Thursday 9 February 2017

RUWAN KASHE GOBARA.. 78-End

[2/2, 3:14 PM] Itz Ummi A'isha🏻: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_

  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*


    _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

aishaummi.blogspot.com

  _*78*_

~~~Daren ranar sam lamido bai samu damar yin bacci ba saboda tsananin farin cikin da yake ciki, koda ya idar da salla zuwa yayi kusa da abdallah ya zauna ya zuba masa ido yana kallonshi,

Sai daf da sallar asuba sannan lamido ya dan samu bacci ya daukeshi kwata kwata baccin da yayi baifi na minti talatin ba ya tashi yayi sallar asuba, yana nan zaune har gari ya waye wurin karfe 7 abdallah ya tashi, kamashi lamido yayi yana kallon fuskar yaron mai dauke da beautiful point irin nashi,

"Abdallah ka tashi? To maza muje kayi alwala kazo kayi salla kaji"

"To daddy" abdalla ya amsa masa yana sake makaleshi, tare suka shiga cikin bathroom din abdallah yayi alwala sannan suka dawo tsakiyar dakin yayi salla,

"Abdallah kayi mana addu'a nida momynka kaji"

"To daddy zanyi muku"

"Yawwa abdalla, Allah yayi maka albarka" lamido yafada yana murmushi, suna nan acikin bedroom dinshi a zaune ikhlas ta shigo saboda tana son taje ta yiwa abdallah wanka, k'in koda kallonta lamido yayi saboda jiya taki amsa gayyatarshi,

"Abdallah zo muje nayi maka wanka ko" ta fada tana murmushi domin ta lura da shariyar da lamido ya fara yi mata,

"Abban sadiq ina kwana?" Sai da ya juyar da kanshi sannan ya amsa mata da "lafiya" daga haka bai kara cewa komai ba ya koma saman gadonshi ya kwanta,

Jan hannun abdallah ikhlas tayi tana murmushi, dakinta suka koma tayi masa wanka ta shiryashi cikin bakar riga da brown din wando nan tayiwa sadiq ma shima ta shiryashi sannan itama ta shiga tayi ta fito, kwalliya ta zauna ta tsara cikin wani blue din material mai zanen flower ajiki, abdallah na zaune yana rike da sadiq yana yi masa wasa,

"Anty zanje wurin daddy.."  Inji abdallah,

"Tashi kaje yana dakinshi, bani sadiq din" karbar sadiq tayi shikuma abdallah ya tafi wurin lamido yana kwance kamar me yin bacci dan haka abdallah yaje bayanshi ya kwanta ya nanuk'a cikin jikinshi ya rungumeshi,rungumeshi shima lamido yayi yana jin tamkar ya mayar dashi cikin cikinsa saboda tsananin so.

Sai da misalin karfe 9 sannan suka hallara akan table domin yin karin kumallo, lamido daukar abdalla yayi ya dorashi asaman cinyarsa ya soma bashi abincin,

Suna ci suna nishadi har suka kammala, suna gamawa lamido ya dauki abdallah suka nufi gidan innah, innahn bata sashenta tana sashen baffa dan haka yabisu can, suna zaune suna tattaunawa bayan sun kammala yin breakfast,

Suna shiga innah ta zabura ta tashi zaune tana kallonsu ita duk a tunaninta ma haydar ne dan marigayi,

"Lamido waye wannan?" Innah ta jefo masa wannan tambayar tana bin abdallah da kallo,

"Innah abdallah ne d'ana.."

Ba innah ba hatta Baffa sai da ya zabura ya tashi daga kishingiden da yake,

"Lamido wanne d'a kuma?" Baffa ya tambayeshi, zama lamido yayi yana murmushi ya dora abdalla akan cinyarsa,

"Baffa wannan yaron d'anane, ikhlas ce mahaifiyarshi..." Nan lamido ya kwashe labarin komai ya sanarwa dasu innah,

K'walla innah ta fara yi wacce ta kasance k'wallar farin ciki,

"Lallai Allah shine gagara misali.." Innah ta fada cikin murna,

"Wannan haka yake domin kuwa gashi munga zahiri da idonmu, Allah ya raya yaronnan cikin kyakkyawar rayuwa, hakika da ace mutane zasu rinka daukar kaddara su daina zubar da ciki da jefar da yara to da ba asamu bata gari dayawa daga cikin yara masu tasowa ba, ya kamata mutane su ringa rungumar yaran da aka samesu bata hanyar aure ba domin ba laifinsu bane,basu da wani hakki saboda basu san ta yanda akayi aka haifesu ba, mudai insha allahu zamu rike wannan yaron irin rikon da har ya girma bazai taba sanin cewar shi ba dan halak bane sai dai idan har ku iyayensa kune kuka yi ra'ayi kuka sanar dashi" baffa ya kammala jawabin yana mikawa abdallah hannu,

"Zo nan abdallah zo mu gaisa"

Tashi abdallah yayi yaje wurin baffa ya zauna,

"Yawwa zaka zauna anan ko?"

"A'a daddy na zanbi" abdallag ya bashi amsa,

Dariya dukkaninsu suka yi cikeda farin ciki, su lamido sun jima agidan har sai da 12 na rana yayi sannan suka tafi wurin bash, lokacin da bash yaga abdallah kuma yaji cewar wai dan lamido ne ba karamin murna yayi ba yace,

"Shege on top ashe kai ka dade da ajiye mai yi maka addu'a ni ka bari acikin matsala"

Dariya lamido yayi "kaima ka kusa ai domin wallahi bash rayuwar aure da dad'i musamman ma idan kayi dace da mace ta gari wacce ta iya kulawa da miji, idan kana da mata komai sai dai ayi maka, kaga ni yanzu komai yimin ake yi tun daga kan wanka, shafa mai, sa kaya, babu abinda nake yi gashi uwa uba....!". Shiru yayi bai karasa maganar ba sakamakon ganin abdallah yana kallonshi,

"Allah ya shiryeka.." Bash yace dashi yana dariya,

"Gaskiya ai na fada maka bash wallahi ka dage ka shiga daga ciki tun kafin hunturun nan ya dawo ya tarar da kai..."

"To gani nan dai kawai, amma wannan yaron babu ta inda ya barka wallahi, photocopy dinkane sak..."

"Dagaske muna yin kama?" Lamido ya tambayeshi cikeda tsokana,

"Ai da gani babu tambaya duk wanda ya ganshi ya ganka yasan danka ne, kai ko? Kai mugun jarababbe ne tsabar jaraba ma dan kamarka ya biyo"

"Ya isheka haka bash.." Lamido yace da bash yana dariya, tashi bash yayi suka fita tare da lamido da abdallah wanda tunda suka fita basu suka koma gida ba sai da yamma tayi,

A falo ya iskesu dukkaninsu sun kammala cin abinci suna hira, zama yayi da alamun gajiya a tare dashi shi kuma abdallah ya nufi wurin ikhlas yaje ya fara kokarin shiga jikinta,

Sannu da zuwa suka yiwa lamido sannan ihsan ta mike taje ta fara shirya masa table shida abdallah,

"Bari nayi wanka sai nazo naci abincin" lamido yafada tareda mikewa ya nufi sashensa, ihsan ce ta dawo ta zauna tana yiwa abdallah magana,

"Abdallah ina da ina kuka je ne?"

"Gidansu daddy da... Da gidansu uncle"

"Iye ashe ka gaisa da su innah ko?" Fadila ta fadi tana murmushi, itama ikhlas murmushin take yi saboda tana jin dadin irin yadda su ihsan ke kula abdallah babu kyamata,

Suna nan zazzaune har lamido ya fito yayi wanka yasaka green din t shirt da bakin wando iya gwiwa, table ya hau ya zauna domin cin abinci, da gudu abdallah yaje ya haye cinyarshi suka soma cin abincin tare,

Ikhlas na zaune tana kallonsu tana ganin yadda lamido yake bawa abdallah abincin sunata faman dariya, suna kammalawa suka sake fita shikenan ikhlas bata sake yin ido hudu dasu ba sai da karfe 9 na dare yayi.

  Dakinta lamido ya shiga bayan yakai abdallah dakinshi ya kwantar dashi, tana kwance ta gama yin shirin bacci cikin milk colour din rigar bacci,

"Abban sadiq ya kamata fa ka daina irin wannan shigar saboda yanzu ka girma.."

Murmushi yayi ya juya ya fita ba tare da yace da ita komai ba saboda dama zuwa yayi yaga kyakkyawar fuskarta kafin ya kwanta bacci.

  Washe gari tunda safe su ihsan itada fadila suka samu lamido a dakinshi suka sanar masa cewar zasu cigaba da zama dashi koda bazai haihun ba domin dama saboda Allah suke sonsa kuma abinda ya sameshi kaddara ce daga Allah wacce babu wanda ya wuce ta sameshi, ba karamin murna lamido yayi ba har sai da yayi hawaye saboda tsananin murna nan yayita saka musu albarka tareda addu'ar Allah yaci gaba da zaunar dasu lafiya.

  Acikin satin duk lamido ya zauna agidane babu inda yake fita kullum yana tareda iyalinsa, wata makaranta mai tsada yaje ya saka abdallah sannan ya siyo masa dukkan abubuwan da zai bukata a matsayinsa na dalibi, ga kayan wasa da ya siyo masa kamar babu gobe banda su biscuit, chocolate, juice, da sauran kayan zaki irin na yara,

Lokacin da ya dawo daga kaishi school din a falo suka tarar da ikhlas tana yanka cabbage,

"Anty daddy na yace yanzu sunana Abdallah Usman, yanzu ba abdallah Hussain bane sunana"

Kallonshi ikhlas tayi tana murmushi ita kwata kwata ma bata san sunan lamido na gaskiya Usman ba sai yau gaskiya fa shiyasa yake da zuciya da fushi ashe sunan mazaje gareshi,

"To abdallah Allah ya bada sa'a" ta fada tana kallon lamido kasa kasa domin tunda abdallah yazo gidannan nan kullum lamido daukarshi yake yi zuwa dakinshi su kwana tare.

*_79_*


~~~Acikin satin abdallah ya fara zuwa school wanda kullum lamido ne yake kaishi yake zuwa ya daukoshi idan an tashi ya dawo dashi gida, komai yawan aiki a office haka yake tsallakeshi da zarar lokacin tashinsu abdallah yayi,

Haka rayuwa taci gaba da tafiya har abdallah yayi sati uku da dawowa gidan, yau tunda sassafe ikhlas ta samu ta tashi ta shiryawa abdalla abincinshi na tafiya school sannan tayi masa wanka, tana tsaka da shiryashi lamido ya shigo daga shi sai jar t shirt da blue din wando three quarter,

"Good morning daddy" abdallah yace da Lamido yana murnar ganinshi,

"Morning my sweet boy" lamido ya bashi amsa cikin fara'a,

"Abban sadiq yanzu abinda kakeyi ka kyauta kenan?" Ikhlas tace da lamido tana kokarin sakawa abdallah riga,

"Me nayi kuma?" Ya tambayeta yana mai zuba mata manyan idanuwanshi,

"Tunda abdallah yazo gidan nan ka daina kwana adakin kowa kullum sai dai ka daukeshi ka kaishi dakinka ku kwana tare"

"Gani nayi bakuda bukata ta shiyasa, tun ranar da ya dawo ai nace miki ki rakani dakina mu kwana kika k'i basai in kyaleki ba lokacin da kika bukaceni sai ki nemeni..."

Shiru tayi masa saboda abdallah yana wurin, tsallaketa yayi yaje ya dauki sadiq wanda ya tashi daga bacci ya dan fara kuka, jijjigashi ya fara yi yana rarrashinshi,

"Saddiquna.." Sadiq najin maganar lamido ya daina kukan ya bude idonshi yana dariya.

"Tunda kina son in baki hakkinki sai ki shirya kafin na dawo.."

Ya fada yana kallonta, "wanne hakki kuma? Ni azumi ma nake yi" ta bashi amsa tana harararshi,

"Azumi? Azumin me? Wallahi gara ma ki hada tea mai kauri kisha kafin na dawo idan ba haka ba kuma kece zaki sha wuya.."

Kallonshi ta sakeyi cikeda mamaki, "hmm zancen kakeso"

"Kema kina so kuma wallahi yau dai kam sai na kashe kishin ruwata"

Sake kallonshi tayi "abdallah dai yana jin duk abinda kake cewa"

Kwantar da sadiq yayi ya kama hannun abdallah, "kisha tea dinfa kafin na dawo"

Bai jira amsarta ba ya fita rikeda hannun abdallah, baifi minti 20 ba ya dawo lokacin ta fito daga wanka tana goge jikinta da dan karamin towel,

Wayarshi ce ta fara kara da kamar bazai daga ba ganin xahar ce amma sai ya daga ya kara a kunnensa tareda matsawa kusa da ikhlas ya rike towel din hannunta,

"Hello xahar" ya fadi ahankali gamida kaiwa ikhlas kiss a kuncinta, kokarin zamewa daga jikinsa ta fara dan haka yayi saurin rikota nan ta fara kokarin kwacewa turata saman gado yayi yana dariya,

"Xahar ina zuwa zan kiraki anjima"

Tun kafin ta bashi amsa ya ajiye wayar  yabi ikhlas suka ci gaba da kokawar da suka fara, xahar har lokacin tana makale da wayar tana jinsu har sai da taji abin yana neman wuce saninta sannan tayi maza ta kashe wayar tana hawaye tun daga wannan lokacin tayiwa kanta alkawarin cire lamido daga cikin zuciyarta domin ta fahimci akwai wacce yake so.

Sai da komai ya lafa sannan ikhlas ta tayar masa da boren abinda ke tsakaninsa da xahar, rungumeta yayi yana shafar gashin kanta,

"Pretty na karki sakawa kanki damuwa ni babu auren da zan sake yi,ita wannan xahar dinma so nake yi na hadasu da bash ya aureta tunda kinga shima ya fara aiki a kamfanina amma ya kika gani?"

Sake rungumeshi ikhlas tayi ta yi masa kiss a baki tace "hakan yayi daidai abban sadiq, indai kayi haka to zaka samu lada mai tarin yawa"

"Allah yasa ta sanadiyyar wannan hadin auren da zanyi su abdallah su samu kani nan bada jimawa ba"

Murmushi tayi ta riko hannunshi "ni ai nagama haihuwa.."

"Sauranki tara domin guda goma nake son ki haifa min"

Makale kafada tayi tana murmushi "Idan na sake yin guda biyu ma nayi kokari"

"Sai na kawo amarya ta karasa miki ko..?"

Duka ta kai mishi a kirji tana dariya, kare dukan ya shiga yi ya hada hannuwanta dakyar ya ciccibeta ya nufi bathroom da ita.


_Gaisuwa mai tarin yawa ga ummu fahad & matar officer_

*_Ummi Shatu_*
[2/2, 3:14 PM] Itz Ummi A'isha: *RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
_(Labari mai tab'a zuciya)_

