Tuesday 21 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 33

*RAMUWAR GAYYA...*💘

  _Love story 50,50_

  *_UMMI A'ISHA_*

         _With_

*_PHERTYMAH XARAH_*

33

GWS my besty phertyma Xarah!

*J*ijjiga kai hajiya raliya tayi zuciyarta cunkushe da bacin rai gamida kunar zuciya, ido ta zubawa ummulkhairi wacce ke durkushe agaban mami mahaifiyar sawwam tana gaida ita,

Cikin sauri mami ta dago ummulkhairin ta rungumeta tana murmushi,

"Haba ummulkhairi wannan irin gaisuwa haka, gaisuwar ta isa haka maza zauna asaman kujera..."

"Mami kibarta tayita durkuson mana har kafarta sai ta tari jini" sawwam yafada cikin tsokana yana kallon khairi,

"Naki nabarta din, ni matsa kabani wuri ja'iri kawai" Mami tace dashi tana kokarin zaunar da ummulkhairi akan kujera,

"Ina yini?" Ummulkhairi ta katsewa hajiya raliya tunaninta ta hanyar gaisar da ita, sai da ta danyi firgigit kafin ta amsa da

"Lafiya lau yanmata" fuskarta adan sake amma kuma can kasan zuciyarta damuwace fal alla alla take su kebe da aminiyar tata tabaje mata abubuwan dake cikin ranta,

In banda kallon umkulkhair babu abinda take yi gashi babu laifi taganta kyakkyawa ce wacce bata da makusa,

Itama rukayyan duk hankalinta yana kansu sawwam da ummulkhair wanda suke zaune akujera daya, tayi tayi dashi ya tashi saboda su mami amma sam yaki yana zaune kusa da ita hannunshi rikeda remote yana canja channel,

"Um hajiya Raliya yi hakuri wallahi bakuwa nayi ne, sannu da zuwa, mukarasa ciki" mami tace da aminiyar tata fuskarta kumshe da murmushi,

"To Hajjaju mukarasa" hajiya raliya tace bayan ta mike dauke da jakarta,

Ummulkhair ce ta dubi sawwam wanda ya take mata kafarta daya da tashi,

"Sawwam wai menene haka? Dan kaga nazo gidanku shine zaka rinka yimin mugunta ko? Babu komai"

Murmushi yayi ya kalleta, kafin ya juya ya kalli baba lami daya daga cikin masu aikin gidan wacce taketa faman jajjera kayan marmari da kayan jika makoshi akan center table,

Sai da yabari baba lami tafita sannan ya juya ya kalleta,

"Kizo muje part dina kiga dakina"

Harararshi tayi ta koma jikin kujerar ta kishingida,

"Nikuma menene zai kaini dakinka yanzu? Tab Allah ya sawwake.."

Gyara zamanshi yayi yana kallonta,

"To me kike nufi? Tunani kike yi ko cutar dake zanyi ko?"

Murmushi ya sake yi ya sassauta muryarshi tayadda Rukayya bazata jiyosu ba domin yaga kamar kunnenta yana wurin,

"In banda abinki ana cutar da wadda watanta ya zagayo ne?"

Juya mishi baya tayi tana kallon Rukayya wacce fuskarta take adaure tamau sakamakon ganin ummulkhair da tayi domin bata manta lokacin da suka hadu a supermarket ba lokacin da sawwam yakaita shopping ashe dama budurwarsa ce yatsaya yana raina mata hankali sai dai amma tasha alwashin daukar fansa akansu.

  Hajiya raliya suna shiga dakin mami ta zauna abakin gado ranta abace,

"Mamin sawwam wacce yarinya Nagani ne tareda sawwam afalo?"

Murmushi mami tayi itama ta zauna tana mai fuskantar hajiya raliyan,

"Wallahi wai budurwarsa ce yace ita yake so zai aura"

Bata fuska hajiya raliya tayi,

"Haba haba mamin sawwam kuma yanzu ku sai kubarshi ya aureta?"

"To ya zamuyi tunda yana sonta tana sonshi, shi kansa dad dinsa yasan da maganar yarinyar"

Tabe baki hajiya raliya tayi, "tabdijan,amma kuwa wallahi mami kin bani mamaki, yanzu yarinyar da baku san asalinta ba ita zaku bari ya aura, kai duk ma ba wannan ba shin kunsan ko suwaye iyayenta? Hmmm sannan ina maganar alkawarinmu da mukayi na hadasu aure shida Rukayya?"

"Ai yaki amincewa hajiya raliya, wallahi babu yanda banyi dashi ba akan yayarda amma sam yaki yarda, da ace ya yarda ma ai da sai dai kiji labarin za azo ayi maganar bikin"

Tabe baki hajiya raliya tayi ta mike hannunta rike da jakarta,

"Shikenan tunda son ran danki zakibi, ni tawa yarma da take mace na iya tilastata ta amince sai danki ne zai bijire shida yake namiji? Ai shikenan, ni zan tafi sai wani lokacin kuma"

Bin bayanta mami tayi tana babbata hakuri kan cewar ba laifinta bane sawwam dinne bai aminceba,

Su sawwam na zaune afalo shida ummulkhair da Rukayya su mami suka fito, tashi Rukayya tayi suka fita ita da mahaifiyarta mami tana bayansu domin rakiya,

"Nima tafiya zanyi yanzu tunda dare yakusa yi" ummulkhair tace dashi idanunta yana kallon kasa,

"Allah ya kiyaye hanya danni na shigo gida kenan nida sake fita sai gobe"

"Tab ai wallahi baka isaba,yanda ka kawoni haka zaka mayar dani" tace dashi bayan takai masa duka,

Shigowar mami ce tahanashi bata amsa, nemar wuri mami tayi ta zauna tana fuskantarsu,

"Mami kinji wai tafiya zatayi bazata kwana ba"

Murmushi mami tayi tana kallonsu, "ai baka saniba ko wani uzurin zatayi idan ta koma"

"Wallahi mami babu abinda zatayi so take ta tafi da wuri saboda saurayinta zaizo, kar yazo bai sameta ba"

"Mami wallahi da wasa yake yi ni banida wani saurayi"

"Toma menene idan kina dashi ummulkhair ai dama ita mace yar hakace"

"Tab to wallahi mami banda wannan saboda ita ta banbanta da sauran mata" sawwam yafada cikin kishi,

Murmushi mami tayi ta mike ta shiga dakinta domin hadowa ummulkhair kayan kwalliya,

"Kibari ayi salla sai na mayar dake to"

Girgiza masa kai tayi, "kasan fa bana yi, bana son lokacin sallah yayi mami tace nazo nayi, ban san me zan ce mata ba"

"Bari tazo ni sai infada mata cewar bakya yi"

Bakinta ta rufe da hannunta bayan ta kwalalo ido "ka rufa min asiri dan Allah karka fada mata"

"To menene idan nafada? Karya nayi,kawai kin rigada kin girma yanmata"

"Baka da kunya sawwam, yanzu dan tsabar rashin kunya sai ka iya fadawa mami wannan maganar?"

"Tsaya wasa yarinya"

"Wallahi indai kafada nida kaine..."

Dariya yasa ya mike tsaye ya fita, tana zaune a inda suka barta mami ta fito dauke da katuwar leda mai dauke da kayan kwalliya masu tsada aciki harda turmin atamfa,

Mika mata mami tayi tana murmushi, "to gashi aje ayita yiwa yarona kwalliya Allah yabada Sa,ar karatu"

Cikeda kunya ummulkhair ta girgiza kai "a,a mami kibarshi wallahi nagode"

"Bawani nan sai kin karba dama jiya kike fada min kayan kwalliyarki sun kare da mami bata bayar bama da saina siyo, yanzu kuma anbaki ki tsaya kina fulako? Mami miko na rike mata angode madalla"

Tajiyo muryar sawwam yana fada daga bakin kofa, karbar kayan yayi yawuce, itama mikewa tayi tabi bayansa bayan tayiwa mami godiya, har bakin gate mami ta rakata sannan takoma gida ita kuma tawuce motar sawwam,

Zama tayi tana harararsa, "yaushe muka yi haka dakai?"

"Jiya" yabata amsa bayan ya tada motar,

"Jiya a ina?"

"A mafarki" yafada yana dariya, duka takai masa yayi saurin rike hannunta,

"Wai waye yafada miki ana dukan miji ne? Wallahi kibari tun kafin nafara ramawa"

"To waye yasaka ka fadawa mami haka"

Sakinta yayi yafara driving yana yimata gwalo, kyaleshi tayi sai murmushi kawai da fuskarta ke fitarwa.

***

Safa da marwa kawai takeyi a tangamemen falon nata, sai kaiwa da komowa take zuciyarta a bace,

"Lallai ya zama dole nasan irin matakin da zan dauka akan wannan al'amari, kuma wallahi indai muna raye to sawwam bashida matar da tawuce Rukayya, yama za ayi haka tafaru? Sai da nagama cin alwashi nagama buri akan wannan al'amari sannan wai azo ace min abun bazai faruba ba, wallahi karyane..."

Hajiya raliya tafada da karfi wanda har saida bangon dakin ya amsa ta hanyar daukar amon muryarta.

  _Masu karatu kuyi hakuri da wannan babu yawa, muna fatan kuna biye damu._


aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu🏻

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment