Thursday 9 February 2017

RAMUWAR GAYYA.. 3

*RAMUWAR GAYYA...*💘

_Love story 50,50_

*_UMMI A'ISHA_*

        _With_

_*PHERTYMAH XARAH*_

  *_3_*

    *H*annun ummulkhairi alawiyya ta kama suka fara kokarin barin admin block suka nufo cikin makaranta,

"To yanzu ina za muje?" Ummulkhairi tace da alawiyya,

"Muje kawai mu samu wuri mu zauna mu huta kafin lokacin shiga lecture yayi"

"Ok to muje"

Tafe suke suna hira cikeda annashuwa har suka je karkashin wata bishiyar mangoro wacce aka girka wata bakar doguwar kujerar karfe a wurin domin hutawa, zama suka yi bisa kujerar alawiyya ta fara koyawa ummulkhair abubuwan da aka danyi lokacin da bata nan, sun shafe fiye da mintuna goma sha biyar awurin suna tattaunawa sai ga wannan gayen na dazu shida wasu mutum biyu har shi na uku,

"Ke baki san nan wurin wajen da nake zama bane?? Dalla malamai ku tashi ku bawa mutane wuri.."

Ko kallonshi ummulkhair bata yi ba taci gaba da latsa wayar dake rike a hannunta,

"Ke tun ranar da nafara ganinki na lura kema fa yar rainin wayoce, agidanku ba akoya miki bawa babba girmansa bane?"

Nan dinma shiru tayi kuma da alama bata da niyyar tanka mishi kamar yadda ya zata,alawiyya ce ta fara harhada littattafanta tana sakawa acikin jaka,

"Ummulkhair tashi mu tafi"

Sai a lokacin ummulkhair din tayi magana,

"Ina zamu tafi? Shi har ya isa yazo ya tashe mu daga nan? Babu inda za muje har sai lokacin da muka yi niyya yayi sai dai idan shine zai yita tsayuwar jiranmu.."

"K'arya kike yarinya ke baki isa na tsaya ina jiranki ba God forbid"

Murmushi ummulkhair tayi "ehh ai da yake kujerar daga gidanku ka daukota ka kawo nan shiyasa zaka hana kowa zama awurin sai kai",

"Ummulkhair dan Allah ki rabu dasu kizo mu tafi"

Alawiyya tace da ita bayan ta kama hannunta tana kokarin mikar da ita tsaye,

"Ke wallahi idan baki bar wurin nan sai kinyi nadamar yin haka.." Yafada yana huci,

"Idan har ni banyi nadama ba to kuwa kai zaka yi nadama, nonsense kawai.." Ummulkhair ta fada cikeda jin haushi domin ita haushi yake bata,

"Ke ni kika cewa nonsense? Ni kika zaga? Ke har kin isa ki zageni?" Ya fada cikin daga murya tareda zabura yayi kanta zai daketa,cikin zafin nama abokanshi suka rikeshi suna bashi hakuri,

"Dan Allah ku sakeni na koya mata hankali.."

"Ku sakeshi dan Allah in yaso naga abinda zai yimin, kai ka isa ka dakeni ka zauna lafiya? Wallahi baka isaba domin ni yanzu babu wanda ya isa ya dakeni sai ruwan sama..."

"Wai ku sakeni mana bakwa jin irin maganar da yarinyar nan take fada min?" Ya sake fada a zuciya,

Abokan nashi basu sakeshi ba sai hakuri da suke bashi ita kuma ummulkhair sai fama da ita alawiyya take yi akan ta tashi su tafi subar wurin domin mutane har sun fara taruwa amma fur ummulkhair taki tashi tace babu uban wanda ya isa ya tayar da ita daga wurin,

"Ke ni kike zagi..?"

"An zageka din kai dan gidan uban waye da ba za azageka ba?"

Wata kara ya saki take ya kwace daga rikon da abokan nashi suka yi masa ya nufi kanta gadan gadan, aguje suka sha gabansa suka tattareshi, ganin haka yasa alawiyya jan ummulkhair ta karfi suka bar wurin yayinda sawwam in banda huci babu abinda yake yi,

Lokaci kadan idonshi ya kada yayi jawur ranshi in yayi dubu to ya baci saboda zagin da ummulkhair tayi mishi agaban bainar jama'a,

"Wallahi sai na koyawa yarinyar nan hankali domin babu macen da ta taba zagina sai ita..."

Fusgewa yayi ransa a bace yabar wurin ya nufi wurinda motarsa ke ajiye,

Yana zuwa ya shiga ya yi mata key azuciye ya fita daga cikin makarantar bayan ya tayar da kura wacce kai in ba sani kayi ba zakace sansanin yakine,

Yanayin yanda yake tukin ma kana gani kasan ransa a bace yake, ji kake k'uuuuuuu ya taka wani wawan mahaukacin burki sakamakon tsayarsu da danja tayi,

Duk mutanen wurin sai da suka razana saboda sunyi zaton wani aka kade, shi kuwa gogan sai furzar da numfashi mai dumi yake yana shafa sumar kansa alamun ransa ya gama baci,

Kamar zai tashi sama haka yayi lokacin da danja ta basu hannu, da wannan gudun na masifa ya isa gidansu dake unguwar Sharada phase 2,

Wani tangamemen gida ya shiga bayan yayi horn mai gadi ya bude masa, yana yin packing ya fito a fusace ya shiga cikin gidan, falon mahaifiyarshi ya shiga kamar zai ci tuntube saboda bacin rai,

Zaune ya sameta itada wasu yanmata guda biyu kyawawa suna kallon Indian film awata tasha (zee world),

Tsallakesu yayi saboda bai sansu ba yawuce cikin bedroom dinta,tunda ganinshi mahaifiyarshi ta gane yana cikin bacin rai dan haka tayi gaggawar binshi cikin dakin,

A tsaye ta sameshi ya dunkule hannunshi sai naushin iska yake yi yana cewa "ohh my God..."

Saurin karasawa gareshi tayi ta rikeshi "sawwam me ya farune?" Mahaifiyarshi ta tambayeshi cukin kulawa,

"Mami wallahi a school ne aka bata min rai..."

Kama hannunshi tayi ta zaunar dashi a bakin gado itama ta zauna tana murmushi,

"Sawwam sau nawa zan fada maka cewar duk inda mutum ya tsinci kansa to dole sai yayi hakuri,kofa da wa zaka zauna dole sai kayi hakuri, kayita hakuri kaji..." Mami ta fada tana Shafa kanshi,

"Shikenan Mami naji kuma zanyi hakurin"

Mikewa yayi amma har lokacin ranshi a bace yake mutuka,

"Ga baki can a falo 'yayan hajiya rahama ne ta turosu ka duba koda wacce zaka ga tayi maka acikinsu.."

Murmushin yake yayi domin idan har da sabo to ya saba kusan kowanne lokaci kawayen Mami sukan turo yaransu yanmata wai ya duba ko zai ga wacce tayi masa,

"Mami dan Allah nidai mubar wannan maganar.."

Kafin Mami tayi magana har ya fice daga cikin dakin, ko kallon yanmatan bai yi ba ya wuce abinshi, dakinsa ya shiga ya fada toilet ya sakarwa kanshi ruwa yayi wanka ya fito har lokacin bai daina hango fuskar ummulkhair tana zaginsa ba,

Kananan kaya yasa ya fita zuwa wurin mai gadinsu domin dama kusan kowanne lokaci idan yana gida can yake zuwa suyita hira,

Yau dinma zaman yayi suka fara hira baba dan tsoho yana bashi labari mai saka nishadi,

"Yawwa baba dan tsoho dama ina son tambayarka wai dan Allah me mata suka fi jin tsoro ne?"

Dariya baba dan tsoho yayi sannan yace,

"Ai sawwam babu abinda mata suka fi tsoro sama da kadangare komai kankantarsa kuwa, duk mace zaka sameta tana tsoron kadangare..."



🅿herty novels📚
Duniyar makaranta

No comments:

Post a Comment