Monday 20 March 2017

RAMUWAR GAYYA..24

*RAMUWAR GAYYA..*💘

_Love story 50,50_

  *_UMMI A'ISHA_*

         _With_

_*PHERTYMERH XARAH*_


24

    _Masoyanmu muna ganin tarin sakonninku da kuma rokonku na mu kara yawan page din da mu keyi muku arana, kuyi hakuri hakika munso yin haka amma kuma saboda wani yanayi hakan bazai samuba da fatan zakuyi mana uzuri, muna godiya agareku bisa soyayyarku..._


  *W*ani kayataccen murmushi sawwam ya saki yana mai kallon fuskar ummulkhair,

"Banji kince komai ba, ina so kibani amsar tambayar da nayi miki, kina sona?"

Murmushi tayi ta kalleshi ta daga masa gira,

"Will you marry me?" Ya sake tambayarta, nan dinma girar ta daga masa kafin tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta,

"Kunyata kika fara ji tun yanzu..?" Yace da ita bayan ya zira hannayensa duka cikin wandonshi yana murmushi, babu shakka wannan ranar ta yau itace babbar rana agareshi bashida wacce tafita sai ko ranar aurensa da ummulkhair domin ya dade yana sonta tun ranar da ya fara ganinta,

"To yanzu kuma ya zakayi da auren Rukayya.." Ya jiyo ummulkhair ta jefa masa tambayar da bai shirya ba,

Juyo da kanshi yayi yana kallonta, shiru tayi tana kallon kasa tana jiran taji irin amsar da zai bata amma bataji yayi magana ba koda ta dago idonta ganinshi tayi ya zuba mata ido ko kiftawa bayayi,

"Am magana fa nayi maka ko bakaji bane?" Ta sake tambayarshi,

"Naji..." Yabata amsa yana wasa da agogon azurfar dake daure a hannunshi,

"To baka bani amsa ba ai.."

"To me kikeso nace miki? Nidai a iya sanina ke kadai nake so kamar yadda kike sona domin nasan kin dade dama kina sona amma kin kasa fada min saboda zurfin ciki.."

Murmushi tayi tana mai cigaba da kallonshi,

"Kaima ai kana sona amma baka fada ba sai yau..."

"Nafada mana ai nataba fada miki ke barauniya ce daga haduwa dake ranar farko kika tashi kika yimin gagarumar sata..."

Duka takai mishi, "me nasatar maka?, wallahi kadaina cemin barauniya.."

"Wallahi sai nafada ke barauniya ce.." Yasake maimaitawa yana dariya, takalmin kafarta tafara kokarin cirowa ganin haka yasashi matsawa zai gudu,binshi tayi suka fara zagaye motarshi dake ajiye awurin,

Ganin takasa cimmasa yasata yi masa dabara,

"Washhhh wayyo.." Tafada da karfi gamida tsugunnawa, cikin sauri ya dawo wurinda take,

"My lonely..... Meya sameki.."

Saurin rike rigarshi tayi tana murmushi,

"Gaskiya sahibi nafika wayo wallahi, yanzu kai dagaske yarda kayi wani abu ya sameni? Dama wayo nayi maka ai saboda in kamaka, yanzu fada min ta inda na zama thief, me nasatar maka..?"

"Zuciyata da tunanina duk kika hada kika sace a lokaci guda kinga kuwa ai babu satar da tafi wannan ko?" Yace da ita yana kallon fuskarta,

Shiru tayi ta tsaya tana kallonsa amma har lokacin tana rike da rigarshi,

"Oya sakeni to ko kuma in rungumeki..." Tun kafin ya karasa fadi ta sakeshi takoma jikin motarshi ta tsaya,

Tunani kawai take yi na rabuwar da zasuyi ita dashi gobe gashi tayi mutukar shakuwa dashi, tana tsananin sonshi wanda bata san da hakan ba har sai yanzu,

Gefenta yaje ya tsaya yana kallon wasu saurayi da budurwa dake zance acan gaba dasu kadan,

"My lonely nadade ina bawa Mami labarinki, kullum tana tambayata wai yaushe zan kaiki ku gaisa, gashi kuma zaki tafi gobe.."

Murmushi tayi tagyara wuyan hijabinta,

"Idan nadawo sai muje nagaidata, amma dan Allah kabani amsar tambayata ta dazu, ya zakayi da Rukayya?"

"Nifa Rukayya ba budurwata bace yar kawar mamice, da so suke su hadamu aure amma ni dama tun lokacin nacewa Mami inada wacce nake so, kuma da Mami taga hotonki shikenan sai ta bar maganar domin ke dinma kinfi kwanta mata arai, Allah Mami tana mutukar sonki..."

Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke domin tayi zaton ko dagaske itama Rukayyan budurwarshi ce,

"Hmmmmmm" tafada cikin ajiyar zuciya,

"Menene hmmmm, kina kishine?" Ya tambayeta yana kallon zoben dake makale a babban dan yatsanta,

"Ba dole ba nayi kishi,samun irinka ba abune mai sauki ba shiyasa bana son wata ta kwace min kai.."

"Babu mai kwace miki ni kamar yadda nima bazan bari wani ya kwace min keba, ina mutukar sonki ummulkhairi, ban san yanda zan kwatanta miki ba, i don't know how to interpret it,but i know idan mukayi aure you will comprehend, because zan baki duk wata soyayya da kulawa..."

"Ya isa to.." Tayi saurin katseshi,

"Meye na katseni? Bakya son muyi auren ne?"

"A,a ba haka bane najine kafara kokarin wuce gona da iri.."

"Dannace zan baki kulawa shine zan wuce gona da iri? To wallahi ko kin k'i ko kin so sai nafada kuma sai kinji, zan baki kulawa sosai and kisani babu batun saka wannan hijabin ranar, awaje dai ban hanaki ba amma agida babu wannan maganar..."

Juya masa baya tayi ta kyaleshi bata tanka ba,

"Sannan Allah yasa kar akawo min ke kafarki tana fara dan nasan akwai matsala..."

"Sai kayi kuma" tace dashi bayan ta tura masa keya,

"Nadai ji dama ni idan za asamin ranar bikina farko farko za asamin"

Sai lokacin ta jiyo ta kalleshi,

"Nikuma nawa karshe..."

"Wallahi karya kike, karshe salon kizo min kafarki tana kyalli..."

Zubawa fuskarshi ido tayi tana kallonsa acikin zuciyarta tana mamakin yadda akayi wai sawwam yasan sirrinta haka, to wai tayaya yake ganeta ne?? Ita fa babu wanda yasan wannan sirrin nata sai ita sai mahaliccinta amma shi sawwam gashi yanzu yasani,

"Kasha kuruminka next semester da safa zan rinka yawo wallahi tunda ido kake saka min, eye dropper...."

"You can if you like, nidai tunda nariga da nagane shikenan ba zaki cuceni ba.."

"Kaga malam sai ka gayawa keya dan kwali yabaka ams..." Tun kafin ta karasa ya dungure mata keya,

"Keda ko gashin ma bakida shi..."

"Ehhh naji dai, ahaka kagani kake so..."

"Ai kuwa kisaka aranki ki ajiye komai dadewa zan auro miki kishiya mai gashi har baya..."

Juyowa tayi ta kalleshi, "Sawwam kabari, bana son irin wannan wasan, ban so kabari.."

"Wai kishina kike dan Allah?"

"Nidai nafada maka bana so.."

"To naji, nabari yi hakuri.." Yace da ita yana zaro cingum daga cikin aljihunsa, barewa yayi ya jefa a bakinshi,

"Nima bani..." Ta mika masa hannunta,

Na bakinshi ya ciro ya dora mata atafin hannunta,

"Wallahi babu wani ya kare, shikenan sauranshi..."

"Koma dai menene sai naci.." Tafada tareda jefashi cikin bakinta,

Kallonta ya tsaya yanayi yanda take taunar cingum din cikeda manyance,

"Ka aramin laptop dinka naje nayi kallon films tunda nagama exam"

Motarshi ya bude ya ciro laptop din ya mika mata,

"Gashi, zama ki iya tafiya da ita gida idan kina ra'ayi"

"A,a nidai bance ba, gobe zan baka kayarka kafin na tafi"

"Shikenan duk yanda kikace haka za ayi madam"

"Har nazama madam din?" Ta tambayeshi tana fara idonta,

"Ehh mana" yabata amsa yana duban agogon wayarshi, karfe 9 nadare agogon ya nuna, sam baya son tafiya yabar ummulkhair domin wannan lokacin yana cikin farin ciki,

"Sahibi katafi gida kaje ka huta" tafada bayan ta rungume laptop din a kirjinta,

"Zan tafi ai ko baki koreni ba, ina sone nagama kallon kyakkyawar fuskar matata"

Langabe kanta tayi gefe daya tana murmushi,

"Wannan fuskar kuwa dama ta sawwam ce shi kadai bayan shi duk wanda ya cika kallonta zan tsokale idonshi..."

