Monday 20 March 2017

RAMUWAR GAYYA..30

*RAMUWAR GAYYA...*💘


  _Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

          _With_
_*PHERTYMERH XARAH*_

30

  *K*arkatar da kanshi yayi yana kallonta sannan kuma yana yin tuki,

"Ya kikayi shiru? Ko nadameki da surutu ne?"

Juyowa tayi ta kalleshi tana murmushi,

"A'a ba damuna kayi ba kawai dai ina tunanin irin yanda rayuwar aurenmu zata kasance ne bayan munyi aure..."

Burki ya taka sakamakon tsayar dasu da danja tayi,

"Yakamata ki tuna wannan ranar yanda ya kamata domin ki shirya mata, insha Allah zamuyi rayuwa mai dadi da burgewa musamman ma idan kika haifo yan tagwaye a haihuwarki ta farko"

Gefen mayafinta tasa ta kare fuskarta tana murmushi,

"Allah sawwam baka jin kunyata ko kadan, samari suna jin kunyar yan matansu amma kai banda kai..."

"Kunya? Gaskiya nidai ko zanji kunyar wasu to wallahi banda ke"

Murmushi tayi ta dan juya tana kallonsa lokaci daya kuma ta kawar da kanta,

Ganin ya dauki wani titin nadaban bana BUK ba yasata saurin kallonshi,

"Sahibi ina zamuje?" Ta tambayeshi bayan ta kafeshi da ido,

Kallonta yayi ya dauke idonsa ya dora bisa titi,

"Zanje na sayar da ke ne, kin san business dina kenan"

Murmushi tayi ta kalli window "woww ashe dan yankan kai zan aura"

"Ba dan yankan kai ba ne, mai sayar da kayuwan mutane ne" yabata amsa yana murmushi,itama murmushin take yi tana kallon yanayin garin domin bata taba doguwar tafiya hakaba iyakacinta cikin makaranta sai ko wajen makarantar in zataje siyayya ko saloon ko kuma gidansu alawiyya,

Wurin wasan yara ya kaita wato children parck,

"Wowww" tafada tana murmushi domin wurin ya hadu sosai gashi ba iya yara bane harda manya samari da yanmata masoya ko wadanne sai guje gujensu suke yi cikin so da kaunar juna,

Wurin wani lilo yajata suka nufa, gefen wurin ruwane yake kwaranya yana wucewa,

"Wowww sahibi kamar kasan ina son irin wadannan wuraren,

Wowww bari narigaka hawa lilon" tafadi bayan ta wuceshi tana murmushi, lilo taje ta hau tana kallon sauran mutanen dake harkokin gabansu wasu ma'aurata ne wasu kuma saurayi da budurwa ne,

Ji tayi an wullata sama da karfi,bata zataba bata nufaba,

"Woohhhhhhhhh, wayyo sawwam zan fad'o...." Tafada arude, ganin ta tsorata yasashi rike lilon tana ganin haka bata san sa'ilin da ta kamkameshi ba tana kallonsa,

"Ke matsoraciyace my lonely, idan bakya so sauko karki fado kiyi min asara"

"Karka kara turani dan Allah sawwam"

Murmushi yayi ya hau daya lilon na kusa da ita yana tura kansa ahankali yana kallonta,

"Ki rage tsoro khairi, ban san haka kike da tsoro ba sai yau"

Langabe kanta tayi tana kallonsa "ba kaine ka turani da karfi ba, ai laifinka ne kaine ka tsorata ni"

"To am sorry" yace da ita bayan yasaka dukkan hannuwansa ya rike kunnuwansa,

Kallonsa ta tsaya yi batare data bashi amsa ba, yayi mata kyau sosai yau dinnan domin blue din t shirt yasa mai gajeren hannu da bakin trouser, hatta takalmin kafarshi blue ne mai madauri,

Ganin ta zuba masa ido yasashi murza mata yan yatsunshi a saitin fuskarta,

"Tunanin me kike yi dear?" Ya tambayeta yana shillawa sama akan lilon,

"Tunaninka" tabashi amsa bayan ta dauke idonta daga kansa,

"Tunanina bayan muna tare dake? Kidai fadi gaskiya"

Murmushi tayi ta kalleshi,

"Haba sawwam ka yarda dani, akowanne lokaci cikin tunaninka nake ko muna tare ko sabanin haka"

Murmushi yayi cike da jin dadi, ahankali ya dora hannunshi akan nata, ganin haka yasata dabarar zarewa ta sauka daga kan lilon tana cewa,

"Bari kaima naturaka kaji irin yanda naji dazu"

Turashi tayi da karfi tayi saurin matsawa, nan yaci gaba da lilawarsa babu alamun tsoro atare dashi,

Sun jima awurin bayan sun hahhau kayan wasan dake harabar wurin,

Fitowa suka yi ya nufi makaranta da ita,

"Sahibi nagode madalla da wannan fitar tayau, sai yaushe zaka sake kaimu?"

"Duk lokacin da kika shirya" yabata amsa ya kallonta,

"To shikenan zan sake shiryawa sai muje"

"Yakamata kam"

Yabata amsa fuskarsa dauke da murmushi,

Makaranta ya shigar da ita nan dinma kafin ya tafi sai da ya tsaya suka sake wata hirar sannan yatafi,dukkaninsu suna dauke da kewar juna kamar kada su rabu.

  Al'amura sunci gaba da gudana,sun fara lectures sosai duk dai da har yanzu sch din bata dawo normal ba, alawiyya ma ta dawo domin harta fara shigowa lectures,

Kullum sawwam da ummulkhairi suna tare sai kace wasu yan biyu lectures ne kawai ke rabasu, yau kam wuni sukayi ma tare suna hira kasancewar yau basuyi lecture ko daya ba,

"My lonely bari natafi gida bacci nakeji wallahi" yace da ita yana yin hamma,

"Allah bana son katafi, dan Allah ka kwanta anan kayi"

Murmushi yayi ya kalli wurin "ai babu pillow"

"Sai inje hostel in dauko maka"

Kafada ya makale kamar wani karamin yaro, "sai dai inyi pillow din da kafarki"

"Ban isaba" tabashi amsa bayan ta tashi tsaye, bakin glass dinshi yasaka yana kallonta,

"Zaki isa dinne yarinya bari lokaci yayi wallahi bazan daga miki kafaba duk abinda bakiyi ba yanzu sai kinyisu lokacin"

"Naji,yanzu dai kaje kayi baccin sai kadawo, i love you,bye bye"

Mikewa yayi yana kallonta ya nufi motarsa, "i love you too, sai nadawo"

Tana tsaye tana kallonsa har yabar wurin, ganin tafiyarsa yasata barin wurin tatafi hostel.

   Aguje ya karasa gida sakamakon baccin da yakeji sosai, ko takan maganar da baba dan tsoho yake yi masa baibi ba ya wuce falon mami, bata ciki amma ya hangota ta labule a dining area tana aiki, akan center carpet din da yake tsakiyar falon ya kwanta bayan yaja pillow akan kujera, yana kwanciya bacci ya daukeshi, ita kanta mami bata san ya shigoba sai da tafito sannan tayi arba dashi yanata shakar bacci,kallonshi tayi cikeda tausayawa domin tunowa da tayi da gagarumin abinda yake shirin faruwa dashi wanda dole zai jawo su rabu dashi ba ason ransu ba.

  Karfe bakwai da rabi khairi na kwance adakinta tana browsing din wani assignment da aka basu wayarta tafara kara, nan taga sunan faruk ajiki, kamar ta shareshi sai kuma ta dauka da sallama,

Cemata yayi yana cikin sch dinsu ya rako wani abokinsa wurin budurwarsa, tafito su dan gaisa, badan tasoba haka ta tashi ta dauki hijab dunta tafita,

Awani dan fili ta sameshi zaune asaman motarshi yana jiranta, fuskarta babu yabo babu fallasa takarasa suka gaisa nan kuma ya shiga soko mata maganar sonta da yake yi har lokacin,

Sunanan tsaye yanata yimata zance tana amsa masa da uhm har sawwam yazo, sam ita bataga zuwansa ba amma shi Faruk din yaganshi ganin haka yasashi yin amfani da wannan damar yayita mata surutu idan tace zata tafi sai yakara kawo wani sabon topic din da haka har 9 tayi suna tsaye, shikuma sawwam yagama cika yayi fam bai taba sanin yana kishin ummulkhairi ba sai yau,

Dakyar tasamu ta yiwa faruk sallama ta wuce, harda wani kaimata kiss faruk yayi lokacin da zata wuce din, saurin gocewa tayi tana dariya domin ita yanzu faruk dariya yake bata,

Tana yin gaba taga sawwam tsaye, "a'a sahibi yaushe kazo?"

Tace masa tana kallonsa, "ban saniba idan ke baki ganni ba ai shi saurayin naki ya ganni"

Murmushi tayi "sawwam Faruk nefa, ko kamanta kaine ma ka bani number wayarshi?"

"Kinga banida lokacin ki yanzu, sai anjima"

Ganin zai shige cikin motarsa yasata saurin riko rigarshi ta baya,

"Dan Allah kayi hakuri"

"Bazanyi ba" yafada batare da ya jiyoba,

Sakinshi tayi tace "shikenan" tajuya tawuce, juyawa yayi yana kallonta cikin bacin rai, wato ma maimakon ta tsaya ta bashi hakuri shine zata tafi? Nan yaji ransa ya sake baci,

Motarshi ya shiga yatafi gida duk zuciyarsa a zafafe, texts yaga ta tutturo masa naban hakuri fiyeda guda Biyar amma har lokacin baiji sanyi acikin zuciyarsa ba.

  Washe gari koda suka hadu a sch dauke kanshi yayi yaki koda kallonta, kusa dashi taje ta tsaya,

"Sahibi dan Allah ka tsaya ka saurareni"

Shiru yayi yana jinta amma har lokacin bai daga idonshi ya kalleta ba.


aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment