Thursday 26 January 2017

RUWAN KASHE GOBARA...! 75

*RUWAN KASHE GOBARA...!*🔥
  _(Labari mai tab'a zuciya)_


  *_NA_*

*_UMMI A'ISHA_*

    _Sadaukarwa ga k'awata *KHADIJA SIDI*_

   aishaummi.blogspot.com

   *_75_*

~~~Tsayawa Lamido yayi a k'ofar gidan yana jiran fitowar yaya hussain amma acikin zuciyarsa yana jin radadin maganganun da yaya hussain ya jefeshi dasu,

A fusace yaya hussain ya shiga cikin gidan inda ikhlas ke tsaye a tsakar gida ta kasa karasawa cikin falon domin maganganun da yaya hussain ya fadawa lamido sunyi mutukar girgiza ta,

Tana jin tahowarshi tayi saurin shigewa cikin falon kamar an jehota,

"Lafiya..?" Farida matarshi ta fada tana kallon ikhlas,

"Wannan yarinyar ban san cewa shashasha bace sai yau, in banda rashin hankali meye nata na bin shi..?" Yaya hussain ya fada yana huci,

"Kayi hakuri dai dan Allah, abi komai a sannu" farida tace dashi cikin sanyayyiyar murya, juyawa yayi ya fita a fusace, nan farida ta juyo tana duban ikhlas,

"Haba ikhlas meyasa zaki bishi kamar baki da wayo? Kefa kike bani labarin irin wulakancin da yayi miki agidanshi, meyasa bazaki tsaya kija ajinki ba a matsayinki na ya mace ai ya kamata ace kinja masa aji bawai daga baki hakuri zaki hakura ba.."

Kallonta ikhlas tayi idonta cike da kwalla "anty farida ya kuke so nayi ne dan Allah? Yazo ya bani hakuri kuma har kuka ya tisani agaba yana yimin idan ban kulashi ba yaya zanyi..."

"Babu wani kuka kedai kawai kinyi missing din mijinki shiyasa kika bishi"

Juyawa tayi ta fita domin tasan idan ta zauna farida ta rinka tsokanarta kenan. Lamido kam yana nan tsaye har yaya hussain ya fito ya wuceshi fuskarshi babu fara'a, bin bayanshi lamido yayi har zuwa gidan ammi, babu alamun tsoro ko fargaba yasaka kai ya shiga cikin gidan, yaya hussain na zama shikuma yana shigowa, mikewa tsaye yaya hussain yayi yana huci,

"Waye ya baka izinin shigo mana cikin gida? Ka gaggauta fita mana daga gida"

Ammi ce ta fito daga cikin daki saboda jiyo maganar Hussain da tayi,

"Hussain me yake faruwa ne...?"

Ganin lamido da tayi ya sata janyo tabarma ta fara kokarin shimfida masa tana cewa,

"Bako muka yine?"

"Ammi karki saurareshi domin ikhlas ba zata koma gidanshi ba"

"Haba hussain ya isa haka mana, kayi hakuri muji abinda ke tafe dashi"

Zama Lamido yayi amma ranshi ya fara baci da maganganun da Hussain ke yaba masa, zama ammi tayi suka fara gaisawa da lamido, hussain kuwa har lokacin sai masifa yake zubawa har hajiya ta shigo dauke da sadiq a hannunta ai sadiq yana ganin lamido ya fara tsalle kamar zai fado,

Karbarshi lamido yayi yana murmushi, zama hajiya tayi ammi ta fara kora mata jawabin abinda ya faru nan hajiya tace to sai abawa lamido matarsa su tafi tunda gashi har yazo  biko da kansa, fada hussain ya tayar shi a lallai ikhlas ba zata koma gidan lamido ba, da kyar hajiya da ammi suka shawo kanshi suka bashi hakuri ya yarda cewar ikhlas zata koma amma da sharadin ko yaya lamido ya sake yi mata wulakanci ko ya fifita matanshi akanta to ta dawo gida kuma wallahi ba zata koma ba har abada, akan wannan sharadin hussain ya amince da komawar ikhlas, suna nan zaune bayan an sasanta ikhlas ta shigo sai rrrakubewa take yi domin kunyar su ammi da hajiya take yi saboda bin lamido da tayi,

"Ke idan zaki shigo ki shigo ba ason munafurci, kizo ki tattara kayanki kibi mijinki kuje can ku karata" hajiya tace da ita cikin daga murya,

"Hajiya munafurcin me nayi kuma" ikhlas ta fadi cikeda kunya bayan ta shiga cikin dakin,kukan da sadiq ya fara yine saboda ganinta da yayi ya sata juyawa ta karbeshi daga hannun lamido ta shige cikin dakin ammi ta zauna tana yiwa sadiq magana,

