Sunday 26 March 2017

RAMUWAR GAYYA... 40

*RAMUWAR GAYYA...*💘

  _Love story 50,50_

  *_UMMI A'ISHA_*

            _With_

    *_PERTYMERH XARAH_*


  40

  Arude su Abdul sukayi kansa suna salati, shi kansa dad hankalinsa yayi mutukar tashi amma hakan baya jin zai sakashi ya kyale sawwam ya zauna da ummulkhairi a matsayin matarsa,

"Kagama suman ka katashi ka sakar min yata ayanzun nan zan sake daura mata wani sabon auren wanda yafi dacewa da ita..."

Baban ummulkhairi yafada cikin daurewar fuska, yayun ummulkhairi ne suka matsa kusa dashi suna tambayar abinda yafaru sannan suna bashi hakuri,

Wata uwar tsawa ya daka musu wacce ta razanasu,

"Babu ruwanku ackin wannan lamarin, shi yasan waneni ni, sannan yasan dalilina nayin haka, kuma kamar yadda nafada ko da dansa zai mutu to tabbas sai ya sakar min yata domin shima ina son ya dandana bakin ciki kamar yadda na dandana a baya..."

"Zai sakar maka yarka kamar yadda ka umarta domin ba ita kadaice macen da ta rage ba, yanda ka isa da yarka to nima zan nuna maka cewar na isa da dana...." Dad din sawwam ya fadi tareda wucewa fuuuuuuh ya nufi inda su Abdul ke kokarin saka sawwam acikin mota,

Wani specialist hospital suka nufa dashi wanda ke kan titin zuwa kano road,

Suna shiga likitoci sukayi azamar karbarsa nan aka shigar dashi cikin wani daki aka fara bashi taimakon gaggawa,

Minti talatin ya dauka kafin ya samu nasarar iya bude idonsa, gani yayi dakin yana juya masa saboda hajijiyar dake daukarsa duk da akwance yake, ko tantama bayayi da ace a tsaye yake da tuni ya dade da kaiwa k'asa,

Runtse idonsa yayi take wasu zafafan hawaye suka zubo masa, har wani Sarawa yakeji kansa yana yi masa gashi wani abu mai daci ya cika makogaransa,

Ganin ya bude ido yasa dad matsawa gefen gadon, yana fadin,

"Sannu sawwam, kaji karfin jikinka?"

"Dad mutafi gida, muje ka kaini wurin mami..." Yafada yana kuka hawaye na bin kuncinsa,

"Sawwam bana son mubar garin nan batare da ka sakar musu yarsu ba, ka daure ka saketa, nikuma nayi maka alkawarin zan aura maka wacce tafita"

Girgiza kansa yayi yana hawaye acikin zuciyarsa kuma yana cewa "duk duniya babu wacce tafi khairu, idan na rabu da ita bazan taba samun madadinta ba"

"Kaji abinda nafada dan gidan dady?"

"Dad mutafi gida tukunna"

Mikewa dad yayi daga jikin gadon yana gyara babbar rigarsa ya fita, su suhaib ya samu awaje ya sanar dasu suje su fito da sawwam su tafi kano yanzu yanzun nan shikuma zaije ya hau jirgi yatafi gida,

Sai da yaga sun saka sawwam a mota sun tafi sannan shima yatafi airport,

Har lokacin Bai samu zarafin kiran mami ba saboda yafi son suyi maganar face to face,

Babu jimawa ya sauka a kano ya nufi gidansa duk ransa yagama baci, afalo ya samu mami tana kaiwa da komowa gashi gidan yacika dam da baki yan taya murna,

Karasawa cikin falon yayi sai huci yake kamar mahaukacin zaki wanda zaici babu,

"Dadyn sawwam wai meyake faruwa ne? Sawwam yakirani yana kuka kai kuma inata kiran wayarka baka dauka ba"

"Ba lafiya ba, sannan yazama dole sawwam ya rabu da wannan yarinyar, ina nufin sai ya saketa ayau ba gobe ba"

Zaro ido mami tayi cikin tashin hankali,

"Saboda me? Wannan abu da me yayi kama ace daga daura aure tun kafin mutane su baje an warwareshi"

"Hakan shi zaifi zama alkairi agaremu domin yarinyar yar gidan Alhaji aminu mai shadda ce..."

Cikin razani mami ta dafe kirji idanuwanta suka firfito waje take taji jiri yana daukarta, cikin azama ta dafe kujera ta zauna, kafin wani lokaci har gumi ya lullubeta kamar wadda tayi wanka,

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, yar gidan aminu mai shadda, tashin hankali wanda ba asa masa rana, tab..." Tafada tana rike da habarta,

"Kwarai kuwa yarsace, kinga kuwa ya zama tilas sawwam ya sakar masa yarsa ya auri wata.."

Tagumi mami tayi bata kara iya magana ba domin jikinta yagama bata cewar wannan auren nasu sawwam sunansa matacce dakyar idan zai kai kwana daya araye,

"Yanzu ina sawwam din?"

