Tuesday 21 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 35

*RAMUWAR GAYYA...*💘


  _love story 50,50_

     *_UMMI A'ISHA_*

              _With_
     *_PHERTYMERH XARAH_*


35

"Tunda kin hakura yimin murmushi nagani"  sawwam yace da ita yana kallon kyakkyawar fuskarta har lokacin tana rike da yan yatsunshi cikin nata,

"Wanne murmushi kuma bayan wanda nake yi?"

Ta tambayeshi idanuwanta akasa,

"Dago da fuskarki kiga" yafada yana matse dan yatsanta daya,

"Me zan gani?" Ta tambayeshi gamida dago fuskarta,kyas taji karar camera da alama hoto ya dauketa,

Daya hannunta tasa ta kare fuskarta tana murmushi amma kuma acan kasan zuciyarta tausayinsu ne itada sawwam yake ratsata domin ganin sun fara fuskantar matsalar rayuwa tun kafin su kai ga cika burinsu nazama ma'aurata,

"Kalli kiga..." Ya mika mata wayar, karba tayi tana ganin hoton duk da ba ashirye akayi shi ba amma yayi kyau,

Murmushi tayi ta mika masa wayar "dama ai kasaba yimin hoto batare da sanina ba" tafada ashagwabance,

"Kuma wallahi duk wanda nayi sai yayi kyau, ko baki san nadauka ba"

Murmushi tayi tafara kokarin bude kofar motar,

"Tafiya zakiyi kibarni? Shikenan nima bari naje gida"

"Zaka dawo?" Ta tambayeshi idonta rau rau kamar zatayi hawaye,

"Zan dawo mana,zoma kiji.." Yace da ita amma kawai yafada ne saboda tasamu nutsuwa hankalinta ya kwanta amma magana ta gaskiya jinshi yake wani iri gashi dai yana mutukar son yaganta akusa dashi to amma kuma yanajin ranshi wani iri,

Batare data juya ba tace "me zanji?"

"To kijuyo mana indai kina son ji din"

Kanta ta sake daukewa, murmushi yayi ya matsa kusa da ita,

"Acuci maza kikayi ne?"

Hakan da yafurta ne yasata yin murmushi, "wa zan cuta?"

"Ni mana, nikuwa nasan baki da wani gashi sai bayan munyi aure sannan zakiyi"

"Sannunka, naga dai kaima ba gashin gareka ba"

"Kina sone nasake tarashi yafi wannan? Wallahi indai kina so to zan tara har yakamo naki a tsayi"

Dariya tayi ta juya tana kallonsa "har ka mutu gashinka bazai kamo nawa ba"

"Haka kikace?"

"Ehhh"

"Kalli bakinki na rashin kunya,zakiyi bayani ne"

"Ai kai yayane yi hakuri" tafada tana dariya, hannunta yasaki,"to sai anjima,kije hostel sai nadawo"

Fita tayi daga cikin motar tana yimasa bye bye har yabar wurin, hostel ta tasamma shiga amma acikin ranta ta daura niyyar taya sawwam da addu'a akan Allah ya yaye mishi abinda ke damusa.

  Sawwam gida ya wuce yana zuwa ya shiga falon mami tana zaune tana lissafin kudin wasu kaya da aka kawo mata,

Kan cinyarta sawwam ya dora kanshi,

"Mami ban san abinda yake damuna ba kwana biyu bana son ganin khairi, bana son koda jin muryarta gashi ina sonta ina kaunarta bana son rabuwa da ita.." Yana gama fadin haka sai ga hawaye nabin fuskarshi sharrrrrrr!

"Sawwam tun yaushe? Meya hadaku? Fada kukayi?" Girgiza mata kai yayi har lokacin hawaye ne yake fita daga idonsa,

"Yi shiru ka tashi kaje ka kira min baba dan tsoho"

Tashi yayi ya fita zuwa gate, baba dan tsoho na zaune yana sauraren rediyo sai dariya yake shi kadai,

"Baba dan tsoho hajiya tana Kira"

Yana fadin haka ya wuce yakoma cikin gida, ajiye rediyon baba dan tsoho yayi yabi bayan sawwam da sauri,

Cire takalmin kafarsa yayi ya shiga falon mami, tana zaune lullube da mayafi tayi tagumi, zama yayi suka gaisa ta sanar dashi duk abinda sawwam yafada mata dama sha'ani irin wannan tasaba fadawa baba dan tsoho kasancewar yana samar musu da mafita,

Gyara zama yayi ya kalli mami "babu komai insha Allah zanyi istihara kuma da yardar Allah koma menene zai warware"

"Allah yasa" mami tafada duk ranta ahargitse domin ji take kamar ta fashe da kuka.

Tun daga ranar baba dan tsoho ya dage da yiwa sawwam addu'a da rokon Allah, itama mami nayi hakama ummulkhair ba abarta abaya ba domin duk tafi kowa damuwa da halin da sawwam ya shiga, gashi soyayyarsu sai ja baya take ba kamar da ba,

Bayan kimanin sati biyu tana kwance adaki tayi shiru tana tunani sai taji karar wayarta, ganin sawwam ne yasata tashi zaune ta daga wayar,

"Bakya nema nane?" Taji yafada ahankali,

"Ni na isa, ina nemanka mana"

"To kizo gani awaje ina jiranki"

Kashe wayar tayi ta dauki gyalen doguwar rigar dake jikinta ta yafa tafita,

Yana zaune asaman motarshi yasha kananan kaya jeans & t shirt, yana hangota ya diro daga saman motar yana murmushi,

"My lonely barka da fitowa" dadine ya kamata domin rabonta da taji ya kirata da wannan sunan har ta fara mantawa,

Murmushi tayi tana wasa da hannun gyalenta,

"Say something mana my lonely.." Shiru tayi tana kallonsa amma kuma wani farin cikine ke ratsata,

"Kalli bayanki kigani.." Yace da ita yana dariya, tana juyawa taga wani katon kare yana nufota,

Cikin razana tawuce bayanshi ta rungumeshi, sosai ta kankameshi tareda boye fuskarta a bayanshi, in banda rawa babu abinda jikinta yake yi,

Dariya sawwam yake yi sosai yana jinta jikinta sai rawa yake, sannan ta rungumeshi ta baya kam kam,

"My lonely yatafi fa" yace da ita ahankali,

Dago kanta tayi ta lalleka bataga karen ba,

"Muje cikin mota, wallahi ni tsoron kare nake ji kar yazo ya cijeni"

Har yabude mata gaban motar tana rike dashi, zama tayi ya rufe yazagaya ya shiga yana mata dariya,

"Wai dama haka kike da tsoro ban saniba" yafada cikeda tsokana,

"Wallahi bana son kare, yatab'a biyoni ne lokacin ina yarinya, dakyar aka kwaceni da tuni ya cijeni tun daga lokacin nake tsoronsa"

"Ummulkhairi mai tsoron kare" yafada yana dariya, duka takai masa sai kuma tafasa tarike cikinta,

"Wallahi cikina ne yake ciwo washh"

Sunkuyawa yayi yana tambayarta "ciki? Me kika ci?"

"Babu komai.." Tabashi amsa har lokacin tana rikeda cikinta,

"Ciwon ciki kikace?". Kai tadaga masa,hannunshi yasa acikin dan wani aljihu dake bayan kujerarsa ya dauko magani,

"Ga magani kisha indai ciwon cikine yanzu zai daina, idan kuma bashi bane ki fada min gaskiya..."

Dagowa tayi ta kalleshi batayi magana ba kuma bata karbi maganin ba,

"Idan kin san wata ne ya zagayo to kifada min gaskiya in Kuma ciwon cikine to ga magani"

Nan dinma shiru tayi masa tana kallonsa,

"Ciwon cikine ko ciwon mara?" Kai ta daga masa,

"Wanne aciki kike yi? Ciwon Mara? Ciwon ciki?"

Kai tasake daga masa,

"My lonely nidai ban gane wannan daga kan naki ba"

Fitilar motar ya kunna ya janyo kafarta daya yana kallo, kafar ta dan kumbura kuma tayi fari sosai, mayar mata kafarta yayi ya ajiye yana murmushi,

"Tun farko da sai kifada min gaskiya cewar watane ya zagayo amma kya wani tsaya kina kallona..., muje nakaiki chemist nasai miki magani"

Kwantar da kanta tayi ajikin kujera idanuwanta arufe, tana jinshi ya tashi motar, sai da suka fita daga cikin makarantar sannan ya juya yana kallonta,

"Dama can kina irin wannan ciwon ne?"

Girgiza masa kai tayi "sai dai ciwon kafa da tashin zuciya"

"Wannan kumburin da tayi dama na ciwonne?"

Daga masa kai tayi, "ciwo sosai ma, wani lokacin fa dakyar nake takawa"

"Ayya sorry my lonely insha Allahu kin kusa ki daina daga munyi aure shikenan zan baki magani, ai kina so ko?"

"Kai sawwam" tafada cikeda kunya,

"Babu wani kai" yafada yana dariya, wani sabon chemist sukaje wanda ke gaba kadan da makarantar, shiga yayi ya siyo mata magungunan yadawo, maidata makaranta yayi sai faman tsokanarta yake, ba karamin dadi tajiba ganin yanda ya koma mata sawwam dinta sak mai sonta, mai sake mata fuska,mai tsokanarta da sakata dariya akowanne lokaci wanda suke tare,

Ganin bata da lafiya yasashi yana ajiyeta yayi mata sallama yatafi,koda yakoma gidama yana kwanciya ya kirata lokacin ma ita har tayi bacci sakamakon maganin data sha, karar wayarne ya tasheta,

Hira sukayi sosai domin har wurin karfe 2 nadare suka kai suna hira, kamar karsu rabu haka suka daure suka yi sallama da juna.

***
  Baba lami na kitchen tana jajjera abinci akan faranti bayan ta kammala hadawa,

Dan wake ne tayiwa sawwam, ahankali take zaro kullin dake soke acikin zaninta,warwarewa tayi tafara diba kadan tana barbadawa aciki, sai da tagama barbadeshi tas sannan ta mayar ta soke a zaninta, rufe flasks din tayi ta kinkima zata fita, turus tayi sakamakon ganin mami atsaye tana kallonta,

"Ha...hajiya yanzu kika shigo?"

Mika mata hannu mami tayi,

"Bani abinda kika boye a zaninki"

"Hajiya babu koma.."

"Kibani nace" mami ta daka Mata tsawa, cikin rawar jiki tafito da kullin garin maganin ta mika mata ta tsugunna tana neman gafara,

"Ina so ki fada min wanda yasaki"

Shiru baba lami tayi domin dama hajiya raliya sai da ta gargadeta da cewar kada ta kuskura tafadi cewar itace tasata idan ankamata,

Tambayar duniya mami tayi mata amma taki amsawa, ganin haka yasa mami dauko mata kudinta wato albashinta datake biyanta tabata tace tabar mata gida domin duk wanda yayi maka wannan to za a iya hada baki dashi akasheka,haka baba lami ta tattara komatsanta tayi gaba to sai muce Allah ya raka taki gona.

  Ahalin yanzu kam soyayyar sawwam da khairi tadawo normal, kullum suna tare basa nisa da juna, Rukayya kuwa yama manta da ita dama can bata gabansa,

Ganin ankafe time table din exam yasa ummulkhairi shiryawa domin zuwa gida weekend, lokacin da ta sanarwa sawwam sai yabata rai saboda baya son ta tafi amma ganin tunda tazo bataje ba yasashi hakura yarakata tasha ta tafi, amma duk da haka koda yaushe suna makale awaya minti kadan zai kirata ko abinci zaici sai yafada mata,

Yanzun ma tashinsa daga bacci kenan zai shiga wanka ya kirata, tana tsakar gida tana gyarawa mama alayyahu ganin kiransa yasata sadadawa daki ta kwanta akan katifarta ta daga wayar,

"Sahibina har katashi daga baccin?"

Wata hamma yayi sannan yayi mik'a,

"Yanzun nan natashi, baccin ai babu dadi saboda babu ke.."

Murmushi tayi "me kakeci nabaka na zuba, idan munyi auren har gajiya da ganina zakayi watarana ka korani dakina kace hutawa zaka yi.."

Murmushi yayi ya tashi zaune ya ziro kafafunshi daga saman gado zuwa kasa,

"Tab kar Allah ya kawo wannan ranar, ranar dai da zan gaji dake bana fatan ganin wannan ranar,nida nake son irinka ganin ki akusa dani saboda nasan zan samu kulawa, kinga yanzu wanka nake son yi amma duk jin jikina nake a mace, da ace munyi aure kinga da kece zaki yimin ki shiryani tsaf..."

"Hoohhh sawwam ya isa" tafada cikin jin kunya,

"Au bazaki ringa yimin wankan ba idan munyi aure?"

"Zanyi maka, shikenan?"

"Ba shikenan ba" yabata amsa,

"To koma dai me kakeso zanyi maka idan lokacin yayi"

Murmushi yayi yashafa sumarshi,

"Lokacin fa yakusa, wallahi ina gama service ko ban fara aiki ba aure zamuyi, kinga yanzu nanda next year munyi aure may be ma kina da ciki...."

Kit ta kashe wayar tana dariya, "sawwam rashin kunya,duk maganar da tazo bakinka fada min kake" tafada acikin zuciyarta,

Tashi tayi tafita tsakar gida domin karasa aikin data fara, mama tagani zaune tana yi,

"Mama da kanki?"

"Ehh mana tunda ke kin tafi waya, wannan saurayi naki komai zaiyi sai yafada miki ne? Allah ya kaimu lokacin da zamu aurar daku mu huta kuje can gidanku ku karata"

"Haba mama nida bana so narabu dake"

"Tashi kibani wuri ja'ira"

Mikewa ummulkhairi tayi tana dariya ta fada kitchen, satinta biyu tadawo makaranta, lokacin su sawwam har sun fara exam sunyi rabi ma saura kiris su kammala,

Kasa banbance yanayin da take ciki tayi domin wani bangare na zuciyarta yana murna saboda kammala karatun da sawwam zaiyi domin tasan yana gamawa za afara maganar bikinsu dan haka baza ajima ba za adaura musu aure suje sawwam yabata daddadar rayuwar da kullum yake fada mata zai bata, yayinda wani sashe na zuciyarta yake bakin cikin rabuwar da zasuyi da sawwam musamman ma idan aka turashi service gari mai nisa, kullum cikin wannan tunanin take,

Tana tsaye ta rungume hannuwanta a kirjinta shikuma sawwam yana jingine ajikin motarsa shima yayi yanda tayi, ita kanta tsaiwar tasu yanda sukayi abin burgewa ce domin duk wanda ya wuce sai ya kallesu,

"Sawwam bana son katafi nesa a service dinka.."

"Saboda baki yarda daniba? Tsoron me kikeji? Uhm"

Murmushi tayi "ba rashin yarda bane nidai bana son kayi nisane"

"Ki fadi gaskiyarki dai, kina tsoron kar naje kudu nazama dan bariki ko" yafada yana dariya,

"Ni bahaka bane"

"Hakane mana, ai nasan abinda kike jin tsoro kenan"

Matsawa yayi kusa da ita kamar wanda zai rungumeta,

"Ki kwantar da hankalinki sawwam nakine ke kadai babu da wacce zaku rabashi.. Ke kadai zaki mallaki kayanki kiyi yadda kike so dashi".

aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu🏻

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment