Monday 20 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 25

*RAMUWAR GAYYA..... 💘*

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

                &

*Ummy Aysher*


25

     Ta maida laptop ďin ta rufe haďe da ďora kanta akai, idanunta a lumshe tana tunanin sawwam,

da haka barci mai nauyin gaske ya ďauke ta tare da mafarkai iri iri a Wannan ranar,

Washe gari bayan tayi sallah ta soma haďa kayanta, tana fitowa wanka ta Kira sawwam dan shi xai kaita tashiga motar kasuwa,

Ta gama shirinta cikin koriyar atampha sosai tayi kyau duk da hijab ta sanya, ta janyo trolley ďinta ta fito hostel anan ta sameshi har yaxo da alama ko wanka baiyi ba dan kayan barcine ma ajikinsa,

Ya karbi trolley ďin ya Sanya a booth, ta koma hostel ta dauko laptop da sauran kayanta kana ta rufe ďakin tayiwa sauran qawayenta sallama ta fito,

'sai kace wadda ake kora a gari, tunda safe haka khairi,

'inaso na isa da wuri ne bana son tfyr dare, ta buďe motar ta shiga, ta ajiye masa laptop ďinsa a baya,

'bnmayi kallon ba, barci ya ďauke ni,

'ke har xaki iya barci kenan, ni tunanin rabuwarmu ya hana min barci, tayi murmushi har a xuciyarta taji sanya ta juya tana kallonsa,

'sai kace wacce xatabar duniya gabaki ďaya, in banda abinka ai ga waya,

'waya baxata gamsheni ba Kamar yanda xan gamsu idan muna tare, I will miss you,

'miss you more kodan rigimarka,

Yayi dariya dai dai lokacin da suka qaraso tasha ya sami guri yayi parking, ya dubeta,

'kijira bara na duba motar dake lodi ynxu, ta gyada kai tana kallonsa da murmushi har ya fice,

Bai jima ba ya dawo, ya buďe booth ďin ya ciro kayanta yakai motar, ya biya Kuďin kana ya dawo,

'motar ma ta cika ke kaďai kika rage, ta buďe motar ta fito jikinta a sanyaye kamar karta barshi,

Tana fitowa yaja dogon hancinta yana murmushi ganin damuwa a tare da Ita,

'ki Kula sosai kada kije daďin Mota ya bigeki kiyita barci har axo a wuce Bauchi,

Ta saki dariya tana kallonsa,

'sai kace nice kai, da alama baka taba tafiya mai nisa ba, suka Jera tare suna tfy,

'inda ma naje baki taba xuwa ba, ke daga Bauchi sai nan Skul, ta gyada kanta kawai tana tabe baki,

Sun jima suna Sallama kamar kada su rabu dole suka haqura da juna ta shiga motar, tana ďaga masa hannu yana ďaga mata, yana tsaye har suka fice kana ya shiga tashi motar ya fice cike da kewarta.....

Yana shigowa falon yaci Karo da Mami ta fito ďakin abbansa,

'ina kafito da sassafe haka, ya ďan sosa kansa,

'naje na kai khairi ta shiga motane yau xataje gida,

'Ayya har ta tafi kenan baka kawo min ita naganta ba,

'Mami inta dawo xn kawo maki ita ki ganta har sai kin gaji,

Tayi hanyar kitchen tana murmushi
'Allah ya dawo da Ita lfy,
'Amin yayi hanyar ďakinsa.

Khairi Kuwa tana isa gida ta kirasa a waya ta sanardashi,

Qannenta suka xagayeta cikin farin ciki kowa da irin labarin da yake bata iyakarta dariya,

Da dare ta sami mahaifinta tare da sanardashi abinda ke faruwa Wannan karon yafi wancan Karon farinciki ganin ganin burinsa na gab da cika, anan ma addua yayi mata haďe da sanya mata albarka,

Duk ba daďi takeji, she miss him alot, da'a Skul ne da Yanxu suna tare, shi kaďai take gani a xuciya,ruhi da kuma gangar jikinta,

Ta janyo wayarta tana qoqarin kiransa sai ga kiranshi, ta ďauka haďe da karata a kunnenta cikin murmushi,

'guess where I'm? tayi shiru tana tunani,
'inda Rukayya,
'Nooo, bayan yaja guntun tsaki,
'na baka gari,
'gani Skul inda muke xama, yini ďaya kacal nayi kewarki,
'nima kewarka nakeyi, tun ďaxu kai nake tunani sai naji gida ba daďi kamar naxama tsuntsuwa nadawo,
'dana fi kowa farin ciki idan na ganki kusa dani a ynxu, so ya kika sami gida yasu Abba,

'Gida Alhamdulillah, ya Mami,
'Mami tana fushi dake kinxo baki mata Sallama ba,
'Wayyo kabata haquri dana dawo xnxo naganta,
'Allah yasa,
'Amin

Nan suka cigaba da hirarsu cikin so da kewar juna.

Afuwan Pls masu qorafi, wannan ma ayi haquri dashi, inada test gobe next page xakujishi da yawa.....



Pherty xarah

      &

Ummy shatu

My wattpad Phertymerh1

No comments:

Post a Comment