"Yana hanya sun taho shida abokansa suna nan karasowa"

Tagumi tasake rafkawa tana sauraron wakar dake tashi wacce ta cika unguwar, mawakin da aka dauko a bikin sai kiran sunanta yake yana ina uwar ango tafito fili ita kawai yake son gani,

Dakyar ta iya tashi tafita anan tayi kokarin saisaita fuskarta ta shiga cikin taron mutanen dake harabar gidan suna cashewa,

Kallo daya zakayi mata kasan cewa bikin dan lelenta akeyi domin tasha wani hadadden leshi wanda akiyasce kudinsa zai haura dubu tamanin, sannan ko ina najikinta gwalagwalai ne sai daukar ido suke dankara dankara, tun daga kan dankunnenta, da sarkarta da awarwaron da tasaka da zobbuna,

Tana shiga kawayenta da yan uwanta suka hau zubar mata da kudi suna lika mata, amma duk hankalinta atashe yake kololuwa, tana cikin filin ana zubar da ruwan kudi ta samu ta zare jikinta ta fita, daidai lokacin motar su sawwam ta danno kai cikin gidan,

Wurinsu ta nufa jikinta yana rawa, musamman ma da taga yakasa fitowa da kansa sai su abdul ne suka fito dashi,

Mami naganin haka tafara kuka,sashen dad suka nufa yana zaune afalo fuskarsa babu walwala, akan doguwar kujera suka kwantar da sawwam suka fice, gunshi mami ta karasa tana kallonsa cike da tausayawa,

Hannunta ya rike ya kankame sai kuma yafara hawaye,

"Mami kinji abinda ya faru ko? Wai sai na saki khairi..."

Wata tsawa dad ya daka masa, "ba wai bane, dole ne sannan tilas ne kasaketa mutukar kana son farin cikina, mutukar kana son kaci gaba da zama a matsayin dana..."

Runtse idanuwansa yayi wasu sababbin hawayen na sake kwaranya akan kumatunsa,

"Dad i can't, wallahi bazan iya sakinta ba domin itace rayuwata, she's my life, i can't do without her, she's my happiness, my everything..."

Afusace dad yaje ya daukeshi da wani gigitaccen mari,

"Ko zaka mutu sai ka saketa, sai ka saketa inyaso bayan ka saketa ka mutu din..."

Mami ce tayi gaggawar rikeshi tana kuka, "haba Alhaji, haba dan Allah, ya zaka rinka furta irin wadannan maganganun, sawwam fa shi kadaine danmu da muka mallaka bai kamata muyi masa haka ba"

Hawaye sosai sawwam yake yi domin da ace zai iya rabuwa da ummulkhairi to da ya saketa kodan yabi umarnin mahaifinsa tunda tun lokacin da yataso dad bai taba dukansa ba amma yau gashi sau biyu yana sharara masa mari da dazu awurin dauren aure da yanzu, muryar dad ce ta katse shi,

Sassauta murya dad yayi yana cewa,

"Sawwam karka manta da irin gatan da na nuna maka tun zuwanka duniya har izuwa yanzu, baka taba neman wani abu karasa ba, baka taba tambayata wani abu nahanaka ba, duk abinda ka nuna kana so to ina samo maka shi cikin gaggawa, dan haka kaima yanzu lokaci yayi da yadace kayi min biyayya ka aikata abinda na umarceka......

***

  Kwance take tanata faman gursheken kuka domin jikinta yagama bata cewar yanzu kila sawwam ya saketa an daura mata aure da faruk,

"Ummulkhairi kizo inji mahaifinki"

Tajiyo muryar mama tana yi mata magana, tashi tayi jiri yana daukarta domin rabonta da abinci harta manta,

Tana tafiya tana hada hanya ga mutane yan biki sai tsokanarta suke suna cewa "amarya kinsha kamshi",yara kuwa har jan mayafinta suke suna tsalle suna kiranta,

Falon mahaifinta ta shiga yana tsaye ya harde hannuwansa abaya, fuskarsa kamar zata fashe saboda tsabar bacin rai,

"Gani abba.."

"Na kiraki ne domin naja miki kunne akan wannan yaron, ban yarda ki kara kulashi ba har ranar da zai aiko miki da takardar sakinki domin yazama dole ya sakeki idan kuma hakan bai samuba to zan iya makasu a kotu har sai shari'a ta tilastashi ya sakeki"

Kukan datake ta dannewa ne ya subuce, "Abba kayi hakuri kayi min rai, wallahi indai sawwam ya sakeni to mutuwa zanyi..."

"Sai dai kuwa ki mutun domin dole sai yasake ki, tashi kibani wuri..."

Tashi tayi tana layi kamar wacce tasha kwaya ta fita, a tsakar gida ta hango yayyunta tsaye da mamansu suna fada mata abinda yafaru awurin daurin auren wanda har yayi sanadiyar faduwar sawwam aka daukeshi aka tafi dashi yanzu basu san halin da yake ciki ba,

Zabura tayi aguje ta nufi daki mutane sai kallonta suke, wayarta ta dauko ta kunna ta fara kiran Layin sawwam, wayar nata ringing amma ba adauka ba har ta tsinke, haka taci gaba da kira amma shiru, hannu ta dora aka tana kuka domin bata saniba ko sawwam mutuwa yayi bataji ba....

Jikinsa ne yayi sanyi hankalinsa ya sake tashi domin jin kalaman dady dayi,

Matsawa kusa dashi dad yayi ya rikeshi,

"Sawwam ka aikata abinda nace saboda samun farin cikina da kwanciyar hankalina, wannan abinda na umarceka shine Kadai zai samar min da farin ciki, sannan shine Kadai zai dawwamar mana da zaman lafiya"

Ko hannunsa kasa dagawa yayi sai hawaye da suke fita daga idonshi, kai ya daga alamar to,wani farin cikine ya lullube dady,

Ganin bazai iya magana ba dad yayi saurin juyawa ga mami,

"Dauko min takarda da abin rubutu a dakina maza yi sauri.."

Cikin sauri mami taje ta dauko ita kanta kukan take yi hawaye sun wanke mata fuska,

Karbar takardar dad yayi da biron ya mikawa sawwam ya makala masa a hannunsa,

Sawwam yana kuka yana hawaye ya yunkura ya tashi dakyar ya dan jingina ajikin kujera, hannunsa yana rawa ya fara rubutu ajikin takardar......



aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment