Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 22

*RAMUWAR GAYYA..*💘

_Love story 50,50_


_*UMMI A'ISHA*_

       _with_

_*PHERTYMERH XARAH*_


  22


Matsawa daga inda yake tayi tana harararsa,

"Wallahi zaka san ni ka yiwa haka akanma ka samu na daukeka a hoto da wayata shine zaka wani tsaya kana yimin....." Shiru tayi bata karasa ba ta dauke kanta,

"Anyi miki din danme zaki daukeni ahoton, nasaki ne...?" Sawwam yace da ita shima yana harararta,

Mikashi wayarta tayi,

"Ungo karbi ka goge, ban son kayan tashin hankali..." Ta fada bayan ta murtuke fuskarta, shima kunu yasha ya karbi wayar sai kuma ya ajiye mata ya zauna akusa da ita,

"Haba kairu yanmata, yi murmushi muga, ki saki fuskarki mana, yi dariya nagani..."

"Malam nifa babu ruwana dakai dan Allah karka kara yimin magana.."

"Haka kikace?" Yafada yana kallon kafarta, lura da tayi da irin kallon kurullar da yake yiwa kafartata ne yasata janye kafar tata ta baza hijabinta ta lullube kafar,

Mikewa yayi batare da ya kara yimata magana ba ya koma can nesa da ita ya bude handout dinshi ya fara karantawa,kirrr yaji wayarshi ta soma kara kamar bazai dauka ba amma ganin Rukayya ce ke kiranshi yasashi dagawa,

"Hello baby, yakike...?", cikin sauri ummulkhair ta daga kai ta kalleshi,

"Baby ina school karatu nake yi, kina son ganina ne? To da yaushe kike son ganin nawa, no kibari kawai sai anjima bayan sallar magrib sai nazo ki ganni, hakan yayi miki? Ok thank you baby, bye bye"

Ba ummulkhair ba hatta Rukayya sai da tayi mamakin jin wai sawwam ne yau yake amsa mata waya haka babu bata rai babu tsaki balle rashin yin magana, lallai yau ta taki Sa,a,

Ummulkhair har lokacin kallonshi take tana mamakin dama haka ya iya soyayya, kuma shine dan wulakanci ma agabanta zaiyi wayar,

"Nima bari na kira sahibina yaji..." Tafadi acikin zuciyarta amma koda ta kira sai taji wayar akashe, mikewa tayi cikeda takaici ta tattara takardunta zata tafi,

Cikin sauri yasha gabanta,

"Ina zakije? Wallahi yau bakiyi wani kwakkwaran karatu ba dan haka babu inda zakije sai kin sake kara awa biyu..."

Bata rai tayi ta kalleshi, "to ina ruwanka ko tare aka turo mu daga gida? Idanma naci zero ai b damuwarka bace..."

"Ehhh ba aturo mu tare ba amma yanzu muna zama tare so dole idan naga zakiyi ba daidai ba na hanaki..."

Sanin bazai barta ta tafiba yasata komawa ta zauna tana harararsa, shima wurinda yake zaune ya koma ya zauna yana karatu yana kallonta ta wani bata rai ko kallonshi taki yi ita ala dole tayi fushi saboda taji yana waya da budurwarshi to amma tambayar anan itace meye damuwarta da wayar da yayi da budurwarsa?

Wannan itace amsar data kasa bawa kanta,

Jin an fara kiran sallar la,asar ya sanya sawwam mikewa yana kallonta,

"Bari naje salla nadawo, dan Allah kije hostel ki dafa min indomie tunda ke nasan ba zakiyi salla ba..."

Wata harara ta watsa masa, "ehhh saboda ga kafura ba.."

"Am sorry, take it easy ni ba haka nake nufi ba.."

"To koma dai me kake nufi ni babu abinda zan dafo maka saboda babana ni kadai ya hadowa kaya batare da wani ba..."

Murmushi yayi ya tsaya yana kallonta, "malam daina kallona..." Tace dashi tana ciro takalmin kafarta, ganin bai daina kallonta ba yasata jefa masa abin tsautsayi sai akan fuskarshi, sunkuyawa kawai taga yayi ya dafe gwiwowinsa, kamar abin almara sai kawai taga jini yana fita daga hancinsa,

Dagudu ta tashi taje wurinsa,

"Sawwam habo kakeyi, na shiga uku...."

Jakarta ta dauka ta fita da sauri zuwa capteria, cikin rudewa ta debo ruwa masu sanyin gaske harda gudan kankara aciki, kudin kawai ta mikawa mai shagon ba tare da tasan ko nawa bane,

Kamar zata kifa dan sauri dahaka ta koma wurin sawwam har lokacin yana nan ayanda ta tafi tabarshi jinin ya taru awurin da yake diga,

Ruwan sanyin tafara kwarara masa akansa kwalla tana fita daga idonta,

"Sannu sawwam, sannu..." Shine kawai abinda bakinta keta furtawa, shi kuwa sawwam murmushi yake jin duk tabi ta rude tamkar wani wanda ya mutu,

Kansa ya daga sama ya zaro handkerchief daga aljihunsa ya goge fuskarsa, juyowar da zaiyi yaganta tana kuka,

"Meye nayin kuka kuma? Ashe kin damu dani amma shine harda yimin fushi yanzu yanzun nan, sorry stop crying..." Yace da ita yana murmushi,

"Dan Allah kayi hakuri wlh bada sanina bane..."

Murmushi ya sake yi ya zaro glass dinshi yasaka ya kura mata ido wanda har ita ajikinta saida ta fahimci wayo yayi mata kawai yana kare mata kallo,

"Sawwam wallahi ban yarda dakai ba dama nadade ina zargin cewa kana saka glass dinnan ne saboda kayita kallon mata...."

Ayanda tayi maganar sai abin ya bashi dariya, "sharri zaki yimin kuma?"

Zare glass din yayi ya mika mata, "karbi na baki..."

Karba tayi tasaka a fuskarta itama tana kallonsa,

"Kinga naje salla, amma ki fito min da abinci saboda yunwa nake ji...."

"To mai glass" tafada cikin tsokana tana dariya, shima dariyar ya fashe da ita ya wuce, kayanta da nashi ta tattara ta nufi hostel tana zuwa tayi wanka ta shirya tasake wasu kayan bayan tasha turare, indomie ta dafa musu taci sannan ta zubawa sawwam a karamin flask ta fita,

A inda suka saba karatu ta sameshi yana waya d abokanshi nan ta ajiye masa abincin da sauran kayan karatunshi takoma can baya dashi ta zauna,

Suna nan tare suna karatu har mangaruba tayi jin yanata cewa sauri yake yatafi gida saboda akwai wurinda zaije yasata tsarguwa da ko wurin wannan budurwar tashi zaije hakane ma yasata shirya masa plan ta yanda bazai tafi da wuri ba,

"Sawwam gaskiya bazaka tafiba sai ka koya min wannan calculation din gashi ko daya ban iyaba.."

Jin tace haka yasashi fasa tafiya, motarshi yaje ya dauko musu darduma da laptop dinshi ya kawo wurinda take,

Zama sukayi agabanta ya bude laptop din amma cikin sauri ya kare jikin screen din wai gudun kada taga hoton budurwarshi dake jiki,

"Wai me kaketa bobboyewa ne?? Idan bazaka koya min ba ka fada min natafi" tafada cikin tamke fuska,

"Hoton budurwata ne bana son kiga shiyasa na kare.." Ya bata amsa yana murmushi,

"Allah ya baka hakuri dadinta ma nidai ba mayya bace bare ace zan cinyeta kuma ni ba barauniya bace balle ace zan sace..."

"Ke barauniya ce mana, ko kin manta lokacin da aka samu waya a cikin jakarki sannan kuma nima ai kin taba satar min abuna...."

Katon text book din kusa dashi ta dauka takai masa duka tana cewa,

"Dama ka taba daura min sata yanzu ka fada min mai na satar maka..."

Littafin ya rike yana dariya harda kwarewa,

"Amma dai kinsan ba karya nayi miki ba ko...."

"Malam ban son ji ya isheni kawai, mai kallon mata kawai, kasa glass kayita kallon mata..."

"Dama maganar bata wuceba..." Yafada yana murmushi,

"Ehhhh" tabashi amsa, ahaka suka shantake batare da sunyi karatunba har 9 tayi sannan ta kyaleshi ya tafi domin ta tabbatar lokacin gida kawai zai nufa bazai iya zuwa wani wuriba.

Koda ya koma gidama bayan yayi wanka ya kwanta kiranta yayi awaya domin yabar mata laptop dinshi amma duk wurin da ya ajiye hotuna yasa security ta yanda bazata iya budewa ba,

"Kar ki kuskura kiyi min bincike a laptop dina..." Yace da ita cikin sigar jan fada,

"Ai wallahi baka da gaskiya tunda har kaki barin wurin hotuna abude..."

Dariya yayi sannan ya bata amsa, "gaskiyarce ta kawo haka akwai abinda bana son kigani ne..."

"Hmmm sawwam Kodai kaima kana kallon...." Shiru tayi ta kasa karasawa tana saurarensa,

"Wallahi karki yimin mummunan zato, ai nabar miki videos abude kiduba ki gani idan ina kallon shirme zaki gane idanma bana kallo zaki gane, shima hotunan akwai na budurwa tane ban son kigani.."

Tab'e baki tayi "Ku kuka sani dai, malam sai da safe karatu ni zanyi..." Ko jiran abinda zaice batayi ba ta katse wayar, shima ajiye tashi wayar yayi yana murmushi sakamakon tunota da yayi,

Ko Minti 20 ba ayiba ta kirashi,

"Gobe zaka kaini gyaran gashi..."

"Sai na kaiku tare keda budurwata itama tace zataje..."

"Toni nafasa..." Tabashi amsa,

"Yi hakuri ita nafasa kaita ke zan kai..."

Murmushi ta saki wanda har saida ya doki dodon kunnenshi....

aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment