Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA..,15

*RAMUWAR GAYYA*......💘

_love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

            &

*Ummy Aysher*

15

Kallon Ummy Aysher nayi dan son tabbatar da xargin da khairi keyi...... No answer,

'qanwar mu.....ya faďa bayan ya shiga gabanta, kallonsa take tana nanata mgnr a xuciyarta wai qanwarmu

'naga fuskarki da alamar mamaki, kinji wani iri banbarakwai wai namiji da suna hajara, ba komai ya janyo Hakan ba illah sonki nakeyi ummulkhairi....

Ta tsuke fuskarta xuciyarta na bugawa, Allah ya sa bashi bane ke tura mata wannan saqon dan baxata amince da shi baxata manta rashin mutuncin  da suka mata farkon xuwanta Skul ďin ba....

Sawwam a kishingide Kan motarsa Idanunsa cikin baqin glass sosai ya xuba mata ido yana kallonta yana son ganin re'action ďin ta akan Mgnr Abdul xata amince dashi ne ko Kuwa?

Xatayi mgn kenan saqo ya shigo a wayarta jikinta har rawa yake ta buďa ta gani,

    _'kin sani Ina matuqar kishin ki khairi......._

  Tayi ajiyar xuciya har a cikin ranta taji daďi kenan ba Abdul bane to waye wannan da bayason bayyana mata koshi Waye, she need to know him,ta juya tana waige waige bata ga kowa ba, ta dubi sawwam dake cire glass ďin sa taja tsaki shi Kuma yabita da harara atare suka ďauke kansu ga juna kowa cike da haushin ďan uwansa....

Abdul yace karki damu, shi wancan Yanxu ki kyalesa ba ruwanki dashi ko ranar da akayi party ďinnan Wanda ya fansheki hannunsa ni na turasa saboda ban yarda da abokina ba, Allah khairi I mean it sonki nakeyi, kallonsa tayi Qasa da Sama taja tsaki ta fice da sauri ganin take wani plan suke son haďa mata ta dan su cutar da Ita, ta Allah Kuwa bata su ba....

Raf.... Raf.. Raf... Sawwam ya ďauki tafi bayan ya diro daga Saman motarsa,

'wow tayi matuqar birgeni kabani haushi, ai sai dana gayama girma kawai xaka xubar a Wannan yarinya dan Allah ynxu wa gari ya waya?

'Abokina da gske nakeyi fa, ynxu birgeni takeyi xnyi qoqari mu fara soyayya da Ita,

Sawwam ya yatsina fuskarsa bayan ya tabe bakinsa,

'is left for you, Allah yasa watarana ta mare ka acikin mutane,

'And so, duk cikin so ne... Sawwam ya qara bata fuskarsa cikin son kawar da xancen baisan meyasa yakejin haushin Abdul dan yace yana son khairi ba....

'muje hall Pls is olmost tym, suka fice a tare.

Khairi Kuwa da kyar ta gano inda Alawiyya take, anan ta labarta mata ynda sukayi da Abdul,

'Hhhhhhhh to fa ke abokai biyu xaki haďa kiyi soyayya dasu kenan, gsky na xaba maki sawwam domin kunfi dacewa, tsiwarku da girman kanku yaxo ďaya....... Khairi taja tsaki

'ke wannan ya dama, Wanda ya damu dani nakeso, Allah Alawiyya am eager naga wannan mutumin dake turomin text, xuciyata ta aminta dashi inajinsa a raina....

'ke khairi Kinsan me kikeyi, bakisan mutum ba, bakisan kowa ye ba mutum ko aljan, Mai lfy ko musaki kawai kin amince kina sonsa....

'yes koma shi waye inason abuna, inbaxaki min addua ba kiyi shiru ni ynxu nagane bakya sona tunda bakyason Abinda nake so,

'nikam baxan so abinda bansan kowa ye ba, da dai sawwam ne dashi kuka fi dacewa, gashi ďan gayu ,kyakkyawa, ki dubi matan dake sonsa a skul ďinnan yana wulaqantasu kin ko San dame yake taqama? Khairi ta dubeta a fusace cikin bacin rai...

'duk abinda yake taqama Ina taqama dashi ko da Kuwa *MULKI KO SARAUTA* ne ni miye ruwana da matan dake sonsa ni bakiji nace ina sonsa ba kuma baxan so sa ba....... Alawiyya ta tabe bakinta,

'Allah ya kawo *RUWAN KASHE GOBARA* tsakanin ku......cikin tsiwa tace Amin ta fice cikin jin haushin Alawiyya a Wannan Karon ta nufi wata bishiya ta xauna kafin a shigar masu lectures,

Xaman ta keda wuya message na shigo wayarta, cikin xaquwa ta buďe,

    _'Har ynxu xuciyata tana min raďaďin ganin ki da wannan gayen, Ina kishinki sosai fiye da tunaninki, idan ya qara tunkararsa ki gayamasa *Ni da ke* mun dace, ina son Kare *Martabar ki* domin tawace....._

    Wannan Karon murmushi tayi har cikin xuciyarta taji daďin kalamansa, karo na farko data tsinci kanta dason maida masa martani tun sanda yake turo mata text,

      _kayi haquri......_

    Shine Abinda ta tura tana murmushi, cikin minti biyu taji shigowar wani text...

   _Na haqura amma ki tashi qarqashin wannan bishiyar saboda kare lfyrki daga Abinda ke cikinta_.

Xumbur ta tashi idan akwai abinda ta tsana cutar aljannu, ta soma waige waige tana ja da baya ko xataga aljaninta,

Bata ankaraba taji ta bigi mutum a baya, Kwallon dake hannunsa ta sumulyo akan qafarta,

Wash ta faďa tana kallonsa haďe da riqe qafar, sawwam ne ya bata rai...

'Ajebo ita wannan Kwallon ake wa wani wash, kai mata akwai sharri a rayuwarsu ya faďa yana kallon Wanda suke tare Hafiz,

Hafiz yace wasu matan suka ma sharri sai kaji dama baka duniya, baabaa ka kyaleta muje field ana jiran mu Pls,

Sawwam ya cigaba da tafiya yana cilla Kwallon sama yana cafewa yace

'wannan ma da gangan tayi dan ta taba jikina Kuma ta taba taji, ni daman nasan kiss ďin da ban mata ba tasha mafarki akansa, batasan wannan bakin ba gani nan bari nan......

Sukayi dariya a tare shida Hafiz suka fice yana tambayarsa

'Au daman kasan tane, oh lallai shiyasa.

Sawwam yace tana cikin masu sona ne........

Khairi na tsaye na kallonsu har suka fice ta gane yana son ta kulashi su koma yar gidan jiya, ita Kuwa baxata biye masa a ynxu musamman da take cikin farin ciki, ta tabe bakinta ta juya tana cigaba da latsar wayarta.



Pherty
     &
Ummy shatu

No comments:

Post a Comment