Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 17

*RAMUWAR GAYYA......... 💘*

_Love story 50,50_

*Fertymerh xarah*

              &

*Ummy Aysher*

      17

Abdul bai fahimci komai ba, ya ďauke kansa yana kallon su Alawiyya har suka bacewa ganinsa,

Sawwam Kuwa ya maida hankalinsa ga kallon wata takarda dake hannunsa har acikin xuciyarsa idan ya tuna jiya yakanji wani iri Kuma abin ya basa dariya....

Khairi Kuwa tana isa hostel ta soma rage kayan jikinta kafin ta xauna ta ciro wayarta, noo mahaifinta ta Kira she is in need Akan aikin daya turo ta kai dan da alama tayi kusa cika burinsa a yanda take gani,

Basu jima akan wayar na ta tsinke, cornflakes ta haďa tasha dan ragewa kanta yunwar dake damunta kafin ta kwanta a mattress cikin tunanin aljaninta yau tajisa shiru, Allah yasa dai lfy,

Can wani bangare na xuciyarta ya halbo mata sawwam da yanda suka kasance jiya, nan da nan Kuwa ta bata ranta haďe da Jan tsaki,

Amma fa duk da haka ya cuceni Wlhy, sai Allah ya sakamin dama abinda yake nema bai samu ba ko yana xaton cewa ni yar iska ce idan Kuwa hakane Gobe sai na nuna masa iyakarsa....

Da Wannan qudurin tayi barci ta qagu safiya ta waye ta ganshi....

Washe garin Ranar ya fito cikin shirinsa na manyan kaya kasancewar yau Friday, da hularsa a hannu ya sami Mami a falo tana haďa breakfast,

'Mrng Mami,
'har ka fito kenan,
'eh...... yaja kujera ya xauna dai dai lokacin da mahaifinsa ya fito shima cikin shirinsa na fita office, sawwam ya gaida sa,

Suna cikin ci ne yake sanardashi, Dad Mgnr xuwa Umrah ayimin uxuri har wani watan,

'meyasa ya tambayesa yana kallonsa da mamaki,

'Cos Muna gab da fara exam ynxu, I don't want to lose it, idan mun gama exam ďin sai muje,

'Allah ya bada Sa'a,
'Amin ya tashi ya fice daga falon,

Yana shiga harabar Skul ďin ya tsinkayo su Hafiz, Abdul da Suhaib tsaye suna jiransa, inda suke yayi parking ya fito....

Hhhhhhhhhhhh suka ďauki dariya tare a lokacin da suke faďin yau harda hula three pointer... ya gyara xaman hular akansa yana faďin,

'Dan na birge budurwata ne, Kunsan ni sabon shiga ne a Wannan fannin, kallonsa suke da mamaki,

'ita kuma wacece acewar Suhaib, sawwam ya kalli Abdul,

'Abdul yayi Saurin cewa karka kalleni malam bansan ko Wacece ba,

'Hafiz yace inaji itace wannan yarinyar da muka haďu da ita ranar xamuje kwallo,

'No ba Ita bace ya faďa yana yatsina fuskarsa koma Wacece idan lokaci yayi xaku ganta ku Santa Kuma......

Abdul yace kai ka sani, ni muje inaso na duba assignment ďina a laptop,

Sawwam yace ba inda xanje sai na ganta taga kwalliyata saboda ita nayi, bari ma kagani ka ďauki abin da wasa ne, ya haye Saman motarsa,

Abdul ya juya shida Hafiz suna dariya suka barshi da Suhaib gurin ,

A dai dai Wannan lokacin Alawiyya tuni ta fita class, test sukayi saboda suna gab da exam ake masu rushing akan test,

Fitowar ta kenan daga test ďin wayarta na đauki qarar shigowar test tana dubawa sahibintane,

   _'Mrng sahibata, my eyes need to see you_.

tayi murmushi ta sami guri ta xauna kafin Alawiyya ta fito, ta tura masa

    _da gaske, ina xan ganka...._

  Oh yau xata ganshi kenan, tana son sanin ko shi waye, how did he looks, tana wannan tunanin kuwa taji reply ďinsa..

     _'xaki ganni sanye da farar shadda ynxu ina tunkaroki_...

Cike da xaquwa ta ďago da sauri, caraf suka haďa ido dashi,

Wani babban mutum ne sanye cikin farar shaddarsa da hula akansa, mai kakkauran jiki, ta tashi tsaye daga inda take xaune xuciyarta na bugawa Kada dai shine wannan, no it can be him, wata xuciyar nace mata idan shine fa, accept him yana sonki ya damu da ke...

Ga mamakinta mutumin ya wuceta batare da ya mata mgn ba, nan da nan ta bata rai kenan yana nufin ni xn masa mgn....

    _'ban ganki ba....._

    taja tsaki a fili, taji haushin nuna ko in kula da yayi akanta, sai tayi fushi yama raina mata wayo bayan sun haďa ido xai ďauke kansa yayi ficewarsa, da sauri tabar gurin itama sai ta rama, ta cusa wayarta a jakarta tana tafiya taji dariyarsu sawwam da Suhaib akan Mota, ta juya tana kallonsu wayace suke kallo suke dariya ďagowar da sawwam xaiyi suka haďa ido, sai ta fashe da dariya cikin matuqar mamaki suka xuba mata ido suna kallonta,

Dariyarta yau sawwam acikin manyan kaya, farar shaddar tayi masa kyau, ita kanta tasan tanayin dariyar ne dan taci xarafinsa domin har nuna sa take da yatsa qasa da Sama,

Cikin tsarguwa yake kallon jikinsa, baiga wata miskila a tare dashi ba,

Suhaib yace ita wannan fa? Kai tsaye sawwam ya bashi amsa da,

'mahaukaciya mana, kasan mahaukata suke irin Wannan dariyar ta babu gaira babu dalili,

Suhaib yace ita kuwa tana cikin yanayi cos haukarta bamai warkewa bace, suka taba hannayensu suna dariya sosai suma,

'Kuma ai mahaukatan ne, Mtseww taja tsaki tana hararar sawwam,

'wai dan ace yayi kyau, bakayi kyau ba, ni nasan dan ka birgeni kayi Kuma baka birgeba, Sam baka yimin ba🏻 akai kasuwa ummulkhairi bataso akai kasuwa ta fice tana dariya sosai,

Yayi shiru yana kallonta a qasan xuciyarsa yaji daďi, yasan yayi kyau ne take kushewa, ya diro daga Saman motar yana faďin,

'muje Suhaib wannan ta bata min rai na fasa ganin sahibata,

Khairi Kuwa qin Kunna wayarta tayi she mean it fushi take da sahibinta tunda ya mata Wulaqanci, sai dai tana mamakin girman mutumin, black beauty ne, tana xaune Alawiyya ta shigo itama a gajiye.

Yau ya Kama weekend sai ta shirya ta nufi cikin gari saloon, saboda kanta ya cunkushe guri ďaya yana buqatar gyara,

Bayan ta gama ta fito tana tafe tana kallon yanayin garin, bata fiye fitowa ba sai idan tare da Alawiyya ne,

Wasa Wasa sai tafiya take takasa samun napep ga shi magrib ta kusanto,

Tayi tsaye bakin titi cike da jin haushi, tana gurin faďa ya kaure tsakanin wasu matasa uku, ga mamakinta kowa da makaminsa daka gansu Kaga yan ta'adda,

Da sauri ta tsallaka titi ta ďayan bangaren hankalinta a tashe, ganin mutane sai gudu ake kowa na ta kansa,

Tafiya take sauri sauri bata ko waiwayen bayanta kamar daga Sama taga Mota ta tsaya gabanta taja da sauri, batayi tunanin komai ba ta faďa motar cikin tashin hankali,

Ta sauke ajiyar xuciya tana kallon masu Faďan ta window kafin ta juyo dan ganin Waye ya taimaketa,

Sawwam ne, xuciyarta tayi wani irin bugawa kamar xata  faďo ta qirjinta,

Ko kallonta baiyiba fuskarsa a murtuqe, fitowarsa kenan daga wurin snooker ya ganta tana wannan uban Saurin ganin ana faďa, Unguwar ce kullum cikin faďace faďace suke shima ba koda yaushe yake xuwa gurin ba,

Ta maida kallonta ga titi bayan ta haďiye wani yawu da kyar, ba bakin mgn sai ma xuciyarta dake bugawa,

Har suka iso ba Wanda yayi mgn acikinsu, ta soma qoqarin bude motar, Kamar daga Sama taji muryarsa na faďin,

'Kibi ahankali wannan Unguwar ba gurin xuwa bace....

Batayi mgn ba burinta taga ta fita daga motar, tana fitowa yaja motar da qarfi yabar gurin batare da ya waiwayetaba, tana tsaye a gurin tana kallonsa har ya fice.




Pherty xarah

        &

Ummy shatu

My wattpad Phertymerh1

No comments:

Post a Comment