Thursday 30 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 45

*RAMUWAR GAYYA...... 💘*

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

         &

*Ummi Aysha*

45

      Tana fitowa ta soma waige waige ba Abba a waje, ta fice da sauri,

Inda ya saba ďaukarta anan suka haďu, ta shiga motar suna kallon juna sukayi murmushin farin ciki kafin suja motar,
Sai da suka biya yayi masu take away na abinci kana suka nufi masaukinsa,

Bayan sun gama cin abincin ya dubeta ,

'Dad ya gano bn sake ki ba, ya matsamin ko ya yafeni, miye mafita?

Tayi shiru tana kallonsa, shima ita yake kallo,

'ko xamu gudu ne?
Tayi Saurin girgixa kanta,
'a'a Abba xai iya yafeni,
'nida xnbar nawa mahaifin fa, ko kin fison kullum nayita xarra akan titi,
'nida ke jure duka saboda kai fa,
'wake dukan ki,
'Abba mana, ta nuna masa tabon bulala dake hannunta, ya dubeta,
'saboda me xai riqa dukanki, ni ba mijinki bane?

tayi shiru tana kallonsa,
'nifa nagaji da wannan takura xamu gudu,

Jikinta ya fara rawa tana tsoron ta gudu tabar iyayenta batasan halin da xasu shiga ba Kuma baxata iya bijirewa sawwam ba,

'kasan bnda waya ynxu, da kyar nasamu na fito ka maidani tun abba bai dawo ba,
Yayi mata kallo kasa kasa yana harararta,
'kin ma isa, tun yanxu, ok guduna ma kikeyi,

'kayi haquri,
'alqawarin mu mekikace xaki bani idan naxo,
'komai fa, kabari ka sake dawowa,
'saboda kin raina min da wayo ko? baki isa ba kafin tayi mgn ya janyota xuwa qirjinsa, jikinta ya ďauki rawa sai ta qanqame jikinta guri ďaya,

'wai me kikeyi haka ne khairi? am your husband ko xn cutar dake ne, beside ma kinsan baxaki bani ba meyasa kika kwadaitamin a waya?

'Dan Allah kayi haquri har na tare bana so a ynxu, don't mean to hurt you.... ga mamakinsa sai ya ganta tana hawaye,

Ko khairi bata lfy ne shi baiga matsala anan da xatace sai sun tare ba, yaushe tarewar ma, ko xai xuba ido yana ta kallontane, matsalar ďayace ace basuda aure amma kowa ya Shaida matarsace, ya tashi a harxuqe batare da ya kalletaba ya soma xira takalminsa yana faďin,

'tashi na maidaki gida,
taqi tashi sai ma kuka da take tana bashi haquri, tafiso harta tare xatafi mutunci a idanuwansa, ya daka mata tsawar dana firgitata ba shiri ta tashi da gyalenta a hannu,

Kafin ta fito tuni ya shiga motarsa, tun bata qarasa shiga motar ba yajata da qarfi, ta juyo tana kallonsa fuskarsa a murtuqe take sai taji tsoro,

'kayi haquri please,
'enough please bana son damuwa, daďin abin inada yan mata abinda kike taqama dashi kijiqa kisha,

Gabanta yayi mummunan faďuwa, hankalinta ya tashi,
'karkaje inda wata, zina ba kyau,

Wani mugun kallo yayi mata,
'tor waye sanadi.... xatayi mgn ya katseta a harxuqe,
Nace karki dameni please,

Tayi shiru xuciyarta kamar xata tsinke, sai hawaye take sharewa akai akai yana kallonta ta gefen idanuwansa bai damu ba,

Isowarsu Unguwar yayi dai dai da dawowar Abba daga asibiti yaje nemanta bai sameta ba, yana tsaye yaga motar sawwam murmushi kawai yayi yaran sun raina hankalinsu,

Ganin Abba hankalinta ya tashi ta juyo tana kallon sawwam shi baima ganshi ba, kuďi ya ďora mata akan cinyarta batare da ya Kalle taba,

'Dan Allah kayi haquri...
'please get out,
Jikinta a sanyaye ta ajiye masa kuďin gefen seat ta fito daga motar, yaja motar da qarfi yabar unguwar sai ta kasa karasawa gida ta tsaya suna kallon kallo da Abba,

tana tsaye taga Nafi'u ya fito da trolley ďinta ta kaya ya Sanya cikin motar Abba,

Da hannu yayi mata alamar taje ta shiga motar, ba gardama kai tsaye ta nufi motar xuciyarta na bugawa,

Abba da kanshi yaja motar suka bar unguwar batasan inda xasu je ba tana ganin sun ďauki hanyar gombe hankalinta ya tashi ta juyo tana kallonsa amma ba fuskar mgn, ta maida kanta jikin cinyoyinta tana kuka sosai Kamar ranta,

Shikenan an rabata da sawwam gashi yaje yana fushi da Ita, matsalarta ynxu sun kusa resuming Skul batasan isalin karatunta ba,

Sanda suka iso gombe Alhaji mukhtar baya gida sai yabar sallahu ga matarsa umma akan Kula da khairi, ba Ita ba waya Kuma Kada abari ta kuskura fita daga gidan ko lalurar mecece, batasan kowa a gombe ba batada qawayen da xataje garesu, yasa kai ya fice a harxuqe sai kuka take,

'umma tace wai har ynxu ba'a daidaita wannan auren ba?

'yaqi yarda umma, ina sonsa yana sona, mama ma ta amince dashi Shikadai ne bnsan ya xnyi ba,

'wannan auren ai baxaa rabashi ba, dole xa'a sasanta tsakanin Iyayen, fadansu ma shiryen banxane Abinda ya wuce ya riga ya wuce kawai a yafi juna duk da mahaifin sawwam ďinne yaci amana,

Bayan sati biyu khairi ta dawo wata iri gatanan dai ba fasali duk ta rame abinci ma bataci sai dole idan umma ta tursasata matsalarta sawwam har ynxu fushi yake da Ita yaqi ya saurareta idan ta sami waya ta kirashi dayaji muryarta xai tsinke,

Ynxuma tana kwancene tana kuka bayan umma ta gama yi mata Faďan damuwar da take sanyawa a xuciyarta,

Wayar umma ta ďauka ta kirashi, yana xaune yana ganin kiranta yaqi ďauka, duk da shima juriya kawai yake amma yana tsananin buqatar ta,

Karo na biyu da ta kira ya ďauka sai dai baiyi mgn ba, sai ta fashe masa da kuka, sosai yaji tausayinta musamman dayaji tana bashi haquri, sai yaji wani iri ba daďi,

'is ok na haqura shikenan,
'kaxo ka ďauke ni na yarda xn bika,
'da gaske?
'Ina gombe Abba ya kawoni tun ranar da kaxo, ko ina bana fita a takure nake kaxo kaje dani mu gudu,

'kibari xnyi wani plan ynda abin xaixo da sauqi, a gidan wake son xamana dake,

'Duk suna so, har Alhaji baya goyon bayan Abba amma umma tafiso,

Yace tor ki kaimata waya ynxu xamuyi mgn, ba musu taje ta kai mata,

Sun jima suna waya yanda xasu bullowa Al'amarin daga baya ya tsinke Wayar, umma ta kalleta,

'kishirya kayan ni banaso ana raba ma'aurata ballantana irinku, sawwam xai turo qawayensa gobe da motoci axo a daukeki xa'a gayawa Alhaji daga abbankine shiya turo, kinga kafin mgn ta fito qila komai ya daidaita,

Khairi ta soma murna sosai ta rungume umma tana godiya itama umma taji daďin yanda taga khairi a yau,

Sawwam Kuwa mami ya kira yayi mata bayanin komai kuma tabashi hadin kai 100% baxasu gayawa dad ba,

Dama gidan su a shirye yake olready tun kafin aurensu akayi mata jere, yaje yasa aka share gida tare da qara tsabtace shi,

Washe gari su Abdul sukaje gombe suka daukota Alhaji baisan komai ba sai yayi mata nasihohi sosai kana suka fice ko kaďan baiyi tunanin kiran Abba ba to sunce shiya aiko aje da ita,

Koda suka isa Kano ana magrib sukaje gidan suka ajiye ta suna mata tsiya,

Sawwam Kuwa wanka yayi ya ďauki Abinda yake buqata masu muhimmanci a gidan yaje ya kai a motarsa,

Mami tabashi abinci ya kaiwa khairi yaje ya Sanya a mota,

Sai wajajen 9 dad ya shigo gidan, sawwam na ganinsa ya tashi xai fita,

'Ina xakaje ynxu da dare, ya bata fuska batare da ya Kalle sa ba,
'xnje gidan abokaina, yasa kai ya fice, dad yabisa da kallo ya lura yaron na fushi da shine, mami na tsaye tana kallonsa,

Yana isowa gidan yayi horn Mai gadi ya buďe masa ya shiga, parking yayi ya fito da kayan ya nufi cikin gida,

Sai ynxu yake ganin gidan yayi masa kyau ba kamar kullum idan ya shigo ba, har wani qamshi falon yake yi masa, ya duba bata falon, sai ya ajiye abincin anan falon ya nufi ďakinsa da sauran kayansa, ya sauya kayansa xuwa na barci,

Yana fitowa yayi ďakin ta, tana xaune tana duba wata jarida da Suhaib ya bata wai xata ďebe mata kewa kafin yaxo, tana jin sallamarsa ta ajiyeta gefe, ta amsa sallamar tana kallonsa,

'oh ashe haka khairi sa ta koma, duk tayi rama, sai ya ware mata hannuwansa alamar taje ba musu taje a kunyace ta faďa qirjinsa ya rungumeta sosai tamkar xa'a kwace masa ita,

Sun jima ahakan kafin yajata xuwa toilet arwalla sukayi sukaxo sukayi sallah domin godewa Allah, sun jima suna adduo'i kafin ya dubeta,

'Abinci na falo kije kici inji mami,

Ta girgixa kanta tana kallonsa,

'na qoshi,
'me kika ci?
'Hafiz ya kawo min abinci daga gidansu,
'Kice abokaina sunyi hidima, Allah ya saka masu,
'Amin ta faďa a kunyace,

Lokaci ďaya suka tashi tayi falo yana bayanta, abincin ta ďauka taje ta sanya a fridge gudun kar ya lalace, ya riqa hannunta suka nufi ďakinsa bayan sun kashe komai,

Yau ma qanqame jikinta tayi a tsorace take dashi ynda taga jikinsa na rawa akanta ba kamar ynda suke haďuwa a hotel ba, sai taga yau yafi xumudin ta har wani rarrashinta yakeyi cikin muryarsa mai sanyi,

Tana jin lokacin da ya haďa bakinsa da nata haďe da xira hannayensa cikin rigarta, ta rumtse idanuwanta...........

Asuba ta gari🏻



*Pherty xarah*

       &

*Ummi shatu*



My wattpad Phertymerh1

RAMUWAR GAYYA.. 44

*_Ramuwar gayya..._*💘

  _Love story 50,50_

*_Ummi A'isha_*

             _*&*_
  *_Phertymarh xarah_*


  44

     Kallon dad sawwam yayi zuciyarsa tana zafi kirjinsa yana bugawa dum dum,

"Bakaji abinda nafada bane? Nace ka sakar musu yarinya sudaina yimin aike na wulakanci gidana, kai in banda ma rashin tunani baka duba cin mutuncin da baban wannan yarinyar yayi maka agaban mutane ranar daurin aurenku?..."

Dagoda idanuwansa sawwam yayi wadanda nan take suka rine izuwa jajaye,

"Dad ya kuke so muyi ne? Kun hanamu mu zauna da junanmu, kun hanamu sakewa kuna neman ku haramta mana junanmu bayan kuma Allah ya riga da ya halatta mana..."

Tun kafin ya rufe bakinsa dad ya sake daukeshi da wani zazzafan mari,daidai lokacin mami ta shigo tayi gaggawar shiga tsakiyarsu tana kallon dad fuskarta cikeda tashin hankali,

Nuna sawwam dad yayi da yatsa,

"Kaima har kayi girman da zaka kalli idona ka rinka fada min duk maganar da tazo bakinka? Yaushe kayi girman da har zan rinka fada kana fada?

To ka saurareni dakyau ni ba shasha bane sannan kuma ni ba sokon uba bane bare nabarka karinka yin abinda kayi niyya, sannan ya zama dole kayi abinda nasaka in bahaka ba to sai dai ka nemi wani uban amma badai niba.."

Yana gama fadin haka yasa kai ya fita Mami ta rufa masa baya, yayinda sawwam yake tsaye dafe da kuncinsa yana jin wani irin radadi acikin zuciyarsa, shi bawai zafin marinne yayi masa ciwo ba a'a dagewar dasu dad sukayi akan lallai sai sun rabashi da khairi,

Zama yayi abakin gadon ya tallafe kumatunsa duka yana tunani acikin ransa, wannan wanne irin al'amarine wanda yayi silar katsewar farin cikinsu shida khairi,

Wayarshi ya dauka domin kiranta amma shiru wayar akashe taki shiga haka ya hakura ya gaji ya ajiye wayarshi ya zubawa screen din laptop dinshi ido yana kallon kyakkyawar fuskar ummulkhairi..

  "Haba alhaji abinfa da yaron nan yafada wallahi gaskiya ne domin harga Allah muna neman tauye masa hakkinsa, Allah ya halatta masa matarsa mukuma muna neman mu haramta masa.."

Mami tace da dad bayan sun shiga falonsa, cikin takaici dad ya juya ya kalleta,

"Kema kin goyi bayansa kenan, kin goya masa baya ya bujirewa umarnina duniya ta tozartani ko? Kina son nahakura na zuba masa ido yaci gaba da zama da auren wannan yarinyar wadda ubanta yake barazanar kaini koto ko,

To bari kiji nafada miki wallahi baki isaba daga ke harshi baku isaba, yazama dole kubi maganata domin dukkanku a karkashin ikona kuke.."

"Ba maganar goyon baya bane ai, gaskiya nafada maka, tunda yaron nan yafito kiri kiri ya nuna mana yana bukatar matarsa to babu dalilin da zaisa mudage sai munga mun rabashi da ita, indai gaskiya za abi to akyaleshi ya zauna da matarsa..."

"Ba zai zauna da itaba mutukar ina raye, idan kuma auren yake so to yaje ya nemo wata sai in aura masa amma wannan kam sai ya rabu da ita"

Sassautowa mami tayi tafara bawa dad hakuri,

"Haba alhaji dan Allah muyiwa yaron nan adalci mu barshi da matarsa karmu rabasu da ita, wallahi sawwam tun jimawa yake son aure ni nasan haka, idan muka hanashi zama da wannan yarinyar tofa Allah ne kadai yasan irin halin da zai shiga..."

Samun kujera dad yayi ya zauna batare da yakara cewa komai ba.

  Tun wannan fadan da dad yayiwa sawwam, sawwam bai kara fita daga dakiba, yana nan akwance yana ta faman gwada kiran layin ummulkhairi amma shiru bai sameta ba, har karfe 2 nadare idonshi biyu,

Hankalinsa ba karamin tashi yayiba, koda safiya tayi ma bai fitoba sai wurin karfe 10:30 bayan yayi shirin office,

Falon mami ya shiga tana dining tana hada musu abincin karyawa, gaisheta yayi fuskarsa babu alamun fara'a,

Tashi yayi bayan sun gaisa yanufi hanyar fita,

"Sawwam breakfast dinfa?" Mami tafada cikin kulawa,

"Mami azumi nakeyi.." Yabata amsa yana cusa hannuwanshi cikin aljihunsa, wani irin tausayinshi mami taji domin tasan abinda yake damunsa, kamar zata yimasa kuka haka takeji,

"To shikenan, me zan shirya maka na shan ruwa?"

"mami anything...."

Yafada tareda ficewa ya nufi motarsa, yau ko gaisawa da dad basuyi ba, koda dad dinma yafito zai tafi office bayan yayi breakfast mami ta soko masa maganar sawwam, bai saurareta ba yawuce ya shiga mota driver yaja suka fita,

  Zama sawwam yayi a office shiru yanata tunane tunane acikin ransa har suhaib yazo kasancewar shi suhaib bama ya kasar bai jima da dawowa ba tun lokacin da suka gama makaranta yafita business shida mahaifinsa,

"Kaga ango" suhaib yafada cikin zolaya, hannu sawwam yabashi yana murmushi amma acan kasan ransa bacin raine kwance,

"Suhaib ya garinne?" Sawwam yace dashi yana murmushi,

"Normal wallahi, ya naganka duk wani irine"

"Bacci nakeji ne wallahi"

Dariya suhaib yayi "da alama daren jiya bakayi bacci ba"

"Wallahi har wurin 3 saura idona biyu"

Dariya suhaib yasake sawa "har yanzu baka gama amarcin ba"

Murmushi sawwam yayi shi sai yanzu ma yagano abinda suhaib din yake nufi,

"Kajika da mayar da hannun agogo baya, yasu Hafiz kun hadu ne?"

"Nagano ka wato ka waskewa maganar ka dauko wata, no bamu haduba domin nima jiya da daddare fa nashigo"

"Ok to anjima sai kazo majalissarmu mu hade"

Sun jima suna hira wadda ta sanadiyyarta ne sawwam yadan ji damuwarsa ta ragu, sai wurin sallar azahar sannan suhaib yayi masa sallama yatafi,

Koda ya tashi daga office B. U. K yashiga, tunda yashiga yake ganin kamar zaiga ummulkhairin shi, kasancewar yamma ce duk yawancin daliban suna waje, wasu suna karatu wasu suna hira, wurin hirarsu shida khairi yaje yayi packing ya kwantar da kujerarsa ya kishingida yana kallon masu wucewa.

***

  Tunda mahaifin ummulkhairi  ya kwace wayarta ta shiga damuwa saboda rashin jin muryar sawwam,

Dakin mama ta shiga tasamu bata nan tana wajen abbansu, har zata fita idonta yakai kan wayar mama dake ajiye akan gado, wayar ta dauka tafita ta shiga dakinta ta shige toilet, wayar sawwam tafara kira amma bai dagaba,

Text massage ta tura masa,

  _Sahibi nice ka kirani pls_

Yana zaune afalon mami yana shan ruwa yaga sakon da khairi ta aika masa, tashi yayi yabar kayan shan ruwan yafita zuwa dakinsa, sai da yasakawa kofar dakin key sannan yafara kiranta,

"Hello sawwam"

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya iya amsa mata,

"My lonely menene yasamu wayarki?"

"Abbane ya kwace, yanzu babu waya a hannuna wannan ma ta mamace nadauko bata saniba,ina fata dai lafiya kake,me kakeyi yanzu"

"Lafiya nake khairi, ruwa ma nakesha naga text dinki shine nadawo dakina na kiraki"

"Ayya sawwam azumi kayi...?"

"Azumi nayi my lonely saboda wallahi hakurina yagama karewa akanki, idan ban sameki kwana kusa ba Allah ne kadai yasan makomata, gashi koda nazo rowa kikeyi min sai kina cewa wai in bari komai ya daidaita gashi har yanzu daidaituwar bata samuba kullum abun sake ta'azzara yake"

Jin kalamansa yasa dandanan zuciyarta ta karye hawaye suka fara bin kumatunta,

"Sawwam kodai ina cutar dakai ne ban saniba, nashiga uku, dan Allah sawwam ka yafemin wallahi bazan karaba, kayafe min kar mala'ikun rahama su la'anceni, kar Allah yayi fushi dani..."

"Ya isa khairi, nifa ba laifi kikayi minba sannan ba fushi nakeyi dakeba, daina wannan kukan please..."

"To kace ka yafe min..."

"Nayafe miki amma idan nasake zuwa kika ki to bazan yafe mikiba koda kin bani hakuri"

"Nayarda, kagama shan ruwan?"

"Ban gamaba amma jin muryarki kadai tasa naji nakoshi bana son ma nakara ganin abincin"

Murmushi tayi domin jin kalmar da yafada,

"Naje makarantarku dazu har nayi budurwa tunda bakya nan"

Ido ta zaro tamkar yana ganinta,

"Dan Allah? Haba sawwam tun yanzu,nima fa har yanzu amarya ce da har zaka fara neman wani auren"

Murmushi yayi saboda jin har ta nuna kishinta, "kina sone kitashi daga amaryar ki koma matar gida kamar kowacce mace?"

"Nidai a,a nafi son nazauna a amaryarka har abada.."

"A'a ai kuwa sai kin canja daga amarya zuwa matar gida indai kin bani dama zuwan da zanyi zan baki cikakken matsayi na matar gida idan kuma kin ki to zanyi budurwa"

Jin alamun zata yi mishi kuka yasashi saurin tsayar da zancen,

"Dawasa fa nake yi miki, wallahi dawasa nake, haba ai kece one and only"

"Har kasa hankalina yatashi wallahi"

"To hankalinki ya kwanta dan da wasa nake..."

"Zan rama ai" tafada cikin shagwaba,

"To me zaki bani idan nazo?"

"Duk abinda kake so"

"Promised?

"Yes...!" Tafada tana murmushi,

Sun dan jima suna wayar sannan sukayi sallama, fita tayi ta mayarwa da mama wayarta bayan ta goge number sawwam da text din da tayi masa cikin Sa,a kuwa har lokacin mama tana can a wurin abba bata dawoba.

  Tun daga ranar kusan kullum sai ta dauki wayar mama aboye ta shiga bathroom tayiwa sawwam plashing yakira suyi hira, last wayar da sukayi yace mata zai zo acikin week din,

Kosu mami bai sanarwa da cewar zaije bauchi ba saboda baya son ahanashi shikuma ya matsu da yaga khairinsa musamman ma yanzu a yan kwanakin nan duk hankalinsa yatafi gareta,

Boye murnarta tayi bata bari kowa yagane ba, ranar alhamis ya shiga garin tunda safe yasamu zuwa domin so yake yau yasake sosai da matarsa, wata shadda yasaka kalar ruwan toka dinkin rigar iya gwiwa ne yasa hula kalar kayan dama tun adaren jiya ya sanar mata da cewa da wuri zaizo, tana tare da mama suna aiki a kitchen ta rike cikinta,

"Mama wallahi cikina ya matsanta min da ciwo kwana biyun nan, gashi da daddare baya barina nayi bacci"

"Ai kedai zanga ranar da zakiyi hankali, kina fama da lalura amma bazaki fadaba a nema miki magani? Ki shirya idan yayanki yazo yakaiki asibiti"

"Mama idan banje da wuriba bazan samu damar ganin likita ba"

"Kuma fa hakane, to kinga jeki cikin jakata ki dauko dari biyar kitafi, wanne asibitin zakije?"

"FMC zanje mama"

"To sai kin dawo"

Dakin mama taje ta dauko kudin ta koma dakinta ta canja kaya zuwa purple din less fitet riga da skirt, tashafe jikinta da man touch me mai dadin kamshi ta shafa turare ta fito tayiwa mama sallama tafita....



aishaummi.blogspot.com

Ummi A'isha

Pherty Xarah

RAMUWAR GAYYA.. 43

*Ramuwar gayya...... 💘*

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

          &

*Ummy Aysher*


43

Qarasowar su da mai napep yayi dai dai da qarasowar Abba,

Da sauri ta baiwa mai napep ďin kudinsa tayi cikin gida jikinta na rawa,

Tun a waje yake kwala mata Kira, tana jinsa bata amsa ba har ya qaraso, mama na jinsa ta fito,

'Uban Waye naga ya ajiyeki bakin titi,

'yayan maryam ne, xasuje kasuwa da budurwarsa shine ya ajiyeni acan na qaraso, dama Muna can tare a asibiti,

Ya sauke ajiyar xuciya kana ya juya da sauri, Numfashi taja haďe da lumshe idanuwanta,

'God save me....

'ya Mai jiki mama ta tambayeta,

'Mai jiki da sauqi, tayi cikin ďaki da sauri, kayanta ta soma cirewa kana ta shiga toilet domin watsa ruwa,

2 days~

Ranar da sawwam ya dawo sai da ya tsaya a inda suka saba haďuwa, ya kirata a waya,

Ta duba Abba yaje masallaci mama Kuwa ta shiga sallah, ta ďauki takalminta saďaf saďaf ta fice da sauri taji daďin da ko yayyunta bata gani a hanya ba,

Tana xuwa ta shiga motar tana sauke numfashi, ya kalleta,

'gudu kika yi hala?
Tayi far da ido tana kallonsa,

'wane irin gudu kuma sai kace yarinya,
'ai bakida Banbanci da yarinya naga sai maida Numfashi kike,

Ta janyo hannunsa ta ďora kan qirjinta,
'kaji ynda xuciyata ke bugawa, ina tsoron Abba ya ganni ne, ranar fa yaso ya gane sai da ya bini a baya,

Ya janye hannunsa yana kallonta,
'ni ai naganshi tare da wani tsaye, ban gayamiki ba Kada hankalinki ya tashi nasan ki da tsoro, da fatar bai taba min lfyr jikinki ba, ya faďa yana tattaba jikinta,

Ta girgixa kanta tana kallonsa,

' bana son abinda xai sami wannan jikin ki kula da shi sosai,

ta gyada kai tana kallonsa,
Yasa hannun ya mintsini bakinta,

'shi bakin baya mgn ne, sai dai kita gyada kai kamar kurma,

Ta tunxuro bakin cikin jin xafin mintsinar da yayi mata,

'oh sorry dear da xafi ko? nan ma gyada kai tayi,

Ya janyota sosai xuwa jikinsa, a hankali ya xira harshensa cikin bakinta, a Yanxu ta soma sabawa da wannan itama sai ta shiga maida masa martani, sun jima a hakan kafin ya saketa, ya gyara mata hijab ďinta ya qara haďa fuskarsa da tata,

'Ina son ki khairi, ta lumshe idanuwanta xuciyarta nayi mata sanyi, itama tana jinsa har cikin ranta,

'Yanxu idan ka tafi Kuma sai yaushe xaka dawo?
'I don't know too, duk ynda hali yayi,
tayi shiru tana kallonsa, yaja hancinta,
'kinaso na dawo da wuri ne? ta gyada Kai tana kallonsa,
'kimin Abinda xai sa nadawo gobe ma,
'Tace menene,
Ya matsa yayi mata raďa a kunne (na tabe bakina Ina kallon Ummi Aysha)

Rufe fuskarta tayi da tafin hannuwanta tana murmushi,

'kin amince? Ta girgixa kanta, shima murmushin kawai yayi,

Sun ďauki lokaci suna hira kafin yabarta ta tafi, sai da yaje gidansu maryam suna tare sai ga qaninta yaxo nemanta gidan ba shiri suka fito,

Sanda taga Abba a bakin qofar gida sai da gabanta ya faďi,

'kai Nafi'u Ina ka sameta?
'gidansu maryam na ganta,

Ga mamakinta baice komai ba ya juya cikin gida, ta sauke numfashi tabi bayansa.

Tana shiga mama ta soma mata faďa sosai akan yawan fitar da take a ynxu Wanda ada batayi,

Abba ma yasa bakinshi, tanajinsu bata tanka ba, batada matsala a ynxu tunda taga sahibinta koma menene suyi tayi,

Abinci taje ta diba kitchen tadawo tsakar gida tana ci, yanayinsu da sawwam take tunawa sai faman murmushi take ita kaďai a tsakar gida, tana haka wayarta ta soma ringing, tana ganin shine tayi Saurin karata a kunneta,

'badai ka isa ba,
'Nooooooo na tsaya hotel ne gobe xn qarasa, hope kina lfy,
'lfy kamar ynda kake,
'kinsan yanda nake kuwa, Ina matuqar buqatarki a kusa dani, ta juya tana waige waige bakowa,

'kayi haquri watarana muna tare har xaka gaji dani,
'baxan gaji da ke ba bakisan ynda nakejin ki a xuciyata bane,
'I feel what you feel, kayi haquri,
'haquri idan nagaji da yinsa xnxo na ďauke kine mu gudu,

Fitowar Abba yasanyata yin shiru jikinta na soma rawa,

'baxaki bini ba shiyasa kika min shiru, tayi Saurin cewa
'A'a qawata baxan xo ba ke kixo gobe sai ki tayani haďa kayana, ni hr ynxu bnsan matsayina ba mai aure ko marar aure,

Abba ya juyo yana kallonta har xaiyi mgn sai Kuma yasa kai ya fice,

Ta sauke ajiyar xuciya, taji sawwam na dariya
'dariya ma kake shikenan,
'ni xaki maida Mace saboda Abba ne ko mama,
'Abba ne,
'OK we talk later xn shiga wanka......

Bayan sati biyu basu qara haďuwa ba olways suna kan waya, tun lokacin bata qara fita ba ko qofar gida ma bata xuwa, sai Abba ya qara yarda da Ita yasan baxata iya cin amanarsa ba,

Ranar da sukayi waya ya gayamata xaixo, tayi shirinta ta feshe jikinta da turare Mai sanyin qamshi kana taje inda Abba,

'Abba xnje duba Farida ta haihu gobe suna baxan iya shiga taro ba saboda bakin mutane,

'yace hakane ummu, yasanya hannu a aljihunsa ya ciro kuďi yabata,

'Gashi sai kibawa Mai jego ko, ta karba tana godiya kana ta tashi ta fice da sauri,

Hotel ďin daya sauka nan suka nufa, sunyi planning yanda xasu gudu idan Iyayen sunqi saukowa, sun sha soyayya kamar kada su rabu,

Yaxo maidata sunyi Sallama kenan ta fita motar, yana kallonta ta baqin glass ďin motar tana tafiya, sai ya sauke glass ďin da sauri ya Kira sunanta, duk akan idon Abba yana hangosu daga inda yake xaune,

Tana juyowa ta saki murmushi, yayi mata kiss a tafin hannunsa ya hura ta iska xuwa gareta,
'I love you....
'Love you too muah ta tura masa itama,

Yayi murmushi ya maida glass ďin motar kana ya fice xuciyarsa cike da farinciki,

Hankalin Anna yayi matuqar tashi, yaushe khairi ta xama yar iska, bama Wannan ba yaushe ta fara masa qarya tun yaushe ma suke haďuwa da wannan yaron? ya tashi yabita da sauri,

Tana shiga gida gyalenta kawai ta ajiye, ba xato ba tsammani ta soma jin duka ta ko ina ajikinta,

Da waya yake dukanta sai ihu take, mama taxo da sauri ta kwace ta hannunsa,

'metayi kake dukanta haka, idan kajimata ciwo da wannan bulalar fa?

'gwanda na jimata ciwo da ta kunyatani idon jama'a, Ashe bata rabu da wannan yaron ba, tun yaushe kuke tare Ina kuke haďuwa ne,

Khairi ta boye bayan mama tana kuka tana duba jikinta, bulalar harta kwanta mata,

'Haba Alhaji ya kamata a sassautawa yarannan haka tunda suna son junansu, laifin iyaye bai kamata ya shafe su ba, badasu xakayi *Ramuwar gayya* ba tsakaninku Iyayen,

'ke kimin shiru kina Goyon bayanta ne tor wallahi daga yau karna qara ganin qafarta a waje, ba qawarkiba ko qanwar uwarki taxo nan kika rakata bakin gida sai ranki ya baci ballantana kije ganin mai jego, shashashar banxa kawai,

Mama tayi shiru amma kalamansa sun mata xafi, har xai fita ya juyo yana kallonta,

'bani wayarki nan, ba musu ta miqa masa jikinta na rawa, ya fice sai mamakin abinda idonsa ya gane masa yau yake, idan labari aka xo masa baxai yarda khairi xata iya haka ba, ya yarda namiji shike bata Mace, tunda gashi khairi bata masa biyayya ta koyi yimasa qarya hartana bijire masa duk saboda ďa namiji,

ďakinsa ya nufa ya sami takarda da Biro yayi rubutu akai kana ya fito yabawa ďaya daga cikin ya'yansa yaje ya kaiwa mahaifin sawwam,

Wasiqar bata samesa ba sai a Washe garin ranar ,

Yayi mamakin da jin wai sawwam bai saki khairi ba gashi har mahaifinta yana baraxanar maka su a kotu idan har bai sake ta ba,

Sosai Ransa ya baci wato sawwam ya raina masu hankali,

Koda mami taji batun batayi mamaki ba dan taga take takensa yayi yawa akan tafiye tafiye Kuma ta taba kamasa yana waya da khairi bata damu ba saboda farincikinsa shine nata, ita da xasu sasanta kansu subar yaran da tafi kowa farinciki,

Sawwam na xaune a ďakinsa da laptop a hannunsa dad ya shigo, ba xato ba tsammani yaji saukar Mari a kuncinsa,

Ya dafe kuncin yana kallonsa cikin tsananin mamaki,

'ni xaka rainawa wayo kace ka saki yarinya alhali baka sake taba, me kake nufine?

Sawwam ya ajiye laptop ďin gefe ya tashi yana kallon mahaifinsa,

'Dad let's bygone be bygones, abinda ya riga ya wuce ya xama past dad, abinda ke tsakaninku iya kune , mu miye laifin mu anan dan Allah dad kuyi haquri kubarmu mana,

'Baka isa ba sai ka saketa a yau ko ranka yayi matuqar baci.......



    *Pherty xarah*

           &

    *Ummi shatu*


My wattpad Phertymerh1

Sunday 26 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 42

*RAMUWAR GAYYA...*💘

  _Love story 50,50_


*_UMMI A'ISHA_*

        _with_

   *_PHERTYMERH XARAH_*


  42

   Nutsuwa sukayi dukkaninsu suna kallonsa sannan suna jira suji abinda zai fada,

"Tunda kun matsanta sai kunji dalilin dayasa nake son raba auren ummulkhair da wannan yaron to zan sanar muku amma ke ummulkhair ki sani bafa zan janye kudirina ba, yazama dole kiyi min biyayya ki hakura da wannan yaron..."

Maihaifin nata yafada yana kallonta, bata iya cewa komai ba sai hawaye dake faman bin kumatunta,

Mayar da hankalinta tayi ta nutsu wuri daya ta fara sauraron labarin da abbanta yake shirin basu,

"Nida alhaji mustapha abokan junane ko kuma nace aminai domin tun lokacin danaje jahar kano karatu muka hadu dashi kasancewar makarantarmu daya sannan ajinmu daya,

Mun shaku dashi mutuka komai tare mukeyi, bama rabuwa sai dai idan har hutu akayi, hatta iyayenmu sun san shakuwar dake tsakaninmu, da haka har muka kammala karatun secondary anan muka yanke shawarar cewa zamu dora karatu na diploma a jami'ar bayero dake cikin kano tunda dukkanmu mun samu sakamako mai kyau,

Lokacin da muka fara karatu anan nikuma nahadu da wata yarinya yar gidan manyan mutane gidansu yana nan a unguwar rimin kebe, farkon haduwata da ita a kasuwa muka hadu naje siyan takalmi ita kuma an aiketa siyan kayan amfanin gida, daidai shagon danake tsaye tazo tawuce sai jakarta ta fadi bata saniba,

Zuwa nayi na dauki jakar nabita abaya har shagon da ta shiga nayi mata sallama nabata jakarta nace mata ahanya ta yasar bata saniba, nan taji dadi tayi murna domin na ga hakan akan fuskarta,

Tun kallon farko da nayi mata naga tayi min sosai kuma awurin naji ina sonta,sunanta na tambaya tafada min nima nasanar da ita sunana mukayi sallama bayan ta sanar dani adireshin gidansu,

Kwana biyu da haduwarmu da ita na shirya naje gidan nasu anan nasamu kyakkyawar tarba awurinta da wurin iyayenta,mun dan taba hira da ita har nake sanar da ita cewa ni dalibine sannan kuma ba dan asalin cikin garin kano bane,

Lokaci kankani muka saba da ita muka shaku soyayya mai karfi ta shiga zukatanmu, ganin mun shaku sosai sannan har mutane sun dan san tarayyarmu yasani nasanar da mustapha maganarta sannan na umarce shi da ya shirya muje nakaishi su gaisa da ita,

Aranar mukaje dashi suka gaisa shima ya yaba mutuka da hankalinta da kuma nutsuwarta, haka muka cigaba da tafiya har akayi hutun makaranta anan nabarwa mustapha amanarta saboda ni nayi nisa dan haka nace masa ya runka zuwa yana dubata,hakan kuwace tafaru domin kusan kullum mustapha yana hanyar gidansu wannan yarinyar,

Abinda ban saniba ashe shima mustapha sonta yake yi dan haka sannu ahankali ya hure mata kunne yabatani awurinta ya shigar da kansa suka fara soyayya, koda aka koma hutu sai bai nuna mini ba itama kuma bata nuna min ba sai dai ta dan canja min ba kamar daba,

Haka dai naci gaba da hakuri domin ina yimata so nagaskiya kuma mai tsanani,

Lokacin da muka kammala karatu nasanar mata da zan turo magabatana domin asaka mana ranar aure, bata ki ba tace min to haka shima mustapha nasanar masa,

Satina hudu da gama karatu na tura iyayena neman auren amma koda sukaje sai akace musu ai anbada ita yanzu hakama saura sati daya daurin aurenta,

Nashiga tsananin tashin hankali sannan raina ya baci, ana sauran kwana uku bikin na shirya natafi kano wurin mustapha domin ina son nasanar dashi cin amanar da wannan yarinyar tayi min, koda naje banma sameshi ba sai mahaifiyarshi nasamu itace take fada min cewa ai yana can yana shirye shiryen bikinsa wanda za adaura masa nanda kwana uku, har gidansu yarinyar saida tafada min da sunanta anan nagane cewar lallai mustapha amanata yaci shiyasa yayi biris da lamarina lokacin da nake sanar masa da irin canjin da Nagani atare da ita,

Tun da nadawo gida daga gidansu mustapha nakwanta rashin lafiya wacce bakomai ke damuna ba face bacin rai ta sanadiyyar haka nahadu da lalurar hawan jini gashi nakasa mantawa da ita koda yaushe acikin tunani nake,

Dan haka na shirya daukar fansa na shirya mayarwa da mustapha abinda ya shuka shekaru 30 baya da suka wuce, ayanzu ne zai gane cewar RAMUWAR GAYYA TAFI TA GAYYA ZAFI, domin abinda ya tabayi to gashi zai faru akan dansa, shima yanzu zai dandana bakin ciki irin wanda na dandana abaya..."

Dukkaninsu sun razana dajin abinda yafaru,

Ajiyar zuciya khairu ta sauke ta kalli abbanta,

"Abba hakika abinda abban sawwam yayi maka bai kyautu ba sai dai bai kamata ka hukunta sawwam akan laifin da bashine ya aikata maka ba, idan...."

Dakatar da ita mahaifinta yayi ta hanyar daga mata hannu tare da cewa,

"Ba neman izininki nakeyi ba dan haka ki rabu dani na aiwatar da abinda najima ina shirin aiwatarwa, sanin kankine saboda sawwam na turaki kano badan wai kiyi karatu ba a,a sai don ina son burina yacika na rama abinda mustapha yayi min, kuma ma ai ni ban saki kiyi soyayya tagaskiya dashi ba, dama cemiki nayi kiyi duk yanda zakiyi kija ra'ayinsa gareki yasoki bance kema ki soshi ba dan haka kima cire ran cewar zakiyi zamantakewar aure tare dashi..."

Mikewa yayi zai fita yayunta sukayi hanzarin tsayar dashi,

"Haba Abba..." Cewar babban yayansu,

Hannu yadaga masa ya dakatar dashi,

"Wannan fada tace dan haka dole kubi abinda nace" yana kammala fadin haka yasa kai yafice yabarsu zaune kowa zuciyarsa cikeda sake sake,

Babu wanda ya iya magana acikinsu amma ummulkhairi har lokacin bata daina kuka ba, daya bayan daya suka rinka tashi suna barin falon, ganin kowa yabaje yabarta yasata itama tashi tafita anan ta rinka cin karo da yan tafiya wadanda suka zo bikin, kowa sai Allah yasanya alkairi yake yimata ya tafi saboda sunga kaiwa amarya gidan mijinta ya gagara,

Dakinta ta shiga ta kwanta shiru taci gaba da kuka tayi kuka kamar ranta zai fita yabar jikinta......

  Tashi sawwam yayi yana kallon iyayensa bayan dad dinsa ya kammala bashi labarin abinda ya hadashi da mahaifin ummulkhair wanda komai sai da yafadawa sawwam bai boye masa koda kalma daya ba,

"Shikenan dad Allah ya rufa asiri yasa haka shine yafi zama alkairi.."

Fita yayi ya shiga dakinsa ya kwanta ransa fal kunci,

Wayarshi ya dauka yashiga kiran layinta, har lokacin kuka take amma haka ta daure ta daga wayar,

"Matata kuka kike yine? Fada min menene yasaki kuka?"

Yace da ita yana saurarenta domin yagama fahimtar cewar kuka take yi,

"Dad yabaka labarin abinda ya hadashi da abbana?" Ta tambayeshi cikin kuka,

"Ehh yafada min, nifa nayi tsammanin wani babban abune ashema wai akan mami ne fadan..."

"Ehhh akaine" tabashi amsa tana share hawayen fuskarta,

"To share hawayenki, kidaina kuka kinji"

"Tayaya zan iya share hawayena sawwam?" Tafada tana kuka,

"Daurewa zakiyi, kinji matata, kicire damuwar komai aranki, ina sonki bazan iya rabuwa dake ba"

"Dagaske?" Ta fada tana murmushi,

"Dagaske nake, kin ganni nan babu abinda yake damuna sai son kasancewa da matata, bana son ganin komai sai kyakkyawar fuskarta, bana son jin komai sai kamshin jikinta, gaskiya bazan boye miki ba ina bukatarki..."

Hannu tasa tarufe fuskarta tana murmushi,

"Kai ana ta shirin yanda za ayi adaidaita kai kuma ta wannan kake.."

"Hmm amma dai kin san dole na bukaci matata ko?"

"Hmmm hakane"

"To kin gani, wallahi hakurina yakusa karewa..."

"Ka kara hakuri dai dan Allah kaji mijina..."

Ajiyar zuciya ya saki, "to dan yimin kiss naji"

Bata bashi amsa ba ta shiga aika masa da zazzafan kiss wanda yafara kokarin ruguza masa dodon kunne....

2 days later...

   Kokari sawwam yayi ya cire damuwa aransa,hakan da yayi ba karamin dadi yayiwa dad dinsa ba domin ya tsammanci cewar sawwam yacire khairi daga cikin zuciyarsa,

Ganin zaman gidan baya yimasa dadi yasashi kawai komawa office yaci gaba da zuwa aikansa, sannan idan ya tashi kuma sai yawuce wurinsu Abdul, baya komawa gida sai misalin karfe tara nadare, da zarar ya koma kuma kusan kwana suke suna waya da ummulkhair,

Ita kanta ummulkhair ta danyi jarumta wajen rage damuwar dake ranta.

  Yau kimanin sati biyu da bikinsu shida ummulkhair, abuja aka turashi shida abokan aikinsa, har ya shirya zai tafi sai yaga kuma bazai iya tafiya batare da yaga lonely dinshi ba,

Bauchi yafara zuwa, misalin karfe 12 narana yasamu ya isa, lokacin da yafadawa ummulkhair zuwansa rasa yanda zatayi tafita tayi gashi abbanta ya hanata koda leka kofar gida,

Tana nan zaune tanata sassaka yanda zatayi sai dabara ta fado mata ta tuno cewar an kwantar da kawar mama a asibiti,

Tambayar mama tayi cewar zataje dubiya, bata hanata ba amma ta gargadeta akan tadawo da wuri kafin abbanta yadawo,

Wani material tasaka pink da bakin hijabi har kasa tafita, acan tsohon titi tasameshi yayi packing akasan wata bishiya yana jiranta,

"My lonely ai nayi zaton ko bazan samu ganinki ba.."

Murmushi tayi tana kallonsa yasha kananan kaya gashi kamshin turarensa duk ya cika mata hanci,

"Nasamu nafito dakyar..."

"To yakike, ya gida, ya missing dina? Ko bakiyi ba?"

Murmushi tasaki ta dauke kanta,

"Missing dinka sosai ma, bafa na iya yin bacci.."

Hannunta yakamo acikin nasa,

"Idan dagaske kike to nuna min nagani sai na tabbatar"

Jin ya matso jikinta yasata boye fuskarta a kirjinsa,

"Nuna min mana nagani, kodai dama bakiyi missing din nawaba kawai dadin baki kike yimin?"

Kanta ta girgiza ta dago tana kallonsa, kiss takai mishi a kumatunsa,

"Shikenan?" Ya tambayeta yana murmushi, kai ta daga,

"To ni bari kiga yanda nayi missing dinki"

Rungumeta yayi ajikinshi yafara laluben bakinta......,

Sake matseta yayi ajikinsa,

"In taba?" Ya rada mata a kunnenta,

Cikeda kunya ta girgiza masa kai,

"Yauma hanani zakiyi, nida halal dina? Bari kigani.."

Cusa kanta tayi ajikinshi saboda tagane abinda yake nufi,

Sai da ya nuna mata salon soyayyarshi sosai sannan ya kyaleta yana murmushi,

"Bari natafi karki sa nayi shigar dare.."

Jitake kamar kada ya yatafi yabarta,hawaye tafara yi sharrrrrr, cikin kuka tafara yimasa magana,

"Allah ya kiyaye hanya, dan Allah sawwam karka rabu dani, karka tsaneni dan Allah karka ce zaka sakeni, wallahi ina tsananin sonka.."

  Sake rungumeta yayi yana shafar bayanta kamar wata jaririya,

"Ummulkhair nayi miki alkawari zan kasance dake bazan rabu dakeba domin kece rayuwata, saki kuma indai nine maiyi to har abada bazan yiba.."

"Allah yakaika lafiya, idan kadawo zaka biyo tanan?"

Murmushi yayi yana kallonta, "kina son nadawo ne?"

"Ehh" tabashi amsa,

"To zan dawo naganki, kije kitafi gida"

Sakinta yayi tafara kokarin zuge zif din rigarta tana harararsa,

"Nayi laifine?" Ya tambayeta yana kashe mata ido tareda yimata dariya,

Baki ta turo ta bude kofar motar ta fita aranta tana jin cewar tasan zatayi missing dinshi sosai, dariya yake mata har tabar wurin ta tsaya abakin titi tana tarar mai keke napep,

Mahaifinta dake tsaye abakin titi shida wani abokinsa wanda suka hadu suna gaisawa sunyi packing din motocinsu agefe sai kawai yahango wata tafito daga cikin wata bakar mota mai bakin gilasai kamar ummulkhair, gabansa ne yafadi domin ko tantama babu itace, yana ganin ta shiga keke napep yayi saurin yiwa abokinsa sallama ya shiga motarsa yabi bayansu......

Ummi A'isha🏻

Pherty Xarah

RAMUWAR GAYYA.. 41

*RAMUWAR GAYYA...... 💘*

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

          &

*Ummy Aysher*

41



Ya ďago yana kallon mahaifinsa, fuskarsa a kansa, Idanunsa taf da hawaye,

'please dad....
'don't pleased me sawwam...,
'Dad xn rubuta mata amma kabarni na kaimata da kaina,
'shikenan rubuta idan ka Kai da kanka xasu ga Baka damu ba, saki uku xaka mata dan baxaka qara aurenta ba,

Sawwam na hawaye ya duqufa yana rubutu, ido mami da dad suka sanya mashi cike da tausayinsa, ba ynda xasuyi dole raba auren shine mafita,

Yana gama rubutun ya dunqule takarda ya Sanya aljihunsa, ya ajiye biron qasa kana ya tashi yana share hawayen fuskarsa ya fice batare da ya qara waiwayensu ba,

Yana xuwa ďakin sa ya ciro wayarsa anan yaga missed calls na khairi, kamar baxai kirataba sai Kuma ya kirata lokacin tagama sallah tana Kan darduma, tana jin wayar ta fara qugi ta tashi da sauri saboda ringing tone ďin sa daban ne, toilet ta nufa kafin ta ďauki Wayar,

Lokaci ďaya suka saki ajiyar xuciya, ba Wanda yayi mgn acikinsu kowa najin xafin xuciyarsa,

Kusan minti biyar suna haka, batare da sun kashe Wayar ba kuďin na tfy a banxa sai tayi qarfin halin mgn,

'kayi shiru,
'kema kinyi shiru,
'da gaske xaka sakeni? sai ta fara hawaye sharrrrr hannunta har rawa yake gani take rabuwarta da sawwam tamkar rabuwa da rayuwartane,
'Ina hanya ynxu idan naxo xamuyi Mgnr, Kiyi haquri khairi I don't know what to do, tana jin haka ta fashe da kuka mai tsanani kenan ya sake ta,
'Ashe xaka iya rabuwa dani dan Allah ka maida auren baxan jure rashinka ba,
'ke kina tunani xn iya rayuwa ba kene, we have to br it, kidaina Wannan Kukan bana so,
'ai kasan baxaa barni tsayuwa dakai ba, Abba baxai Bari ba,
'kiyi dabarun nan naki na mata mana Kisan ynda xaki fito tunda da dare ne sai muje hotel ďin dana sauka muyi mgnr,
'hotel Kuma? Meyasa xamuje can,
'OK baxaki iya bina acan ba, ni ba mijinki bane ko kina tunanin xn cutar dake, jin ya ambaci miji xuciyarta nayi sanyi,
'tor kayi haquri sai kaxo,
'shikenan ki kula da kanki, kidaina kukan nothing can separate us,
'shikenan kaima ka Kula da kanka,
'to Kiyi murmushi naji mana, tayi murmushi kamar yana ganinta tana jin lokacin da ya sumbaci wayar kafin ya tsinke,

Yana gama wayar da Ita wanka ya shiga, a gurguje ya shirya ya ďauki Abinda xai ďauka ya fito, har lokacin suna xaune falo suna maimaita Mgnr,

'Ina xuwa haka cewar mami, ya dubesu fuskarsa a yatsine,
'xanje na basu takardar yar'su na haqura tunda bakwaso,

Dad ya taso cikin farinciki yaje ya rungumesa harda sumbatarsa,

'Allah shi maka albarka, sai kadawo Allah ya kiyaye I will surprise you sawwam,

Murmushi kawai sawwam yayi ya ďagawa mami hannu ya fice ita kanta tasan qarfin haline kawai yake bawai dan ya haqura ba,

Suna gama wayar ta fito ta nufi kitchen abinci ta diba taje falon Abba ta xauna tanaci,

Hakan da tayi Abba yaji daďi sosai a tunaninsa ta haqura da sawwam xata Karbi xabinsa,

Suna cikin haka ta fakaici idonsa ta dannan ringing tune na wayarta tana kuka ta ďauka bayan ta kashe kamar gaske,

'wow da gaske kikeyi, shikenan gani xuwa ynxu kice su siyama ma su jirani ynxu xnxo ta tsinke tana murmushi yaqe ta dubesa,

'Abba kabarni naje gidansu maryam yau xa'a kawo mata kayan aure Kuma qawayen mu na Skul sun xo mun dade bamu haďu ba tunda Muka gama secondary school,

'wace maryam kike mgn inaji an kawo mata kaya Tuntuni ai, sai da gabanta na faďi muryarta ta soma karkarwa,

'a'a Abba wannan kayan nagani ina so ne Wannan kuma kayan aure ne, lefe kenan, dan Allah Abba kabarni naje baxan jima ba,

Yayi shiru yana kallonta Kamar baxai amince ba sai Kuma ya gyada Kai alamar taje, Kada ya gane xumudin ta tunda sawwam bai isa isowa ba, sai ta xauna tana cin abincin tana Jan sa da hira kamar dama ba damuwa a tare da Ita,

Shi da kansa yaga batada alamar tashi yace wai baxakije bane,

'a'a xnje ina jiran mama ta shigo ne ingayamata karta nemeni bana nan,

'kije ki mata bayani daga can sai ki tafi,

Ta tashi ta fice.

sanda ta fito gida ana kiraye kirayen sallar magrib, ta shiga gidansu maryam ďin a gurguje tayi mata bayanin komai in case idan an aiko kiranta tasan yanda xata kareta,

Tana gama sallah kiransa ya shigo, ta ďauka yayi mata bayanin inda yake inda baxaa ganshi ba, ta fice da sauri,

Ta ďan yi tfy kafin ta isa inda yake, yana xaune sai kallonta yake ta hasken wata, wani qaton hijab ne ajikinta har qasa sai wani abu da take boyo ta cikin hijab Wanda baisan ko menene ba, ta buďe motar ta shiga, ba Wanda yayi mgn acikinsu ya tada motar ya fice,

Suna xuwa hotel yayi parking, Atare suka fito suka nufi ciki ďakin daya tara,

Xuciyarta har bugawa take dan dai bata iya yimasa gardama ne, Idanunsa akanta,

'meke cikin hijab ďin ki? ta yane hijab ďin kular abinci ce, ta dubesa,

'nasan baka ci abinci ba shiyasa na xoma da wannan kaci ko kaďan ne, yaja Numfashi da kyar kafin ya karbi abinci ya ajiye a qasa ya riqa hannunta suka shiga cikin ďakin bakin gado suka xauna yana faďin

'I need you not food, tayi rau rau da idanuwanta tana kallonsa sai taga ya ciro farar takarda a aljihunsa ya sanyamata a tafin hannayenta yana kallonta,

Lokaci ďaya xuciyarta na buga sai ga hawaye sharrrrr shikenan ya sake ta ,muryarta na rawa ta soma mgn,

'shikenan ka sake ni?
Ya girgixa kansa yana kallonta,
'idan kinje kibawa yaro ya kaiwa Abba inji sawwam amma Kada ki buďe,
'meyasa ta tambayeshi,
'ke meyasa kike tunanin xn iya rabuwa dake?
'saboda tursasawar iyayenmu,
'kenan bama son junan mune shiyasa har xamu yarda su rabamu, saboda naxo nagankine fa nayi wa dad dabarar xuwa garinnan amma ni bana son Wannan Kukan da kike, yasa yatsun hannuwansa yana goge hawayen fuskarta,

Bata ankaraba taji bakinsa Akan labbanta, ya soma kissing ďinta sosai, sai ta saduda duk da xuciyarta na tsananin bugawa amma batajin xata iya hanasa cos tana sonsa tanajin Abinda yake ji a xuciyarsa,

Hannuwanta tasa ta rungumeshi idanunta a lumshe, a hankali ya buďe nashi idanuwa yana kallonta yana jin sonta ta ko ina baya jin akwai abinda xai rabashi da Ita,

Sun ďauki kusan minti goma a hakan abin na neman canxa salo, hijab ďin jikinta ya cire sai tayi qoqarin sai ta hankalinta bata so wani abu ya faru tsakaninsu a ynxu, bata ankaraba sai ji tayi ya xuge zip ďin rigarta, ta soma kiciniyar kwace jikinta,

'please khairi, ta maida zip ďin rigar ta rufe, ta saqalo hannuwanta ta wuyansa, ta girgixa kanta,

'Kefa matatace you know it,
'kayi haquri har adaidaita, ya sauke numfashi haďe da janye hannunta akansa ya juya fuskarsa gefe alamar yayi fushi,

'am sorry please kaima kasan is not the right place Kuma ma.... sai Kuma tayi shiru,

'kayi haquri please,
'shikenan tashi na maidaki gida,
'abincin fa,
'baxan ci ba,
'Dan Allah kayi haquri, taje ta ďauko abincin ta dawo gabansa ta tsugunna, da rarrashi da komai tasamu yaci Kuma sosai rabonsa da abincin kirki tun jiya sai ga sawwam na xuba shagwaba Abinda ko mami baya yiwa lallai ya yarda mata ma rahama ne, yaji ya qara son ta ba abinda xai rabasu komai runtsi komai wahala,

Sun jima suna hira kamar basu da damuwa a ransu kafin ya ďauketa ya maidata gida, nan ma sai da yayi mata kiss,

'karki manta Mgnr mu gobe ki tambayi iyayenki su gayamaki dalilin dayasa suke son raba auren mu nima I will asked them tomorrow sai muji dalilinsu, tayi murmushi

'shikenan I will miss you,
'miss you more,

Kamar kada su rabu yaja motar ya koma hotel,

Koda taje gida ba'a gane ba, kuma tana yaro yakai takardar acewar inji wani bata buďa taga Komenene ba,

Ranar sunyi barcin daďi cike da kewar juna sai faman juye juye suke a gadonsu sun qagu safiya ta waye,

Washe gari sawwam yabar garin, yayi Sa'a koda yake gida ya sami dad na gidan,

Ya Shaida masu yabata takarda,

Dad ya soma sa masa albarka,

'amma dad meyasa kuka rabamu, meke tsakaninku?

'a'a ba ruwanka da wannan,
'mami tace ya kamata a gayamasa dalili tunda har an rabasu,

'dad yayi shiru kafin ya gyara xamansa yana kallonsa.

Khairi Kuwa Washe gari Faďan mahaifinta ya tada ta barci a tare suka fito da mahaifiyarta suka nufesa harda yayyunta ma,

'yaronnan ya rainamin hankali ya sakarmin ya shine xai rubutomin wannan abin,

Mama ta karba tana karantawa kafin ta miqawa khairi,

     _I can't divorce my wife, I truly loves her, Dan Allah Abba kayi haquri kabarni da matata fadanku karya xo kanmu._

'dole ya sakarmin yarinya kona kaishi ga hukuma,

'Tace Abba Dan Allah ka gayamin dalilin dayasa kakeson rabamu, Abba dan Allah ka gayamin abinda kuke boyewa,

'gsky ne Abba ya kamata musani ansanyamu a duhu cewar Mustapha yayan khairi,

Abba yayi shiru yana kallonsu kafin ya nemi guri ya xauna.



*pherty xarah*

       &

*ummi shatu*


My wattpad Phertymerh1

RAMUWAR GAYYA.. 41

*RAMUWAR GAYYA...... 💘*

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

          &

*Ummy Aysher*

41



Ya ďago yana kallon mahaifinsa, fuskarsa a kansa, Idanunsa taf da hawaye,

'please dad....
'don't pleased me sawwam...,
'Dad xn rubuta mata amma kabarni na kaimata da kaina,
'shikenan rubuta idan ka Kai da kanka xasu ga Baka damu ba, saki uku xaka mata dan baxaka qara aurenta ba,

Sawwam na hawaye ya duqufa yana rubutu, ido mami da dad suka sanya mashi cike da tausayinsa, ba ynda xasuyi dole raba auren shine mafita,

Yana gama rubutun ya dunqule takarda ya Sanya aljihunsa, ya ajiye biron qasa kana ya tashi yana share hawayen fuskarsa ya fice batare da ya qara waiwayensu ba,

Yana xuwa ďakin sa ya ciro wayarsa anan yaga missed calls na khairi, kamar baxai kirataba sai Kuma ya kirata lokacin tagama sallah tana Kan darduma, tana jin wayar ta fara qugi ta tashi da sauri saboda ringing tone ďin sa daban ne, toilet ta nufa kafin ta ďauki Wayar,

Lokaci ďaya suka saki ajiyar xuciya, ba Wanda yayi mgn acikinsu kowa najin xafin xuciyarsa,

Kusan minti biyar suna haka, batare da sun kashe Wayar ba kuďin na tfy a banxa sai tayi qarfin halin mgn,

'kayi shiru,
'kema kinyi shiru,
'da gaske xaka sakeni? sai ta fara hawaye sharrrrr hannunta har rawa yake gani take rabuwarta da sawwam tamkar rabuwa da rayuwartane,
'Ina hanya ynxu idan naxo xamuyi Mgnr, Kiyi haquri khairi I don't know what to do, tana jin haka ta fashe da kuka mai tsanani kenan ya sake ta,
'Ashe xaka iya rabuwa dani dan Allah ka maida auren baxan jure rashinka ba,
'ke kina tunani xn iya rayuwa ba kene, we have to br it, kidaina Wannan Kukan bana so,
'ai kasan baxaa barni tsayuwa dakai ba, Abba baxai Bari ba,
'kiyi dabarun nan naki na mata mana Kisan ynda xaki fito tunda da dare ne sai muje hotel ďin dana sauka muyi mgnr,
'hotel Kuma? Meyasa xamuje can,
'OK baxaki iya bina acan ba, ni ba mijinki bane ko kina tunanin xn cutar dake, jin ya ambaci miji xuciyarta nayi sanyi,
'tor kayi haquri sai kaxo,
'shikenan ki kula da kanki, kidaina kukan nothing can separate us,
'shikenan kaima ka Kula da kanka,
'to Kiyi murmushi naji mana, tayi murmushi kamar yana ganinta tana jin lokacin da ya sumbaci wayar kafin ya tsinke,

Yana gama wayar da Ita wanka ya shiga, a gurguje ya shirya ya ďauki Abinda xai ďauka ya fito, har lokacin suna xaune falo suna maimaita Mgnr,

'Ina xuwa haka cewar mami, ya dubesu fuskarsa a yatsine,
'xanje na basu takardar yar'su na haqura tunda bakwaso,

Dad ya taso cikin farinciki yaje ya rungumesa harda sumbatarsa,

'Allah shi maka albarka, sai kadawo Allah ya kiyaye I will surprise you sawwam,

Murmushi kawai sawwam yayi ya ďagawa mami hannu ya fice ita kanta tasan qarfin haline kawai yake bawai dan ya haqura ba,

Suna gama wayar ta fito ta nufi kitchen abinci ta diba taje falon Abba ta xauna tanaci,

Hakan da tayi Abba yaji daďi sosai a tunaninsa ta haqura da sawwam xata Karbi xabinsa,

Suna cikin haka ta fakaici idonsa ta dannan ringing tune na wayarta tana kuka ta ďauka bayan ta kashe kamar gaske,

'wow da gaske kikeyi, shikenan gani xuwa ynxu kice su siyama ma su jirani ynxu xnxo ta tsinke tana murmushi yaqe ta dubesa,

'Abba kabarni naje gidansu maryam yau xa'a kawo mata kayan aure Kuma qawayen mu na Skul sun xo mun dade bamu haďu ba tunda Muka gama secondary school,

'wace maryam kike mgn inaji an kawo mata kaya Tuntuni ai, sai da gabanta na faďi muryarta ta soma karkarwa,

'a'a Abba wannan kayan nagani ina so ne Wannan kuma kayan aure ne, lefe kenan, dan Allah Abba kabarni naje baxan jima ba,

Yayi shiru yana kallonta Kamar baxai amince ba sai Kuma ya gyada Kai alamar taje, Kada ya gane xumudin ta tunda sawwam bai isa isowa ba, sai ta xauna tana cin abincin tana Jan sa da hira kamar dama ba damuwa a tare da Ita,

Shi da kansa yaga batada alamar tashi yace wai baxakije bane,

'a'a xnje ina jiran mama ta shigo ne ingayamata karta nemeni bana nan,

'kije ki mata bayani daga can sai ki tafi,

Ta tashi ta fice.

sanda ta fito gida ana kiraye kirayen sallar magrib, ta shiga gidansu maryam ďin a gurguje tayi mata bayanin komai in case idan an aiko kiranta tasan yanda xata kareta,

Tana gama sallah kiransa ya shigo, ta ďauka yayi mata bayanin inda yake inda baxaa ganshi ba, ta fice da sauri,

Ta ďan yi tfy kafin ta isa inda yake, yana xaune sai kallonta yake ta hasken wata, wani qaton hijab ne ajikinta har qasa sai wani abu da take boyo ta cikin hijab Wanda baisan ko menene ba, ta buďe motar ta shiga, ba Wanda yayi mgn acikinsu ya tada motar ya fice,

Suna xuwa hotel yayi parking, Atare suka fito suka nufi ciki ďakin daya tara,

Xuciyarta har bugawa take dan dai bata iya yimasa gardama ne, Idanunsa akanta,

'meke cikin hijab ďin ki? ta yane hijab ďin kular abinci ce, ta dubesa,

'nasan baka ci abinci ba shiyasa na xoma da wannan kaci ko kaďan ne, yaja Numfashi da kyar kafin ya karbi abinci ya ajiye a qasa ya riqa hannunta suka shiga cikin ďakin bakin gado suka xauna yana faďin

'I need you not food, tayi rau rau da idanuwanta tana kallonsa sai taga ya ciro farar takarda a aljihunsa ya sanyamata a tafin hannayenta yana kallonta,

Lokaci ďaya xuciyarta na buga sai ga hawaye sharrrrr shikenan ya sake ta ,muryarta na rawa ta soma mgn,

'shikenan ka sake ni?
Ya girgixa kansa yana kallonta,
'idan kinje kibawa yaro ya kaiwa Abba inji sawwam amma Kada ki buďe,
'meyasa ta tambayeshi,
'ke meyasa kike tunanin xn iya rabuwa dake?
'saboda tursasawar iyayenmu,
'kenan bama son junan mune shiyasa har xamu yarda su rabamu, saboda naxo nagankine fa nayi wa dad dabarar xuwa garinnan amma ni bana son Wannan Kukan da kike, yasa yatsun hannuwansa yana goge hawayen fuskarta,

Bata ankaraba taji bakinsa Akan labbanta, ya soma kissing ďinta sosai, sai ta saduda duk da xuciyarta na tsananin bugawa amma batajin xata iya hanasa cos tana sonsa tanajin Abinda yake ji a xuciyarsa,

Hannuwanta tasa ta rungumeshi idanunta a lumshe, a hankali ya buďe nashi idanuwa yana kallonta yana jin sonta ta ko ina baya jin akwai abinda xai rabashi da Ita,

Sun ďauki kusan minti goma a hakan abin na neman canxa salo, hijab ďin jikinta ya cire sai tayi qoqarin sai ta hankalinta bata so wani abu ya faru tsakaninsu a ynxu, bata ankaraba sai ji tayi ya xuge zip ďin rigarta, ta soma kiciniyar kwace jikinta,

'please khairi, ta maida zip ďin rigar ta rufe, ta saqalo hannuwanta ta wuyansa, ta girgixa kanta,

'Kefa matatace you know it,
'kayi haquri har adaidaita, ya sauke numfashi haďe da janye hannunta akansa ya juya fuskarsa gefe alamar yayi fushi,

'am sorry please kaima kasan is not the right place Kuma ma.... sai Kuma tayi shiru,

'kayi haquri please,
'shikenan tashi na maidaki gida,
'abincin fa,
'baxan ci ba,
'Dan Allah kayi haquri, taje ta ďauko abincin ta dawo gabansa ta tsugunna, da rarrashi da komai tasamu yaci Kuma sosai rabonsa da abincin kirki tun jiya sai ga sawwam na xuba shagwaba Abinda ko mami baya yiwa lallai ya yarda mata ma rahama ne, yaji ya qara son ta ba abinda xai rabasu komai runtsi komai wahala,

Sun jima suna hira kamar basu da damuwa a ransu kafin ya ďauketa ya maidata gida, nan ma sai da yayi mata kiss,

'karki manta Mgnr mu gobe ki tambayi iyayenki su gayamaki dalilin dayasa suke son raba auren mu nima I will asked them tomorrow sai muji dalilinsu, tayi murmushi

'shikenan I will miss you,
'miss you more,

Kamar kada su rabu yaja motar ya koma hotel,

Koda taje gida ba'a gane ba, kuma tana yaro yakai takardar acewar inji wani bata buďa taga Komenene ba,

Ranar sunyi barcin daďi cike da kewar juna sai faman juye juye suke a gadonsu sun qagu safiya ta waye,

Washe gari sawwam yabar garin, yayi Sa'a koda yake gida ya sami dad na gidan,

Ya Shaida masu yabata takarda,

Dad ya soma sa masa albarka,

'amma dad meyasa kuka rabamu, meke tsakaninku?

'a'a ba ruwanka da wannan,
'mami tace ya kamata a gayamasa dalili tunda har an rabasu,

'dad yayi shiru kafin ya gyara xamansa yana kallonsa.

Khairi Kuwa Washe gari Faďan mahaifinta ya tada ta barci a tare suka fito da mahaifiyarta suka nufesa harda yayyunta ma,

'yaronnan ya rainamin hankali ya sakarmin ya shine xai rubutomin wannan abin,

Mama ta karba tana karantawa kafin ta miqawa khairi,

     _I can't divorce my wife, I truly loves her, Dan Allah Abba kayi haquri kabarni da matata fadanku karya xo kanmu._

'dole ya sakarmin yarinya kona kaishi ga hukuma,

'Tace Abba Dan Allah ka gayamin dalilin dayasa kakeson rabamu, Abba dan Allah ka gayamin abinda kuke boyewa,

'gsky ne Abba ya kamata musani ansanyamu a duhu cewar Mustapha yayan khairi,

Abba yayi shiru yana kallonsu kafin ya nemi guri ya xauna.



*pherty xarah*

       &

*ummi shatu*


My wattpad Phertymerh1

RAMUWAR GAYYA... 40

*RAMUWAR GAYYA...*💘

  _Love story 50,50_

  *_UMMI A'ISHA_*

            _With_

    *_PERTYMERH XARAH_*


  40

  Arude su Abdul sukayi kansa suna salati, shi kansa dad hankalinsa yayi mutukar tashi amma hakan baya jin zai sakashi ya kyale sawwam ya zauna da ummulkhairi a matsayin matarsa,

"Kagama suman ka katashi ka sakar min yata ayanzun nan zan sake daura mata wani sabon auren wanda yafi dacewa da ita..."

Baban ummulkhairi yafada cikin daurewar fuska, yayun ummulkhairi ne suka matsa kusa dashi suna tambayar abinda yafaru sannan suna bashi hakuri,

Wata uwar tsawa ya daka musu wacce ta razanasu,

"Babu ruwanku ackin wannan lamarin, shi yasan waneni ni, sannan yasan dalilina nayin haka, kuma kamar yadda nafada ko da dansa zai mutu to tabbas sai ya sakar min yata domin shima ina son ya dandana bakin ciki kamar yadda na dandana a baya..."

"Zai sakar maka yarka kamar yadda ka umarta domin ba ita kadaice macen da ta rage ba, yanda ka isa da yarka to nima zan nuna maka cewar na isa da dana...." Dad din sawwam ya fadi tareda wucewa fuuuuuuh ya nufi inda su Abdul ke kokarin saka sawwam acikin mota,

Wani specialist hospital suka nufa dashi wanda ke kan titin zuwa kano road,

Suna shiga likitoci sukayi azamar karbarsa nan aka shigar dashi cikin wani daki aka fara bashi taimakon gaggawa,

Minti talatin ya dauka kafin ya samu nasarar iya bude idonsa, gani yayi dakin yana juya masa saboda hajijiyar dake daukarsa duk da akwance yake, ko tantama bayayi da ace a tsaye yake da tuni ya dade da kaiwa k'asa,

Runtse idonsa yayi take wasu zafafan hawaye suka zubo masa, har wani Sarawa yakeji kansa yana yi masa gashi wani abu mai daci ya cika makogaransa,

Ganin ya bude ido yasa dad matsawa gefen gadon, yana fadin,

"Sannu sawwam, kaji karfin jikinka?"

"Dad mutafi gida, muje ka kaini wurin mami..." Yafada yana kuka hawaye na bin kuncinsa,

"Sawwam bana son mubar garin nan batare da ka sakar musu yarsu ba, ka daure ka saketa, nikuma nayi maka alkawarin zan aura maka wacce tafita"

Girgiza kansa yayi yana hawaye acikin zuciyarsa kuma yana cewa "duk duniya babu wacce tafi khairu, idan na rabu da ita bazan taba samun madadinta ba"

"Kaji abinda nafada dan gidan dady?"

"Dad mutafi gida tukunna"

Mikewa dad yayi daga jikin gadon yana gyara babbar rigarsa ya fita, su suhaib ya samu awaje ya sanar dasu suje su fito da sawwam su tafi kano yanzu yanzun nan shikuma zaije ya hau jirgi yatafi gida,

Sai da yaga sun saka sawwam a mota sun tafi sannan shima yatafi airport,

Har lokacin Bai samu zarafin kiran mami ba saboda yafi son suyi maganar face to face,

Babu jimawa ya sauka a kano ya nufi gidansa duk ransa yagama baci, afalo ya samu mami tana kaiwa da komowa gashi gidan yacika dam da baki yan taya murna,

Karasawa cikin falon yayi sai huci yake kamar mahaukacin zaki wanda zaici babu,

"Dadyn sawwam wai meyake faruwa ne? Sawwam yakirani yana kuka kai kuma inata kiran wayarka baka dauka ba"

"Ba lafiya ba, sannan yazama dole sawwam ya rabu da wannan yarinyar, ina nufin sai ya saketa ayau ba gobe ba"

Zaro ido mami tayi cikin tashin hankali,

"Saboda me? Wannan abu da me yayi kama ace daga daura aure tun kafin mutane su baje an warwareshi"

"Hakan shi zaifi zama alkairi agaremu domin yarinyar yar gidan Alhaji aminu mai shadda ce..."

Cikin razani mami ta dafe kirji idanuwanta suka firfito waje take taji jiri yana daukarta, cikin azama ta dafe kujera ta zauna, kafin wani lokaci har gumi ya lullubeta kamar wadda tayi wanka,

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yar gidan aminu mai shadda, tashin hankali wanda ba asa masa rana, tab..." Tafada tana rike da habarta,

"Kwarai kuwa yarsace, kinga kuwa ya zama tilas sawwam ya sakar masa yarsa ya auri wata.."

Tagumi mami tayi bata kara iya magana ba domin jikinta yagama bata cewar wannan auren nasu sawwam sunansa matacce dakyar idan zai kai kwana daya araye,

"Yanzu ina sawwam din?"

"Yana hanya sun taho shida abokansa suna nan karasowa"

Tagumi tasake rafkawa tana sauraron wakar dake tashi wacce ta cika unguwar, mawakin da aka dauko a bikin sai kiran sunanta yake yana ina uwar ango tafito fili ita kawai yake son gani,

Dakyar ta iya tashi tafita anan tayi kokarin saisaita fuskarta ta shiga cikin taron mutanen dake harabar gidan suna cashewa,

Kallo daya zakayi mata kasan cewa bikin dan lelenta akeyi domin tasha wani hadadden leshi wanda akiyasce kudinsa zai haura dubu tamanin, sannan ko ina najikinta gwalagwalai ne sai daukar ido suke dankara dankara, tun daga kan dankunnenta, da sarkarta da awarwaron da tasaka da zobbuna,

Tana shiga kawayenta da yan uwanta suka hau zubar mata da kudi suna lika mata, amma duk hankalinta atashe yake kololuwa, tana cikin filin ana zubar da ruwan kudi ta samu ta zare jikinta ta fita, daidai lokacin motar su sawwam ta danno kai cikin gidan,

Wurinsu ta nufa jikinta yana rawa, musamman ma da taga yakasa fitowa da kansa sai su abdul ne suka fito dashi,

Mami naganin haka tafara kuka,sashen dad suka nufa yana zaune afalo fuskarsa babu walwala, akan doguwar kujera suka kwantar da sawwam suka fice, gunshi mami ta karasa tana kallonsa cike da tausayawa,

Hannunta ya rike ya kankame sai kuma yafara hawaye,

"Mami kinji abinda ya faru ko? Wai sai na saki khairi..."

Wata tsawa dad ya daka masa, "ba wai bane, dole ne sannan tilas ne kasaketa mutukar kana son farin cikina, mutukar kana son kaci gaba da zama a matsayin dana..."

Runtse idanuwansa yayi wasu sababbin hawayen na sake kwaranya akan kumatunsa,

"Dad i can't, wallahi bazan iya sakinta ba domin itace rayuwata, she's my life, i can't do without her, she's my happiness, my everything..."

Afusace dad yaje ya daukeshi da wani gigitaccen mari,

"Ko zaka mutu sai ka saketa, sai ka saketa inyaso bayan ka saketa ka mutu din..."

Mami ce tayi gaggawar rikeshi tana kuka, "haba Alhaji, haba dan Allah, ya zaka rinka furta irin wadannan maganganun, sawwam fa shi kadaine danmu da muka mallaka bai kamata muyi masa haka ba"

Hawaye sosai sawwam yake yi domin da ace zai iya rabuwa da ummulkhairi to da ya saketa kodan yabi umarnin mahaifinsa tunda tun lokacin da yataso dad bai taba dukansa ba amma yau gashi sau biyu yana sharara masa mari da dazu awurin dauren aure da yanzu, muryar dad ce ta katse shi,

Sassauta murya dad yayi yana cewa,

"Sawwam karka manta da irin gatan da na nuna maka tun zuwanka duniya har izuwa yanzu, baka taba neman wani abu karasa ba, baka taba tambayata wani abu nahanaka ba, duk abinda ka nuna kana so to ina samo maka shi cikin gaggawa, dan haka kaima yanzu lokaci yayi da yadace kayi min biyayya ka aikata abinda na umarceka......

***

  Kwance take tanata faman gursheken kuka domin jikinta yagama bata cewar yanzu kila sawwam ya saketa an daura mata aure da faruk,

"Ummulkhairi kizo inji mahaifinki"

Tajiyo muryar mama tana yi mata magana, tashi tayi jiri yana daukarta domin rabonta da abinci harta manta,

Tana tafiya tana hada hanya ga mutane yan biki sai tsokanarta suke suna cewa "amarya kinsha kamshi",yara kuwa har jan mayafinta suke suna tsalle suna kiranta,

Falon mahaifinta ta shiga yana tsaye ya harde hannuwansa abaya, fuskarsa kamar zata fashe saboda tsabar bacin rai,

"Gani abba.."

"Na kiraki ne domin naja miki kunne akan wannan yaron, ban yarda ki kara kulashi ba har ranar da zai aiko miki da takardar sakinki domin yazama dole ya sakeki idan kuma hakan bai samuba to zan iya makasu a kotu har sai shari'a ta tilastashi ya sakeki"

Kukan datake ta dannewa ne ya subuce, "Abba kayi hakuri kayi min rai, wallahi indai sawwam ya sakeni to mutuwa zanyi..."

"Sai dai kuwa ki mutun domin dole sai yasake ki, tashi kibani wuri..."

Tashi tayi tana layi kamar wacce tasha kwaya ta fita, a tsakar gida ta hango yayyunta tsaye da mamansu suna fada mata abinda yafaru awurin daurin auren wanda har yayi sanadiyar faduwar sawwam aka daukeshi aka tafi dashi yanzu basu san halin da yake ciki ba,

Zabura tayi aguje ta nufi daki mutane sai kallonta suke, wayarta ta dauko ta kunna ta fara kiran Layin sawwam, wayar nata ringing amma ba adauka ba har ta tsinke, haka taci gaba da kira amma shiru, hannu ta dora aka tana kuka domin bata saniba ko sawwam mutuwa yayi bataji ba....

Jikinsa ne yayi sanyi hankalinsa ya sake tashi domin jin kalaman dady dayi,

Matsawa kusa dashi dad yayi ya rikeshi,

"Sawwam ka aikata abinda nace saboda samun farin cikina da kwanciyar hankalina, wannan abinda na umarceka shine Kadai zai samar min da farin ciki, sannan shine Kadai zai dawwamar mana da zaman lafiya"

Ko hannunsa kasa dagawa yayi sai hawaye da suke fita daga idonshi, kai ya daga alamar to,wani farin cikine ya lullube dady,

Ganin bazai iya magana ba dad yayi saurin juyawa ga mami,

"Dauko min takarda da abin rubutu a dakina maza yi sauri.."

Cikin sauri mami taje ta dauko ita kanta kukan take yi hawaye sun wanke mata fuska,

Karbar takardar dad yayi da biron ya mikawa sawwam ya makala masa a hannunsa,

Sawwam yana kuka yana hawaye ya yunkura ya tashi dakyar ya dan jingina ajikin kujera, hannunsa yana rawa ya fara rubutu ajikin takardar......



aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

RAMUWAR GAYYA.. 39

*RAMUWAR GAYYA...... 💘*

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

          &

*Ummy Aysher*

39

    Da sauri ta turesa, ta matsa baya haďe da tunxuro bakinta yayi dariya yana kallonta qasa qasa,

A fakaice ta juya tana kallon Abdul sai taga kwata kwata hankalinsa baya gunsu, ta maida kallonta ga sawwam,

'tor sai anjima,
'korata ma kike yi, lallai ma yarinyar nan, to jibi sai kihanani abinda naso ko ki korani daga gidan,

Ta juya tana murmushi tayi hanyar gida shima murmushin yayi yana kallonta,
'bako sallama ,ta juyo tana kallonsa,
'gobe da wuri xaka shigo ko, banaso ka bata lokaci,
'baxan ma bata ba dear, Inaso dinner ta qayatar...
'Allah yasa,
'yace Amin, sukayi Sallama da juna.

Washe garin Ranar ta Kama dinner, 

Amarya khairi tayi matuqar kyau sai kyalli take tamkar wata sarauniya, kalar fatar jikinta Mai kyau da sheqi, tayi kyau sosai cikin wata gown doguwa pink, an yane kanta da wani qaramin net shima , komai in pink daga cikinta hr waje, tayi matuqar kyau sosai,

Yayin da ango ke sanye cikin wani lallausan yadi Mai shara shara fari sol, yayi matuqar kyau sosai

Kallo ďaya xakayi wa sawwam ka sake marmarin kallonsa saboda haske da kwarjininsa ya dushe hasken Duk wani matashi Mai ji da kansa dake harabar hotel ďin,

Su Abdul ma ba'a barsu baya ba, cikin nasu anko sai waige waige suke Acikin abokan amarya ko xa'a dace....

Dinner tayi kyau ta qayatu anci ansha anyi raye raye harda amarya da ango,

Sanda aka tashi dinner ango yaja amaryarsa motarsa da kansa ya kawota gida, yana xaune a motarsa har ta shige gida kana yabar gurin, yana son khairi sosai ya qagu safiya tayi ta xama mallakinsa.

Daren ranar sun jima a waya, sun sha soyayya sosai baxasu manta wannan ranar a tarihin rayuwarsu ba domin sun amayarda irin qaunar da suke wa junansu,

Washe gari ta kama asabar ranar ďaurin aure,

Acan gidan alhaji mukhtar xa'a ďaura auren, shiyasa suka dunguma acan,

Ango yasha manyan kaya cikin farar shadda harda babbar riga da hula, anko sukayi da Dad,

Mami ta dube su da murmushi,
'kunyi kyau, Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, suka amsa da Amin, sawwam ya sumbaceta yana faďin,

'khairi will be part of us mami K......
'karka tsaya gurin surutu lokaci na tafiya ga dad ďin ka harya fice,ya fita da sauri yana dariya,

Sun iso gombe kai tsaye gidan baba mukhtar suka nufa, yayi ta kiran wayar khairi tana ringing bata ďauka ba, xai sanarda ita xuwansu ne, daga qarshe ma sai yaji wayar switch off,

Bai kawo komai a ransa ba yacigaba da amsar wayar friends ďinsa masu taya sa murna, yana tare da dad yan uwansa suka fara isowa,

Suma su Abdul tuni sun iso da tasu gayyar, yauma anko suka sha abokan 3 pointers,

Wuri ya taru, jama'a sai son barka, mutane kamar da bakin kwarya sun hallaro bikin sawwam da khairi, kowa na gurin bnda mahaifin amarya, sai suka tsaya jiran isowarsa,

Mutane sun soma damuwa ďaurin aure nason xama lalura Abinda ya kamata ayi tun ďaxu Gashi kusan awa ďaya da xuwa baa daura auren ba kuma har lokacin Abba bai xo ba,

Kowa gurin ya damu bama kamar sawwam, hankalinsa ya soma tashi Allah yasa lfy Gashi ya Kira Wayar har lokacin switch off.

*

Khairi xaune hannuwanta da suka sha qunshin baqin lalle da surkin ja akan fuskarta,

Kuka take sosai gwani tausayi, kuka take Kamar ranta xai fice daga jikinta, a halin da take ynxu gwanda mutuwarta  da rayuwarta dan baxata iya rayuwa batare da sawwam ba,

Mama ma cikin damuwa da halin da yar'ta take ciki ta dubi Abba,

'wannan hukunci Sam baiyi ba alhaji, bai kamata ka hukuntar da ummu ta wannan sigar ba, amma meyasa baxaka haqura kabarsu ba tunda suna son junansu,

'saboda *Ramuwar gayya* nayi wannan so bnga dalilin ki na sanyo bakinki acikiba, kinfi kowa sanin meke faruwa Kuma kinfi kowa sanin dalilina nayin haka,

'ummulkhairi baxata auri sawwam ba, faruq xata aura kuma dole xata min biyayya ynxu xnje can a gudanar da komai,

Jin kalaman sa ya Sanya khairi fashewa da wani irin kuka, idanunta sunyi jawur sosai ta dawo gabansa ta tsugunna haďe da riqe qafafuwansa,

'Dan girman Allah Abba kayi haquri ka tausayawa rayuwata, na kasance mai biyayya agareka Abba, na cika ma burinka nayima biyayya kabarni da Wanda nake so, shi kaďai nake so Abba baxan iya rayuwa da wani namiji idan ba sawwam ba, bana son faruq Abba ka tausayamin,

Ya janye qafarsa a hankali yana kallonta,

'Kinsan ina son ki ummulkhairi, kinsan baxanyi Abinda xai cutar dake a rayuwarki ba, kin kasance mai biyayya agareni shiyasa xn xaba maki miji dai dai rayuwarki, faruq shi kaďai xai iya riqeki amana yana son ki khairi kema ki koyi sonsa domin shine uban Ya'yan ki,

'Abba sawwam ma yana sona xai iya riqeni amana, wlhy baxai cutar dani ba, maminsa ma tana qaunata Abba, karka raba soyayyar mu Abba, ka cika min burina na kasancewa da sawwam kamar yanda na cika maka naka burin,

'idan na kasance mai laifi a gareki ummulkhairi to Kiyi haquri amma baxaki auri sawwam ba yasa kai ya fice da sauri, ta durqushe gurin tana kuka Kamar ranta, mama ma tausayinta take,

Mutane sun soma gajiya wasu har sun fara qorafi da yawa suna da abinyi gurin, wasu Kuma nesa suke, wasu Kuma suna da wani ďaurin auren shiyasa suka qagu, barin ma kamar dad daxai bar qasar gabaki ďaya ya dubi baba mukhtar,

'Alhaji ai gurinka Muka xo neman aure Kuma kai kabamu yarinya, kaine waliyinta kai Yakamata ka ďaura mata aure tunda mahaifinta baya kusa kowa nan gurin ya qagu wani ba'a San uxurinsa ba,

'hakane, tor bara a ďaura......

Nan take aka daura auren sawwam da khairi, dai dai lokacin Abba ya iso gurin, da sauri ya fito cikin motar ya soma kutsawa cikin dimbin mutanen dake gurin,

Suna haďa ido da alhaji mukhtar abinda ya tambaya,
'Kada dai an ďaura auren ne? Sawwam kaďai ya lura da xuwansa dad nacan na gaisawa da mutanen sai dai yanayin da ya ganshi ya tabbatar masa ba lfy,

'eh an ďaura yaya saboda mutane sun gaji da.... ya katsesa a fusace Wanda ya janyo hankalin jama'a harda dad xuwa garesa,

'amma meyasa xakamin haka, nikeda haqqin auradda ita, dole ya sakarmin yarinya ynxu,

Xuciyar sawwam ta buga ya xare ido yana kallonsa kome ya faru yayinda gurin yayi tsit,

'dad ya dubi sawwam,
'Kada dai wannan ne mahaifiyar yarinyar da kake aure sawwam? Jikin sawwam ya ďauki rawa yana kallonsa ya gyada kansa,

'baxai yiwu ba, ai tun farko danasan shine mahaifinta baxaka neme ta ba, wannan auren Kuwa xa'a warwareshi ynxu,

Sawwam ya tashi tsaye idanunsa sun sauya Kala,
'why dad? wai meke faruwa ne?
'you must divorce her sawwam,
'I can't dad, Ina sonta and you know it...... Bai qarasaba ya ďauke sa da Mari,

Mutane suka shiga ruďani abin ya ďaure masu kai, su Abdul suka matso jikinsu a sanyaye suka riqe sawwam dake dafe da kuncinsa yana kallon yanda faďa ya qaure tsakanin mahaifinsa da mahaifinta, miye tsakaninsu Ina suka San juna?

Sabon al'amari ne Wannan ga dimbin mutanen dana xo ďaurin aure gurin, musamman ganin mahaifin ango da mahaifin amarya suna faďa Kamar xasu cinye junansu,

Sawwam ya fita gefe ya Kira mami yana sanarda ita, kuka yake sosai yana roqonta ta taimaka masa baxai iya rabuwa da khairi ba.......

Sosai hankalinta ya tashi to meke faruwa meya janyo fitinar, ta tsinke Wayar da sauri dan baxata jure jin kukan sawwam ba, ta soma qoqarin nema layin dad da jin meke faruwa,

Yana ganin kiranta baxai iya ďaga wayar ba kasancewar hankalinsa baya jikinsa, kallo ďaya xaka yiwa Iyayen biyu ka gane suna cikin bacin rai sosai na tsawon wasu shekaru da suka shuďe a baya,

Manyansu tsofaffi suka sanya baki,

'yace lallai sai an sakar masa yarinya,

'dole ma xai sake ta saboda muma bamu buqata,

'ya saketa ynxu xa'a ďaura mata aure da Wanda ya dace faruq,

Dad ya dubi sawwam,
'ka saketa ynxu xn ďaura ma aure da wacce ta dace Rukayya,

Hankalin sawwam ya tashi Cak numfashinsa na ďauke ya xube gurin a sume....



*pherty xarah*

         &

*ummi shatu 🏼*



My wattpad Phertymerh1

Tuesday 21 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 37&38

*RAMUWAR GAYYA...*💘

_Love story 50,50_

  *_UMMI A'ISHA_*

          _with_

  *_PHERTYMERH XARAH_*

37

   *Z*ama ummulkhairi tayi sukuku hankalinta ya dan tashi zuciyarta sai harbawa take yi,

"Oh Allah gani gareka, ya Allah kai kadai kasan abinda kake nufi da haka...." Tafada ahankali sai kuma hawaye ya hau tsiyaya daga idonta, kuka tayi sosai wanda ita kanta bata san ko na menene ba,

Ta dade tana risgar kuka wanda anan take kanta yafara ciwo, dolenta ta nemi wuri ta kwanta sakamakon ciwon da kanta ke yi,

Bacci ne ya samu damar daukarta wanda tajima tana yi daga karshe ta tashi afirgice sakamakon wani mummunan mafarki da tayi da sawwam,

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, allahuma inni a'uzubika min sharri fi manami an yadurruni fi dini wa duniyaya..." Tafada atsorace tana dube duben gefenta da kusa da ita,

Wayarta ta dauka takira number din sawwam, akasalance ya daga wayar sakamakon shima barcin yake yi,

"Hello matata..." Yafada cikin muryar bacci,

"Sawwam lafiya kake? Babu abinda ya sameka?" Ta tambayeshi jikinta har rawa yake,

"Lafiyata lau bacci nake yi amma yanzu tunda natashi wanka zanyi nataho wurinki"

"Dagaske babu abinda ya sameka?"

Murmushi yayi "meya farune? Ance miki wani abu ya sameni ne?"

Kai ta girgiza masa kamar yana ganinta,

"A,a kawai dai wani mafarki nayine wanda ya razana ni, nikuma wallahi na tsorata gashi bana son wani abu ya sameka" yanda tayi maganar kamar zata saka kuka,

"Ashe kina sona da yawa haka, wohhhh ashe nima dan gatane ana sona sosai ba ason wani abu ya sameni"

"Kayi hakuri na katse maka baccinka, am sorry"

"Babu komai my lonely, naji dadi ai da naji muryarki awannan time din"

"To sai ka shigo"

Murmushi yayi yafara kokarin tashi, "kiyi min kwalliya fa"

Bata bashi amsa ba ta katse wayar tana zazzare idanu domin tayi mutukar tsorata da mafarkin da tayi, fatanta dai guda dayane na Allah yasa ba wani abu neba yake shirin samun sawwam.

   Daurewa tayi ta cire damuwar dake ranta tayi wanka ta shirya tayi kwalliya, riga da skirt tasaka na atamfa ta saka farin hijab ta fita Inda sawwam ke tsaye yana jiranta,

"Kinyi kyau" taji yafada lokacin da ta karasa gabansa,

"Kaima haka"

"Nidin kyau nayi?" Ya tambayeta cikin tsokana,

Murmushi tayi ta matsa jikin motarshi ta jingina,

"Yau ina cike da farin ciki saboda yanzu nasan kin kusa zama mallaki na"

Kallonsa tayi tana jin faduwar gaba atare da ita "wai kai da kafara neman aure baka fara aikiba waye zai rinka ciyar damu?"

Dariya yayi yana kallonta, "Allah ne zai ciyar damu amma ta silar dad, ke nifa wallahi idan nakara wata biyar nan gaba ba ayi min aure ba to sai an kwantar dani agadon asibiti..."

"Allah yabaka lafiya, kana nufin kenan yanzu nan da wata nawane bikin?"

Kallonta yayi ya harde hannuwansa a kirjinsa duka,

"Ai samun lafiyata kawai a aura min ke wallahi, biki kuma nan da wata biyu insha Allah zaki zama amarya"

Murmushi tasaki tajuya ta fuskanceshi,

"Sannu fa, nan da wata biyu fa kace? sai kace wani a film aure nanda wata biyu?"

Dariya yayi sannan yabata amsa, "to shikenan ki zauna kigani, wallahi bikinmu bazai wuce hakafa kuma zakice nafada miki, sannan da kike wani zancen kamar a film to ba a film zaki ganiba afili zaki gani filin ma kuma akanki"

Kallonsa kawai take tana yin murmushi amma bata gasgata shi ba saboda atunaninta koda za ayi bikin to kila sai kamar nanda wata biyar ko shida domin yanzu suna dab da shiga level 4,

"Ke kinfi sone ayi bikin bayan kin gama karatu?"

Kai tadaga masa, "ehh wlh"

"Tab ai kuwa hakan bazai yiyuba garama ki ware" yafada yana tabe baki,

"Shikenan Allah ya tabbatar da alkairi" tafada cikin sigar kalar tausayi,

"Amin, da tun farko ma hakan kika fada da yafi miki"

Zuba masa ido tayi kawai tana kallonsa ko kiftawa batayi, ba karamin sake haduwa yayi ba, yayi kyau sosai fiyeda lokacin da yana dalibi,

Matsawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta,

"Gaskiya wannan ramar da kikayi ki mayar da ita kafin lokacin aurenmu"

Murmushi kawai tayi batace dashi komai ba domin ita dai tun lokacin dataji angama maganar aurensu sai ta nemi nutsuwarta ta rasa gashi duk jikinta yayi sanyi hankalinta ya tashi,

"Wai ke duk fargabar auren ce haka?" Yace da ita yana dariya,

"Hmmm dama ai kai dariya zakayi nasani"

"Wallahi kamar kin sani kuwa, kina kuka ranar nikuma ina dariya..."

