Monday 20 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 28

*RAMUWAR GAYYA..*💘

_Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

       _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*


28

*K*allonta yake sosai ko kiftawa baya yi yana jiran yaji amsar da zata bashi,

Murmushi tayi itama tana kallonsa,

"Sawwam shine mutumin da ya saukaka min hanyar nemanka domin asali ma shine yabani number wayarka..."

Kallonta ya sake yi cikeda mamaki,

"A ina ya sanni...?" Ya jefa mata wannan tambayar lokaci guda,

"Ni ban san a inda ya sanka ba but yadai cemin ya sanka, shima dan kanone..."

"Three pointer?" Ya tambayeta,

Daga mishi kai tayi alamun ehhhh,

Murmushi ya dan saki kadan yaci gaba da kallonta,

"Ok shi kike son aura kenan? Kinfi son bare akan dan uwanki,haba ummulkhair kiyi tunani mana, itafa rayuwa yanzu naka sai naka, kowacce mace tana kokarin samun wanda zai riketa bisa amana da gaskiya ne..."

Katseshi tayi domin da alama maganganun nashi sun fara kokarin sosa mata zuciyarta,

"Faruk kar muyi haka dakai, tun farko na fada maka sawwam nake so tsakanina dakai babu wata maganar soyayya sai dai ta zumunci so dan Allah kar kayi abinda zai jawo rashin fahimtar juna a tsakaninmu..."

Tana kaiwa nan ta mike zata wuce, cikin sauri faruk ya riko hannunta, fisgewa tayi tareda ja baya,

"Karka kara rike min hannu, ina ganin mutumcinka karka bari girmanka ya fadi a idona..."

Mikewa tsaye yayi yana kallonta,

"Alright, zan barki amma kafin nabarki din ya kamata ki zauna kiyi tunani sannan kiyi nazari.."

Juyawa yayi ya fita daga falon, duk sai taji ranta ya baci hankalinta ya tashi, juyawa tayi itama ta shiga dakinta ta zauna a bakin katifarta tana tunanin wannan al'amari na faruk,

Karar wayarta ne yadawo da ita cikin hayyacinta, dagawa tayi babu yabo babu fallasa atattare da ita saboda yanayin bacin rai wanda ta samu kanta,

"Sawwam..." Shine kawai abinda ta fada,

"My lonely ya akayi?" Sawwam yace da ita daga daya bangaren,

"Lafiya lau,yakake?"

Murmushi yayi kafin ya bata amsa,

"Ina cikin wani hali na rashinki akusa dani, ina ji kamar inama zan iya dawo da shekaran jiya tazama yau da nayi hakan domin ban gaji da kallonki akusa dani ba"

Duk da cewar ranta abace yake amma sai da tayi murmushi,

"Nikuma da za abani dama domin indawo da lokacin da nake so yafi burgeni to da kasan wanne lokaci zan dawo dashi?"

"No,fada min wanne" yabata amsa,

"Lokacin da muke fada a school, lokacin da muke soyayya a boye babu wanda yasani"

Murmushi yayi mai dan sauti,

"Dama ni soyayyarki bata buya ba agareni domin har friends dina sun gane ina sonki saboda duk Wanda yayi min maganarki haushinshi nake ji, lokacin da Abdul yace yana sonki ji nayi kamar na naushe shi wallahi..."

Dariya kairi tasa harda kwarewa, "to kuma da ace nima na amince da ya za kayi?"

"Ina jin da mutuwa zanyi my lonely, ranar fa wallahi kasa bacci nayi, ki godewa Allah domin ya jarrabeni da ciwon sonki mai tsanani, bazan iya jure rashinki ba"

"Nima haka sahibi, nima ina sonka and i can't do without you, you are my life..."

"Dagaske kike Kodai kawai fada kika yi?"

"Dagaske nake mana" tafada bayan ta zame ta kwanta asaman katifarta,

"Nabawa mami da dad labarin irin karramawar da kika yimin, suma sunji dadi fiyeda yadda naji naganin na samu karbuwa sosai, amma zan baki hakurin abu guda daya"

"Hakurin me kuma?" Tayi saurin tambayarsa,

"Hakurin sai na gama school sannan zamuyi aure ina fata lokacin bai yimiki nisa dayawa ba..."

Murmushi tayi bayan ta sauke ajiyar zuciya,

"Indai akan wannan ne karka damu domin ba kai ya cancanta kabani hakuri ba nice nafi cacanta da in baka hakuri domin kafini dokin ganin ranar"

"Babu komai naji na yarda idanma nayi dokin ai nagirma ne shiyasa"

"To shikenan, kaji Anfara kiran salla bari nabarka haka"

"Kajita sai kace yi zatayi, kibari nida zanyi in fadi haka bake ba"

Shiru tayi masa ta kyaleshi bata bashi amsa ba,

"Bari naje salla nadawo, idan nadawo zan kiraki, i love you.."

"I love you too" ta furta ahankali.

Katse wayar tayi ta shiga duniyar tunani.

  Haka soyayyarsu taci gaba da gudana har aka fara shirye shiryen komawa makaranta,

Iyayenta sun hada mata kaya masu yawan gaske wanda zatayi amfani dasu a makaranta batare data nemi wani abu ta rasa ba,

Ranar lahadi ta shirya ta koma makaranta tana cike da kewar gida da kewar iyayenta, wannan tafiyar ma kamar ta farko da kuka ta tafi.

Karfe 3 na yamma ta sauka atasha,tana sauka sawwam na karasowa tashar,

Ganinta tana kuka abin yabashi dariya, abayan boot din motarshi ya sassaka mata kayanta tashiga suka tafi,

Tsokanarta yafara yi yana driving,

"Shiyasa ni ban san yanda zanyi ba ranar da aka kawoki domin nasan kwana zamuyi kina yimin kuka"

Hawayenta ta share idonta jajur ta kalleshi,

"Dole kace haka mana tunda kai kana kusa da mami da dad duk lokacin da ka so zakaje ka gansu nikuwa fa"

"Kema ai zaki ga su mama duk lokacin da kike so zan kaiki"

"Nidai ban yarda ba" tafada cikin shagwaba,

"Haba baby na, yi shiru kinji" yace da ita ganin har lokacin bata daina kuka ba,

Packing yayi agefen titi ya juya yana kallonta, hannuta ya kamo yana kallon fuskarta,

"My lonely yi shiru kinji, daina kuka dan Allah, ko kina so nima nayi kukan?"

Kai ta girgiza masa tana share hawayen fuskarta,

"To yi hakuri kiyi shiru, kina so nakaiki wurin mami yanzu?"

"Ehhh, amma kafara kaini naje na ajiye kayana a hostel"

"To sahibata yanda kikace ai haka za ayi"

Yace da ita cikeda tsokana, murmushi tayi ta zare hannunta daga cikin nashi cikin jin kunya,

Makaranta ya kaita ya fiffito mata da kayanta, daya bayan daya ta rinka dauka tana shigar dasu cikin hostel har ta kammala kwashewa,

Fitowa tayi ta iskeshi zaune acikin motarshi yana jiranta, ajikin motar ta jingina tana kallonsa, ita sai yanzu ma tasamu damar kallon irin shigar da yayi,

Bakar riga yasaka budy hug ajiki an rubuta you, da brown din wando,

"Kayi kyau" tace dashi tana kallonshi,

"Kema kinyi kyau gashi kinyi kumatu zo ki fada min me mama take baki kika yi kumatu haka?" Yafadi hakan yana kokarin fitowa daga cikin motar,ganin ya miko hannu zai kamo kumatunta yasata guduwa tana dariya,

"Kika gudu ko? Idan kika yi nauyi da yawa nakasa dagaki shikenan"

"Da taya zaka dagani? Sai kace wata baby?" Tace dashi tana dariya,

"Dagawa ma tamkar baby" yabata amsa bayan ya dora hannuwanshi asaman motar yana kallonta,

"Nafasa zuwa gidan mami sai gobe, yanzu zuwa zanyi nawanke dakina na shirya kayana"

"Shikenan to Allah ya kaimu, bari nabarki kije kiyi aikinki"

"Anjima da daddare fa kadawo, amma kataho min da shawarma ko abin dadi"

"To sai nadawo" yace da ita ya shiga cikin motarshi ya tafi, itama hostel ta koma ta shasshare dakinta tawanke ta shirya kayanta danma tayi Sa,a hostel din an daddawo babu laifi.

  Bayan sallar magrib sawwam ya dawo ya kirata, fitowarta daga wanka kenan, daya daga cikin dogayen rigunan da ya kawo mata tasaka tafesa turarruka masu kamshi ta fita,

Yana zaune yana jin music ta karasa,

Bangaren mai zaman banza ta bude ta shiga ta zauna tana kallonsa, shi dinma ya kara sake sabon wanka ya sauya kaya daga na dazu zuwa wasu kalar daban sai kamshi yake, har azuciyarta taji sawwam yayi mata dari bisa dari domin yana da tsananin tsafta da tsantseni gashi komai nashi sai kamshi yake,

Kallonta yayi yana leken kafarta, wayarshi ya kunna yahaska light yafara kokarin hasketa, cikin sauri tafara yunkurin kwace wayar,

"Wallahi ni kunshin kawai zanga ba wani abu ba"

Tabe baki tayi "ai da yake nasan kasaba saka min idone shiyasa"

"To yau ba sa idon zanyi ba.." Yafada yana murmushi, hannunshi ya mika sit din baya ya dauko wata leda mai kyalkyali ya mika mata,

"Ga abincin nakawo miki"

Hannu ta mika zata karba sai yafasa bata yana murmushi,

"Idan bazaka bani ba in tafi..."

Murmushi ya kara saki batare da yace da ita komai ba...

aishaummi.blogspot.com

Ummi shatu🏻

Pherty xarah

No comments:

Post a Comment