"Saddiqun abba jiya na barka acikin maraici ko? Allah sarki yarona kayi hakuri abbanka ne ya jawo maka..."

Tana daga cikin daki tana jinsu suka gama sasantawa da zummar gobe lamido zai zo su tafi, karar shigowar text massage cikin wayarta taji tana dubawa taga lamido ne ya turo mata sako kamar haka,

   _pretty shine ko sallama babu ko? To ai ni ban sallameki ba kika tafi amma shikenan  na tafi,ki shirya da wuri gobe domin da sassafe zamu tafi, sai kinji wayata nagode da kulawar da kika bani, I know zanyi mutukar missing dinki yau, i love you....!_

Murmushi tayi bayan ta gama karanta sakon nashi, sadiq ta kwantar ta tashi ta fara harhada kayanta tana shiryawa acikin akwati har ammi da hajiya suka shigo,

"Kin dawo?" Hajiya ta tambayeta tana rike habarta,

"Ke yarnan wato shine kika bi mijinki ko sallama babu ko? Anata kokarin a kwato miki yancinki amma ke bakya gani, to ai shikenan sai ki shirya ku tafi dama ba mune muka je muka daukoki ba kece nan kika zo da kafarki"

Shiru ikhlas tayi bata tanka ba domin ta fuskanci cewar duk abinda zata fada musu ba ganewa zasu yi ba saboda basu san tsakaninta da lamido ba, sam ba zata iya jurar ganinshi cikin damuwa ba mutukar tanada ikon rabashi da damuwar,itadai ammi na jinsu batace dasu komai ba har hajiya ta gama bambaminta ta tafi,

Har tsawon lokaci ikhlas na zaune ta kasa daga kanta ta kalli ammi, murmushi ammi tayi tai gyaran murya tasoma yi mata fad'a akan idan ta koma yola ta yi hakuri ta zauna da kishiyoyinta da mijinta lafiya sannan ta zama mai rufe sirrin mijinta acikin kowanne lokaci.

Kammala shirya kayanta tayi wuri daya, acikin daren yaya hussain ya kawo mata abdallah domin suyi sallama, k'in bin yaya Hussain abdallah yayi yace awurin ikhlas zai kwana hakan kuwa akayi domin rungumeshi tayi ajikinta ahaka suka yi bacci.

Washe gari da safe da wuri ta tashi ta shirya ta shirya sadiq sannan ta shirya abdallah domin akwai school yaya hussain zai zo ya kaishi, su abdallah na tafiya lamido yazo, agurguje suka gaggaisa dasu ammi ya dauki kayan ikhlas da sadiq ya fita, sallama tayiwa su ammi da dukkan mutanen gidan ta fita wurin lamido, dakyar ta lallabashi ya kaita gidan yayunta tayi sallama da matansu ta fito, nan suka dauki hanyar yola lamido sai hira yake yi mata.

Karfe 2 na rana suka shiga cikin garin yola, kai tsaye gida suka wuce, itace ta fara shiga cikin gidan nan ta ganshi babu alamun mutum aciki tasan duk yanda aka yi fadila da ihsan suna makaranta, bedroom dinta ta karasa lamido yana biye da ita dauke da kayanta a hannunshi, ajiye mata kayan yayi yai mata sallama ya fita domin yanada abubuwa da yawa wadanda zai gudanar a kamfaninshi,

Zama ikhlas tayi ta gyara part dinta sosai ta shiga kitchen ta dafa jalop din taliya da kifi, tana kokarin fitowa daga cikin kitchen din fadila ta shigo rikeda littattafai a hannunta,

"Ashe kun dawo? Sannu da zuwa" fadila tace da ita tana yayyatsina fuska,

"Ehh mun dawo, barka da dawowa" ikhlas ta bata amsa daga nan kowa ya wuce sashensa ba tare da sun kara yin wata magana ba.

Tunda ikhlas ta shiga daki bata sake fitowa ba har dare yayi, shi kanshi lamidon shima bai samu damar dawowa gidan ba sai bayan sallar magrib, kansa tsaye dakinsa ya shiga yayi wanka ya fito gashi wata irin yunwa yake ji domin rabonshi da abinci tun safe, salla yayi ya nufi dakin ikhlas,

Tana zaune agefen gado tana turawa yaya Hussain text lamido ya shiga cikin dakin, kamshin turarenshi kawai taji ta gane zuwanshi, dago da kanta tayi ta kalleshi, yasha kyau cikin farar t shirt wacce aka rubuta home boy ajiki da bakin wando,

