Saturday 4 March 2017

RAMUWAR GAYYA.. 11

*RAMUWAR GAYYA*💘

_Love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

              &

*Ummy Aysher*

       11

   Shiru yayi yana kallonta hannunsa sarqe a qirjinsa harta fice kansa a matuqar ďaure,

Baisan ya bata haquri ba, shi baima San inda xainemi numberta ba talk less of ya bata haquri, amma taya hakan ta faru? sai ya soma xargin abokansa da sune suka haďa masa wannan plan ďin...

Nan fa faďa na kauraye tsakanin su, kowa na musu da ďan uwansa da haka suka rabu kowane Ransa a matuqar bace.....

Ummulkhairi tana xuwa ta sami Alawiyya ta dawo hrta ďora masu girki, ta cillar da Jakarta kan katifa ta sami guri ta xauna hankalinta a kwance ba sauran damuwa a xuciyarta,

'ya akayi ta sawwam hala yau baku haďu ba shiyasa naga kin shigo da fara'a, ta tabe bakinta

'Wai ta sawwam, bakiji bakinki ya maki nauyin faďa ba, ni ko samari na rasa mexanyi da wannan yaron? Ke bakisan wani abu ba da Kinsan yanda nakejinsa a xuciyata da baki fadi Wannan Mgnr ba,

'mai da wuqar hajiya, it seems like na bata maki rai am sorry ta juya Kan girkin da take....

'khairi taja qaramin tsaki tana faďin,
'ke bakima San wani abu ba, yaron ya bani haquri fa.....

Cikin rashin gamsuwa da Mgnr ta Alawiya ta juya tana kallonta,

'Waye xai baki haquri, sawwam ko Waye?

'shi ďin dai in kuma kinyi musu duba kigani, ta miqa mata wayar ta karba tana dubawa kafin ta kalli khairi,

'lallai amma Waye ya bashi number ďinki,

'Oho masa ni ba wannan ne damuwata ba, haquri ne anbani shikenan mgn ta wuce nidashi Kuma.........

'da dai yafi maku....

2 days~

Tun daga lokacin sawwam bai qara Kula ummulkhairi ba, bawai basu haďuwa bane suna haďuwa amma kallon inda take bayayi gani yake a ynxu ya cigaba da kulata rainin xaifi yawa bayan wanda abokansa suka siyamasa suka bata haquri,

Idan ya tuna abin Ransa baci yake, kenan Yanxu girma ya faďi....

Khairi Kuwa ko ajikinta, ynxu komai yayi mata sauqi ta maida hankalinta sosai a gurin karatunta bata da sauran damuwa a xuciyarta bayan aikin da mahaifinta ya turo ta yi, ko yaushe xata fara? Shine batasan lokaci ba, dan haka xata ďaura aniyar fara Abinda ya rabata daga gida ya kawota Skul ďin.....

Ta qara duba pic ďin da mahaifinta yabata tana naxari sosai kafin ta furxar da iska mai xafin gaske daga bakinta...

'wannan guy ďin ya haďu fa, ta Ina xn soma inama xan ganshi?

ta lalubo wayarta ta Kira mahaifinta sun dade a waya suna tattauna Mgnr kafin ta Kira mahaifiyarta nan ma ta jima sosai suna waya...

Jin Motsin shigowar Alawiya ya sanyata boye pic ďin da sauri,

'khairi ga qaramar wayarki, kamar an turo maki test baquwar number but ban buďa ba... Khairi ta Karbi saqon tana dubawa..

    _You may be out of my sight but never out of my mind. I miss you so much._

Number ce ba suna to waye ,ita wannan abin ya soma isarta haka jiya wani ya kirata Wai yana sonta, a ina ma suke samun numberta, tayi tsaki haďe da cillar da wayar gefe....

'meya faru Kuma, Alawiya ta tambayeta,

'ba komai ta soma haďa takardunta, idan kin shirya mutafi it's olmost tym Kada muyi missing ďin lectures ďin,

A tare suka fito daga hostel.....

Fiye da kwana huďu bata qara ganin sawwam a idonta ba sai dai taga abokansa, bata damu ba kuma batason tasan halin dayake ciki dama wai batana son hulda dashi bane....

Bangaren sawwam Kuwa kusan kwanan sa huďu a kwance ba lfy, Mura ke damunsa da ciwon kai,

Koda yaushe su Abdul suka taso daga makaranta suna gidan tare dashi,

'munga khairi yau Kuma bata tambayi abokin fadanta ba duk da tadaina ganin ka,

'And so, Nima Kaga alamar na damu da itane kona taba tambayarka ita, nifa na riga Nafita batun yarinyar kudaina min mgnrta bana so kuna tuna min da Ita....

'shi kenan mun daina, amma gobe xaka fita ko munga jikin da sauqi, ya tashi yana fadin

'me xai hana, kai ni nama gaji da wannan Skul Yakamata muyi exam haka kowa yakama gabansa...

'Wallahi kam.

Washe gari suna fitowa da Alawiya idanunta na sauka akansa yana sanye cikin qananan kaya yayi kyau sosai amma daga nesa xaka gane ya ďan yi rama,

Bai gantaba yana can yana sabgogin gabansa shida su Abdul sai tsokanar mutane suke suna dariya wannan yana daya ďaga cikin halayyarsu,

Abdul ya tabosa yana nuna masa su khairi, ko kaďan baiyi xaton itace Abdul ke nuna masa ba da baxai juyaba,

Yana juyawa Kuwa suka haďa ido ita dashi, kamar mai jira ta galla masa harara haďe da ďauke kanta, shima dogon tsaki yaja yana kallon Abdul fuskarsa ba walwala.......

Pherty
    &
Shatu

No comments:

Post a Comment