*_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

   _Sadaukarwa ga k'awata KHADIJA SIDI_


_*80*_

~~~Kamar yadda lamido ya kudiri niyyar hada auren bash da xahar hakance ta faru domin bash bai k'i ba haka itama xahar bata musa ba domin ta fuskanci shi lamido sam hankalinsa baya gareta yana ga wata ta daban, babu dogon bayani soyayya ta kullu tsakanin bash da xahar nan aka sanya ranar biki wata uku masu zuwa.

  Akwana atashi haka rayuwa taci gaba da gudana agidan lamido cikin jin dadi da kwanciyar hankali, a lokacin lamido ya shirya musu tafiya zariya shida ikhlas da abdallah batare da ya sanarwa da ita ikhlas dinba domin yana son ya sasanta tsakaninta da abbanta,shiryawa suka yi suka tafi su hudu dashi da ita da abdallah da sadiq,

Tun akan hanyarsu yake bata hakuri sannan yaci gaba da yimata nasihar cewar ba a fushi da mahaifa, duk abinda suka yiwa mutum to haka zai daure yayi musu biyayya,shiru kawai tayi tana sauraronshi domin ita kanta tasan tayi dacen miji mai kaunarta mai kaunar dukkan danginta bama yan uwanta ba duk wanda ya danganceta to lamido yana kaunarshi,

Kasancewar da wuri suka tafi yasa suka isa zariya da wuri, hotel suka je ya kama musu sai da suka ci abinci suka huta sannan suka tasamma gidan abbanta, kamar yanda gidan yake ada yanzun ma haka yake sai dai kuma babu jami'an tsaro kamar da nan ikhlas tafara tunanin to Kodai su abban sun tashi ne?

Da wannan tunanin acikin ranta suka karasa cikin gidan nan suka ganshi tamkar babu kowa aciki amma koda suka karasa shiga sai suka iske goggo kakar ikhlas a tsaye tana rikeda babban fo na yin fitsari ai suna hada ido da ikhlas ta saki fo din ta fashe da kuka mai ban tausayi,

Sakin baki ikhlas tayi tana kallonta yayinda lamido ya razana ya fara tambayar goggo abinda ya faru, kasa basu amsa goggo tayi illah wucewa da tayi cikin daki tana sharar kwalla nan suka mara mata baya suna shiga suka ga abbansu ikhlas kwance barin jikinshi a shanye duk ya rame yayi baki,

Cikin rudu ikhlas ta ajiye sadiq idonta fal da kwalla,

"Goggo meya samu abban?"

"Ikhlas ki yafe mana, hakika abinda mukai mukune keda mahaifiyarki yake bibiyarmu, tun bayan tafiyarki babu jimawa mahaifinki ya yanke jiki ya fadi sakamakon bai yi nasara a zabe ba tun daga wannan lokacin ya haduda lalurar shanyewar barin jiki ita kuma nafi ta hura masa wuta akan cewar dole sai ya saketa nan ya saketa saki daya ta tattare dukkan kudadensa ta gudu, yanzu gashi bamu da komai gidan nan ma da muke ciki mun sashi a kasuwa sayar dashi zamu yi..."

Goggo ta karasa maganar tana kuka,

"Allah sarki ki daina kuka goggo insha Allah zai samu lafiya" lamido yace da goggo, ahankali baban ikhlas ya bude idonsa yana kallonsu yana ganin ikhlas ya fara kwalla,

"Ikhlas ce?.." Ya fadi maganarshi a shawude bakinsa a karkace,

"Ehh nice abba" ikhlas ta bashi amsa tareda matsawa kusa dashi,

"Ikhlas ki yafe min kinji,nasan ban karbi kaddarar da Allah ya aiko min ba nasaki kin zubar da ciki gashi zaben ma ban ciba"

"Abba ai nadade da yafe maka sannan bayan tafiyata na haihu har nayi aure na sake haihuwa"

"Kin haihu? Ina yaran?"

Matso dasu abdallah tayi ta nuna masa su nan ya kamo abdallah da hannunshi mai lafiya,

"Yanzu wannan shine yaron da kika tafi da cikinsa? Lallai Allah shine gagara misali babu shakka bamu isa mun hana kaddarar ubangiji ba, Allah ya rayasu yayi musu albarka.."

"Amin abba" suka amsa gaba dayansu, tashi ikhlas tayi ta ajiye mayafinta ta soma gyara gidan domin ko ina a hargitse yake babu bata lokaci ta kalkale ko ina shi kansa abban nata sai da ta dafa ruwa tayi masa wanka ta debo wasu daga cikin kayanshi ta wanke masa,

Tunda suka zo har dare yayi bata hutaba aiki kawai take yi har karfe 9 na dare, sallama lamido yayi musu ya tafi hotel tare da abdallah, kwanansu uku agidan suna jinyarsa acikin kwana na hudune lamido yazo musu da maganar cewar zai fitar da abba kasar waje domin sama masa lafiya, kuka awurin goggo kamar wacce akayiwa mutuwa domin yau ta yarda ranar wuya sai naka amma ranar dadi kuwa sai dai bare,babu bata lokaci aka fitar da abba kasar chairo, nan su ikhlas suka tattara suka koma gida saboda makarantar abdallah.

  Rayuwarsu haka taci gaba da tafiya kullum lamido hankalinsa yana kan ikhlas bashida wani buri wanda ya wuce ya kyautata mata ita da yaranta ko hira suka hadu suna yi gaba dayansu dasu fadila to yafi mayar da hankalinsa kan ikhlas wani lokacin har kunya yake sakata ji saboda su Kansu su ihsan din har sun fahimci yafi ji da ita acikinsu,

Yauma suna kitchen suna aikin girkin abincin dare ita da ihsan fadila kuma tana falo tana yiwa abdallah home work, lamido ne ya dawo daga office yasha suit bakake wadanda suka karbeshi,

Kitchen din ya shiga ya samesu suna aiki,ihsan yaje ya mannawa kiss a kumatu yace "sannu da aiki my ihsan" ya wuceta ya nufi wurin ikhlas wacce take tsaye ta juya baya tana yanka alayyahu,

Ta bayanta ya tsaya ya rungumeta yadora kansa akan kafadarta,

"Barka da aiki pretty na...."

"Abban sadiq sannu da zuwa" tace dashi tana kokarin tureshi daga jikinta,

"Zo muje kiyi min wanka.." Ya rada mata a kunnenta,

"Aiki fa nake yi" ta bashi amsa,

"Wallahi kizo mu tafi tun kafin na daukeki"

"Kai abban sadiq gaskiya ka cika rigima"

"Ehh na yarda" ya fada yana shafa cikinta,

"To sai ka bari na karasa ai"

Yana nan tsaye yana rungume da ita har ta karasa yanka alayyahun yaja hannunta suka fita ita duk ya gama sata ta tsargu saboda ga ihsan nan a cikin kitchen din a falo kuma ga fadila nan,sai take ganin kamar ba zasuji dadiba duk da cewar ranar girkinta ne,

Dakinshi suka shiga, suna shiga ya jata jikinsa ya rungumeta, dauke kanta tayi ta fara kokarin cire masa kayan jikinshi,

"Haba pretty ki saki fuskarki mana irin wannan tsare gida haka..." Yace da ita yana lakuce mata hanci,

"Ni wallahi abban sadiq..."

Tun kafin tayi magana yayi sama da ita zuwa kan gadonshi,

"Dama tunda naga kanata wannan mammanne min din nasan abinda kake so kenan.." Tace dashi fuskarta a tsuke,

"To meye na bata ran kuma? Ba hakkina bane?"

Kawar da kanta tayi "nidai gaskiya ka daina yimin haka saboda zaka sa su ihsan su rinka jin babu dadi.."

"Wai me nayi ne ?" Ya sake tambayarta,

"Ya za ayi ace kullum sai muna tare dasu sai ka rinka zuwa kana kawoni dakinka bayan kuma duk lokacin da nazo bana komawa akan lokaci kuma nasan suna gane abinda ya faru tunda su ba yara bane"

"Dan Allah ni ki kyaleni nayi abinda zai fissheni.."

"Akan me zan kyaleka ka rinka yin rashin adalci? Duk ranar girkina baka barina acikinsu, da safe da rana da yamma da daddare, ko abincin rana fa kazo ci baka tafiya yanda kazo sai ka kawoni nan kuma saboda iya cin fuska sai ka sake sauya kaya, gaskiya wannan cin fuskar ya isa haka"

"Kin gama?" Ya tambayeta,

"Nagama" ta mayar masa da amsa,

"To wannan maganganun naki dai ba hanani abinda nayi niyyar yi zai yi ba"

Bai barta ta sake magana ba ya fara nuna mata soyayya bayan ya rufe mata baki da nashi, sai bayan sallar magrib sannan suka fito daga sashen nasa ita dai ikhlas duk kunyar hada ido dasu fadila take yi domin tasan ko waye ake yi masa haka dole bazai ji dadiba amma shi lamido babu ruwanshi ko kunya ba yaji wani lokacin ma sai suna zaune suna hira koda rana ko yamma sai yazo ya kira ikhlas kuma da zarar ta tafi shikenan bazasu dawo akan lokaci ba,

Dakinta ta koma ta shirya tayi salla ta fita, su fadila suna zazzaune suna cin tuwon shinkafa suna kallo, ko a fuskarsu bata ga alamun damuwa ba amma tasan acikin zuciyarsu akwai damuwar, zama tayi acikinsu tasa hannu suka ci gaba da cin abincin tare har lamido ya shigo sai faman kamshin turare yake budadawa da sun hada ido da ikhlas sai yayi mata gwalo.

Watan mahaifinta 3 akasar chairo ya dawo gida ya warke ras nan ikhlas ta shirya ta tafi tayi masa sannu da zuwa, yayunta ma sai da tayi musu waya ta sanar musu da abinda ya faru nan suka taho dubashi bayan ammi ta babbasu baki,lokacin da suka zo kuka abbansu ya shiga yi yana neman gafararsu tareda rokonsu akan su daure su shawo kan mahaifiyarsu ta dawo gareshi,da kyar ammi ta amince da komen nan kowa ya shiga murna, satin ikhlas daya ta koma yola domin bikin bash yazo, tana komawa suka sha bikin bash da amaryarsa xahar,

Bikin bash da sati biyu ammi ta koma gidan abbansu ikhlas bayan an daura musu aure, kudi mai yawa lamido ya bawa abbanta akan yayi jari yaci gaba da kasuwancinshi kamar yadda yake yi a baya.

  Rayuwarsu rayuwace mai dadi kowa yana jin dadin zaman gidan kullum cikin farin ciki suke gashi duk su ukun kansu ahade yake babu fada babu gaba kamar ba kishiyoyi ba,lokacin dasu abdallah suka samu Hutu alokacin lamido ya biyawa fadila da ihsan da abdallah umarah, iya shida ikhlas ne kawai da sadiq bai biya musu ba dalilinsa nayin haka kuwa shine baya son ikhlas tayi nisa dashi, tanaji tana gani su ikhlas suka tafi suka barta,

Zama tayi tai tagumi duk ranta ajagule,lamido ne ya biyota cikin dakin yana murmushi,

"Pretty na.."

Harararshi tayi ta kawar da kanta "ni ai babu abinda zakace min wallahi"

Zama yayi ya dauketa ya dorata akan cinyarshi,

"Kiyi hakuri dama nayi hakane saboda mu samu mu sake musha soyayyarmu kafin su dawo"

Makale kafadarta tayi tana harararshi,

"Haba pretty na, yimin murmushi nagani.."

Dolenta babu yadda ta iya haka ta biyeshi suka fara gudanar da soyayya mai wuyar fassarawa,

Tunda su fadila suka tafi babu abinda suke yi agida domin aikinma ba kullum lamido yake fita ba soyayya kawai yake gwadawa prettynshi,

Ita kanta ikhlas tasan sunyi daddadar rayuwa da lamido acikin kwanakin domin ya nuna mata ita kadaice mace guda daya tilo acikin zuciyarshi.

  Dawowarsu ihsan da watanni hudu shima lamido ya biyawa prettynshi dashi kanshi umarar nan suka tattara suka tafi dama lokacin ta yaye sadiq domin shekarunshi biyu cif, tunda sukaje kasa mai tsarki soyayya kawai suke yi da ibada ikhlas kam ta dage da yiwa lamido addu'a akan Allah ya basu haihuwa duk da abinda likitoci suka fada gameda lamido amma tasan fadar likitoci ba fadar Allah bace kuma Allah yakan iya nuna ikonshi akowanne lokaci, satinsu uku suka tattaro suka dawo,

Allah maji rokon bayinsa dawowarsu babu jimawa ikhlas ta soma zazzabi koda sukaje asibiti aka gano tana dauke da juna biyu, nan gida ya gauraye da murna, cikinta yanada wata biyar itama fadila ta soma nata laulayin, babu jimawa itama ihsan ta fara nata, wai ai murna awurin lamido ba acewa komai saboda ganin abin yake kamar a mafarki lallai Allah shine gwanin iya kyauta,shiryawa yayi ya koma umarah yaje yayi addu'a ya nunawa ubangiji godiyarsa,

Nan ya shiga riritasu ya samo musu masu aiki yanzu babu abinda suke yi agidan sai hidimarsa ikhlas kuwa idan abinda yafi mayen karfe to lamido ya zame mata domin wannan cikin da take dauke dashi manne mata yasa lamido ya sake yi, cikinta yana cika wata Tara daidai ta haifo santaleliyar yarinyarta mai kama da lamido sak nanfa lamido ya dau murna ya shiga nunawa jaririyar gata da ita kanta ikhlas din ranar suna yarinya taci sunan innarshi wato A'isha suna kiranta da humaira.

Duk wanda yaga humaira yasan yar gatace sosai kusan kullum tana cikin kwalliya gata kamarta daya da abbanta, su fadila da ihsan kusan tare suka haihu domin tsakaninsu kwana biyune kowacce ta samu da namiji, rana daya aka hada akayi suna yaran sukaci sunan Aliyu da umar.

  Lamido yanzu kam hankalinshi ya kwanta yayi kyau yayi fes domin babu wanda zai ganshi yace yanada mata biyu bare uku,

Watan humaira goma sha daya ikhlas ta tashi da zazzabi, shima lamido zazzabin yake yi dan haka yace taje asibiti, tunda taje gwajin farko akace tana da juna biyu,

Hankalinta atashe ta shiga gidan ta nufi dakin lamido yana kwance shida humaira ya lulluba da bargo, bude idonshi yayi yana kallon ikhlas,

Takardar test din da akayi mata ta ajiye masa akan hannunshi,

"Gashi nan daga zuwa sunce cikine dani ni dama nasan wannan zazzabin da kake tayi ba a banza ba"

Murmushi yayi ya lumshe idonsa, "to meye na fushin kuma? Ba kece kika hana zuciyata sakat ba, kece kika hanani son kowacce mace sai ke daya shiyasa kullum nake manne dake.. Allah ya raba lafiya, sai ki yaye Humairaa saboda karta sha ciki ko.."

Tashi tayi ta fita ta zumburo baki,fitowa yayi daga cikin bargon ya fita ya bita, tana zaune a gefen gadonta tana tsotsar goba, zama yayi ajikinta ya rungumeta yana cewa,

"Godiya ta tabbata ga Allah kwanan nan sai haihuwa aketa yi mana kinga xahar din bash itama ta kusa sauke yan biyunta,gaki kema kila yan biyun ne, saura fadila da ihsan"

Murmushi ikhlas tayi ta sake shiga jikinshi sosai,

"Ai gara ayita zube maka 'yayan ko ka tsufa da wuri in huta da amarya..."

Dariya yayi mata yaja hancinta, "tsufa? Ai ko na tsufa zan iya auro yarinya budurwa.."

Dagowa tayi ta kalleshi ganin irin kallon da tayi masa ya sashi rikicewa ya fara inda inda,

"Pretty da wasa fa nake yi miki, haba dai aure,wallahi da wasa nake"

"Kaji tsoro kenan?",tace dashi tana murmushi,

"Ehh naji, ai kin san tsoro wajibine..."

"Kaifa mai sunan mazaje ne bai kamata ka zama mai tsoro ba"

  Murmushi yayi ya rungumeta yana shakar daddadan kamshin turaren dake fita daga cikin jikinta,

"Allah dai yayi miki albarka pretty hakika kin zama wani bangare na rayuwata... I love you"

Murmushi tayi ta rungumeshi itama "i love you too abban sadiq..."

Rungume juna sukayi suna dariya...!

  ALHAMDULILLAH!

Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki wanda cikin amincewarsa da yardarsa na kammala wannan littafi mai suna ruwan kashe gobara, ina addu'ar Allah yasa ya amfanar damu baki daya.

  SADAUKARWA
Na sadaukar dashi gareki k'awata mai sona mai kaunata KHADIJA SIDI,ubangiji Allah yasa albarka acikin rayuwarki.

TUKWICI
Na bayar da ruwan kashe gobara tukwici babba agareku,

NANA HAFSAT (miss Xoxo)

SADIYA L BALA

ANISA A RIMI

A'ISHA (E'eshmal)

HAJJA (Maman Ihsan)

GAISUWA MAI YAWA

Gareki uwar dakina HAWWA M JABO,

INA JI DAKE..
Aminyar arziki KAUSAR LUV,Allah ya barmu tare

INA ALFARI DAKU
Hawwa jidda Aliyu
Besty na phertymah Xarah

KUNA RAINA

Fido Sodangi k'awata
Ummi Hambali
Batool Mamman
Momy sady Jegal
Baby lilmeerahcute
Mimi Bee
Anty bebeelo
Xarah bb
Aisha Dansabo
Teemah cool
Hafsat Bunxa
Humaira Zaria
Khaleesat haydar
Maman Ihsan
Stylish bich

KUN CANCANCI YABO
Big Aunties
Anty jamila moh (maman bobo)

Anty Adama (maman fatima)

Anty sis (maman sultan)

Anty Maijidda musa (maman twins)

Anty zubaida (maman ansar)

Anty Naseeba (maman Sadeeq)

Nagode da soyayyarku agareni ina addu'ar Allah ya raya muku zuri'arku yabarku da mazajenku, ya kara musu arzikin da zasu kawo muku abokan zama nagari......

Gaisuwar fatan alkairi agareku masoyana masu karanta rubutuna suna yimin addu'a ako yaushe, hakika ina alfahari daku kuma ina sonku fiyeda yadda kuke sona, duk wata masoyiyar ummi A'isha to ina gaisheta aduk inda take wannan gaisuwar taku ce, sai mun hadu cikin littafi nagaba mai suna RAMUWAR GAYYA.. Wanda zamu rubuta nida besty na phertymah Xarah, karku bari abaku labari,taku ahar kullum UMMI A'ISHA.

*_Ummi Shatu_*

2 comments:

  1. Awwwn at last...masha Allah...more basira❤❤❤

    ReplyDelete
  2. Awwwn at last...masha Allah...more basira❤❤❤

    ReplyDelete