Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 20

*RAMUWAR GAYYA...*💘


_Love story 50,50_


*_UMMI A'ISHA_*

          _with_

*_PHERTYMERH XARAH_*


   20


*D*akatar da ita sawwam yayi ta hanyar cewa,

"Wait yanmata..."

Tsayawa tayi cak batare da ta jiyo ba, ahankali ya taka zuwa inda take tsaye ta bashi baya,

"Basai kin biyo tanan zan san cewar kina sona ba, ni nasan babu wani abdul da kike nema ni kike nema kawai dai kin fake da neman abdul ne gudun kada ki ji kunya, sai dai kuma kin makaro domin ni bakya daga irin matan da nake son aura, amma may be zan iya karawa dake a matsayin ta biyu bayan na auri sarauniyar mata wacce kika gani jiya....."

Murmushi ta saki har lokacin bata jiyo ta kalleshi ba,

"Sawwam kenan, gaskiya zuciyarka ta zalunceka da har wai ta yaudareka da cewar ni ummulkhair ina sonka, hmmmm ikon Allah, wallahi kayi kuskure da kake zaton ina sonka, ni baka yimin ba abdul abokinka shine yayi min shi nake so...."

Dariya maganarta ta saka sawwam,

"Amma ke yarinya ce ke kina tsammanin abdul sonki yake?? Gaskiya kin yaudari kanki.."

Sai alokacin ta juyo ta kalleshi,

"Ko kuma kai ka yaudari kanka ba"

"To ya isa wuce kibar nan...." Yafadi bayan ya gintse fuskarsa,

"Kai har ka isa ka koreni daga nan? Ko ka dauka har yanzu tsoronka nake, to banyi niyyar tafiya ba har sai lokacin da nayi niyya.."

Matsawa yayi kusa da ita,

"Fine, ai kinga abinda nayi miki rannan da daddare ko? To wallahi yanzu ma indai baki bar wurin nan ba haka zanyi miki a idon jama,a and kinga kece zakiji kunya baniba ni hakanma wani suna zai sake saya min...."

Kamar ba zata tafiba sai kawai tayi gaba ba tare da tace dashi komai ba, hannuwanshi duka ya saka cikin aljihunshi yana murmushi,

"Ashe dai har yanzu din kina tsorona" ya daga murya yadda zata iya jiyoshi,

Ko saurarenshi batayi ba taci gaba da tafiyarta, ahanya suka haduda alawiyya wacce tun daga nesa take mata murmushi,

"Sai yanzu kuka gama soyewar?" Alawiyya tace da ita cikin tsokana,

"Hmm muje hostel kedai kiga kayan da ya kawo min, kullum kina cewa soyayya muke idan nace miki ba haka bane sai ki k'i yarda muyita musu dake to albishirinki?"

"Goro.." Alawiyya ta amsa mata,

"To wallahi jiya naga budurwarsa wacce zai aura kyakkyawa da ita yar gayu..."

"Shine yace miki budurwarshi ce...?" Alawiyya ta tambayeta,

"Ehhhh shine ya fada min mana wai harda wani cewa naci albarkacinta ya biya kudin kayan da na siya.."

Dariya alawiyya ta fara wadda har saida ummulkhair taji haushi,nan ta zallake gaba ta barta abaya tana cewa,

"Idan kin gama dariyar sai ki taho nidai nayi gaba..."

Har sukaje hostel suka shiga daki alawiyya bata daina dariya ba, dakyar ta dakatar da dariyar ta kalli kairi,

"Kairi kin san me nake yiwa dariya? Wallahi sawwam dinnan A ne, ayanda na fuskanta kece budurwar tasa ita kuma waccan nufinshi taci albarkacinki zai siya mata kaya, watakila ma awurin ya ganta ba tare suka zoba...."

"Hmmm sai kiyi kuma, ke dama bakya yarda da Abu acikin sauki sai anyita musu dake, keni ko tare suka zo koma awurin suka hadu duk su ta shafa ba kairi ba, fito da kayan kiga..."

Ummulkair ta fada tana cire hijab din jikinta,

Zama alawiyya tayi ta fara firfito da kayan, provision ne sosai su indomie,kifin gwangwani, kayan tea, cabin, cornflakes, dasu taliya zuwa macaroni, sannan ga wata leda daban mai kyalkyali da kayan kwalliya aciki irinsu powder, jan baki, jagira da turare,

"Ummmmm lallai sawwam ya iya siyayya, to yanzu in tambayeki pls, shi wadannan kayan da ya kawo miki su kuma a matsayin me suke? Ko suma duk acikin fadan ne?" Alawiyya ta tambayeta tana murmushi,

"Oho....." Ummulkhair ta bata amsa bayan ta dauki wayarta domin yau kwata kwata bata ji mutuminta ba shiyasa zataji ko lafiya,

Text ta tura mishi domin tana son shima yasan ta damu dashi kamar yanda ya damu da ita,

_Farin cikina yau banjika ba ina fata kana lafiya aduk inda kake..._

Saida tayi sending din text massage din sannan ta mayar da hankalinta kan maganar da alawiyya keyi mata,

"Nidai kairi da ku yarda keda sawwam da karku yarda wallahi soyayya kuke yi, son junanku kuke yi, kina sonshi yana sonki kuma insha Allah sai kunyi aure kun haifi yara..."

Saurin toshe kunnuwanta ummulkhair tayi, "malama kar kiyi sabo domin ni inada abin kaunata wanda nake so.."

"Koma dai menene.."  Alawiyya tace da ita tana murmushi,

Tashi tayi taje ta fara kokarin dora girki tanayi tana jiran reply din sahibinta, kirrr taji ya turo, cikin azama ta ajiye tukunyar dake hannunta ta yi saurin daukar wayar tana duba sakon,

_Lafiya lau nake abar sona, ashe dama kin damu dani? Gaskiya nayi farin ciki sosai, i luv you..._

Ita kadai tafara dariya tana rubuta masa reply _I love you too_,

"Allah ya baki lafiya kairi" alawiyya dake kwance akan katifarta tace da ita,

"Amin amin, sahibina ne yace min i love you shine farin ciki ya kamani na mayar masa da reply..."

"Allah yasa sawwam ne..." Alawiyya tace,

"Ba amin ba.."

Kairi tace tareda ajiye wayar ta koma kan girkin da zata Dora.

  Sawwam yana tsaye har ummulkhair ta bace,

"Three pointer.." Ya jiyo muryar su abdul na kiranshi, juyawa yayi ya nufi kasan bishiyar da suka saba zama domin asalima nanne majalirsassu,

"Kaida wacce yarinya naganka atsaye ne three pointer?" Hafiz ya tambayeshi yana kiftawa su abdul ido,

"Wannan yarinyar ce wacce abdul yake so.." Yafada bayan yasha mur,

Dariya suka fashe da ita dukkaninsu,

"To kuma meye na bata ran daga tambaya?" Abdul ya fada yana kyakyata dariya,

"Kunga malamai sai anjimanku dama ni abinda nazo yi makarantar nan yau daban kuma nariga da na gama so sai kun fito kawai.."

Dira yayi daga kan motar da yake zaune ya wuce ya shiga motarsa yayi gaba yana jiyo su abdul suna yi masa dariya yana tafiya suka kafa zancensa shida kairi kan cewar son juna suke.

Lokacin da yaje gida ko sashen mami baije ba ya nufi dakinshi, kwanciya yayi yana tunanin dariyar da su abdul keyi masa, Kodai suna zaton son ummulkhair yake?

Girgiza kanshi yayi "wannan bazai taba faruwa ba..." Yafada yana mai cigaba da girgiza kansa,

Yana nan akwance yana kallon  wani American film a laptop dinshi mai suna bad boys, Mami ce ta shigo tana dauke da tiren abinci, daga shi sai gajeren wando da yar singileti ta maza,

"Sawwam yanzu dama ashe ka dawo shine baka shigo ka dauki abinci ba..?" Mami tace dashi bayan ta ajiye masa tiren abincin akan wani karamin stool,

"Mamina wallahi nagaji ne shiyasa.."

"To ai shikenan" Mami tace bayan ta juya zata fita, har takusa kaiwa kofa idonta ya sauka akan pad din da ya wurgar jiya, dawowa tayi da baya cikeda mamaki,

"Sawwam wannan fa...?" Mami ta tambayeshi cikeda mamaki,

Dagowa yayi ya kalleta sai kuma ya dauke idonshi domin yama rasa amsar da zai bata,

"Mami.... Mami na budurwata ne"

"To kuma sawwam in banda abinka ai sai kasata taji kunya idan kabata wannan abun, idan so kake ka yi mata kyauta ai kayan kwalliya zaka hada mata inyaso sai ka kara da wannan din aciki..."

"To Mami" ya amsa yana shafa kansa,

"A ina take?" Mami ta sake tambayarsa domin duk dadi ya isheta jin yanada budurwa,

"Mami a makarantarmu take amma yarinya ce dan yar level one cema"

Murmushi mami tayi "to ai hakanma babu laifi sawwam ni duk kasa ma nafara sonta tun kafin naganta, ya sunanta?"

"Mami sunanta Ummi, kinga hotonta" yace da mami bayan ya juyo mata da screen din laptop dinshi,

Gaban laptop din mami taje tana kallon hoton, wata kyakkyawar yarinya ta gani tana sanye da blue din material tayafa mayafi blue, gashinta ya zubo tagaba, fuskarta dauke da murmushi,

"Wai, wai, wai,zankadi amma sawwam ka iya zabe, wannan blarabiyar yarinyar fa? Tubarkalla wallahi kyakkyawa da ita, yaushe zaka kawo min ita?"

Murmushi yayi ya dauke kanshi cikeda kunya, "mami wannan din ba na fita kyau ba"

Dariya mami tayi "wallahi tafika kyau sawwam, ai ka zabo kyakkyawa.."

"To mami zata zo ta gaisheki amma ba yanzu ba"

"To ina jiranta sai tazo"

Juyawa mami tayi tafita cikeda farin ciki domin dama babban burinta taga sawwam yafara zancen aure.

    Washe gari da safe ummulkhair ta shirya kayanta ta tafi tasha domin tafiya bauchi kasancewar tun zuwanta bata taba zuwa gidaba gashi har semester ta dauko karewa,

Tun a mota tayiwa alawiyya text cewar tatafi gida sannan ta turawa sahibinta ma cewar yau tatafi bauchi, shiru taji bai dawo da reply ba da alama baya kusa da wayar.

Karfe 2:30 na rana suka sauka agarin bauchi, cikeda farin ciki tahau napep zuwa gidansu, tun da tashiga gida ta ruga da gudu tana murna,

Dukka yayunta na falo suna kallon ball mamansu kuma na daki tana wanka shikuma abbansu yana sashensa,

Dagudu taje ta fada kan yayyenta tana dariya, "ko nemana bakwa yi?" Tafada idonta ya ciko da kwalla,

"Haba autar mama taya zamu ki nemanki" babban yayansu yace da ita yana bata hannu domin su tafa, alla alla take tayi tozali da mahaifinsu domin ta sanar dashi daddadan labari.


aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment