Thursday 30 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 44

*_Ramuwar gayya..._*💘

  _Love story 50,50_

*_Ummi A'isha_*

             _*&*_
  *_Phertymarh xarah_*


  44

     Kallon dad sawwam yayi zuciyarsa tana zafi kirjinsa yana bugawa dum dum,

"Bakaji abinda nafada bane? Nace ka sakar musu yarinya sudaina yimin aike na wulakanci gidana, kai in banda ma rashin tunani baka duba cin mutuncin da baban wannan yarinyar yayi maka agaban mutane ranar daurin aurenku?..."

Dagoda idanuwansa sawwam yayi wadanda nan take suka rine izuwa jajaye,

"Dad ya kuke so muyi ne? Kun hanamu mu zauna da junanmu, kun hanamu sakewa kuna neman ku haramta mana junanmu bayan kuma Allah ya riga da ya halatta mana..."

Tun kafin ya rufe bakinsa dad ya sake daukeshi da wani zazzafan mari,daidai lokacin mami ta shigo tayi gaggawar shiga tsakiyarsu tana kallon dad fuskarta cikeda tashin hankali,

Nuna sawwam dad yayi da yatsa,

"Kaima har kayi girman da zaka kalli idona ka rinka fada min duk maganar da tazo bakinka? Yaushe kayi girman da har zan rinka fada kana fada?

To ka saurareni dakyau ni ba shasha bane sannan kuma ni ba sokon uba bane bare nabarka karinka yin abinda kayi niyya, sannan ya zama dole kayi abinda nasaka in bahaka ba to sai dai ka nemi wani uban amma badai niba.."

Yana gama fadin haka yasa kai ya fita Mami ta rufa masa baya, yayinda sawwam yake tsaye dafe da kuncinsa yana jin wani irin radadi acikin zuciyarsa, shi bawai zafin marinne yayi masa ciwo ba a'a dagewar dasu dad sukayi akan lallai sai sun rabashi da khairi,

Zama yayi abakin gadon ya tallafe kumatunsa duka yana tunani acikin ransa, wannan wanne irin al'amarine wanda yayi silar katsewar farin cikinsu shida khairi,

Wayarshi ya dauka domin kiranta amma shiru wayar akashe taki shiga haka ya hakura ya gaji ya ajiye wayarshi ya zubawa screen din laptop dinshi ido yana kallon kyakkyawar fuskar ummulkhairi..

  "Haba alhaji abinfa da yaron nan yafada wallahi gaskiya ne domin harga Allah muna neman tauye masa hakkinsa, Allah ya halatta masa matarsa mukuma muna neman mu haramta masa.."

Mami tace da dad bayan sun shiga falonsa, cikin takaici dad ya juya ya kalleta,

"Kema kin goyi bayansa kenan, kin goya masa baya ya bujirewa umarnina duniya ta tozartani ko? Kina son nahakura na zuba masa ido yaci gaba da zama da auren wannan yarinyar wadda ubanta yake barazanar kaini koto ko,

To bari kiji nafada miki wallahi baki isaba daga ke harshi baku isaba, yazama dole kubi maganata domin dukkanku a karkashin ikona kuke.."

"Ba maganar goyon baya bane ai, gaskiya nafada maka, tunda yaron nan yafito kiri kiri ya nuna mana yana bukatar matarsa to babu dalilin da zaisa mudage sai munga mun rabashi da ita, indai gaskiya za abi to akyaleshi ya zauna da matarsa..."

"Ba zai zauna da itaba mutukar ina raye, idan kuma auren yake so to yaje ya nemo wata sai in aura masa amma wannan kam sai ya rabu da ita"

Sassautowa mami tayi tafara bawa dad hakuri,

"Haba alhaji dan Allah muyiwa yaron nan adalci mu barshi da matarsa karmu rabasu da ita, wallahi sawwam tun jimawa yake son aure ni nasan haka, idan muka hanashi zama da wannan yarinyar tofa Allah ne kadai yasan irin halin da zai shiga..."

Samun kujera dad yayi ya zauna batare da yakara cewa komai ba.

  Tun wannan fadan da dad yayiwa sawwam, sawwam bai kara fita daga dakiba, yana nan akwance yana ta faman gwada kiran layin ummulkhairi amma shiru bai sameta ba, har karfe 2 nadare idonshi biyu,

Hankalinsa ba karamin tashi yayiba, koda safiya tayi ma bai fitoba sai wurin karfe 10:30 bayan yayi shirin office,

Falon mami ya shiga tana dining tana hada musu abincin karyawa, gaisheta yayi fuskarsa babu alamun fara'a,

Tashi yayi bayan sun gaisa yanufi hanyar fita,

"Sawwam breakfast dinfa?" Mami tafada cikin kulawa,

"Mami azumi nakeyi.." Yabata amsa yana cusa hannuwanshi cikin aljihunsa, wani irin tausayinshi mami taji domin tasan abinda yake damunsa, kamar zata yimasa kuka haka takeji,

"To shikenan, me zan shirya maka na shan ruwa?"

"mami anything...."

Yafada tareda ficewa ya nufi motarsa, yau ko gaisawa da dad basuyi ba, koda dad dinma yafito zai tafi office bayan yayi breakfast mami ta soko masa maganar sawwam, bai saurareta ba yawuce ya shiga mota driver yaja suka fita,

  Zama sawwam yayi a office shiru yanata tunane tunane acikin ransa har suhaib yazo kasancewar shi suhaib bama ya kasar bai jima da dawowa ba tun lokacin da suka gama makaranta yafita business shida mahaifinsa,

"Kaga ango" suhaib yafada cikin zolaya, hannu sawwam yabashi yana murmushi amma acan kasan ransa bacin raine kwance,

"Suhaib ya garinne?" Sawwam yace dashi yana murmushi,

"Normal wallahi, ya naganka duk wani irine"

"Bacci nakeji ne wallahi"

Dariya suhaib yayi "da alama daren jiya bakayi bacci ba"

"Wallahi har wurin 3 saura idona biyu"

Dariya suhaib yasake sawa "har yanzu baka gama amarcin ba"

Murmushi sawwam yayi shi sai yanzu ma yagano abinda suhaib din yake nufi,

"Kajika da mayar da hannun agogo baya, yasu Hafiz kun hadu ne?"

"Nagano ka wato ka waskewa maganar ka dauko wata, no bamu haduba domin nima jiya da daddare fa nashigo"

"Ok to anjima sai kazo majalissarmu mu hade"

Sun jima suna hira wadda ta sanadiyyarta ne sawwam yadan ji damuwarsa ta ragu, sai wurin sallar azahar sannan suhaib yayi masa sallama yatafi,

Koda ya tashi daga office B. U. K yashiga, tunda yashiga yake ganin kamar zaiga ummulkhairin shi, kasancewar yamma ce duk yawancin daliban suna waje, wasu suna karatu wasu suna hira, wurin hirarsu shida khairi yaje yayi packing ya kwantar da kujerarsa ya kishingida yana kallon masu wucewa.

***

  Tunda mahaifin ummulkhairi  ya kwace wayarta ta shiga damuwa saboda rashin jin muryar sawwam,

Dakin mama ta shiga tasamu bata nan tana wajen abbansu, har zata fita idonta yakai kan wayar mama dake ajiye akan gado, wayar ta dauka tafita ta shiga dakinta ta shige toilet, wayar sawwam tafara kira amma bai dagaba,

Text massage ta tura masa,

  _Sahibi nice ka kirani pls_

Yana zaune afalon mami yana shan ruwa yaga sakon da khairi ta aika masa, tashi yayi yabar kayan shan ruwan yafita zuwa dakinsa, sai da yasakawa kofar dakin key sannan yafara kiranta,

"Hello sawwam"

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya iya amsa mata,

"My lonely menene yasamu wayarki?"

"Abbane ya kwace, yanzu babu waya a hannuna wannan ma ta mamace nadauko bata saniba,ina fata dai lafiya kake,me kakeyi yanzu"

"Lafiya nake khairi, ruwa ma nakesha naga text dinki shine nadawo dakina na kiraki"

"Ayya sawwam azumi kayi...?"

"Azumi nayi my lonely saboda wallahi hakurina yagama karewa akanki, idan ban sameki kwana kusa ba Allah ne kadai yasan makomata, gashi koda nazo rowa kikeyi min sai kina cewa wai in bari komai ya daidaita gashi har yanzu daidaituwar bata samuba kullum abun sake ta'azzara yake"

Jin kalamansa yasa dandanan zuciyarta ta karye hawaye suka fara bin kumatunta,

"Sawwam kodai ina cutar dakai ne ban saniba, nashiga uku, dan Allah sawwam ka yafemin wallahi bazan karaba, kayafe min kar mala'ikun rahama su la'anceni, kar Allah yayi fushi dani..."

"Ya isa khairi, nifa ba laifi kikayi minba sannan ba fushi nakeyi dakeba, daina wannan kukan please..."

"To kace ka yafe min..."

"Nayafe miki amma idan nasake zuwa kika ki to bazan yafe mikiba koda kin bani hakuri"

"Nayarda, kagama shan ruwan?"

"Ban gamaba amma jin muryarki kadai tasa naji nakoshi bana son ma nakara ganin abincin"

Murmushi tayi domin jin kalmar da yafada,

"Naje makarantarku dazu har nayi budurwa tunda bakya nan"

Ido ta zaro tamkar yana ganinta,

"Dan Allah? Haba sawwam tun yanzu,nima fa har yanzu amarya ce da har zaka fara neman wani auren"

Murmushi yayi saboda jin har ta nuna kishinta, "kina sone kitashi daga amaryar ki koma matar gida kamar kowacce mace?"

"Nidai a,a nafi son nazauna a amaryarka har abada.."

"A'a ai kuwa sai kin canja daga amarya zuwa matar gida indai kin bani dama zuwan da zanyi zan baki cikakken matsayi na matar gida idan kuma kin ki to zanyi budurwa"

Jin alamun zata yi mishi kuka yasashi saurin tsayar da zancen,

"Dawasa fa nake yi miki, wallahi dawasa nake, haba ai kece one and only"

"Har kasa hankalina yatashi wallahi"

"To hankalinki ya kwanta dan da wasa nake..."

"Zan rama ai" tafada cikin shagwaba,

"To me zaki bani idan nazo?"

"Duk abinda kake so"

"Promised?

"Yes...!" Tafada tana murmushi,

Sun dan jima suna wayar sannan sukayi sallama, fita tayi ta mayarwa da mama wayarta bayan ta goge number sawwam da text din da tayi masa cikin Sa,a kuwa har lokacin mama tana can a wurin abba bata dawoba.

  Tun daga ranar kusan kullum sai ta dauki wayar mama aboye ta shiga bathroom tayiwa sawwam plashing yakira suyi hira, last wayar da sukayi yace mata zai zo acikin week din,

Kosu mami bai sanarwa da cewar zaije bauchi ba saboda baya son ahanashi shikuma ya matsu da yaga khairinsa musamman ma yanzu a yan kwanakin nan duk hankalinsa yatafi gareta,

Boye murnarta tayi bata bari kowa yagane ba, ranar alhamis ya shiga garin tunda safe yasamu zuwa domin so yake yau yasake sosai da matarsa, wata shadda yasaka kalar ruwan toka dinkin rigar iya gwiwa ne yasa hula kalar kayan dama tun adaren jiya ya sanar mata da cewa da wuri zaizo, tana tare da mama suna aiki a kitchen ta rike cikinta,

"Mama wallahi cikina ya matsanta min da ciwo kwana biyun nan, gashi da daddare baya barina nayi bacci"

"Ai kedai zanga ranar da zakiyi hankali, kina fama da lalura amma bazaki fadaba a nema miki magani? Ki shirya idan yayanki yazo yakaiki asibiti"

"Mama idan banje da wuriba bazan samu damar ganin likita ba"

"Kuma fa hakane, to kinga jeki cikin jakata ki dauko dari biyar kitafi, wanne asibitin zakije?"

"FMC zanje mama"

"To sai kin dawo"

Dakin mama taje ta dauko kudin ta koma dakinta ta canja kaya zuwa purple din less fitet riga da skirt, tashafe jikinta da man touch me mai dadin kamshi ta shafa turare ta fito tayiwa mama sallama tafita....



aishaummi.blogspot.com

Ummi A'isha

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment