Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 18

*RAMUWAR GAYYA...*💘

  _Love story 50,50_


*_UMMI A'ISHA_*

          _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*

   18


*N*annauyar ajiyar zuciya ta ajiye ta juya ta nufi hostel bayan ta daina hango motar sawwam din,

"Ikon Allah yau kuma sawwam ne ya taimakeni mutumin da idan banda fada babu abinda yake hadani dashi amma yau gashi shine harda taimakona.." Ta fadi hakan acikin zuciyarta,

Kasancewar tana fashin salla ya sanyata bin katifa ta kwanta tana nazarin masoyinta wanda ya shareta ya nuna halin ko in kula akanta bayan kuma tasan ya ganta,

"Hmmmmmm" taja ajiyar zuciya, k'arar shigowar sako cikin wayarta ne ya sanyata dan tashi daga kwancen da take,

  _kiyi hakuri bamu haduba,amma gaskiya naso ganin kyakkyawar fuskarki_

Kamar ba zata mayar masa da amsa ba domin fushi take dashi sai kuma wata zuciyar tace ta mayar masa da amsa,

_ai ni dear fushi nake dakai, bana nan ma dawowata kenan daga cikin gari._

Mintuna kadan taji shigowar wani sakon,

  _kiyi hakuri masoyiyata wallahi nima ba haka naso ba, me kikaje yi acikin gari?_

Murmushi tayi da alamar ta hakura kuma a yanda ta ganshi bata jin zata daina kulashi domin shima babu laifi kyakkyawa ne,

_gyaran gashi naje_

Ta mayar masa da amsa,

_wow, nasan dama kinada gashi ko ban ganiba i know yayi kyau.._

Murmushi tayi tana tunano kyakkyawar fuskarshi,

_kar kayi saurin yabona ni banida gashi karma ka sakani acikin sahun masu gashi kuma daga baya kaga bani dashi ka tsaneni.._

Mikewa tayi bayan ta tura masa sakon ta nufi flask din data adana abincinta, daukowa tayi ta zauna ta fara ci tanayi tana murmushi domin bata da burin da ya wuce na ta cikawa mahaifinta burinsa kamar yadda ta daukar masa alkawari,

K'irrrr taji sahibinta ya dawo mata da reply, cikin zakuwa ta bude sakon tana murmusawa,

_hmmm kece kike ganin haka, ai bazan taba tsanarki ba har karshen rayuwata, idan akwai abinda zanyi to bai wuce na kara sonki ba, ni ko kinada gashi ko baki dashi ina sonki domin ba gashinki nake so ba_

Dariya tayi batare data mayar masa da reply ba domin kudin wayarta ya kare, kamar ya sani sai kawai jin karar shigowar sako tayi tana dubawa taga recharge card ya turo mata na 2,000 through transfer,

Sakon godiya mai dauke da kalmomin soyayya masu sanyaya zuciya ta tura masa tayi shirin kwanciya ta kwanta tana tunanin sahibinta acikin zuciyarta.

  Koda sawwam ya fita daga cikin school din gidansu ya hara yana tuki yana tsaki,

"Mtswww nima dai wallahi ban yiba, meyasa na taimaketa? Meyasa na tsaya har na dauketa acikin motata? Mtswww may be ma tayi tunanin ko sonta nake alhalil ni ba burgeni tayi ba..." Ya fadi haka cikeda jin haushin kansa saboda taimakon ummulkhairi da yayi,

"Hmm nan gaba ko me zai sameta sai dai ya sameta amma bazan sake taimakonta ba" yafadi bayan yaja dogon tsaki,

Cike da wannan haushin aranshi ya shiga gida, falon mami ya shiga bata falo dan haka ya bita cikin dakinta,tana zaune a bakin gado ita da yar aminiyarta Rukayya,

Tsuke fuska yayi yana ciccin magani,

"Mami ashe kina ciki?" Yafada fuskarsa babu annuri, ita mami yanzu abin nasa yafara bata tsoro domin indai kana son ganin fushinsa to akawo budurwa gidan nan za aga bacin ransa,

"Wallahi muna ciki Rukayya ce tazo yar gidan hajiya Amina.."

Ta kasan idonshi ya kalli fuskar yarinyar sannan ya dire kallonsa akan kafarta, shi bai taba ganin kafar da take yi masa kyau kamar ta ummulkhair ba sai dai yau yaga kafar tata tayi fari sol kamar ta baturiya may be period take ya raya hakan acikin ranshi,

"Wai sawwam baka jine tana gaisheka..?"

Muryar mami ta dawo dashi cikin hayyacinsa, firgigit yayi yafara shafa sumar kanshi,

"Mami wallahi banji ba, umm lafiya lau" bayan ya juya ya kalli Rukayya wacce keta faman sussunkuyar da kai cikeda kunya, ita mami sai abin yayi mata dadi domin duk a tunaninta Rukayya tayi masa sai dai shi acikin zuciyarsa sam yarinyar bata yi masa ba,

Juyawa yayi ya fita yana cije lebenshi na kasa, dakinshi ya shiga ya zauna ya jawo katuwar laptop dinshi yafara danne danne.

  Dare ya raba yana kallon wani american film mai suna prison break, bashi ya kwanta bacci ba sai wurin karfe 3 nadare wannan dalilin ne yasa da safe ya makara domin sai karfe 11 ya iya tashi,

Ganin ya makara yasa ko makaranta bai shiga ba yayi zamansa agida ya shiga daki ya kulle kanshi ya kunna kallo.

  Ummulkhair yau sam bata ga sawwam ba abokin fadanta,kasa hakuri tayi har sai da ta fadawa alawiyya,

"Alawiyya yau fa banga mutuminki ba wannan dan rainin hankalin, ko kin san jiya bayan nadawo daga saloon shine y kawoni?"

Dariya alawiyya tayi ta dafa ummulkhair "kodai har kun daidaita kanku mu kuka mayar garori.."

"Allah ya sawwake, ni inada masoyina jiyama katin 2000 ya turo min, kuma in baki labari dazun nanma muka gama shan soyayyarmu..."

Dariya alawiyya tayi harda rike ciki, "kema dai wallahi baki da wayo, to kika sani ko sawwam dinne yake yimiki text massage?"

"Bashi bane ai indai sawwam ne to da kuwa sai nafasa wannan wayar tawa, nasanma ba shi bane domin ai shi inada number dinshi tun lokacin da yayi min massage ya bani hakuri.."

"Hmmm to shikenan.." Alawiyya tace da ita tana murmusawa,

"Ni kinga yanzu siyayya zan je, kayan kwalliyana sun kare gashi kuma kayan amfani na ma sun kare, jiya abba ya turo min da kudi.."

"Sai kin dawo" alawiyya tace da ita tawuce,

Juyawa ummulkhair tayi ta fita ta samu keke napep tace ya kaita store zatayi siyayya,

Wani babban store ya kaita ta shiga tabarshi awaje yana jiranta,

Sawwam yana daki yana bacci mami tazo ta tasheshi akan yazo yakai Rukayya shopping domin ita momy so take tayi amfani da wannan damar sawwam ya dan shaku da Rukayya din kafin tabar gidan,

Yana kunkuni yana komai ya shiga wanka ya fito duk ransa abace shi da yasan hakane ma da yayi tafiyarsa sch akan ya zauna yakai wannan yarinyar shopping,

Ransa abace ya shiga sashen mami yana sanye da blue din jeans da bakar riga, batare da yayi magana ba ya juya ya fita domin yasan sun ga shigowarsa,

"Tashi kibishi kinji, kiyi hakuri dashi kin san wani irin yarone sawwam sam baya son kula yanmata narasa dalili.."

Mami tace da Rukayya, tashi Rukayya tayi tabi bayanshi tasha kwalliya cikin leshi golden colour mai duwatsu ajiki tasa farin mayafi da farin takalmi sai kamshin turare takeyi,

Acikin mota ta sameshi ta shiga suka tafi, bakin glass yasa kamar yanda ya saba amma fuskarshi babu wlwala tamkar zai saka kuka haka yakeji,

Perfect store ya nufa da ita yana zuwa yayi packing ya fito itama ta fito suka shiga tare, layin kayan kwalliya suka bi Rukayya tana dan daddaukar abinda yayi mata, suna karyo kwana ya hango wata kamar kairi hannunta rikeda karamin basket ta cikashi da kaya,lokacin da sukaje kusa da ita ne yagane ashe ita dince, pad ta diba guda biyu tasaka acikin kwandon, kura mata ido yayi da abinda ta dauka,

"Tana off kenan ni dama nasan arina domin naga kafarta ta sake yin haske fiyeda ko yaushe..." Yafada yana kallon kafarta, barin Rukayya yayi abaya ya matsa wurin ummulkhair,

Kamar besan da ita ba yayi, tana jiyowa itama ta ganshi sai yan kalle kalle yake yi,

"Basai kin nunawa duniya kin fara period ba idanma baki dauko wannan abun kin tallata ba mun san kin fara.."

Harararshi tayi aranta tana ganin kokarinshi na iya fada mata haka da yayi,

Banza tayi dashi saboda ta fuskanci shima kwallo ne idan ta biye masa hayaniya zasuyi awurin,

Wuceshi tayi ta nufi wurinda za a lissafa mata kayan, hakan da tayi yasa sawwam yin murmushi domin yafara samo lagonta, hanzartawa yayi yaje wurin da take tsaye,

Angama lissafi kenan an zuba mata kayan a leda,

"Barshi zan biya miki kinci darajar budurwata..." Ya nuna mata Rukayya da dan yatsanshi wacce ita rukayyan ma bata san abinda yake faruwa ba kasancewar tana can tana zabar turaruka, bude ido ummulkhair tayi ta kalli yarinyar da ya nuna mata a matsayin budurwarshi.....

aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment