Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA..16

*RAMUWAR GAYYA...*💘

  _Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

        _With_

_*PHERTYMERH XARAH*_

  16

*H*ar suka kule daga wurinda take tsaye bata sake kallon koda inda suke ba sai dai amma kuma maganarshi ta tsaya mata arai cewar wai dama so take yayi kissing dinta may be ma har mafarki tayi,

"Mtswwww,kai ka isa ma" tafadi bayan taja dogon tsaki, gyara tsayuwarta tayi tana jiran alawiyya wacce taga ta nufota,

"Yadai..?" Alawiyya tace da ita bayan tazo daf da ita,

"Wallahi wancan banzan gayen ne dan rainin hankali kuma wallahi sai na mayar masa da martani domin bai nemi zaman lafiya ba, har ni zai cewa wai sonshi nake..?" Ta fada cikin kunar rai,

"Hmmmm nidai babu abinda zance domin fadanku ne na masoya.."

Wani sabon haushi ne ya sake ziyartar ummulkhair domin bata kaunar taji ana hadata da sawwam a matsayin masoya, caraf ta hangoshi shida abokansa sun nufi motarshi suna kokarin shiga,

Kamar wata zakanya haka ta zubura ta nufi wurinsu, yana kokarin shiga gaban motarshi ta dakatar dashi,

"Kai sawwam kake ko kawwam ko me, har kaine zaka budi baki kace wai ina sonka? Mtswww Allah ya sawwake domin ni banga abin so a tattare dakai ba,sannan wannan kazamin bakin naka da ko brush may be baya samu shi zakace wai ina mafarki akanshi, mtswww amma kuwa Allah ya yaye min mutukar nayi mafarkin wannan kazamin bakin naka to na cancanci a jajanta min, bakin da Allah ne kadai yasan kazantar dake tattare dashi perhaps har na wasu arnan ma ya taba...."

Tana kaiwa nan ta juya ta wucesu yana tsaye sororo yana kallonta shi bai karasa shiga cikin motar ya zauna ba sannan shi bai fasaba,

"Tab...." Sawwam ya fadi acikin zuciyarshi, shi da ko mata acikin makarantar nan baya kulawa amma shi zata kalla tayi wa wannan maganar wai ya saba kissing din mata watakila ma harda arna aciki, duk makarantar nan kowa yasan yan group dinsu basa kula yanmata sannan basa shan komai sudai barsu da shakiyanci da tsokanar mutane,batare da yayi yunkurin yin komai ba ya shiga cikin motar ya tadata yana tsaki,

"Three pointer ko yarinyar nan sonka din takeyi da gaskene?" Yaji muryar hafiz yana tambayarshi,

"Oho mata..." Shine kawai abinda ya fada ya dauke kansa, yana jinsu Abdul sai shakiyanci suke yi masa suna dariya.

Alawiyya na tsaye tana kallonta har ta karaso wurinta tana murmushi,

"Ai sai yanzu naji dadi da naje na sanar dashi bai yimin ba balle har na soshi.." Kairi tace da alawiyya tana murmushi,

"Allah dai ya sassauta muku zuciyarku"

Alawiyya ta fadi tana kallonta, tun da wannan abun ya faru basa haduwa da sawwam,wannan abu ba karamin dadi yayi mata ba domin dama shine babbar matsalarta a makarantar nan, wani lokacin tana hangoshi daga nesa ko acikin abokanshi ko kuma a motarshi,

Yau dinma a motarshi ta hangoshi zaune amma yabar kofar motar a bude, bakin takalmi yasa da bakin wando sai blue din riga mai dogon hannu, kawai zaune yake domin baya ra'ayin shiga lecture yau dama wani lokacin zamanshi kawai yake yi yaki shiga lecture,

Ta gefenshi taje ta wuce tana ta yan harare hararenta, ta cikin glass din dake manne a idonshi yake kallonta sai wani daddauke kai take yi,

"Mtswww" yaja dogon tsaki tareda kawar da kanshi,

Murmushi tayi najin dadi domin dama burinta ta bakanta masa rai kuma gashi tayi nasara,

Sake juyawa yayi ya kalleta tana sanye da blue din leshi mai stones ajiki tasa bakin hijabi da bakin takalmi,

K'irr taji massage ya shigo, tana dubawa taga sahibinta ne,

  _Shigarki ta yau tafi ta kowacce rana kyau, da fatan dai kinci abinci domin bana son zamanki da yunwa_

"Hmmm Allah sarki masoyina" tafadi tana murmushi,

  _tnx dear, naci abinci ina fata kaima baka tareda yunwa.._

Ta mayar masa da reply bayan ta samu wata baranda ta zauna, dama yau alawiyya ba zata zoba ta danyi tafiya dan haka ita kadai ce, wani calculation ta fara yi saboda sunada text gobe, har yamma tayi tana zaune tanata karatunta ita kadai sai misalin karfe biyar sannan ta tashi zata shiga hostel anan yan department dinsu suke cemata da daddare tasamu ta fito domin zasuyi group discussion, kamar ba zata amsa musu ba sai kuma tace to, hostel ta shiga taje ta kwanta ta huta domin ta gama gajiya kasancewar ta wuni tana karatu.

  Misalin karfe 8 tafita tana zuwa ta iske yan ajinsu anan aka fara tattaunawa duk wanda yakeda wata tambaya ko wani abu wand ya shige masa duhu sai ya fada sai ayi masa bayani da hausa dalla dalla yanda zai gane gashi harda marker domin rubutu a bord,har 9:30 sunata tattaunawar sai wurin karfe goma saura sannan suka kammala, fitowa ummulkhair tayi zata koma hostel diffff taga an dauke wuta gashi tabar wayarta a hostel tana charge, nan ta fara lalube domin gurin ya gama gaurayewa da duhu dimm,

Sawwam dake class shi kadai yana karatu sai yaga diff yan wuta sun dauke, tsaki yayi ya tattara kayanshi ya fito dama shi haka yake yi da daddare karatunshi yake yi da rana kuma yayita biye friends dinshi suna shakiyanci,

"Mtswww ashe fa nabar wayar a mota.." Yafada ahankali bayan ya fito daga cikin class din, ahaka ya dauki hanya domin zuwa wurinda yayi packing din motarsa,

Ummulkhair tafiya kawai take yi tana laluben hanya cikin duhun taci tuntube da wani katon dutse wanda ke girke agun

Babu zato karaf sawwam yaji yaci karo da mutum ya fado jikinsa, ba ita ba shi kanshi ya tsorata,

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un..." Ummulkhair ta fada bakinta yana rawa,

K'amshin da yaji ne yasashi fahimtar cewar itace, gam ya riketa ajikinshi, jikinta ne yahau rawa,

"Nashiga uku, waye..?" Tafada da karfi tana kokarin kwacewa daga jikinshi,

"Sawwam ne...!" Ya fada cikin soft voice dinshi,

Ai tana jin haka ta bude baki zata yi masa rashin kunya,

"Mallam meye haka, dallah sakeni ni ba yar iska bace irinka.."

"Nine dan iska...?" Ya fada yana sake hadata da jikinsa,

"Me zanyi da wannan kazamin bakin naka wanda may be ma ko brush baya samu.." Maganar data fada masa rannan ta dawo cikin brain dinshi tafara circling,

Bai san lokacin da ya zubar da kayan hannunshi ba ya kankameta ajikinshi ya fara luluben bakinta acikin duhun,

"Wai meye haka....." Ji tayi yakaiwa bakinta cafka,

"Yau na shiga uku na hadu da dan iska.." Tafadi acikin mind dinta,

"Yau kuwa zaki gane nidin dan iskane kamar yanda kika kirani da sunan..."

Kokarin kwatar kanta da bakinta take yi amma ta kasa, sawwam kuwa shi ba taba kula kowacce mace yake ba asalima bashida budurwa baima taba yin budurwa ba inba ta kuruciya ba lokacin da yana secondary school ita dinma bai wani damu da itaba, baima san yanda soyayyar take ba sai dai yana gani a finafinai kasancewar mayen kallon american films ne, shi dai kawai yana ganin suna hugging da kissing da sunan soyayya amma bai san abinda suke jiba,

Tun ummulkhair na kokarin kwatar kanta harta hakura ta kyaleshi amma sai tutture shi take yi,

"Dan iska kawai dama abinda yake ta so kenan rannan bai samuba shiyasa ya biyoni yau" haka taketa fada acikin zuciyarta,

Gaba daya kamshin jikinshi ya gama baibaye kowanne sassa nata, haka shi dinma kamshin jikinta duk ya cika kofofin hancinshi wannan dalilin ne yasashi kasa sakinta,

Dakyar ya iya sakinta yana maida numfashi ahankali, ai yana sakinta kairi tace kafa mai naci ban bakiba wanda har saida abin ya bashi dariya,

Sunkuyawa yayi ya tsince kayanshi dake yashe awurin ya nufi motarshi ya shiga yana murmushi,

Ummulkhair na shiga hostel aka kawo wuta, haki take yi sosai kamar wacce ta shekara tana gudu,

"Yau na shiga uku..ashe sawwam dan iskane ashe?" Ta fada har lokacin jikinta rawa yake yi,

Kirrrr sakon masoyinta ya shigo,

  _i love you dear_

Ko amsa bata mayar mishi ba saboda yau sawwam ya sata acikin wani hali, dakyar ta samu ta iya yin bacci domin da zarar ta rufe idonta numfashin sawwam take jiyowa acikin kunnenta lokacin da yake nuna mata halinsa.

   Da safe sukuku ta shirya ta fita misalin karfe 9 domin 9:30 zasu shiga test, tana fita ta hango sawwam atsakiyar abokanshi sunata hira sai dariya suke, kura mata ido yayi yana kallonta yana murmushi, ko wurinda yake bata kalla ba balle ta harareshi, wucesu tayi kanta akasa domin yanzu kuma kunyar hada ido take dashi,

"Yau babu fadanne..?" Abdul yafadi yana dariya,

Shiru sawwam yayi bai bashi amsa ba amma acikin zuciyarshi cewa yake "ai babu wannan maganar tunda jiya na koya mata hankali..".




Ummi Shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment