Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 13

*RAMUWAR GAYYA*......💘

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

              &

*Ummy Aysher*

             13

   Ta ďauke fuskarta daga garesa tana kallon Alawiyya,

Wasu maxane Dake gurin Waďanda nasan sawwam suka soma kiran sunansa,

'3 pointer yane....., bai Kalle su ba ya ďaga masu hannu kawai ya fice da abokansa,

Basu jima da tsayuwa ba lecturer ďin yaxo, suka soma shiga hall ďin, xamanta keda wuya wayarta na đauki qarar shigowar txt,

   _kibi a hankali dear gurin shiga hall bana son wani ya rabi jikinki_.

Tayi murmushi, ta Kira number switch off, tana son sanin mai number nan yayi matuqar damuwa da lamarinta, she feels him tun bata ganshi ba ta yarda dashi....

Bayan sun fito lecture wata course mate ďinsu ke sanardasu birthday party ďin ta da xa'a yi anjima, she is inviting ol her course mate.....

'wow wasu maza suka ďauki shewa, suna yi suna kwaso shoki yau akwai casu...

Bayan sun dawo hostel khairi tace gsky ni baxan jeba, bn taba xuwa wani party maxa da mata ba,

'Allah sai Munje, wannan shine na farko agaremu kibari Ina shirya xn biyo maki muje muga ynda abin yake,

'shikenan kawai ta faďa......

Da dare tana xaune da waya a hannunta, chatting take a facebook, qaramar wayarta ta ďauki qara tasan baxai wuce aljaninta bane tana dubawa Kuwa shine,

_idanuna nason ganin ki, ko xaki taimakamin ?_

  tayi murmushi dai dai lokacin da Alawiya ta shigo da sallama,

'tashi muje khairi Gashi can Xaa fara, ko shiryawa bakiyi ba ashe,

'shirin me xnyi qaton hijab ďina xan sanya, ta tashi tana gyara hijab ďinta, Alawiyya na qara gyara fuskarta, basu jima ba suka fito a tare,

So quiet kamar ba kowa a skul ďin, duk suna gurin party sai kiďa kakeji yana tashi, tayi waige waigenta ko xataga aljaninta Babu shi,

Suna xuwa gurin ya cakuďe maxa da mata, a filin Kuwa wasu maza biyu ne ke rawa, celebraty na xaune da saurayinta a gefe sunyi kyau sosai,

Suka sami guri suka xauna, wayarta na đauki qara,

_no makeup kinyi kyau, naji daďin da kika suturta min jikinki with hijab._

   Wannan Karon ma murmushi tayi tana waige waige ko Allah xai sa ta dace da mai turo saqon,

'3 pointer.... 3 pointer, taji gurin ya ďauki sowa Sanda suka shigo,

Yayi kyau sosai cikin qananan kaya kamar bashi ba, su Abdul na bayansa, wannan Karon murmushi yake duk da idanuwansa a boye suke cikin baqin glass amma yana cikin farin cikin tarbar da aka masa,

Ya sami guri ya xauna,
ba su jima da xama ba, aka kawo masu qananan papers a dunqule mai ďauke da numbers a ciki, sawwam ya ďauki ďaya su Abdul basu ďauka ba,

Aka xo gurin mata suna ďauka banda su khairi,

Bayan an gama addua, akayi introducing mai birthday da taqaitaccen tarihinta kana suka soma game ďin numbers ďin da suka bayar.....

'Number 1 suka kira......bai jima ba ya fito suka ďauki tafi kafin ace ya fiddo budurwarsa, dama tare suka xo kai tsaye ya nuna ta, ta fito tana murmushi, suka karanta mishi Abinda number tace ya cire abu biyar a jikinta,

Tsit akayi ana kallonsu, yayi murmushi ya matso gareta,
Ya cire gyalenta...... Suka ce one,
Ya cire takalminta..... Two
Ya cire awarwaronta..... Three,
Ya karbi wayarta..... Noo is not accepted sukaji muryar sawwam daga inda yake xaune, duk aka juya ana kallonsa,

'bamu yarda da waya ba,
Yaron yace amma ai a hannunta take,
Sawwam yace Abinda ke jikinta akace ba Wanda ke hannunta ba, saurayin ya juya ya ciro sarqar wuyanta suka ce..... Four,  yayi shiru yana kallon mai xai ciro na qarshe kowa su ake kallo,

Ya ciro ear rings ďinta ďaya..... Five aka ďauki sowa,

Aka kira number 2,3,har akaxo Kan na qarshe wanda sawwam ne kamar baxai fita ba sai Kuma ya fita ai Kuwa aka ďauki sowa, 3 pointer, Alawiyya ta dubeta

'gafa naki can ya fito, inaji baisan kina nan gurin ba,

Khairi taja tsaki tana latsar wayarta,

'sawwam your girlfriend Pls.... Yayi shiru kafin ya juya yana kallon su Abdul dan shi baida budurwa, matan dake gurin sai gyara mayafin su sukeyi, Abdul ya nuna masa wani gun da yatsa ya juya yana kallon gurin caraf idanunsu na sarqe dana juna, ya yatsina fuskarsa bayan ya ďauke idanuwansa

'kai ake jira sawwam....

Da hannu ya nuna khairi sai da gabanta ya fadi ita kanta Alawiyya tayi mamaki,

Akace ta fito, ba musu Kuwa ta fito sai dai fuskarta ba walwala, matan dake gurin aka soma kus-kus,

Gabansa ta tsaya daga ita har shi bamai walwala kowa na cike da jin haushin ďan uwansa,

'sawwam you are to kiss her for five minutes.....

Khairi ta xaro ido ta juya tana kallon mutanen gurin, duk idanu akansu can ta tsinkayo Alawiyya na dariya, a gefe daya ma su Abdul dariya suke ta juya tana kallon sawwam ga mamakinta ko a jikinsa, yaja Numfashi kafin ya xare glass ďin idonsa ya soka a gaban rigarsa, kallonta yake qasa qasa kafin ya matso gurinta,

da sauri ta matsa baya, shima ya matso, ta matsa, ya matso ta matsa cikin jin haushi sai abin ya bawa mutane dariya,

Ta rumtse idanuwanta dai dai lokacin da taji bugun numfashinsa a fuskarta....

'wait sawwam an fanshe ta.... ya tsaya cak he mean it da sai yayi ba ruwansa ya juya yana kallon sa,

Wani gaye ne a tsaye gurin ya bada kuďi amatsayin belinta ne komiye Oho,

Sosai khairi taji daďi tabi saurayin da kallo,

Sawwam ya tabe bakinsa haďe da ďaga kafadarsa ko a jikinsa yayi nuni da a sanya masa music,

Da sauri khairi suka fito gurin wayarta na ďauki qara,

_ina sonki, ina matuqar kishin ki, shikuma Waye?_

tayi shiru xuciyarta na bugawa ta juya ko xataga wannan saurayin acan ta tsinkayo sawwam yana rawa sosai, ya birgeta ashe haka ya iya rawa.........




Pherty
     &
Ummy shatu

No comments:

Post a Comment