*RAMUWAR GAYYA...*💘
_Love story 50,50_
*_UMMI A'ISHA_*
_with_
*_PHERTYMERH XARAH_*
37
*Z*ama ummulkhairi tayi sukuku hankalinta ya dan tashi zuciyarta sai harbawa take yi,
"Oh Allah gani gareka, ya Allah kai kadai kasan abinda kake nufi da haka...." Tafada ahankali sai kuma hawaye ya hau tsiyaya daga idonta, kuka tayi sosai wanda ita kanta bata san ko na menene ba,
Ta dade tana risgar kuka wanda anan take kanta yafara ciwo, dolenta ta nemi wuri ta kwanta sakamakon ciwon da kanta ke yi,
Bacci ne ya samu damar daukarta wanda tajima tana yi daga karshe ta tashi afirgice sakamakon wani mummunan mafarki da tayi da sawwam,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, allahuma inni a'uzubika min sharri fi manami an yadurruni fi dini wa duniyaya..." Tafada atsorace tana dube duben gefenta da kusa da ita,
Wayarta ta dauka takira number din sawwam, akasalance ya daga wayar sakamakon shima barcin yake yi,
"Hello matata..." Yafada cikin muryar bacci,
"Sawwam lafiya kake? Babu abinda ya sameka?" Ta tambayeshi jikinta har rawa yake,
"Lafiyata lau bacci nake yi amma yanzu tunda natashi wanka zanyi nataho wurinki"
"Dagaske babu abinda ya sameka?"
Murmushi yayi "meya farune? Ance miki wani abu ya sameni ne?"
Kai ta girgiza masa kamar yana ganinta,
"A,a kawai dai wani mafarki nayine wanda ya razana ni, nikuma wallahi na tsorata gashi bana son wani abu ya sameka" yanda tayi maganar kamar zata saka kuka,
"Ashe kina sona da yawa haka, wohhhh ashe nima dan gatane ana sona sosai ba ason wani abu ya sameni"
"Kayi hakuri na katse maka baccinka, am sorry"
"Babu komai my lonely, naji dadi ai da naji muryarki awannan time din"
"To sai ka shigo"
Murmushi yayi yafara kokarin tashi, "kiyi min kwalliya fa"
Bata bashi amsa ba ta katse wayar tana zazzare idanu domin tayi mutukar tsorata da mafarkin da tayi, fatanta dai guda dayane na Allah yasa ba wani abu neba yake shirin samun sawwam.
Daurewa tayi ta cire damuwar dake ranta tayi wanka ta shirya tayi kwalliya, riga da skirt tasaka na atamfa ta saka farin hijab ta fita Inda sawwam ke tsaye yana jiranta,
"Kinyi kyau" taji yafada lokacin da ta karasa gabansa,
"Kaima haka"
"Nidin kyau nayi?" Ya tambayeta cikin tsokana,
Murmushi tayi ta matsa jikin motarshi ta jingina,
"Yau ina cike da farin ciki saboda yanzu nasan kin kusa zama mallaki na"
Kallonsa tayi tana jin faduwar gaba atare da ita "wai kai da kafara neman aure baka fara aikiba waye zai rinka ciyar damu?"
Dariya yayi yana kallonta, "Allah ne zai ciyar damu amma ta silar dad, ke nifa wallahi idan nakara wata biyar nan gaba ba ayi min aure ba to sai an kwantar dani agadon asibiti..."
"Allah yabaka lafiya, kana nufin kenan yanzu nan da wata nawane bikin?"
Kallonta yayi ya harde hannuwansa a kirjinsa duka,
"Ai samun lafiyata kawai a aura min ke wallahi, biki kuma nan da wata biyu insha Allah zaki zama amarya"
Murmushi tasaki tajuya ta fuskanceshi,
"Sannu fa, nan da wata biyu fa kace? sai kace wani a film aure nanda wata biyu?"
Dariya yayi sannan yabata amsa, "to shikenan ki zauna kigani, wallahi bikinmu bazai wuce hakafa kuma zakice nafada miki, sannan da kike wani zancen kamar a film to ba a film zaki ganiba afili zaki gani filin ma kuma akanki"
Kallonsa kawai take tana yin murmushi amma bata gasgata shi ba saboda atunaninta koda za ayi bikin to kila sai kamar nanda wata biyar ko shida domin yanzu suna dab da shiga level 4,
"Ke kinfi sone ayi bikin bayan kin gama karatu?"
Kai tadaga masa, "ehh wlh"
"Tab ai kuwa hakan bazai yiyuba garama ki ware" yafada yana tabe baki,
"Shikenan Allah ya tabbatar da alkairi" tafada cikin sigar kalar tausayi,
"Amin, da tun farko ma hakan kika fada da yafi miki"
Zuba masa ido tayi kawai tana kallonsa ko kiftawa batayi, ba karamin sake haduwa yayi ba, yayi kyau sosai fiyeda lokacin da yana dalibi,
Matsawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta,
"Gaskiya wannan ramar da kikayi ki mayar da ita kafin lokacin aurenmu"
Murmushi kawai tayi batace dashi komai ba domin ita dai tun lokacin dataji angama maganar aurensu sai ta nemi nutsuwarta ta rasa gashi duk jikinta yayi sanyi hankalinta ya tashi,
"Wai ke duk fargabar auren ce haka?" Yace da ita yana dariya,
"Hmmm dama ai kai dariya zakayi nasani"
"Wallahi kamar kin sani kuwa, kina kuka ranar nikuma ina dariya..."
"Wallahi dan baka san yanda nakeji bane, zuciyata har wani harbawa take yanda kasan gobe ne auren"
Dariya yasaka yana kallonta, haka yasata agaba yanata yi mata dariya, sun dade suna hirarsu sannan yayi mata sallama yatafi,tunda yatafi kuma kullum yana hanyar zuwa wurinta koda yaushe suna tare gashi takusa fara exam.
Gidansu sawwam kam dagaske shirin aure suke yi sosai domin mami harta fara hada lefen sawwam, kaya kam masu mutukar tsada ta siyo, kullum cikin yin waya take tana bada sautin kaya asiyo mata daga dubai, kasancewar bata san abinda hajiya raliya mahaifiyar rukayya tayi mata ba yasa take bata sautin kayan kusanma fin rabin kayan hajiya raliyan ce ta sissiyo,
Tashinsa daga bacci kenan bayan yagama waya da ummulkhairi ya nufi part din mami,samunta yayi acikin bedroom dinta tana dudduba wasu kaya wanda zata saka acikin lefen, zama yayi akan gadon mami yana kallon kayan,
"Mami wai har yanzu ba agama hada kayan bane?"
"Ankusa agama ai, nanda sati biyu masu zuwa zamu kaimusu asaka maka date din biki"
"To mami Allah ya kaimu"
"Yawwa amma fa ba asaka inner wears ba, menene size dinta?"
Sosa keya yayi sannan ya kalli mami,
"Mami wallahi ni ban saniba amma tunda yanzu zanje wurinta sai na tambayeta"
"To shikenan amma karfa ka manta saboda nafi so komai ya zama ready"
"To mami, barima natashi naje"
Mikewa yayi da niyyar fita sai kuma yaga dad dinshi ya shigo cikin dakin cikin shirinsa na zuwa office,
"Dan gidan dady ka shirya fa ranar Monday zaka fara fita aiki domin har an fitar da offer dinka"
Cikeda farin ciki sawwam ya isa gaban dad ya rungumeshi,
"Thank you dad, thank you dad, thank you..."
Murna mami tafara yi tana addu'ar Allah ya sanya alkairi, zuciyarta jinta take tayi mata sanyi domin ganin danta datafi so tafi kauna yakusa zama cikakken mutum ga aiki ga aure,
"To duk da nidai ba asaka ni acikin maganar ba amma zanyi magana, naga wariyar launi ake nuna min, awanne ministry zai fara zuwa aikin?"
Mami tafada cikeda zolaya,
"Ba wariya bace maganar ce iya dan gidan dady dani ta Shafa, a code of conduct bureau ne kin san abinda ya karanta bangaren statistics ne dan haka dole sai a irin wadannan wuraren zaiyi aiki, suna da headquarter a abuja amma nace shi abarshi anan kusa dake.."
Murmushi mami tayi cikin barkwanci tace, "to ai nima nakusa sallama dashi tunda ya kusa aure kaga shikenan"
Sum sum sawwam yasa kai yafice daga dakin ya nufi nashi, wanka yayi yana wankan yana tunanin irin zaman da iyayensa suke yi wanda tun tasowarshi bai taba ganin suna kace nace da junaba idanma suna yi to basu taba yi agaban idonsa ba,kullum cikin barkwanci suke gashi sai kace wasu kakanninsa wannan ya tsokaneshi tacan wannan ya tsokaneshi tacan fata yake aransa shima Allah yasa irin wannan zaman zasuyi da lonely dinshi.
Shiryawa yayi sosai cikin kananan kaya gashi ba karamin kyau suka yi masa ba,
Makarantar su ummulkhairi ya nufa, fitowarta kenan daga lecture sai gashi aguje tagabanta kamar zai kadeta, cikin razani ta kankame alawiyya, burki yataka yana dariya ya koma baya, bude idonta tayi tana kallonsa,
"Alawiyya kinji yanda na tsorata, tab lallai sawwam wallahi zaka sani bari nazo"
Dariya alawiyya tasa ta juya tafara tafiya tana cewa "kunfi kusa nidai kinga nayi nan sai gobe idan kuma nasamu nashigo karatu da yamma shikenan"
Wurin sawwam ta nufa yana cikin mota yana waya dasu Abdul yana fada musu cewar yasamu aiki yanzu ma haka ranar monday zai fara fita office, nan Abdul yake fada masa shima yaje yayi interview awani ministry suma su suhaib duk sun halarci interview din"
Murmushi sawwam yayi ya daki sitiyarin motarshi,
"Hohhhhh! Lucky guys, kace mun kusa fara amsar salary....."
Ganin ummulkhairi tsaye tana jiransa yasashi yiwa Abdul sallama ya kashe wayar ya fita wurinta,
"Meye naga kinbi kin wani bata rai"
Harararsa tayi ta juyar da kanta, "to meyasa zaka wani zo ka tsoratani daka kadeni fa?"
Murmushi yayi yana kallonta, "koda ace na kadeki ai ba fasa aurenki zanyi ba, ke matsoraciya ce wallahi"
"Nayarda" tafada har lokacin bata kalleshi ba,
"To nidai ba fada nazo ba yau, mami ce ta aikoni in tambayeki size dinki,nasan na takalmi dai 38 ne shi harma an sissiyo, yanzu na inner wears nake so"
Shiru tayi takasa magana domin kunyar fada masa take, dakyar ta bude bakinta,
"36"
"36 fa? Tab" yace da ita yana dariya,
"Sai kayi kuma" tafada tana harararshi,
"Kin san me? Kinata cewa wai idan munyi aure waye zai ciyar damu to nasamu aiki ranar monday ma zan fara fita office"
Juyowa tayi gaba daya ma tamanta da cewar tana jin kunyarshi, tsalle tayi ta rungumeshi, tana fadin,
"Congratulations dear....."
Sai kuma tayi saurin sakinshi ta rufe fuskarta,
"Au, wallahi duk tsananin murna ce"
Dariya yayi ya kalleta,
"Bawani murna kedai kawai kinyi missing dina kina so kiji farin ciki"
Dariyar itama tayi, "koma me zakace dai nayarda, nidai yau ina cike da farin ciki"
Hira sukayi mai cike da kaunar juna lokacin, sai bayan isha sannan yatafi,
Ranar monday yafara fita aiki, duk kuma sai ummulkhair taji babu dadi saboda rashin ganinshi wuni guda domin da dane da tare zasu wuni duk kuwa da cewar suna yi suna fada amma dole haka zasu zauna tare,
Shima a bangaren sawwam din yayi missing dinta sosai dan haka yana tashi daga office wurinta ya wuce,
Lokacin da tafito ganinshi tayi agajiye yana tsaye yasha farar shadda riga da wando ita sai abinma yabata dariya domin duk yayi mata kalar tausayi, baifi minti goma ba yatafi gida, tun daga lokacin haduwar tasu tazama sai dare sai ko a weekend domin kullum yana office,
Salary dinshi nafarko gida uku ya raba yabawa maminshi kashi daya ya dauki daya sannan ya kai daya kason cikin daya account dinshi yafara tarawa ummulkhair, duk da haka sai da ya cira acikin kudinsa ya siyo mata turaruka da kayan kwalliya.
38
Lokaci babu wuya har su ummulkhair sun kammala exam dinsu, ranar da suka gama ranar ta tafi gida dayake jarabawar safe sukayi, kwananta biyu da tafiya aka kawo lefenta aka yanke date din biki karshen wata mai zuwa, murna awurin yan gidansu ba a magana, sawwam kuma yafi kowa farin ciki ganin ansaka masa ranar kamar yadda ya nema, ita dai ummulkhair tana cikin wani hali gaba daya jinta take sukuku gashi tanata jin tausayinsu ita da sawwam,
Satinta biyu agida sai gashi ya jemata,da murna ta tareshi tana fara'a,
"Kai yarinyar nan kiba zakiyi, ji fa tun yanzu har kinyi kumatu daga dawowa"
Murmushi tayi ta zauna bayan ta gabatar masa da kayan motsa baki wadanda ta tanadar masa,
"Kin fara zama yar lukuta wallahi idan kikayi nauyi dayawa bazan rinka daukarki ba..."
"Kai sawwam dan Allah" tafada cikin jin kunya, kwaikwayon maganarta shima yayi yace,
"Kai khairi dan Allah" dariya suka saka daga shi har ita.
Hira sukayi sosai lokacin da yatashi tafiya yajata motarshi ya dauko mata wata katuwar leda,
"Mami tace akawo miki wannan"
Karba tayi tana leka cikin ledar tana dubawa taga kayane kayan gyara irin na amare, "lallai mami tana son danta" tafada acikin zuciyarta,
Hannunta taji ya dan buga, "wai kayan menene? Nifa mami nagane yanzu tafi sonki akaina"
Murmushi tayi, "wallahi mami tana sonka kaima"
Gyada kai yayi "naji wannan, fita zan tafi"
"Haba sawwam meye abin fushi? Harda korata..."
"Na koreki din"
Murmushi tayi ta kalleshi "nima fa ban san menene ba sai naje ciki zan duba"
"Tace ai akwai takarda anrubuta komai ajiki, mantawa ma nayi da ban dauka na karanta ba"
Hannu ya mika zai kwace ledar tayi saurin kankameta ajikinta, yanaja tana ja, ganin ledar zata yage yasashi sakar mata ya tabe bakinshi,
"Idan tayi tsami zamuji"
Dariya tayi aranta tana cewa "mami ai kai take yiwa gata"
Amma afili sai tace masa "bama zatayi ba"
Sallama yayi mata suka rabu cikeda kaunar juna, lokacin dataje gida ta nunawa mama kayan ba karamin mamaki mama tayiba saboda ganin irin soyayyar da maman sawwam ke yiwa ummulkhair,
Nan itama mama tadage wurin gyara yarta, amma kullum ita ummulkhair cikin kuka take shikuma sawwam sai zumudi yake domin bikin yazo, shida abokansa koda yaushe cikin shirin bikin suke,
Itama ummulkhair ita da kawayenta sai tsare tsaren yanda bikin zai kasance suke,
Sawwam kullum cikin yimata waya yake yana zolayarta gashi tsabar zumudi kullum agidansu wanda zasu zauna da ita yake kwana,
Yauma yana gidan akwance shi kadai ya kirata yana tsokanarta,
"Wai kana inane?" Ta tambayeshi,
"Ina gidanki, a dakinki"
"Gidana kuma? Saboda kaine gandoki"
Murmushi yayi, "wallahi dagaske fa ina cikin dakinki, acan zan kwana"
Katse wayar tayi tana cewa "ohh sawwam zumudinka yayi yawa"
Wayarta ta latsa ta kira alawiyya tafada mata biki yakusa saura sati biyu, sai dai alawiyyan bazata samu damar zuwaba domin itama sunada bikin cousin dinta amma tayi musu addu'ar samun zaman lafiya.
Angama dukkan shirye shirye ranar alhamis za ayi kamu, aranar aka yiwa ummulkhair kunshi na jan lalle da baki kuma aka yimata gyaran gashi nan tafito a amarya sak tayi kyau sosai,
Misalin karfe biyar akayi kamun awani hall dake harabar hotel din nishadi hotel babu karya kamun ya kayatu kuma ya hadu sosai, aranar shima sawwam suka taho dasu Abdul duk cikinsu shi kadai ne zaiyi aure domin su koma shiri basu fara yiba,dan haka sai tsokanarshi suke suna cewa zai rigasu tsufa,
Karfe 6 aka gama kamun suka koma gida lokacin suma su sawwam sun sauka suna hotel suna hutawa,wayarta yakira sai daf da zata katse sannan ta dauka gabanta yanata faduwa,
"Sawwam.."
"Kun dawo daga wurin kamun?"
"Ehhh" tafada a takaice domin ita yanzu sam bata son ganinshi bata son jin muryarshi asalima tsoronshi taji tanaji,
"Bakya nemana ne?
Yasake tambayarta"
"Uhm" tabashi amsa,
"Kikace uhm? Dagaske bakya nemana? Nito ina nemanki kuma zanzo yanzu"
"To" tace dashi tareda katse wayar tana turo baki tamkar yana ganinta.
Karfe takwas suka je gidansu kairin, ko ina yan uwane duk sun tattaru sun cika gidan, dakyar ta samu ta fita ko kayan da tasaka taje wurin kamu bata cireba, mayafi kawai tayafa ta fita,
Suna cikin mota shida abdul ta tsaya daga waje suka gaisa, kallonta kawai sawwam yake yi ganin yanda tayi kyau tasha kwalliya a fuskarta ga kunshi yazanu radau ahannunta da kafarta,
Gaisawa sukayi da abdul yanata tsokanarta, kallon sawwam tayi,
"Kaina ciwo yake bari nakoma ciki"
"To kafin ki tafi kiyi kissing dina"
"A'a wallahi...."
Hannunta ya riko yajata da karfi kawai sai jinta tayi tafada kan jikinsa, kunyace duk ta kamata ganin abdul yana wurin, shikuwa Abdul naganin haka yafita daga cikin motar yabasu wuri,
Rungumeta sawwam yayi yana kallon fuskarta
"Da haka zaki barni natafi babu kiss babu hugging?"
"Dan Allah kayi hakuri"
"Kiss me..." Yace da ita yana sake matseta ajikinsa,
"Kayi hakuri"
"Ok bakya son kije ki huta din kenan"
Dagowa tayi da niyyar yi masa magana taji lips dinshi kan nata........
Ummi Shatu
Pherty Xarah
No comments:
Post a Comment