Shima langabe kan nashi yayi kamar yadda tayi,

"Indai hakane kuwa to sawwam yayi alkawarin rike mamallakiyar fuskar nan bisa amana da kyautatawa, bazai taba rabuwa da ita ba sannan duk tsawon zamansu bazai sakata kukaba sai alokaci guda daya... Amma daga wannan lokacin zata dawwama cikin dariya"

Baki ta turo cikin shagwaba ta kalleshi,

"Wanne lokaci ne wannan?"

"Baki saniba? Nabaki assignment.." Yafadi yana murmushi,

"Wallahi a,a yanzu zaka fada min babu wani assignment da zaka bani, leave my brain to rest.."

Murmushi yayi "bafa zan fada ba, is an assignment kamar yadda nafada dafarko"

Kafada ta makale, "wallahi ban yarda ba"

Matsawa yayi kusa da ita,

"Ranar da aka kawo min ke a matsayin mata, nasan ranar da kuka zanzo nasameki kina kukan rabuwa da gida, dakyar zan iya lallashinki ki daina"

Lumshe idonta tayi har wani imagining din abun take acikin brain dinta,

"I love you sawwam" tafurta batare data sniba,

"I love you too my lonely.." Shima yafadi bayan ya sunkuyar da fuskarshi saitin tata,

"Sahibi bari naje nayi bacci, nagaji, kaima nasan ka gaji.."

"Kafin ki tafi ki bani wannan ring din na hannunki"

"Yayi maka kadan, nima dakyar idan zai fita daga hannuna saboda ya matseni.."

"Ai kuwa yau zoben nan a hannuna zai kwana" babu wata wata ya kamo hannunta yafara kokarin cire zoben,

"Sahibi bazai fita ba kabari kar ya yankeni" tafada tana runtse idonta,

"Yi hakuri..." Yace da ita tareda jan zoben da karfi nan yafita dakyar,

Hannunta tafara yarfewa tana kallonsa,

"Tunda ka rabani da nawa ai sai kabani naka"

"Gashi" yafadi tareda zare na hannunsa ya mika mata, karba tayi tasaka a babban dan yatsanta na tsakiya,

"Sahibi akwai wani saurayi da abbana ya bani hotonshi cewar in nemeshi muyi zumunci domin dan babban yayansu ne nikuma har yanzu ban ganshi ba sunanshi Faruk, bari kaga hotonshi, abbana yace tunda babansu ya rasu shikenan zumunci ya yanke tsakaninsu"

Wayarta ta bude ta mika mishi hoton ya karba yana gani,

"Wallahi nasanshi kuwa, bari ma naga kamar inada phone number dinshi..."

Wayarshi ya zaro ya fara laluben number din, saka mata yayi acikin wayarta ya bata,

"Yawwa naji dadi dama abba ya dade yana burin sake kulla zumunci dasu nasan yanzu zaiyi farin ciki"

Murmushi yayi "Allah yayi miki albarka"

"Amin sahibina, thank you, i love you, good night, have a nice sweet dream, bye" tace dashi bayan tafara tafiya da baya da baya tana daga mishi hannu,

Shima hannun yake daga mata batare da ya furta koda kalma daya ba,

Yana tsaye yana kallonta har ta bacewa ganinsa sannan ya shiga motarsa ya fita,

Hostel ta shiga ta zauna tafara neman layin faruk dakyar ta sameshi suka gaisa tayi masa bayanin ko ita wacece sannan sukayi sallama,

Kwanciya tayi rub da ciki ta bude laptop din sawwam take hotonta mai kyau ya mamaye kan screen din laptop din....

aishaummi.blogspot.com

Ummi shatu

Pherty Xarah

No comments:

Post a Comment