Monday 20 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 26

*RAMUWAR GAYYA..*💘

 
_Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

         _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*


  26

*D*ukkaninsu suna dauke da kewar juna tamkar wadanda suka shekara da rabuwa,

Kwance take adakinta tana tunanin sawwam, duk hankalinta yatafi gareshi,

K'irrr taji wayarta na kara nan ta dauka a kasalance tana murmushi ganin sawwam ne,

"Sahibi..." Tafadi cikin siririyar muryarta me kamada ta yara,

"My lonely nayi missing dinki, amma kafin adawo school zanzo bauchi porpusely saboda ke..."

Zaune ta tashi daga kwancen da take,

"Are you serious??"

"Yes dear am serious but sai nadawo daga umarah, next week zamuje umara nida dad dina so idan nadawo zanzo gurinki.."

"Allah yadawo dakai lafiya sahibi, idan kaje dan Allah kayi min addu'a.."

Murmushi yayi yasake makale wayar a kunnenshi,

"Wacce irin addu'a kikeso nayi miki?"

"Kayi min addu'a Allah yasa ba zaka yimin kishiya ba har abada..."

Dariya yafara yi mata har saida yayi mai isarsa sannan yayi magana,

"Wai haka kike da tsoron kishiya? Ko bakiyi addu'a ba dama ni bazan yimiki kishiya ba my lonely..., you are the only one i love, ban taba son wata mace ba sai ke, only you i love,ki daina tada hsnkalinki akan sauran mata domin duk bana ganinsu idan ina tare dake, babu wacce zata hada miji dake indai nine mijin i promise you this..."

Zamanta tagyara ta tankwashe kafafunta tana murmushi,

"Kar kayi min alkawarin da bazaka iya cikawa ba sahibi"

"Wanne alkawarin ne bazan iya cikawa ba? Ni banida ra'ayin mata biyu ke kadai kin isheni rayuwata daga ni sai ke sai 'yan yaranmu"

"Hmm kar dai sai lokacin yayi idan nace maka kayi min alkawari kace kai baka san maganar ba"

"Pls bar wannan maganar muyi wata, yara nawa kike so mu haifa? Tara ko goma?"

Dariya tayi kafin ta bashi amsa, "sai kace haihuwar babu wuya zaka wani ce goma, ai idan nayi biyar ma ka yaba min"

"Biyar? Gaskiya sunyi kadan ina laifin ma takwas" yafadi yana yimata dariya,

"Hmmm sawwam kenan kayi mana addu'a dai akan Allah ya bamu masu albarka"

"Insha Allah zanyi mana wannan addu,ar my lonely before kema kije kiyi da kanki ko?"

"Hmmm" kawai tace bayan tayi murmushi,

"Ina zuwa yunwa nakeji, bari naje wurin mami naci abinci"

"Ai baka son cin abinci sawwam inajin idan munyi aure dura zan runka yimaka.."

"Ehhhh dan Allah ki rinka yimin ina so indai kece zaki bani..."

Daidai lokacin ya isa falon mami tana tsaye a dining area tana shirya table domin tasan dady yana daf da zuwa cin abinci daga office,

"Idan banyi maka dura ba bazaka ciba kenan?" Yajiyo muryarta tana tambayarshi,

"Ehhh mana ni ke nake son ki rinka bani da kanki"

Dagowa mami tayi tana kallonsa daga shi sai boxer da body hug ja, girgiza kai Mami tayi tana murmushi,

"Sawwam baka da kunya ko?" Mami tace dashi tana zuba masa abinci acikin flate,

Kallon abincin yayi ya dan yatsina fuska,

"My lonely kin san wanne irin food zanci yanzu?"

"A'a wanne irine?"

"Sakwara da miyar kifi" yabata amsa bayan yaja kujera ya zauna,

"Ga mami zaku gaisa" tun kafin tayi magana ya mikawa mami wayar yana cewa,

"Mami ga in-law dinki zaku gaisa"

Karbar wayar mami tayi ita kuma ummulkhairi duk kunya ta lullubeta da ace tasan ma zai hadata da mami su gaisa da tun dazu tayi masa sallama,

Dad dinshi ne ya shigo fuskarsa dauke da murmushi, mika masa wayar mami tayi tafara yiwa abbanshi sannu da zuwa,

"Hello my lonely.. My dad done come back" yace da ita cikin rada,

"Wai yanzu da kai agaban mamin kake fada min wannan maganar dan rashin kunya? Ni wallahi kasani naji kunya tunda hakane munyi fada dakai..."

