Monday 20 March 2017

RAMUWAR GAYYA..29

*RAMUWAR GAYYA....... 💘*

_Love story 50,50_

29

*Fertymerh Xarah*

           &

*Ummy Aysher*

  Ta qara kallonsa,
'kabani xnje gyaran ďaki na, ya miqa mata ledar yana kallon qafafunta,

'Ina son wannan lallen sosai ya birgeni, ďago kafar ingani,

'kajika da wani xance, ta Karbi ledar haďe da qara lullube qafafuwanta da hijab ďinta,

Ya ďauke kansa daga kallonta yana kallon wani gun alamar yayi fushi, tayi mgn yayi mata banxa sai tayi murmushi haďe da sunkuyowa,

'Haba nawan, miye abin fushi akan abinka, yayi mata banxa,

'ko in baka qafar ne ka cinye duka, ya juyo haďe da faďin,

'da dai yafi, tayi murmushi haďe da lumshe idanuwanta,

'duk na gaji sosai, kamar baxan iya gyaran ďakin ba,

'sorry dear, ko inje in gyara maki ne,

Ta girgixa kanta tana kallonsa cikin dariya, ya kwantar da seat ďin da take xaune akai yana faďin bari nayi maki tausa it may help you,

Tayi saurin tayar da seat ďin tana faďin,
'see you bana son haka, kan wane dalili xaka min tausa nace ma Ina buqatane,

Ya koma ya xauna yana faďin,
'da dai kinbari nayi maki xaki ji daďina, ko banxa ma hannuna taushine dashi dan yafi naki,

'ban yarda ba, nawa yafi naka,
'to kawo a gwada, ta kwashe da dariya haďe da buďe motar,
'naqi wayon salon ka taba min hannune, murmushi yayi yana kallonta bayan ya tayarda motar,

'inma tabi ne da sauqi akan.....bari dai nayi shiru na tuna kefa yarinyace,

'ta tabe bakinta cikin murmushi ta rufe motar ta sunkuya ta glass ďin tana faďin sai da safe dear,

'idan kin gama aikin flash me I will call you back,

'shikenan sahibina, a gaida Mami,

'xataji Insha Allah, ya tayar da motar cikin murmushi, ta ďaga masa hannu ta fice,

Tana xuwa hostel tayi gyare gyarenta tayi wanka kana ta xauna cin shawarma, bayan ta gama ta kora da ruwan lemu kana ta Kira Alawiyya taji ko ta dawo,

'gobe dai xn dawo, bngama kimtsawa bane amma gobe Ina hanya,

'Allah ya kawo ki lfy,
'Amin ta tsinke Wayar,

Sawwam ya kirata suka shiga waya...

*

Washe gari kasancewar Alawiyya abokiyar yawonta bata nan duk inda sawwam yake tana tare dashi, shima sai ya kyale su Abdul ya nacewa sahibarsa,

'3 pointer fa ďan iskane, yaron dake cewa bai iya soyayya da waccan yarinya amma ynxu yafi jinta akan mu, cewar hafix

Abdul yace sanda nace ina sonta sai ka gani naushine kawai bai kaimin ba, wai na xubar da ajinmu mexanyi da waccan Ashe shegen sonta yakeyi,

'itama ai sonsa takeyi baka ganinsu kamar xasu jinye junansu, sawwam an shiga kogin soyayya kaga ko xama damu ba'a yi ynxu sai an sami matsala ya dawo mana,  suka kwashe da dariya,

Ranar ya ďauki khairi yaje da Ita gidansu, tun da suka shigo harabar gidan take kallon yanayin gidan, lallai su sawwam masu kuďi ne,

Da kansa ya buďe mata motar yana murmushi, itama ta fito fuskarta da murmushi rataye da Jakarta,

Yana gaba tana biye dashi a baya har suka shigo falon,

'ki xauna kina wani ďar ďar, ko kina xaton xn cutar dake ne?

Ta xauna har lokacin bata tankaba sai dai fuskarta taqi gushe murmushin dake kanta,

'let me call mother, yayi hanyar ďakinta ta bisa da kallo kafin ta juyo tana kallon tsarin falon,

Ba qaramin birgeta yayi ba, falon baida hayaniyar kaya sai dai komai mai tsada ne, tana kallon hotunansa dana iyayensa ya dawo kusa da ita ya xauna yana faďin,
'Mami tana xuwa, ta gyada kanta kawai, shi ya riqa janta da fira ganin taqi Sakin jikinta har Mami ta shigo,

Khairi ta russuna cikin girmamawa tana gaidata a kunyace, Mami tayi murmushi kafin ta amsa,

Yau naga ummulkhairi, na dade inajin labarinki a gun sawwam, bashi da mgn sai taki Ina roqonki da ki riqeshi amana domin yana sonki,

Khairi ta sunkuyarda kanta cikin jin kunya bayan ta dubi sawwam, Mami ta dubi sawwam,

'na yaba da matar ďana, kaima ka riqe amana,

'Mami ni baxanci amanartaba kinsani, bnda wadda nake so bayan ita, kice karta cutar dani tabarni taje ta sami wani,

Lokaci ďaya Mami da khairi suka yi dariya, suna xaune gurin masu aiki suka soma kawo mata abinci, sosai Mami ta tsareta sai taci duk a takure take musamman da sawwam yace tare xasuci kamar xata nutse qasa saboda kunya,

Kabarta son taci kada ka takurawa ya'ta,

'au Mami har kin yayeni kin kama ta,

'sosai ma kuwa,

Cikin barkwanci suke hirar su gwani sha'awa kamar ba surukai ba, sosai khairi ta saki jiki da Ita sukayi hira...

Sanda xataje, kayan kwalliya da sarqoqi ta bata masu kyau da tsada kana ta roqeta ta riqa xuwa nan ma ai gidane,

Jinjina kai kawai khairi tayi tana murmushi bayan tayi mata godiya,

Suna cikin Mota ta dubesa da murmushi,
'Mami is simple batada hayaniya naji Ina sonta, murmushi yayi

'nima karamcin da mama tayimin ya Sanya naji ina sonta, duk iyayenmu suna son mu, auren mu xaiyi albarka,

'tayi murmushi xuciyarta cike da farin ciki tana kallon gefen hanya.


Pherty

     &

Ummy shatu

My wattpad Phertymerh1

No comments:

Post a Comment