Murmushi ya sakar mata ya karasa cikin dakin ya je kusa da sadiq yana kallonshi,

"Saddiquna har kayi bacci? Yau ban ganka sosai ba aiki ya rikeni"

Dagowa yayi daga kallon sadiq ya kalli ikhlas, "pretty yunwa nake ji kinada abinci ki bani?"

"Akwai abinci bari na baka" tashi tayi taje ta zubo mishi abincin data dafa da rana tazo ta ajiye mishi, hannunta ya rike yana kallon fuskarta,

"Tsaya ki bani mana..."

Zama tayi ta soma bashi a baki yana ci amma sai shhhhh yake yi alamun akwai yaji a abincin,

"Abban sadiq gaskiya ka fiya raki da yawa naga babu wani yaji sosai"

"Haka dai kika ce" ya bata amsa yana wasa da zoben dake sanye cikin dan yatsanta,

Murmushi tayi ta dauko masa juice ta tsiyaya masa,makale kafada yayi,

"Ni dai wallahi na bakinki nake so.." Lallabashi taci gaba dayi domin ta fuskanci lamido tamkar yaro yake sai da rarrashi, da wayo da dabara ta samu ya gama cin abincin yasha juice,

Cikinta ya shafo, "ki rage cin yaji kinga kinada juna biyu.."

Saurin kallonshi tayi sai kuma tayi murmushi, "wanne irin juna biyu kuma?" Ta tambayeshi,

"Wanda kike dashi"

Yabata amsa yana matsawa kusa da ita, murmushi tayi ta rike hannunshi,

"To wallahi ni banida wani juna biyu saboda dazun nan ma..."

Bude idonshi yayi sosai yana kallonta "dazu me? Bako kika yi? To wallahi kice masa ya koma,wai ma tsaya yanzu kina nufin duk wannan zazzabin da kika rink'a goga min dama ba ciki ne dake ba...?"

"Na goga maka zazzabi kodai ka goga min..?"

"Kece kike goga min ni kar kiyi min sharri, wallahi kece.."

Dariya tayi ta fara tattare kayan da yaci abincin ta fita, binta yayi ya kama hannunta zuwa babban falo inda su fadila suke zaune suna kallo,

Agefensu ya zauna ita kuma ta zauna a gefenshi, dukkaninsu sunsha kwalliya musamman ma ihsan wacce taci gayu cikin riga da wando,

Bayani yayi musu sosai akan su zauna lafiya banda fada banda daukar magana sannan girki zasu rinka yin kwana daya daya, nan ya tambayesu ko akwai mai magana acikinsu sukace babu amma yau ya kwana a dakin ikhlas in yaso washe gari sai afara rabon kwanan, ba karamin dadi lamido yaji ba,

Tashi ikhlas tayi ta koma dakinta ta barshi zaune awurinsu fadila suna hira, wanka ta shiga tayi ta fito ta zauna ta fara tsarawa fuskarta kwalliya, jagira, jan baki, kwalli, lip glow, powder, mascara, eye shadow duk sai da ta sakawa fuskarta cikin wannan daren domin tana son yau ta burge lamido, turare kuwa kamar barinshi akayi ajikinta domin ko wanne bangare na jikinta kamshine ke tashi na daban, wata light purple din rigar bacci ta saka mai dan siririn hannu wacce bata da nauyi,gashi ta gyara gashin kanta ta tufkeshi wuri guda,

Tana zaune tana feeding din sadiq ya shigo cikin dakin yana sanye cikin kayan bacci riga da wando,

"Woww..." Yafadi ahankali bayan ya zauna a kusa da ita,

"Kinyi kyau pretty na sai kace wacce zata je dinner"

Murmushi ikhlas tayi ta fara masa idanuwanta batare da tayi magana ba nan yaji ya sake rikicewa, da kanshi ya dauki sadiq ya kaishi cikin dan karamin gadonshi ya kwantar dashi ya koma gareta.

Tun misalin karfe 8 ikhlas tayi wanka ta shirya tayi kwalliya sosai ta saka wata koriyar atamfa tasha dauri bayan ta game dukkan sassan jikinta da turare, gefen lamido taje ta zauna ta kwantar da kanta akan gadon bayanshi,

Hannunta ya riko ya soma kissing dinshi har lokacin idonshi a rufe yake,

"Abban sadiq ka tashi.."

"Me zanyi idan na tashi?" Ya tambayeta idonshi arufe,

"Shirin office"

"Ba yanzu ba"

"Sai yaushe?" Ta sake tambayarshi,

"Sai 10 lokacin nagama ganawa dake"

Murmushi tayi ta matsa hannunshi "to ka tashi kaje ka gaisa da matanka karsu fita school baku gaisa ba.."

Sai a lokacin ya bude idonshi domin har ga Allah ya manta dasu saboda idan yana tare da ikhlas dinshi mantawa yake yi da kowacce mace,

Zaune ya tashi yana binta da kallo domin ba karamin kyau tayi ba tasha ado sosai gashi har sarka da awarwaro ta saka,

"Kinyi kyau, zo muje ki rakani mu gaisa da su ihsan"

Tashi tayi ta bishi suka fita ita ihsan har ta tafi makaranta lokacin ita kuma fadila ta fito zata tafi, yana jikin ikhlas rungume da ita suka gaisa da fadila ta juya ta wuce ta fita, dakinshi suka shiga acan suka sake bude sabon babin soyayya.

Sai karfe 11 lamido ya samu ya fita wanda ahakan ma da kyar ya iya daurewa ya fice, amma koda yaje office dinma bini bini sai ya kirata awaya yaji muryarta, har ya taso daga office ya dawo gida hankalinsa na ga ikhlas, yau kam a dakin fadila yake dan haka duk sai ikhlas taji ta shiga damuwa amma haka ta daure suka yi sallama dashi ya tafi. Daren ranar daga shi har ita basuyi baccin kirki ba gari yana wayewa ya nufi dakinta tana zaune tana yiwa sadiq wanka tasha kwalliya sosai cikin shadda orange colour wacce tasha dinkin sirfani,dagowa tayi ta kalleshi tana murmushi,

"Abban sadiq har ka tashi?"

Kiss yayi mata a kumatu yace "dama nazo ganinku ne tunda kuna lafiya shikenan"

"Lafiya lau muke abban sadiq"

Mikewa yayi ya fita ya nufi dakinshi.

Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya cikin farin ciki da kulawa da juna domin ikhlas tana mutukar kulawa da lamido kullum cikin yi masa kwalliya take kala kala, gaba daya ta gama mamaye zuciyarsa da soyayyarta domin duk cikin matanshi yafi sonta yafi kaunarta kowanne lokaci cikin begenta yake,

Tafiya ce ta kamashi zuwa abuja nan ya fara ahiri yaso ya tafi da ikhlas amma taki saboda bata son matanshi su gane tafisu fada awurinshi ko kuma yafi fifitata akansu, tsayawa yayi yaki koda kallonta ya juyar da kanshi yana kallon wani wuri ita ikhlas sai hakan da yayi ya sake burgeta tana tsaye ta jingina da bangon falonta kallonshi kawai take yi yasha kyau sosai cikin jar t shirt mai zagayayyen wuya da bakin wando ya daura jan agogo da jan takalmi sauciki ga kuma lollypop a bakinshi yana sha,sunfi minti biyar a tsaye amma yaki kallonta, juyawa yayi ya shiga cikin dakinta ya yiwa sadiq kiss a kumatunshi ya fito, sai da yazo daf da ita zai gifta tayi saurin shiga gabanshi ta rungumeshi, wata sanyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke amma sai bai nuna mata yaji dadin hakan da tayi ba,

"Haba handsome kar kayi fushi dani mana.."

Maimakon ya bata amsa saima kawar da kanshi da ya sake yi,jin yaki kulata ya sata kai masa kiss a bakinshi bayan ta cire lollypop din da yake tsotsa, yana jinta tana kissing din lips dinshi amma bai mayar mata da martani ba, dauke bakinta tayi daga kan nashi tana zumbura baki,

"Mantawa ma nayi nai kissing din bakinka bayan bani kadai ce dashi ba"

Nan dinma shirun yayi mata bai tanka ba amma acikin zuciyarshi dariya yake yi mata sakamakon abinda yaji ta fadi,

"Koda yake ya na iya, babu yanda zanyi dole haka zan daure.."

Bakinshi ta sake kamawa tafara kissing dinshi har na tsawon wani lokaci kafin ta sakeshi, duk wannan abun da tayi da fushi suka rabu dashi saboda yana jin haushin bata bishi ba amma ita sam bata so wannan tafiyar tashi ba domin jikinta yayi sanyi kwatankwacin irin sanyin da yayi ranar da Abubakar sadiq zai bar duniya....



*_Ummi Shatu_*

3 comments:

  1. Pls ki daure ki dinga mana.post da wuri. Allah ya Kara basira

    ReplyDelete
  2. Pls ki daure ki dinga mana.post da wuri. Allah ya Kara basira

    ReplyDelete