Monday 20 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 31

*RAMUWAR GAYYA........ 💘*

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

          &

*Ummy Aysher*

     31

Shiru yayi yana saurarenta amma har lokacin bai ďaga kanshi ya kalleta ba,

Jikinta yayi sanyi, she is not happy a yanda yake yi mata kamar xatayi kuka, ta qara marairaice murya,

'kayi haquri idan na bata ma, wallahi faruq is nothing to me Kuma ni bansan da xuwanka ba da baxan tsaya gurinsa ba,

Ya tabe bakinsa haďe da ďaga kafadunsa ko ajikinsa, ya maida glass ďin sa ya rufe idonsa, ta ciki yake kallonta yaga duk ta damu, yaji daďin ganin yanda take bashi haquri tayi masa laifi, ya haqura amma yaqi ya nuna mata,

Alawiya ce ta qaraso da textbook a hannunta ta miqawa khairi,

'ga book ďin ki gida xn tafi duk na tafi, khairi ta karba tana faďin,

'anjima xaki shigo, kitso nake son kimin,

'ban maki alqawari ba dan xn raka qawata biki amma idan mun dawo da wuri xn shigo,

'shikenan sai Kindawo, Alawiyya ta dubi sawwam,

'mutumin mu yau ba mgn ni naga yau sai wani daurewa kakeyi, yayi mata banxa, ta dubi khairi,

'meke damunsa,
'fushi yake dani,
'shine ni Kuma abin ya shafeni, to kayi haquri ko menene ka sassautawa qawata haka,

Ya juya ga motarsa alamar xai shiga khairi taqi ta matsa, Alawiya ta fice tana dariya,

'haquri nake ta Baka kake min shariya haka,

'matsa xn shiga mota, ba musu ta matsa ta bashi guri ya shiga motar yaja ta a fusace tana tsaye tana kallonsa har ya fice daga Skul ďin,

Jiki a sanyaye ta nufi hostel,  baxata qara xubar da ajinta gurin bashi haquri ba har ya gaji da fushin ya sauko,

Sosai ta damu, ranar duk a kwance ta jini jikinta sukuku hankalinta da tunaninta duk yana kansa, ko ringing wayarta tayi da sauri take dubawa ko shine idan ba shi bane sai ta cillar da wayar tana tsaki, wayar kowa bata amsa ba ranar kamar yanda itama bataji muryar sahibinta ba,

Sawwam Kuwa har Ga Allah ya haqura, yayi mata Hakan ne dan ta gane laifinta sosai ta daina tsayuwa da wani, yana tsananin sonta da kishinsa baxai jure ganinta da wani ba, so a gobe xasu shirya ya nemi sulhu tunda yaga ta damu duk da itama yasan tayi fushi da shi tunda gashi bata nemesa ba, ba text ba Kira.

Washe gari da sauri tayi shirinta ta fita lectures kasancewar 8:00am suke da lectures,

Tana fita ta haďu da Alawiya xata shigo hostel sai suka wuce tare,

'shine kika qi xuwa jiya ko, kinbar ni dakai duk ya cunkushe,

'bamu dawo da wuri bane amma yau baxan je gida ba sai nayi maki,

'kinxo min da assignment ďina kuwa?
'yes yana jaka sai muyi submitting idan mun fito lectures,
'shikenan,  suka shiga hall ďin,

10:00am suka fito lectures, bayan sun fito Alawiyya tayi gurin saurayinta, sai ta sami guri ta xauna cos xasu shiga wata lecture basu gama ba, kamar wacce aka ce ta ďago, tana ďagowa idanunta suka sauka akansa, yana tsaye jingine da motarsa hannuwansa sarqe a qirjinsa, wata budurwa ce a gabansa batasan ta ba yau ta soma ganinta,

Jikinta ya ďauki rawa sosai hankalinta ya tashi, kada sawwam ya barta ne ya sami wata da Kuwa ta shiga uku yanda take mutuwar sonsa a ynxu takejin ba abinda xai iya rabasu,

Suna haďa ido da sawwam tayi Saurin ďauke kanta, ta tattara kayanta ta tashi daga wurin ta shige hall inda sauran friends ďin ta,

Sawwam yayi murmushi yana kallonta,
'kingane farida, Suhaib wani irin mutum ne mai wuyar al'amari, dole sai kina haquri dashi amma duk da haka bai kyauta ba xn mishi magana,

Tace Nagode sawwam, ina mutuniyarka yau duk ban ganku ba,

'ita nake jira ma anan inaji bata fito lectures ba, tayi murmushi,

'kuna birgeni dama haka Suhaib yake dana dace,

'kinma dace abokina fa First Class ne matsalar shi ďaya Kuma xn mashi mgn xai gyara,

'Nagode sosai ta juya ta fice, ya jingina yana jiran khairi yasan tayi fushi a ynda yaga fuskarta,

Wannan Karon lecture ďin da akayi komai bata fahimta ba duk hankalinta da tunaninta yana gurinsa gani take har ynxu yana tare da wannan budurwar,

Sun fito lectures Alawiya tace kije gani xuwa, man bai gaji da gani na ba,

Murmushi tayi kana tayi hostel fuskarta a ďaure ganinsa tsaye, inda yake ma bata kalla ba, ganin da gaske take yasha gabanta,

'kin ganni fa shine kika wani fuske, tun ďaxu Ina jiranki ingayamiki na haqura shi kenan komai ya wuce, tabi ta gefensa xata wuce ya qara tare ta,

'Ni ynxu Kuma menayi kike fushi dani,

Takaici na qara rufeta tambayarta yake meyayi bayan yasan abinda yayi, ta qara bata fuskarta taqi ma ta kallesa,

'Ni ynxu koma menene kiyi haquri sulhu naxo muyi Kinsan banda wacce tafiki fa ya faďa cikin xolaya, harara tabisa da Ita kamar kwayar idonta xata faďi qasa,

'ita wacce nagan ku tare fa?
'au na manta... taja tsaki ta fice yayi saurin riqo hannunta,

*'Ramuwar gayya* ce da gangan nayi dan kiji yanda naji jiya dana ganki da wani, tunda kinji ynda naji shikenan, _50,50_ kiyi haquri,

Tayi shiru tana kallonsa, batare da ta tankaba,

'budurwar Suhaib ce fa, mun fito lecture take gayamin abinda ya hadasu shine na jawota nan Muna mgn dan kigani, ni ynxu bama Wannan ba, abar mgnr, fushin ma kidaina nima na daina, Alawiya tayi maki kitson?

Kamar baxata tanka ba sai Kuma ta girgixa kanta,

'muje saloon ayi maki acan bnga alamar ta iya kitso ba fa,

'ta iya ita kemin ai, ynxu ma xataxo tana hanya, ya sauke ajiyar xuciya,

'idan tayi ki dauki pic ďin ki turomin ta whatsapp ingani inyayi kyau, dama ga gashin ba fasali,

Ta saki murmushi tana kallonsa,
'Kuma a hakan wani ya gani yace yana so,
'to ya xanyi tunda Ina son kayana, da haka suka bige da hira har Alawiya taxo itama tasa bakinta kana suka nufi hostel yayi gida.

*pherty xarah

        &

*ummi shatu

No comments:

Post a Comment