Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA...23

*RAMUWAR GAYYA.......*💘

_love story 50,50_



*Fertymerh Xarah*

            &

*Ummy Aysher*

      23

          'Murmushin me kika haka,

'yaushe nayi murmushi, Mtseww saboda me xanyi ma tor?

'ai naji sound ďin shine,

Ta tsinke Wayar da sauri tana dariya, can kuma sai taji alamar shigowar test bata duba ba cos tasan waye, ynxu she don't have crush on him, idan ya matsu da Ita ya bayyana kansa gareta ta ganshi.

Washe gari bayan sun gama lectures koda suka fito da Alawiyya yana tsaye shida Suhaib suna jiranta,

Tun daga nesa suka sakarwa junansu murmushi, Alawiyya ta tabe bakinta tana fadin wonder shall never end, wai khairi da sawwam,

Sarai khairi taji ta sai dai bata kulata ba har suka qaraso gurinsu, handout ďinta gabaďaya ta ďora akansa tana tsaye a gabansa tana kallonsa shima kallonta yake,

'ka ganni da tulin handout shine ko kaxo ka karbamin kayi tsaye kawai kana kallona,

Ya karbi handout din haďe da janye hannunta akansa,

'Afuwan yayata,

Suka ďauki dariya,

Alawiyya ta soma tafiya tana faďin,

'tafiya xanyi khairi nagaji Inaso nayi barci kafin nayi karatu,

Khairi ta jingina jikin motar kusa da sawwam tana faďin,

'to qawata yau baxan rakaki ba,

'ke kika sani ta fice, sawwam ya dubeta,

'kije kici abinci kixo muje ko kin fasa ne,

'oh yes harna manta but.... sai Kuma tayi shiru ta juya da sauri kawai xuwa hostel, sawwam yabita da kallo kafin ya maida kallonsa Ga Suhaib,

'Su Abdul ina suka tsaya wai,
'nima Yanxu can xnje Inaso na buga snooker, kai kuma nasan baxakaje yau ba saboda khairi,

'kaje in nadawo xn sameku acan,

Suhaib ya fice yayinda sawwam ya shiga motar yana xaman jiranta,

Bata jima sosai ba ta fito daga hostel, tana qarasowa inda yake xaune ta yatsina fuskarta,

'Ni nafasa xuwa saloon ďin ka tafiyarka,

Ya dubeta da kallon mamaki,

'kin fasa baki gayamin ba tun ďaxu sai kika barni ina xaman jiranki,

Tayi masa shiru, Ransa a bace ya riqa murfin motarsa ya dubeta,

Matsa xn rufe motar, taqi ta matsa,

'ki matsa mana,

Tayi masa banxa haďe da ďauke kanta gefe Kuma bata matsa ba,

Yayi shiru yana kallonta, sai Kuma ya tabe bakinsa haďe da maida qafafuwansa cikin motar ya Kunna music,

Murmushi tayi ta rufa masa motar kana ta xagaya ta shiga tana faďin muje ba dan halin ka ba,

'yace a'a ni ba inda xanje ynxu kifita kawai daga nan sai gida,

'nidai muje bana son qorafi nace ma baxan jeba sai ka tambayeni dalili amma kawani bata ranka,

Ganin ta bata rai ya sanyashi tada motar yana faďin ynxu na tambayeki gayamin dalili,

Ta fakaici idonsa tayi masa gwalo juyowar da xaiyi suka haďa ido, ta saki dariya sosai bada kai nakeyi ba,

baice komai ba har suka iso saloon ďin,

A tare suka shiga, bata sani mutane sosai aciki ba sai aka fara mata yana xaune a gefenta yana chatting binni binni yake kallonta yana mamakin kanta, baida tsawo sosai amma sai cika,

'Ni kadaina kallo na haka,

Yaja tsaki haďe da juya mata,
'kome xn kalla akanki ko gashin kirki bakida,

'Naji dai amma a hakan kake kallo,

Mai saloon ďin murmushi kawai takeyi,

Bayan angama ya biya kuďi suka fito sai da ya biya da Ita tayi mata siyayya kana ya maidata hostel, kallonsa tayi,

'ban gode ba,

Ya tabe bakinsa haďe da ďaga kafadunsa ko ajikinsa ya shiga motar sa yaja,

Haka suke kamar Farah da Assad

After a week aka sanya masu exam,

Ba Wasa kowa qoqarinsa to make it, sai suka daina haďuwa karatu makes them busy sai dai suyi waya,

Yau suka kammala exam ďin su, da yawa mutane yau xasu tafi gida wasu Kuma a gobe , khairi na cikin mutanen da xasu je gobe cos batason tafiyar marece,

Tunda ta fito exam take neman sawwam bata ganshi ba kuma bataga motarsa ba, tayi trying numbers baya shiga duk inda takesa ran ganin sa ta duba bayanan, so take ta sanardashi xuwan gidanta a gobe, da haka ta isa hostel ta soma parking na kayanta,

Alawiyya taxo tayi mata Sallama a ranar xata tafi, saduwar alheri Allah yasa munada rabon cin exam mudawo khairi,

Amin, Insha Allah ma xamu dawo,

Sukayi Sallama cike da kewar juna ta tafi,

Da dare bayan tagama haďa kayanta tana kwance da wayarta a hannu tana kiran number sawwam still bata shiga ko ina yaje, test ya shigo wayarta

    _'Gashi xaki tafi gida batare da kin gayamin matsayina a xuciyarki ba,_

Ta tura masa

   _idan baxaka damu ba Inaso na ganka._

Cikin qanqanin lokaci ya turo mata,

   _'kifito ina wajen hostel ďin ku ina jiranki._

Da sauri ta tashi ta sunkuci qaton hijab ďinta ta sanya yau xataga aljaninta Allah sa baxai mata Wulaqanci irin na ranar ba, tana tafe tana gwada number sawwam cikin Sa'a Kuwa ta shiga, harta gama ringing baa ďauka ba, taja tsaki dai dai lokacin da ta tsinkayota akan motarsa Idanunsa akan wayarsa, da sauri ta qarasa gurinsa tana faďin,

'Ashe kana ganin kirana shine kaqi ďagawa ko, ya ďago yana kallonta,

'saboda nasan xaki fito shiyasa bn ďaga ba, taja tsaki tana dube duben inda xata hango mutuminta,

'me kike nema, kai tsaye ta bashi amsa da

'wani nake nema Wlhy, ya dade yana min test a waya bansanshi ba bamu taba haduwa ba sai yau yace nafito yana wajen hostel ďin mu Kuma ni bn ganshiba,

'ki kirasa mana,

'nasha gwada kiran number baya shiga ai,

'try and see....

Ba musu tayi dialing number Ga mamakinta sai taji Kukan wayar a hannun sawwam ta ďago tana kallonsa a hanxarce shima Idanunsa akanta,tsananin mamaki da kaďuwa sun hana mata magana, ya diro daga Saman motar ya tsaya gab da Ita kamar xai rungumeta har numfashinsu na bugun juna,

'Am d one, nine sahibinki sunan da kika raďa min, lol

Ta haďe fuska sosai,

'gwanda kisaki fuskarki, *Ni da ke* munjima muna son junanmu kawai girman Kai ya hana mu bayyanawa junan mu, so forget the past kada ma ki tuno komai ko qorafi duk abinda kikaga ina turo maki a test kinsan bamai iyawa sai ni cos nafi kusanci dake nasan komai akanki amma baki taba tunanin haka ba,

Ta sauke ajiyar xuciya tana tuna Alawiyya dake gayamata sawwam ne tana qaryatawa, no wonder duk sanda xai mata test ďin sai bayan sun rabu a skul ne ko kuma tana cikin Skul ďin yaga Abinda take, Ashe mutumin da tagani ranar bashi bane bayan ta qaraso daga wurin ta ganshi akan Mota har suka yi faďa amma bata taba kawo shi bane,

'kinyi shiru, bana son ki tuna duk wani Faďan mu, forget ol d inconvenience ki tuna alherin dake tsakaninmu saboda *Alheri danqo ne*,

Ta tabe bakinta haďe da sarqe hannuwanta a qirjinta tana kallonsa, shima sai ya kwaikwayeta yayi yanda tayi hakan yabata dariya sosai bayan ta ďan matsa daga kusa dashi,

'kigayamin kin yarda xakiyi soyayya dani, xaki aure ni?

Tayi far da ido tana kallonsa da murmushi, Hakan kaďai ya isa ya gane amsar tambayarsa koda bata bashi amsar ba........



*pherty xarah*

       &

*ummy shatu*






My wattpad Phertymerh1

No comments:

Post a Comment