Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 14

*RAMUWAR GAYYA...*💘

  _Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

          _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*

     14


  *T*sayawa suka yi ta zuba masa ido tana kallon yanda yake rawa sai kace Michael Jackson domin rawar da yake yi yayi mutukar burge kowa dake wurin,

"Yan mata ai yau naso ace kinsha lab'b'a..." Muryar alawiyya ta dawo da ita cikin hayyacinta,

"Hmm ai wallahi kuwa da hakan ta faru to da sai yayi regrating.." Ummulkhair ta bata amsa tana tabe bakinta,

"Akan me? Saboda shine ya kawoki wurin ko yaya?"

"To dan bashi ya kawoni wurin ba meye dalilinshi na nuna ni a matsayin budurwarsa?"

Dariya alawiyya ta fashe da ita wadda har sai da ummulkhair ta kule mutuka,

"Ke yanzu in banda tsabar rainin hankali ni zaki kalla kiyiwa wannan maganar? Haba khairi ai kowa yasan wallahi soyayya kukeyi da sawwam kawai dai ban san meyasa ku taku soyayyar ta faro da haka ba"

Shiru tayi tana sauraren alawiyya har ta kammala maganarta,

"Idan kin gama sai da safe,amma kisani nikam tuni inada saurayina wanda yake sona ya damu dani yake kula da dukkan al,amurana ba wancan gajan gayen ba..."

Tana gama fadin haka ta yi gaba tabar alawiyya tana yi mata dariya,

Hostel ta wuce har lokacin a tsorace take kuma jikinta bai daina rawar da ya dauka ba lokacin da sawwam yake niyyar kissing dinta,

"Yau da na shiga uku da shikenan gayen nan yagama rainani" ta fadi hakan acikin zuciyarta,

Bude dakinta tayi ta shiga ta kwanta asaman katifarta tana jiran sakon masoyinta kamar yadda ta rada masa sunan domin yanzu tafara sonshi duk da bata taba haduwa dashi ba,

Kamar kuwa wanda yasan jiran nashi take yi sai taji karar wayarta kirrrr,

Dauka tayi ta bude sakon tafara karantawa,

  _Gareki yake wannan ma'abociyar kyawu da nutsuwa, hakika ban taba ganin macen da takaiki kyawu da kamala ba, nasan yanzu kin kwanta bacci to ina yi miki fatan wayar gari lafiya cikin aminci,masoyinki mai son farin cikinki..._

Murmushi tayi taci gaba da maimaita karanta sakon sai kace wacce aka bawa haddarshi, ji take kamar zata mayar mishi da amsa sai kuma ta fasa amma tana jin sonshi har cikin ranta gashi ko muryarshi bata taba jiba ahaka bacci ya sureta yayi gaba da ita.

  Su sawwam kuwa sai misalin karfe 11 da wani abu suka tashi daga wannan party din, abdul ne ya kamo hannunshi yana yi masa magana kasa kasa,

"Three pointer wallahi nafa kamu da son kanwar nan taka.."

Jiyowa sawwam yayi yana kallonsa "wacece kanwata kuma? Ni tunda muke daku kun taba ganin wata wai kanwata? Ni ai banida kowa banda kanwa banida yaya.."

"I know three pointer, i mean wannan yarinyar da kuke ta fada da ita.."

"Mtswwww, wai kana nufin wannan yarinyar ta dazu? Waye yace maka kanwata ce? Kaga malam wallahi baka isa ka saka yarinyar nan ta sake rainani ba dama sam na fuskanci bata ganin girmana.."

"Haba babban yaya..." Abdul yafadi cike da tsokana,

"Kaga ni kar ka bata min time idan tafiya zakayi kazo mu tafi idan kuma anan zaka kwana sai kayita zama.."

"Allah ya baka hakuri three pointer wai me yayi zafi? Daga maganar arziki?"

"Yes, me zakayi da wannan yarinyar yar kauye ko wayewa ma batayi ba kullum tana lullube cikin hijab, yanzu ka auri wannan kace ka auri wa?"

Murmushi abdul yayi daidai lokacin da suka karasa inda sawwam yayi packing din motarshi,

"You are right but nidai tayi min ahakan...."

"Wannan kuma ya rage gareka.." Sawwam ya fadi yana yatsina fuskarshi bayan ya ciro cingum daga cikin aljihun wandonshi,

Daga shi har abdul din babu wanda ya sake magana har ya kaishi gida yayi dropping dinshi shima ya wuce zuwa gidansu,

Driving yake yi yana sauraren wakar falguni wanda ya karade cikin motar, shi kadai ba tare da ya shirya ba kawai sai yaji ya fashe da dariya sakamakon tuno ummulkhair da yayi da yanayin da yaga ta shiga na tashin hankali lokacin da taji cewar zai yi kissing dinta,

"Yanmata ashe kina tsoro..." Yafada yana murmushi, jin yanayin garin ya sauya daga zafi zuwa kadawar iska ya sashi jin wani farin ciki yana ratsashi,

  A inda aka tanada domin ajiye motoci yaje yayi packing din motarshi bayan baba dan tsoho ya bude masa gate, fitowa yayi yana rike da rigarshi a hannu domin tun daga cikin motar ya cireta, sunkuyawa yayi yana duba tayar motarshi har baba dan tsoho yazo ya iskeshi awurin,

"Barka da dawowa uban gidana" baba dan tsoho yace dashi yana fara,a,

"Yawwa baba ya gida?" Sawwam ya bashi amsa bayan ya mike ya nufi cikin gida, yana kokarin shiga dakinshi suka yi kicibus da dad ya fito daga part din mami,

"Dan gidan daddy sai yanzu aka dawo? Dama kuwa ina nemanka domin nazo maka da albishir, insha Allahu acikin wannan satin zamu tafi umara domin visa dinmu ta samu.."

"Wow, am very happy dad"

"Anything for you my son, kai kadai na mallaka saboda haka you deserve more than this..."

"Thank you dad.."

Sawwam ya fadi yana murmushi daidai lokacin mami tazo ta iskesu,

"Ai Alhaji ba wannan kadai zaka sanar dashi ba sai ka fada masa cewar bayan kun dawo kuma zai fitar da matar aure idan kuma ya kasa to ni zan fitar masa..."

Zunbura baki sawwam yayi kamar wani karamin yaro, "haba mami sai kace wani..."

"Yiwa mutane shiru sai anyi magana kafara cewa kai kaza da kaza this and that.." Mami ta katseshi,

"Hajiya adai sake bashi dama mugani.." Inji dad,

"Wacce dama kuma zan bashi wacce da ban bashi ba.." Mami ta furta tare da wucewa ta barsu awurin, murmushi dad yayi ya wuce yabi bayanta, kada kai shima sawwam yayi ya fada cikin dakinshi yana korafin maganar da Mami ta fada domin shi har yanzu baiga matar da tayi masa ba a matsayin matar aure.

   Washe gari da misalin karfe 9 ya shiga makaranta yasha jar riga da bakin wando, yana tsaye ajikin motarshi da bakin glass a fuskarshi ummulkhair suka fito itada alawiyya tasha jan hijabi da bakin material,

"Kunyi anko keda sahibinki.." Alawiyya ta fadi cikeda tsokana,

"Wanne sahibi kuma..?" Ta fada tana kallon wurinda sawwam yake ai tana ganinshi da jar riga ta juya,

"Wallahi babu wani anko da zanyi dashi dan haka hostel ma zan koma na sake wasu kayan"

  Bata saurari kiran da alawiyya ke yimata ba ta nufi hostel da sauri taje ta cire kayan ta sako wata pink din shadda da farin hijabi ta fito,

Tun daga bakin gate din hostel dinsu sakon masoyinta ya shigo dan haka da murmushinta ta bude sakon,

  _Barka da fitowa, kuma yau Kinyi kyau my love.._

Murmushi tayi tana dan waige waige wai ko zata ganshi amma hakan bata faruba, wata harara ta aikawa da sawwam daidai lokacin da tazo wucewa ta gabansu, glass din fuskarshi ya cire shima ya harareta yaja dan karamin tsaki tareda dauke kanshi,

Ganin zata wuce yasa abdul yin tsalle ya diro daga saman mota ya nufeta yana kokarin tsayar da ita, jiyowa tayi tana kallonsa to ko dama wannan shine mutumin da yake yi mata wannan sakon? Wannan tambayar itace ta ziyarci kwakwalwarta damu masu rubutun.



Ummi Shatu

      &

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment