Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 19

*RAMUWAR GAYYA....... 💘*



_Love story 50,50_


*Fertymerh Xarah*

                &

*Ummy Aysher*


     19


   Ta tsaida idanuwanta sosai tana kallonta kafin ta juyo tana kallon sawwam suna haďa ido ya kanne mata ido ďaya cikin murmushi,

Ta ďauke fuskarta haďe da gyara tsayuwarta dai dai lokacin aka gama sanya kayan acikin Leda,

Ta karba batare da ta Kalle sa ba ta nufi inda Rukayya ke tsaye da turare a hannunta ta miqa mata ledar,

Kallon mamaki Rukayya ke mata alamar kayan menene, ke Wacece? Khairi ta tabe bakinta haďe da nuna sawwam dake kallonta da tsananin mamaki a fuskarsa,

'haka yace inkawo maki, wai yana kunyar baki da hannunsa saboda pad ďin dake ciki,

Rukayya najin haka ta saki murmushi cikin jin daďi ta Karbi kayan a kunyace ta kasa haďa ido da sawwam ynxu kenan ya fara sonta,

Khairi ta juya ta fice sai da taxo dab dashi tayi masa wani kallon Baka isa ba kana tace,

'Nafi qarfin naci albarkacin budurwarka, so budurwarka ka biyawa kuďi ba ni ba, Mtseww tasa kai ta fice,

Ya tabe bakinsa haďe da ďaga kafadunsa alamar ko ajikinsa ya dubi Rukayya dai dai lokacin da take duba kayan dake cikin ledar,

She don't need them..... ta bata fuska, ai wannan provision ne, is not a gift da xai ce xai bata, did he mean gidansu ya ďauka basa shan tea da indomie ne or what bayan yasan ita ba xaman hostel takeyi ba, but ga pad, ta soma juya ledar a hannunta,

Sawwam ya miqa hannu ya karbi ledar ya juya batare da ya sake kallonta ba
ganin haka tabi bayansa tana faďin,

'Baka biya Kuďin kayan dana ďauka ba....

Batare da ya Kalle taba yaje ya biya kudin suka nufi Mota, ta kasa haquri bayan ya tayar da motar sun nufi hanyar gida ta dubesa,

'amma wannan kayan na waye?

'wadda kika karba a hannunta meyasa baki tambayeta ba?

'tace nawa ne daga gareka, but kayan dake ciki seems like not to be mine...

'yeah kayan ta ne ta miki qarya and what else? Nan da nan ta bata fuskarta taji wani kishi ya taso mata har batasan sanda tayi subutal baki ba,

'Ita kuma Wacece? ya ďan dubeta kafin ya maida hankalinsa ga tuqin da yake,

'itace ummulkhairi, wadda nakeso xn aura...

'Hmmm ta sauke naunanniyar ajiyar xuciya gabanta na faďuwa tsananin sonsa da kishinsa sun mamaye xuciyarta,

'Ni kuma me kake nufi dani? Yayi mata wani irin kallo,

*'Ni da ke* mun taba mgnr so ne, inba yau da Mami ta tirsasani ba na taba tsayuwa dake ko mgn dake? ke a tunaninki kamata xa'a xabawa mace Kuma na amince, kibar umma ta gama neme nementa ta barni ba wacce nakeso daga cikin xabinta...... kamar xatayi kuka saboda takaici,

'Amma Mami tana son muyi aure saboda tana tsinkayo *wani haske* a tattare da rayuwar auren mu,

'A gareni babu shi, ki gayamata bn amince ba, yayi parking motar ya fito ya barta ciki ya nufi part ďinsa da kayan khairi a hannunsa, da kyar ta fito daga motar da kayanta a hannu ta nufi cikin gidan yanayinta ya Sanya Mami xargin wani abu,

'me ya faru naganki wata sukuku haka ko sawwam ne,

'A'a Mami.... ta nuna mata kayan Mami taji daďi sosai ganin Kuďin daya kashe mata,

'Rukayya ta tashi tana fadin Bari naje gida kada hajiya taji shiru,

'Ina sawwam yaxo ya kaiki gida,

'A'a Mami kibarshi xn shiga napep,

'baxaa yi haka ba kijirani, ta nufi sashensa,

'yana ďaure da towel a qugunsa ta shigo,

'wanka xakayi kenan to bari nace ta jiraka idan ka gama ka sauketa gida,

'Wacece Kuma? ya tambayeta Idanunsa qasa qasa,

'Rukayya mana, yaja guntun tsaki ya nufi hanyar toilet,

'tayi tafiyarta Mami, ni ba inda xnje idan nayi wanka karatu xnyi, bai saurari amsarta ba yayi shigewarsa,

'haka taje ta lalaba Rukayya ta tafi tana mamakin sawwam shi wannan da bayason son mace kodai aljana ke auren sane?

Koda ya fito wanka bayan ya shirya ya ciro kayan yana dubawa,

Duk kayan tea ne, sai macaroni da spaghetti, ya ciro pad ďin yana kallo yana juyata a hannunsa bakinsa a tabe,

'lallai ma yarinyar nan, ganin tayi ta girma shiyasa take min rainin wayo, ya cillar da duka pad ďin gefe ya haďa mata sauran kayan a Leda da niyar gobe xai qara mata wasu akai ya kaimata....

Khairi Kuwa ko kaďan batayi Dana sanin bar masa kayan ba tunda da kudinsa ya biya sai dai gobe ta qudira akan xataje ta qara siyayyar,

Duk wani motsi da xatayi Rukayya take gani a idanuwanta batasan meyasa ta damu da yarinyar ba, Mtseww taja tsaki kafin ta kwanta,

Washe gari sun fito library da Alawiyya suna tsaye suna Mgnr exam ďinsu saurayin Alawiyya naxo, suka gaisa kana suka Tafi suka barta,

Duk yau bataji message ďin sahibin ta ba daga inda take tsaye ta tsinkayo sawwam shi kaďai tsaye a gurin motar sa batare da tunanin komai ba ta nufesa, suna haďa ido tayi far da idanunta

'Abdul nake nema.... ya ďan dubeta cikin basarwa,

'kodai ni abokin Abdul kike nema Kuma kinganni sai anjima, taja ta tsaya a kusa dashi haďe da sarqe hannuwanta a qirjinta,

'daďina dakai kana so kana basarwa just send your request meyiwuwa  it will be accepted..... yayi mata wani kallo bayan shima ya jingina a motar kamar yanda tayi idan ka kallesu xakayi xaton wasu masoyane sabanin tunanin mutum,

'sai ynxu nagane nufinki akaina, gwanda da kika fitomin da maitarki wato na turo request kiyi accepting and I will not request, bansan me xanso anan ba Abdul dayace yana so kijirasa ni ai kinga budurwata a jiya......

'yes na ganta, ta juyo tana kallonsa shima ita yake kallo,

Xatayi mgn ya tsaidata ta hanyar bude motarsa ya ďauko mata kayanta ya miqa mata,

'saqo ne daga matata Wai a maida maki ta gode mijinta xai iya siyamata fiye da Wannan, kamar baxata Karbi kayan ba ta karba tana dubawa ya qara kaya sosai a ciki sai dai ba pad ďinta Kuma baxata iya tambayarsa ba, ta tabe bakinta,

'ka gayamata Nagode nima ta Jira nawa saqon ta juya ta fice.....




Pherty

   &

Ummy shatu

R. I. P our director

My wattpad Phertymerh1

No comments:

Post a Comment