Thursday 9 February 2017

RAMUWAR GAYYA.. 1

*RAMUWAR GAYYA...*💘

   _Love story 50,50_


*_UMMI A'ISHA_*

       _with_

*_PHERTYMAH XARAH_*


*_1_*

_Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai...._

~~~"Wannan shine abinda nake son kiyi kamar yadda nafada miki abaya, hakika ummulkhair nadade ina burin Allah ya bani ya mace domin wannan burin nawa ya cika amma Allah bai baniba sai yanzu, ina fata zaki dage ki zama silar cikar Burina kamar yadda nadade ina fata,

Idan kikayi haka kin gama yimin komai kuma zanyi alfahari dake sannan koda na mutu to zan mutune da farin cikin abinda kika yimin, ina fata zaki mayar da hankali kan abinda natura ki sannan banda kula kawayen banza da samari barkatai idan kikayi haka to lallai ranki zai baci, Allah yayi miki albarka ya baki nasara"

Idonta fal da kwalla ta dago tana duban mahaifin nata wanda ke kishingide akan kujera fuskarsa cikeda walwala da annuri,

"Abba nayi maka alkawari zan zama silar cikar burinka kamar yadda ka dade kana fata sannan zanyi abinda ka turani batare da an samu kuskure ba"

Sai alokacin mahaifiyarta dake zaune agefe tayi magana itama idonta dauke da kwalla,

"Yanzu Alhaji abinda kayi ka kyauta kenan? Ka dauki yarinya karama yar shekara 22 katurata har nan da garin Kano kawai dan kanada buri acikin ranka kuma ka dage sai burin nan ya cika.."

Katseta yayi ta hanyar cewa "ya isa haka hajiya fati, ai dai 'ya tawace ko? To ki barni na zabar mata abinda naga yafi cancanta da ita, tun shekaru 30 da suka wuce nake burin Allah ya mallaka min ya mace amma bai baniba sai yanzu, yayunta duk samarine maza d'ai d'ai har hudu, to yanzu tunda lokaci yazo dama ta samu ai sai ayi amfani da ita"

"Gaskiya Alhaji nidai ban goyi bayan ka tura min yarinya wata uwa duniya har kano ba kawai dan kana son cikar burinka"

"Mama kiyi hakuri babu komai insha Allah bazan yi abinda duniya zatayi Allah wadai dani ba, zan kare kimar gidan nan da mutuncinsa abinda abba ya tura ni shi zanyi bazan taba yin wani abuba sabanin haka" ummulkair ta fada tana share hawayen idonta,

"Allah yabada sa'a yayi miki albarka, maza ki tashi kije kar kuyi dare, Allah ya kiyaye hanya" mahaifinta yace da ita,

"Ummulkair Allah yabaki sa'a" mahaifiyarta tafada tana goge hawayen dake kwarara akan idonta,

Tashi tayi taja katuwar jakar kayanta (trolley) tafita tana share hawayen idonta,

Awaje ta iske yayanta wanda take bi yana jiranta, kayan ya karba ya saka acikin Mota ta shiga ta zauna suka lula,

Tunani take yi aranta domin wannan shine karo na farko da zataje garin kano kanon ma wai jami'ar bayero,

"Allah kabani sa'a" tafada acikin ranta tana kallon hanyar da zata fitarsu daga garin bauchi zuwa kanon dabo.

  Tafiyar awa ukuce ta kaisu cikin kano lokacin karfe 3:30 na yamma atsakiyar makarantar kusa da hostel din da aka tanada domin mata yayanta ya ajiyeta yafara kokarin fito mata da kayayyakinta,

Tana ganinsa ya juya zai tafi take tasa kuka kamar yarinya ko saurarenta baiyi ba yayi tafiyarsa kasancewarsu sako da sako,

Kayanta tafara dauka tana kaiwa cikin hostel kofar dakin da aka bata, sai da tagama kwashewa tsaf sannan ta shigar da kayan cikin dakin wanda ya kasance nata ita daya domin bata son kazanta wannan dalilin ne yasa zata yi zamanta ita kadai,

Shisshirya kayan tayi ta mike akan gadonta ta kwanta ga wata irin yunwa da takeji gashi babu wanda tasani,

"Gaskiya bazan iya girki yanzu ba bari kawai naje na siyo abinci awaje" tafada acikin zuciyarta, mikewa tayi taja hijabinta tasa ta dauki yar karamar jakar hannunta ta fita,

Babu inda tasani dan haka taketa waige waige gashi ranar weekend ne makarantar babu dalibai da yawa,

Wani shago ta hango dan haka ta nufi can, wasu samari guda uku tagani suna zaune akofar shagon,

"Dan Allah me da me ake sayarwa anan?" Tafada tana kallonsu,

Shiru suka yi mata babu wanda ya tanka,

"Bayin Allah magana fa nake yi muku"

"Ke bar nan" wani saurayi acikinsu yafada fari dogo mai saje,

"Ba zaki bar nan ba sai nataso?" Yasake fada yana kallonta,

Da sauri tafara kokarin barin wurin har tana hadawa da gudu, dariya suka saka gaba dayansu tareda Tafawa,

"Sai 3 pointer" suka fada suna ihu,

Hostel takoma tana tunanin to shi wannan waye a makarantar? Itadai bakuwa ce bata da masaniyar ko waye shi, dambun naman da  mamanta ta yi mata ta dauko tafara ci da biredi har ta koshi,

Zama tayi jugum tana jin hayaniyar mutane har dare yayi, atsorace ta kwanta adakin bayan ta kulle, baccine ya dauketa sakamakon gajiyar da tayi.

  Tun asuba ta tashi tayi salla ta dauko alqur'aninta ta bude ta karanta har gari yayi haske,bucket ta dauka taje ta debo ruwa ta wuce bathroom tayi wanka ta zo ta shirya,

Ruwan zafi ta jona a heater ta hada tea ta saka kayanta riga da zani da katon hijab taja dakinta ta kulle ta fita,

Koda ta fita ganin makarantar tayi acike sabanin jiya da babu mutane da yawa,

"Yau ake yinta" tafada azuciyarta sakamakon bata san takamaimai wurin da zata samu yan ajinsu ba kuma babu wanda tasani aciki,

Wasu samari ta hango su hudu asaman wata mota daya daga cikinsu ya bata baya yana sanye da kananan kaya yana taje sumar kanshi da cumb,

"Ohh samarin jami'a kenan" tafada aranta tareda dosar wurin da samarin suke.





🅿herty novels

Ummi Shatu

My wattpad Phertymerh1

No comments:

Post a Comment