"No my lonely karki yi fushi dani please, am so sorry, ai ba wani abu nafada ba ko?, ko wani abu nace wanda zai saki kiji kunya?"

Mami ce ta yafuto dad da hannu ta nuna mishi sawwam,

"Yaronka fa yakusa ya girma dan ya samo matar aure yanzu ma ya hadani da ita muka gaisa kuma naga alamun yana sonta sosai.." Mami tace da dad ahankali,

Karasawa wurinshi dad yayi yana murmushi gamida dafa kafadarsay,

"Dan gidan dady a ina ka samo matar ne?"

Ummulkhair najin haka tayi saurin katse wayar amma  kuma rayuwar gidansu sawwam ba karamin burgeta yayiba saboda yanda suke tafiyar da rayuwarsu shida iyayenshi tamkar wasu abokai,

Dagowa sawwam yayi yana kallon dad cikeda kunya sai faman sosa keya yake,

"Dad a bauchi ne..."

"To Allah ya sanya alkairi yasa adace" dad yafada tareda jan kujerar kusa da sawwam ya zauna,

"Amin dady amma ai naga ita wannan din tayi masa" mami tace da dad tana zuba mishi abinci,

"Ai shiyasa nace miki dama ki rabu dashi zai nemo da kansa.."

"Ai kuwa dai gashi nan ya nemota kyakkyawar gaske"

Dariya dukkaninsu suka saka banda sawwam wanda yau duk kunyar iyayenshi suka rufeshi alla alla yake yagama cin abincin yaje dakinsa yasake kiran ummulkhair ya fada mata abinda mami tace,

Yana ganin mami da dad sun fita shima ya mike yayi Waje ya nufi dakinshi tun ahanya yake kiranta,

"Sahibi ya akayi?" Ta tambayeshi bayan ta kara wayar a kunnenta,

"Kinji me mami tacewa dad? Wai nazabo kyakkyawar gaske..."

Murmushi tayi, "nima ai nazabi kyakkyawan gaske danma dai danma dai lebenshi ja ne" tafadi cikin tsokana,

"Naji din, kema ai bakida gashi sai munyi aure sannan zan sanmiki..."

"Kaji shi"

"Wai dan Allah baki sani ba? Wallahi muna yin aure gashinki zai fito.."

"Naji to ya isa"

"Shikenan tunda bakya son ji sai anjima" tsinke wayar yayi yana murmushi, itama ummulkhair din murmushin take yi,ajiye wayar tayi tafita zuwa dakin mahaifiyarta.

Zaune ta taradda ita tana ninke kayan kannen ummulkhair wato yayan kanwarta wadanda suka zo mata hutu domin ita ummulkhair ce autar yarta,

Zama ummulkhair tayi akusa da ita tana kallon ta,

"Mama sannu da aiki.."

"Yawwa kairi.." Maman tabata amsa tana mai cigaba da ninke kayan,

"Mama dama dangane da maganar aikin nan da abba yasani ne to yanzu ina daf da kammala masa amma kuma zuciyata tana daf da shiga damuwa, wallahi mama zan iya rasa farin cikina asakamakon wannan abunda yake shirin faruwa.."

Barin ninkin kayan mama tayi ta maida hankalinta duka gaba daya ga ummulkhair,

"Babu komai ummulkhairi, kici gaba da addu,a amma tabbas nadade da sanin cewar mahaifinki yana da wannan burin zan iya cemiki ma tun lokacin da na aureshi nasanshi da wannan burin atattare dashi, amma nasan tunda yana sonki yana son farin cikinki to zai baki abinda kike so, amma shi faruk din ya nuna miki cewar yana sonki ne?"

Girgiza kai ummulkhair tayi, "mama nida banko taba ganinsa ba inba a hoto ba, nidai fatana daya kar abba yadage cewar sai ya hadani aure dashi domin wallahi inada wanda nake so.."

Murmushi mama tayi takama hannunta, "haba autar mama ai babu wanda zaiyi miki auran dole, sai wanda kikeso kika kawo mana zamu aura miki mu kaiki dakin mijinki shikenan kuma munyi sallama dake sai dai kizo mana da yawo kizo Ki gaishe mu gaisuwar samun lada"

Rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta tana dariya nan kuma taji sawwam ya fado mata aranta, "sarkin azarbabi dama abinda yake so kenan"

Tafada acikin zuciyarta domin koda yaushe bashida zance sai dai yace "ranar da aka kawoki gidana"

Murmushi tayi ta debi kayan da mama take ninkewa tayi waje dasu zuwa dakinta ta zauna taci gaba da ninkewa, shikenan hirarsu da mama ta kare sai wani karon kuma.

Kullum suna manne ita da sawwam awaya suna hira har ya tafi umarah anan dinma wayar basu fasa ba sai dai ta dan ragu kasancewar tana son ta bashi dama ya gudanar da ibadarsa yadda ta kamata, satinshi uku suka dawo aranar da ya dawo kwana suka yi suna waya da ita, tsaraba kam akwati guda ya jibgo mata da dogayen riguna masu kyau da turarruka designers sai takalma masu dan karen kyau,

Kwananshi Biyar da dawowa ya shirya ya tafi bauchi ko fada mata baiyi ba kawai dai ya kirata awaya yace yabawa wani sako zai kawo mata,

Shagwaba tasaka masa harda kukanta saboda yace bashine zai zoba abokinsa ne zaizo yabashi tsarabarta ya taho mata da ita,

Tun yana zaton kukan nata nawasane har yagane dagaske take yi domin ga sautinsa nan tana rerashi yana jiyoshi acikin kunnensa, jin kukan nata yake kamar zubar wuta ajikin zuciyarshi, rarrashin duniya yayi mata taki ji daga karshe ma katse wayar tayi bayan ta tura masa da address din gidan nasu domin yace mata ta turo saboda yana son zai turawa abokin nashi,

Tunda ya kusa shiga garin bauchi yaketa kiran wayarta amma akashe murmushi yayi domin yasan fushi tayi shiyasa harda su kashe masa waya,

Karfe 2 narana ya shiga garin, wani hotel kayatacce yaje ya kama ya shiga ya huta yayi wanka ya sake sabon kaya,

Manyan kaya yasaka shadda ash colour harda hula, kasancewar bai saba da dogayen kayaba shiyasa duk yaji ya takura,

Motarshi ya shiga ya nufi kwatancen da tayi masa yana yi yana tambaya har Allah yasa yasamu unguwar bai wani sha wahala ba ya samo gidan nasu, cikin Sa,a lokacin da ya kira wayarta sai yaji ta shiga amma harta katse bata dauka ba nan yasake kira, tana kwance tana kallon wayar amma taki dauka har saida yayi mata miss called biyar ana shidane ta dauka ranta abace,

"My lonely kifita bakonki yazo yana waje zai baki sakon"

Ko amsashi batayi ba ta katse wayar ta dauki hijabinta har kasa pink colour tasaka, kafarta kawai ake iya gani sai hannunta data zira a hannun hijabin,

Fita tayi fuskarta kunshe da damuwa anata ganin sawwam bai damu da ita kamar yadda ta damu dashi ba domin yanzu fa satinsu shida basu ga junaba,

Har ta karasa gaban motar bata daga kanta ta kalli motarba balle tagane wanda ke ciki,

Tunda tafito yake kallonta ko kiftawa bayayi, kwalliyarta simple tayi amma ba karamin burgeshi tayiba,

Ajikin motar ta tsaya tana jiran fitowarsa, ahankali ya bude motar ya fito ya tsaya yana kallonta bayan ya dafe murfin kofar,

Wani sanyin kamshi taji ya doki hancinta irin na sahibinta domin bata manta kamshin nan tun ranar da yayi hugging dinta a makaranta da daddare,

"My lonely fushinne?" Taji muryar sawwam babu zato babu tsammani,

Cikin sauri ta jiyo ta kalleshi nan ta ganshi yayi mutukar kyau yana tsaye yana yi mata murmushi ya dan cije lebenshi na kasa da hakorinshi, tamkar ta rungumeshi haka taji dan tsananin farin ciki,

"Sahibi..." Tafada kwalla ta ciko idonta,

Girgiza mata kai yayi bayan yakai dan yatsanshi ya share kwallar dake shirin zuba a idonta,

"Don't cry dear.... Tun dazu kike yimin asarar hawayenki"

Yace da ita yana murmushi,

"Dama zaka zo? Shine kuma kaki fada min?"

Dan yatsanshi yakai kan lips dinta,

"Shhhhh ba fushi kike yi daniba...."

"Tayaya zanyi fushi da rabin raina..."

"Kinga" yace da ita, idonta ta daga ta kalleshi nan ya kashe mata idonshi daya,

Dagashi har ita murmushi suka saki mai dauke da soyayyar juna.

aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment