zan barki kiyi har sai kince kin gaji da baccin"

"Abban sadiq kaine zaka bar mutum yayi bacci? Hmm wallahi ba zaka iya ba"

"To ai ni pretty ke dince rudani kike yi shiyasa bana iya hakuri dake amma ni ke kadai nake yiwa wannan nacin, Allah idan bake bace zan iya yin 1 month ba tare da..."

"Wa fa?" Ta tambayeshi

"Mace,tunda na sameki naji kishin ruwana ta tafi, yanzu bana bukatar kowacce mace bayanki" ya bata amsa yana murmushi,

"Abban sadiq kaga driving kake yi,idan ka sauka za muyi magana"

"To tunda korata kike shikenan, Allah sarki ni, bani da gata" ya fadi cikin kalar tausayi, kafin tayi magana har ya fara kissing dinta ta cikin wayar,

"Nagode abban sadiq" tace dashi tana murmushi saboda har yasa tsikar jikinta ta fara tashi,

"Sai munyi waya" ya fada tare da katse wayar,

Juyi tayi ta ajiye wayar tana murmushi, "abban sadiq rigima" ta fadi ahankali,sake kwanciya tayi nan wani baccin ya dauketa.

  Misalin karfe biyar na yamma a hanyar abuja motar lamido ta samu matsala burki ya tsinke, wani katon rami motar ta nufa taje ta fada, nan mutane suka taru aka fara kokarin fito da ita domin lokacin da abun ya faru anyi sa'a akwai mutane awurin, sai da aka nemo kugiya sannan aka samu damar fito da motar tashi, dakyar aka zaro Lamido wanda yayi dogon suma aka nufi asibiti dashi.

Baffa aka yiwa waya aka sanar masa da accident din, arude ya nufi sashen innah yaje yace itama ta shirya zasu tafi abuja yanzu,

Babu wanda baffa ya fadawa su biyu suka tafi sai da dare ya raba sannan suka karasa asibitin da lamido yake, jikinshi duk ya yanyanke da glass,

Likita ne ya kira baffa yayi mishi bayanin cewar lamido bai karye ba kuma baiji koda targade ba sai dai amma yasamu babbar matsala domin glass ya yankeshi ya sake masa sabuwar kaciya wanda har suna ganin ba zasu iya yi mishi aiki ba sai dai in a fitar dashi kasar waje sannan glass din ya dan yanyankeshi,

Fitowa daga office din likitan baffa yayi yana goge kwallar idonshi hankalinshi duk ya gama tashi, innah ya samu ya yiwa bayani kamar yadda likitan yayi masa, cikin tashin hankali ya kira bash ya fada masa abinda yake faruwa,

Karshen tashin hankali bash yajishi a wannan lokacin domin dama ya jima yana kiran wayar lamido amma bai sameshi ba, suna gama waya da baffa gidan lamido yaje lokacin da yaje ma duk sun kwanta kowacce tana dakinta,zagewa bash yayi ya rinka kwada sallama iya karfinshi,

Ikhlas ce ta fara fitowa ta amsa sallamar dama sam ta kasa bacci domin hankalinta atashe yake saboda ta kasa samun lamido a waya,

Tunda taga bash tasan akwai abinda ya samu lamido, dakin ihsan ta nufa akaro na farko domin bata taba shigaba sai yau, tasota tayi ta fito ta shiga dakin fadila itama ta tasota, ganin su duk hankula atashe yasa bash kasa magana,

Nan kuma duk hankalinsu ya kara tashi saboda sun fahimci lamido ya mutu kasa fada musu bash yayi, kuka fadila da ihsan suka soma yayinda ikhlas kuma ta shiga addu'a tana hawaye, dakyar bash ya iya dakatar dasu ya fada musu cewar lamido bai mutu ba yana raye amma yana asibiti, ai suna jin haka suka ce basuga ta zama ba tafiya zasuyi a daren, babu yadda bash baiyi dasuba akan su bari sai gobe da safe amma suka ki,

Acikin daren suka kama hanya, bayan sallar asuba suka shiga garin abuja,lokacin da sukaje asibitin innah suka iske tana zaune a reception tana ta faman jan carbi shikuma baffa ya tafi cuku cukun yanda za ayi asamu visa domin fita da lamido kasar India,

Tare suka dunguma da innah zuwa dakin da lamido yake, yana kwance idanuwanshi arufe da alama ma baya cikin hankalinshi, cika dakin su fadila suka yi da kuka in banda ikhlas wacce hawaye kawai take yi tana addu'a acikin rants gaba daya tausayin lamido take ji.

Sai wurin karfe 9 na safe sannan baffa ya dawo tareda yayan lamido nan suka rankaya wurin likitan suka kara samun bayani dangane da lalurar data samu lamidon.

Kwanan lamido Biyar a asibitin ana jinyarshi su ihsan kuwa kullum cikin kuka suke aranar aka samu visa tafiya India ta tashi, amma visa din ta mutum biyu aka samu dan haka baffa yace da Lamido da fadila ne zasu tafi tunda fadila itace uwar gida, da kuka duk suka rabu bayan sun rakasu airport, daga nan kuma yola suka koma.

Ikhlas dai faruwar wannan lamari yasa ta rasa nutsuwarta amma kullum cikin yiwa lamido addu'a take akan Allah ya bashi lafiya, bacci kuwa rabonta dashi har ta manta duk tabi ta rame ta kanjale kullum kwana take tana salla tana yiwa lamido addu'a, yanzu tsakininta da ihsan zamane na zumunci da mutumci domin tunda wannan abun ya faru ihsan din ta sauke abinda ke kanta.

Satin lamido uku acan ya warware amma sai dai tunda ya fahimci abinda ya sameshi yaji hankalinsa ya tashi, ikhlas ya kira awayar fadila amma koda ta dauka sai ya kasa yi mata magana hawaye kawai yake yi jin yakasa yin magana sai kuka yasa hankalin ikhlas ya tashi nan itama ta shiga rera kukan, kullum aikin kenan kuka shi kuka ita kuka kafin wani lokaci tuni har hawan jininshi ya sake bunk'asa sai dakyar likitoci suka samu nasarar saukar dashi,

Watanshi daya da sati biyu aka sallamoshi suka tattaro suka dawo gida shida fadila bayan likitoci sun bashi lokacin dawowa domin za asake dubashi, ranar da zai dawo ranar ikhlas kamar za tayi me dan murna, daga ita har ihsan haduwa suka yi suka shirya masa kayan sauka sannan suka gyara gidan, karfe biyu dai dai na rana su lamido suka sauka bash yaje ya daukosu,

Lokacin da suka shiga gidan ikhlas da ihsan suna zaune a falo suna jiran dawowarsu, ai suna shigowa ihsan ta tashi da gudu taje ta rungumeshi, rungumeta yayi yana kallon ikhlas wacce ke zaune ta danyi ado cikin wata brown din atamfa, itama ikhlas din shi take kallo tana murmushi, idonshi guda daya ya kashe mata,sunkuyar da kai tayi ta sake dagowa har lokacin ita yake kallo suna hada idanu yayi mata nuni da ta zo gareshi, kafada ta makale tana murmushi, sakin ihsan yayi dukkaninsu suka nemi wurin zama,

Bayan yan gaishe gaishe su ikhlas suka gabatar musu da abinci, ikhlas ce ta matsa gabanshi tana zuba masa abincin kugunta ya riko yajata jikinshi ya matseta, gaba daya ikhlas ji tayi kunya ta rufeta domin gasu fadila awurin sannan ga bash yana nan, da kyar da dabara ta samu ta zame daga jikinsa ta nufi bedroom dinta domin tana tsammanin sadiq ya tashi,

Tana zama agefen gado lamido na shigowa, abayanta ya zauna ya rungumeta bayan ya dora kanshi akan kafadarta daya,

"Wato shine ko gaisawa ba zaki tsaya muyi ba ko?" Ya rada mata acikin kunnenta,

"Kayi hakuri abban sadiq ai kaga ba mu kadai bane awurin"

"Naki wayon" ya fada yana wasa da jelar gashinta wanda yake tufke akan dokin wuyanta,

"Yaya jikin naka?"

Ajiyar zuciya ya sauke yasake kwanciya ajikinta "jiki da sauki pretty amma sai na sake komawa next month..."

"Ai babu komai insha Allah zaka samu lafiya"

"Allah yasa pretty"

"Amin" ta bashi amsa tana zame hannunshi,

"Meye haka kuma?" Ya tambayeta cikin shagwaba,

"Abban sadiq daga dawowarka kuma sai...."

Hannunshi yasa ya rufe mata baki, "shhhhh ya isa tunda rowa zaki yimin shikenan bari natafi"

Saurin rikeshi tayi tana murmushi,

"Yi hakuri abban sadiq"

Bakinta ya zubawa ido yana kallon yanda take yi masa magana bata fargaba taji ya dora nashi bisa nata.

A ranar da suka dawo da daddare su baffa suka zo suka dubashi, sun dade tare har wurin karfe 10 sannan suka tafi, dakin ikhlas ya shiga kai tsaye tana kwance ita da sadiq tana feeding dinshi,

Bayanta yaje ya kwanta ya rungumeta, gaba daya ya gama kanannadeta acikin jikinshi yana shakar kamshin jikinta,

"Abban sadiq..."

"Anan zan kwana pretty, kasantuwa ta dake ne kadai zai rage min radadin abinda ke damuna"

Shiru tayi masa bata bashi amsa ba domin ahaka dai gashi nan zaka ganshi kamar lafiyarsa kalau amma kuma ba lafiya lau din yake ba, wasu zafafan hawaye ta fara yi saboda tsananin tausayinshi, sadiq ta matsar daga jikinta ta juya ta rungume lamido tsam tsam ajikinta tafara shafa sumar kanshi, tana jinshi sai sauke ajiyar zuciya yakeyi lokacin da yana baccin,wani irin tausayinshi taji yana shigarta, kissing din bakinshi tayi ta sake rungumeshi.

Tunda ya dawo gidan nasu kullum baya rasa mutane yan dubiya har yan maiduguri ma sunzu dukkaninsu sun dubashi, kwananshi Biyar da dawowa ya koma office yaci gaba da harkokinsa, da misalin karfe biyar ya dawo gida yana zaune a babban falo yana aiki a laptop dinshi su fadila itada ihsan suna gefe daya suna shirya wata kujerar hutawa suna daureta da notina ita kuma ikhlas tana kusa da lamido azaune tana rikeda sadiq suna yin hira amma su kadai suka san abinda suke cewa ko su fadila basa jiyo abinda suke fada kawai dai sun ganshi yana murmushi,

"Wallahi kika kuskura kika yaye min yaron nan da wuri ko, hmmm" yace da ikhlas yana murmushin mugunta,

"Ban ganeba, me zaka yi?" Ikhlas ta tambayeshi tana kallonshi,

"Me kuwa zanyi miki? Babu abinda zanyi miki amma sai kinji dama ace baki yayeshi ba"

Murmushi tayi "to ai babu damuwa indai dan hakane yana yin wata goma sha biyu zan yayeshi"

"To ki yayeshi kigani"

"Me zanga? Da ban gani ba sai yanzu?"

Dariya lamido ya fara, "ki fito fili ki fadi abinda kike son fadi, nasan manufar maganarki nufinki da banyi miki ciki ba sai yanzu da banida lafiya ko? Zaki sha mamaki ne pretty ki gama hasashenki akaina daga karshe kuma kisha kunya"

Dariya ikhlas tafara shima lamido dariyar yake yi yana kallon laptop dinshi, shigowar bash ce ta katse musu hirar tasu,

"Ah kaga mijin Mace hudu, mijin fadila da ihsan da ikhlas da amarya mai zuwa xahar" bash yafadi cikin tsokana,

Dagowa lamido yayi ya kalli bash yana cewa,

"Ban son hadi bash wacece kuma wata amarya me zuwa?" Ya fada yana satar kallon ikhlas wacce tayi kamar bata san abinda suke fada ba,

"Budurwarka mana xahar, wallahi ta kirani jiya saboda tana ta son ganinka to amma tace bata son tazo gidanka"

"Malam ya isheka haka muje na baka sakonka yana cikin mota" lamido ya fada bayan ya tashi yaja hannun bash zuwa waje, suna fita ya daki kafadarshi,

"Kai bash yau ka hada min bomb agidan nan, meyasa zaka yimin wannan tonon asirin agaban pretty, wallahi yau ka jawo min rigima saboda har yau bata san da xahar ba su fadila ne kawai suka santa"

Dariya bash ya fara "kajika ai to menene dan ikhlas taji? Ba aurenta itama xahar din zaka yi ba?" Bash yafadi cikin tsokana,

"Bawani nan malam nidai kawai ka tada min da rigima zaka tafi ka barni da ita batare da nasan ta inda zan fara kokarin kwantar da ita ba..."

Juyawa lamido yayi ya shige cikin gida yabar bash tsaye anan, yana zuwa falo yaga ikhlas bata nan sai su fadila, dakinta yabita a falo ya isketa zaune tana daddanna wayarta,

Zama yayi akusa da ita ya tarairayota jikinshi gaba daya,

"Pretty.." Ya kira sunanta yana kai mata kiss a goshinta,jin bata amsa mishi ba yasashi sake matseta acikin jikinshi

"Wasa fa bash yake yi miki, ni wallahi babu auren da zanyi, wallahi Allah ni babu wata mace wacce nake so bayanke kuma babu wacce zan sake aurowa ku ukun nan kun isheni"

Sai alokacin ikhlas tayi magana "ai ba laifi bane dan ka kara ta hudun"

"Haba pretty sai kace wani inji? Mata hudu fa, tab gaskiya bazan iyaba"

Duka ta kai mishi a kirji tana dariya "kaima fa lazy ne,yanzu dama ba zaka iya kulawa da mata hudu ba?"

Murmushi yayi yai kissing din bakinta "nine lazy din ko? Ki kiyayi ranar gamuwarmu dake acikin gidan nan"

Daukarta yayi a kafadarshi ya nufi falo da ita suna dariya, sai da suka je kofar falon sannan ya direta saboda su fadila suna nan.

Satin lamido hudu da dawowa ya shirya ya koma India amma wannan tafiyar shi kadai ya tafi, yaje yaga likitanshi sun gana ya dubashi amma kuma binciken da suka gudanar akanshi shine bazai k'ara haihuwa ba duk da cewar ya warke sumul amma kuma akwai abubuwan da suka samu matsala ajikinsa,

Kwananshi uku ya dawo amma bai iya fadawa kowa ba sai ikhlas saboda ita kadai ce baya iya boye mata damuwarshi, adaki suka k'ule ya rungumeta yana kuka, shi kuka ita kuka, tausayinsa ne ya mamaye zuciyar ikhlas,

Dago da kanshi tayi ta soma shafe masa hawayen fuskarshi,

"Abban sadiq ka daina kuka dan Allah"

Sake rungumeta yayi ya dora kanshi a kirjinta yana hawaye,

"Dole nayi kuka pretty, ina son haihuwa ashe banida rabon ganin jinina a duniya sai dai sadiq shi kadai..."

Rufe mishi baki ikhlas tayi itama tana kukan,

"Abban sadiq kaima kana da gudan jininka a duniya, kana da d'anka wanda yake naka ne halak malak,kaima kana da d'a baka daga cikin wadanda Allah ya jarraba da rashin 'yaya...!"

   _Sakon gaisuwa da fatan alkairi ga Zee tareda Takwarar kawata wato Khadija maikano_



_*Ummi Shatu*_

No comments:

Post a Comment