Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 12

*RAMUWAR GAYYA...*💘

_Love story 50,50_


  *_UMMI A'ISHA_*

         _with_

_*PHERTYMERH XARAH*_


   *_12_*

   *K*allonsa Abdul yayi yana murmushi,

"Three pointer kai da waye kuma..?"

"Waccan marar kunyar yarinyar mana..."

"Ohhh budurwarka..?" Abdul ya fada cike da zolaya, wani naushi sawwam ya kai masa yayi saurin gocewa yana dariya, kallon inda su ummulkhairi suke yayi sai dai bai gansu ba domin har sun bar wurin itada alawiyya,

Sauka yayi daga saman motarshi suka tafi fatymah hall inda za agudanar musu da lecture.

Ummulkhair na shiga class taji wayarta na tsuwwa dubawar da zatayi kawai sai taga sako daga wannan number da ta saba ganin anturo mata da text,

   _You look so fine dear, kinyi kyau yau..._

Shine kawai abinda ta ga an rubuta, shiru tayi tana nazarin sakon domin ta kasa gane ko waye ke aiko mata da massage kullum gashi idan ta kira number din sai tajita arufe,

Kallon kanta tayi ajikin mudubun wayar babu laifi kam tayi kyau kamar yadda mai sakon yace, sharewa tayi taci gaba da sabgarta har suka kammala lecture sukayi sallama da alawiyya ta tafi ita kuma ta nufi hostel,

Tana bullowa kwanar da zata sadata da hostel din ta hango su sawwam suna alwala kasamcewar lokacin sallar azahar ya kawo jiki, daure fuska tayi saboda duk atunaninta zai tanka mata, har taje daf dashi tana kallonshi yayi dan rama tabe baki tayi ta kawar da kanta,

Yana shafar kai sai kawai ya hangota, kafarta ya fara kallo yaga dagaske ita dince, bashi da bukatar ya kalli fuskarta domin yasan ita ce din ba wata ba, cigaba da alwalarshi yayi ba tare da yako kalleta ba, yana jin abokanshi sai k'us k'us din gulmarsa sukeyi shida ita, bai kulasu ba ya mike yayi gaba domin gudun kada su bata masa rai.

  Washe gari kamar kullum ummulkhair ta shirya ta fita lecture domin alawiyya tuni har ta shigo makarantar, fita tayi tana tafiya tana waya da babban yayansu yaya bello, tana gama wayar taji karar shigowar massage,

  _Yau kin makara dear, kawarki tun da jimawa take jiranki baki fitoba_

Tsaki taja "wannan mutumin kodai aljanine sai haka" ta fadi hakan acikin zuciyarta domin komai nata mutumin nan yasani,da wannan tunanin ta karasa wurin alawiyya suka rankaya zuwa hall,

Zasu shiga hall din su kuma su sawwam sun fito, hada ido sukayi dashi nan ta harareshi, shi dinma harararta yayi yawuce,

"Kuna nan dai da halinku, kuna son junanku amma kun kasa bayyanawa junanku sirrin dake cikin zuciyoyinku.." Alawiyya tace da ummulkhair tana murmushi,

"Wa nake so??  Mtswww wallahi kin cuceni amma, na rasa wanda zan so sai wannan dan rainin hankalin..."

"To ya isa haka.." Alawiyya tayi saurin katse zancen tana dariya domin ita ta dade da fahimtarsu,

Koda suka fito daga lecture ma kogin tunani ta fada to meyasa wai alawiyya take cewa itada sawwam soyayya suke? Dama ana soyayya da fad'a ne? Wadannan tambayoyin sune suketa kai kawo acikin kwakwalwarta,

K'arar shigowar wani sabon sakon ne taji ya shigo cikin wayarta akasalance ta dauko wayar ta bude sakon,

  _kyakkyawar fuskarki bata kyau da rashin dariya, idan kina murmushi kinfi kyau, pls ki daina daure fuska domin baya yi miki kyau.._

Murmushi ta saki ita kadai tana kallon sakon, "koma wanene wannan to hakika ya gama sanin wacece ni" tafada tana murmushi,

"Lafiya?" Taji muryar alawiyya tana tambayarta,

"Lafiya lau, wani sakone yasani murmushi"

"Kodai sawwam din nakine ya turo..."

Hannu ummulkhair ta dagawa alawiyya "dan Allah ki daina yimin zancenshi ni wallahi bana so, ki taso muje hostel muci abinci nayi girki before na fito"

Alawiyya bata kara cewa komai ba ta mike suka nufi hanyar hostel, jinsu sawwam a bayansu yasata nutsuwa tana son ganin yanda ummulkhair da sawwam zasu dubi juna, ganinsu tayi kowa yana harare harare musamman ma ummulkhair, murmushi tayi ta dafa khairi,

"Taku salon soyayyar dabance data sauran wallahi kuna burgeni.."

Shiru ummulkhair tayi mata tawuce gaba ta barta a baya,

Hostel suka shiga suka ci abinci suka yi salla alawiyya ta fara yi mata kitso,

Kitson gaba tayi mata domin rabonta dashi tun tana karama, sake shiryawa tayi suka fita tare domin tana son yin karatu, sallama suka yi da alawiyya ta tafi gida ita kuma ta wuce inda ta saba zama domin gudanar da karatunta.

  Sanye take cikin jar atamfa da digon baki ajiki, jan mayafi ta yafa akaro nafarko domin tunda tazo makarantar bata taba saka mayafi ba sai dai hijab,

Sauri kawai take yi bata son ashiga lecture batare da ta karasa ba, tana zuwa ta iske yan ajinsu awaje kowa yana harkar gabansa ba ashiga ba,

"Washh alawiyya kinga saurin da nayi, duk tunanina anshiga..."

"Ba ashiga ba tukunna, kinyi kyau" alawiyya ta bata amsa, tun kafin ta sake yunkurin yin wata maganar taji karar shigowar sako, da hanzarinta ta duba,

  _Gaskiya kinyi kyau yanmata na amma kuma kin bar min gashin kanki awaje wasu mazan suna kalle min, kiyi hakuri ki koma ki saka hijab dan Allah, i love you..._

Murmushi tayi taja dan kwalinta ta gyara domin kitson da akayi mata jiya yaki rufuwa duk kokarinta na ganin ta rufe gashin dole sai da ya fito musamman ma taa gaba,suna nan atsaye itada alawiyya ta hango mutumin nata shida abokanshi yasha bakin glass duk inda suka wuce sai kiransa dalibai suke yi,

Ta cikin glass din ya kura mata ido yana kallonta taci kwalliya sosai cikin jar atamfa da mayafi gashi kitsonta siri siri tagaban goshinta ya rufe barin fuskarta daya, tabe baki yayi yaci gaba da kallonta dama amfanin bakin glass din da yake sawa kenan yayita kallonta bata san ita yake kalloba tunda bata ganin kwayar idonshi......


Ummi Shatu
Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment