*RAMUWAR GAYYA...*💘
_Love story, 50,50_
*_UMMI A'ISHA_*
_With_
*_PHERTYMAH XARAH_*
32
*T*un daga ranar suka shirya suka cigaba da gudanar da soyayyarsu cikin kaunar juna da kwanciyar hankali,
Koda wanne lokaci suna tare basa rabuwa, darene kawai ke rabasu da haka har semester tayi nisa, karatu kam suna yinsa babu kama hannun yaro musamman ma sawwam domin yanzu a final year yake kuma semester din karshe, khairi dai hankalinta yafara tashi da tunanin rabuwarsu da sawwam domin tasan idan yagama makaranta shikenan rabuwarsu tazo bazasu sake irin zaman da suka yi abaya ba, kullum cikin aikin rarrashinta yake yana nuna mata cewar koda ace yagama makaranta tofa basu rabuba, duk da hakan da yake fada mata dai hankalinta baya kwanciya yanda ya kamata,
Jin anfara kishin kishin din Cewar ankusa fitar da exam time table yasata shiga cikin wata damuwar,
Tana tsaye itada alawiyya sun fito daga lecture suna sallama domin alawiyyan gida zata tafi,
Sawwam ta hango yana zaune asaman motarsa idonshi sanye cikin bakin glass sai faman kallonta yake,
"Ohhh ni alawiyya ina ganin ikon Allah, anya kuwa ranar da aka daura muku aure da sawwam ba cinye junanku zakuyi ba..." Alawiyya tafadi tana dariya,
"Ehhh ai dayake kin san mu mayune"
"A,a karki yimin sharri malama ni bahaka nake nufi ba, gani dai nayi mutumin naki ya zauna ya kura miki ido ko kiftawa bayayi shiyasa"
Waiwayawa ummulkhairi tayi ta hangoshi zaune, murmushi tayi ta juya ga alawiyya tana cewa,
"Sannunki da sa ido in banda haka tayaya kika gane ni yake kallo bayan yasaka glass?"
"Uhm kinga tafiyata, kema ki hanzarta ki je wurin bita zaizai din naki kar yagaji da jiranki" tana kammala fadin haka tajuya tayi gaba,
Murmushi ummulkhairi tayi ta nufi wurin sawwam wanda har lokacin bai daina kallonta ba,
"Shine kaketa kallona gashi har kasa alawiyya tana tsokanata" tafadi cikin shagwaba bayan ta karasa kusa dashi tana kallonsa,
"Zo ki fada min abinda tace miki gobe idan tazo sai na rama miki"
Yace da ita yana murmushi, kafada ta makale tana kallonsa,
"Ba kaine kasa ta tsokaneni ba"
"Shine ai nace ki fada min sai na rama miki"
Zuba mishi ido tayi tana kallonsa, rigar jikinsa ja ce da fara aciki sai jan wando da jan takalmi,
"Kayi kyau" tace dashi ba tare data saniba,
"Dagaske?" Taji ya tambayeta,
Sake kallonshi tayi tana murmushi,
"Dagaske Mana, ina fata yan matan makarantar nan yau basu kalle min kaiba"
Murmushi yasaki yana sake kallonta ta cikin glass din idonshi,
"Babu wacce ta kalleni saboda duk sun san ni nakine ke daya..."
Murmushi tayi, "Allah yasa dagaske kake"
Tsalle yayi ya diro daga saman motar tashi ya bude mata gaban motar ta shiga ta zauna,
Shima budewa yayi yashiga ya zauna,
Hannunshi ya tura baya ya dauko project ya mika mata,
"Karbi kigani nagama project dina harma nayi submitting..."
Karba tayi tana gani sai dai tayi shiru kawai tana kallo, hawaye ya hango yana diga daga idanuwanta yana disa akan takardar project din,
Kanta ya dago ya juyo da fuskarta sai yaga hawaye fal,
Girgiza mata kai yashiga yi yana rikeda hannunta,
"Haba my lonely menene abin yin kuka kuma keda ya kamata kiyi murna nakusa gama karatu nafara aiki muyi aure mu zauna tare mu rayu tare har abada,
Kullum fa baccina marar dadine saboda rashinki akusa dani gashi dakin har tsoro yake bani domin yayi min girma ni daya, idan na makara babu mai tashina sai dai idan mami taga rana tafito ban fitoba ta taimaka min taje ta tadani,
Gashi kullum cikin...." Shiru yayi yana kallonta,
"In fada miki? Amma sirri nane.."