"Wallahi dan baka san yanda nakeji bane, zuciyata har wani harbawa take yanda kasan gobe ne auren"

Dariya yasaka yana kallonta, haka yasata agaba yanata yi mata dariya, sun dade suna hirarsu sannan yayi mata sallama yatafi,tunda yatafi kuma kullum yana hanyar zuwa wurinta koda yaushe suna tare gashi takusa fara exam.

Gidansu sawwam kam dagaske shirin aure suke yi sosai domin mami harta fara hada lefen sawwam, kaya kam masu mutukar tsada ta siyo, kullum cikin yin waya take tana bada sautin kaya asiyo mata daga dubai, kasancewar bata san abinda hajiya raliya mahaifiyar rukayya tayi mata ba yasa take bata sautin kayan kusanma fin rabin kayan hajiya raliyan ce ta sissiyo,

  Tashinsa daga bacci kenan bayan yagama waya da ummulkhairi ya nufi part din mami,samunta yayi acikin bedroom dinta tana dudduba wasu kaya wanda zata saka acikin lefen, zama yayi akan gadon mami yana kallon kayan,

"Mami wai har yanzu ba agama hada kayan bane?"

"Ankusa agama ai, nanda sati biyu masu zuwa zamu kaimusu asaka maka date din biki"

"To mami Allah ya kaimu"

"Yawwa amma fa ba asaka inner wears ba, menene size dinta?"

Sosa keya yayi sannan ya kalli mami,

"Mami wallahi ni ban saniba amma tunda yanzu zanje wurinta sai na tambayeta"

"To shikenan amma karfa ka manta saboda nafi so komai ya zama ready"

"To mami, barima natashi naje"

Mikewa yayi da niyyar fita sai kuma yaga dad dinshi ya shigo cikin dakin cikin shirinsa na zuwa office,

"Dan gidan dady ka shirya fa ranar Monday zaka fara fita aiki domin har an fitar da offer dinka"

Cikeda farin ciki sawwam ya isa gaban dad ya rungumeshi,

"Thank you dad, thank you dad, thank you..."

Murna mami tafara yi tana addu'ar Allah ya sanya alkairi, zuciyarta jinta take tayi mata sanyi domin ganin danta datafi so tafi kauna yakusa zama cikakken mutum ga aiki ga aure,

"To duk da nidai ba asaka ni acikin maganar ba amma zanyi magana, naga wariyar launi ake nuna min, awanne ministry zai fara zuwa aikin?"

Mami tafada cikeda zolaya,

"Ba wariya bace maganar ce iya dan gidan dady dani ta Shafa, a code of conduct bureau ne kin san abinda ya karanta bangaren statistics ne dan haka dole sai a irin wadannan wuraren zaiyi aiki, suna da headquarter a abuja amma nace shi abarshi anan kusa dake.."

Murmushi mami tayi cikin barkwanci tace, "to ai nima nakusa sallama dashi tunda ya kusa aure kaga shikenan"

Sum sum sawwam yasa kai yafice daga dakin ya nufi nashi, wanka yayi yana wankan yana tunanin irin zaman da iyayensa suke yi wanda tun tasowarshi bai taba ganin suna kace nace da junaba idanma suna yi to basu taba yi agaban idonsa ba,kullum cikin barkwanci suke gashi sai kace wasu kakanninsa wannan ya tsokaneshi tacan wannan ya tsokaneshi tacan fata yake aransa shima Allah yasa irin wannan zaman zasuyi da lonely dinshi.

  Shiryawa yayi sosai cikin kananan kaya gashi ba karamin kyau suka yi masa ba,

Makarantar su ummulkhairi ya nufa, fitowarta kenan daga lecture sai gashi aguje tagabanta kamar zai kadeta, cikin razani ta kankame alawiyya, burki yataka yana dariya ya koma baya, bude idonta tayi tana kallonsa,

"Alawiyya kinji yanda na tsorata, tab lallai sawwam wallahi zaka sani bari nazo"

Dariya alawiyya tasa ta juya tafara tafiya tana cewa "kunfi kusa nidai kinga nayi nan sai gobe idan kuma nasamu nashigo karatu da yamma shikenan"

Wurin sawwam ta nufa yana cikin mota yana waya dasu Abdul yana fada musu cewar yasamu aiki yanzu ma haka ranar monday zai fara fita office, nan Abdul yake fada masa shima yaje yayi interview awani ministry suma su suhaib duk sun halarci interview din"

Murmushi sawwam yayi ya daki sitiyarin motarshi,

"Hohhhhh! Lucky guys, kace mun kusa fara amsar salary....."

Ganin ummulkhairi tsaye tana jiransa yasashi yiwa Abdul sallama ya kashe wayar ya fita wurinta,

"Meye naga kinbi kin wani bata rai"

Harararsa tayi ta juyar da kanta, "to meyasa zaka wani zo ka tsoratani daka kadeni fa?"

Murmushi yayi yana kallonta, "koda ace na kadeki ai ba fasa aurenki zanyi ba, ke matsoraciya ce wallahi"

"Nayarda" tafada har lokacin bata kalleshi ba,

"To nidai ba fada nazo ba yau, mami ce ta aikoni in tambayeki size dinki,nasan na takalmi dai 38 ne shi harma an sissiyo, yanzu na inner wears nake so"

Shiru tayi takasa magana domin kunyar fada masa take, dakyar ta bude bakinta,

"36"

"36 fa? Tab" yace da ita yana dariya,

"Sai kayi kuma" tafada tana harararshi,

"Kin san me? Kinata cewa wai idan munyi aure waye zai ciyar damu to nasamu aiki ranar monday ma zan fara fita office"

Juyowa tayi gaba daya ma tamanta da cewar tana jin kunyarshi, tsalle tayi ta rungumeshi, tana fadin,

"Congratulations dear....."

Sai kuma tayi saurin sakinshi ta rufe fuskarta,

"Au, wallahi duk tsananin murna ce"

Dariya yayi ya kalleta,

"Bawani murna kedai kawai kinyi missing dina kina so kiji farin ciki"

Dariyar itama tayi, "koma me zakace dai nayarda, nidai yau ina cike da farin ciki"

Hira sukayi mai cike da kaunar juna lokacin, sai bayan isha sannan yatafi,

Ranar monday yafara fita aiki, duk kuma sai ummulkhair taji babu dadi saboda rashin ganinshi wuni guda domin da dane da tare zasu wuni duk kuwa da cewar suna yi suna fada amma dole haka zasu zauna tare,

Shima a bangaren sawwam din yayi missing dinta sosai dan haka yana tashi daga office wurinta ya wuce,

Lokacin da tafito ganinshi tayi agajiye yana tsaye yasha farar shadda riga da wando ita sai abinma yabata dariya domin duk yayi mata kalar tausayi, baifi minti goma ba yatafi gida, tun daga lokacin haduwar tasu tazama sai dare sai ko a weekend domin kullum yana office,

Salary dinshi nafarko gida uku ya raba yabawa maminshi kashi daya ya dauki daya sannan ya kai daya kason cikin daya account dinshi yafara tarawa  ummulkhair, duk da haka sai da ya cira acikin kudinsa ya siyo mata turaruka da kayan kwalliya.

38

  Lokaci babu wuya har su ummulkhair sun kammala exam dinsu, ranar da suka gama ranar ta tafi gida dayake jarabawar safe sukayi, kwananta biyu da tafiya aka kawo lefenta aka yanke date din biki karshen wata mai zuwa, murna awurin yan gidansu ba a magana, sawwam kuma yafi kowa farin ciki ganin ansaka masa ranar kamar yadda ya nema, ita dai ummulkhair tana cikin wani hali gaba daya jinta take sukuku gashi tanata jin tausayinsu ita da sawwam,

Satinta biyu agida sai gashi ya jemata,da murna ta tareshi tana fara'a,

"Kai yarinyar nan kiba zakiyi, ji fa tun yanzu har kinyi kumatu daga dawowa"

Murmushi tayi ta zauna bayan ta gabatar masa da kayan motsa baki wadanda ta tanadar masa,

"Kin fara zama yar lukuta wallahi idan kikayi nauyi dayawa bazan rinka daukarki ba..."

"Kai sawwam dan Allah" tafada cikin jin kunya, kwaikwayon maganarta shima yayi yace,

"Kai khairi dan Allah" dariya suka saka daga shi har ita.

Hira sukayi sosai lokacin da yatashi tafiya yajata motarshi ya dauko mata wata katuwar leda,

"Mami tace akawo miki wannan"

Karba tayi tana leka cikin ledar tana dubawa taga kayane kayan gyara irin na amare, "lallai mami tana son danta" tafada acikin zuciyarta,

Hannunta taji ya dan buga, "wai kayan menene? Nifa mami nagane yanzu tafi sonki akaina"

Murmushi tayi, "wallahi mami tana sonka kaima"

Gyada kai yayi "naji wannan, fita zan tafi"

"Haba sawwam meye abin fushi? Harda korata..."

"Na koreki din"

Murmushi tayi ta kalleshi "nima fa ban san menene ba sai naje ciki zan duba"

"Tace ai akwai takarda anrubuta komai ajiki, mantawa ma nayi da ban dauka na karanta ba"

Hannu ya mika zai kwace ledar tayi saurin kankameta ajikinta, yanaja tana ja, ganin ledar zata yage yasashi sakar mata ya tabe bakinshi,

"Idan tayi tsami zamuji"

Dariya tayi aranta tana cewa "mami ai kai take yiwa gata"

Amma afili sai tace masa "bama zatayi ba"

Sallama yayi mata suka rabu cikeda kaunar juna, lokacin dataje gida ta nunawa mama kayan ba karamin mamaki mama tayiba saboda ganin irin soyayyar da maman sawwam ke yiwa ummulkhair,

Nan itama mama tadage wurin gyara yarta, amma kullum ita ummulkhair cikin kuka take shikuma sawwam sai zumudi yake domin bikin yazo, shida abokansa koda yaushe cikin shirin bikin suke,

Itama ummulkhair ita da kawayenta sai tsare tsaren yanda bikin zai kasance suke,

Sawwam kullum cikin yimata waya yake yana zolayarta gashi tsabar zumudi kullum agidansu wanda zasu zauna da ita yake kwana,

Yauma yana gidan akwance shi kadai ya kirata yana tsokanarta,

"Wai kana inane?" Ta tambayeshi,

"Ina gidanki, a dakinki"

"Gidana kuma? Saboda kaine gandoki"

Murmushi yayi, "wallahi dagaske fa ina cikin dakinki, acan zan kwana"

Katse wayar tayi tana cewa "ohh sawwam zumudinka yayi yawa"

Wayarta ta latsa ta kira alawiyya tafada mata biki yakusa saura sati biyu, sai dai alawiyyan bazata samu damar zuwaba domin itama sunada bikin cousin dinta amma tayi musu addu'ar samun zaman lafiya.

Angama dukkan shirye shirye ranar alhamis za ayi kamu, aranar aka yiwa ummulkhair kunshi na jan lalle da baki kuma aka yimata gyaran gashi nan tafito a amarya sak tayi kyau sosai,

Misalin karfe biyar akayi kamun awani hall dake harabar hotel din nishadi hotel babu karya kamun ya kayatu kuma ya hadu sosai, aranar shima sawwam suka taho dasu Abdul duk cikinsu shi kadai ne zaiyi aure domin su koma shiri basu fara yiba,dan haka sai tsokanarshi suke suna cewa zai rigasu tsufa,

Karfe 6 aka gama kamun suka koma gida lokacin suma su sawwam sun sauka suna hotel suna hutawa,wayarta yakira sai daf da zata katse sannan ta dauka gabanta yanata faduwa,

"Sawwam.."

"Kun dawo daga wurin kamun?"

"Ehhh" tafada a takaice domin ita yanzu sam bata son ganinshi bata son jin muryarshi asalima tsoronshi taji tanaji,

"Bakya nemana ne?

Yasake tambayarta"

"Uhm" tabashi amsa,

"Kikace uhm? Dagaske bakya nemana? Nito ina nemanki kuma zanzo yanzu"

"To" tace dashi tareda katse wayar tana turo baki tamkar yana ganinta.

Karfe takwas suka je gidansu kairin, ko ina yan uwane duk sun tattaru sun cika gidan, dakyar ta samu ta fita ko kayan da tasaka taje wurin kamu bata cireba, mayafi kawai tayafa ta fita,

Suna cikin mota shida abdul ta tsaya daga waje suka gaisa, kallonta kawai sawwam yake yi ganin yanda tayi kyau tasha kwalliya a fuskarta ga kunshi yazanu radau ahannunta da kafarta,

Gaisawa sukayi da abdul yanata tsokanarta, kallon sawwam tayi,

"Kaina ciwo yake bari nakoma ciki"

"To kafin ki tafi kiyi kissing dina"

"A'a wallahi...."

Hannunta ya riko yajata da karfi kawai sai jinta tayi tafada kan jikinsa, kunyace duk ta kamata ganin abdul yana wurin, shikuwa Abdul naganin haka yafita daga cikin motar yabasu wuri,

Rungumeta sawwam yayi yana kallon fuskarta

"Da haka zaki barni natafi babu kiss babu hugging?"

"Dan Allah kayi hakuri"

"Kiss me..." Yace da ita yana sake matseta ajikinsa,

"Kayi hakuri"

"Ok bakya son kije ki huta din kenan"

Dagowa tayi da niyyar yi masa magana taji lips dinshi kan nata........

Ummi Shatu

Pherty Xarah