Tuesday 21 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 34

*RAMUWAR GAYYA....... 💘*

_love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

            &

*Ummy Aysher*

     34


   2 days later~

  Momin Rukayya taje gidan, sun jima suna hira da Mami Duk mgnrta dai akan irin son da rukkaya ke yiwa sawwam ne,

Mami tayi murmushi tana kallonta,
'a ynxu sawwam bashida buri kamar khairi duk ynda kike tunani ba haka bane a ynxu domin sawwam baxaa mashi dole ba,

'amma ai tun farko munyi niyar hadasu aure ne har kika amince da Rukayya taxo gidannan saboda shi, inaji har shopping yaje da Ita, ba mami taja numfashi,

Sawwam baya son rukkaya, khairi yake so, baxan tursasa mashi ba haka kuma baxanyi baqin ciki idan har yace Rukayya take so ba sai dai itama khairi abinso ce, fatana Allah ya bashi mace ta gari wadda xata riqesa da ya'yansa amana shine burina,

Maman Rukayya tayi shiru kafin tace Ina Swiss lace ďin da mukayi magana dake ki ďauko su naje dasu ko xa'a samu masu siye sai a saro wasu,

Shikenan mami ta faďa bayan ta tashi ta nufi dakinta da sauri maman Rukayya tayi kitchen inda Mai aikinsu, ta ciro magani Acikin Leda baqa ta bata,

'Kan Mgnr da mukayi dake a waya gashi ki sanyawa sawwam a abinci Kuma ki tabbatar da yaci kada kibari a ganki, ga dubu goma idan aikin yayi xn qara maki wasu akai, Mai aikin ta karba jikinta na rawa,

Xamanta a falon yayi daidai da fitowar mami ďaki ďauke da kayan ta xube su a gabanta tana kallonta,

'gasu guda goma ne, kinsan kuďin ni banason masu riqe bashi,

'hakane ni ma banaso nasan Waďanda xn baiwa, ta soma haďa kayan.......

*

'kibari anjima xn shigo, kinga ynxu Inaso nayi wanka, ga yunwa, ga barci.....

'tor kabari nayima girki anan Pls sahibina, ni banaso ka tafi ne,

'idan kinmin girki shi Kuma wanka fa? Ya faďa Idanunsa akanta, murmushi tayi,

'kaje gida kayi mana, ya tayarda motar yana faďin,
'shima abincin kibari naje gida naci, through out yau fa muna tare, bawai nagaji da ganinki bane is just that kamar banajin daďin jikina,

'shikenan Allah ya kaika lfy ta juya xata fice ya riqo hannunta ta dubesa,

'hope bakiyi fushi ba, ta gyada kanta,
'smile... ta bata fuska,
'Pls khairi..... taqi,
'anjima xnxo I promise you, I will be with you, pls smile, tayi murmushi tana kallonsa,

'kaxo min da irin Wannan cake ďin na jiya,

'oh Mami tayishi fa, kinji daďin sa kenan, ta gyada Kai tana kallonsa da murmushi,

'shikenan idan akwai sauran xn xo maki dashi, but remember me kafin naxo,

'Tace shikenan safe trip,
'yace bako kiss ko sau ďaya ne a kumatu,

'lol kai kafiye shirme wani sa'in,
'shikenan ni Kuma baxan xo ba, ya ďauke kansa daga kallonta, tayi dariya ta fice daga motar, ta rufe kana ta sunkuya ta glass ďin motar,

'idan kaxo anjima xn yima, ya dubeta,
'you promise....
ta gyada Kai tana murmushi,
'idan kika qi fa?
'baxan qi ba.... yayi murmushi yaja motar ya fice....,

Yana xuwa gida Kai tsaye dinning ya xauna yaci abinci sosai Mai aikin na labe tana kallonsa, bayan ya gama wanka yayi, bayan yayi sallah ya kwanta barci.....

Yinin ranar basuyi waya ba Kamar yanda suka saba, bata damu ba tunda ya gayamata barci xaiyi,

Da dare tayi kiran wayarsa tana ringing bai ďauka ba kuma bai kirata ba, sai ta shiga damuwa kada dai bai lfy ne....

Sawwam xaune a ďakinsa da robar ruwan swan yana kwararawa cikinsa, yana ganin kiran khairi yaqi ďauka haka kawai ya tsinci kansa cikin jin haushinta bai san meyasa ba, message ya shigo wayarsa yana dubawa khairi ce,

  _'Ina fatan ba jikin bane, idan shine Allah ya baka lfy, lonely without you....._

  Yaja tsaki ya cilla wayar aljihunsa, ya fice daga gidan, gidansu Rukayya ya nufa, daga ita har mamanta sunyi murna da xuwansu aikinsu yayi kyau kenan,

Sanda ta shiga motar ta xauna idanu kawai ya xuba mata yana kallonta, baisan dalilin dayasa xuciyarsa ta takuramasa da tunaninta ba bayan yasan ba itace a xuciyarsa ba,

'Sannu da xuwa sawwam, nayi farin cikin ganinka, yaja Numfashi batare da ya tanka ba ya ďauke kansa daga kallonta,

'baxaka shiga ciki ku gaisa da mama ba,
'not now, shikadai  ya faďa batare da ya Kalle taba,
'me xan kawo ma,
'nothing,
'uhm... uhm daman Abba ne yayi mgn kan auren mu, yaushe xaka turo ayi mgnr....

Ya juya yana kallon ta, sai Kuma ya tabe bakinsa,
'xn wuce gida ko xaki iya fita, ba musu ta fice jikinta a sanyaye yaja motar ya fice, taje tayiwa mama bayani ynda sukayi,

'kibarshi komai xai daidaita da kansa xaki ganshi yaxo neman aurenki,

Bayan fitarsa gidan kamar xaije Skul sai Kuma ya fasa har lokacin khairi na kiransa a waya daga qarshe ma kashe Wayar yayi gabaki ďaya,

A ranar khairi ta shiga damuwa, barci gagararta yayi tunani iri iri ba Wanda xuciyarta bata ayyana mata ba,

Washe garin ranar, daka ganta kasan bata cikin walwala gashi Alawiyya bata xoba ranar ballantana ta gayamata damuwarta, sukuku ta yini harta gama lectures ďin ta, koda ta fito babu sawwam bai jirataba kamar kullum alhali taga motarshi,

Xuciyarta na soma bugawa hankalinta ya tashi sosai, duk tunaninta ta kasa gano laifinta a jiya, tasan ba Mgnr kiss bane cos sun saba wannan rigimar dashi,

A waya ta kira Alawiyya take gayamata komai,
'bana tunanin wani abune amma Kiyi addua may be akwai abinda ke damunsa gobe xn shigo,

Sai ga hawaye nabin kumatunta, so painful, tana jin sonsa har cikin xuciyarta, ta qara gwada kiran layinsa tana ringing ba'a ďauka ba daga qarshe ma aka kashe wayar, ta haďa kanta da gwiwarta tana kuka sosai, Ashe haka so yake?

Kwana biyu, yana tsaye bakin motarsa yana waya ta tunkaresa, yana haďa ido da ita sai da gabansa na faďi harda sauke numfashi sai dai fuskarsa ba walwala, ta matsa kaďan kusa dashi,

'miye laifina da kake hukuntani haka, ko daman ka shigo rayuwatane dan ka yaudareni.... sai ga hawaye sharrrrr, yaji tausayinta sosai sai yaji kamar ya rungumeta yabata haquri, ya riqa hannunta suka shiga mota kana ya juyo da Ita suna fuskantar juna,

'bansan meke damuna ba, kawai na tsinci kaina cikin jin haushinki, in short kamar bana son ganinki amma kina xuciyata,

Gabanta yayi mummunan faďuwa ta ware idanu sosai tana kallonsa jin kalamansa, baya son ganinta, meyasa, saboda wane dalili,

Ya soma share mata hawayen fuskarta,
'I think komai xai daidai ta but just pray for me, ina sonki khairi... ga mamakinta sai ji tayi ya rungumeta sosai a jikinsa yana rarrashinta, da sauri ta xame jikinta daga nasa har lokacin idanunsa akanta, ta soma share hawayenta, gskyr Alawiya da tace ta tashi da addua meyiwuwa maqiya suka shiga alamarinsu gashi shima ya gayamata ta tayashi da addua, dole xata tashi tsaye akan xamantakewarsu,

Ta saqala hannunta cikin nasa, ya juyo yana kallonta har numfashinsa ke fita da sauri da sauri,

'ba kiyi fushi ba, kin haqura,

'ta gyada Kai tana kallonsa da murmushin yaqe, shima murmushin yayi cikin farin ciki.



Pherty

    &

Ummi shatu 🏼

Getting better, tnx 4 d Luv an care my fans....

No comments:

Post a Comment