Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA... 10

*RAMUWAR GAYYA..*💘

   _Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

         _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*


  *_10_*

*Y*i tayi kamar bata san dashi ba awurin ta juya taci gaba da tafiyarta tana shasshekar kuka ta cikin nikab din dake daure a fuskarta, yan matan nan kuwa sai masifa suke yi suna cewa sai sun biyota sun yi mata duka alawiyya sai basu hakuri take domin ita tasan ba ummulkhair ce ta daukar musu wayaba tunda tare suke, to amma taya akayi wayar ta shiga cikin jakar ummulkhair din? Wannan itace amsar da take nema,

Cigaba da tafiya ummulkhair tayi yayinda sawwam yake biye da ita yana yi mata dariya,

"Hmmmmm, dama na fada miki yarinya wallahi duk wanda yaci tuwo dani to miya kawai yasha domin bana barin ta kwana, ke ni nan ma da kika ganni ban taba magana da wata mace acikin makarantar nan ba balle har ta nemi ta rena min hankali sai ke, ke kin isa ki mari kamata sannan kiyi tunanin zaki zauna lafiya? Wannan ma wasa ne, idan har muka ci gaba da irin wannan dake, to wallahi sai nayi miki abinda yafi wannan ciwo..."

Batayi niyyar tanka masa ba amma wannan maganar tashi ta karshe ita ta kular da ita har ta juya ta kulashi,

"Tabbas a wannan fagen kayi kokari kuma kayi nasara sakamakon daura min sharrin sata da kayi amma kasani fagen gaba bazai yi maka kyau ba domin ba zaka ji dadin shigarshi ba, kuma wallahi ba nice da jaje ba kaine da jaje, ni ban daukeka a matsayin namiji ba saboda namijin da ya amsa sunansa namiji baya sa'insa da mace..."

Wata uwar tsawa ya sakar mata wacce take taji mararta ta cika da fitsari yana shirin fara zuba,

"Control your tongue, idan ke marar kunya ce to wallahi daidai nake dake..."

Juyawa yayi ya wuce yabarta awurin, wani sabon kukan ta saka,

"Wallahi baka isa ka daura min sata kuma na rabu dakai ba, wallahi baka isaba mun rinka masifa kenan sai dai idan a koremu daga makarantar nida kai..."

Karasowar alawiyya ne ya katse mata maganar da take yi ita kadai,

"Khairi gaskiya nayi mamakin yadda akayi wannan wayar tashiga cikin jakarki.."

"Alawiyya babu abin mamaki aciki domin wannan kadan ne daga cikin sharrin sawwam,wallahi shine yayi min wannan abun"

"Oh my God, wai har yanzu baku daina wannan fadan ba? Khairi kinga ki rabu da wannan sawwam din domin na lura sharri yake nemanki dashi, ki fita a sabgarsa.."

"Ai babu wannan maganar alawiyya, ada dai nace miki bazan sake kulashi ba to amma banda yanzu, wallahi yanzu sai na mayar masa da martani, shi waye da zai hanani sakat a makarantar nan sai kace ubanshi ne ya gina..."

"Kenan kina nufin zaki cigaba da biyeshi kuna fadan?"

"Kwarai kuwa dan wallahi sai na rama.."

"Fine, tunda bazan fada miki kijiba shikenan kiyi abinda ranki keso.."

Alawiyya nagama fadin haka tayi gaba ta barta awurin, har lokacin ummulkhair kuka take saboda bata taba sha,awar daukar kayan wani ba amma gashi abanza wani ya daura mata sata.

Tunda haka ta faru ta rage fita karatu area class, tafi zama a hostel adakinta sai dai idan lecture zasuyi shine take fita wannan dalilin yasa suka kwana biyu basu hadu da sawwam ba amma ita ba hakura tayi da abinda yayi mata ba tana nan akan bakanta na sai ta rama abinda yayi mata,

Tana kwance tana karatu da tsakar rana a dakinta kamar wacce aka cewa ta tashi kawai sai ta mike ta dauki hijab dinta ta fita daga hostel, tana fita ta hango mutumin nata yana alwala zai tafi masallaci karamar wayarshi na ajiye gefe, tana kallonshi ya gama alwalar ya mike yawuce ya manta wayar awurin,tana ganinshi ya wuce yana gyara kwalar rigarshi abinku da dan gayu sai aikin karkade jikinshi yake, tana ganin ya kule tayi saurin zuwa inda wayar ke ajiye dauka tayi tana budewa taga ta bude domin babu password akai,

Sauri tayi ta shiga massage ta saka number dinta tayi sending din massage din ta ajiye wayar tana kallon hotonshi dake kan screen din wayar, yasha purple din shadda harda hula ya wani karkaceta gefe fuskarshi sanye cikin bakin glass ya saka hannuwanshi acikin aljihunan wandon yana tsaye a wani garden mai kyau,

Saurin buya tayi saboda jiyo maganganunsu shida abokanshi suna dosowa wurin,

"Na manta phone dina but inajin awurinda nayi alwala ne.."

Ta jiyo muryar sawwam yana yiwa friends dinshi magana, tana jinsu suka karaci maganganunsu ya dauki wayar suka shisshiga motarshi suka tafi,

Fitowa tayi tana dariya "sawwam kenan, kagama naka acting din nikuma gobe zan fara nawa.."

Hostel ta shige zuciyarta cikeda murna saboda gobe zata ciwa sawwam mutunci karshe kuma zata kunyata shi acikin friends dinshi da idon mutane.

Sawwam bai san abinda ke faruwa ba yana zuwa gida falon dad dinshi ya shiga ya cire rigarshi ya yar agafe ya kunna air condition ya hau doguwar kujera ya kwanta ya rufe idanuwanshi domin so yake yayi bacci kafin 3 tayi, hoton kafar ummulkhair ya fara gani acikin idonshi, juyi yayi ya koma rub da ciki yana mamakin wai meyasa ya kasa mantawa da ita? Gashi ya rasa koda me kafarta tafi ta sauran mata domin burgeshi take yi sosai kusan ma ko suna da yawa itada wasu matan idan suna tafiya to ta kafarta yake ganeta,hakama idan ta rufe fuskarta da nikab to ta kafa yake gane cewa itace,

"Wai ni wannan yarinyar zata cewa bata dauka a matsayin namiji ba, hmmm zan kuwa nuna mata ni cikakken namiji ne.."

Murmushi yayi sai kuma yaja tsaki ya sake juyawa ya rungume dan karamin pillow din kujerar, kasa baccin yayi ganin haka ya sashi tashi domin in banda tunaninta babu abinda yakeyi, rigarshi ya dauka ya fita ya nufi sashen mami,

Yana rike da rigarshi a hannu ya shiga falon Mami sai tsaki yakeyi, ganin mami da mufida zaune ya sake bata mishi rai domin yasan wurinshi mufidan tazo,

"A'a sawwam dama ka dawone?" Mami ta tambayeshi cikeda fara'a,

"Ban jima da dawowa ba.." Yabawa Mami amsa fuskarshi babu walwala,

"Ko baka da lafiya ne?" Mami ta sake tambayarshi cikeda kulawa,

"Kaina ke ciwo, bari naje na kwanta" yafadi tareda juyawa ya fice batare da yako kalli mufida ba, dakinsa yaje ya fada akan gado ya kwanta yana nan a kwance mufida ta shigo dauke da flasks din abinci akan wani farantin silver, ajiye kayan tayi ta je gefen gadon ta zauna, ko kala bai ce da itaba har tagama zamanta ta tashi ta fita, kwanciyar yaci gaba dayi har bacci yayi nasarar saceshi.

Washe gari wurin karfe 9 ummulkhair ta fito cikin shigar atamfa red colour, jan hijabi tasa ta daura nikab, awaje suka hadu da alawiyya dama basu da lecture sai 11 sannan zasu shiga, suna zaune suna hira tana kallon agogon hannunta,

Karfe tara da yan mintuna sawwam ya shiga cikin makarantar, yana shiga ya hadu da abokansa awurin da suka saba zama, saman motarshi ya dale yana sanye cikin blue din riga da bakin wando,fuskarshi tasha black face,

Sai da ta bashi minti biyar da zama sannan ta nufi wurinda suke zaune har lokacin bata bude fuskarta ba,

Sam hankalin sawwam ba agun yake ba dan haka bai ma san da zuwanta ba,

Jin wani kamshin turare nadaban da ya ziyarci hancinsa ya sanyashi jiyowa ayangance yana basarwa, kafarta ya fara kallo anan ya gane cewar ummulkhair ce,

"Assalamu alaikum, naga sakonka babu komai na hakura komai ya wuce kamar yadda ka nema.."

Kawar da kanshi yayi tamkar bai ganta ba,

"Three pointer dakai fa take.." Abdul yafada yana dariya kasa kasa,

"Ke dawa kike..?" Sawwam yace da ita bayan ya daure fuska,

"Dakai nake, ko ba kaine ka turo min da text kan cewa nayi hakuri da abinda kayi min ba.."

Tun kafin ta karasa ya diro daga kan motar afusace,nan ya doki bayan motar da karfi,

"Karya kike, ke kin isa na baki hakuri? Wallahi bakida wannan matsayin saboda duk duniya babu macen da ta isa nabata hakuri baya ga uwar data haifeni.."

Murumushi tayi ta dauko wayarta ta fara karanto sakon daga karshe ta karanto phone number dinsa,

"Ko wannan ba number dinka bane?,ya za ayi kayi min text kuma sannan kazo kana cewa wani kaza da kaza, ohh koda yake ba kason friends dinka su sani, da kasani tun farko sai kace min kar nayi maganar a gabansu...."

Tsura mata ido yayi cikin takaici, abdul ne ya karbi wayarta ya karanta sakon sannan ya mikawa sauran ma suka karanta, nan suka dau ihu,

"3 pointer kai dai kawai ka sauko tunda har ka bata hakuri" abdul yafada yana ihu wanda ya jawo hankulan mutane garesu, bakin ciki ne ya hana sawwam magana yayi shiru kawai yana kallonta amma yasan bashida hanyar karyatata tunda babu wanda zai yarda dashi kan cewar ba shine ya tura mata wannan sakon ba,

"Karka damu babu komai na hakura, sai anjima" ummulkhair tace bayan ta cire nikab din fuskarta tana yi masa mayaudarin murmushi wanda ya sake kularshi yana kallonta ta juya tabar wurin abokanshi sai dariya suke yi masa suna cewa,

"Lallai 3 pointer kaji tsoronta tunda har ka bata hakuri, babu shakka wannan tafi karfinka shiyasa ka sauko mu ai bamu zaci cewar akwai macen da zaka iya bawa hakuri ba"

Yana jinsu ya kasa furta koda kalma daya.....


Ummi Shatu
Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment