Thursday, 9 February 2017

RAMUWAR GAYYA..2

*RAMUWAR GAYYA...!*💘

   _Love story 50,50_


_*UMMI A'ISHA*_

       _with_

*_PHERTYMAH XARAH_*


  *_2_*

~~~ Sallama ta yiwa samarin tareda cewa "dan Allah tamabaya nake, inane wurinda yan level 1 suke lectures?"

"Ke, yauma dawowa kikayi? Wai ke mu sa'anninki ne?" Wani saurayi ya fada sai da suka hada ido sannan ta gane ashe shine saurayin jiya,

"Kuyi hakuri" tafada atsorace zata juya ta tafi,

"Ina zakije? Zo nan" taji yafada da karfi,

Dawowa tayi ta tsaya, "wanne course kike karantawa?"

"Mathematics" ta bashi amsa,

"Ya sunanki?"

"Ummulkhairi" ta sake bashi amsa,

"Ungo jeki ki siyo min lemo, kuma indai baki kawo min ba kika gudu to zan nemoki duk inda kika shiga"

1000 ya zaro ya bata ta karba ta wuce,

Capteria ta nufa acan ta siyo masa lemon ta dawo duk hankalinta atashe yake domin bata san dalili ba kawai tsoronshi taji tana yi,gashi bata san cewa a jami'a kowa gashin kansa yake ci babu sawa babu hanawa ba, tayi zaton irin secondary school ne akwai seniority,

Wurin da suke ta karasa takai masa lemon,

"Ke wayasa ki siyo min fanta? Saboda ke villager ce ko? Karbi ki je ki canjo"

Hakuri tafara bashi "dan Allah kayi hakuri dan Allah"

Fashewa da dariya taji abokannshi sunyi sannan ga dalibai sun zagayesu suna yi mata dariya kun san jami'a komai abin kallo be kuma abin dariya ne, nutsewa ne kawai batayi ba dan kunya, kudin da lemon ta cilla masa ta juya idonta duk ya ciko da kwalla,

Wata tagani sanye da hijab nan budurwar ta kamo hannunta,

"Yar uwa me yakaiki wurinsu wadancan yaran marassa mutunci?"

Kwallar idonta ta goge tace "wallahi ban sansu ba daga zuwa tambayarsu wurin lecture dinmu shikenan fa harda aikena"

"Yi hakuri to share hawayenki, wanne department kike?"

"Mathematics"

"Level 1?"

Kai ta daga mata alamun ehh,

"Ayya department dinmu daya dake amma gaskiya naji dadi saboda dama ni kadai ce mace kullum atakure nake dama kuma ance mu biyune mata wadanda muka nemi course din"

Murmushi ummulkhairi tayi "kin san ai maths bashida farin jini majority din dalibai sun tsaneshi saboda akwai caja brain, nima fa da ban iyaba lokacin da ina primary school sai da naje secondary school sannan nadage na iya daga karshe har quiz nake zuwa na maths"

Dariya budurwar tayi "ah lallai ashe daya muke, wallahi nima yanzu bazan iya theory ba saboda tsananin sabon da nayi da lissafi"

"Koni gaskiya yanzu bazan iya theory ba nafi ganewa in zauna inyita Tarawa da debewa" ummulkhairi ta bata amsa,

"Allah Sarki ya sunanki?"

"Sunana ummulkhairi"

"Ayya nikuma sunana alawiyya"

"To inane wurin lectures din?" Ummulkhair ta tambayeta,

"Canne new side fa, ai abun namu muhimmi ne dan yau ma bamu da lecture sai 12"

Zaro ido ummulkhair tayi "kai amma akwai damuwa wallahi ni ai nayi tunanin tun 8 ake fara lectures din"

Hannunta alawiyya ta kama tana murmushi, "zo muje admin block kiga time table dinmu saboda nima bani dashi"

"Yawwa to muje"

Tafiya suke suna shan hirarsu tamkar dama can sun san juna ko kuma sun dade suna kawance, har suka karasa admin block din wurinda aka kafe time table na kowanne department,

Biro da dan karamin memo ummulkhair ta ciro ta fara kwafar musu time table din tana murmushi,

"Alawiyya wai wannan gayen na dazu wanene?"

"Meyasa kike son sanin waye shi?" Alawiyya ta tambayeta tana kallon fuskarta,

"Kawai ina son sanine domin inada wani buri akanshi" ummulkhair tace da ita tana rubutu ajikin memo dinta,

"Buri? Wanne irin buri ummulkhair? Ko dai kin kyasa ne?"

Murmushi ummulkhair tayi wanda har biro hannunta yana kokarin subucewa ya fadi kasa,

"Ko kadan bai yimin ba saboda na fuskanci dan rainin hankaline"

"Hmmm ummulkhair kenan ai duk makarantar nan kowa yasan three pointer saboda tsabagen kwakwalwarsa, yana ja fiyeda yadda bakya tunani shiyasa ma kika ga yana rashin mutuncinsa son ransa saboda yaga yanada ilimi, ni kaina yaron yana burgeni domin yasan abinda yake yi yana zama yayi karatu kuma bai taba samun carryover ba tun farawarsa har kawo yanzu, haka ake son mutum bawai yazama dan iskaba amma brain empty, shikam wannan gayen ya iya wulakanci amma kuma yasan me yake yi sannan yanda kika gansun nan shida friends dinshi to haka suke duk school dinnan kowa yasan basa kula yanmata."

"Alawiyya kenan nifa duk wannan yabon da kika dage kina yi akanshi ba burgeni zaiyi ba"

"Dama nasan bazai taba burgeki ba ummulkhair tunda three pointer yasaki kuka, amma kisani ni ina fada miki ne abinda na sani agame dashi, sunanshi na asali *SAWWAM MUSTAPHA* ance shi kadai mahaifanshi suka haifa gidansu yana nan a unguwar sharada phase 2, kamar yanda na fada miki yaron nan yana ja domin baya wasa da karatu, shine president na makarantar nan domin lokacin da akayi zabe dalibai duk shi suka zaba"

"Yayi kyau" ummulkhair ta fada tana kokarin saka biro dinta da memo acikin jaka.





🅿herty novels📚

Duniyar makaranta

1 comment:

  1. I'm a huge fan Ummi Aisha.I really don't like missing your novels. I've read many to be listed like kwarya tabi kwarya and many more. More grease to your elbow sweery keep it on.
    Lover/fan
    Khadeejat Buba (f.b)

    ReplyDelete