Thursday 9 February 2017

RAMUWAR GAYYA.. 5

*RAMUWAR GAYYA...*💘

_Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

        _With_

_*PHERYMER XARAH*_

  *_5_*

*B*atare data sake magana ba ta dauki kayanta ta fice daga cikin hall din ta nufi hanyar hostel,

Sawwam ta gani atsaye ajikin wata bishiyar dogon yaro shida wasu dalibai sai faman murmusawa yake yi,

Bata sake duban inda yake ba ta wuce amma sai taji ya biyota yana mata magana,

"Dama na fada miki indai kikace zaki yi sa'insa da ni to wallahi ina mutukar tausaya miki saboda wuya zaki sha, ni dinnan da kika ganni bani da mutunci muddin aka shiga gonata, ko babu komai nasan yau kin fara gane halina da kuma ko ni waye,

Shawara daya Zan baki shine ki fita daga hanyata domin duk wanda ya taboni wallahi ya tabo gidan rina..."

Gabanta yasha dan haka babu shiri taja ta tsaya, glass din fuskarshi ya zare yana murmushi,

"Ke kadai ce macen da ta taba kokarin raina mini hankali duk cikin makarantar nan dan haka ina gargadinki and this is the last waning da zan baki karki sake garajen shiga hanyata, idan kunne yaji..."

Murmushi ya sake yi ya juya ya mayar da glass dinshi fuskarshi yayi tafiyarshi, juyawa tayi tabi bayanshi da kallo,

Ringing din da wayarta keyi ne ya dawo da ita cikin nutsuwarta, cikin gaggawa ta daga wayar saboda ganin sunan mahaifinta ajikin screen din wayar,

Gaisawa suka yi ya sake gargadinta akan ta dage ta aiwatar da abinda ya turata banda wasa, sun dan jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama ta katse wayar ta tunkari hostel.

Tana shiga dakinta ta cire hijabinta tana karkadewa domin gani take kamar har yanzu kadangaren yana jiki gashi sai ta rinka jin kamar tafiyar kadangaren a jikinta,

Alawiyya ce ta biyota tana zaune sai gata ta shigo,

"Wai ummulkhair meyasa kike da taurin kaine..?"

"Da nayi me fa?" Ummulkhair ta tambayeta tana kallon fuskarta,

"Dama sai da na fada miki ki rabu da wannan gayen ba abokin fadan ki bane amma kika ki yarda to gashi yanzu kin gani tun ba aje ko inaba kin fara kwasar kashinki a hannu, nidai shawarar da zan baki itace tunda kin jarraba kinga ba zaki ci riba ba to ki sallama masa ki rabu dashi, ko me zai ce miki ki kyaleshi ki tura masa aniyarsa saboda idan fadan nan naku yaci gaba da faruwa to wallahi komai yana iya faruw..."

Ummulkhair ce tayi saurin katseta gamida mikewa tsaye hawaye na malala daga idanuwanta,

"Haba alawiyya, yanzu ni kika dorawa laifi? Shin bakiga abinda shi yayi min ba? Haba alawiyya ta yaya zaki tsammaci hakuri daga gareni,

Tayaya zaki zaci rashin mayar da martani daga gareni? Wallahi bazan kyaleshi ba sai dai idan shi ya gaji ya kyaleni, fada dani dashi yanzu muka fara so ki barmu muci gaba dayi har muzo gab'ar da marar juriya zai hakura ya sallamawa dan uwanshi.."

"Haba ummulkhair yanzu ashe bazan fada miki kiji ba? Karfa ki manta duk abinda yaje yazo daga karshe kece zaki ji kunya domin kece mace shi namiji ne kin san kuwa duk abinda namiji yayi shi ado ne agareshi.."

"Banda wannan karon, a wannan karon bazai taba zama ado agareshi ba..."

Ummulkhair ta mayarwa da alawiyya amsa har lokacin hawaye yana fita daga idanuwanta,

"Ummulkhair kiyi hakuri ki kyale yaron nan saboda a makarantar nan kowa sonshi yake, mutane da yawa suna girmama shi saboda kokarinshi wasu kuma suna girmama shi saboda tsabar kwarjininshi ke ko ma badan haka ba ana girmama shi saboda kyawunshi.."

"Ahakan? Mtswwwww" ummulkhair tace tareda jan wani dogon tsaki,

"Ke dama nasan tsananin gabar dake tsakaninku ba zata taba barinki kiga wadannan abubuwan da na lissafa miki ba amma ke kanki kin san yayi babu karya, ke dinma ina kyautata zaton soyayyar sa ce acikin zuciyarki shiyasa kiketa wannan..."

"Ubangiji Allah ya rufa asiri, wallahi babu abinda zanyi da wannan gajarabul din yaron.."

Dariya alawiyya ta fashe da ita wacce bata shirya ba,

"Duk abunki dai sawwam yafi karfin a kirashi da gaja, ko hasadun iza hasadi bazai kusheshi ba, kedai yanzu na gane tsakaninki dashi, sai anjima"

Jakarta ta saba ta fice tabar ummulkhair tsaye sororo tana kallonta.

  Yau cike da farin ciki sawwam yaja motarsa zuwa gida, tuki yake yana bin wakar da ya kunna ta larabci,

Horn yayi baba dan tsoho yazo ya bude masa,

"Barka da dawowa magaji..."

"Baba dan tsoho nace maka dan Allah ka daina kirana da sunan nan, wallahi gaba daya sunan nan baiyi min ba"

"Sawwam ai magajin da kaji ina ce maka saboda kaine magajin Alhaji, ehh kaine magajin masu gida..."

Murmushi sawwam yayi ya fito daga cikin motarsa bayan ya ajiyeta a muhallinta,

"To baba nidai kaci gaba da kirana da sawwam din abar magajin nan.."

"To, to, to uban gidana ai duk yanda kace haka za ayi.."

Naira Dubu daya sawwam ya ciro ya mika masa yawuce cikin gida cikeda farin cikin abinda yayiwa ummulkhair,

Yana shiga falo ya iske mami zaune gefenta kuma wata farar budurwa ce take mammatsa mata kafafunta,

"Mami mai yanmata yau kuma ko wa aka samo?" Ya fadi hakan acikin ransa saboda yasan duk yadda akayi shi aka kawowa yagani ko Allah zai sa ya kyasa....




Ummi Shatu

No comments:

Post a Comment