Dagowa tayi ta kalleshi bayan tadaga masa kai, "fada min.."
"To kullum cikin mafarkinki nake, gashi bana jin dadin baccin ko kadan saboda babu ke, amma kinga idan muka yi aure, tare zamu runka yin bacci dake, ajikina zan rinka kwantar dake,inyi miki pillow da kirjina, in tayi miki tausa har bacci ya daukeki kinga ai irin wannan baccin bama zamu san asuba tayiba..."
Dariya da kunyane suka ziyarceta a lokaci guda, daya hannunta tasa ta kare fuskarta tana murmushi,
"Gaskiya namiji bashida alkunya wallahi" tafada ahankali batare da tasan zaiji ba,
"Babu wani rashin kunya, abinda zai farune fa nake fada miki, ko ban fada miki yanzu ba ai idan lokacin yayi zaki ga hakan tafaru"
"To ni basai ka fada minba" tace dashi har lokacin fuskarta arufe take taki budewa,
"A'a gara dai in fada miki kiji, kar naje idan munyi auren kina rufe min kofa kina gudun daki, kin san da idan akayiwa yarinya aure guduwa take, to ban sani ba ko kema hakan zakiyi min"
Dariya tasaka tana kallonsa, "ai kuwa nima guduwar zanyi dama kakata ta bani labari"
Dariya yayi ya cire glass din fuskarshi ya ajiye tareda kwantar da kujerarsa baya kadan,
"Nima babar mami ce take bani labari wai lokacin da akayi aurenta tafi wata biyar tana wannan gudun sai daga baya sannan ta zauna tadaina guduwa, ke dai idan kika gudu wallahi binki zanyi ko inane"
Dariya ta sake yi "gidan mami ai zan gudu"
"Ta kwana gidan sauki indai gidan mamine wallahi zan iya binki, gidanku ne kawai zaki je na kyaleki ban biki ba saboda kar ace nayi rashin kunya"
Kallonsa tayi tana murmushi, "dama ai baka da ita"
Kallonta shima yayi yasaka murmushi, "sai kinji wani labari da baba dan tsoho yabani wai su a kauyensu idan an yiwa yarinya aure to sai an hadata da karamar yarinya kamar yar shekara takwas ko bakwai sun tafi gidan mijin tare, waima tare za akaisu.."
Kallonsa tayi cikeda tsokana tace, "muma haka al'adar garinmu take so be prepare dan nima da yar kanwata za akawo mu"
Dariya yayi kafin yajuya ya kalleta, "babu damuwa Ku taho tare inada extra room wanda zata rinka kwana nidai ba mai nisantani da matata dan wallahi bazan rinka kwana ni daya ba"
Dariya tasa harda kwalla dan tsabar dariya,
"Kiyi dariya da kyau, nidai ban hanaki zuwa da yar rakiya ba amma wallahi ko tazo sai dai ta rinka zama ita kadai danni wata daya zanyi agida ban leka ko inaba har sai nagama ganawa da matata"
Murmushi tayi ta ajiye masa project dinshi akujerar baya,
"Wasa nake maka ma, nasan abbanmu ma bazai bariba wallahi"
Dadi yaji ganin ya rabata da damuwar da take damunta gashi yanzu ta ware sunata hira kamar ba itace da tafara yi masa kuka ba,
"To idan ke kadaice idan aka kawoki da kwana biyu honey moon zamu tafi zamuje ki zazzaga gurare kiyi kallo"
"Hmmm sawwam kenan kaci buri akan wannan ranar, Allah dai ya nuna mana lokacin da alkairi"
"Kema nasan kina tason ranar tazo kawai kukan munafurci kike, amma aranki har addu'a kike Allah ya kawo ranar, nasanma ji kike kamar ki janyota da karfi ta dawo kusa.." Yafada cikin zolaya,
Murmushi tayi ta dan harareshi, "sai kace kai, ni barima natafi hostel yunwa nakeji"
"Muje nakaiki kici abinci a restaurant"
Kai ta girgiza masa, "wallahi indomie nake sha'awa, ita zanje na dafa yanzu"
Baki ya tabe ya girgiza mata kai, "Abin yazo kenan domin shima yana saku kwadayi"
Bude kofar motar tayi tafita batare data bashi amsaba domin sawwam sai kace maye yake duk lokacin da take cikin wannan yanayin sai ya ganeta tarasa tayaya yake fahimta,
"Ki shirya da yamma zanzo muje kigaida mami wallahi tun jiya take yimin magana akan na kaiki wai kwana biyu baku gaisa ba"
"To sai kazo" ta bashi amsa gamida juyawa ta nufi hostel, shi dinma reverse yayi ya fita daga school din ya nufi gida.
Kamar yadda yace da yamma zai dawo haka kuwa akayi sai gashi yadawo, waya yayi mata ta shirya tafita, irin dogayen rigunan da ya kawo mata tsaraba daga saudiyya aciki ta saka daya, blue din doguwar Arabian gown mai stones ajiki, tayi rolling da mayafin rigar tafita sai kamshi take zubawa,
Acikin mota ta iskeshi zaune yana jiranta amma fuskarsa ahade,
"Sahibi muje ko"
Motar kawai ya tada batare da ya kalleta ba,har saida suka fita daga makarantar sannan yayi magana,
"Kar nasake ganin kin fito haka, kinga yanda shape din jikinki ya fito acikin rigar nan? Duk yanda akayi ma wannan rigar rage mata fadi kikayi, ko kunya bakiji ba kika keto ta cikin maza kika fito ahaka ana kallonki, maimakon kisaka hijab shine kika dauko dan wannan mayafin"
Kallonshi tayi domin tagane abinda yake yiwa fushi yanzu,
"Amma naga dai ai kaine ka siyo min rigar ko? Danma dai banice na siya ba bare kaji dadin yimin fada"
Packing yayi agefen titi, to kuma danni na siyo miki sai ki rinka fitowa ahaka duk shape dunki awaje?"
"To yanzu me kakeso ayi? Kaga idan ba zaka kaini ba ka fada min na koma"
Shiru yayi mata yana kallon titi tunani yake dazu lokacin data fito wasu samari sun kai su shida azaune ganinta duk sai suka maida idonsu kanta harda waiwayenta yana kallonsu ta mirror din motarsa,
Bude kofar motar tayi zata fita, cikin zafin nama ya janyota yamaida kofar ya rufe,
"Bakida hankali? Titi zaki fita ahaka wasu su sake ganinki?"
Atsorace take kallonsa ganin yanda idanuwanshi suka sauya lokaci guda, kishine dankare aciki, ita sai taji ma tafara jin tsoransa,
"Kayi hakuri bazan sake ba"
Ajiyar zuciya yasaki ahankali ya kunna motar yana kallonta,
"Kairi saifa kinyi hakuri dani saboda wallahi bana son kowa ya kallar min yanda siffar jikinki take, nafi son ni kadai zan ga kayana a lokacin da mukayi aure"
Ajiyar zuciya itama ta ajiye tace dashi "baka son wani yaga jikina amma kasaka min kadangare ajikina har saida nacire hijabina acikin mutane?"
Murmushi yasaki babu shiri, "ai wannan duk acikin rashin sanine"
"Babu wani rashin sani kawai dai neman fada"
Dariya yayi yakama kunnensa daya "to am sorry, ai nabaki hakuri sai ki yafe min"
"Ni ban hakura ba" tace dashi,
"Sai yaushe zaki hakura?"
"Sai kace min i love you sau dari"
Dariya yayi yafara fada mata tana kirgawa da haka har sukaje gidan mami, suna shiga motar su hajiya Raliya mahaifiyar Rukayya na shigowa kamar tare suke,
Bude mata yayi ta fito yakama hannunta zuwa ciki hajiya raliya na kallonsu itada yarta Rukayya,
Afalo suka samu mami tana dudduba wasu hadaddun swiss lace wadanda aka kawo mata ta siya, ganinsu yasata ajiye kayan ta maida hankalinta garesu cikeda fara'a, daidai lokacin su Rukayya suka shigo ita da mahaifiyarta,
Wuri suka samu suka zazzauna Rukayya sai kallon sawwam take cikeda so shikuma duk hankalinsa naga abar sonshi kairi, zungurarta mahaifiyarta tayi,
"Wannan din wacece?" Ta tambayeta cikin rada,
"Momy inajin budurwarsa ce"
Zaro ido mahaifiyarta tayi, ai kuwa abinda bazai taba faruwaba kenan, lallai yazama dole su tashi atsaye tun kafin kwado yayi musu kafa,hajiya raliya mahaifiyar rukayya ta ayyana hakan acikin ranta...
aishaummi.blogspot.com
Ummi Shatu
Pherty Xarah
No comments:
Post a Comment