Tuesday 21 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 36

*RAMUWAR GAYYA....... 💘*

_Love story 50,50_

    *Fertymerh Xarah*

              &

    *Ummy Aysher*

     36

   Murmushi tayi tana kallonsa har cikin xuciyarta taji daďi,

Shima murmushin yayi yana kallonta,

'xan tafi na barki da faruq, I know xaku kasance tare, ta bata fuska harda harararsa,

'saboda Baka yarda dani bane kome, I told you ba komai tsakanina dashi idan ma da akwai a gurinshi to ni kaine xabina Kai nakeso,

'I trust you nasan you can't cheat on me, bama faruq kaďai ba Duk Wanda kika tsaya dashi I will know,
tayi far da ido tana kallonsa,

'taya xaka sani, Suhaib, Hafiz and Abdul ma duk xaku tafi to Waye xai gayama,

Ya tabe bakinsa,
'baxaki san kowaye ba amma ki gwada kigani, ko kin ďauka suka ďai ne frnds ďina, I have many, a class ďin ku ma akwai,

Itama tabe bakin kawai tayi,
tace nima duk ka tsaya da wata budurwa xn sani Kuma xa'a gayamin,

Dariya yayi sosai yana kallonta,
'Waye xai gayamiki, wa kika sani, su Abdul ne Kuma ba guri ďaya xamu je ba idan ma an hadamu ai baxasu gayamiki ba,
Ta tunxuro bakinta,

'shikenan Allah yana ganinka,ya mintsini bakinta,

'Allah baxai kamani da laifin komai ba cos baxanci amanarki ba, I so much love you dear,
tayi murmushi tana kallon wani gu,

'kinga baxan iya haqura har kigama Skul kafin muyi aure ba dana dawo xa'a fara mgnr aure, kin qarasa a gidana,

'ban yarda ba, Nima sai nagama karatuna kamar yanda kagama,

'Wasa kike yarinya, kibari kigani......

Posting ďin su ya fito, sawwam a Lagos shida Suhaib, Hafiz Kuma a Niger, sai Abdul dake kusa yana kaduna,

Abdul yaji daďi sosai sai dariya yakewa friends ďinsa, sawwam yaji dama shine aka ajiye a kaduna, yasan da xai bada kuďi xa'a cnxa mishi komai hanyane amma kuma yana son xuwa Lagos ďin,

Ranar da xai tafi kamar kada su rabu, harda hawayenta shima namijin qoqarine kawai yayi, da kyar ya samu ya lallabata ta haqura,

Yaja hancinta yana murmushi,
'sai kace idan nadawo baxamu tabbata a tare ba, indai nine sai kingaji dani,

ta hararesa da jajjayen idanuwanta haďe da turo bakinta tana kallon wani gu,

'gayamin me kikeso na siyo maki,
'komai banaso,
'harda ni bakyaso? ta gyada kanta tana kallonsa,
'shikenan ma baxan dawo ba xn sami wata inyamura acan na aura... ta kaimasa duka ya goce yana dariya..... da dabaru yasamu ya rabu da Ita sukayi Sallama yabar garin cike da kewar sahibarsa haka ma ita ďin.....

Tunda ya tafi kullum suna waya dare da rana, watansa uku yaxo garin Kuma tunda ya koma bai sake dawowa ba, they are missing each other.

*

Kwana asarar mai rai, Alhamdulillah sawwam ya kammala karatunsa,

Lokacin khairi itama saura shekara ďaya ta kammala nata karatun,

Sawwam yayi wani Haske ya qara kyau kamar bashi ba da alama Lagos ta karbesa sosai har wata qiba yayi,

Sanda ya dawo mami kamar xata haďiye sa dan murna, harda Rukayya ďa mamanta ma taxo tarbarsa, ganin ynda sawwam ya koma hankalin Rukayya ta tashi tunda suka koma gida kuka takewa mamanta akan sawwam, baxata iya auren kowa ba idan ba sawwam ba,

Dole su San abinyi...

Mami Kuwa ta rasa inda xata sanya tilon ďanta, cimma iri iri ta haďa masa amma hankalinsa na gun khairi,

A gurguje ya gama cin abincin yayi wanka ya shirya ya fito,

Mami tace sai Ina haka Wannan Saurin da kake daga dawowarka baxama ka tsaya ingankaba,

'inda in-law xnje mami kema nasan kina so naje,

Murmushi kawai tayi tana kallonsa har ya fice,

Tun da yagamata yaxo ta kasa nutsuwa a hanxarce ta gama shirinta ta fito, burinta kawai tasanyashi a ido,

Kamar su rungume junansu haka sukaji, sunyi matuqar kewar juna har wani kunyar juna suke domin su kasa mgn sai dai su kalli juna suyi murmushi,

Ta ganshi ya sauya yayi kyau abinsa baida wata damuwa lallai sawwam,

Anashi bangaren Kuma sai yaga duk ta faďa, sai wani Haske da tayi sosai idanunta sun xurma, ya rankwafo dai dai kunnenta,

'dear ko kin fara bleaching ne? ta ďan dubesa,

'kafara ko, kaima ai bleaching ďin kake yi,

'Ni naga kinyi haske kin rame, ramar ta mecece idan nine gani na dawo sai kin cinyeni, ya juyo kacokan yana kallonta sai taga ya mata girma sosai a gabanta,

'tor ka matsa min,
'baxan matsa ba, ni naga kamar bakiyi missing ďina ba yanda nayi, tayi murmushi tana kallonsa,

'Ni Nafi kowa missing ďin ka....

Haka suka cigaba da hirarsu kamar xasu cinye junansu,

Sawwam yayi Mgnr yana so ya tura iyayensa neman aurenta, sai ta Kira gidansu ta gayawa Abbanta,

Abba ya amince suje gun qaninsa Alhaji mukhtar su nemi aurenta cos shi baya gari,

Sunyi murna har sawwam ya qagu aje neman auren,

Shida Dad dinsa, da uncles ďinsa sukaje neman auren a gombe,

Sun sami tarba, karamci da mutunci a gidan Dad yaji daďi sosai domin mutanen sunsan darajar ďan Adam,

Batare da bata lokaci ba suka gabatar da kansu, kuma aka amince an bashi ummulkhairi,

Sunyi murna Kuma sunyi godiya sosai bama kamar sawwam har ya Kira mami ya sanarda ita,

Taji daďi sosai, kuma tayi masa addua,

Basu bar garin ba sai da suka biya Kuďin komai har sadaki ma,

Suna dawowa gida ya kirata,

'you are mine khairi....
'Tace da gaske,
'Allah sun bani ummulkhairi, tayi murmushi batare da tayi mgn ba xuciyarta na bugawa sosai, batasan a wane yanayi take ciki ba farin ciki ko sabanin haka,

'why silent dear, are you not happy?
'am happy, is just.... sai Kuma tayi shiru,
'tell me, Kada ki boyemin komai,
'bafa komai kawai najini somehow, naji inajin nauyinka and I feel so happy,

Murmushi yayi yana faďin,

'tun ynxu lallai da sauran rina a gaba, itama dariya tayi,

'xaka shigo anjima,
'kina so na shigo ne,
'yes am missing you,
'shikenan xn shigo, yayi mata kiss ya tsinke Wayar, sai da taji wani yarrrr,

Ta kwanta a ďakin cikin farin ciki, anbawa sawwam ita, ta Kira Alawiyya tana gayamata cikin farin ciki......




    *pherty xarah

             &

      *ummi shatu*



My wattpad Phertymerh1

No comments:

Post a Comment