Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 21

*RAMUWAR GAYYA*.......💘


_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

             &

*Ummy Aysher*

     21

Da dare suka sami kebewa da mahaifinta, ta bashi lbrn komai da yanda abin yake xuwa a ynxu kan abinda ya turata,

Sosai yaji daďi ganin tayi kusa biya masa buqatarsa, ya kusa cimma burinsa akan qudirin daya ďauka a rayuwarsa,

Sai ya shiga sanya mata albarka tare da qara nuna mata yanda abin xai kasance, tana xaune tana saurarensa cikin ladabi har yagama faďa mata,

Wannan Karon taji daďin gida sosai sai nan nan ake da Ita tun daga iyayenta har yayyunta bama kamar mahaifinta, satin ta biyu ta soma shirye shiryen komawa Skul saboda sunyi waya da Alawiyya ta sanar da Ita exam is at the corner.....

Sahibinta Kuwa akai akai suna Kan charting, suna nunawa juna yanda sukayi tsananin missing ďin juna duk da ba wai haďuwa suke ba,

Sawwam Kuma 2days baiga mutuniyar ba sai da yaji lbr daga Alawiyya wai yaje gida tabe bakinsa kawai yayi amma har cikin ransa baiji daďi ba saboda ko sallama basuyi ba,

Tun daga lokacin shima bai qara shiga Skul ba baiga amfanin xuwansa mutuniyarsa bata ciki ba ganinta kawai farinciki yake sanyashi ballantana idan suna tare suna faďa yana kallon bakinta,

Su Suhaib sun xata bai lfy ne sukaje dubasa a gida ko lfy ya daina xuwa Skul,

'haka kawai shine amsar da ya basu,

Kyalesa kawai sukayi cos sun san komai Abdul ya basu lbr, abin nasu mamaki yake basu shida khairi suna son juna sunqi su fito su nunawa juna sai dai suyita  noqe noqe suna basarwa suna harare hararen juna....

Sanda ta dawo ta shiga Skul itama bataga mutumin taba batasan yayiwa Skul ďin kaura ba sai ranar da ta dawo, ta tambayi Abdul ina sawwam

'yana gida tunda kikaje gida ya daina fitowa shima,

Murmushi tayi Wanda batasan dalilin yinsa ba,

'ka kirashi kace yaxo gani nadawo...

Abdul ya kirasa yace Fitowarsa wanka kenan amma gashi xuwa,

Fiye da minti talatin Kuwa sai ga motarsa ta shigo, tun cikin glass ya tsinkayota harda sauke ajiyar xuciya dai dai lokacin da yayi parking motarsa ya fito fuskarsa a ďaure sai wani basarwa yake yaqi su haďa ido da ita ya nufi inda Abdul,

Dariya ta soma yi tana kallonsa kafin ta maida kallonta ga Abdul,

'Ana so ana kai kasuwa sai nayi mgn ace qaryane, saboda ni mutum ko skul ya daina shigowa Ashe dai ni ďin ta dabance,

Ya xare madubin idonsa yana kallonta yana kallon Abdul ya nuna ta da yatsa,

'baabaa ita wannan da wa take, kagayamata inda ni take nafi qarfinta bnga abin so a tare da Ita ba,  bata isa ta hanani shigowa Skul ba sai rashin lfy....

'gsky ne naga kayi rama sosai ta faďa tana murmushi,

Abdul dariya kawai yayi yasa kai ya fice, ta matso kusa garesa tana faďin,

'daga ni sai kaine gayamin ynda kayi missing ďina,

'yace ke kinyi missing ďina ne?

'tace A'ah

'yace tor nima banyi ba,

'tace tor nayi

'yace nifa banyi ba, bansan dalilin da xaisa nayi kewarki ba, ta tabe bakinta kawai,

'Ina tsaraba, kinyi missing ďina Kuma shine baki siyamin komai ba,

'ni banyi missing ďin ka Waďanda nayi missing sunayiwa tsaraba,

Ya tabe bakinsa alamar ko a jikinsa ya buďe motarsa ya ďauko wata baqar leda ya miqa mata,

'ki karba inkinje xaki gani

da murmushi a fuskarta ta Karbi kayan, ta tabe bakinta batare da tayi godiya ba tayi masa wani kallo ta fice kawai.

Kallo ya bita da shi qasan xuciyarsa wani irin farin ciki yake ji kasancewarsa tare da khairi yau ba faďa,

Yanda yake ji kamar sun jima tare kamar su masoyane....

Itama khairi she don't know why she feels happy today, ita kanta tana jin wani abu game da shi sai faman murmushi takeyi ita kaďai a ďaki ta xube kayan tana kallo exam success ne aciki har, wasu Kuma cards masu ďauke da test na love, ga biros masu kyau da tsada xasu kai goma, pencils, cleaner, sharpener, calculator da sauransu,

Ga wasu irin turarukka masu qamshi da tsada, harda sweet da chocolate, kaya gasu nan birjik sai kallo take tana mamaki,

Tana xaune taga saqon masoyinta,

  _My most brilliant achievement was my ability to be able to persuade my wife to marry me, will you marry me?_

Tayi shiru tana nanata karanta text ďin, how will she accepts to marry him, mutumin da basu taba xaunawa sun fahimci juna ba, batasan halayensa ba, sau ďaya rak ta taba ganinsa Kuma ya wulaqantata kamar baisan da Ita ba,

Ta tabe bakinta tana Mgnr xucci, if that is the case yaxo su fahimci juna, baxata gujesa ba mutumin dake sonka shine masoyinka a duniya, sai ta tura masa,

   _idan ba mun xauna mun fahimci juna ba, I will not marry you cos bansan halayanka ba_,

Tayi matuqar mamakin reply ďin sa har xuciyarta na bugawa,

  _kinfi kowa sanin halina, kamar yanda xn iya bada labarinki a jarida kema nasan xaki iya bada labarina a duniya, wace irin fahimta ce tsakanin mu bayan wacce mukayi a baya,_

Tayi Saurin kashe Wayar batare da ta tura masa reply ba, whatsapp ta hau cikin xaquwa tana so ta duba grups ďin taurarinta biyu ko an turo novels ďin da take matuqar so a yanxu, sabuwar number ta gani tayi mata text,

     _ina son ki khairi, kibani dama na nuna miki kalar kaunar dana ke maki._

Shi Kuma Wannan Waye ta faďa cikin tsananin mamaki, profile ďin sa ta duba cos taga photo akai, kafin yakai ga budewa tuni an cnxa dp xuwa wata jar flower mai ďauke da tambarin love,bataga ko Waye ba amma taji haushi sosai....

*

Sawwam Kuwa har ynxu pad din na ajiye a ďakinsa, idan ya kalleta xai tuna da khairi sai yayi dariya kawai ya girgixa kansa, shi kaďai yasan nufinsa na ajiye pad ďin......

Tun daga ranar sai suka xama friends ba faďa tsakaninsu sai dai tsokanar juna, olways xaka gansu tare cikin Skul suna yawo, yadaina xama dasu Abdul itama ta daina xama da Alawiyya,

Abincima tare suke xuwa suci, wani sa'in Kuma ita xatayi masa girki ta kawo masa yaci, har lokacin ta kasa yarda tana sonsa illah ta ďauke sa a matsayin friend ďin ta shi Kuma a xatonsa ta fara sonshi ne, har cikin gari xata bisa yaje yayi yawo da Ita su dawo,

Skul ďin kowa yasansu tare a ynxu, haka Mami tasan da xaman khairi a ynxu duk da bata taba ganinta ba amma tana adduar Allah ya sa ta gari ce. illah ta ďauke sa a matsayin friend ďin ta shi Kuma a xatonsa ta fara sonshi ne, har cikin gari xata bisa yaje yayi yawo da Ita su dawo,

Skul ďin kowa yasansu tare a ynxu, haka Mami tasan da xaman khairi a ynxu duk da bata taba ganinta ba amma tana adduar Allah ya sa ta gari ce.

Karatun exam ma tare sukeyi, da dare xai shigo da sunan karatu xasu yi idan sun haďu suyita faďa, in Kaga sunyi karatun nutsuwa to basu tare amma idan suna tare ba karatu sai faďa kowa da handout ďinsa a hannusa idan ya bata haushi tayi ta dukansa da Ita yana dariya ko ajikinsa,

Yau ma Faďan suke, kowane ya ďauki xafi,

'karki qaramin magana,
'kaima Karka qaramin magana,

Ya ďauki handout ďinsa ya koma gefe yana karatu ransa a bace ta bisa da kallo tana dariya kafin ta ciro wayarta tana daukarsa pic, sai ya qara tasowa yana faďin mugani yayi kyau,

'kace karna qara ma mgn ina ruwanka dani,

'ke meyasa xaki daukeni pic..... nan suka ďauki wata gardama ( Skul life is d best😂)




*Pherty xarah*

       &

*Ummy shatu*

My wattpad Phertymerh1

No comments:

Post a Comment